Hausa Novels

kalaman yabon budurwa

Abar sona abar sona,
Abar ƙauna abar ƙauna,
Abar marari a rayina,
Yau ga ni da so cikar ƙauna,
Cikar buri cikar komai.

Related Articles

Gare ki masoyiya tawa,
Ki ji ni da zantukan baiwa,
Na ƙaunar nan da ba tsaiwa,
Cikin mararin cikar sowa,
Na bayyana baitukan so dai.

Idan na gane ki don ƙauna,
Na manta abin da ke raina,
Cikar buri ki zo guna,
Ki amshi buƙatuna,
Ki share min duhun komai.

Ranar wanka Bahaushe de,
Ya ce cibi waje buɗe,
Nufinsa a wangame buɗe,
Kowa ya gano ido buɗe,
A san shi a san kalar komai.

Kin san so ba a mai yarfe,
Ba a ƙyamar tuwon safe,
Zoben so ba a sa ƙarfe,
Burina na tattaro lefe,
Na kai ki garin da ba kome.

Kin san so ba a mai kulle,
Gararinsa yawa na ‘yan talle,
Shuhurarsa a zuciya zille,
A ganta a fuska ba kyalle,
A san ya zarce duk komai.

Idan na taho a motata,
Cikin tafiya ta ƙasaita,
Idan na gane ki ‘yar auta,
Kina tafiya ta ƙasaita,
Na manta batu na tukin dai.

Kalarki daban a mataye,
Sunanki daban na ‘yar yaye,
Sautinki daban a Karaye,
A soyayya ana maye,
A sonki ko za na yo komai.

Naman da ake kira soye,
A cakuɗa kafi zabaye,
A sa naman a sa maye,
A sa gishiri a yo soye,
A so haka duk ake komai.

Maimaita aji fa sai dolo,
A so kam ba a son gwalo,
Ba a kome cikin salo,
Jifa kam sai da ɗan kwallo,
A so ba a barin komai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button