Health

MAGANIN KUMBURIN CIKI DA KUMA SANYI

TAMBAYA TA 1515


Assalamu alaikum malam ALLAH Ya kara maka kusanci da SHUGABAN HALITTA(S.A.W) bisa wannan gagarumin aiki da kake gudanarwa, ALLAH Ya kara karfin gwiwa. Malam ina bukatar a taimaka min da magunguna kamar haka:

  1. Ina Fama da yawan kumburin ciki duk lokacin da na ci abinci, ina da matukar son zama tare da alwala koyaushe amma wannan matsalar ta hana ni, domin cikin yakan kumbura ne kamar ganga, daga nan kuma sai hutu(tusa) ba kakkautawa.

2.Majina da mura wannan matsalar na kai kusan shekara 8 kenan da ita kuma na sha magunguna kala-kala amma ALLAH bai kawo warakar ba.

Duk lokacin da na gama cin abinci to na dinga kakin majina kenan tsawon lokaci, sannan idan ina karatun Qur’ani majinar ce ke tokare min makogwaro koyaushe murya ta ba ta fita yadda ya kamata yayin karatun, kuma malam har flasko na yi amfani da shi amma ban samu waraka ba.

Don ALLAH malam ka taimaka min ina mutukar bukatar hakan

Daga Munzali Ibrahim Mai aduwa.
Malam ka huta lafiya.

AMSA


Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuh.

Malam Munzali wannan Matsalar ta Kumburin ciki tana damun mutane da dama. Kuma hakan yana faruwa ne asanadiyyar Basur ko majinar ciki.

Daga cikin abubuwan da suke magance wannan matsalar akwai:

  • Man Jirjeer yana narkar da majinar ciki, yana kuma maganin Gas din dake taruwa cikin hanjin mutum. zaka iya shansa cokali guda acikin ruwan zafi rabin kofi. kullum da safe kafin kayi breakfast.

Sannan ka samu Man tafarnuwa ka rika cin abinci dashi. Insha Allahu shima zai magance maka matsaloli da dama kamar Sanyi, Mura, Kumburin ciki, Kumburin jiki, Ulcer (Gyambon ciki).

Ka rika cin abinci maras nauyi, ka guji kwanciya da zarar ka gama cikin abinci. har sai ka motsa jikinka sosai.

Man Jirjeer din nan zai narkar kuma ya fitar maka da duk majinar da take damunka. insha Allahu.

WALLAHU A’ALAM.

Dr-Nuraddeen katsina
08068962793

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button