MAGANIN KURAJEN PIMPLES

SHARE πΏ
Kurajen fuska na pimples matsala ce da taddabi matasa Mata da maza musamman masu kananan shekaru wadan da suka fara balaga sabida samun canji daga sinadaran hormones.
Duk da kurajen fuska tana Kama Mata da maza , Amma Mata sunfi damuwa sabida za kaga har nikab suke sanyawa a fuskokin su saboda kar aga taβadin da kurajen suka yi musu a fuska.
Kurajen pimples ba a fuska kadai take fita ba suna fita a wadannan wuraren:
πΏ- Kirji
πΏ- gadon baya
πΏ- Cinya
πΏ- wuya
Abubuwan da suke taimaka wajen tunzura kurajen fuska:
π- Yawan cin Abu Mai maiko.
π- Amfani da mayukan da Basu dace da fatar jiki ba
π- Kwayoyin cuta
π- Shiga rana sosai
π- Wassu magunguna
Abinda ya kamata ayi domin kariyar yawaitar kurajen fuska da samun waraka sune:
1π- A rage amfani da abinci masu maiko diyawa.
2π- idan kuraje suka fito kada a yawaita tabawa.
3π- Idan zakai dogon waya kada ka daura wayar a fuskar ka kusada kurajen.
4π- A samu ruwan dumi a Masa lemon tsami a wanke fuska da shi a kalla so biyu a rana.
5π- Idan kurajen a kirji ko baya kada ayi amfani da matsesen kaya sabida samun iska.
6π- Za’a iya shafa zuma bayan dan mintuna a wanke da ruwan dumi.
Idan wadannan hanyoyin basuyi amfani ba a tuntubi ma’aikacin lafiya domin akoi magunguna da dama masu kashe kurajen pimples.
Dr-Nuraddeen katsina
08068962793