KE ALHERI CE HAUSA NOVEL

BIEBEE ISA
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION(NWA)
Pg1⃣
KATSINA
Duk wanda ya san Jami’ar Umaru Musa Yaradua dake garin Katsina yasan wajen gari take, a k’alla ba a kasara ba tafiyar minti arba’in da biyar (45) ne zuwa cikin gari.
Daliban aji d’aya, na (Department of MicroBiology) ne suka fito a gajiye daga aji misalin karfe shidda da minti biyar (6:05) na yamma kasancewar sunyi lectures 4-6.
Mimi tayi wujiga-wujiga don tsabar gajiya, ta kalli kawayenta biyu tace
“Wayyo Allah! da alamun zamu kwana a Hostel yau, ji yanda garin ya hade rai, ko dai ruwa zaayi?”
Usheey cikin damuwa tace “kai! dole captain ya nema mana sauki gun lecturer nan, a yi rescheduling lectures din, ko wednessdays ne da safe, don bala’i 4-6 ran saturday?”
Dayar me sanye da nikaf tace
“Don Allah ku mu daga kafa, kar su cike bus din, kun dai san mazan nan ba hakuri zasu yi ba, balle yanda suka ga hadarin nan kowa so yake ya tafi gida.” Miemee tace “nikam i dont have dat strength.”
Usheey tace “aikam tafiyarmu zamu yi mu bar ki, suka cigaba da tafiya.
Mai sanye da nikaf din tace “laahhh! kun gani ko, school bus2 sun tafi.” Miemee tace “wallahi kina da damuwa, mu kadai ki ka ga bus din ta bari?”
Mai nikaf din ta dauke kai don tasan da ta sake bude baki tana iya fashewa da kuka. Usheey tace
“Ai ke Mimi ko karfe nawa zamu kai na san ko a jikin ki.”
Daga nan ba wacce ta kara magana, ko da suka karasa Student center duhu ya fara yi, kuma matan da ke gurin daidaiku ne, wasu an basu lift. Miemee tace “ko mu zauna a kujerun SUG kafin bus ta dawo?”a Usheey tace “chap sabod gamu gantaIallu ko?”
Dayar tace “to ya zamu yi? ko mu karasa gate kila mu samu ko commercial a chan?”
Mimi tace “chap wallahi bazan iya tafiyar minti ashirin ba.”
Usheey tace “toh bari mu barki nan.”
Tafiya su ka fara yi miemee tace “bala’i wlh ba za ku barni nan ba, ta bi bayan su da sauri. Tafiya su ke yi suna fira jefi-jefi, dare kam har ya fara yi ga hadari ya kara haduwa, Agogon wayar ta karfe7 saura minti 15, Idon mai nikaf ya ciko da hawaye, tsiraran motoci suke wucewa, miemee tace “wlh a ruwa muke, dama mu samu lift. Usheey tace “eh wlh”.
Ba su rufe baki ba sai ga wata bakar mota mai bakin gilashi ta danno a guje, har ta dan gifta su, sai kuma motar ta fara dawo da baya da baya. Miemee tayi saurin gyara zaman rigarta, tace “yauwa ai nasan na annabi ba sa karewa, ga lift nan na zuwa” usheey tace “Barkan mu Allah ya takaita mana wahala ba sai mun je gate ba” me nikaf cike da mamakin kawayenta tace “yanzu motar nan mai tint zaku shiga? Kuna jin sauti na tashi kamar ba dare ba?” Usheey da miemee suka buga tsaki a tare, Usheey tace “kinga dai Besty idan muka bar motar nan ta tafi, ba mu san lokacin tafiyar mu gida ba, daga cikin makaranta ta fito balle mu ce sace mu za ayi, ” Miemee cikeda takaici tace “Abu mai sauki, idan ba ta shiga sai mu yi tafiyar mu mu barta nan” kafin tace wani abu motar nan ta iso ta tsaya daidai su.