Hausa Novels

LULLUƁIN BIRI – EPISODE 43

©️Halima h.z

Related Articles

43
Taraba Satate, Wurkum district, Late Alhaji Aminu Barkinɗo Residence.

tafkeken gida ne me irin ginin gidan sarauta, sai dai ginin irin na zamanin da ne bana yanzu ba, but an ɗan sabunta shi ba kamar yanda yake ainihinsa ba. ƙofar gidan na marigayi tsohon Hakimin Wurkum danƙare yake da jama’a kace ɗaurin auren wani babban mutum ake ko kuma za’a ƙara yin naɗin sarauta ne.
daga cikin rumfar tempol ɗin da akayi, Maudo ne zaune akan kujera yasha rawani yana amsar ta’aziyya daga bakunan mutane da dama, shine Babban ɗa a wurin marigayi Alhaji Aminu Barkinɗo, kuma shine wanda ya zauna a hannun mahaifiyar Hayyo a lokacin da ta na raye, domin shi tasa mahaifiyar ta rasu, kuma tun bayan rasuwar mahaifin nasu ya maye gurbin kujerar tasa har zuwa wannan ƙarni da muke ciki.

daga cikin gidan, ɗumbin mutane ne ƴan gaisuwa ke ta hada-hadar shige da fice a ƙaton tsarkargidan da yay kusan filoti guda, kana kallon yanda aka kakkasa ɓangare ɓangare zaka san family house ne.
wata farar tsohuwa tukuf ta fito daga wani ɗaki tana dogara sanda, sai da suka ƙaraso tsakiyan tsakargidan sannan ta tsaya tana kallon mai yi mata hidima wadda ke biye da ita a baya tun fitowarta, hannunta riƙe da ƙwaryar fura babba, ita ɗaya ta rage acikin matan Alhaji Aminu Barkinɗo, cikin su uku da ya aura ita ɗaya tayi tsawo rai haka.

cikin yaren fulatanci tace da Hadimar,”ki nemo Gaji ki basa furan ya kaiwa Dottijo, tun ɗazu ya aiko Manga kuma ba’a samu an kai masa ba, kuma ƙila zai sha tare da baƙi ne, yi maza du Allah”.
Hadimar ta wuce da sauri tabi dogon soron da zai kai ka wani babban fili kafin ka fita zuwa waje.

Dada ta waiga tana kallon masu fitowa daga ɓangaren Hakimi, ta ƙwala kiran,”Munyoɗo”. sai da ta kira sau biyu tukunna wata farar dattijuwa ta fito da sauri tana amsawa, tazo gabanta ta rissina tana faɗin,”Dada gani, lafiya kika fito ke ɗaya?, kuma kin tsaya ai a rana, me kike da buƙata?, ina Petel din?”.
tai maganar tana kamata ta matsar da ita daga cikin ranar.

ta kalleta ta cikin glass ɗinta tace,”ina wannan shike, amnn mata na wurin Hayyo?”.
Munyoɗo tace,”wacce daga ciki Dada?”.
Dada ta ɗan ɓata fuska da muryar ƙorafi tace,”wannan yaro dai Allah ya jiƙan shi kawai, du yaje ya haɗo mata da yawa in ka tashi neman ɗaya sai kayi ta faman kwatance”. tayi tsaki sai kuma tace,”wasu sun ƙara zuwa ne?”.

Munyoɗo tace,”ai Dada jiya duk sun gama zuwa, su bakwai ne yanzu sauran huɗun ance sun rasu, suna babban parlo yanzu haka”.
Dada ta girgiza kai alamar Allah ya kyauta sannan tace,”to wannan Balarabiyar za ki kirawo min”.
Munyoɗo tace,”tom Dada bari na duba”.
ta faɗa tana juyawa ta nufi ɓangaren da yake nanne na mahaifiyar Hayyo, ta shiga babban parlon da ya tara ƴan zaman makoki, ta dinƙa wuce su har ta ƙetara inda Ammi da Ummi suke zaune tace da Ummi,”Dada tana kiranki”.

Ummi ta amsa da to tana yunƙurawa ta miƙe, Ammi ma ta miƙe tana faɗin,”kin san Allah na sha’afa gaba ɗaya Dada tana nemana”.
tare suka fito gaba ɗaya, suka tadda har an ajiyewa Dada kujera ta zauna akai, suna zuwa ta ɗaga sandar hannunta ta bugawa Ammi, Ammi ta kauce tana faɗin,”kiyi haƙuri baƙi ne suka tsayar da ni”.

Dada ta harareta ta cikin glass bata ce mata komai ba, ta mayar da dubanta ga Ummi dake tsugune a gabanta tace mata,”kije ki sako mayafinki mu wuce asibiti, ance tun shekaranjiya baki koma wurin yarinyar nan ba, ban sani ba ko isashshen hankali ne baki da shi”.
Ummi ta miƙe cikin sanyi jiki ta wuce, Dada ta kalla Ammi tace,”kije ɓangaren Giɗaɗo kice da matarsa ta bayar da ferfesun kaji da nace ayi, na santa da ɗan banzan cin yajin jaraba, idan ta san yayi yaji da yawa to ta zubar da shi ba mayu ne zasu sha ba, ta ɗora sabo na mara lafiya ne”.
har Ammi ta wuce sai kuma ta ƙara tsayar da ita,”kice da Belɗo ya fito da mota zai kai ni asibiti, yace da Safara’u taje ta haɗa min kayana a kawo min yau can ina kwana”.

tana tafiya sai ga wata hadima daga bangaren Modibbo ta fito, tayo wurin Dada da sauri tana zubewa tare da cewa,”Allah juttin balɗe ma, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana Dada, da akwai abunda kike buƙata ne ayi miki cikin gaggawa?”.

Dada ta dubeta tace,”a’a bana buƙatar komai”. Hadimar bata tashi ba ta cire takalmanta ta zauna akai ta shiga matsa ƙafafun Dada. lokacin maƙwabtansu suka shigo, da girmamawa matar ta tsuguna tana gaida Dada tare da ƙara yi mata ta’aziyya, Dadan ta amsa tana yi mata godiya sosai. matar tace mata tare da mijinta suke, Dada tace taje ta shigo da shi,ba jimawa sai gasu tare, suka gaisa da Dada wadda ke ta sanya masa albarka.

“Dada wajen kuma da zafin rana da kin koma daga ciki”.
tace da shi,”zanje dubo yaron Hayyo ne, zafin mutuwar uban ya taɓata tana can asibiti kwance rai hannun Allah, Belɗo nake jira yanzu zai fito”.
daga nan suka yi mata sallama suka wuce.

a ƙofar gida sanda su Ummi suka fito zasu tafi motar su Hajiya Ramla tayi parking, tun ranar ɗaya da suka zo suka koma sai yau suka dawo, Ummi ta ƙarasa wajensu tana yi musu barka da zuwa, su kuma suna ƙara yi mata ta’aziyya, Ummi tayi musu godiya sosai da sosai akan irin kyatatawarsu gare su.
Hajiya Madina da damuwa a tare da ita tace da Ummi,”to ya jikin Fillon?”. Ummi tace,”Alhamdulillahi da sauƙi, yanzu ma can zamu je, wataƙila ma dai zuwa dare su sallamota”.

Hajiya Madina ta kalla Hajiya Ramla tace,”to ko ni na bisu ne?”. Hajiya Ramla tace,”ah ki dai bari mu shiga muyi gaisuwan, idan muka fito tafiya sai mu biya ta can ɗin ko”.
Hajiya Madina tace,”to shikenan”. sai kuma tace da Ummi,”Me Babban suna yana nan ɗin ko yana can asibitin?”.
Ummi tace mata,”acan asibitin yake kwana ai, ya hana kansa natsuwa kwata-kwata, jiya ma nai ta fama da shi kan ya dawo gida ya huta yace min to, sai bayan su Lamiɗo sun dawo suke ce min yana can ɗin dai bai tafi ba, dan Allah Hajiya ku wuce da shi yau ɗin ya samu yaje ya huta shima”.

Hajiya Madina tayi ɗan jimm kamin tace,”to bari dai muga yanda za’ai, sai kun dawo”.
Ummi ta kira wani cikin jikokin gidan tace yaywa su Hajiya Ramla iso zuwa wajen Dadda wadda itace matar Maudo babban yayan su Hayyo hakimin yanzu kenan.

direct Taraba State Specialist Hospital motar su Dada ta nufa, a reception su Ummi suka tadda Kaka ita da ƙannan Hayyo da suke uba ɗaya su biyar, tare suka wuce ward ɗin da aka kwantar da Fillo, suna tafe Dada nata ƙorafin asibitin basu iya aikin komai ba, ace mutum kwanansa biyu yau amma shiru jiki babu sauƙin arziƙi, to ita dai idan jikarta bata sami lafiya yau ba to gobe ƙasar waje za’a fitar da ita ƙwararrun likita su dubata.

Belɗo dai sai bata haƙuri yake yana tayi shiru kar likitocin suji, in suka ji ba zasu ji daɗi ba, tayi masa banza bata saurare shi ba har suka iso room ɗin da Fillo ke kwance.
Ummi ta dakata daga ƙofar room ɗin bata shiga ba saboda nauyin sirikinta da take ji, tunda taga su Kaka a reception ta san shine zaune a wurinta.
Turaki ya miƙe cikin sauri daga gefen gadon a sanda su Dada suka shiga room ɗin, ba shi yake cutar ba amma kallo ɗaya zaka masa ka hango bala’in ramar da yayi, ga damuwa kamar a lakuta a fuskarsa, ya matsa daga gefen gadon yana yi musu sannu da zuwa.

Dada ta kallesa ta girgiza kai saboda tausayinsa taje,”sannu namijin ƙwarai, Allah ya baka ladan kulawa da matarka, ka kwantar da hankalinka zata sami lafiya insha’Allahu”.
ya kalli Fillo da ke ta bacci sannan yay ƙasa da kansa kamar zai yi kuka yace,”Allah ya amince”.
Kaka na kallonsa tace,”Me Babban suna ko zaka je gida kai wanka ka samu ka ɗan huta, rabonka da abinci ma tunda jiya da rana, dan Allah kaje kaci tunda likitan yace gobe da safe zasu sallame mu”.
da damuwa tsantsa a muryarsa yace,”Kaka ina so naga ta farka ne tukunna”.
Kaka ta gyaɗa kanta tace,”to Allah ya farkar da ita cikin ƙoshin lafiya”.

Dada ta zauna kan kujera tana fuskantar Fillo cike da jin tausayin yarinyar, sai adu’a take tayi mata a sanda ta kama hannunta ta riƙe, ta zaro wani diamond ring daga yatsanta ta saka ma Fillo, kuma sai ya zama kamar dama na Fillon ne, yay cif a yatsan nata.
kamar zata yi kuka ta dubi Kaka tace,”se yaushe ne zata farka ni kam?”.
Kaka ta kalli Turaki shi kuma ya kalli agogon hannunsa sannan yace,”nan da awa ɗaya insha’Allahu”.

Dada ta dubi Hadimar dake ta shigo da kayan abinci tana ajiyewa tace,”Uwar wannan yarinya shina waje ko?”.
Hadimar tace,”ehh ranki ya daɗe”.
ta gyaɗa kai tare da jan tsaki tace,”sam matar Hayyo uwar banza ce, kije kice da ita ta shigo ta yiwa ƴarta adu’a, ni ban sani ba ko ƙaunar ƴar ne bata yi”.
sai kuma ta hau bambami yi take kamar zata haɗiye kowa, da yake mafaɗaciya ta kata’i, sai da ƙyar Belɗo ya tausheta tayi shiru yace in bata so Fillo ta tashi to taci gaba da ɗaga murya sannan aka samu ta rufe baki.

Turaki ya kalla ƙofar ɗakin da Adda Asma ke shigowa, idonsa ya sauka akan gyalen Ummi da ya leƙo ta jikin ƙofar, ya juya ya ɗauki wayarsa dake kan drower ya fita cikin sanyi jiki kamar mara laka, ya sani in har yana cikin ɗakin Ummi ba zata taɓa shigowa ba, tun zuwansu asibitin sau ɗaya ta iya zama a ɗakin shima duk a takure kuma saboda shi, irin iyayen nanne masu bala’in jin kunyar sirikansu.

tana ganin fitowarsa ta matsa gefe, ya durƙusa har ƙasa ya gaida ita, sai ta kasa amsawa ta bisa da kallo tana tsananin jin tausayinsa, kwana uku rak amma ya dawo kamar shine mara lafiyar da aka kwantar, idon nan yay jawur ya ƙanƙance tsabar baya samun bacci.
ya katse shirun nata da cewa,”Ummi ki shiga daga ciki”.
tace,”a’a da ka koma kawai, ai ina jin ma yanzu zamu wuce”.
yace,”a’a Ummi ki shiga”.

sai ta ƙara kallonsa tace,”ya kamata ka huta haka”.
yay shiru bai iya cewa komai ba, kowa nata ce masa ya huta ya huta, ta ina zai iya hutawa alhalin Fulaninsa na cikin wannan halin.
Ummi tace,”baka ce komai ba”.
yace,”tom Ummi”. ya amsa ba dan yana jin zai iya aiwatar da abinda tace ɗin ba.

Ummi na shiga room ɗin likita yazo, Turaki ya tsaya daga jikin window yana sauraron bayanin da Dr ɗin ke yi.
“karku damu allurar bacci ce muka yi mata domin ta samu ta huta yanda ya kamata, ta yacca ba za’a samu damuwa ba idan ta farka, saboda gaskiya tana buƙatar hutu shisa ku ka kalla an ɗau tsayin wannan kwanakin bata farka ba, amma insha’Allah in the next 50minutes zata farka kuma lafiya lau da izinin Allah”.
duk suka amsa da amin, shi kuma ya ƙara da cewa,”sai dai akwai abinda ya kamata a kula da shi, kamar yanda na faɗa muku tunda farko ta samu heart failure, dan haka ya zama dole a kiyaye duk wani abu da zai iya zama damuwa a gareta, ai ƙoƙarin kiyaye ɓacin ranta sosai, ko stressing kanta da yawa kar ake bari tana yi, zan ƙara nanata muku duk wani abu da zai zamar mata damuwa ko ya sanyata ɓacin rai ko ya haifar mata da fushi to ya zama dole a kiyaye shi in har kuna sonta da ranta”.

da sauri Dada tace,”insha’Allahu za’a kiyaye hakan, baza ma mu bari ranta ya ɓaci ba balle kuma damuwa, ai ƴar gata ce gaba da baya, fatanmu dai Allah ya tashi kafaɗunta lafiya lafiya”.
Dr ya dubi ƴan dubiyan da ke ta shigowa ɗakin, da kuma hayaniyar waɗanda yake ji daga waje, ya sauke numfashi yace,”amm ya kamata a bata space dan wannan hayaniyar ma zata iya zamar mata matsala, da za’ai haƙuri ma ƴan dubiyan su dakata har zuwa ta farka”.
Dada ta ama masa”to shikenan yanzu kowa zai wuce kam”.

ya ɗauko wata takarda acikin file ɗinsa ya miƙawa Bobbo wanda ya dawo daga pharmacy siyo magunguna, Bobbo ya karɓa ya karanta sannan ya miƙawa Lamiɗo shi kuma yabi bayan likitan zuwa office ɗinsa.
asibiti dai sai ya zama kamar gidan biki, dan cikin lokaci ɗaya ya ɗinke da ƴan dubiya waɗanda suke zuwa gaisuwa a shaida musu ƴar Hayyo na kwance a asibiti to duk sai suyo asibitin, kace wata ƴar ƙusan ce ke kwance dan manyan mutane ma sai zuwa dubata suke, a shiga a fita a shiga a fita haka aka dinƙa yi.
irin karramammun mutanen da ke wajen in akace maka ƴan’uwan Hayyo ne sai mutum ya ƙaryata, zaka sha mamaki matuƙa in akace mutum me wannan gatan ne ya tsiyatar da rayuwarsa a iska.

ba’a sami sasaucin mutane a asibitin ba sai ƙarfe sha ɗaya da rabi, shima kuma saboda Dada ta koma gida ne, dan tana ta waya tana cewa a bar mutane su daina zuwa haka, Dottijo yace mata ai duk wanda aka hana sai yace a’a sai yazo ya nan asibitin yay mata ta’aziyya, sannan Dada taga tafiyar tata is the solution saboda Dr na ta complain akan hayaniyar da ake samu.
ƙarfe sha biyu dai-dai Fillo ta farka, motsin hannunta dake cikin na Turaki shi ya ankarar da shi, take yaja wani wawan ajiyar zuciya ya sauke tare da faɗin Alhamdulillah.
Fillo ta shiga buɗe idanuwanta a hankali ta sauke su akan Turaki da ya ƙura mata ido yana sakar mata murmushi me haɗe da damuwa.

tana jan numfashi a hankali tace,”ruwa”. da ƙyar ya iya sakin hannunta yaje ya ɓare carton ɗin faro ya ɗauko ɗaya ya dawo, ya zuba a cup sannan ya ɗagota ya bata tasha, sai da ta shanye tass sannan ya ajiye cup ɗin.
ya sanya mata pillow daga bayanta ya jinginar da ita, ita kuma ta shiga bin ɗakin da kallo, daki daki kuma abinda ya faru da ita ya dinƙa dawo mata.

abinda zata iya tunawa shine Abbanta ya mutu, kuma har an kwana anyi masa wanka za’a fita da shi ai masa sallah a kaishi, to tunda aka fitar da gawar ba zata ce ta ƙara sanin inda kanta yake ba sai a yanzu da ta farka ta ganta a asibiti.
Turaki ya dinƙa kallonta yana jin kamar zai yi kuka, duk ta zabge tai wani muguwar rama, ƙasusuwanta kamar sayi magana, haka idonta yayo waje ya ƙara ƙwalele kace idon aljanu. ya kama karan hancinsa yana rumtse idonsa, hoton wancan ranar ya dinƙa haska masa, sanda aljanun Fillo suka tashi ta dinƙa bige bige, tun ana iya samu a riƙeta a danneta har ta kai ga hakan ya gagari kowa, sai ƙyaleta akayi tana ta murginawa akan duwatsun compound tana ta ife-ife, ƙarar ihu kuwa har na bakin titi zai iya cewa yaji, kuma sanda aka kira wani malamin ruƙiyya yazo me mamakon a sami sauƙi sai gida ya kacame da masu aljanu, ƙannan Hayyo da Yayyansa da jikoki wancan ta faɗi waccan ta kwasa da gudu waccan ta shaƙe na kusa da ita, haka akaita fama da su, ƙarshe sai da aka tara Malaman Ruƙiyya har biyar a gidan sannan aka sami lafiya, ashe aljanun nasu duk na gado ne na kan Kakarsu wadda ta haifi mahaifin su Hayyo, ita kuma Fillo har da waɗanda ta samu acikin dajin nan sanda da ta ɗauke asirin ɗakin Turaki.

tasha buƙar wuya sosai dan duk jikinta sai da ya farfashe, fuskarta tai ta jini saboda burgimar da tayi akan duwatsu compound ɗinsu. wan mahaifin su Hayyo da suke kira da Dottijo shi ya kira waya yace idan an kaishi to a tattaro a dawo nan gida aci gaba da zaman adu’a kuma, aka shaida masa halin da ake ciki na tashe-tashen aljanun, yace to suyi gaggawar tahowa nan ɗin saboda a samu ai masu magani tunda dama akwai babban malamin da suke da shi acan wanda ke kula da matsalar tasu tunma mahaifiyar tasu na da rai.

aiko dai Fillo tasha baƙar wuya, dan Malamin da yay mata ruƙiyya azababbe ne, bai ƙyale Fillo ba a wannan ranar sai da ya ƙona aljanun da suka shigeta na asirin da ta ɗauke, na gadon ne kawai masu shegen taurin kan bala’i da suka ƙi fita, suka ce su ai suna tare da ita ne saboda bata kariya, yinin ranar curr akanta akai ta fama, kuma sai ya zaman in an samu na waɗancan sun lafa da sun jiyo ihunta sai su ƙara tashi, ƙarshe ita sai ɗauketa akayi aka kaita can gidan Malamin, duk wanda yaga halin da take ciki kuwa sai yayi mata hawaye.

kuma hankula sai suka ƙara tashi a sanda aljanun nata suka lafa, dan tun ana tsammanin baccin wahala take har abin yazo yafi ƙarfin wannan tunanin, cikin gaggawa aka tafi da ita asibiti lokacin Ummi har ta saddaqar itama ta rasu, bama ita ɗaya ba da dama sun zaci ta mutu, sai da likita ya fito yake shaida musu tana raye tayi dogon suma ne sai dai ba’a san ranar farkawarta ba.

sai da Dottijo yayi magana sannan aka ragu a asibitin dan da kowa ya tare acan, yace a bar Kaka da su Adda Asma su zauna tare da ita, sai hadiman ɓangaren Jagarɗo su biyar da suke tare, aka barsu su goma suke kwana a wajenta, sai Turaki da yaƙi tafiya ya kafa ya tsare ko su Kakan baya bari su kwana a ɗakin sai shi, ya kwana da ita ya yini da ita baya ko matsawa daga kusa da ita.

Fillo ta ɗago ido ta kalli Turaki, cikin raunin murya dake ƙoƙarin ɓallewa da kuka tace,”da gaske mutuwa ta rabani da Abbana?”.
Turaki bai iya ce mata komai ya ƙara damƙe hannunta a nasa, nan da nan sai ga hawaye nan zirrr kamar an kunna famfo, ba shiri Turaki ya bar kan kujerar da yake ya hayo gefen gadon ya tattarota jikinsa gaba ɗaya ya shiga lallashinta, ya dinƙa shafa bayanta tamkar jaririya yana faɗa mata kalamai tausasa na kwantar da hankali da sa natsuwa a zuciya, haka har ta daina kukan sannan ta zame daga jikinsa tace,”ina Ummi na?”.

yace,”Ummi taje gida ita da su Kaka yanzu zata dawo”.
tai ƙoƙarin zame hannunta daga nasa ya hana hakan, with much concern yace,”me kike so yanzu?”.
zata fara sabon kuka tace,”Abbana nake so, sai da ya fara sonmu shine mutuwa tazo ta ɗauke mana shi, kuma ni ina so na rayu tare da shi, ina so na sami wannan gata da kulawa da soyayya na mahaifi da ban samu ba, ina so nima na kyautata masa na sami lada, dan Allah kace ta dawo min da Abbana ina sonsa sosai bana so na rasa shi yanzu, albarkar da ya saka min sanda zai mutu bata isheni ba, tayi min kaɗan”.

idanuwan Turaki suka kawo ruwa calmly yace da ita,”kin tabbatar kina son Abba?”. tayi saurin ɗaga masa kai, yace,”to indai kina sonsa ki nuna masa hakan ta hanyar yi masa adu’a ko da yaushe, itace abar da yafi buƙata daga gareki ba kuka ba, kuma ta hakan zai yarda da cewar kina sonsa, sai yay ta saka miki albarka daga can”.
ya ɗago haɓarta yana kallon cikin idonta yace,”Fulani nah wanda ya mutu baya dawowa, Abba ya tafi tafiyar da ba zai ƙara dawowa garemu ba sai dai muje mu same shi a aljannah a yayinda muma muka zama tarihi, dan haka ki daina kuka kinji Fulani nah, idan Abba ya tafi kina da ni, ni zan maye miki gurbin Abbanki, zan baki wannan gatan da kike buƙata, zan baki kwatankwacin irin wannan kulawar da kike biɗa, uba dabanne ba zance zan baki soyayya irin tasa ba, amma zan baki soyayya irin wacca ba zaki yi maraici ba”.

Fillo ta janye hannunsa daga haɓarta ta faɗa jikinsa ta kewaye shi da duka hannayenta, tayi ta kukanta a hankali a hankali yana jin hawayenta na sauka a bayansa masu ɗumi, hawayen da yake jin zafinsu kamar garwashi, bai hanata ba har sai da tayi me isarta tukunna ya janyeta yana tambayarta me take son ci.
kanta na ƙasa tace,”bakina babu daɗi”.
“daurewa za kiyi, kinga cikinki babu komai, idan baki ci abinci ba Ummi zata shiga damuwa”.

ya sauka akan gadon yaje ya buɗe duka coolers na abincin kusan guda goma yace,”look here”.
ta ɗago ido tana kallon coolers ɗin abincin da mamaki, kamar abincin da sarki ya biɗi a kawo masa, kowanne kuma babu na yarwa, yaga idonta ya manne akan cooler ɗin ferfesun kayan ciki, sai yabi duk ya rufe sauran sannan ya ɗauko plate ya zuba kayan cikin da yaji ganyen zogala aciki, yazo ya ajiye akan table ya rufe.

ya dawo bakin gadon ya kamo hannayenta yace,”muje ki wanke baki”. tana kallon babban yatsanta tace,”ya akayi naji wancan ciwon?”.
ya ɗan rufe idonsa yaja numfashi sannan yace,”kin manta?”. ta ɗaga masa kai, yace,”ok to zo muje mu dawo sai in tuna miki”.
yay helping ɗinta ta sauko akan gadon suka wuce toilet, shi ya shiga ciki ya tatsa macline ajikin sabon tooth brush sannan ya fito ita kuma ta shiga, after 4minutes ta fito tana yamutsa fuska saboda jikinta da take jin duk gaɓɓanta na mata ciwo, yana kallon fuskarta ya san alwala tayi, ganin ƙafar ma janta take yi yace,”ko in ɗauke ki?”.

tayi saurin girgiza masa kai alaman a’a,dan haka ya kama hannunta suka tafi a hankali har kan gadon, babu yanda bata yi ba akan ya barta taci ferfesun da kanta san yaƙi, shi ya dinƙa bata har sai da ta cinye shi akan dagewar da yay tukunna ya aje plate ɗin.
kusan duk abinda aka ajiye a wurin nan sai da ya dinƙa ɗiba yana bata ko da 1 spoon tayi sai ya haƙura, ya ɓalle murfin hollandia shima ya zuba a cup, ta dinƙa sha da kaɗan kaɗan. yana cikin bata ne wayarsa ta shiga ringing, ƙwayar idon Fillo ta sauka akan sunan me kiran, ta ɗago ta kallesa sau ɗaya, ta kauda fuska daga cup ɗin da yake kawowa bakinta, bata san me yasa ba ta tsinci zuciyarta na yi mata wani irin zafi, kawai sai ta koma ta kwanta ta juya masa baya tana zura duka yatsunta a baki tare da rumtse idonta.

ya aje cup ɗin hankalinsa tashe ya shiga tambayarta menene, ya kai hannu zai shafa fuskarta ta ma-ke hannun tana janyo top ɗin rigarsa dake aje a gefen gadon ta rufe fuskarta, ya dinƙa kallonta a ruɗe yana jin kamar bai san yanda zai yi ya lallasheta ba.
a karo na uku wayarsa ta kuma yin ringing, yaja gajeran tsaki ya ɗaga wayan ransa babu daɗi, yay shiru ba tare da yace komai ba, sallamar ma a ciki ya amsa.

daga ɓangaren Ilham tace da shi,”Hammah mun dawo”.
tayi maganar da sauti me bala’in ban tausayi. jin yay shiru ta sake cewa,”Hammah”.
sai da ya taushi zuciyarsa sannan yace,”kun dawo lafiya?”. tace,”lafiya lau”. yace,”ya me jikin?”. ta fashe da kuka tace,”ba sauƙi, har gwanda ma Mami ta mutu akan halin da take ciki”.
yace,”Allah bada lafiya, ina abu ne yanzu”. yana faɗar hakan ya katse kiran ya mayar da hankalinsa kan Fillo, duk yabi ya rikice da sheƙar kukanta da yake ji na fita a hankali, yay ƙoƙarin ɗagota taƙi bari sai da ya shiga roƙonta kamar ƙaramin yaro sannan ta yarda ta miƙe zaune.

yaga uban hawaye duk sun wanke mata fuska, ya zare yatsun nata daga bakinta, daidai da kukan da ta ɓoye ya samu ƴancin fitowa, hankalinsa ya kai ƙololuwar tashi ya rungumeta yana cewa,”da kin san irin azabar da nake ji da zubar hawayenki, da kin tausaya min kin ƙara taimakona a karo na biyu, na roƙe ki dan Allah dan Annabi ki daina kar hakan yaywa zuciyarki dake cikin ƙirjina illa”.
ta janye a jikinsa ta kallesa tace,”dan Allah”. yace,”dan Allah what?, me kike so nayi miki? faɗi duk abunda kike so Fulani nah am ready to do it”.
tai ƙoƙarin dakatar da kukan tace,”ka sakeni dan Allah”.
sai ya ƙame ƙam kamar wanda aka dannawa remote, ya zareta daga jikinsa, kallonta kawai yake da wani irin yanayi da shi ɗaya ya san me yake ji, in har da tasan wannan kalmar ta saki abinda take haifar masa da ba zata dinƙa faɗarta ba, to amma bai san ta yanda zai yi ya fahimtar da ita hakan ba, kuma yanzu lallaɓata yake ita da lafiyarta shiyasa ba zai yi amfani da fushinsa wurin nuna mata cewar baya so ba.

ta ƙara cewa,”in kana ƙaunar Allah da Annabi ka sakeni, ni ba zan iya zama da kai ba”. ta faɗa tana kuka sosai.
ya sauke doguwar ajiyar zuciya yana furzar da iska daga baki sannan yace,”idan ban sake ki ba zaki mutu?”.
ta ɗago kumburarrun idanuwanta tace,”ni ban sani ba amma dai zan cutu”.
idanuwansa cikin nata kamar yanda nata ke cikin nasa ya kama hannunta ya ɗora a saitin zuciyarsa yace,”to ni muddin na sakeki wallahi mutuwa zanyi, so please karki ƙara faɗin haka i beg you”.

ta dinƙa masa kuka Turaki ya rasa inda zai tsoma ransa, ƙiris shima yake jira yasa kukan, ga kiran wayar Boɗejo sai shigowa yake yi, yay banza da kiran yaƙi ɗagawa.
sai da kiran Baffa ya shigo sannan yay picking, kuma yana ɗagawa abinda Baffa yace da shi yasa shi damƙar hannun Fillo ba shiri.
Baffa ya kashe wayarsa ransa a ɓace, Boɗejo na tsaye akansa sai zazzaga bala’i take yi.
Turaki yay calling lambar Maama, ko da ta ɗaga daga muryarsa ta shaida ɓacin ran dake danƙare a xuciyarsa, tace,”lafiya me babban suna?, ba damuwa naji a muryarka ba illa zallar ɓacin rai, mene ya faru?, kai da wa?”.
ya rumtse ido yace,”Maama Baffa ne ya kirani”.
“yace maka me?”.
kamar zai yi kuka yace,”wai na koma yanzu Ilham ta dawo, Maama…”.
bai ƙarasa ba tace da shi,”baka ce masa mahaifin matarka ne ya rasu ba?”.
yace,”Maama to ba ya sani ba, ina jiyo muryar Boɗejo nata hayagaga”.
tai tsakin takaici tace,”kayi haƙuri me babban suna, kashe wayar ga shi yana kirana, i will call you letter”.
Turaki ya kashe wayar yana kallon Fillo dake ta kokawa da shi tun ɗazu tana so ta sauka daga kan gadon shi kuma ya hanata.

“da me kike so naji wai?”.
ta kifa kanta a ƙirjinsa tana ƙara faɗin,”dan Allah ka sakeni ni bana sonka”.
yace,”naji, yanzu dai ki yi shirun zan yi abinda kike so”.
tai shirun tana ɗagowa ta kallesa tace,”yanzu ai nake so, ni ka sakeni yanzu sai. kayi tafiyarka can ɗin”.
yace,”ehh zanyi amma idan kin yarda kin bini munje gida tare, zan miki abinda kike so a daren yau gobe sai da safe sai na dawo da ke”.

yana faɗar hakan tasa hannunta da iya ɗan ƙarfinta ta ture shi ta fita daga ɗakin, a ƙofar ɗakin ta sami Kaka zaune akan kujera ta faɗa jikinta tana fashewa da sabon kuka.

Vote, Comment and Share.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button