
🌈 IDAN BA KE 🌈
True Life story
Nimcyluv sarauta
Arewabooks@Nimcyluv
1.
Jimeta/Yola
Njoɓoli Rugar Rome
Gudu Saniyar take tana bin ta a baya itama, hannunta riƙe da sanda na korar Nagge, tamkar wanda suke wasan tsere haka Saniyar ke gudu a cikin jejin ita ma bata fasa bin ta ba, sauran Naggen suna gefe guda ko wacce na cin ciyayi wanda bisa kuskure tana can tana bin Saniya ɗaya tilo, sauran Naggen suka faɗa cikin gonar wani manomi, a yunwace suka rufarwa albarkatun gonar. Cikin siririyar muryarta mai nuni da Yarintar ta, da kuma nuna cewa ita ɗin zallar bafullatanar Yola ce ƴar Usul. “Waru! Waru! Waru” shi ne abin da yarinyar ke ta nanatawa cikin hausarta ta Fulani, yayinda Saniyar tuni tai mata nisa cikin gajiya wa da bin Saniyar ta tsaya a wajan wata gaɓar ruwa tana riƙe ƙugunta ta ce “Bone, lalashewa ta samu Nagge Aradu” da sauri kuma ta ɗauki sandar tana ƙara yin kan Saniyar ganin ta tsaya da gudun da take, cikin sa’a ta cimmata tana zuwa ta kama ƙahonta tare da ƙifƙifta idanunta alamar zallar fitsarar dake tattare da ita “d’ume ngid’d’a?” Ma’ana “me kake so?” Kallon ta Saniyar ta yi sai kuma ta kaɗa jela tare da zubewa a wajan ta shiga shura ƙafafuwa kamar zata mutu, cikin tsoro haɗi da razani HALISA ta ce “Jomirawo ka taimakeni” ta faɗa tana kallon Saniyar wacce tai male-male a ƙasa ga wani ruwa mai kama da jini na fitowa ta ƙasanta, kuka Halisa ta sanya domin idan Saniyar ta mutu a nan wajan ta shiga uku, itama watan mutuwarta ya kama. Tsayar da kukan tai kafin ta fara duba cikin jeji babu kowa sai ita, ga wani kwantaccen baƙin hadari dake ƙasa wanda a koda yaushe zai iya tashi.
Juyawa tayi ta nufi wajan wata bishiya inda ta hangi ƙaramar igiya a jiki, tana zuwa jikin bishiyar ta zame hular Fulanin dake kanta, nan da nan sumar kanta ta sauka wacce take jajir babu alamar baƙi ko ɗaya, gashin ba wani cika ne dashi ba, kawai tsayin gashi gareta, domin har fatar tsakiyar kanta ana iya ganowa. cikin sayin jikinta ta fara jan igiyar tana ƙoƙarin kunce igiyar gaba ɗaya daga jikin reshen bishiyar, kamar daga sama taji saukar wani abu mai sanyin gaske zuwa kafaɗunta. Cak ta tsaya tana sauraren yadda abin ke tafiya sululuuuu a jikinta har ya gama sauka, hannunta ta miƙa da nufin kama abin da ya sakko mata domin bata da tsoro ko kaɗan, cikin rashin sa’a hannunta ya sauka saman ƙaton kan maciji wanda yake kwance a jikinta, wani santsi-santsi ta ji a jikin macijin ga wani sanyi sosai dake ratsa fatar jikinta, bata gama yadda da abin da zuciyarta ke ayyana mata ba, a hankali ta juya wani ihu ta kurma wanda ya yi daidai da ɗaukewar numfashinta, baya tayi zata faɗi kafin ta kai zuwa ƙasa macijin ya yi wata girgiza cikin sakanni ya juye zuwa wani saurayi wanda jikinsa ya ke sanye da wasu haɗaɗɗun kayan sarauta na farin saƙi, fari ne tas amma kamar Fatar mace haka fatar hannunsa da sauran jikinsa suke gaba ɗaya gashi ya kwanta luff. Zubewa ya yi a ƙasa ta faɗo jikinsa idanunsa a kan fuskarta, ya jima yana kallonta kafin cikin izza da nutsuwa ya ce “kin tsoratani, kin tsorata kanki Danejo, banyi niyyar zuwar maki ba yanzu” Danejo sunan da ƴan rugar Rome suke faɗawa Halisa ke nan. Sai da ya gama Kallon ta sosai, kallon da ya jima bai mata ba tun tana zanin goyo matsayin Jaririya. Ɗaukanta ya yi ya nufi inda Naggen suke yana zuwa ya tarar da wannan Saniyar dake Shure Shure ta haihu, ashe daman ciwon haihuwa ke damunta. Halisa ya kalla yana sakin Murmushi kafin ya zaro harshesa waje sai ga wani zobe ya bayyana, cikin sauri ya saka mata zoben mai ɗauke da tambarin wata masarauta, kafin ya yi Girgiza sai ga shi ya sauya kama, kamarsa a fuska na nan, amma kayan jikinsa sun sauya sun koma irin kayan Fulani sak komai da komai, goya Danejo ya yi a bayansa, ya ɗauki jaririn Saniyar cikin nutsuwa ya fara kaɗa Naggen zuwa Rugar Rome. Kamar ƙifatawar idanu haka ya ƙaraso Rugar..
Iskar dake kaɗawa na alamar tashin hadarin ya sanya matashin ɗaga kansa sama, yana kallon yadda gajimare ke haɗa kansa. A nutse kuma ya fara bin Rugar Rome da kallo ba wata babba bace, amma Ubangiji ya albarkaci rugar da dabbobi musamman Nagge, gasu manyan gwanin sha’awa yawancinsu jajaye ne kafin ka samu farar saniya zaka daɗe. Wasu sun dawo daka kiwo wasu kuma na hanya sbd rashin yawaitar mutane da babu a rugar, daidai wajan wata bukka ya Ƙarasa yana gyara riƙon da ya yi wa Jaririyar Saniyar kafin ya ce “Sannunmu dai” ya faɗa a taushashe jin shiru ya sanya ya ƙara buɗe muryarsa mai sanyi ya ce “Afuwanku dai” daga cikin bukkar wata ƙaramar murya ta amsa da faɗin “Waye nan?” Ta faɗi hakan tana fitowa, lokacin da Idanunta ya sauka acikin ƙwayar matashin gabanta taji ya faɗi saboda yadda taga ƙwayar idanunsa, gane cewa kamar ta tsorata da yanayinsa ya sanya ya lumshe idanunsa kaɗan tare da buɗewa ya ce “Ga ɗan uwanki na kawo shi, arado bashi da lafiya ne can na ganosa yashe a jeji ba rai, har naggenku ya samu zuri’a” yana faɗin hakan ya ajjiye Jaririyar Saniyar a ƙasa wacce take jajir da ita Kuma ƙatuwa. Shatu dai binsa take da Idanunta domin bata taɓa ganin mai kama dashi a rugar ba sai yau, kallon da yaga yai yawa ne yasa ya ce “Shai a mata magani” a hankali ya sauke Halisa Dajeno ya kwantar a ƙasa a nan gaban bukkar kamar zai juya ya tafi sai kuma ya ƙurawa zoben hannunta idanu wanda yake sheƙi sosai ga tambarin masarauta nan ya fito sosai a jikinsa, a ransa yake ji kamar bai dace daya mallaka mata wannan zoben ba, amma bashi da wani zaɓi dole ya bata ta haka ne kawai zai lalubota a duk sanda ta ɓace masa, tun tana ciki yake fama da rainonta lokacin haihuwarta ne kawai bai sani ba.
Ba tare da ya ƙara cewa komai ba ya juya da sauri ya fara tafiya tare da shankwana, yana barin wajan ya ƙara yin girgiza wata iska mai daɗi da guguwa ta mamaye gaba ɗaya cikin Rugar Rome. Nan take ya koma asalin macijinsa kamar yadda ya bayyana a farko, yana iya komawa duk suffar da yaga dama cikin ƙaramin lokaci amma zama maciji yafi masa daɗi sbd yawaitar macije dake cikin jejin daya zagaye Rugar Rome, a haka ya sulale tare da komawa cikin jejin.
Iskar dake kaɗawa ce tai sanadiyyar farkawar Dajeno daga barcin dolen da macijin ya sanyata a ruɗe ta miƙe tana dafe kanta dake mata ciwo sosai cikin sanyin murya ta ce. “Miyyati Allah” Shatu dake gefen Dajeno tana ɗaure Naggen a garken dake dab da bukkar ta ce “Nassu, ka shigo” Shiru Danejo tai kamar zata tuna wani abu sai kuma tai saurin ware manyan idanunta ta ce “Shai Shatu ina Dadana ya tashi daga barci hoo?” Shatu ta ce “E, yana ta kiranka baka dawo ba, ciwonsa ya tashi yana ta masa zafi” da sauri Danejo ta faɗa cikin bukkar Idanunta ya sauka akan Dada (her mother) tana kwance a rufeta da wani farin zani jikinta sai rawa yake, fara ce matar sosai amma yanayin jikinta kamar ta shekara 60 nan kuma ba tafi shekaru 50 ba idan ma ta cika. “Shannu shannu Dadana” Idanu Dada ta buɗe da ƙyar ta ce “Zakiyi Albarka Halisa ki riƙe gaskiya da amana ki zama mai haƙuri ki daina saurin fushi da rashin kunya” Kallo juna sukai da Shatu da Halisa wacce akafi sani da Dajeno “Dada me yasa kake shaiwa haka?” Dada ta kalli Shatu kana ta juya ta kama Hannun Dajeno ta haɗa dana Shatu ta ce “Meyasa ba zance haka ba? Shatu kece ƙarama Halisa ita ce babba amma zafin zuciya ne da ita, rauninta akai na yake, kuma dole na tafi na barta” da sauri Shatu ta kalli Dada tana faɗin “Ina zaka Dada kuma?bayan Rugar Rome ina muke dashi” Dada ta numfasa ta ce “Babu da inda yafi wannan Rugar, zan tafi zuwa ga Mahaliccin daya samar da Rugar Romen, ciwon nan ba zai barni ba kuɗin amanata ce musamman ke Halisa” Dajeno kasa cewa komai tai sai ƙurawa Dada fararen idanunta da tayi zuciyarta cike da fargaba. “Dadana ba zaki mutu ba, idan kin mutu wa muke dashi a nan rugar wazai dinga kulawa damu?” Dajeno ta ƙare maganar cikin sanyin murya gaba ɗaya jikinta yai sanyi sosai. Shiru kawai Dada tai can kuma ta ce “Hamma Yabi ya dawo?” “A’a birni da nisa Dadana yace gobe zai kai ki can asibitin birnin”. Jinjina kai Dada tai Dajeno ta miƙe bayan ta ce Shatu ta kula da Dada yanzu zata wajan Sarkin ruga ta amso magani.
Cikin sanyin jikin nan nata take tafiya kanta a ƙasa domin bata fiya kallon mutane ba, a yadda jikin Danejo yake da sanyi zaka ɗauka babu ruwan ta, musamman da fuskarta yai kala dana salihai amma zafi da zuciya gareta, ga kuma taurin kai da naci akan abu, idan tace zatai to tabbas zatai, amma idan tace A’a babu wanda ya isa juyata ko Dada sai dai ta zuba mata Idanu. Abin birgewa ga rayuwar Halisa Dajeno tana da saurin yafiya, da kuma tausayi da kuma kawaici. Cikin tafiyar nutsuwa ta Ƙarasa gaban wata bukka wacce tafi ko wacce bukka kyau da girma a cikin Rugar Rome. “Shai shai Mene haka kamar makauniya ina kwaɗa miki shandan nan Aradu” da sauri Danejo ta ɗaga idanunta ta kalli Gwaggo Niyabi wacce ke zaune tana kaɗa audiga, murguɗa baki tai ba tare data ce komai ba, jin tai shiru yasa Gwaggo faɗin “Ko njid’ud’a?” “Magani za’a bawa Dadana” Gwaggo Niyabi ta ce “To baya nan” shiru tai kamar zatai Mgn sai kuma ta juya sai da tayi nisa kaɗan Gwaggo Niyabi ta ce “Yaka Dajeno waru” tsaye Dajeno tai domin ba shiri suke da Gwaggo ba, Murmushi Gwaggo tai sosai kafin ta numfasa ta ce “Idan kinje ki tambayi Dada waye mahaifinki, mene yasa daya rasu bata bar Rugar Rome ba, ta tafi danginta ko dangin mijinta” da mamaki Danejo ta ce “To bayan Baffa ya rasu mene na tambayarsa, ki daina maganar Uwayena” Gwaggo ta miƙe tana kallon Danejo “To ana gab da kurarku a Rugar Rome, domin bama son mara gurbi” harara Danejo ta watsa mata ta ce “Miyidi saro’am” ma’ana ina son iyayena “Kalleki mai ƙaton baki da ƙwalaƙwalan idanu” tana faɗin hakan ta kwasa da gudu zuwa bukkarsu.
Da ƙyar suka samu zazzaɓi Dada ya sauka tasha paracetamol sai 12 na dare ta samu barci. Shatu ma barci take kusa da Dada a hankali Danejo ta miƙe daga kwancan da take har yanzu fararen kayan Fulani ne sanye a jikinta, hula ta ɗauka ta rufe kanta a nutse ta fita daga cikin bukkar kai tsaye garken shanun dake dab da bukkar ta nufa, wanda aka kunna musu wuta tana ci kaɗan kaɗan. Gobe da sassafe take son tafiya tallan kindirmon. ƙwarya ta ɗauka ta tsuguna tare da kama nonon jikin wata Nagge ta fara tatsa gaba ɗaya hankalinta baya jikinta sai a lokacin maganar Gwaggo Niyabi ta faɗo mata, a haka ta gama tatsar nonon acikin ƙwayar ta ajjiye can gefe guda a bukkar tasu. Gari na waye ba tare da yin wanka ba ta shasshafa ruwa ƙafa duk lam’a ta dungura sallah. Dada na gefe tana kallon yadda take sallah tana son tuna wani abu amma ta kasa har zuciyarta take jin kamar yadda Danejo ke sallah ba haka ake yi ba, amma ta kasa ganewa da kuma tuna yadda ake?. “Ina Hamma Yabi?” Danejo ta kalli Dada tace “Mi naddi mo (na kira shi)”. Jinjina kai Dada tai, Danejo sai kallon Dada take kamar zatai shiru sai kuma tace “Dada waye Baffa?” Da sauri Dada ta juya gabanta na faɗuwa sosai na rashin amsar tambayar Danejo tace “Kamarya Halisa? Baffa mahaifinku ne kuma ya rasu mene?” “Na sani Dada, ina dangin Baffana suke me yasa muke zaune a Rugar Rome?” A hargitse Dada ta ɗaga hannunta tare da ɗauke Danejo da mari sai kuma ta fashe da kuka ta ce “Wacce masifa ce wannan kika koya Dajeno? Bance miki nice Dangin uwa dana uba a gareku ba? Ban gaya miki ba Halisa?” Hawaye na sauka a fuskar Halisa ta ce “Kiyi haƙuri Dadana ba zan sake ba, ban san mene yasa nai miki wannan tambayar ba” kasa magana Dada tai saboda hakin daya fara cin ƙarfin ta, zuciyarta na bugawa da ƙarfi Danejo na ƙwala ihu ta shiga kiran sunan Hamma Yabi wanda ke garken shanu, tattara Dada Hamma Yabi yai zuwa wani ƙaramin asibiti dake gefen Rugar, suna zuwa kusan sune na farko amma abin mmki sai kwasar wasu ake ana barinsu sbd cin hancin da suke bawa Nurse’s ɗin, har lokacin tashi yai ba’a samu damar duba Dada ba a haka suka dawo gida.
Yola South
Abti America
Babbar makaranta ce Wacce ta kasance Private school tun daga primary school har zuwa University makarantar dake da ita, Abti America mallakin mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na yanzu Atiku Abubakar ce. Makarantar na cikin Yola South ko ace Yola town duk ɗaya. Makaranta ce wacce sai ɗan wane da wane suke zuwanta duk wanda ka gani a ciki to ka tabbatar ubansa ya mallaki arziƙi ba dukiya ba.
Adamawa/jimeta.
Yola shi ne babban birnin jihar Adamawa. Yola South ana kiranshi da Yola town acan fadar lamiɗon Adamawa yake ma’ana gidan sarauta (LAMIƊO’S PALACE).
Yola North, jimeta kenan. Acan fadar gwamnati yake, jimeta yafi kyau haɗuwa da tsari fiye da Yola South. Manyan abubuwa gaba ɗaya acan Yola North wato jimeta suke. Babu wani nisa tsakanin Yola South da Yola North/jimeta hasali ma roundabout ne ya raba tsakaninsu, akwai wani roundabout mai ƙwayoyin ƙwaryar nono da ludayi a kai muna ana kiransa da Yola roundabout, akan hanyar express yake daga shi sai wata ƙofa, to wannan ƙofar shine da zarar ka shigeta ka shiga yola kenan, sunan ƙofar “JIPPAJAM” da kuma “JAƁƁAMA” Ma’anar Jippajam shi ne Ka sauka lafiya. Wannan idan kazo fita kenan ta cikin yola zaka ganshi, idan shiga garin zakayi kuma za ka ga an rubuta Jaɓɓama ma’ana Sannu da zuwa.
Njoɓoli wani ƙauye ne sosai dake cikin ƙauyukan dake zagaye da Yola south wato yola town,ƙauyen yawancinsu fulani ne makiyaya,amma akwai manoma ma, babu nisa da cikin gari, sannan suna da tashar mota mai tafiya ƙauyen a cikin yola. Wannan kenan.
Tana tafe hannunta riƙe da sanda tana kaɗawa, a hankali bakinta ke motsawa tana karanta 1,2,3-10 cikin fillatancin karatunta bai nisa ba, babu arabi ba boko kuma ba za’a kirata da jahila ba,ita dai gata nan ne dai, ba wanka sosai ma’ana ba tsafta.
Go’a 1 D’id’i 2 Tati 3 Nay 4 juy 5 Je go’o 6 haka ta dinga maimaitawa har ta ƙarasa can nesa da gate ɗin makarantar Abti America. Ajjiye ƙwayar kanta tai tare da neman waje ta zauna tana jira a tashi duk da cewa ba’a talla amma sbd ƙarancin masu sai da kindirmo yasa ake siyan nono a wajanta sosai. Tana zaune wata mota baƙa ta taho da gudu gadan-gadan zata take Danejo cikin tsoro da firgita har tana ture ƙwayar nonon Danejo ta miƙe tsaye tare da fasa ihu tana ƙanƙame jikinta idanunta rufe sbd gaba ɗaya motar kanta tayo da alama giyar motarce ta ƙwace. Motar na gab da taka Dajeno ba zato taji an saka hannu tare da yin sama da ita…
😌🫣 let’s see yadda zaku amshi labarin HALISA DAJENO wanda ya faru a gaske bawai fiction story bane.
🌈 IDAN BA KE 🌈
Nimcyluv sarauta
Arewabooks@Nimcyluv
2.
Ihu Danejo ta fasa lokacin da taji an saka hannu tare da yin sama da ita cikin muryarta ta Fulani ta ce “Mi boni Dada’am mi nasti tati hande mi mayi” gaba ɗaya ta tsorata ta ɗauka motar za tabi ta kanta. Jin an direta gefe guda ya sanya ta buɗe idanunta a hankali a tsaye ta gansa nesa da ita kaɗan hannunsa harɗe a ƙirji yana ƙare mata kallo tare da nazartar yanayinta. Kasa daina kallonsa Danejo tai sbd yanayin shigar jikinsa wani farin yadi ne a jikin nasa amma yai baƙiƙƙirin sbd dauɗar daya haɗa gaba ɗaya yadin ya yayyage har ana iya ganin farar fatar jikinsa, sumar kansa rabi furfura rabi baƙa. Ajjiyar zuciya ta sauke da sauri kuma ta juya sbd ƙarar motar da taji sai a lokacin lura da shegewar motar cikin Abti America.
Ƙugu ta riƙe tana fari da manyan idanunta cike da tsiwa ta ce “Shai mutum ya tsaya yaga yadda ake tijara aradu ina iya fasa gilahin moto ɗin” daga bayanta taji murya mai sanyi ta daki kunnenta ance “Zaki biya?” Juyawa tai ta kallesa mutumin ɗazo ne dai wanda ya taimaketa kafin motar ta bigeta, harara ta banka masa ta ce “Kai Almajiri Sukajo meye ruwanka dani? Ina ruwanka idan moto ya takani, da kayanka duk a yage” ta faɗa tana murguɗa masa baki. A hankali ya nanata kalmar “Sukajo” a ransa idan ya fahimta Sukajo na nufin “Saurayi” Girgiza kai kawai yai ba tare da yace mata komai ba ya juya zai bar wajan. Da sauri ta sha gabansa tana faɗin “hani inbano ina ka kai mini kindirmon shaniyata? Waye ya tittila a tumbinsa?” Juyawa yai tare da kallon ƙwayar nonon babu komai a ciki sbd tuni ta zubar da nonon dalilin tsoran da taji, amma ta kasa fahimtar ita ta zubar ɗin. Yana dai tsaye bai ce komai ba can kuma ya kalli cikin idanunta da sauri ta ɗauke nata idanun tana murguɗa masa baki cikin ƙasa da murya ya ce “Siya akai ai” baki ta buɗe ita ai ba taga wanda yazo ya siya ɗin ba kuma gaba ɗaya nonon aka siya kenan? “Ina kuɗin to ɗan Almajiri mai yagaggun kaya?” Da hannu ya nuna mata ƙasan ƙwayar yana rufe idanu da buɗewa ya ce “Gasu can” ta durƙusa ta ɗaga ƙwayar sai ga kuɗi da gudar dubu ɗaya da ɗari biyar guda biyu sai ƴan ɗari guda goma. Zaro idanu tai waje jikinta na rawa ta ce “Kai ɗan Almajiri mai ƙarya wannan kuɗin duk na kindirmona ne? Ai aradu kuɗin yai yawa” hannunsa dake harɗe a ƙirji ya wara tare da ɗaga kafaɗa ya ce “haka suka bayar ai” “su waye?” Shiru yai mata yana ƙoƙarin juyawa ta ce “Mene wannan a ƙafarka?” Zaro idanu waje yai tare da yin baya ganin tana ƙoƙarin zuwa inda yake yasa yai saurin faɗin “ke fillo bayanki” juyawa tai da sauri amma babu kowa a wajan tsaki taja tana kakkaɓe zanin jikinta ta ce “Mai ƙarya dai ɗan wuta” ta ƙare zancan tana ɗago kanta babu Almajirin kamar yadda ta raɗa masa suna babu ko inuwarsa sai wani farin Zomo data gani kyakkyawa dashi ya ƙura mata idanu, itama kafesa tai da idanu kamar zata kamasa sai kuma ta ɗauki ƙwayarta ta nufi bakin hanya inda zata samu motar da zata kaita Njoɓoli. Da idanu Zomon ya bita har tayi nisa sosai yana kallon sanda ta samu abin hawa, girgiza yai yana kaɗa kunnuwansa sai gashi ya koma mutumin ɗazo wanda take ce masa Almajiri mai yagaggun kaya. Murmushi yai mai kyau a kuma fili ya furta “Danejona”
Da gudu motar mai ƙirar Toyota Rav 4 ta Ƙarasa shiga cikin compound na Abti American University Yola (AUN). A hankali akai parking motar a tsakanin jerin motocin da suke cikin harabar. Buɗe murfin motar tai cikin faɗa faɗa ta ce “No! I mean I lost my eye sight for a while, my Mom slapped me and i was very shouked da marin, Sbd kawai wancan banzan ya kai ƙarata gida i hate him wallah ai babu dole cikin aure ko? I’m 29 years mene ya sa za ana damuna akan wani aure?” Yanayin yadda take maganar kaɗai zai sanya kasan ranta ya ɓaci har buga kan motar take sbd zafin zuciya tsaki tai ta ce “No am okay nazo ganin Zahrah ne, i will catch you later” kashe wayar tai baki ɗaya tana fitowa daga cikin motar tunawa da yadda Yarinyar ɗazo da yadda ta firgita ya sanya tai Murmushi tana nufar hanyar wani office. Office ɗin ba kowa sai some of things da suke saman table zama tai tana danna number Zahrah.
Zahrah na tsaye cikin hall ɗin da take lecturing wayarta tai ringing ta san babu wanda zai kirata at this time sai Surayyerh da sauri ta kalli students ɗin dake hall tana faɗin “Ok guys Conservation biology has two central goals 1. to evaluate human impacts on biological diversity and 2. to develop practical approaches to prevent the extinction of species (Soulé 1986, Wilson 1992)” tana faɗin hakan tace “You get it?” Gaba ɗaya suka ce “Yes Maaa” jinjina kai tai tana taɓe baki idanunta akan wani matashi da sauri kuma ta juya hannunta riƙe da Ink pen ta nufi wajan bord da sauri ta shiga rubuta.
“What is Bachelor of Science in Conservation Biology?” Dake tana ɗaukar su course ɗin Conservation Biology Under Faculty of Sciences ne. Shiru duk sukai suka kasa bata amsa hakan yasa Zahrah sakin tsaki a file ta ce “Is an assignment, ba zan wasting time ɗina wajan yi muku explanation ba, i have so much work to do bye” wani daga cikin students ɗin ne ya miƙe yana dariya tare da ƙwaiƙwayar yadda Zahrah ke tafiya ya tsaya gaban ɗaliban ya ce “I have so much work to do bye… Big Maaaa The arrogant one I hate this woman. But i like her style” gaba ɗaya Students ɗin suka saka dry ba kuma kowa ke ƙaunar Zahrah ba, wulaƙanci da disga mutane ya mata yawa, kuma idan ta shiga hall babu wanda ya isa ya shiga ga bada Assignment da shegen text da Attendance. Zahrah na fita ta nufi Office a nutse take tafiya cikin takun isa da gadara tana sanye cikin wata atamfa Amarya collection mai tsada ɗinkin riga da skert ya kama jikinta sosai, idanunta sanye cikin farin cat eyes wanda ya ɗan haska ɓakar fatar jikinta she’s classes and educated ƴar wanka ce ga tsafta da tarin ilimi. Ƙafarta dake sanye cikin Derby shoes ta tura cikin office ɗin tana ya tsona fuska ta ajjiye handbag ɗin L.v akan kujera idanunta akan Surayyerh ta ce “Lafiya dai?” Surayyerh taja tsaki ta ce “ina lafiya? Can you imagine yau Mom ce ta mareni sbd wancan banzan?” Buɗe idanu Zahrah tai kamar ba zatai Mgn ba sai kuma tace “mene abin damuwa?” “Zahrah mari fa? Wallahi ba zan ƙara ɗauka ba idan aka sake marina, Look at me am 29 going to 30 ace Mom bata bar marina ba?” Girgiza kai kawai Zahrah tai ba tare da ta ce komai ba. “Ina magana Kinyi shiru, wannan miskilancin naki na tsana fa” “uban me kike son nace maki Surayyerh? Your mother has been slapped you sbd kinyi kuskure sai nace bata kyauta ba? Babu abin da zaki iya sbd Uwa ce dole ki hqr” Zahrah ta faɗa cikin ɓacin rai. “i can’t bazan iya jurewa ba” cewar Surayyerh “ok zaki rama kenan? Are you going to beat your mother?” Surayyerh ta girgiza kai cikin damuwa ta ce “A’a kawai zan faɗa mata kada ta kuskura ta sake marina, Nasan Uwa tace kuma sai tai ta dokana akan wanne dalili, ɓacin rana nake gudu” Kallon Surayyerh kawai Zahrah keyi kafin taja numfashi ta ce “Ina cikin damuwa Surayyerh na fara tsorata fa” Surayyerh ta ce “Damuwa akan me?” Hannu Zahrah ta ɗora akan cikinta ta ce “Am pregnant Surayyerh ina da ciki wata uku, kuma na gaji da zubar da ciki wallahi” zare idanu Surayyerh tai tana faɗin “Pregnant? ciki na huɗu kenan fa Zahrah? Kina da hankali kuwa? Wannan karan dole ki yafe cikin kin manta mai Dr yace miki ko?” Ajjiyar zuciya Zahrah ta sauke kafin ta kalli Surayyerh da kyau ta ce “I’m not ready for this, kin san ba aure gareni ba, idan na bar cikin na haihu me zance a gida? Me zan faɗawa Mimi? daman Kullum cikin faɗan naƙi aure take wai na girma da yawa, karatun boko ya buɗe min idanu yanzu kusan shekaruna 31 ne Surayyerh” Surayyerh ta numfasa ta ce “Me kike jira? Ki kira Deen mana kuyi magana ya turo iyaye kuyi aure, Mimi nada gaskiya Kinyi primary, secondary, N.c.e, degree, kinyi masters to what are you waiting for wanda ya shige kiyi aure, haba ai ta boko ai ta boko nifa idan yanzu ne wlh ba zan wata boko ba, shekara 31 ana abu ɗaya sai zallar iskanci kawai da kike kina zubar da ciki a banza, sai kin gama zubar da ƙwayayen da Ubangiji ya baki matsayin zuri’a a banza wlh” Tsaki Zahrah tai “wani lokacin wlh ke Mahaukaciya ce, ni kike tunanin zan iya auren Deen yanzu? Inda a yanzu nasan rayuwa nai boko naje ƙasashe kala-kala da ace ko secondary schl ban rufa ba shi ne zan iya auren Deen amma yanzu kam i can’t, zanje hospital a cire cikin, da kike maganar haihuwa waye ya faɗa miki daman ina son raya da haihuwa da yawa ne? Abeg ta shi muje Madam am not in the mood” Surayyerh ita dai mamakin Zahrah take bata, ta rasa ita da Zahrah waye yafi laifi, ita tana ganin mahaifiyarta na takura mata domin har kusan zaginta take a zuciya, ta hanata jin daɗin rayuwa komai sai ta ce wai taji tsoran Allah, ita kuma Zahrah iyayenta sun sake mata duk abin da zatai babu me cewa dan me gidansu gidan boko ne a waye suke gaba ɗaya, hakan yasa Zahrah keta aikata alfasha hankali kwance. “Kinzo da mota ne?” Surayyerh na miƙewa tsaye ta ce “E, kefa?” Zahrah ta ce “A’a, ba zan iya driving ba wannan cikin duk ya sauyani muje kiyi dropping nawa gida” “ok let’s go” Fita sukai Zahrah da Surayyerh aminai ne duk faɗan da za suyi har abada babu mai ji, su gama fushi su shirya. Mota suka shiga Surayyerh na driving Zahrah na gefe a haka suka bar cikin Abti America.
Da idanu Dada take bin kuɗin da Danejo take bata, a sanyaye ta ce “Duk wannan?” “E, Dadana ɗan Almajirin mai yagaggun kaya ne yace mini aradu duk kindirmo ake siya dasu, kuɗin da yawa” Dada ta jinjina kai ba tare da tace komai domin magana bai dameta ba, tun bayan rasuwar Baffansu Danejo ta zama shiru-shiru sanadin hakan ciwonta ya sake yin tsamari. “Dadana nawa ce wannan?” Danejo ta tambaya tana nunawa Dada gudar dubu ɗaya, girgiza kai Dada tai bayan ta tsurawa dubu ɗayar idanu ta ce “Ban san sunanta ba, ki bari Hamma Yabi ya zo sai ki tambayeshi ko?” Miƙewa Danejo tai ta ce “Bari naje wajan Shatu na tayata irga Naggenmu” fita tai a hanya taci karo da Hamma Yabi, da sauri Hamma Yabi ya kama hannun Danejo ya shiga duba Funa, Fobbina, Wayla, Hirna. Ma’ana Gabas, Kudu, Arewa, da Yamma, ganin ba kowa yasa Hamma Yabi faɗin “Mun shigesu Danejo, gobe ake bikin gasar wasa da maciji, wanda Sarkin ruga yake sawa, kuma yau za’a zaɓi wanda za’ai wasan dashi” fararen idanunta ta juya sosai cikin rashin damuwa ta ce “Hamma mene abin damuwa, ni Dadana kawai nakeso ta samu lafiya ina ta mafarki wani kala” girgiza kai Hamma Yabi yai kaifn ya kama Danejo sosai ya ce “Baka iya wasa da Mashiji ba Danejo, kuma Sarkin ruga zai iya zaɓarki matsayin wacce zatai wasan, idan baki iya ba Mashijin zai iya saranki ki mutu murus, ko baki mutu ba idan baki iya ba Sarkin ruga zai iya korar mutum daga cikin Rugar Rome” cike da tsoro Danejo ta zaro idanu waje ta ce “Mi boni Hamma Yabi yaya zanyi?” “Yanzu shai mu jira muga wa za’a zaɓa, kije ki ɗauki kindirmo mai man shanu ki bawa Dada gobe zamu koma ashibiti” kai ta ɗaga alamar to Hamma Yabi ya nufi cikin jejin nemo wani sassaƙen magani ita kuma ta nufi wajan garke a nan ta samu Shatu ta kama bakinta a nonon Nagge tana ta sha hankali ƙwance. Zama tai kan wani Leggal (Icce amma kututture) samun kanta tayi da tunani wanne kalar Mashiji za’ai wasan dashi? Meyasa idan taje Birni take ganin wasu mutanan ba irinsu ba komai nasu daban ne, meyesa birni ta banbanta da Rugar Rome?. Ajjiyar zuciya ta sauke tana murza yatsun hannunta da sauri takai dubanta zuwa ga ƙadamin yatsarta idanunta ya sauka akan zoben dake maƙale da yatsar da tsananin mamaki take kallon hannu yaushe wannan abun ya zo hannunta? Mene sunansa ita bata taɓa ganin abu mai kama da zobe ba sai yanzu, ga wani zane a tsakiyar zoben kamar tambarin abu amma bata san ko mene ba, ƙoƙarin zare zoben take amma ta kasa hakan yasa dole ta hqr. Suna zaune a garken suka ji ana shelar Sarkin ruga yana neman jama’ar Rugar Rome baki ɗaya. Da Shatu da Halisa suka kalli juna zuciyarsu cike da zullumi amma Danejo tai ta maza ta kama hannun Shatu suka nufi wajan. A tsaye suka samu mutane wasu na sanye da fararen kaya na Fulani wasu kuma Kuraye yawancin su gaba ɗaya farare ne, amma sam babu cikakken addini ga rashin tsafta. Sarkin ruga ya gyara tsaiwa yana faɗin “Kamar yadda kowa ya sani, a gobe ne zamu gabatar da gasar wasan Mashiji, za’a zaɓi mutum ɗaya ya buga wasa da ƙaton Mashiji kamar yadda muka saba, idan mutum ya kashe Mashiji akwai kyautar Nagge da kuma ƙwayar nono guda hamsin, idan Mashiji ya kashe mutum Shi kenan wasa ya zo ƙarhe, idan mutum bai mutu kuma za’a kuresa daga Rugar Rome baki ɗaya, don haka yanzu zamu fito da alƙalin wasa ya zo ya zamu wanda za’ai wasan da shi” Shatu ta ƙankame hannun Danejo ita ko kalmar Mashijin bata so taji an faɗa balle ta gansa a gabanta. Dajeno kam shiru tai kanta a ƙasa tunani fal ranta domin gaba ɗaya ma hankalinta baya wajan. Alƙalin wasa ya fara zagaye mutane har ya shige kan Danejo gama dubawa yai sannan ya gyara murya ya ce “Mun zaɓi Halisa Dajeno Rome a matsayin wacce zata fafata da ƙaton Mashijin mu a gobe….
Sarautar marubuta
True life story
🌈 IDAN BA KE 🌈
Nimcyluv sarauta
Arewabooks@Nimcyluv
3.
“Na shiga uku ta ya ya zan iya wasa da maciji? Wallahi kashe ni zai yi” Danejo ta faɗa a fili cike da tsora wanda ya sanya har ta kusan sakin fitsari gaba ɗaya ta firgita. Shatu ta ce “Ki faɗa masa ba zaki iya ba a zaɓi wata, idan Mashijin ya kashe ki na shiga uku na lalashe aradu” da sauri Danejo ta fito tsakiyar fili idanunta akan Alƙalin wasan muryarta na rawa ta ce “A yi mini afuwa Alƙalin wasan ba zan iya wasa da maciji ba aradu sarata zai yi” Alƙalin wasan ya kalli Danejo sosai, shi ya ɗan jima bai ganta ba, ta ƙara girma da wayo sosai ta zama ƴar budurwa irin girman ƙauyen nan dai. Sai rashin tsafta da addini dake ɗawainiyya da ita duk da ana ƙoƙarin ganin an magance hakan a cikin Rugar Rome. Murmushi alƙalin wasan ya sake yi cikin kulawa ya ce “Zaki iya mana? Ai Baffanki ya ƙware wajan iya sarrafa maciji, a wasan ƙarshe kuma macijin ya zama silar mutuwarsa, ki yi wasan ko dan ƙarasa cikawa Baffanki burinsa na zama gwarzo a Rugar Rome. Tabbas zaki iya Halisa Dajeno Rome” girgiza kai tai da sauri idanunta cike da hawaye ta ce “Ba zan iya wasa da maciji ba, mene ya sa sai ni? Baffana daban ni daban kalleni ƙarama ga maza nan da yawa a zaɓi wani daga ci” Sarkin rugar yai saurin faɗin “Ke aka zaɓa, kuma dole kiyi domin ba zamu taɓa sauya ra’ayinmu ba, ya zame miki wajibi muddin kina cikin Rugar Rome” a tsorace Shatu ta ce “Hande en boni, yau mun shiga uku” kasa cewa komai Danejo tai domin gani take kamar ma ta mutu ne lokaci kawai take jira.
Da sauri ta juya idanunta cike da hawaye ta nufi cikin bukkarsu zuciyarta cike da zullumi da kuma fargabar abin da zai je ya dawo. A haka ta shiga cikin bukkar Idanunta akan Dada wacce take kwance cikin halin ciwo, domin a kullum ciwon nata ƙara tsanani yake. “Dada Alƙalin wasan ya zaɓi Danejo matsayin wacce zatai wasa da maciji a gobe” da sauri Dada tana jan numfashi ta kalli Danejo cikin damuwa ta ce “Mene ya sa baki cewa masa ba zaki iya ba?” Shatu tai saurin faɗin “Sarkin ruga ya ce wai dole tayi domin cika muradin Baffanmu” Dada ta miƙawa Danejo hannunta cikin kulawa ta ce “Waye yace muku Baffanku wasan maciji shi ne burinsa?” Danejo ta kasa magana sai ajjiyar zuciya take saukewa Shatu ce tai ƙarfin halin cewa “Sarkin ruga ne ya faɗa” Murmushin taƙaici Dada tai bata taɓa ganin zalunci irin haka ba, ta rasa me suka tsarewa Sarkin ruga da yake shirin ƙarar dasu ta hanyar kashesu da maciji wanda wasu suka tabbatar macijin tsafi ne. Cikin ƙonar zuci ta ce “Baffannku bai taɓa sha’awar yin wasa maciji ba, halima babu wannan al’adar ta wasa da maciji a Rugar Rome, daga baya Sarkin ruga ya samar da ita, bayan ya samar da ita ya zaɓi Baffanku matsayin wanda za’ai wasan dashi” shiru tai sbd tarin daya sarƙe mata numfashi, da sauri Shatu ta ɗauki ruwa ta bata, numfashi ta sauke kafin ta ce “Bisa dole Baffanku ya amince, yasha wahala kafin ya kashe macijn bayan ya samu raunuka wanda ya sa ya kwanta jinya, da shekara ta zagayo aka ƙara zaɓar Baffanku abin mamaki shi ne babu bambanci tsakanin macijin shekarar data shige da kuma wanda aka fito da shi, Baffanku ya tsorata, gashi idan ya ce ba zai ba to za’a kuresa daga Rugar Rome, tun daga wannan shekarar Baffanku ke gabatar da wasan Maciji, har zuwa shekarar da maciji ya kashe shi wanda kuma anyi hakan ne domin aga bayansa. a ruɗe Danejo ta ce “Kenan kashe Baffa akai Dada?” Dada ta girgiza kai ta ce “Ba zance ba, bani da hujja akan haka koma mene hukuncin na wajan Allah”.
Danejo taja numfashi cike da raunin murya na rashin sanin mafita zuciyarta cike da tarin zullumi ta kalli Dada ta Shatu ta ce “Dada ba zan iya ba, ina jin tsoro” “Halisa idan ba kiyi korarki za su yi daga cikin Rugar Rome, ni kuma ba zan jure hakan ba, Ubangiji na tare dake. Dole kiyi wasan imma ki mutu ko kiyi rai Kinji ko?” Kafin Danejo tai magana Hamma Yabi ya shigo da sauri idanunsa akan Danejo yana faɗin “Tashi mu tafi Danejo daman nasan bayanki suke son gani kamar yadda suka kashe Baffa” kallo Hamma Yabi Danejo tai idanunta ya kumbura sbd kuka ta ce “Hamma ina zamu?” Muryarsa na rawa ya ɗaga ta tsaye ya ce “Zanje na ɓoyeki sai an gama wasan zaki dawo, zan nuna ban san idan kike ba” Dada tai saurin cewa “A’a Yabi, kada ai haka kamar Halisa tare damu, idan ta tafi to Shatu ce zata maye gurbinta kasan haka ai” zama yai sosai ya ce “Yanzu haka zamu zauna? Ke baki da lafiya ita kuma muna kallo maciji ya kashe ta?” “Akwai Allah” Dada ta bashi amsa tana rufe idanunta. Halisa kasa bacci tai ga yunwa ga tsoro can cikin dare ta tuna ai ha tayi sallar issha ba, da sauri ta fito daga bukkar gaba ɗaya rugar shiru babu kowa sai wutar da aka kunnawa ko wanne garke dake ci hankali. Can bayan bukkarsu ta nufa tai tsari a wajan tai alwala babu ko shafar kai ta kwararan ruwan ta dawo. Sallar ma dungure tai Fatiha kawai ta iya cikakkiyar babu gyara. Yadda taga rana haka dare, dab da Asuba ta nufi garke tare da tatsar nono, tana gamawa ta Ajjiye. Gari na fara haske bayan tai sallah ta kaɗa shannun zuwa cikin jeji. Har zuwa lokacin bata da nutsuwa ita a yanzu ba wasan majin ya dameta ba, illar rashin lafiyar Dada idan har macijin ya kasheta waye zaici gaba da kula da Dada? Zama tai a gefen wani dutse ta shiga rusa kuka da iya ƙarfinta.
Commissioners Quarter’s
Haɗaɗɗiyyar unguwa ce wacce take cikin Jimeta, iya haɗuwa da tsari unguwar tayi, wanda bai saba fita kasashen waje ba idan ya shiga Commissioners Quarter’s zaka ɗauka a ƙasar turawa kake. Gidajene duguwa zaka gansu kamar tangaran sbd yadda suka haɗu aka zuba dukiya. Unguwa ce ya masu kuɗi wanda talaka sam bai isa ya shige ta ba. Unguwannin masu ci da gindin biro kenan.
A hankali take sakkowa daga kan strains ɗin benan hannunta riƙe da waya tana latsawa, jikinta sanye da wani Short pencil jeans sai Balenciaga top a saman t.shirt ɗin jikinta. Ƙafarta cikin wani Hermes slippers. “Binta! Binta!!” Ta shiga kiran maid ɗin dake yi musu abinci tana zama saman Kujera, jinin Binta na rawa ta ƙaraso tana zubewa a gaban Zahrah ta ce “Hajiya gani” harara ta watsa mata cikin rashin ko ina kula ta ce “Kin san ban son buɗe murya sbd kawai zan kiraki?” Binta wacce a ƙalla zata iya yin shekaru 55 zasu iya kusan sa a da mahaifiyar Zahrah ta sunkuyar da kanta ƙasa cike da girmamawa ta ce “Afuwa Hajiya, ina can ina duba time table na list ɗin abincinki na me za a dafa miki zuwa dare” shiru Zahrah tai ba tare data ƙara cewa Binta komai ba, hankalinta yana kan wani abu da take searching akai, ita dai da karatun boko na yin magana a jikin mutum da tuni ya jima dayi a jikin Zahrah domin kaf gidan tafi kowa zurfi karatun boko shi ya sa take taka kowa hankali kwance. “Hajiya me kike buƙata?” Binta ta tambaya. Idanunta ta ɗaga ta kalli Binta a hankali taja tsaki ta ce “Nikam Binta na tambayeki?” “Ina jinki Hajiya” Zahrah ta gyara zama sosai tana ajjiye wayar hannunta a gefe kafin ta ce “Wai yaushe za kiyi hankali ki fahimci abin da nake buƙata, matsalar rashin ilimi kenan fa, gaba Binta ƙwaƙwalwarki bata riƙe abu ba lallai ko primary kin cika ba, wallahi na tsani harka da midille class,uneducated, villagers” da tsananin mamaki Binta ke kallon Zahrah ƴar cikinta ke faɗa mata wannan maganganun? “Kiyi haƙuri Hajiya” a fusace Zahrah ta ce “Sorry for yourself Binta, kije ki haɗa mini salad ki saka lemon sosai ciki” Binta ta jinjina kai tana Miƙewa tsaye tare da barin wajan idanunta cike da hawayen baƙin ciki. Wata mata wacce ta fito cikin parlourn ta kalli Zahrah ta ce “Why are you shouting?” Murmushi Zahrah tai ta ce “No Mimi ina game ne, akai mini game over” Zama Mimi tai ta ce “Ok, kwana biyu na jin labarin Deen a bakinki? Lafiya dai?” Zahrah ta ce “Baya nan ne Mimi” Mimi ta ce “Ai fa, naga idan yazo sai ku kai awa uku zuwa huɗu a part ɗinki kwana biyu shiru” Murmushi kawai Zahrah a haka Binta ta kawo mata haɗin salad ɗin. Mimi tabi Zahrah da kallo kafin ta ce “Wai lafiyarki ƙalou kuwa? Kullum cikin cin haɗin Salad kike?” “Lafiya Mimi, kawai zuwa makarantar nan ke sani gajiya da kwaɗayi naji bana son cin komai” Mimi ta jinjina kai ta ce “Lallai, ni banga me zaki da kuɗi ba da kuka zaɓi lecturing Zahrah” ba tare da data amsa ta ba ta ce “Mimi ina Daddy ne?” Mimi ta ɗauki waya ta ce “Jiya ya dawo, but yaje kano wajan wani babban abokinsa” “Ok” cewar Zahrah a nutse Mimi ta kalli Zahrah cikin damuwa sosai ta ce “Fatima-Zahrah yaushe kike tunanin yin aure ne, boko kin gama ta, completely sai abin da yai saura, familyna sun fara mini surutu akan wai na zuba miki idanu, wasu har cewa suke maybe yawonki kawai ki ke, ni dai nasan ba haka bane i trust you babyna” marairaicewa Zahrah tai kamar ƴar 20 nan kuwa shekaru 31 take da shi. “Mimi kin san familyn nan naki basu san darajar karatun boko ba, ta ya ya zan haɗa karatu da aure? Kana yin auren kuma ace ka haihu, kuma ba zan iya haɗa aikina da aure ba gsky Mimi a barni zuwa 35 na gama komai sai na fara tunanin auren, su kansu mazan ai mai ilimin boko suke buƙata ba kuwa ya damu da ilimin addinin nan ba, suna buƙatar mace wayayyiya a very educated women” murmushi Mimi tai cike da gamsuwa da maganar ƴarta kafin ta ce “Na fahimta, ko Dadynki sai dana kammala University mukai aure muna dai soyayyya a waje, dake kuma na wuri na shiga shcl shi ya sa na gama before we getting married” jinjina kai kawai Zahrah tai hankalinta akan salad ɗin da take ci sbd yadda cikin jikinta ya sanya mata kwaɗayi kala-kala. Da sauri Mimi ta ce “Subuhanallahi, maza kunna mini Plasma ɗin nan ki jonata da DS.TV tafsirin Sheikh sai shigeni” kwaɓe fuska tai kafin ta ce “Mimi wai kin damu da wani Sheikh, ni wallahi ban son tafsirin ɗin ko kaɗan, ga wata ƙinƙina da yake, da ƙyar fa yake iya karatun sbd ƙinƙina wani time ɗin har hawaye yake to me za’a gane?…” Da idanu Mimi tabi Zahrah tana mamakin jikar ƙirjinta a kullum “To ai kuwa da yadda, ƙinƙina kuma ai larura ce kuma a hakan Ubangiji ya ba shi bawai Zahrah”.
Gudu take sosai hankali a tashe sai haki take ita kam sam ba zata iya irin wannan wasan na sai da rai ba, wacce ƙaddara ce take shirin bibiyarta ne? Tsayawa tai tana mai da numfashi, sai a lokacin idanunta ya sauka akan wasu fararen Kurciyo masu kyau da tsari ita a rayuwa tana son ko wacce kalar dabba ta daɗe tsaye tana kallonsu, ɗaya daga cikin kurciyoyin ya tsora mata idanu. Tunawa da tai ana gab da fara wasan macijn ya sanya ta ƙara saurayi domin samun wajan ɓoya. Girgiza kurciyoyin sukai wata iska da guguwa ta mamaye ilahirin wajan iskar data kasance mai daɗi sosai wacce ta haddasawa Halisa Dajeno rufe idanunta wani barci na fisgarta a hankali ta sulale a wajan babu jimawa barci mai nauyi ya ɗauketa. Kurciyoyin suka rikiɗe zuwa wasu samari masu zubin halitta ɗaya daga ciki wanda yake sanye da farar Alkyabba mai taushi wacce ta sauka har ƙasa ta rufe masa ƙafafuwansa yaja numfashi a hankali cikin ƙasa da murya ya ce “Danejona ba zata iya wasan nan ba” ɗayan dage gefensa ya ce “Haba Prince me ya sa kake da taurin kai ne? Sarki yace ka yanke duk wata alaƙa tsakaninka da bil-adam musamman wannan yarinyar Danejo amma kaƙi” murmushi mai taushi Wanda aka kira da Prince yai yana sake kallon Halisa Dajeno ya ce “A wannan karan ba zan iya yiwa Sarki biyayya ba, babu haɗi tsakanin mutum da aljani, amma kasan ba zan iya zutar da wani rai ba, muddin idan ba Danejo zai cutar ba? Na jima a jikin mahaifiyar Danejo tun tana da cikinta, amma rana ɗaya akai mata magani suka rabani da ita, wanda ya sanya na kwanta jinya, wannan dalilin yasa na koma kan ɗiyarta Danejo na shirya duk wani abu da sarki zai faɗa, ƙarshe dai ya ce zai koreni daga duniyar Aljanu ba?” Ɗayan zai magana Prince ya daka mishi tsawa ya ce “Ka saurara mini Safwan” ya faɗa idanunsa na juyewa zuwa kalar na aljanu a tsorace Safwan ya ce “Afuwa nake Yariman Aljanu, yanzu me ka shirya akan raba Danejo da wasan macijin nan?” Gyara Tsaiwa Prince yai tare da durƙosawa daidai inda Danejo take kwance tana barci ya ɗauke ta cikin nutsuwa ya ce “Ubangiji nake nema ya bani Sa’a, ina son Matata bana jin zan jure ganinta da duk wani wanda zai cuceta, balle kuma ya taɓa mini ɗana dake cikinta” buɗe baki Safwan yai da Mmki yace “Prince yaushe ta zama matarka? Har kuka samu ɗa?” Murmushi Prince yai yana shafa cikin halinsa wanda yake jin farin ciki na ratsa masa zuciyarsa kafin ya ce “Matata ce ita ɗin, duk wanda ya shirya rabani da ita to ya shirya zuwansa lahira, bani da lokacin magana Safwan, maza ku ɓace daga wajan nan” kamar gilmawar walƙiya haka suka ɓace, nan da nan Prince ya rikiɗe zuwa Almajiri mai yagaggun kaya. A nutse ya fara tafiya da ita zuwa cikin Rugar Rome dai da yaje daidai bakin bukkar su Danejo ya ajjiyeta da sauri ya bar wajan, sbd gaba ɗaya jama’ar Rugar suna filin da za’a gabatar da wasan Maciji. Prince ya ce “Ubangiji ka bani Sa’a da nasara” yana faɗin hakan yai Girgiza nan take ya zama ƙaton wani baƙin maciji mai narkeken kai a hankali ya sulale ya fara tafiya tsakanin bukkokin Rugar Rome har ya Ƙarasa wata bukka kai tsaye ya kutsa kansa ciki, kwance ya samu wani maciji shima baƙine sosai, da alama shi ne macijin da Matarsa Danejo zatai wasa dashi. Kallon kallo aka fara tsakanin Maciji Prince da kuma Macijin da Danejo zatai wasa dashi. Kamar haɗin baki haka suka fasa kai a tare lokaci guda kuma suka nufi kan juna.
🫣Bala’i🚶🏽♀️kada a manta labarin ya faru a gaske babu ragi babu ƙari👌🏾. Muje zuwa
Sarautar marubuta
True life story
🌈 IDAN BA KE 🌈
Nimcyluv sarauta
Arewabooks@Nimcyluv
4.
A kusan tare macizan guda biyu suka ƙara fasa kai tare da kaiwa juna sara, ko wanne maciji ƙoƙarin jiwa ɗan uwansa ciwo yake da ganin ya kashesa har lahira. Gaba ɗaya macizan suka sarƙafe juna tare da nan na ɗewa waje guda ko wane huci yake yana fitar da hayaƙi ta baki nisan yadda Prince wanda ya a rikiɗe zuwa maciji ya matse macijin da Za’ai wasa dashi, gaba ɗaya ya ji masa rauni a hankali kuma Prince ya buɗe bakinsa ya fara haɗiye Macijin zuwa cikinsa sai daya haɗiyesa tsaf kafin ya sulale gefe guda ya kwanta yana mai da numfashi Wahala, sai fasa kai yake kamar zaici babu zuciyarsa tayo sama baki ɗaya zai iya sarar ko waye a wannan lokacin.
Sarkin ruga ya kalli tarin jama’ar da suke wajan hadda Shatu da Hamma Yabi, da sauran mutanan rugar kafin ya numfasa ya ce “Lokaci ya yi ake a kawo mana Halisa Dajeno Rome cikin fili, domin su fafata da maziji yau ranar tace” Wani mai suna Giɗaɗo ya rusuna tare da faɗin “Yanzu za’a kawota” yana faɗin hakan ya kalli Hamma Yabi tare da faɗin “Maza jeka kawo ɗiyar taku, tana ɓata mana lokaci” Hamma Yabi ya ce “Yanzu za’a kawota” yana faɗin hakan ya juya da sauri ya nufi bukkarsu tun daga nesa ya hangeta kwance a bakin bukkar inda Prince ya kwantar da ita tana barci.
Cikin sassarfa ya ƙara yana faɗin “Assha Subuhanallahi barci a ƙasa Danejo” ya faɗa yana ɗagota tare da jijjigata sosai, da sauri ya buɗe idanunta tana zabura “Hamma Yabi yaushe na dawo nan?” Kallonta yai ya ce “Kina nufin baki san lokacin da kika kwanta a nan ba?” Girgiza kai tai ta ce “Aradun Allah ban shina ba, kawai naji iska mai daɗi ta lulluɓeni wani barci yazo mini daga nan ban san komai ba” Girgiza kai yai yana kama Hannunta ya ce “Danejo ƙurushiya, maza muje sarkin ruga na jiranmu” dafe ƙirji tai cike da tsoro ta ce “Na shiga uku na lalashe, Kur’ani na manta yanzu hamma yabi shikenan mutuwa zan, zan mutu na bar Dada? Zan mutu banyi karatu na zama babbar mace ba? Don Allah kada na mutu yanzu bana son wasan nan” rirriƙeta Hamma Yabi yai sosai ya ce “Ma zaki mutu ba Danejo, sai na kai ki burni Kinyi karatu kin zama babbar mace abar ƙwatance, sai kin zama mace ta farko wacce zata kawo sauyi cikin Rugar Rome, ki daina kuka kinji” kai ta ɗaga masa kafin da sauri ta ce “Kuma zan zama wannan mutumin na jikin bango?” Zare idanu Yabi yai kafin ya ce “Wannan gwamna ne fa” murɗa baki tai cikin shagwaɓa ta ce “Ni dai irinsa nake son zama” Yabi ya dungure mata kai ya ce “Aradu ƙarya kike, ina zaki iya yin siyasa tayaya zaki zama gwamna daman mata na zama gwamna ne?” Banza tai masa bai ƙara ce mata komai ba ya jata zuwa filin da za’a gabatar da wasan.
Giɗaɗo dake tsaye shi da Sarkin ruga suna jiran zuwan Hamma Yabi da Danejo ya ce “Me ya sa ka zaɓi Danejo kasan ba zata iya wasan ba” murmushi Sarkin ruga yai kafin ya ce “Ina son ganin bayanta ne, kuma a hankali zan ƙarar da zuri’ar Manga a cikin Rugar nan, wannan macijin na tsafi ne hatta mutuwar Manga ni na shiryarta”… “Amma me Manga yai maka haka?” Cewar Giɗaɗo. Sarkin ruga ya ce “Sirri ne..” kaifin su ƙara magana Hamma Yabi ya ƙaraso hannunsa riƙe da Danejo wacce ta ƙanƙamesa sosai jikinta na rawa da ɓari.
Alƙalin wasan ya ce “Yawwa yanzu zamu fara, Danejo ta shigo cikin fili jama’a ku buɗe idanunku da kyau yau za kuga wasa wanda baku taɓa ganin irinsa ba” Halisa Dajeno Rome na tsakiyar fili ko kuka ta kasa a wannan lokacin ta tsaya ne kawai tana jiran taga ta inda mutuwa zata zo mata, domin abune mai wahalar gaske ace yau ta rayu ko ta tsira da ranta. Sarkin ruga ya bada umarnin a fito da Macijin, da sauri Alƙalin wasan ya nufi bukkar da macijin yake. Yana kwance sharkaf yau lamo a ƙasa tare da yin gammo da jikinsa, wani irin zabura yai tare da fasa kansa a lokacin da alƙalin wasa ya shigo cikin bukkar, ƙuri yai masa da idanu yana ƙare masa kallo. Ko me ya tuna Ohhu a hankali ya fara sauka daga dokin zuciyar ya koma ya kwanta, shi kansa Alƙalin wasan ya tsorata jikinsa na rawa yasa hannu ya ɗauki Macijin da ƙyar sbd nauyin da yake da shi.
Tun da Halisa Danejo Rome ta saka idanunta akan macijin taji gabanta ya faɗi, jikinta ya ɗauki rawa hawaye suka fara sintiri a saman Fuskarta, bata taɓa ganin maciji mai girman wannan ba, tama rasa wacce kalar addu’a zatai duk da ba wani abu ta iya sosai ba. Alƙalin wasan ya ajjiye macijin nesa da Halisa, aka fara kallon kallo tsakanin Danejo da Macijin, an shafe tsayin wasu daƙiƙo aka rasa waye zai fara kaiwa wani hari tsakanin Danejo da Maciji Prince?. Zaro idanu tai waje ganin ya fara warware tare da yin tsayi sululuuuu kuma ya nufo inda take, tana ja baya yana biyota har ya ƙaraso dab da ƙafarta tare da tsorawa zoben hannunta idanu. Juya tai tana neman inda zata gudu can idanunta ya sauka akan wani ƙaton dutse. Da sauri ta ɗauka tare da riƙewa a hannunta, ganin haka yasa Macijin bin ƙafafuwanta suuu haka ya dinga sufa a jikinta, har ya naɗeta ciff kansa daidai Fuskarta yana tsora mata idanu tare da kallon cikin idanunta.
Jirkinta na ɓari ta ɗaga dutsen tare da kwaɗa masa a tsakiyar kansa, wani kalar ihun azaba macijin yai yana fasa kai kamar zai sarata, sai kuma ya saki kansa tare da ɗorasa saman ƙirjinsa gaba ɗaya naman Macijin rawar azaba yake, kansa tuni ya fashe ya fara zubar da jini. Ganin nasarar da Halisa Danejo Rome ta fara samu yasa Hamma Yabi da Shatu tare da sauran jama’ar Rugar Rome suka fasa ihun murna, Sarkin ruga da Alƙalin wasan hankali tashe suka kalli juna tare da faɗin “Me ya samu macijin nan? Ki dai asiri akaiwa Yarinyar nan?”.
Halisa a tsorace Macijin a tsorace amma a haka cikin dakiyar zuciya ta ƙara ɗaga dutsen a karo na biyu ta ƙara bugawa Maciji, Innalillahi a wannan lokaci kururuwar da Macijin yai sai da kowa na wajan yaji, jini ya sake ɓalle masa a hankali ya sulale ƙasa baya ko motsi alamar ya mutu… ajjiyar zuciya ta sauke haka kurum taji kuka ya ƙwace mata, durƙushewa tai a wajan ta shiga rera kuka tausayin macijin ya kamata musamman yadda taga jini na zuba a jikinsa, Hamma Yabi ya ƙaraso wajan Halisa Dajeno Rome tare da ɗagata yana dariya ya ce “Danejon Dada kin kashe macijin, kin kashe sa bana faɗa miki cewa ba zaki mutu ba? Zamu samu ƙwayar nono da Nagge masu yawa” ƙanƙame Hamma Yabi tai cikin kuka ta ce “Bana so Hamma Yabi, mu bar nan wajan kaina juyawa yake, bana son ganin jinin nan kaji” hannunta ya kama sukai gefe guda. Cike da taƙaici Sarkin ruga yake bin Macijin da kallo bai taɓa tunanin haka ce zata kasance ba, cike da baƙin ciki ya amshi wani sanda ya shiga kwarɗawa macijin aka tun macijin na motsi har ya daina jikinsa yai face face da jini tare da raunuka. “Ka ɗauke sa ku cillar a gefen gaɓar ruwa wani abin yai kalace dashi” Giɗaɗo da Alƙalin wasan suka ɗauki Macijin tare da nufar cikin jeji da shi. Suna zuwa suka cillar gefe guda da sauri suka juya cikin Rugar Rome.
Sanyin gaɓar ruwan daya ratsa cikinsa ya sanya ya fara Girgiza yana juyi tare da murmurɗe jinsa gefe guda, wani kalar ihu yake mai nuni da azabar da yake ciki, ya daɗe cikin wannan halin kafin yai Girgiza tare da rikiɗewa ya dawo siffarsa yadda yake fitowa a mutum ba Aljani ba, yana kwance sambal gefen ruwan Farar Alkyabbar jikinsa duk ta ɓaci da jini. A hankali ya ɗaga hannunsa tare da dafe kansa inda yake zubar da jini, runste idanun yai sosai cikin ƙasa da murya ya ce “Ya Allah” yana nan ƙwance yaji iska ta mamayesa baki ɗaya kafin kace wani abu iskar ta ɗaukesa zuwa sama.
Duk farin cikin dasu Shatu suke ciki banda Danejo rasa abin da yake mata daɗi tai, gashi jinin Dada ya matsa ga tunanin dake wanzuwa a cikin zuciyarta. Dada ta kalli Shatu ta ce “Farin ciki za kiyi Halisa ba damuwa ba, da tuni an rabani dake Allah bai ba, akwai ƙaddarorin da suke biye dake, amma duk wahala duk tsanani waya rana zaki zama abar ƙwatance tabbas zaki samu miji wanda zai kula da maraicinki” Danejo ta ce “Dadana nifa ba marainiyya bace, ina dake ga Hamma Yabi ga kuma Shatu” jinjina kai Dada tai idanunta akan zoben hannunsa Halisa ta ce “Ina kika samu wannan Halisa?” Girgiza kai tai cikin damuwa ta ce “Ban sani ba Dada, kawai na gansa a hannuna”… “Bana son ƙarya fa” da sauri Halisa ta ce “Da gaske nake miki, kalli kiga” ta faɗa tana nuna mata tambarin zoben, Dada ji tayi kansa ya sara idanunta akan Zoben da sauri ta riƙe kanta tare da rufe idanunta, kamar mai son tuna wani abu babu abin da take gani a cikin idanunta sai tambarin masarauta dake manne cikin zoben. Ganin yadda Dada ta rirriƙeta kanta ya sa Hamma Yabi fita da gudu ta tatso mata kindirmo mai zafi, da taimakon Halisa Dajeno Rome suka bawa Dada kindirmon nan da nan zufa ga shiga saukar mata bacci ya ɗauke ta.
Juyawa Halisa tai ta kalli Shatu dake barci a nutse ta kalli Hamma Yabi ta ce “Hamma yaushe Dada zata samu lafiya ne? Kullum a ƙwance take ina tsoran na rasa ta aradu” Hamma Yabi ya kama hannun Danejo ya ce “Ba zaki rasa Dada ba, gobe zan koma asiti bamu da kuɗin kai ta asibitin burni” Da sauri Danejon ta ce “A siyar da Nagge to” zare ido Hamma Yabi yai ya ce “Aradu ƙarya ne, Uban waye zai taɓa Nagge ai mu dasu mutu karaba” ba tace masa komai ta miƙe tsaye tare da yin waje lokacin rana ta faɗi, can gefe ta nema ta zauna ita ɗaya sai tunani take a haka har akai magariba tana zaune, ganin duhu ya fara yasa ta miƙe tare da zagayawa bayan bukka ta kwaɓe kayan jikinta, halittar jikinta ta tsorawa idanu, musamman ƙirjinta tana mamakin abun mene amfaninsu a jikinta? Ita a gareta basu da wani abu kullum sai dai su ƙara girma. Ruwa ta sheƙa babu ko sabulu tana gamawa tai alwala, wasu kayan fulanin ta ɗauka farare ta saka tare da Ajjiye waɗan can, da sauri tai sallah tana gamawa taci tsiran da Hamma Yabi ya kawo musu, tana ci ta kwanta barci domin da wuri take son zuwa kiwo ta dawo ta tafi tallan kindirmo.
Ciki zafin nama Prince ya saka hannu tare da ɗauke Safwan da mari ya ce “Ka fita a sabgata, kaje ka faɗawa Sarki halin da nake ciki ya ɗaukeni, kuma kasan yana gab da rabani da matata wanda ba zan iya jure hakan ba sam” Safwan ya kalli Prince cike da mamaki ya ce “Ban taɓa ganin mai taurin kai a duniyar Aljanu irinka ba Prince, cutar da yarinyar nan kake fa, babu haɗi tsakanin mutum da Aljani na faɗa maka, abin kunyane ka rasa wacce zaka so sai Bil adam? Allah zai saka mata fa” banza Prince yai da Safwan a wannan lokacin rabinsa na mutum rabi kuma na siffar Aljani da sauri ya juya zai tashi sama Safwan ya ce “Ina zaka? Ba dai wajanta ba?” Prince ya ce “Ba zan iya yin wasu daƙiƙo ba, ba tare da naga matata ba, da matata nake son kwana a yau ɗin nan” yana faɗin haka ya ɓace ɓat kai tsaye Rugar Rome ya nufa. Halisa juya cikin barci taji wani sanyi na ratsa mata jiki, ga wani mafarki da ke ƙafafuwanta sai motsawa suke amma ta kasa koda motsi bada ji take kamar ana danneta. Can dai ta farka a firgice Innalillahi a ruɗe ta fara kallon inda take, tana kwance tsakiyar dokar daji ba gida gaba ba gida baya…
Waye ya kawo Halisa Dajeno Rome cikin dokar daji?…
Sarautar marubuta
true life story
🌈 IDAN BA KE 🌈
Arewabooks@Nimcyluv
https://wa.me/+2348119237616
5..
A zabure ta miƙe tsaye tana ƙarewa cikin dokar dajin kallo, babu abin da ya bata mamaki irin yadda taga an sauya mata kayan jikinta, daga na Fulani zuwa na wasu saƙi farare masu kyan gaske. Jikinta na rawa sbd tsoro da tarin fargabar dake ratsa dukkan wasu lunguna na ƙofofin zuciyarta ta shiga ƙarewa jikinta kallo. Idan hankalinta yai dubu to ya tashi ta ƙara razana da halin da take ciki a yanzu, domin ba iya kayan jikinta da aka sauya mata ne kaɗai ya bata mamaki ba, zanan jan lallen data gani kwance a hannunta shi ne ya ƙara ta hanyar mata da hankali, ga sumar kanta da akai mata wasu irin kalba manyan gwanin sha’awa ita bata taɓa ganin kanta yai irin wannan kyan ba sai yau. Waye ya kawota nan Meke shirin faruwa da rayuwarta ne, ina Dadarta?.
Ƙare wa cikin dajin tai babu ko hanyar da zata bi ta nufi Rugarsu, daɗin daɗawa ita kanta bata san a inda take ba, wacce kalar rayuwa ce haka? Daga yin barci kuma sai mutum ya farka ya gansa a tsakiyar daji? Bayan tasan a bukkar Dada tai barci. Tafiya ta shagayi idan ta kalli gabas da Arewa, guda da yamma sai ta saki kuka tare da faɗin “Na lalashe jama’a ina nake ina rugar rume tayi, ina Dadata, ina Shatu, ina Hamma Yabi duk kuna ina wayyooo Hande en boni, Yettore jaumirawo” ta faɗa ɗora hannunta aka tare da sakin kuka, ta fiya kawai cikin dokar dajin tun tana kuka har tai shiru sai idanunta da take rarraba wa a ciki dajin.
Kukan da tayi da kuma gudun data jima tana yi sune suka taru suka haifar mata da wata gajiya wacce ta sanya ko idanunta bata iya buɗewa sosai sbd yadda kanta ke juyawa da kuma yunwar data keji, lokaci zuwa lokaci tana buɗe idanunta tare da zubawa zanan lallen hannunta idanu, tana cikin wannan hali ta ƙaraso wani waje wanda yake da rana sosai hakan yasa Danejo ta wahala fiye da zaton mutum, ga ƙishin da take ji. Daurewa tai taci gaba da tafiya sai dai duk yadda takai da daurewa ta kasa bata san lokacin da jiri ya kwashe ta ba, tai baya luuu zata kifa da sauri aka tareta ana faɗin “Subuhanallahi” mutumin ya faɗa a taushashe yana mai riƙe Danejo wacce ta faɗo jikinsa babu numfashi alamar ta soma kenan.
Kyakkyawan idanunta mai ɗauke da kuriyar ƙwayar ido su ya ware akan Danejo yana mai ƙara jin nutsuwa na saukar masa a jikinsa, a hankali a kuma dukkan wata ƙaunarta ta shiga nunkuwa a zuciyar Prince Bilal. Yanzu ne zai samu cikakken lokacin kasancewa da ita, irin kasancewar nan ta har abada domin baya jin akwai mutumin daya isa ya raba shi da Matar Danejo a cikin wannan Dajin, zai zauna da ita zai rayuwa da ita, tai ta haifa masa yara, ya kuma yi alƙawarin ba zata taɓa sanin shi aljani bane, zaici gaba da zuwar mata a suffar Balarabe kamar dai suffar wani Sheikh ɗin Malami. Ɗaukarta ya yi a hannunsa zuwa gaɓar wani ruwa, jallabiyar jikinsa ta sauka har ƙasa tare da rufe masa ƙofatonsa, a haka ya Ƙarasa tare da kwantar da ita a gefen ruwan wajan da yake da ɗan danshi danshi musamman daya lura da jigatar da tai duk da cewa duk wani abu da take akan idanunsa ne. Yana kwantar da ita ya zauna gefenta idanunsa na juyawa tare da sauya launi zuwa wata kalar, hankalinsa ya karkata gaba ɗaya zuwa cikinta idan yake hango ɗansa dake maƙale a mararta hakan sai cike da farin ciki Prince ya saki Murmushi bakin na rawa ya ce. “Ubangiji ya saka mini sonkiwa zuciyata, tun kina cikin mahaifiyarki, zanci gaba da sonki ba zanyi saken da za a rabani dake ba, kamar yadda aka rabani da mahaifiyarki tun tana asalin inda take rayuwa” shafa cikin nata yai idanunsa na tsiyyayar da wani ruwa ya ce “Babu alaƙa tsakanin mutane da Aljanu, amma naji a wannan karan dama Ubangiji a suffar mutane ya halittoni, mene yasa bakwa iya ganinmu a suffarmu ta zahiri sai dai mu muganku? Ina son ki matata Danejo,ina gab da ɗaukeki zuwa duniyarmu” dariya ya saka gaba ɗaya wajan ya ɗauki rawa da Girgiza can kuma ya ɓace da wajan.
Acan Rugar Rome kowa gari na wayewa suka saba Danejo na tashi zuwa garken Nagge ƙara tatsar nono, hakan yasa Dada bata damu ba sbd ganin Danejon bata cikin bukkar sai Shatu dake kwance a gefe tana barci, Hamma Yabi ya fita tun sassafe zuwa asibitin dake gefen Rugar Rome domin samawa Dada layi. Yana tsaye a a ɗan wajan da mutane suke tsayawa gaba ɗaya mutanan ba sufi mutum goma ba, suna zuwa kamar mutum biyar zai koma ya ɗakko Dada. Wani Likita ne hannunsu riƙe da waya yana dubawa ya raɓa ta gefen Hamma Yabi ya shiga office, Fuskarsa ɗauke da fara’a ya kalli mutumin dake cikin office ɗin ya ce “Dr Hamza na ganka a zaune ina patients ɗin?” Dr Hamza ya dubi Dr Iliya yana ƙara ware idanunsa ya ce “Patients suna can waje, bani da time na duba su serious,idan zaka shekara kana duban jama’ar Rugar nan ba zaka taɓa samunsu da cikakkiyar lafiya ba, ƙazanta ita take ƙara lalata musu lafiyar jikinsu na gaji wallahi, sai Shegen son shanunsu amma basu san yadda zasu kula da lafiyar jikinsu ba” Dr Iliya yaja kujera tare da zama sosai yana faɗin “Ai Dr Hamza sai haƙuri, kasan cikin karkara musamman ruga haka ba komai suka sani ba, kai dai barsu da arziƙinsu wato Nagge su kawai suka sani” Dr Hamza ya ce “Let’s leave this matter, it is not in front of me” ya faɗa yana duba wani file, “I got the message you want to see me up, lafiya dai kake mini kiran gaggawa haka?” Dr Iliya ya tambayi Dr Hamza cike da jin don abin dake faruwa. Gyara zama Dr Hamza ya yi kafin ya ce “The government has given free medicine to the people of Ruga, maganin da gwamnati ta bayar suna da yawa, akwai maganin Suger, Hawan jini, Maleriya, da sauran maganin cuccutikan, yawwa sai maganin sikila irin folic acid, Paludrine, Peniciillin V,Hydroxyurea. Anfi kawo maganin Sickler sbd yawaitar samunta da ake cikin karkara, shiyasa nace a kiraka” cikin jin Daɗi Dr Iliya ya ce “Masha Allah yanzu yaya za’ai kenan?” Wani kallo Dr ya Hamza yaiwa Dr Iliya kafin ya ce “Ya kowa za’ai? Kasan Rugar nan ko an basu magani a banza, basu san important ɗinsa ba, so that zamu kwashi 88% a cikin 100 mu siyar mu raba kuɗin, kai ba kana da chamist ba? Sai ka zuba kawai acikin chamist ɗin naka” cike da gamsuwa Dr Iliya ya ce “that’s good, amma gwamnati ƙoƙari sosai fa, banda haka wannan maganin sunfi ƙarfin miliyan 3 da wani abu fa,ana kula yanzu da ɓangaren lafiya sosai da masu juna biyu, anywhere zuwa dare zan zo da mota na ɗauki rabona” Sallama sukai tare da fitowa a tare ganin hakan yasa Hamma Yabi saurin kallon Dr Hamza ya ce “Aradun Allah na shafe awanni a nan gashi muna ta jira” a faɗace Dr Hamza ya ce “Wai kai fillon nan wani irin banza ne bagidaje ne kai? You doesn’t know anything akan asibiti ka addabi mutane da wautarku ta Fulani, mu bamu da wasu kayan aiki cikin Asibitin nan kana kallo da idanunka ai, dan haka kada ka sake zuwa idan an kawo kayan aiki zamu sanar get out” jiki babu ƙwari Hamma Yabi ya koma cikin Rugar Rome, yana zuwa ya sake tarar da wani tashin hankalin babu Danejo gaba ɗaya acikin Rugar, sanadin hakan yasa jikin Dada ƙara rikicewa abu kamar wasa duk inda suke tunanin ganin Danejo babu ita sam har kusan kwana biyu.
Tunda ya kwantar da ita a gaɓar ruwan har gari ya waye ta kwana a wajan, wani daren ya yi ta sake kwana, kwana biyu kenan amma bata motsa ba. Bata kuma da ranar tashi sai lokacin da Ubangiji ya nufa ko kuma ya tsara. A can cikin barci ta fara mafarki gata da namiji suna kasancewa waje guda, wani abu mai kama dana auratayya na gilmawa a tsakaninsu. Numfashi ta sauke tana motsa ƙafafuwanta zuwa cinyoyinta da suke mata zafi, tana jin kamar an daddaneta a firgice ta farka tana kurma ihu tare da kiran sunan Dada, ba addu’a babu komai. Cikin tsoro ta fara bin jikinta da kallo babu komai lafiyarta ƙalau domin ba wani sauyi da taji. Ajjiyar zuciya ta sauke a bayyane tare da kifa kanta a tsakanin cinyoyinta ta shiga rera kuka, kenan haka rayuwarta zata ƙare cikin dokar dajin ko yaya ne? ya akai ta tsinci kanta a dajin gaba ɗaya ta rasa amsar tambayoyin zuciyarta. A hankali ta fara jin dariya na karaɗe wajan, tare da surutu ƙasa ƙasa. Miƙewa ta yi da sauri ta shiga duba inda take jiyo sautin dryar a haka ta ƙaraso jikin wata ƙatuwar bishiya, cike da tsoro da kuma tarin zullumi ta ɗaga kansa zuwa saman bishiyar idanunta ya sauka akan wani ganyen bishiya dake lilo shi ɗaya, sai ka ɗauka iska ke kaɗa shi amma abin mamaki shi kaɗai ne yake lilo daga cikin sauran ganyen bishiyar. Prince Bill wanda a yanzu ya rikiɗe zuwa suffarsa ta asalin aljani yana kwance saman ganyen yana karkaɗa ƙafarsa wacce ita ce take sanya ganyen bishiyar motsawa, Danejo dai kallon ganyen take cike da mamaki tana tsaye taci mangoro ya faɗo kanta abinka da mai jin yunwa da sauri ta ɗauki mangoron babu Bisimillah ta shiga sha idanunta na lumshewa sbd daɗi. Daga bayanta taci ance. “Kisha a hankali da wasu da yawa idan kina buƙata” juyawa tai da sauri baki buɗe take kallon mai maganar, iya tsoro da razani ta shiga domin bata taɓa ganin halitta irin wannan ba, mangoron ta saka tare fasa wani Ihu ta ɗaga ƙafa zata gudu yai saurin riƙe hannunta.
Share🥰🥰🥰
🌈IDAN BA KE 🌈
6….
Arewabooks@Nimcyluv
“Na shiga uku Aljani Balarabe” Danejo ta faɗa a ruɗe tana ƙoƙarin kwace Hannunta daya riƙe cikin nasa. A nutse Prince ya ware idanunsa sosai a kanta yana Mmkin Yadda duk ta ruɗe kamar taga mugun abu. “Me ya baki tsoro” murguɗa masa baki tai tana suɗe hannunta dake ɗauke da ruwan mangoron ba tare data ce komai ba. Prince ya saki tattausan murmushi mai kyau da tsari yana binta da kallo musamman idan ya tuna abubuwa da suke faruwa a tsakaninsu, sai yaji nutsuwa ta kamasa. Hannunsu ta make ta ce “Sakeni haka kurum kai mini ciki, bayan Dada ta ce ba kyau namiji ya taɓa mace” ta ƙare Maganar tana binsa da kallo, sai a lokacin da a shiga ƙarewa tsarin hallitar jikinsa da kallo, fari ne tas kamar ka taɓa shi jine ya fito, yana da faɗin ƙirji fuskarsa mai cike da ilhama, ga wani gudun saje wanda ya kewaye fuskarsa zuwa ƙasa wajan gemunsa, fuskarsa mai faɗi ce babu wani abu da zai bamban tasa da jinsin larabawa. Prince ya saketa yana mai faɗin “Ciki na nawa kuma?” Zuciyarta na bugawa sosai ta ce “Me kace?” Ya girgiza mata kai yana ware hannun shi ya ce “Babu komai Danejo” zare ido tai tana dafe ƙirji sosai a tsorace ta ce “Kasan sunana? don Allah kasan rugarmu wallahi ɓata nayi ka taimaka kaji ɗan Balarabe” idanunsa ya ɗaga sama tare da daidaita juyawar launin idanunsa ganin yana neman rikiɗe masa, jikinta duk rawa yake tai saurin cakumarsa tare da rirriƙesa wanda yai sanadiyar fitowar wata jela a bayansa, sbd ko yaya ya samu kusanci da ita, baya iya zama a zallar mutum, dole sai wani sashi na jikinsa ya juye zuwa na aljani. “Ukkkkk heee” ya faɗa cikin kumburarriyar wacce ta amsa kuuwa cikin kunan Danejo. Gaba ɗaya rikicewa tai ganin yadda take neman maƙalesa baki ɗaya saboda tsoro da fargaba har take shirin bayyanar da kofatonsa yasa yai saurin riƙo Fuskarta tare da hura mata iska a fuska. Ƙuri tai masa da idanu a rarrabe ta shiga faɗin “Ka kaini wajan Dadata kaji, bana son zama a nan tsoro na keji Da…da…ta..” ta kasa ƙarasa maganar sbd idanunta da suka ruf wani barci mai nauyi ya ɗauketa.
Fuskarta yabi da ido yana hango lokacin da yake tare da mahaifiyarta, duk yadda ya nunawa Dada so da ƙauna amma haka wani mugun babban Malami ya raba shi da ita, ba shi da niyyar cutar da Dada kawai ƙauna ce tasa yake tare da ita, yai ihun tare da magiya amma haka Malamin ya fatatakesa daga cikin Dada bayan ya ƙona shi. Wannan dalilin ya sa yai jinya sosai har bai san inda Dada tai ba sai kwatsam ya ganta lokacin tana ɗauke da cikin Danejo, tun daga wannan lokacin ya ɗauki son duniya ya ɗora akan Danejo, ya manta da batun Dada ɗan tayin dake cikinta kawai yake muradin yaga ya zo duniya.
Sauke numfashi yai yana binta da idanunsa daya gama rikiɗewa har wani hayaƙi yake fiddawa, hannunta ya riƙo ya kama yatsan dake ɗauke da zoben daya saka mata ya jima yana kallonta kafin ya saketa zuwa ƙasa ya kwantar. Tsakiyar dajin ya koma yana Girgiza da surutai cikin ƙaramin lokacin ya koma asalin suffarsa ta aljani yana wani ihu da gurnani kafin kace wani abu ya gama haukata dajin can kuma ya ɓace ɓat.
Yamma Yabi ne da Shatu tare da Sarkin ruga da kuma Giɗaɗo kwance a gaban Dada wacce take cikin halin rayuwa ko mutuwa, bata san inda kanta yake ba, sunan Halisa Dajeno Rome ne kawai a bakinta. Giɗaɗo ya ce “A jiƙa wannan maganin a bata” da sauri Hamma Yabi ya amsa tare da jiƙawa da taimakon Shatu ya ɗaga Dada suka ɗora mata maganin, wani shaƙuwa tai jikinta ya shiga jijjiga can kuma ta kwanta shakaf barci ya ɗauketa. “Na shiga uku na lalashe Hamma Dada ta mutu wayyo yanzu yaya za mu yi Dada ki tashi” idanun Hamma Yabi na taruwa da ruwan hawaye ya kama Shatu tare da riƙeta ya ce “Assha Assha Shatu Dada nada rai, daina kuka yaro barci Dada tai” kuka kawai Shatu take, duk da ƙarancin shekarunta amma ta fahimci cewa Dada ita ce cikon farin cikin su, tare da jin daɗinsu. Sarkin ruga ya sauke ajjiyar zuciya ya ce “Allah shi bata lafiya, Aradu tana gab da mutuwa” jin kalmar Sarkin ruga yasa Shatu ƙara sakin kuka tana jijjiga Dada tare da faɗin ta tashi kada ta mutu ta barsu cikin ƙuncin rayuwa. Cike da takaicin kalamar Sarkin ruga Hamma Yabi ya bisa da kallo yana addu’ar Ubangiji shi ya ɗauki rayuwarsa yabar Dada a duniya ko dan farin cikin Shatu da Halisa. “Ba a samu labarin Danejo ba har yanzu?” Girgiza kai Hamma Yabi yai yace “Aradu ta ɓace babu ita kaf cikin ruga da kuma daji” cikin tausayawa Giɗaɗo ya ce “Wayyo Allah shi baiyyanata” “Kawai iskanci ta tafi, amma ina ne Danejo bata sani ba cikin ruga da dajin ba har kiwo take zuwa ba?” Da sauri Hamma Yabi ya ce “Danejo ba zatai iskanci ba, domin bata san shi ba” fita duk sukai daga cikin bukkar. Hamma Yabi ya dubi Shatu da barci ya ɗauketa a jikinsa a hankali ya kwantar da ita, tare da fita daga cikin bukkar. Yana fita ya shiga irga Nagge wanda ya zama al’adarsa kullum tunaninsa za a iya sace musu Nagge shi ya sa a rana sai ya irgasu sau biyar. Kai tsaye asibiti ya nufa lokacin ana zubawa Dr Iliya magani a cikin mota.
Saukar ruwan ruwan sama ne ya haddasa farkawar ta daga barci, da sauri ta miƙe tsaye jirkinta na rawar ɗari sbd gaba ruwan ya gama yi mata doka, ganin bata da wata mafita ya sa ta fara ƙoƙarin ɗaga ƙafarta Innalillahi sai a lokacin ta lura ashe a kan wani ƙaton dutse mai tsayin gaske take, ita kanta bata iya hango ƙasan dutsen, a hankali ta koma tare da zama saman dutsen “Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un wacce kalar rayuwa ce take ciki haka? kenan akan dutsen ta kwana? ina ne nan kuma kwananta nawa? ta haukace ne ko mene? Anya ita ce ba wata Danejon bace daman?” Wani raunataccen kuka ta saka kuka take da dukkan ƙarfinta kenan ita da Rugarsu har abada ina za taga Dadarta? Kuka take sosai na rashin mafita ga rayuwarta ga ruwan sama na dukanta, yunwa take ji sosai, hannunta ta tara ruwa ya shiga sauka a hannun cikin sauri ta shiga shan ruwa sai daya isheta sosai sannan ta koma ta kwanta barci ya ƙara ɗauketa saman dutsen.
“Ke! Ke! Baiwar Allah” aka shiga kiran sunanta wanda yasa ta buɗe idanunta da sauri tare da fatan Allah ya sanya a cikin Rugar Rome take, wasu fatake ta gani su wajan biyar tsaye a kanta ko wanne hannunsa riƙe da abu. Sai a lokacin ta lura ashe a kwance take saman wani ya shi saɓanin ɗazo da take kan dutse. Idanunta take rattabawa tare da binsu da ido ganin ba wanda ta sani yasa ta mayar da kanta ƙasa “Baiwar Allah wace ke daga ina kike? Kin san ina ne nan a Maiduguri kike fa?” Da sauri ta kalli mai maganar sai bata ce komai ba. Wani daga ciki ya ce “Ko bata magana ne? Kamar bafulatana” “Akwai abin da ke damunta Allah kaɗai ya sani” cewar wani, yin duniya sukai tai magana ko ta faɗi garin da take amma tai shiru kamar an kulle mata baki dole suka barta bayan sun yi mata fatan alkairi.
“Danejo” aka kira sunan a taushashe sautin Muryarsa da taji yasa tai saurin Miƙewa yana tsaye kamar kullum sanye da fararen kaya ga tarin nutsuwa da ilhama a tattare da shi. da sauri ta nufesa kamar zata riƙesa sai kuma ya tsaya dab dashi tana sakin kuka tare da faɗin “Ɗan Balarabe ka kaiki gida kaji, tsoro na keji ina son nasan halin da Dadata ke ciki” Prince ya sake mata murmushi yana faɗin “Waya kawoki nan?” Hannu ta watsa alamar bata sani ba da sauri ta ce “Amma ka sanni ko? naji ka iya kiran sunana do Allah ka kaini wajan Dadata” yana kama hannunta ya ce “Ban san inda kike ba, Danejo kuma sunan matata ne ina iya kiran sunan kowa da ita” da fararen idanunta ta kallesa ba tace komai ba, sai hawayen dake suntiri a cikin idanun nata. Hannunta ya riƙe yana janta da Shira tun tana kuka harta daina, tana zaune taga ya kawo mata naman kaji da yawa da kuma kayan marmari ƙin cin komai tai sai da ya fara mata wasa yana bata labarin abin dry sannan ta saki jiki taci kayan marmarin. “Zan kaiki gida” da sauri ta ce “Da gaske kake Balarabe?” Kai ya ɗaga mata yana faɗin “E, Matata” turo baki tai ta ce “Ni ba matarka ce ba” ya ce “Daman ba dake nake ba” kamar ba zatai Magana ba sai ta ce “Yaushe zaka kaini wajan Dada” yana riƙo hannunta ya ce “Ko yaushe, amma kiyi mini Al’ƙawarin na dinga zuwa ina koya miki karatu, kuma kiyi al’ƙawarin zamu zama ƙawaye a duk sanda na buƙace ki, kizo gareni ba zan cutar dake ba na rantse da Ubangiji al’arshi, ba zan bari kuma kowa ya cutar dake ba” tunda ya fara magana take kallonsa cikin rashin sani ya ce “Kuma Dadata zata samu lafiya?” Shiru yai mata an riga anyi masa iyaka da mahaifiyarta, babu abin da zai iya a gareta, sai dai ya sanya Safwan yai wani abu akai. “Uhm ni kayi magana mana” ta faɗa tana jijjiga hannunsa kai ya ɗaga mata ya ce “E, kina zuwa ya kiga ta samu lafiya” Murmushi tai Wanda ya bayyanar da kyanta a hankali ya dinga ɗauke mata tunani harta manta da batun gida sulalewa tai ta kwanta saman ƙafarsa barci ya ɗauketa.
ISLAMIC UNIVERSITY OF MADINA.
Jami’ar Musulunci ta Madinah masarautar Saudi Arabiya ta kafa jami’ar bisa umarnin sarauta a shekarar 1961 a tsattsarkan birnin Musulunci na Madina. Koda yake wasu sun danganta akidar Salafiyya da bude jami’ar, ana ganinta a matsayin rashin fahimta sakamakon halayyar da cibiyar ta ke da ita ga kowane akida. Jami’ar ta sami takardar shaidar digiri na jami’a ba tare da banbanta ta ba daga Hukumar Kula da Ilimin Kimiya da Nazari a watan Afrilun 2017.
Jami’a ce mai tsarin gaske musamman Ɓangaren Addini. Ga nagartattun Malamai, da yawan ɗaliban na son karatu a jami’o’in Saudi Arabia sbd dalilai masu yawa. Manyan jami’o’in Saudi Arabia an basu shaidar yabo a bangaren ilimin kimiyya. Wasu daga cikin jami’o’in Saudi Arabia suna cikin manyan jami’o’i a duniya dangane da cibiyoyin bincike. Jami’o’in Saudiyya suna ba da kyakkyawan yanayin binciken ilimin, ta hanyar ingantattun cibiyoyin bincike. Yankunan ilimi da al’adu iri daban daban a jami’oin Saudiyya. Akwai daliban duniya daga sama da kasashe 165 da ke karatu yanzu haka a jami’o’in Saudiyya. Baya ga manyan masana ilimi da ma’aikata da ke aiki a waɗannan jami’o’in. Jami’o’in Saudiyya suna ba da cikakkiyar kulawa mai kyau ga ɗalibanta da kuma malamanta. ire-iren wannan manyan dalilai yasa akeso da burin karatu a jami’o’in Saudi Arabia.
Da sauri ya fito daga ɓangaren hall ɗin da aka ɗauki darasin Islamic Studies and History. Kansa a ƙasa ya tatatare hannayensa cikin milk ɗin Arabian jallabiya daya saka sai wani ƙaramin baƙin hirami da yai rawani dashi, ɗaya hiramin kuma ya ɗora saman kafaɗarsa. Wasu matasa ne manyan suke take masa baya hadda wasu securities. Yanayin yadda yake tafiyar kaɗai zai tabbatar maka babu sassauci a zuciyarsa, idanunsa yai jajur bai taɓa shiga ta shin hankali na yau ba, yana zuwa bakin wata farar mota jikin Umar-khan na rawa ya buɗe masa murfin bayan motar ya shiga, Malamin na shiga mota, Umar-khan ya shiga gaban motar bayan driver ya shiga. Da sauri Driver yai wa motar key ganin haka yasa Saif-Wazir ya shiga wata motar kai tsaye daga cikin University ɗin Prince muhammad bin abdul’aziz international airport suka nufa.
Ta cikin madubin motar Umar-khan yabi Sheikh Aliyu Haydar wanda ke bayan motar da kallo, ya jingina da jikin Kujera sai huci yake fitarwa, ya rirriƙe Jallabiyar jikinsa da hannu bibbiyu, gumi na tsastsafo masa ta tsakiyar goshinsa sbd yadda zuciyarsa ke masa zafi da ta fasa. Girgiza kai Umar-khan yai cike da tausayin yanayin yadda Sheikh Aliyu Haydar ke gabatar da rayuwarsa. Juyawa yai yaci gaba da kallon yadda driver ke sharara gudu, har suka ƙaraso filin tashi da saukar jirgin, The plane is ready to take off. Tun daga bakin wajan securities ɗin suka firfito tare da mamaye motar Sheikh, Umar-khan ya buɗe murfin motar ciki. Sauri Sheikh Aliyu Haydar ya fito a wannan lokacin ma kansa a ƙasa, yana hawa strains ɗin jirgin Saif-Wazir na biye dashi, sai Umar-khan wanda ya ɗan tsaya yana amsa kiran Father. Cikin damuwa Umar-khan ya ce “Kayi haƙuri Father, Sheikh ba zai taɓa aikata hakan ba, zargi ne kawai ake masa, yanzu jirginmu zai tashi be patient Father” tsaki Father yai ta cikin wayar kafin ya kashe. Yana shiga jirgin aka bawa Pilot daman keta hazo, a hankali jirgin ke zagayawa a ƙasan kwalta ya jima a haka kafin ya kete zuwa sararin samaniya.
Jeniyar motocine suka tabbatar da Father Sheikh Aliyu Haydar ya ƙaraso gida Nigeria, da sauri ya miƙe daga zaunan da yake yana zaga haɗaɗɗan parlon gidan, tare da jiran shigowar Sheikh ɗin. Da mamaki Umar-khan ke bin ƴan jaridu da kallo, daga na gidan Redio, T.v, media. Abin har yai tsamari haka yana da tabbaci Sheikh ba zai taɓa aikata abin da ake tuhumarsa ba, zargi ne kawai. A nutse ya sakko da ƙafarsa daga cikin motar kai tsaye ƙofar shiga cikin gidan nasu ya nufa, Umarninka da Saif-Wazir na karesa daga ɗaukan da ƴan Jaridu suke masa. Sako ƙafar da Sheikh Aliyu Haydar yai cikin parlon yai daidai da lokacin da Father yake sauke masa wani lafiyayyan mari wanda yasa Umar-khan saurin juyawa ya fita, domin ba zai iya jure ganin ana cin zarafin babban mutum akan idanunsa ba kamar Sheikh Aliyu Haydar, Saif-Wazir Hawayen da yake maƙalewa ne suka sakko masa, da sauri ya karawaw Umar-khan baya. Cikin faɗa da tsawa Father ya ce “Ka kyauta Aliyu Haydar, ashe wannan dalilin ya hanaka auren tsayin shekaru talatin da huɗu? Ka yaudareni kaci amanar Musulmai kana fakewa da karatun addininka kana lalata yaran mutane a makarantar Jami’ar Madina?” Har wannan lokacin kan Sheikh a sunkuye yake banda cukurkuɗe Jallabiyar jikinsa da yake da hannu babu abin da yake. Father ya girgiza idanunsa cike da hawaye ya ce “Ba shakka biri yai kama da mutum, tunda nake baka taɓa zuwa wajena kace Father na zaɓi yarinya ina son aurenta ba,You betrayed me Aliyu, you deceived me as your father” Ya faɗa yana saukewa Sheikh wani marin cikin tsawa ya ce “Talk Aliyu, kayi magana ka amsa mini Sheikh..!!!” Father ya faɗa yana Girgiza kafaɗar Sheikh. Ɗago kai Sheikh yai bakinsa na rawa laɓɓansa na karkarwa alamar yana son cewa wani abu, amma sam ya gagara sbd rashin iya magana da bai ba. “Ban damu da duk yadda zakai magana ba Aliyu, a yanzu ba zanwa ƙinƙinarka uzuri ba ka bani amsa da gaske wata kaiwa ciki?” Shaaa hawaye ya sauka fuskarsa Sheikh sbd yadda yake son furta wani abu ya kasa. Matsawa ya yi kusa da Father yana buga hannunsa a cinya a hankali hannu na rawa ya miƙa tare da kama kwalar rigar Father, idan ya ɓalle bottle ɗin gaban rigar Father sai ya mayar rufe, da ƙarfi ya buga ƙafarsa yana riƙe wuyan Father hawaye ba zubu masa cikin ƙinƙina ya ce. “Ya….ya…. ya Allah…” Ya ƙare mgnar cikin ƙinƙina yana mai buga ƙafarsa a ƙasa.
Share as so much as you can💋… Not Edited👏🏻
Sarautar marubuta
True life story
🌈 IDAN BA KE 🌈
Arewabooks@Nimcyluv
Follow my account👇🏾
https://arewabooks.com/u/nimcyluv
7…
“Heeeyyy..faaa..Father,babb babu uhmuuu macen dana taɓa laaahhh latawa” a wahale ya Ƙarasa maganar sbd zafin ƙinƙinar dake cinsa take basa wahala, yana buga ƙafa a ƙasa tare runste idanunsa zuciyarsa na maza zafi da raɗaɗi sosai na cin zarafi da sharrin da ake son yi masa, amma ko kaɗan fuskarsa bata nuna damuwar da yake ciki ba, ƙinƙinar ita ke azabtar da zuciyarsa wacce take kassara dukkan wani mafarki nasa. Hannun Sheikh dake wuyan Father ya ture cikin ɗaga murya ya ce “Ok ƙarya za ayi maka kenan Sheikh? Mutane dubu nawa ne a makarantar ba ace sune suka aikata haka sai kai? Kasan halin da ake ciki yanzu gidan Jaridu na gab da sakin labaran? Mata nawa ka lalata, mata nawa kai wa ciki?” Cikin zafin maganganun Father Sheikh ya ƙara runste idanunsa kansa ma sara masa, shiru kawai ya yi ba tare da ya ce komai ba. Father ya yi tsaki yana juyawa zuwa upstairs har lokacin bai dai na faɗa ba. “Kaje ka kare kanka daga zargi Aliyu, at anytime jami’an tsaro na iya zuwa, You are accused of a serious crime, we have no evidence to defend you in court”
“Wanne Irin Court Father? Laifin Aliyu har ya yi girman da za a kaisa court? Wallahi babu mai kai mini ɗana Court” Hajiya Maryam wacce suke kira da Mother ta ƙare maganar tana sakkowa daga upstairs, domin lokacin da motocin su Sheikh suka shigo Sallah take. Father ya Kalli Hajiya Maryam tare da nuna Sheikh wanne yake ta damƙi Jallabiyar jikinsa. sam bai damu da duk zargin da za a yi masa ba, idan ƙaddararsa ce ta zo da haka babu yadda za ayi ya goje mata. “Sai ki tilasta masa ya yi magana, na faɗa masa ya nutsu ya ajjiye ƙinƙinarsa a gefe ya bani bayani, amma yaƙi, kina tunanin iyayen yaran zasu ɗaga masa ƙafa ne akan laifin fyaɗe da ya yiwa yaransu? Sbd kasancewarsa Malami kuma mamallakin S.A.H BANK..? ki Ajjiye son da ki ke masa a matsayin ɗanki, ki kwatantanta adalci tsakaninsa da sauran yaran daya lalata Maryam” Cikin faɗa Mother ta ce “Look Aliyu, idan kai ba zaka iya ƙwatarwa ɗan ka ƴanci ba, zan shiga ko’ina domin ganin an wanke Sheikh daga zargin da ake masa, ba abin kunya bane ace wai kai ne mai bada goyon baya akan Aliyu Haydar ya aikata hakan?” Father wanda Hajiya Maryam ta kira da Aliyu dake sunansa aka sakawa Sheikh ya yi Murmushin ta kaici. “Idan taƙamar maki Lawyer ce, kada ki manta su ma yaran Gwamnati na iya ɗaukar musu lauyoyi, dake da gwamnati sai ku zuba muga, kada ki manta daga can Madina aka zo da zan can, an kai maganar state C.i.d idan jami’an Nigeria bata ɗauki mataki ba, na Madina zasu ɗauka suna gab da bashi takardar kora daga aiki” yana faɗin hakan ya haura sama cike da baƙin cikin abin da Sheikh Aliyu Haydar ya ja musu a cikin Alhhali.
Mother ta bi bayan Father da kallo, tana mamakin rashin ko’in kula da Father yake nunawa Sheikh kamar ba ɗan cikin sa ba. Juyawa tayi tare da kallon Sheikh da har yanzu kansa yake ƙasa tasan he never talk domin damar maganar bata damesa ba, sbd ƙinƙinar da Ubangiji ya jarabce shi da ita. Tana ƙoƙarin yi masa magana ya juya da sauri zai bar parlourn sbd raunin daya hango cikin ƙwayar idanun mahaifiyar ta shi. Yana saka kansa zai bar parlourn Umar-khan ya shigo da sauri jikinsa na rawa ya ce. “Innalillahi wacce irin masifa ke shirin tunkaro Mother?” Mother na ɓoye damuwar ranta ganin yadda Umar-khan ya firgita ta ce “Me ne ya faru Umar-khan?” Idanunsa akan Sheikh wanda ya ɗan jinkirta da fitar Umar-khan ya ce “Na rasa tayaya ƴan Jaridu suka samu wannan labarin, gaba ɗaya sun cika gidan nan da waje baki ɗaya, duk yadda securities sukai ƙoƙarin hana faruwar hakan amma abu ya gagara” Sheikh na jin haka ya juya alakar tafiyarsa zuwa haɗaɗɗan sashinsa dake cikin gidan nasu. Mother ta bi bayansa da kallo kafin ta juya ta kalli Umar-khan tace “Na jima banga mutum mai taurin kai da tsayayyiyar zuciyar irin Sheikh ba, duk abin da za ayi masa ba zai taɓa cewa komai ba” Umar-khan yaja numfashi yana mai ƙara gasgata zan can Mother, domin babu wanda bai san Sheikh da kafiya ba. “Yanzu ya za mu yi Mother? Al’amarin nan ya shige tunaninmu, ba tsammaci haka ba” Mother ta zauna kujera tana tunani ta ce “Zan shigar da ƙara Court, da kai da Saif-Wazir kuji da ƴan jaridu subar ƙofar gidan nan Immediately”
“Court Mother? Waye zai tsaya masa? bakya tunanin shiga Court ɗin kamar latata rayuwar Sheikh ne?” A taƙaice Mother tana danna waya ta ce “Hakan ne mafita Umar-khan, batun lawyer ni ce zan tsayawa ɗa na da kai na” “but Mother” hannu ta ɗaga masa cikin sakin murya ta ce “Umar-khan…!!! Stop asking to much” jinjina kai yai ya fita yana jinjina girman yadda abin ya lalace cikin ƙanƙanin lokaci haka.
Sheikh na shiga bedroom ɗinsa yaja numfashi sbd wani sassayan ƙamshin turarensa na ROJA daya daki hancinsa wanda ya jima da zama abokin hirar ɗakin. Ƙamshin daya haifar masa sauƙi a zuciyarsa, kasa zama ya yi ya shiga kaiwa da komowa a tsakiyar bedroom ɗin, tunani fal ransa wacce yarinya ya lalata? ba mace ɗaya ba har mata da yawa, kuma harda ciki? Bayan tunda yake maganar minti 20 bata taɓa haɗa shi da mace ba, idan ka ɗauke mother. Bai taɓa jin sha’awar mace ba, duk daɗin muryar mace bai taɓa ji ba, kamar an saka masa tsanar mata haka yake ji a ransa balle a wayi gari yau wata ta birgesa ba. Yinin ranar a sashinsa yake, Mother ba tai tunanin zuwa wajansa ba, ta san ba zai taɓa saurararta ba, koda Maimoon ta nufi part ɗinsa ɗauke da try na dinner yadda taje haka ta dawo, bugun duniya yaƙi buɗewa haka ta juya tana mai jin tausayin yayan nata.
Mother dake zaune a Parlourn Father dake cikin sashinsa ta gyara zama ta ce “I couldn’t believe what was happening,Aliyu is your son, you gave birth to him. Me ya sa ka yarda a ranka zai aikata hakan?” A nutse Father ya ɗaga kansa ya kalli Mother kafin ya ce “na fiki sanin ɗana ne, tunda akan idanuna ki kai Labour ɗinsa, amma hakan baya nufin zan saka masa Idanu, sai yanzu na fara tunanin tsayin shekarun da Aliyu ya kwashe a wannan duniyar ba tare da tunanin yin aure ba, kamar ko wanne namiji, nasan Aliyu nada lafiya balle nace, ke shaida ce how many times da zan kira Aliyu nace ya fitar da matar aure ya ce na bashi shekara ɗaya ko wata kaza? He is thirty-three years old now, but to this day there is no thought of marriage in his mind. Ni da kai na, na fara shakku da tantama idan ba lalata yaran mutane yake” wani irin ɗaci Mother taji a ƙasan zuciyarta, wanda ya sa ta fara ladamar yarda da Mijin nata da tayi. Magana ɗaya zai yi a janye Case ɗin amma yaƙi infact bai damu da matsalar ɗan nasa ba. Miƙewa tsaye ta yi tana kallonsa idanunta na sauyawa amma ta hana kanta zubar da hawaye ta ce.
“Court zata tantance mai gaskiya, kuma zata wanke Sheikh daga sharrin da ake masa” tana faɗin hakan tai waje cikin ƙonar zuciya. Bayanta yabi da kallo yana faɗin “If you give evidence that Aliyu is innocent, zan tsaya wajan karɓar masa haƙƙinsa Maryam” sosai kalamansa suka daki kunnanta amma ta share.
Tana zuwa parlour ta samu yaranta zaune sun zabga tagumi “Maimoon zugi driving nawa, Zeefa ke da Fattoumah ku zauna, I’ll be back 10:00 ki tabbatar kunyi alwala tare da sallah kun kwanta barci, kada na dawo naga kuna kallo ok” Fattoumah ta ce “Mother ina zaki? Yaa Lee har yanzu bai fito ba fa?” Mother ta ce “Kada ki takura Sheikh, idan kika takurasa sai ya shaƙeƙi tas kafin ya baki amsa, You better be careful, bye my babies”… “Bye Mother” fita sukai har lokacin wasu ƴan jaridun na ɓoye suna jiran ganin motar Sheikh ta fito. Maimoon na fita taja motar da gudu ta ɗauki hanyar da zata kaita Maiduguri road.
Tafiya kawai Danejo take babu takalmi kalbar kanta duk ta hargitse duk wanda ya ganta a wannan lokacin babu tantama zai kirata da mahaukaciya wacce ta jima cikin ciwon haukan. Tafi futu futu baya hayyacinta baki ɗaya,ita kanta ba zata taɓa tuna kwanakin data shafe tana tafiya ba, kuma abin mamaki ko gajiya ba tayi duk wanda ya ganta tambayar duniya idan zai mata ba zata taɓa kallon inda yake ba, balle kuma ta bashi amsa. Cikin ikon Allah ta samu kanta a gefen Rugar Rome inda take zuwa kiwo, tana zuwa nan ta yanke jiki ta faɗi babu numfashi. A hankali jikinta ya shiga Girgiza wani hayaƙi nafitowa ta jikinta a hankali hayaƙin ya cure waje guda, a haka ya rikiɗe zuwa suffar Prince.. idanunsa na kanta yana ƙoƙarin zuwa inda take yaji an daka masa tsawa wacce ya sanya ya tsaya da zuwa inda take, ko ba a faɗawa Prince ba ya san wane yake masa wannan tsawar domin shi kaɗai ya isa ya yi masa tsawa ya saurara.
“Ka Saurara Prince, kada ka kuskure ka taɓa Bil’adama ɗin nan” Prince ya juya idanuna ya sauka akan mahaifina wanda yake cikin suffar mutane cike da kamala. “Matata ce Abba, ina da ikon taɓa ta a lokacin da nasu kada ka hanani aikata hakan” Wanda aka kira da Abba ya kalli Prince ya ce “Ban san yaushe ka zama mai son zuciya ba, zuciyoyi nawa zaka baƙantawa? yanzu bayan wannan ƴar tayin kaje ka saka bawan Allah cikin masifa me ya yi maka?” Prince yana huci ya ce “Abba wannan bawan Allan shi ke shirin rabani da farin cikina, na jima da sanin haka shi ya sa na fara yin abin da ya dace, kashe sa naso yi ma..” Abba ya kalli Prince da mmki kafin ya ce “Shi ne daidai da rayuwarta, shi ne Bil-adam shike da ikon kasancewa da ita, ba kai ba da kake Hallitar Ubangiji ta ban ƙasa ina rabaka da son zuciya, koda muke aljanu hakan bai zama lasisin da zamu cutar da wata hallita dake duniya ba, ko me zakai ba zaka taɓa iya cutar da shi ba” A hargitse Prince jiki na rawa yana rikiɗewa zuwa suffar aljanu ya kalli Safwan ya ce “Kai ne ka faɗa masa abin da na aikata ko? Kai ke ko?” Kafin Safwan ya yi magana Prince ya ɗaga sa zuwa sama tare da buga ƙasa da jikin dutse yana ƙoƙarin sake ɗaga Safwan, Abba yai wata kururuwa hakan yasa Prince yin kururuwa shima lokaci guda suka koma aljanu…
08119237616…
🌈 IDAN BA KE 🌈
Zaku samu cikakken labarin a Arewabooks, kuyi searching sunan littafin ko username Arewabooks@Nimcyluv
8….
Ihu da kururuwa Prince ya din ga yi, sbd tsananin azabar da Abba ya ganawa masa. Cikin wata kakkausar murya wacce take nuna cewa ko a cikin Aljanu shi ɗin nada banne, kuma taƙadiri ne. “Akan aurena dake kan Halisa banƙi na kashe kowa na illata shi ba, daga ci hadda kai Abba, ba ruwana da kasancewar ka mahaifina, kada ka rabani da Danejona zakai babban kuskure zanyi ɓarna a duniya” Bakin Abba na fitar da hayaƙi kamar zai kunna wuta a ciki ya ɗaga hannunsa sama gaba ɗaya ya naɗe Prince cikin wata sarƙa da yana bakinsa ɗauke da addu’ar neman samun nasara akan Prince ɗin.
Duk ihun da yake bai hana Abba ya sarƙafesa cikin yanar ba idanunshi ya yi wata kala. Cikin ɗaga murya mai amo! Ya ce “Na raba aurenka da Halisa, babu kai ba ita, kuma a yanzu zan cire cikin dake jikinta mara imani mai muguwar zuciya” yana faɗin haka ya yi girgiza tare da ɓatar da Prince ɗin baki ɗaya daga wajan. A hankali Abba wanda Asalin sunansa ya kasance MURWAS ya sauke numfashi, tare da juyawa ya kalli Halisa dake kwance a ƙasa tana barci, juyawa ya sakeyi ya kalli Safwan dake kwance shi ma. Cikin nutsuwa wacce ba zata addabi dabbobin dajin ba ya yi Girgiza tare da rikiɗewa ya koma suffar mutane sak. Hannuna ya ya ɗauki Halisa Dajeno Rome da sauri ya nufi cikin Rugar Rome zuciyarsa fal farin ciki ganin yau ya raba ɗansa Bilal da Bil-adam.
Babu kowa cikin rugar kamar an share hakan yasa ya fara bin bukkokin Rugar da kallo kamar daga sama Hamma Yabi ya fito daga cikin ruga zufa na yanko masa hannunsa riƙe da ƙwarya maganin gaba ɗaya tunaninsa ya yafi wani wajan bai lura da mutumin dake tsaye yana binsa da kallo ba. “Jamɓanduna” Abba ya faɗa yana kallon Hamma Yabi dake ƙoƙarin yin gaba, tsayawa ya yi yana duba mutumin da ya ce masa Ina kwana, cike da mamaki ya ce “Jamni tawon” ma’ana lafiya. Abba ya jinjina kai ba tare da ya ce komai ba, jikin Hamma Yabi na rawa ya amshi Danejo daga hannun Abba kafin ya ce “Ikon Allah, ina kasa meta? Tsayin mako guda ta ɓace mana ba ita ba labarinta, shai Allahamdulillah” Murmushi mai sanyi Abba ya yi cikin nutsuwa ya ce “Ayyah ni ma yanzu ina iyu a cikin ruwan na ganta kwance gefen ruwan” cikin nuna jin daɗi da manta halin da Dada ke ciki wanda duk rashin Danejo ya haifar da haka ya ce “Shannu, wallahi shannunka kaji” kai kawai Abba ya ɗaga yana ƙarewa yanayin rugar kallo kafin ya juya bayan sun yi Sallama da Hamma Yabi yabar wajan. Yana fita ya ɓace a wajan baki ɗaya.
Dada na kwance bakinta na fitar da wani ruwa kamar dafara Shatu na gefe tana kuka tamkar ranta zai fita. A cikin wannan halin Hamma Yabi ya shigo cikin bukkar hannunsa ɗauke da Danejo wacce har yanzu take bacci. Jikin Shatu na rawa ta miƙe fuskarta cike da hawayen halin da mahaifiyarsu ke ciki, amma hakan bai hana Fuskarta baiyyanar da farin cikin da zuciyarta ke ciki ba na ganin Yayarta Danejo. Bakinta na rawa ta ce “Hamma ina ka samu Danejo, da gaske ita ce yanzu Dada zata tashi naji daɗi sosai” bai ce komai ba ya kwantar da Danejo gefen Dada idanunsa akanta ya ce “Maza kawo mini ruwa” Shatu ta miƙe da sauri tare da nufar tulo ta tsiyayi ruwan mai ɗan sanyi, tana bashi ya shiga shafawa Danejo yana kiran sunanta. A hankali ta sauke ajjiyar zuciya tana buɗe ido a nutse. “Danejo”… “Halisa” Shatu da Hamma suka kira sunanta lokaci guda,a sanyaye cikin sanyin jikinta kamar kullum ta shiga binsu da idanu. “Kin farka?” Kalmar Hamma ta sanya ta lumshe idanunta kana ta buɗe a hankali tana sake binsa da kallo kafin ta yunƙura zuwa zaune “Naga kuna ta kallona kamar za a cini ɗaya?” Murmushi Hamma ya yi ya ce “Munji daɗin ganinki Danejo, mako guda kenan mun rasaki kin ɓace daga idanunmu” da Mmki take kallonsa ɓata? Mako guda? Taje ina? Ita gani tayi kamar barci take mai ɗauke da mafarkai kala-kala. Shiru tayi tana ƙara sauke numfashi tare da fara tunanin maganar Hamma Yabi. “Hankalinmu ya tashi, Kullum Dada cikin kiran sunanki take, gashi yanzu ko buɗe ido ba tayi jikinta ya tashi ina tsoro kada mu rasa Dada kamar yadda muka rasa Baffa” ambaton sunan Dada ya saka Danejo saurin juyawa zuwa gefenta manyan idanunta ta buɗe “Dadata” ta furta a ruɗe ganin yadda Dada ta ƙanƙame jiki, idanunta na kafewa kamar mai shirin mutuwa cikin muryar kuka ta ce “Na lalashe ni Danejo Dadata kada ki barni kada ki mutu do Allah,Kada kibi Baffana” sai girgizata take amma ina Dada ko motsi ba tayi.
Da sauri Hamma ya fita zuwa bakin hanya tare da samu abin hawa yana zuwa suka ɗauki Dada a mota zuwa asibiti, asibitin babu jama’a sosai. Dr Hamza na zaune a Office gabansa cike da kuɗi ya kalli Dr Iliya ya ce “Kawo maganin nan ya yi mana rawa sosai, na ƙara tura saƙo zuwa ɓangaren lafiya akan magungunan da suka bayar ya ƙare, sbd cututtukan da suke damun jama’ar rugar, ina saka ran cikin satin nan za a kawo maganin” Dr Iliya ya numfasa yana jinjina kai kafin ya ce “That’s good. Amma da gaske maganin ya ƙare ne?”.. “No ba wani ƙare wa da ya yi, har yanzu ban bawa ko mutum ɗaya ba” cikin fahimta Dr Iliya ya kalli Dr Hamza yana faɗin “huh! za a kawo maganin sauro kyauta ma a raba, sbd yawaitar Maleriya”
“Na samu Information ɗin hakan, amma idan an kawo gidan sauron, asibitin nan za a Ajjiye mu zamu raba, so za a bawa Kowa akan 1500 each one” waro ido waje Dr Iliya ya yi kafin ya ce “baka ganin zamu iya samun matsala, tunda kyauta gwamnati ta bayar?” Ɗaga hannu Dr Hamza ya yi yana dakatar da Dr Iliya da faɗin “Hakan shi ne ribarmu, ba za mu yi musu bauta ba kamar wasu bayi, they have to pay”
Kafin Iliya ya yi magana Hamma Yabi ya faɗo office ɗin da sauri cikin tsawa Dr Hamza ya ce “Malam ya haka zaka faɗo kamar wani mahaukaci? Me ya sa duk fulanin nan baku da ilimin zaman rayuwa ne, baku san yadda ake mu’amala ba?” Hamma baya gane zancan nasu ya ce “Don Allah ka taimaki Dadarmu, kada ta mutu cikin wannan halin ita kaɗai ta rage mana, sau wajan goma ina zuwa” “Idan munje kanta lafiya zamu bata kenan? Ko zamu hanata mutuwa? Zan maka last warning Kada na sake ganin ƙafarka cikin asibitin nan, na faɗa maka bamu da maganin ko ɗaya me kake so nayi maka? Haba kuna yi mana adalci mu likitoci sai an bimu a hankali mai ya sa zan zuciyarku ya yi yawa ne?” kasa magana Hamma yai sbd Hawayen daya cika masa idanu me ya sa su Fulani ake musu kallon mahaukata wanda basu san me suke ba? Akwai wani bambanci a jikinsu wanda ya bambanta su da sauran jama’a ne? Juyawa ya yi yana zuriyarsa babu daɗi. Danejo na ganinsa ta ce “Hamma ya naga ka daɗe, numfashi Dadata zai gudu ka taimaka, ina masu bada lafiya ɗin?” A hankali ya kama hannunta ya riƙe yana shafa kanta dake ɗauke da suma mai kyau can ƙasa ya ce “Muje gida, ba zamu ƙara zuwa asibitin nan ba, Allah ya a bamu Kuɗi mu kaita asibitin burni” shiru kawai tayi tana kallonsa tare da son fahimtar abin da yake nufi a haka suka koma gida jiki babu daɗi, kwana sukai ba su yi bacci ba, Shatu kawai ta runsta sbd ƙarancin shekarunta. A daren Danejo ta sanyawa ranta zata sai da nono iya iyawarta ta tara kuɗi masu yawa akai Dada asibiti. Hakan yasa ta tashi da asuba ta tatsi kindirmo a ƙwayar gari na fara haske ta nufi cikin burni wajan Abti America.
Mother ce ke sakkowa daga upstairs kunnanta maƙale da waya idanunta sanye cikin farin glasses ta fito a Barrister Maryam ɗinta sak. A hankali ta ce “Na riga nayi reporting case ɗin, idan ba a samu good evedance ba akan wanda suka kawo ƙarar Aliyuna, kai tsaye zan maka ko wacce ƴar banza a court dama kawai nake jira” daga cikin wayar aka ja numfashi tace “Barrister Maryam kasa aje court,idan akaje to kin bawa duniya damar zata fahimci halin da ake ciki,abi komai a sannu” ɓayayyiyar ajjiyar zuciya Mother ta sauke idanunta na sauka akan Zeefa da Fattoumah “Ok za mu yi magana bari naje wajansa Allah ya sa ya yi magana, al’amarin Sheikh na bani tsoro yana bani mamaki” ƙara tattaunawa sukai kafin sukai sallama. “sannu da sakkowa mother” idanunta akan Plasma ɗin da suke kallo ta ce “Fattoumah sau nawa zan ce bana son kuna kallon zee world ne? Ashe ban isa daku ba ko?” A sanyaye Fattoumah ta ce “We’re sorry Mother ba zamu sake ba” zama tayi ta ce “Change the channel immediately Mamana” Sauya channel Fattoumah ta yi zuwa Aljazeera tana faɗin “Ok Mother” kallonsu ta yi sosai ta ce “Where’s Maimoon and Auta?” Zeefa ta bata amsa da “She’s inside the kitchen, Auta barci take” Mother ta ce “Bana son barcin yamma taso mini ita” tana faɗin ta miƙe tare da nufar kitchen daga bakin ƙofa ta tsaya tana kallon Maimoon dake haɗa coffee ta ce “Ina Lunch ɗin Sheikh?”… “Gashi a tray mother bari na kai masa” tsareta tayi da idanu ta ce “Bani nan” tray ɗin lunch ta bawa Mother tana ci-gaba da aikin gabanta.
Haɗaɗɗan part ɗinsa ta nufa tun daga nesa ƙirar arar Sheikh Muhammad didat ta ratsa cikin kunnuwanta da Mmkin fal fuskar Mother ganin ƙofar shiga parlournsa a buɗe. Ƙamshin air-cod ya ratsa cikin hancinta. Tana shiga idanunta ya sauka akan Umar-khan dake zaune gabansa ɗauke da system yana duba wani abu, ganin Mother ya sa Umar-khan saurin miƙewa tsaye ya ce “Sannu da zuwa Mother” “Yawwa Umar-khan ina Aliyun?” Hanyar da zata sadaka da bedroom ɗin Sheikh ya kalla yana faɗin “a Parlour na samesa lokacin da nazo, ina fara yi masa magana akan wannan case ɗin ya tashi ya shige bedroom har yanzu bai fito ba” jinjina kai tayi ta nufi bedroom ɗin, babu abin da bedroom ɗin yake sai ƙamshin turarensa ROJA wanda ya a jima da kama ɗakin duk da cewa bai fiye rayuwa a cikin gidan iyayen nasa ba, yafi rayuwa a Madina idan yana ƙasa Nigeria kuma yafi rayuwa a gidan Hakimi. ba kowa nan ma a bedroom ɗin sai tsarin ɗakin da Mother tabi da kallo wanda a kullum yake Sauya mata, komai na ɗakin fari ne tas, ɓangaren clothes, shoes, perfumes. Komai daban yake. Juyawa tayi zuwa parlourn tana faɗin “Umar-khan Aliyu baya nan fa? Ko dai ya tafi gidan Hakimi?” Umar-khan yai shiru ya ce “Bashi da ikon fita, kamar kullum ƴan jaridu na waje ta ko’ina maybe yana Library ɗinsa” sai a lokacin ta tuna da Library tana zuwa ciki ta samesa zaune akan wata ƙyakkyawar kujera wacce take juya kanta da kanta ya rufe idanunsa, sumar kansa ta ɗan bayyana sbd yanayin naɗin rawanin nasa wanda ya yi da farin hirami. Hannunsa harɗe a ƙirji. Zama tayi kujerar dake kusa dashi tana kama hannunsa ta ce “Abbana Babana” ajjiyar zuciya Sheikh Aliyu Haydar ya sauke sbd jin sunan da Mother’s ta kirasa da shi amma ya kasa buɗe idanunshi domin baya son ta fahimci halin da idanunsa ke ciki wanda sune kaɗai suke fallasa raunin zuciyarsa. “Buɗe idanunka mu yi magana Babana, ba zan taɓa bari kayi gidan yari ba, zan tabbatar da kai a matsayin mai gsky ba zaka wulaƙanta ba” nan ma shiru ya yi mata bai ce komai ba kamar yadda ta tsammata. Hawayen da take maƙalewa ne ya kwance mata wanda ya zuba a tafin hannun Sheikh. Da sauri ya ƙankame hannunsu dake riƙe da nata yana buɗe idanunsa a hankali wanda suka sauya daka rinewar da sukai. Fararen idanun nasa ya ɗora akanta ganin hawaye a Fuskarta ya ƙara sashi cikin damuwa amma sam hakan bai bayyana a garesa ba. “Kayi magana Babana rashin maganarka shike sawa a dinga tunanin baka da gasky, zuciyata ba zata jure ganinka haka ba” Kallonta yake har lokacin bai ce komai ba. Ganin bashi da niyyar magana yasa Mother fashewa da kuka sosai tana miƙe tsaye da sauri ya riƙe hannunta gam! Yana miƙewa tsaye jallabiya ce jikinsa mai kyau da tsada ga laushi da tsantsi. Kai ya fara Girgiza mata yana matse hannunta sosai babu abin da Sheikh yake ƙauna sama da mahaifiyarsa sai Father daga su Hakimi sune duniyarsa. Hannunsa mother ta riƙe ta ce “Try to speak Sheikh ban damu ba nasan zan fahimce ka, zamu Court bani da wani proof da zan kareka, mene gasky?” Riƙe hannun Mother Sheikh ya yi tare da fara buga ƙafa yana ƙoƙarin buɗe bakinsa. Ganin haka yasa Mother taimaka masa wajan riƙe hannunsa tana faɗin “Ahha say something, speak Babana, say it” hannunta duk biyun ya kama ya riƙe yana runtse idanunsa sai buga ƙafa yake tuni hawaye ya fara cika idanunsa. “Yee… Ƙaƙƙƙaaa… M…mmm” kai ta ɗaga masa tana shafa kansa a fisge bayan ya buga ƙafarsa da ƙasa yana saka hannun Mother a bakinsa ya ce “Babbbban akaita ba, bbbb ba zan taɓa yin yin yin haka ba mother” yana faɗin hakan yana ƙara saka hannun Mother a bakinsa duk ya jiƙa mata hannu da yawunsa mai ƙamshi a ƙoƙarinsa na ganin ya yi magana daidai waya baiwa ta Sheikh idan koyarwa zai yana samu maganarsa ta fita yake fara karatu cikin sauri baya tsayawa sai ya gama yana gamawa baya ƙara cewa komai yake fita daga hall. Wani irin rauni ya kama zuciyar Mother tausayi da ƙaunar Sheikh ya ƙara wanzuwa a zuciyarta wacce irin larura ce haka wacce bata barin har babban mutum? Zare hannunta ya yi domin har ransa bai san lokacin daya saka hannunta a baki ba a hankali ya juya zai bar wajan da sauri mother tana goge hawaye ta ce “Aliyu” cak ya tsaya tana ƙoƙarin magana Umar-khan ya shigo wajan da sauri gaba ɗaya suka bisa da kallo Umar-khan ya ce “Sheikh na shirya mota a ƙofar baya, yanzu zamu bar gidan nan jami’ai na hanyar zuwa nan zasu kamaka” ko motsawa Sheikh bai ba shi dai ya san ba zai taɓa hana abin da Ubangiji ya tsara afkuwa ba. “Jeka Aliyu ka bisu su fitar dakai Sheikh” Mother ta faɗa tana jan hannunsu ganin haka yasa ya bita har zuwa bakin wata sabuwar mota shiga ya yi. Drivern yaja, Umar-khan shima ya shiga mota, Saif-Wazir ya shiga wata motar. Motar ƙarshe kuma Ishaq-hakim ya shiga kai tsaye suka nufi wata hanya ta daban. Sbd gujewa haɗuwa da jami’an da kuma ƴan jaridu, kasancewar duk sunyi connecting wayoyinsu dana juna yasa Umar-khan gyara bluetooth na kunansa ya ce “Saif-Wazir” Saif ya amsa da “Ina kan layi” haka Ishaq-hakim da kuma Drivern Sheikh. Cikin jin daɗi Umar-khan ya ce “Saif-Wazir idan mun isa Shatalelen gidan gwamna kabi hanyar Amado bello way” Saif-Wazir ya ce “Noted bro” Umar-khan ya ce “Ishaq-hakim kabi hanyar Asibitin nasarawa, Drivern Sheikh Kabi hanyar ƙofar nasarawa,ni kuma zanbi hanyar kasuwar tarauni, gaba ɗaya hanyoyin zasu haɗamu a titin Dawaki roud zamu sauka gidan Hakimi..” haka duk suka amince suna zuwa Shatalelen gidan gwamna ko wacce mota ta ɗauki hanyarta suka ɗauke tunanin jami’an tsaron daka hanyar da zasu bi, Sheikh na bayan mota ya zubawa ikon Allah idanu a haka suka ƙarasa Dawaki roud motocin suka haɗu waje guda kai tsaye suka ƙarasa gidan Hakimi. Sheikh na fito da ƙafarsa waje aka riƙe hannuna tare da saka masa sarƙa kamar daga sama yaji ance “You are under arrest…..
08119237616.
🌈 IDAN BA KE 🌈
Nimcyluv sarauta
E.O.W
9…
“You’re under arrest?” Umar-khan daya fito daga cikin mota ya ƙara maimaita kalmar ɗan sandan wanda ya yi ɓadda kama cikin kayan gida. Ɗan sandan ya kalli Umar-khan fuska ba walwala ya ce “As you heard” Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un! Shi ne kalaman da Saif-Wazir ya faɗa domin Umar-khan kasa motsawa ya yi idanunsa a ƙasa baya taɓa jin zai iya haɗa idanu da babban mutum kamar Sheikh Aliyu Haydar cikin wannan halin. “Yallaɓai kayi mana afuwa mu shiga ciki mu tattauna, ba sai an tafi da Yaa Lee police station ba please” Wanda aka kira da Yallaɓai ɗin ya ce “Stop interfering with our work, because we know our work well, kuma wane ya faɗa maka police station zamu kai Aliyu Haydar Aliyu? State C.i.d zamu” da tsoro sosai akan fuskar Saif-Wazir ya ce “C.i.d? Wajan da ake ajjiye manyan masu aikata criminals, ƴan fashi,ƴan daba, Kidnappers Sheikh bai dace da wannan wajan ba, don Allah kada ko taɓa mana martabarsa…..,” Ishaq-hakim ya katse Saif-Wazir da faɗin “har yanzu ba a tabbatar da abin da ake tunanin ya yi ba, zargi ne kawai” Wani daga cikin ma’aikatan ya ce “Say whatever you want to say,We must arrest Sheikh Aliyu Haydar Aliyu” cikin zafin zuwa Ishaq-hakim ya kalli ɗan sandan yana nu nasa da hannu ya ce “Idan ta ƙamar kai uniform ne a jikinka mu kuma mune da garin, wallahi idan ya tabbata Sheikh bashi da laifi sai munyi Shari’a da kai” yana faɗin hakan ya juya da sauri ya nufi babban gate ɗin shiga gidan Hakimi, kasancewar daman a ƙofar gidan suke. Sheikh dai na tsaye tamkar ba akan sa ake wannan muƙabalar ba, ya tsorawa hannunsa dake maƙale da ankwa ido shi kaɗai zai iya fasalta halin da zuciyarsa ke ciki sai kuma Abba Hakimi dake iya fahimtar raunin zuciyar Sheikh ɗin lokaci guda. Suna ƙoƙarin saka Sheikh cikin wata baƙar mota mai kyau wacce babu wanda zai iya ganin Sheikh ɗin a ciki gyarar muryar Abba Hakimi ta karaɗe wajan. Cikin mutuntawa da tarin ladabi duk jama’ar wajan suka sunkuyar da kansu ƙasa. A hankali Sheikh ya ɗago kansa tare da sauke ganinsa akan Abban nasa Hakimi, raunin idanun Sheikh ya bayyana sakamakon zuwan Hakimi wanda shi kaɗai ya fahimci hakan, shi kansa ya kasa yiwa Sheikh ɗin gwaggwaran kallo, idan akwai abin da Hakimi ya keso a rayuwa bai shige Sheikh Aliyu Haydar Aliyu ba, son da yake masa ko ƴar ƴan cininsa su Ishaq-hakim ba ya yi wa soyayya ce ta musamman tun Sheikh na zanin goyo.
Zame ido Abba hikima ya yi daga kan Sheikh yana mayar wa kan jami’an tsaron da suke jiran suji mai zai ce, domin su basu da wani laifi akan aikinsu suke komai, ko da basu aikata hakan ba, gwamnatin ƙasar Madina zata ɗauki mataki, matakin da zaiwa kowa ciwo da zafi a zuciya. “Zaku iya tafiya da shi” Abba Hakimi ya furta a nutse yana shafa sumar Sheikh tare da ɗaukan hiraminsa ya fara naɗa masa sabon rawani. Da sauri Ishaq-hakim ya ce “Abba ta ya ya zaka bari a tafi da Yaa Lee? Kai ne wanda nake tunanin zaka dakar dasu daha tafiya da shi?” Murmushi mai laushi Abba Hakimi ya yi yana ɓoye damuwar ransa kafin ya ce “Mulki daban, hukuma daban Ishaq-hakim a barsu suyi aikinsu muma muyi namu” Umar-khan juyawa ya yi tare da shiga mota ya kifa kansa jikin Kujera ba zai iya zuba idanu a gabansa a tafi da Sheikh ba. Saif-Wazir idanunsa ya yi jajur gaba ɗaya yanayin baya yi masa daɗi. “Aliyuna” Abba Hakimi ya kira sunan a taushashe yana kallon Abban nasa, cikin kulawa ya ce “Kayi haƙuri, ƙarya fure take bata ƴaƴa, lashakka gaskiya zatai halinta ka ɗauka kai ni kana daga cikin bayin da Ubangiji zai gwada imaninsu” ƙanƙame hannun Abba Hakimi Sheikh Aliyu Haydar Aliyu ya yi, hakan ya tabbatar wa da Abba Hakimi Sheikh ya amince da zan can nasa. Sakin hannunsa ya yi gaba ɗaya jikin jami’an tsaron ya yi sanyi bisa dole suka saka Sheikh cikin mota tare da tafiya da shi.
“Ishaq-hakim kawo mota, zuwa wajan Aliyu da Barrister Maryam” jinjina kai kawai Ishaq-hakim ɗin ya yi, tare da buɗewa Abba Hakimi bayan mota ya shiga, Saif-Wazir da Umar-khan suka bi bayan motar su Sheikh domin suji inda zan can zai tsaya.
Mother na tsaye ta kasa zama sai number ɗaya daga cikin samarin take gwadawa amma basa ɗagawa, hankalinta ya ƙara tashi fiye da ko yaushe tunanin abin da ya samu Sheikh ya wanzu a zuciyarta. Upstairs tayi da sauri kai tsaye part ɗin Father ta nufa yana zaune a ƙawataccen parlournsa mai kyau, hannunsa riƙe da jarida cikin baƙin ciki yake karanta inda aka saki zan can Sheikh tare da photonsa,gaba Al’amarin ya wanzu a duniya dama media baki ɗaya. Shigowar mother ya sanya Father Kallonta yana jiran jin abin da zata faɗa wannan karan. “Barrister Maryam lafiya ki kai mini tsaye?” Da mmki ta dubesa sosai kafin ta ce “lafiya kake tambaya? Wai me Aliyu ya yi maka da baka kula da al’amarinsa ne?” Hannu ya ɗaga mata ya ce “Saurara Barrister Maryam ni na aiki Aliyu ya aikata hakan? ko da izinina ya ke lalata yaran jama’a yana musu fyaɗe?At Aliyu’s age, I will not be surprised at all that he did, ba a shaidar ɗan yau Maryam da ace yana da mata babu mai zarginsa da aikata haka” tarin mamaki da ya gama cika Mother ya sanya ta kasa cewa komai sai kallon Father kawai da take “Aliyu ɗan ka na cikinka kake wa wannan shaidar, shaidar iyaye ita ce shaidar Allah fa, banda na san kai ne mijina kai ka samar da Aliyu da babu abin da zai sanya nace ba kai ka haife shi ba, amma kaje lokaci ne zaka fahimta idan baka son sa muna son shi” kai kawai ya girgiza mata yana faɗin “Zaki iya zuwa ki nemi Mahaifinsa a waje, tunda kina tantama” kafin Mother tayi magana Fattoumah ta shigo Parlourn kallon iyayen nata tayi ganin kamar hayaniya suke, fahimtar hakan yasa Mother yin murmushi ta ce “Mamana ya akai? Ban hanaku zuwa waje ba without permission zan fara bulala fa” marairaice fuska tayi ta ce “Am sorry mother ina ta sallama tun ɗazo” kallon yadda Fattoumah ta tsare Father da ido mother tai cikin sauri ta ce “Ya akai to?” Da sauri ta ce “Abba Hakimi yana Parlour kizo ke da Father” tana faɗin hakan ta juya da sauri tana jin Father na faɗin “Fatimah.. Zarahh..!!” Amma tai banza da shi, Fattoumah irin yaran nan ne masu riƙo da kuma kishin iyayensu mata gaba ɗaya taji abin da Father yake faɗa akan Sheikh.
Fita Mother tai tana sakkowa fuskarta ɗauke da fara’a tasan tun da taga Abba Hakimi to Sheikh yana can gida cikin kwanciyar hankali. A ƙasa ta zauna tana gaida shi ya amsa a nutse kafin ya yi magana Father ya fito shi ma ya zauna saman Kujera ya ce “Sannu da hanya Abba Hakimi” kai kawai ya jinjina idanunsa akan Fattoumah yana faɗin “Matar zo nan mana ke dawa haka?” Turo baki tayi idanunta na sauyawa ta ce “Mijin me ya sa Father baya son Yaa Lee?” Sa mamaki Hakimi ya kalli Father yana faɗin “Aliyu ya akai haka? Me ya sa kake barin raya su san abin da ke zuciyarka ne?” Father ya ce “Abba Hakimi ta ya ya zan ƙi ɗana? Shirman Fatimah ne” da sauri Fattoumah ta ce “Da gaske nake Mijin,ina jin yana faɗawa mother wai a nemo mahaifin Yaa Lee kuma ai ba kyau ƙarya” surutun Fattoumah ya jijjiga Mother bata taɓa haifar yarinyar mai kaifin bakin Fattoumah ba. “shige ki bamu waje Mamana kafin ranki ya ɓaci laɓe kike mana kenan?” Turo baki Fattoumah tayi tace “Mother kawai ki nemowa Yaa Lee Abbansa wanda zai so shi tunda father baya son sa” Abba Hakimi da Mother suka kalli juna da sauri kuma suka janye idanunsu ko wanne tunani fal ransa. Tsawa Mother ta yiwa Fattoumah ta tafi ɗakinu Maimoon tana sakin kuka ta fara bori a ƙasan carpet.
A nutse Abba Hakimi ya kalli Mother ya ce “Aliyu yana state c.i.d Barrister Maryam” a ruɗe Mother ta Kalli Hakimi hankali tashe take faɗin “An kama Babana? Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un wallahi sharri ne ba gaskiya ba, kuma zan tabbata da hakan” Hakimi ya ce “Samu nutsuwa Barrister Maryam, mu duka ba zamu ja da ikon Allah ba, kuma da hujjar kare Aliyu, shi ya sa nazo naji ko ya faɗa muku wani abun?” Father ya yi dariyar baƙin ciki ya ce “Wannan ne zai magana? Ko ya yi bata da wani amfani me zamu fahimta banda, A…Aaaa…ƙikkkk… Yeee gaba ɗaya Aliyu bashi da amfani a rayuwarmu, naji baƙin cikin samunsa Matsayin ɗa namiji” wani baƙin ciki ya tukare zuciyar Mother idanunta na cika da hawaye ta ce “Sai yanzu na fahimta larurar Aliyu ta sanya kake ƙinsa? Ubangiji ya ɗora masa shi nake roƙa kuma ya ye masa” Abba Hakimi ya numfasa kalam Father sun bashi mmki a haka ya share ya ce “kayi babban kuskure Aliyu, kuma Sheikh abin Alfaharin duk wani ɗan Kano dama Najeriya ne, muhimmancin bai tsaya iya ƙasar shi ba, har ƙasa mai tsarki.. Allah ya kyauta wata rana zaka gane gaskiya lokacin da za kaji kunya” juyawa kan Mother yai ya ce “Akwai abin da ya faɗa miki ne, ina son shigar da maganar zuwa court ne” Mother ta ce “Yana cikin ƙoƙarin fahimtar dani suka taho wajanka ya faɗa mini bashi ya aikata ba, kuma ni ma na shigar da ƙara ni zan tsaya masa tare da Barrister Zainab” wayar Mother ce ta fara ringing ganin sunan Umar-khan ya sanya ta ɗauka cikin sauri ta miƙe tana faɗin “Ohhh ok on our way” kashe wayar tayi idanunta akan Abba Hakimi ta ce “Umar-khan ya ce muzo yanzu al’amarin ya shige tunani” da sauri ta nufi ɗaki tare da ɗakko mayafi da key car.
Abba Hakimi da Mother suka nufi state c.i.d hankali a tashe Maimoon da Zeefa da Fattoumah sai kuka suke a rayuwa suna ƙaunar yayan nasu duk da babu wata jituwa a tsakaninsu. Ko abinci suka kasa ci sai sallah kawai da suke suna addu’ar Allah ya kuɓutar da Sheikh ɗin. Hankali kwance Father yake zaune yana waya da babban amininsa ko da wasa bai masa magana akan matsalar da suke ciki ba, duk da cewa al’amarin ya gama zaga ko’ina a faɗin Nigeria.
A kiɗime Mother take bin su Saif-Wazir da kallo ganin yadda idanunshi ya yi jajur alamar kuka suka sha. “Ina Babana ina Aliyu mai ya faru da shi?” Shiru Saif-Wazir ya yi mata, ta juya kan Umar-khan ta riƙe wuyansa sosai cikin faɗa ta ce “Where’s my son Umar-khan? Ina Aliyuna?” Umar-khan ya yi ƙasa da idanun shi ba tare da ya ce komai ba. Sakin Umar-khan tayi ta nufi wajan Ishaq-hakim ta ce “Ishaq-hakim faɗa mini gsky ina Aliyu me akace yana da gsky ko? Ba aikata abin da ake zarginsa ba?” Hannunsa ya ɗaga tare da nuna mata wani waje da sauri ta juya Idanunta ya sauka akan Sheikh Aliyu Haydar Aliyu wanda aka cire masa Jallabiyar jikinsa aka ɗauresa da Sarƙa tun daga wuyansa hannunsa zuwa ƙafarsa farar fatar jikinsa tayi jajir bakin Ishaq-hakim na rawa ya ce “Mother Sheikh ya amsa laifin da ake zarginsa ya tabbatar shi ne ya lalata ƴan matan hadda ciki…..
IDAN BA KE… labari ne da kuka daɗe ba kuci karo da irinsa ba, ƙaddarar labarin akan soyayya ne mai tsayawa a zuciya da saka shauƙi a zuƙatan masu karatu….. Tsammaci abin da baka tsammani salo na musamman🫣💋 08119237616.
🌈 IDAN BA KE 🌈
Arewabooks@Nimcyluv
10….
Kasa magana Mother tayi sai Ishaq-hakim da tabi da kallo tana son gasgata abin da yake faɗa. “Ta ya ya Sheikh zai amsa laifi fyaɗe? Laifin da duk duniya ta san ba zai iya aikatawa ba?” Ta faɗa a fili tana sakin wani raunataccen kuka mai tsayawa a zuciya ba zata iya kallon Sheikh cikin sarƙa a ɗaure ba, kamar wani ɗan fashi ko Kidnapper. Umar-khan ne ya kama Mother wacce take ƙoƙarin zubewa a wajan sbd kukan da take idanunsu ya yi jajur ya ce “Ki daina kuka Mother, wata kila Sheikh ya amsa laifin ne sbd rashin mafita, mu duka abin ya zo mana cikin wani sabon yanayi wanda bamu taɓa riskar kanmu ciki ba, Ubangiji ka ɗai ya san gaskiya kuma shi muke roƙa ya fidda Sheikh Aliyu daga cikin wannan jarrabawar” gaba ɗaya zuciyar Mother ta karaya tunaninta ya tsaya cak duk inda take neman wata hujja ta kare ɗan nata babu.
Da hannu bibbiyu ta riƙe Umar-khan ta ce “Kai ne kake tare da Babana Umar-khan, ka taimaka mini nasan kasan Aliyu ba zai iya aikata hakan ba, yana tsare imaninsa yana amsar rayuwa a duk yadda ta zo masa” Umar-khan ya mayar da hawayen dake cika idanunsa kafin ya zaunar da Mother ya ce “Be patient Mother, muyi addu’a kawai amma da ace zan iya bada shaida, da iya abin da zan faɗa ya isa ya wanke Sheikh daga cikin zargi”
“That’s enough, this is not a place to make noise” Wani daga cikin jami’an tsaron ya faɗa yana daka musu tsawa.
Sai a lokacin Abba Hakimi ya yi ajjiyar zuciya domin shi ma Al’amarin ya girgiza shi fiye da tunanin kowa, zuciyarsa shi zafi take masa sosai. A nutse ya juya ya kalli Ishaq-hakim ya ce “Ka mayar da Barrister Maryam gida yanzu, ka ce ina buƙatar ganin Aliyu immediately” da girmamawa Ishaq-hakim ya amsawa mahaifin nasa, idanunshi akan Mother yana jiran ta miƙe.
Cikin kuka ta kalli Abba Hakimi ta ce “Ina son nayi magana da Aliyu Please Hakimi” Kafin Abba Hakimi ya bata amsa wani daga cikin Jami’an tsaron ya ce.
“No way Madam” tana share hawaye ta ce “Don girman ka bani 2 minutes nayi magana da ɗa na, ina son tambayarsa, tare da kwantar da hankalin shi” cutting nata out ya yi da faɗin. “Isn’t necessary Maaah…” A ƙagauce Abba Hakimi ya ce “take her out Ishaq-hakim” Mother na kuka sosai tana kiran sunan Sheikh Aliyu aka fitar da ita waje, Aliyu shi ne rauninta ka kaf cikin yaranta tafi ƙaunarsa duk abin da Mother ta mallaka daga cikin dukiyar iyayenta Aliyu ta bawa, She owned all her property for him, Lands, houses, companies, all signed in the name of Aliyu’s property.
Su Mother na fita Abba Hakimi ya kalli jami’an tsaron cikin murya mai taushi ya ce “Kun samu hujja mai ƙarfi da kuka kama mini ɗa na?” Ɗaya ya sunkuyar da kai cikin girmamawa ya ce “Har yanzu bamu da hujja, amma a duk bin ciken da mukai Sheikh ƙara shiga ciki yake, yaƙi buɗe baki ya yi magana, gwamnatin Madina da universityn ƙasar sun matsa akan kwana biyu suka bayar idan ƙasa Nigeria bata ɗauki mataki ba, zasu ɗauka da kansu domin su irin wannan cases ɗin kai tsaye suke bincike kuma hukuncin kisa ne” runtse idanu Abba Hakimi hukuncin kisan ya daki zuciyarsa ainun. Umar-khan da bakinsa ke rawa tun ɗazo sbd masifa ya ce “Ita kanta gwamnatin Madinan idan bata da hujja dole ta haƙura, ina masu kawo ƙarar? Daga ina wannan zan can ya fito? Ina ƴan matan da akaiwa fyaɗen suke?”
“Stop raising your voice, we are working on our system, nan ba Court bace” Umar-khan zai sake magana Abba Hakimi ya yi gyara murya kafin ya ce “Ka bari abu komai a nutse, shi ya sa na mai da Barrister Maryam gida” Saif-Wazir dai na tsaye duk yadda suka so a basu Sheikh su yi magana hanawa akai. Kuma a gobe za a kaisa court domin fara gabatar da Shari’a tun da case ɗin ya zo da hargitsi. Haka suka komai gida zuciyoyin kowa babu daɗi.
Sheikh na zaune daga shi sai single da wani farin trousers mai laushi tunda yake a duniya babu wanda ya taɓa ganin tsari da zubin halittarsa sai yanzu, an tuzarta shi tuzarcim daya har zuƙa kuturwar zuciyarsa, shi kaɗai sai tsuma yake shi da ko sauro baya so baya ƙaunar yaga baiwar halittar da tsaraicin jikinsa, yana tsarkake jikinsa domin sirrinsa ne, amma yau da wanda ya dace da wanda bai dace ko wanne tom and jerry gani yake abin ya yi masa zafi ainun. Dalilin daya sanya ya amsa laifin kenan ba tare daya shirya hakan ba.
Mother na komawa gida ta samu Fattoumah na zaune ita ɗaya a Parlour da sauri Fattoumah ta ce “Mother ina Yaa Lee? Ba zai dawo ba?” Murmushi mother ta yi tana ɓoye damuwar ranta ta ce “Ya dawo mana Manana, yan gidan Abba Hakimi where’s your sisters?” Da hannu ta nuna mata part ɗinsu, Mother ya kama hannunta suka shiga ciki. Yaran duk suna zaune sanye da hijabi sunyi shiru bayan sunci kuka sun ƙoshi, cikin faɗa ta ce “Maimoon, Zeefa what’s this? Kuna da hankali zaku shigo ɗaki kuyita kuka kamar anyi mutuwa, Depression kuke son ya kamaku ko mene?” Gaba ɗaya suka miƙe tsaye jikinsu na rawa za su yi magana ta ɗaga musu hannu ta ce “Ku fita a nan wajan, maza aje a kunna kallo ayi” fita gaba ɗaya sukai jiki babu ƙwari mother ta bisu da kallo tausayin su na kamata tasan duk sanadin Aliyu Haydar suka shiga wannan damuwar. Kuma ita idan har ƴar halak ce ba zata sake zuwa wajan Father ba akan maganar Sheikh Aliyu ɗin ba.
Tana fitowa daga cikin bedroom ɗin upstairs ta haura zuwa nata bedroom ɗin wayarta ta ɗauka ta shiga kiran Barrister Zainab akan gobe zasu shiga Court sun daɗe suna waya kafin ta kira Yaya Halima anan ta kwantar mata da hankali ta ce ita ma ta nan zuwa dan sunyi nisa ne. Har Mother ta miƙe da sauri kuma ta koma ta zauna domin gaba ɗaya ta manta da batun Jadda cikin sauri ta danna numberta wayar ta jima tana ringing kafin a ɗaga a fusace akace “Allah dai yai gutsi gutsi da duk wanda yake addabata wannan masifar har ina, ba lallai mutum yaga Annabi ba” A hankali Mother ta ce “Jadda ni ce Maryam” Jadda ta ce “Wata abace Maryam kuma? daga wacce duniya mena haɗa dake?” Shiru Mother can kuma ta ce “Mahaifiyar Sheikh Aliyu” Jadda ta zabga salati da duk ƙarfinta ta ce “Yanzu Maryam cewa nayi ban gane ki ba? Masifar gaisuwa ce bana so, Ina shi Aliyu yana can Madina ɗin ne?” Mother ta ce “Baki san meke faruwa da shi ba?” Jadda dake kishin giɗe tayi saurin Miƙewa zaune tana faɗin “Allah ya isa, dake Maryam da shi Aliyu Allah dai ya isa wani abu ne ya samu Sheikh bani da labari?” Kafin Mother tai mgn father ya ƙwace wayar tare da kashewa baki ɗaya ya kalli Mother ya ce. “Yanzu Barrister akan wannan maganar zaki haɗani da Mahaifiyata? Su kike ta tsine mini tunda kin san bakinta ba shi da tsarki wajan sakin magana da kwasa ta” banza tai masa ba tare da ta ce komai ba, yana ƙoƙarin sake magana ta miƙe tsaye tana faɗin “Idan ka gama ka ajjiye mini wayata, I have something to do with my phone” tana faɗa ta shige toilet domin zuciyarta a kusa dake da shi. da idanu ya bita kana ya ajjiye wayar yana mmkin halin mata a wasu lokutan.
Gari na waye Barrister Zainab ta zo suka fita zuwa State C.i.d ita da Mother abin mamaki gaba ɗaya ƴan jaridu sun cika gidan Redio, da t.v kowa yana jiran a fito da Sheikh Aliyu Haydar Aliyu. Cikin nutsuwa Barrister Zainab dake driving ta kalli mutanan ta ce “Am still wondering ta ya ya zan can nan ya shiga kunnuwan Al’umma” Murmushin taƙaici kawai Mother ta yi wai duk akan Innocent son ɗinta ake wannan tururuwar kamar wanda ya kashe mutum?. “Allah ya kyauta, mutane akwai su da son gulma musamman ƴan jarida wallahi” I.d card ɗinta wanda ke nuna ita cikakkiyar lawyer ce mai zaman kanta ta nuna kana aka basu damar shiga, tun kafin Barrister Zainab ta yi parking idanun Mother ya sauka akan Sheikh wanda aka fito dashi cikin wata ƙatuwar sarƙa tare da wasu manyan ƴan fashi, wani abu ya tsaya mata wanda bata taɓa jin irinsa ba, ko hawaye ta kasa a wannan lokacin. Da sauri ta fita haka ma Barrister Zainab ɗin, ana ƙoƙarin saka Sheikh Aliyu cikin mota wata mota ta shigo da gudu cikin haraba wajan hakan ya sa duk suka daka ta. Wani babban jami’in tsaro ne tare da Abba Hakimi suka fito daga cikin motar sai wata matashiyar budurwa wacce Fuskarta ta kumbura sosai sbd kuka. I.G ya kalli jami’an tsaron cikin tsawa ya ce “Maza a cire sarƙar nan, a bawa Sheikh Aliyu Haydar Aliyu kayansa ya saka, He’s Innocent ya fita daga jikin zargi, Wannan matar ita ce wacce ta shirya komai, she’s the reason behind, She is the one who harmed Aliyu”
Gaba ɗaya kallon budurwar sukai wacce take kuka kamar ranta zai fita. A karo na farko Sheikh Aliyu Haydar Aliyu ya ɗago idanunshi tare da sauke su akan budurwar wani irin lallausan murmushi ya sauke wanda ya kusan ɗauke hankali jama’a tare da basu mamaki, hatta Mother tai mamakin ganin murmushi a fuskar Aliyun. Cikin ƙaramin lokaci aka sakawa Sheikh wata jallabiya mai kama da Alkyabba tare da wani farin hirami nan da nan kamalarsa ta fito haibarsa ta cika Idanun kowa. I.G ya bada umarnin a kama budurwa Sheikh ya yi gyara murya yana tafiya a nutse cike da kamala tsayawa yai daidai inda budurwar take, for the first time a tsayin rayuwarsa daya tsaya gaban mace kana ya juya ya kalli I.G sanin cewa ba zai iya taɓa jikin I.G ba yasa ya kama hannun Abba Hakimi ya riƙe da kyau yana runtse idanunshi, ƙafarsa ya ɗaga ya buga a ƙasa cikin In-ina ya ce “Aahhhh ahhha abarta, dooo.. do.. domin ba ba ba….ba a faɗa da Aljani.
Not Edited
08119237616
🫰🏽kai tsaye ga mai buƙatar littafin.
🌈 IDAN BA KE 🌈
Arewabooks@Nimcyluv
11…..
Abba Hakima ya kalli Sheikh a nutse yana mai sakin murmushi shi ma, tare da juyawa ya kalli budurwar wacce taƙi yarda ta kalli inda Sheikh ɗin yake, tun daga sama zuwa ƙasa Abba Hakimi ya ƙare mata kallo kafin ya ce “A’uzu bi wajhillahil karim, Wabi kalimaatil lahillati la yujawizuhunna barran wala fajiran, wabi asma’illahil husna kulliha, ma alimtu minha wa malam a’alam min sharri ma yanzilu minas sama’i, wa zara’a fil’ardhi, wa min sharri ma yakhruju minha, wa min fitnatillaili wan nahari, wa min ɗawariƙil laili wan nahari, illa ɗariƙan yadruƙu bikhairin ya Rahamanu. Wa min sharri kulli dàabbatin Rabbi akhizun bi nasiyatuha inna Rabbi ala siraɗin mustaƙim” jikin budurwar ne ya fara rawa sosai, tsoran Abba Hakimi da Sheikh Aliyu Haydar Aliyu suka cika mata zuciya, bata son su cutar da ita tunda ita bata zo da nufin hakan ba, kuma daman Ubangiji ya ɗora mata tsoran Sheikh ɗin tun ba yanzu ba, tana jin girma da nauyinsa tare da shakkar sa kwarjininsa yafi komai dagula mata lissafi. Idan ka ɗauke Abba Hakimi, No one understands the words of Sheikh Aliyu.
“No!!!”
Sheikh Aliyu Haydar ya furta a nutse yana riƙe hannun Abba Hakimi wanda bakinsa ya kasa yin shiru da addu’ar da yake, dalilin hakan yasa budurwar ta nemi birkicewa wanda kuma daga Abba Hakimi sai Sheikh ɗin ne kawai suke ganin hakan. Shiru ya yi da addu’ar yana kallonta kafin ya juya ya kalli Sheikh fuskarsa ɗauke da annuri irin na cikakkun dadtawan nan ya ce. “Yaushe Aliyu ya samu abokai haka bani da labari” a wannan karan Sheikh bai murmushi ba sai rirriƙe hannun Abba Hakimi da ya yi yana lumshe idanunsa tare da buɗewa alamar “Bai san yadda akai hakan ya faru ba” riƙe hannu Sheikh ɗin kai tsaye Abba Hakimi ya yi domin kai tsaye ya fahimci karatun idanun na Sheikh.
I.G dake tsaye shi da Barrister Maryam yana bata haƙuri ya ce.
“I’m sorry, action was taken without investigation, we were wrong” kasa riƙe kanta mother ta yi cikin losing control ta ce. “You have defamed Sheikh’s name, all those who respect him have now stopped, Sbd Kuskuren ku my son is innocent na riga dana faɗa muku, but you refused to understand me” Bar Zainab ta numfasa cikin rashin jin daɗi ta ce “Everything that has happened has already happened, kawai a kira ƴan Jaridu a shaida masa Sheikh bashi da laifi, sharri ake masa bai san komai ba a wanke sunan shi daga ɓacin da ya yi” cikin martabawa da nuna rashin daɗin abin da duk ya faru I.G ya ce.
“Aikinmu ne hakan, za muyi abin da ya dace muma ba zamu so sunan Sheikh ya lalace ba yana da girma da daraja a idanun ba” Mother gaba ɗaya haushin duk wasu jami’an tsaron take ji hakan yasa cikin sauri ta juya zuwa inda Abba Hakimi da Sheikh suke tsaye, idan ka gansu zaka ɗauka da gaske Hakimi shi ne ya haifi Sheikh sbd tsananin haibar dake maƙale a jikin ko wanne kusan duk halin Hakimi Sheikh ya kwashe shi tas.
Kallonsu ta yi cike da son ko wanne wanda ke rinjayar zuciyarta ta ce “Thank you Abba Hakimi” murmushi kawai ya yi bai ce mata komai ba, tana ƙoƙarin sake magana ya yi saurin barin wajan zuwa cikin motar da Umar-khan ya buɗe masa baya.
Tsaye Sheikh yana bin mahaifiyar tasa da kallo ganin tai shiru ya waro mata manyan Idanun shi yana son cewa wani abu amma ya ja bakinsa ya yi shiru a hankali ta ce “zaka bini ko Abban naka za kabi?” Bakinsa ya motsa yana rufe idanu tare da fara buga ƙafa yana riƙe jikinsa da kyau cikin In-ina ya ce “Zazzzza… zan zan zanje gida wajan fa… fa.. father ina soooo son ganinsa”
haushi ne ya kama Mother ganin duk abin da ake Sheikh yana maƙale da son mahaifinsa. “Father baya gari, kaje wajan Hakimi ka huta da kyau gobe sai kazo mu tattauna, ina tunanin za a haƙura da zuwa Madina haka” girgiza mata kai ya yi bai ce komai ba ya juya ganin har lokacin Abba Hakimi na zaune bayan motar, yanzu zuwa shima ya shiga baya Ishaq-hakim ya jasu. daga nan Bar Zainab gidanta ta shige hakan yasa Umar-khan ɗaukan Mother a ɗaya daga cikin motocin Sheikh suka nufi gida, Saif-Wazir kuma ya tsaya domin magana da ƴan jarida.
Suna tafe a hanya Sheikh na yiwa Abba Hakimi hira cikin nutsuwa duk da In-ina yake amma Hakimi na fahimtar komai da Sheikh ke faɗa, a duk maganganun Sheikh ba za kaji kalmar MACE ta fito daga bakinsa ba, balle har ya ware wata musamman yana magana a ganta, Murmushi kawai Hakimi yake Ubangiji ne shaidar son da ya kewa Sheikh a jinin jikinsa yake.
A haka suka ƙarasa haɗaɗɗan gidan Abba Hakimi dake Dawaki roud, gida ne irin na sarauta mai kyan tsari da fasali ko’ina ma’aikata ne , motar na tsayawa Sheikh ya fito ƙwayar idanunsa na nuna gajiyar da yake ciki.
Bai tsaya jiran Abba ba, kai tsaye ya nufi part ɗinsa wanda yake cikin gidan Abba Hakimin wanka ya yi da ruwa mai zafi yana gamawa ya fito ɗaure da babban towel idanunshi na janye wa barci na cin ƙarfinsa ya ɗauki wani tsadaddan lotion, Shea body butter ya shiga shafawa saman fatarsa a kasalance, Engage Cologne Spray ya fesa a fatarsa sbd ɗauke zafin da ya keji yana gamawa ya miƙe zuwa clothes ɗinsa ya ɗauki wani trousers mara nauyi ya saka ko riga bai saka ba, ya cilla mint bakinsa ya kwanta saman bed yana lulluɓe jikinsa da bargo, ganin rana ce ya sa ya kunna A.c tare da rufe idanunshi cike da fatan barci ya ɗauke shi.
Washegari gari tun da Sheikh ya farka bai koma barci ba, har ya fita sallar Subhi sai da gari ya yi haske wajan 6:30 ya dawo gida jikinsa duk ciwo yake masa sbd rashin gym da bai ba, wanka ya ƙara yi ya shirya cikin Scabal wool suit white colour sai red ɗin necktie. Sai Diamond Rolex daya maƙala a hannunsa, yau a Yaa Lee ya fito ba a Sheikh ba, domin kusan siffa biyu gare shi, idan zashi bank shigar suit yake duk abin da ya danganci addini ajjiye shi yake a gefe amma yana zuciyar shi, idan kuma ya sanya Alkyabba da rawani yana matsayin Sheikh a wannan lokacin ne ba Yaa Lee ba. Wayarsa ya ɗauka jacket ɗin sa a hannu cikin nutsuwa ya fita zuwa main parlour.
Ƙamshin ROJA shi ne ya fara kaiwa su Abba Hakimi ziraya yana zaune da jallabiya gefensa kuma Ishaq-hakim ne da Saif-Wazir shirya zasu shi wajan aiki, sai Momi A’isha tana zubawa Abba Hakimi Shayi mai zafi. “Mrng Yaa Lee” jinjina kai ya yi idanunshi akan Abba Hakimi ya furta. “B…bar bar barka da safi fifi fiya”.
“Ya ka kwana? da ciwon kan?” Rufe ido ya yi tare da buɗewa alamar “Allahamdulillah” Momi A’isha ta amsa gaisuwar Sheikh ɗin wacce ya yi mata ita cikin In-ina, tea ta haɗa masa mai zafi ta zuba 2spoon na honey ta juya kaɗan tare da bashi. Amsa ya yi a kame yake shan tea ɗin yana sauraran maganar Abba Hakimi da yake ce masa “komawa Madina ba yanzu ba, kada ya fara tunanin hakan” sanin ba zai iya ja da maganar Abba Hakimin ba yasa ya miƙe yana ajjiye cup ɗin hannunsa, Ishaq-hakim da Saif-Wazir suka miƙe tare da bin bayansa, wata farar mota ya shiga mai Sheikh no 5 yana shiga driver ya ja. Ishaq-hakim da Saif-Wazir kowa ya shiga motarsa suka nufi S.A.H BANK.
tun kafin ya Ƙarasa cikin bank ɗin wanda ya kasance mallakinsa ma’aikatan bakin Sheikh Aliyu Haydar bank suka shiga mutuwarsu ƙwarai. miƙewa ake ana gaida shi hannu kawai yake ɗaga musu har ya shige wani baban office. Wunin ranar Sheik cikin duba files and Ducoments yake.
3:30 yana ƙoƙarin barin Office ɗin saƙon father ya sauka Wayarsa. Da fararen idanunsa yake bin message ɗin da kallo yana mamakin yanzu kuma kiran gaggawar mene?. Da wannan tunanin ya shiga mota Driver ya ja suka nufi unguwar su Sheikh.
Tun a harabar gidan ya san akwai matsala domin kai tsaye idanunshi ya sauka akan motar Abba Hakimi data Yaya Halima sai ta Uncle Haroon.
Ƙamshin turarensa ya bayyana zuwansa, Mother dake zaune saman Kujera yana kaɗa ƙafa ta kalle shi kafin ta ɗauke kai, Uncle Haroon ma kallon Sheikh ɗin ya yi, a kame ya ƙarasa kusa da Abba Hakimi ya zauna yana ɗauke idanunshi daga kan jama’ar daya rasa meeting ɗin me ake.
“Tun da Allah ya kawo shi sai aji ta bakinsa, amma Sheikh ya shige lokacin da za a yi masa auren dole, a baya ba ai masa ba balle yanzu?” Yaya Halima ta furta cike da jin haushin father. Shi ma father da zuciyarsa ke kusa ya ce.
“Bashi da amfani, domin ba zai faɗi abin da kowa ke buƙata ba, na daɗe da sanin cewa Aliyu shi ne ƙaddarata, shi da yake namiji wanda ya kamata ya tsaya kan dukiyata amma ya kasa hakan, duk mutanan da suke buƙatar contract daka gareni idan har suka ji yadda Aliyu ke banzar maganar shi suke contract In-inar Aliyu ta ja mini asara mai yawan gaske, don haka ni bashi da amfani a gareni” sai a yanzu suka fahimci rashin jituwar da babu tsakanin father da Aliyu cikin ladabi Abba Hakimi ya ce “Baka yarda Ubangiji ya ɗorawa Aliyu wannan larurar ba? kenan baka alfahari da Aliyun matsayin ɗa?” Cikin sauri Father ya ce “Aliyu bai taɓa yi mini rana ba, to akan me zan yi alfahari da shi? Idan yana so mu shirya dole ya daina wannan In-inar ko kuma ya yi aure cikin satin nan”
“Aliyu akwai wacce ka ke so ne?” Sai a lokacin Sheikh ya kalli Uncle Haroon yana runtse idanunshi zufa na yanko masa a ƙoƙarin shi na ganin ya yi magana babu In-ina amma ina ba zai iya ba ƙaddarar shi ce hakan.
Cikin fitar hayyaci yana rirriƙe jikinsa da kyau tare da buga ƙasa da hannun kujera ya ce “ba…ba ba bana son son kowa uncle.. ba ba bazan iyyyya zama dadda da mace ba” shiru duk sukai baƙin ciki ne kuma ya hana mother magana. Father ya ce “Ok good a Sbd haka ka shirya zama da Zahrah ƴar gidan babban aminina, cikin satin nan za a yi aurenku kai da Zahran babu fashi” miƙewa Mother ta yi cikin faɗa ta ce “Wallahi Aliyu kayi kaɗan ka saka Sheik ya auri wannan Yarinyar da ban amince da tarbiyyar ta ba, me Sheikh zai da ita? Yarinyar da take kusan sa’ar shi kaɗan ne babu ta girme shi ba? duk shekarun da Aliyu ya yi babu aure sai kuma ya ƙare wajan tsohuwa, ban amince ba kuma ban yarda ba, ka bawa Aliyu duk wacce kaga dama amma ban da Zahrah” murmushi father ya yi ya ce “Idan har ni ne uban Aliyu ba wani ba? Ya zama dole ya auri Zahrah idan kuma bani ne mahaifinsa ba sai ki bashi wacce kikai niyya Barrister Maryam” hawaye ya cika Idanun Mother ta ce “Oh yanzu kuma sheganta Aliyu zaka fara bayan zarafinsa da ka ke ci akan larurarsa?” Banza father ya yi mata. Uncle Haroon ya numfasa ya ce “Engineer Aliyu Wannan bai kamata ba, idan kana so Aliyu ya yi aure,Let him choose the woman he wants to marry himself, ka sassauta yanayin da ka keji game da Aliyun” Father ya ce “Abu ɗaya ne zai kawo Shira tsakanina da Aliyun shi ne auren shi da Zahrah idan bai amince ba yaje na zare hannuna daga Lamarinsa kuma ya zare sunana a matsayin Uba” Dakawa Father tsawa Uncle Haroon yai ya ce “Wai Aliyu wanne irin banzar magana ce kake haka? Ni da kai na zan iya samawa Aliyu matar aure, ka daina ganin kai ne ubansa ni ma uba ne a wajansa, ga kuma babban Uba hakimi duk mun isa mu tsayawa Aliyu, ka daɗe baka cire hannunka ba, kuma wallahi ka sake na rabaka da Aliyu ka rabu dashi kenan har abada” Girgiza kai Abba Hakimi ya yi ya ce “Ba za a yi haka ba Haroon, haƙƙin Aliyu ne samawa Sheikh matar aure a barshi ya aura masa Zahrah Allah ya sa albarka,kada ka damu da Sheikh nasan zai amince” miƙewa Sheikh ya yi cikin zafin e da kutuwar zuciya irin ta kurmaye Aliyu ya fara faɗa ta inda ya shiga bata nan yake fita ba, idanunshi gaba ɗaya ya rufe Innar ta hana ya ji abin da yake faɗa, idan kuma ya fara faɗa babu wanda ya isa ya tsayar da shi daga faɗan da yake. Saukar wani zazzafan mari da Sheikh ya ji a saman kamilalliyar fuskarsa ya sanya ya yi saurin rufe idanunsa Father ya nuna Sheikh ya ce “Ni kake ɗagawa murya Aliyu? Ni sannu kuturu uban ƴan zuciya daman zuciyar taka nake buƙata auranka da Zahraan kuma babu fashi” ƙwafa Sheikh ya yi domin baya iya riƙe kansa idan zuciyar ta motsa uban kowa sai ya san babu lafiya a gidan. Wuyan rigar Father ya riƙe da kyau zufa na mamaye dukkan goshinsa a wannan karan bai buga ƙafarsa ba amma tamkar zai ɓalla wuyan rigar haka ya riƙeta da kyau cikin huci da faɗa ya ce “heee na… na na amince amma ka ka ka tabbatar mutuniyar kirki ce” Father da yaji shaƙar Sheikh ɗin har ransa ya ce “Idan kuma ba ita bace ba fa Aliyu?” Sheikh ya girgiza kai idanunshi ya yi jajur ya ce “Haaaaa ɗakkkkkk” yana faɗin haka ya saki Father tare da barin gidan baki ɗaya…
We’re still in free pages🫰🏽 Littafi nan na kuɗi ne, a koda yaushe zan iya datse free pages. Salo na musamman biya 500 ta Wannan acct ɗin 6850917335 Na’ima Shu’aibu sulaiman fidelity bank. Shaidar biya 08119237616.
🌈 IDAN BA KE 🌈
Nimcyluv sarauta
12….
Bayansa suka bi da kallo ganin yadda ya fice a fusace. Father yaja numfashin wahalar da ƙyar kafin ya ce “Irin wannan ban zan yaron za a bawa mace mai ƙarancin shekaru? Ai ko Zahrah sai dai ta yi haƙuri da shi” Mother zatai magana Yaya Halima ta hanata ta hanyar danne hannunta tare da girgiza mata kai. Ganin ba wanda ya sake cewa father komai ya juya zuwa upstairs. Uncle Haroon ya kalli Abba Hakimi ya ce “Afuwa ranka ya daɗe kayi haƙuri da halin Engineer Insha Allah komai za yi daidai, Jadda ba zata barshi ya aikata hakan ba, I’ll talk to him” murmushi Abba Hakimi yai yana faɗin “Me ne na haƙuri Haroon? Sheikh ɗan sa ne ba wanda zai yi jayaya da hukuncin da uba ya yi akan ɗan sa, idan hakan zai sa shi farin ciki da amincewa da Sheikh a barshi ya yi” “She’s 32 years old Hakimi, tayi wa Sheikh girma ba zata iya yi masa biyayya ba, babu tarbiyya a wajan yarinyar nan na jima da saninta” Mother ta faɗa cikin damuwa. Yaya Halima ta ce “Barrister ke uwa ce a kullum, addu’a kawai za kibi Sheikh da shi, addu’ar ki zatai ta zagaya rayuwarsa sai kiga albarkacin haka Ubangiji ya daidaita tsakani kuma ya shirya yarinyar, ba a jayaya a cikin lamarin aure” Uncle Haroon ya ce “Ki bar Barrister ta faɗi abin da yake ranta, idan akwai wanda yafi sanin halin Sheikh da raninsa to ita ce mai biye mata shi ne Hakimi, babu kyautatuwar a zuwa Engineer idanu yana abin da ya ga dama, idan baya ra’ayin Sheikh a rayuwarsa sai muyi yarjejeniya mun ashe sa mu suke sunan shi daga jikin na Aliyun” miƙewa tsaye Abba Hakimi ya yi yana gyara zaman alkyabbar jikinsa cike da nutsuwa ya ce. “Wannan shawara ta Haroon ba dani ba, ban taɓa jin inda aka raba uba da ɗana ba, lokaci ku barshi ya bayyana mana komai” yana faɗin hakan ya yi waje yana dogara sanda. Uncle Haroon ma ya miƙe tare da yi musu sallama.
Bayan tafiyar su Yaya Halima ta kalli Mother ta ce “Barrister ki nutsu kada kiyi jayaya da hukuncin da uban yaron nan ya zartar ni ina ji ajikina akwai wani abu ɓoyayye a ƙasan auren mu amince da hakan” ƙwafa kawai Mother ta yi tana girgiza ƙafa kafin ta kalli Yaya Halima ta ce “Kin san Allah Yaya ko zan amince da auren nan sai dai Sheikh ya auri mata biyu?” Yaya Halima ta waro idanu sosai ta jima tana kallon Mother kafin ta numfasa ta ce “Tab, mata ɗaya ya zata ƙare wajan Sheikh bare mata biyu? Ai Wallahi mantawa zai yi da zamansu a gidan”
“Ai ko zai yi shekara ɗaya bai kalli ko wacce ba, Wallahi sai dai ya auri mata biyu” Yaya Halima ta ce “Naji zaɓin Uba, wace kuma zaɓin uwa?” “Bani da zaɓi amma duk wacce Allah ya nufa data kwanta mini ko ƴar gidan wace zan saka Hakimi ya ɗaura musu aure”
girgiza kai kawai Yaya Halima tai tana faɗin “Wata drama ɗin abin dry a gidan Engineer da Barrister a bani abinci naci ni dai” Mother ta miƙe tana kiran sunan Maimoon. Fitowa tayi daga part ɗinsu jikinta sanye da duguwar riga ta rusuna ta ce “Ina yini Mama?” Yaya Halima ta ce “Lafiya lou Maimoon ya karatu? Kwana biyu Mother ta hanaki zuwa ko?” Maimoon ta juya ta kalli Mother wacce ta ɗauke kai tamkar bata jin abin da suke cewa ta ce “A’a Mama, karatu ne ya yi zafi amma muna exam zan zo”
“To Allah ya taimaka, a kawo mini abinci” murmushi Maimoon tayi ta nufi kitchen. Yaya Halima ta kalli Mother tana mamakin zafin zuciyar ƙanwar ta ta. Arabian Mandi rice wacce ta sha kayan haɗi sai ƙamshi take Maimoon ya zubu a plate tare da haɗin salad da ya sha bama da egg with some of vegetables. “Ki sakko muci abinci Maryam” Mother ta ɗauke tana faɗin “Anya? ci kawai Yaya bana jin zan iya ci” murmushi kawai Yaya Halima tai tana faɗin “Allah ya kyauta komai ya yi zafi maganinsa Allah”
Yana tsaye gaban madubi banda huci babu abin da yake maganganun father nayi masa amsa kuuwa a kunnuwansa “Bashi da amfani, bai taɓa yi mini rana ba, ya yi mini asarar contract ɗina” hannu ɗaya ya sanya ya dafe kansa dake masa ciwo sosai, ɗaya hannun kuma ya rufe kunnansa a zatonsa hakan zai taimaka wajan rage tuna maganar mahaifin nasa. Ɗago jajayen idanunsa ya yi ya tsurawa kansa ido ta cikin madubin. A wannan karan dole ya nunawa father shi ma namiji ne yana shiru ne sbd bai damu da duniya da abin da ke cikinta ba. Juyawa ya yi zuwa Library ɗinsa dake gidan Hakimi. Zama ya yi saman kujera cikin sauri ya duba dukkan mayan kadarorinsa kama daga kan filaye, gidaje, ɓangaren Library na karatun addinin dana kimiyya ya buɗe, S.A.H bank duk yana fahimtar dukiyar tasa har ya kasa shi kansa bai yi tunanin abin da ya mallaka ya kai girman hakan ba, a haka kuma bai haɗa dana wajan Mother ba wanda suke mallakinsa. Tunani ya fara tunda yana da bank a kano me zai hana ya buɗe S.A.H BANK a sauran jahohin da suke Nigeria? Da kuma kamfanin sarrafa shinkafa ƴar hausa mai kyau wacce za taiwa talakawa sauƙin siya kan fara shi mai sauƙi?. Da wannan tunanin ya yi na’am da zuciyarsa cikin nutsuwa ya fita daga Library ɗin ya koma haɗaɗɗan bedroom ɗin nasa, kai tsaye toilet ya shige tare da sakarwa kansa shower yana sauke numfashi a hankali ya fara sauka daga dokin zuciyar yama mance da batun aure baki ɗaya. Domin daman shi bai dame shi ba indai macace da kanta zata gudu ta ce bata son shi domin ba zata samu abin da take buƙata ba daga gare shi. Fitowa ya yi yana ƙamshin shower gel Shea body butter ya shafa jikinsa ko body spray bai fesa ba ya cilla mint bakinsa tare da kwanciya saman bed ya rufe idanunsa.
Umar-khan ne ya shigo cikin parlourn Abba Hakimi bakinsa ɗauke da sallama. A hankali Abba Hakimi ya ajjiye azkar ɗin hannunsa wanda yake na yamma tare da duban Umar-khan cikin kamala da kamewa ya ce.
“Umar-khan yaya dai?” Shafa kai ya yi yana tare da faɗin. “Abba Hakimi daman Mother ta ce ko Sheikh yana nan? Gaba ɗaya baya can gida” murmushi mai laushi Abba Hakimi yai yana zame idanunsa daga kan Umar-khan ɗin “Aliyu ai ba yaro bane?” Abba Hakimi ya faɗa a gajarce Umar-khan ya miƙe ba tare daya samu cikakkiyar amsa daga bakin Abban Sheikh ɗin ba ya ce “Ni ma zan je gida, sai da safe Abba Hakimi” yana buɗe azkar ɗin ya numfasa kaɗan cikin sakin fuska ya ce “A gaida Abdulrashid”
“Zaiji sosai”
Umar-khan ya amsa wa Abba Hakimi yana barin gidan baki ɗaya tare da tunanin inda Sheikh ɗin ya yi domin yana tsoro idan zuciyar ta motsa kowa sai yaji babu daɗi. Momi A’isha ce ta shigo ɗauke da tray ɗin abinci zama tayi bayan ta ajjiye ta ce “Ina ta mamakin abin da ya sanya mahaifin Sheikh ke aikata haka kamar wani mara ilimi, kuma ya dace ace ka saka baki ko auren ya keso Sheikh ya yi sai ka zaɓa masa ƴar mutunci, kaga hankalin Barrister bai kwanta da zaɓin Engineer ba” gaba ɗaya Abba Hakimi ya tattara nutsuwarsa kafin ya ce “Ku dai mata yawanci tunaninku ɗaya, bani da ikon ture umarnin uwa ga ɗan shi,kada ki manta ni uban rana ne kuma mariƙi, I don’t have the courage to deny the Engineer what he wants”
“Gaskiya dai, ni ina tunanin ko sbd Sheikh bashi da lafiyar yin magana cikin jama’a ya sanya Engineer ke yi masa haka? Kuma yana ganin He is the only male among his children, shi ne ya kamata ya tsaya kan harkokinsa na yau da gobe ya ɗauki buri ya saka akan Sheikh ɗin?” Abba Hakimi ya amshi fruits ɗin data gama yanka masa kafin ya kalleta da kyau ya ce
“Baki ke aiki ko ƙwaƙwalwa? Babu wani abu da Sheikh ba zai iya ba, In-ina kuma Ubangiji ya ɗora masa muna fata a koda yaushe ta zama sauƙi a gare shi” “haka ne Allah ya bashi lafiya, anjima zani gidan Barrister ɗin” Abba Hakimi ya ce “Ki yi zamanki” ta kalle shi ta ce “Amma me ya sa?” Shiru ya yi mata tasan ba zai bada amsa ba, kuma tunda ya ce haka yana nufin hakan har ransa.
A can commission Quarter’s dake cikin garin Yola/ jimeta a hankali take driving saman makeken kwaltar da zai sadata har zuwa gida, numfashi ta sauke a karo na ba adadin tana kallon titi kunnanta kuma ma sauraran abin da Surayyerh ke faɗa tsaki ta ja ta ce “You bother me with noise wlh Surayyerh koda yaushe problems ɗinki da mahaifiyarki baya ƙare wa?” Surayyerh ke ta ce “A sbd ba ke bace ko? Gaba ɗaya ta takura ni wani lokacin gani nake kamar ba ita ta haifan ba” da sauri Zahrah ta juya ta kalli Surayyerh ta ce “Ashe daƙiƙiyya ce ke? Whatever is your problems ki barni da tawa matsalar” dry sosai Surayyerh tayi tana tafa hannu ta ce “Oh! Sorry ashe fa ciki yaƙi zubewa yanzu dole ki amincewa Deen kuyi aure” Zahrah stopped Surayyerh from what she was saying ta ce “And who told you cikin Deen ne? Ni kai na ban zan cikin waye ba, ban damu kuma dana sani ba kawai na zubar da shi ba aure a tsarina a yanzu dai” Surayyerh ta gyara zama sosai ta ce “Kin san Allah a yanzu babu abin da nake so sama da aure, sai yanzu na fahimci karatun bokon nan is nothing wani abu ne wanda kana cikin gidan mijinka ma zaka iya yinsa” Zahrah bata ce komai ba tunaninta yana can yana da tabi cikin jikinta ya zube ba tare da Mimi ta lura da shi ba. A haka suka ƙarasa gida gatekeeper ya buɗe musu. Sosai tai mamakin ganin motocin Dady yaushe ya dawo bata da labari? Dawowar gaggawa?. Fitowa tayi hannunta riƙe da L.G bag daman babu mayafi jikinta kayan sun kama jikinta sosai, jerawa sukai ita da Surayyerh zuwa cikin gidan. Dady da Mimi ta bi da kallo ganin suna magana a hankali, Dady yai murmushi ya ce “Finally She’s back zo nan Zonan Zahrah” ya miƙa mata hannunsa ƙara sawa tayi ta zauna kusa dashi tana rungume shi ta ce “Wlcm Dady” kallonta ya yi da kyau ya ce “Zahrah magana za mu yi mai Muhimmanci” ta gyara zama ta ce “All ears Dad” ya ce “Kin san aminina Engineer Aliyu?” Ta ɗaga ta ce “I think I knw him Dad mene ya faru?” Ya ce “Kin san wancan dake jikin photon?” Juyawa tayi ta tsurawa photon Sheikh Aliyu haydar Aliyu dake maƙale jikin bangon parlournsu zuciyarta ta ɗan buga ta girgiza kai ta ce “Ban shi ba Dad, amma na san yana da muhimmanci tunda aka photon sa a gidanmu” ya jinjina kai ya ce “Yana da muhimmanci a gareni da rayuwata baki ɗaya, Zahrah wannan da kike gani akansa duka wasu burukana suke, ina son na haɗaku aure da Sheikh Aliyu haydar Aliyu cikin satin nan” zabura tayi ta miƙe tana zaro idanunta waje zuciyarta na bugawa sosai ta kasa magana baki ɗaya. Mimi ta ce “Daman nasan Zahrah ba zata amince ba, domin ko Tafsir ɗin ta tsana” Dady ya ce “Ya zama dole ta amince sbd karayar arziƙin dake shirin tunkaro mu ba tare da mun shirya ba, Zahrah ki yarda ki auri Sheikh zaki farin ciki namiji ko a maza samun irinsa zai wahala kiyi mini wannan alfarmar” Ajjiyar zuciya ta sauke ta ce “Dady na amince da buƙatar, amma idan har daga ni ba zai sake auren ko wacce mace ba ina nufin babu kishiya…
Na kusa gama free pages. IDAN BA KE it’s 500 gaba ɗaya book 1,2 har ƙarshe. Via 6850917335 Na’ima Shuraihu Sulaiman fidelity bank. Shaidar biya 08119237616 ƴan niger suyi mini magana na faɗa musu yadda zasu biya.
DESTINY
TRUE LOVE
ROMANCE
TRUST
SARAUTAR MARUBUTA
🌈 IDAN BA KE 🌈
Nimcyluv sarauta
13…..
Mimi ta ce “baki son kishiya kuma? Ina ruwanki da wata kishiya?” Dady ya ɗaga hannu yana murmushi ya ce “Ni ma bana fatan Sheikh Aliyu haydar Aliyu ya yi wa Zahrah kishiya,domin za a rage mini abin da nake tunani” cikin rashin fahimta Mimi ta ce “kamarya Alhaji?” “Ba sai kinji ba, ki shirya aurar da yarinyar ki cikin satin nan” ya faɗa yana miƙewa tsaye cikin jin daɗin amincewar da Zahrah ta yi.
Jikinta na rawa ta haura upstairs tana zuwa ɗakinta ta samu Surayyerh ciki daman bata tsaya a parlour ba sama ya shige ɗakin Zahran. “Wayyo daɗi kashe ni, na samu mijin da nake fata da burin samu cikin sauƙi” ta faɗa gado tana sakin ƙarar farin ciki. Surayyerh ta ce “Pardon? Ban fahimta?” Miƙewa Zahrah ta yi ta ce “C’mon yanzu Dady yake sanar mini za a haɗa aurena da Sheikh Aliyu” mamaki ya hana Surayyerh rufe baki sai da Zahrah ta saka hannu ta rufe mata baki, Surayyerh ta samu damar faɗin “Are you serious Zahrah? Gaskiya am happy for you daman kina son Sheikh?” Tayi fari da idanu irin na gogaggun matan nan ta ce “Fiye da yadda bakya zato, soyayyar Sheikh ta hanani aure, abin mamaki ban taɓa ganin shi a zahiri ba sai dai photo a wajan Dady ko idan yana tafsir, nasan shi ma bai sanni ba”
“Yanzu duk ba Wannan ba, ya ya zaki da cikin jikin ki tunda likita ya tabbatar ba zai zube ba? Gashi kuma aure ya zo babu shiri?” Zahrah ta ce “Kada ki damu da cikin zanyi auren, ko da haihuwa nayi sai nace bakwaini ne ai anayi” Surayyerh ta jinjina makircin Zahrah amma ta share ta ce “Idan kin ɓoye cikin ya zaki idan ya san ke ba budurwa ce ba?” “Oh! My God what exactly wrong with you Surayyerh ki ke neman yi mini baki? Ai ba zai sani bama ɗinki zanje ayi mini” Surayyerh ta ce “Uhm shi fa babban Malami ne You never lie to him Malamai sun san komai infact sun fi kowa iya soyayya kiyi tunani ki nemi mafita” share zan can Surayyerh Zahrah tayi a yanzu yadda za taga Sheikh Aliyu haydar Aliyu a zahiri shi ne burinta. Da magrib Surayyerh ta tafi gida akan gobe zata dawo domin fara shirye-shiryen haɗa events.
Tun a bakin parlour Surayyerh ta san akwai matsala tana shiga Umma ta kalleta sosai ta ce “Daga ina kike?” Turo baki tayi tana musmus da bakinta kamar mai zagi ta ce “Wai ke Umma zargina kike ne? Haba don Allah na fara gajiya ciki kike tsoro ko mene?” Umma mamaki ya kasheta a tsaye ta ce “Surayyerh ni mahaifiyar ki kike faɗawa haka sbd ina kare kiwon da Ubangiji ya bani?” “Wani irin kiwo kamar wata dabba Umma? Kawai takurawar taki ce ta yi yawa, ki barni da abin da yake damuna gashi duk iskanci Zahrah rana tsaka ta samu miji na kece raini wanda ba zan taɓa samun irinsa ba” jirin dake neman yadda Umma yasa ta nemi saman kujera ta zauna. Ubangiji ya gani kuma shi ne shaida tayi iya yinta ta fara gajiya tana ganin gaba gaba Surayyerh dokanta zatai ita kam wannan karatun bokon bai mata rana ba. Hawayen daya cika idanunta ta mayar sbd babu dacewar yiwa Surayyerh kuka sai ta sake lalacewa. Surayyerh ta shiga zirga-zirga a bedroom ɗinta tunani ya yi mata yawa abin da bata tsammata ba a yanzu ya kawo mata farmaki.
A firgice Halisa Danejo Rome ya farka daga nauyayyen barcin daya ɗauke ta mai cike da mafarkai wanda bata taɓa yin kamarsa ba, me ya sa Balaraban nan ke zuwar mata cikin barci ne? Amma gaba ɗaya yadda ta gansa a daji ya bambanta a farki, na cikin mafarkinta yafi kyau da kamala nutsuwarsa da kamewar shi tafi bayyana, kwarjinin dana mafarkinta yake dashi na zahiri baya da shi, duk mutum ɗaya ne? Ta tambayi kanta a cikin zuciyarta shiru tayi cike da damuwa domin ta fara gajiya da mafarkinsa. Motsin da taji kusa da ita ya sanya ta juya idanuna ya sauka akan Dada wacce take sanƙame numfashi na fita da ƙurar ciwo yaƙi ci yaƙi cinyewa. “Na lalashe na shiga uku Dada jikin ne? Sannu Dadata zaki samu lafiya” ta faɗa hawaye na wanke mata fuska gaba ɗaya ta ƙara zama wata kala damuwar ciwon Dada ya sata gaba, gashi yanzu Hamma Yabi baya yini gida sbd neman kuɗin zuwa asibitin burni. Jigum tayi tana kallon yadda kumfa ke fita ta bakin Dadar amma bata san me zatai mata ba, bata da wanda zata kira a cikin bukkar. Shatu dake rakuɓe ta kalli Danejo ta ce “Dada mutuwa zatai ko?” Girgiza kai Danejo tayi ta ce “Waya faɗa miki? Babu inda Dada zata yafi ta barmu aradu muna tare da ita” wata ƙara da Dada tayi tana sanƙamewa ya sanya Shatu fashewa da kuka, da gudu kuma Halisa Danejo Rome tayi waje. Karo sukai da Hamma Yabi wando ya shigo hannunsa riƙe da ƙwayar magani daya amsu, ya riƙe Danejo da kyau wacce take ƙoƙarin fita daga hayyacinta. “Hande en boni, Danejo lalashewa ya sameka me ya samu Dada?” Gaba ɗaya ta rikice sai ƙanƙame hannun Hamma Yabi take ganin bata hayyacinta ya jata ciki yana zuwa ya kwantar da ita yana rufe mata fuska shiru tayi har lokacin cikinta bai bar rawa ba, domin gani take kamar Dada tabarta kenan ta mutu ta tafi. Ya girgiza yana komawa wajan Dada tare da ɗagata ya bata maganinsu ya shafa mata zuwa fuska da wuya Ajjiyar zuciya ta sauke tana buɗe idanunta, hannun Hamma Yabi ta kama da kyau tana son tambayar shi mene ya samu Halisarta amma ta kasa, a haka barci ya ɗauke ta cikin mayuyacin hali. Washegari kamar kullum Danejo ta tatsi nono a ƙwayar, tun kafin gari ya yi haske ta fita kiwo da shanunsu, sai da ta ɗauki awa uku ta dawo cikin sauri tana tafe tana kaɗa naggen bayan ta ɗaure su ko abinci bata ci ba ta nufi cikin burni kawai tsaye zuwa Abti America. Yadda taje haka ta dawo babu wanda ya sanya kuɗi ya sai nonon balle su samu na abinci, a wahale ta shiga Rugar idanunta na rufewa ta kafa baki a nonon wata nagge ta shiga sha sai da cikinta ya ɗago taja Ajjiyar zuciya tare da nufar bukkarsu.
Sheikh Aliyu haydar na kwance saman makaken gadonsa idanunsa akan screen ɗin laptop ɗinsa yana sauraran abin da ake faɗa ta cikin laptop ɗin. Can dai ya ja tsaki ya girgiza kai, speaking calmly ya ce “Ni ni niii da dddddd dama zaka zaka zaka sauya labarin nan naka Khalil, in anyway banga amm am am amfaninsa ba…” Dry sosai wanda aka kira da Khalil ya yi ganin yadda Sheikh ke runtse idanunsa yana buga kai duk dan ya kare kansa “To ai ni yana da amfani a wajena tun da abin da ya shafi Sheikh Aliyu haydar Aliyu ai shafi Khalil Ahmad Sarki, look Sheikh don Allah cire son zuciya ka faɗa mini mai mata sukai maka? Let me know” Sheikh ya shafa lallausan gashin kansa wanda yake kwance gwanin sha’awa, cikin son cire damuwar father a ransa ya dage yake hira da Khalil duk da yana shan wahalar magana ya jima bai magana mai tsayin haka ba, idanunsa lumshe ya ce “kakaka….ka kasan me?” Sheikh ya faɗa yana buga kansa jikin pillow yana riƙe ɗaya hannunsa sbd In-ina. Kallonsa kawai Khalil yake yana jiran jin abin da Sheikh ɗin zai faɗa, a wahale cikin In-ina wacce yake son ya saba magana da ita ya mirgina kaɗan yana riƙe kansa da hannu bibbiyu ya ce “man ta ta manta kawai, ya ya yaushe za za kazo?” Murmushi Khalil ya yi cike da ƙaunar Sheikh Aliyu haydar ya ce “Zamu zo da mai martaba wajan Hakimi, I think I will spend my two weeks vacation with you in Kano” jinjina kai kawai Sheikh ya yi ba tare da ya ce komai ba. “You are just afraid of women because you see yourself as a Sheikh, women are the happiness of a man, try and see” Girgiza kai kawai Sheikh ya yi ba tare da ya ce komai ba ya kashe vedio call ɗin.
Umar-khan ne ke driving a hankali idanunsa akan titi amma hankalinsu na kan Sheikh dake manyan mota cikin wata dakakkiyar shadda fara tas ya ɗora golden ɗin Alkyabba sai rawanin daya ƙarawa fuskarsa kyau da haiba ya yi wani irin kyau kamar Balarabe ƙamshin Roja ya cika motar sosai. Yana ki shingiɗe a bayan motar tunani yadda zai sauya ya koma kamar yadda father yake buƙata, a haka suka ƙarasa Wani Restaurant mai kyau da tsari mara hayaniya, Umar-khan ya yi parking kasancewar fitar sirri ce yasa babu wasu masu take masa baya, cikin sauri ya buɗe Sheikh mota a nutse ya fito yana gyara zaman alkyabbar jikinsa tare da goya hannunsa a baya cikin kamala ya yi gaba Umar-khan na biye da shi zuwa cikin Restaurant ɗin. Zama Sheikh ya yi tare da kallon mutanan da zasu tattauna dasu, bayan sun gaida Sheikh ya ɗaga musu kai suka shiga nuna masa zanan bank ɗin daya buƙata na reshe uku, kaduna, Abuja, da Lagos. Baya cewa komai sai da Umar-khan suke tattaunawa gani ya yi zanan bai masa ba, domin babban bank yake so wanda ba a taɓa yin mai girman sa ba. Hakan ya sa ya amshi carbon paper da pen a nutse ya zana yadda yake so, zanan ya bawa ma’aikatan mamaki abin da basu sani ba, kaɗan kenan daga cikin baiwar Sheikh duk abin da ya sanya ransa yana gwadawa yake yi daidai. Sallama sukai bayan anyi musu transfer miliyoyin kuɗi domin fara aiki gadan-gadan. Ɓangaren Kamfanin sarrafa shinkafa ma tuni aiki ya yi nisa, ya yi ordern injina masu kyau daga Chaina. A gajiye ya dawo gida idanunsa na rufewa kansa ya sakarwa shower lokacin 1:30 ya saba barci tsakanin azahar zuwa sallar asr, fresh milk ya tsiyaya a cup tare da zuba honey ya sha kaɗan ya wanke baki, yana kwanciya barci ya ɗauke shi daman ya riga daya saba.
Washegari ya kama weekend Sheikh bai san meke faruwa ba, sai daya farka yaji labarin tun 7 su Uncle Haroon da Abba Hakimi tare da Baffansa suka nufi garin Yola nema masa aure. Ko ajikinsa bai ɗauki auren matsayin wani abu, shi dai ya san ko farcen mace bai taɓa sha’awa ba balle ya birgensa. Da yamma su Abba Hakimi suka dawo cikin jin daɗin an basu auren Zahrah nan da sati mai kamawa za a ɗaura aure. Kasancewar yau Friday ne ya sanya Sheikh ya shirya cikin wata bugaggiyar shadda fara tas da ita mai ɗinki jamper da babbar riga, bai sanya hula ba sai hirami daya saka a saman sumar kansa ya ɗauki zagayayyen abun nan na larabawa Black colour ya ɗora saman hiramin, shekarunsa suka bayyana a jikinsa, domin kowa ya kalli Sheikh Aliyu haydar ya san ba yaro bane, girma ya fara hawa jikinsa babu mamaki ya yi aure a same shi da yara biyar haka, shekaru 34 ba wasa bane ba. Kai tsaye babban masallacin juma’a ya nufa sai da ya yi huɗu ba sosai mai ratsa jiki akan tsaida sallah a lokacin ta, tunda duk In-inar Sheikh inda karatu zai yi yana farawa ake nemanta a rasa. Bayan idar da Sallah ya nufi zaga gidan marayu kamar yadda ya saɓa idan yana ƙasa, a hankali yake tafiya hannunsa goye a bayansa kansa a ƙasa fitowar su kenan daga gidan marayu zasu shiga mota yaje gida wajan Mother, kamar daga sama wata budurwa kyakkyawa ajin farko ta tsaya a gabansu da sauri Umar-khan da Saif-wazir suka sha gabanta tun kafin securities su ƙarasu bakinta na rawa ta ce “Don Allah ku barni nayi magana da shi, na jima ina son haɗuwa da shi” Umar-khan ya daka mata tsawa ya ce “Baya buƙatar ganin kowa, kuma a mu’amalar shi baya yi da mata ki nemi wani wajan” A nutse Sheikh ya dakata tare da juyawa idanunsa zuwa inda budurwar take, waro fararen idanunsa waje ya yi yana mamakin abin da ya haɗa shi da bayin Allan nan da suke bibiyar shi. Murmushi mai laushi ya yi ba tare daya bari kowa ya gansa ba, yana mai ƙarewar budurwar kallo musamman ƙafarta. “Ka taimaka mini daga yanzu ba zan sake zuwa inda yake ba” Umar-khan ya yi mata wani ban zan kallo ya ce “Ke ko mayya ce ke baki isa kije inda Sheikh yake ba, kunne masu ƙullawa mutane sharri ko?” Sosai taji zafin maganar Umar-khan sai kawai ta juya kamar zata kifa sbd sauri. Tana barin wajan Umar-khan ya dafe kansa Saif-wazir ya ce “Are you okay?” Ya ce “Kai na ke ciwo, zazzaɓi nake ji” Umar-khan ya faɗa bakinsa na rawa kafin kace wani abu wani zazzafan zazzaɓi ya rufe Umar-khan. Girgiza kai kawai Sheikh ya yi domin ya san za a rina waya aiki Khan musayar yawo da aljani?.
Da sauri Hamma Yabi ya shigo bukkarsu hannunsu ɗauke da kuɗi ya kalli Danejo wacce take sumar kanta ya ce “shai Alhmd kuɗi shun samu gobe zan kai Dada asibitin burni” murmushi Danejo tayi wanda ya ƙara fidda kyanta na fili ta ce “Kai Allah abin gdy Dadata zata samu lafiya yau ba zan barci ba sbd farin ciki aradu” Hamma Yabi ya kalli Dada dake kwance kamar haka cikin farin ciki ya ce “Insha Allah, da sassafe sai burni” fita ya yi farin ciki ya cika zuciyar Danejo Dada zata tashi su koma yadda suke rayuwa a baya. Hamma yabi bai dawo ba sai dare riƙe da ƙullin buduri da ƙosai mai zafi wanda ake a can wajan gari. Sai dai ko zama bai ba suka fara jiyo harbi ta ko wanne waje alamar ƴan fashi ne suka shigo cikin Rugar Rome. “Bone Hamma harbi harbi….,” Bata ƙarasa faɗa ba suka ji an shigo bukkarsu wani mutum mai riƙe da bindiga ya kalli Hamma Yabi yana faɗin “Kuɗi,kawo kuɗi bamu da lokaci” jikin Hamma Yabi na rawa ya ce “Ba kuɗi bamu da shi” mutumin ya yi wata dry sosai ya ce “Babu? idan na bincika na samu duk hukuncin dana ɗauka akan kai ka sani” yana faɗin hakan ya fara bincike bukkar daga can waje harbi ake ta ko wanne sashe, cikin rashin sa a mutumin yaga kuɗin da Hamma Yabi zai kai Dada asibiti “Aradun Allah kuɗin asibiti ne, kayi mini ka taimaka Dada zamu bawa lafiya…..,” Harbin da akaiwa Hamma Yabi a ciki ya sanya ya fasa ƙara tare da faɗuwa ƙasa ihu Danejo ta fasa ganin yadda jini ke zuba a jikin Hamma Yabi tana ƙoƙarin zuwa inda yake mutumin ya ƙara sakarwa Hamma harbi a tsakiyar kansa……
Wannan littafin na kuɗi zaka samu book 1, 2 akan ₦500 daga farkon labarin har ƙarshe ka tura ta wannan account ɗin 6850917335 Na’ima Shu’aibu Sulaiman fidelity bank shaidar biya 08119237616.
🌈 IDAN BA KE 🌈
Arewabooks@Nimcyluv
14……
Cikin ƙaramin lokaci ƴan Rugar Rome suka shiga cikin tashin hankali musamman wajan su Danejo. Ko kuka ta kasa ta kafe gawar Hamma Yabi da kallo sai Ajjiyar zuciya take, shatu na gefe ta ƙanƙame jikin Dada wacce ke sanƙame bata san meke faruwa ba sbd halin da take ciki. Bata taɓa ganin anyi kisan kai a gabanta ba, yaushe gashi an kashe mata yaya wanda ke kula dasu shi kaɗai ya rage musu. Halisa Danejo Rome ta shiga halin firgici ita kaɗai tai ta razana har lokacin idanunta bai motsa daka kan gawar Hamma Yabi ba a haka Asuba ta risketa. Sarkin ruga da Giɗaɗo ne suka shigo bukkarsu Danejo ba neman iso domin basu damu da cewa Dada matar da za a nemi aminci a wajen ta bace. “Allahu Akbar Allahu ya jiƙan Yabi shai abu bai kyau ba sam” Sarkin ruga ya girgiza kai ya ce “Allah sharki aradu harbi har biyu dole ya mutu” da sauri Danejo ta miƙe jikinta na rawa ta kama hannun Giɗaɗo ta ce “Da gaske Hamma Yabi mutuwa ya yi? Da gaske ba zan sake ganin Hamma ba?” Ta faɗa cikin rauwanin muryar kana ganinta kasan damuwa ta jima da kama zuciyarta ta samu waje ta zauna. “Ya mutu mana kamar yadda Baffanku ya mutu ba zai dawo ba” ƙurr ta kafe Giɗaɗo da idanu kafin taja numfashi mai tsayi sai kuma ta sulale a wajan ta faɗi babu numfashi.
A hankali take buɗe idanunta wanda sukai mata nauyi, hannunta ta kai tare da dafa kanta wanda yake mata ciwo sbd barcin data daɗe ta nayi. “Sannu kin farka Danejo?” Shatu ta furta cikin murnar ganin Danejon na motsi bayan suman da tayi. Danejo ta juya tana kallon Shatu kafin a hankali ta buɗe baki ta ce “Ina Hamma Yabi? Ya tafi da Dada asibitin burni?” Shatu tayi saurin faɗin “Hamma Yabi ya mutu ai kuma har an rufe shi a ƙasa” zuciyar Danejo ta buga da ƙarfi tana runtse idanunta sosai tsoro da fargabar makamar rayuwarsu ta dirar mata a zuciya, yaya za tayi da Dada? Ina zata samu kuɗin asibiti ko shanu zata siyar? Mai Hamma Yabi ya yiwa wannan mutunan da shi kaɗai kawai suka kashe cikin Rugar Rome?.
Juyawa tayi ta sake kallon Dada wacce kawo yanzu ko motsi ba tayi ruwa ma idan aka bata ta gefen baki yake zubewa, hawayen da take maƙalewa suka sakko daga cikin idanunta Shatu wacce ke shirin yin kuka ta ce “Kuka ki ke Danejo? Me akai miki ba ga Dada ba muna tare da ita?” Danejo ta goge idanunta da kyau ta ce “Ba kuka nake ba, ki zauna wajan Dada bari naje wajan sarkin ruga na dawo” miƙewa tayi jikinta sanye da fararen kaya na Fulani sumar kanta ta naɗeta da wani zare mai ɗauke da kuran duwatsu masu kyau. Kanta a ƙasa take tafiya cikin sanyin jiki kamar ko yaushe a haka ta ƙarasa bukkar su Sarkin ruga ta tsaya daga waje tana neman iso. Matar Sarkin ruga ta ce “A’a Danejo ne bismillah shigo” kamar ba zata shiga ba sai kuma ta shiga ta samu Sarkin ruga zaune yana shan kindirmo a diririce ta ce. “Jamɓanduna. Ina kwana” Ya ce “Jamni.. lafiya” zata sake yi masa wata gaisuwar ya dakatar da ita da faɗin “mene ya kawo ki?” Kanta a ƙasa tana wasa da yatsunta ta ce. “daman cewa nayi ko zaka sayi nagge guda biyar daga cikin garkenmu?” Kallon tsaf ya yi mata yana sakin murmushi kafin ya ce.
“Yabi bai faɗa miki ɗan cewa gaba ɗaya ba naggenku bane? Kiwo kawai aka baku?” Cikin rashin fahimtar maganar Sarkin ruga Danejo ta ɗaga kanta da sauri ta kalle shi tana faɗin “Dada ta sanar mini gaba ɗaya garken na Baffanmu ne, shanuwan sa ne, kuma kowa ya sani Hamma Yabi ma yasan da haka” Ya ce “E, to buɗe kunne kiji kaf cikin garken naggen nan guda biyu ne naku, sauran duk mallakina ne kuma yanzu zan ɗauka aje kasuwar burni a siyar dasu, idan kina buƙata sai a haɗa da guda biyun naku a siyar daga nan sai ku biyawa Baffan naku bashin da ake binsa ma” kasa cewa komai tayi ganin ƙarfen ƙafa da ake shirin yi musu, wanne irin son zuciya ne Wannan? A nagge sama da hamsin ace guda biyu ne nasu? Me ya sa Hamma Yabi bai taɓa cewa naggen Sarkin ruga bane? Da gaske nasa ɗin ne ko ba haka bane?. Jiki a saɓule ta dawo gida zazzaɓi na rufeta sbd fargaba. Kenan tana ji tana gani Dada zata sake mutuwa ta barsu basu da kowa a duniya?.
Sheikh Aliyu haydar Aliyu na zaune yana duba yadda ginin bankunan guda biyu suka ɗauki harami cikin ƙaramin lokaci tare da kamfanin sarrafa shinkafa. A nutse cikin kulawa da haibarsa kamar kullum ya miƙawa Umar-khan Album ɗin. “Ina fatan komai ya yi yadda kake so?” Kallo ɗaya Sheikh ya yi wa Umar-khan a hankali ya juya kansa yana mai jinjina shi a nutse alamar “Ya yi” Umar-khan yai murmushi kaɗan yana jinjina halin Sheikh da yawan lokaci ba tare da ya ce komai ba ya juya ya fita. Ɓoyayyiyar Ajjiyar zuciya ya sauke yana mai miƙe ƙafafuwan shi saman table a hankali ya fara tunanin yadda zai gina rayuwar shi wanda zai sanya father farin ciki duk ƙoƙarin shi na gano abin da ke sanya father yaji zafin shi har haka ya rasa, da yawan lokaci abubuwan na damun shi nunawa ne kawai ba ya yi. Zuciyar shi na shiga tunani na tsayin lokaci. Miƙewa ya yi cikin kulawa ya shiga takawa a parlourn na shi, ƙarar wayar shi ta dakatar da shi daga tunanin da yake jin ringtone ɗin is different ya sanya ya fahimci mai kiran na shi. Farar Alkyabbar shi mai fidda ƙamshin Roja ya ɗauka tare da ɗorawa saman jallabiyar jikinsa banda dole ko hannun shi bai son a gani sbd tsarin halittar jikin na shi. Kansa a ƙasa ya nufi Main parlour babu kowa sai Hajjir bai ko kalle ta ba ya nufi sashin Abba Hakimi. A zaune ya same shi saman ladduma gabansa ɗauke da kayan marmari sai ƙwaryar zuba da kuma ta fura da nono. Zama ya yi yana fuskantar Abban na shi cikin mutunci bakin na motsa wa alamar gaisuwa Abba Hakimi ya yi murmushi ya ce. “Ba sai kace ba, Allhamdulillah” Sheikh Aliyu a lumshe idanunsa yana mamakin yadda Abba Hakimi ke fahimtar zuciyarshi da yawan lokuta.
“Naga baka shirin auren naka, kamar dai you’re not ready if i not mistaken?” Sheikh ya buɗe idanu da kyau akan Abba Hakimi cikin mantuwa domin gaba ɗaya ya manta da batun komai cikin In-ina yana riƙe Alkyabbar dake jikinsa da kyau tare da karkatar da kansa yana rufe idanu ya ce. “A…a…au au aure kuma A a Abba?” “E, Aure mana Sheikh haka za ka yi ta zama babu aure ni ma da kaina ban goyi bayan hakan ba, kayi aure kamar yadda Engineer ya buƙata ko dan samun kusanci da shi” Sheikh zai magana Abba Hakimi ya ƙara ɗaga masa hannu ya ce.
“Kada kai musu, ka amince Allah ya sanya albarka, Engineer ya buƙata ka tura kuɗin lefin ita yarinyar tun da ba auren kake so ba, yi maka za ayi na fanshe ka na bada kuɗin lefen kamar yadda suka ce 2.5m zai isa komai na lefen” Sheikh ya ware idanu jin wai 2.5m kuɗin lefen yarinyar da ko sanin kamarta bai ba,baya buƙatar kuma ya sani ɗin.
Cikin kyakkyawan lafazi Sheikh ya sake furta “2.. 2.. 2.5m A aaaa Abba yai yai yawa fa?” Abba Hakimi ya girgiza kansa yana mmkin yadda Sheikh babu abin da ya sani dan gane da rayuwar mace.
“Meke sani Sheikh Aliyu? Kasan kayan mata da tsada, ko kai Alkyabbar nawa kake siya? Duk Alkyabbar ka tafi nawa kuɗi sosai, kuma a arziƙin da Ubangiji ya yi maka dan an taɓa 2.5m har wani abu ne?” Shafa gemunsa zuwa sajansa kawai Sheikh ya yi bai damu da auren ba, amma yaji daɗin yadda Abba Hakimi ke nuna kulawarsa ga duk abin da ya shafe shi.
Abba Hakimi bai nunawa Sheikh ya san komai ga Bankunan da yake shirin buɗewa ba, dan haka sai ya ce “Ka tashi kaje can gidan, kuɗi kuma daman hakƙina ne na aurar da kai daga nan har sadaki” jin Sheikh yaƙi cewa komai ya sanya Abba Hakimi ɗago kansa ganin Sheikh ɗin ya yi zaune jingine jikin kujera ya dafe kansa da hannu bibbiyu zufa na yanko masa tsakanin gashinsa jikinsa na rawa kaɗan kaɗan.
Girgiza kai kawai Abba Hakimi ya yi tare da jawo rubutun da ya yi da safe ya tsiyaya a cup ya zuba zuma a ciki ya juya kaɗan tare da ajjiyeta gefe guda zuwa lokacin da Sheikh ɗin zai daidai a hankali shi kuma yaci gaba da duba wani littafin Tafsir.
Mother na zaune tana girgiza ƙafa cikin damuwa take kallon tilin kayan lefen dake parlourn, da sunan kayan lefen yarinyar da Sheikh zai aura. Yaya Halima ta ce.
“Na daɗe banga kayan lefe mai yawan haka ba, shi Sheikh ɗin har nawa ya bada?” Motar ba ta ce komai ba sai Dr A’isha data kalli kayan da kyau ta ce. “Kalli fa Yaya iya gold guda biyar ne, Wallahi sai na ɗaukar wa su Maimoon kowa ɗaya abar shegiya da ɗaya kawai” Mother ta kalli Dr A’isha ta ce. “Tsinke na kayan nan babu mai ajjiye mini cikin gidan nan, balle su Maimoon su saka ba su rasa komai ba, a barwa wacce aka siyawa”. Dr A’isha ta ce “Amma Barrister kalli kayan fa? Ni dai sai na ɗauka dukiya ai ba hauka bane” cikin faɗa Mother ta ce “Wai meke damunki haka A’isha akwai abin da kika rasa ne balle kayan nan su dameki idan su kike let me know I’ll buy it for you” a sanyaye Dr A’isha ta cewa yayat tata “Am sorry Yaya”… “Sai haƙuri Barrister” cewar Yaya Halima wacce take babba a cikinsu. Miƙewa kawai Mother tai tana faɗin “Idan ban yi haƙuri ba kashe kai na zan? Ina nan dai wlh sai na aurawa Sheikh wata macan ya haɗa mata biyu” Dr A’isha ta ce “Wai ya kaga Sheikh da mata biyu” Dr A’isha ta kalli Yaya Halima ta ce “Nifa ina da shawara Yaya Halima, mai zai hana mu kai kayan lefen nan da kanmu zamu ƙara ganin ita Zahran da ake faɗa sai mu ganu tarbiyyar ta” Yaya Halima ta ce “Gulma zamu kenan? Maza ke kaiwa a bari su kai kawai?” Dr A’isha ta ce “Please mana Yaya Please” da ƙyar Yaya Halima ta amince ta ce zata nemi Engineer domin tasan yadda Mother ta ɗauki Al’amarin ba lallai tai magana ba.
Da daddare duk suna zaune a parlour Mother, Yaya Halima, Dr A’isha dasu Maimoon da auta Fattoumah. Motar Sheikh tai parking a gidan da gudu Fattoumah ta miƙe yana faɗin “Yaa Lee Mother ta Yaa Lee nan” murmushin jin daɗi Mother ta yi ba tare da ta ce komai ba. A hankali ya fito da ƙafafuwansa waje kasancewar shi kaɗai ne da kansa ya yi driving hakan ya sanya gajiya ta saukar masa, yana fitowa Fattoumah na zuwa wajansa da gudu ta ce “Wlcm Yaa Lee” lumshe idanunsa ya yi tare da buɗewa, ganinta ƙarama kuma autarsu ya sanya ya sassauta fuskarsa tare da sunkuyawa ya ɗauke ta da hannu ɗaya, ɗaya hannun kuma ya rufe motar. Gemunsa taja ta ce “Yaa Lee ina kake zuwa muna ta missing naka” ya ware idanu bai ce komai ba sai hancinta da yaja kaɗan.
Da idanu suka bisa yana sanye da shadda ruwan madara babbar riga da jamper bai saka hula ba sai hirami daya rufe kansa da shi fuskar shi mai ɗauke sanje zuwa gemu ta bayyana ta cikin hiramin daya gewaye fuskar. Ƙamshin Roja tuni ya mamaye parlourn da ƙamshi, Maimoon da Zeefa duk suka miƙe tsaye suna sakin murmushi a tare suka ce “Sannu da zuwa Yaa Lee” bai kalle su ba ya tattara hankalinsa gaba ɗaya ga Fattoumah dake masa surutu, bayan ya zauna saman kujera ya daidaita nutsuwarsa da kyau cikin ƙasa da murya ya ce. “Barka” ya faɗa kai tsaye ba tare da In-ina ba, Dr A’isha da Yaya Halima suka kalli juna. “Dani ka ke ko Yaya Halima?” Bai kula Dr A’isha ba ko kallonta bai ba domin yasan nemen magana ce. Tai dry ta ce “Ka gama kame fuska duk girmata da kayi dole ace da mijin iya baba, ko yanzu goma ta faɗi tafi biyar albarka dole na amsa sunan uwa a gare ka” miƙewa yai da Fattoumah ganin Dr A’isha na neman fasa masa kai da surutu. Kai tsaye Upstairs ya nufa ɓangaren father domin amsa kira. Yaya Halima tabi bayan shi da kallo ta ce “Sannu Dr da tsaurin ido, lallai karanki ya kai tsako Sheikh kike faɗawa haka? Sai da Barrister Maryam ta yi aure ta haifi Sheikh da shekaru huɗu ba aka haifeki?” Dr A’isha tai dry ta ce “Wallahi yaya ƙarfin hali ne kawai, amma ba ƙaramin kwarjini ya yi mini ba, gashi ko inuwata bata samu albarkar kallo balle Ni” dry gaba ɗaya sukai. a zaune Sheikh ya samu Father hannunsa riƙe da jarida idan kaga Sheikh da Father ba zaka taɓa cewa Sheikh ne ɗa ba, domin yafi cika idanu da jiki tsayi faɗi uwa uba fuskar Sheikh data samu sumar ƙwarai ta ƙara fidda asalin shi. A kan carpet ya zauna yana sauke numfashi kansa a ƙasa bakinsa na rawar gaida Father ya yi saurin ɗaga masa hannu ya ce. “Bani da lokacin jin faa kakkkkka yayyyya, na kiraka domin ka shirya zuwa Yola wajan Zahrah kafin akai lefe jibi, umarni na baka Aliyu ba shawararka nake nema ba” Jinjina kai kawai Sheikh ya yi bai ce komai ba. “Tashi kaje idan ka zauna ba zaka amfane ni da komai ba, zan bawa Saif-wazir address ɗin” miƙewa tsaye Sheikh ya yi sai da yaje bakin ƙofa Father ya ce “Ka kwana a nan, ban amince ka koma gidan Hakimi ba daga nan har ɗaurin aure” Sheikh ya juya da sauri ya kalli Father wato ya fahimci duk abin da yake masa baya damunsa shi yasa ya sanya Abbansa cikin al’amarin. Juyawa ya yi kamar yadda ya ce ya nufi Part ɗin nasa yana tattare babbar rigarsa.
Washegari tunda ya yi sallar asuba bai koma ba, sbd wani irin mafarki da ya yi, abin ya tsaya masa yana son neman fassarar mafarkin wajan Abba Hakimi amma ya kasa, baya son mafarkin ya dangancin wani jinsi wanda ba nashi ba. Ƙarfe 7 daidai ya shirya cikin Milk ɗin shadda gezner bai saka babbar riga ba, sai golden ɗin Alkyabba daya sanya ya ɗora golden ɗin hirami, da ƙyar ya yi breakfast ɗin da Mother ta kawo masa shi ma sai da ta zauna ya gama jan ajinsa yaci kana ta fita ganin ko ƙala bai ce mata ba. Yana gamawa shirya wa Saif-wazir ya jashi zuwa garin Yola da taimakon Map. Sai da sukai nisa sosai sun ma bar Commission Quarter’s ɗin sun nufi wani waje kamar daga Sama Saif-wazir yaji Sheikh yai gyaran murya kaɗan alamar ya tsaya. Waje ya nema ya yi parking gurin kamar jeji kamar ƙauye kuma. Cikin nutsuwa ya fito yana gyara zaman alkyabbar jikinsa, a hankali ya fara bin wata hanya hannunsa goye a bayansa. Sai da ya yi nisa sosai kana yaja ya tsaya. Kwance ya ganta kanta kife a ƙasa jini na zuba kaɗan a goshinta sai ƙwaryar kindirmon dake gefe guda hannunta guda riƙe da cikinta, da sauri ya zame idanunsa daga gare ta sbd kansa da yaji ya sara yana ƙoƙarin barin wajan wasu ƴan Fulani riƙe da Sanduna suka gewaye shi ɗaya ya ce “Aradu mun kama masu fyaɗen yara” Sheikh ya ware idanu amma bai nuna komai ba, wani ya ce “Wannan kamar kidnama waye kai?” nan ma shiru ya yi bai ce komai ba, Labo da yafi su iskanci ya kalli inda take kwance ganin jini a kanta ya ce “Aradu fyaɗe ya yi mata, kuma tunda kayi mata fyaɗe dole doka ta hau kanka” Sheikh trying to explain amma harshe ya sarƙe. “Kai ku saurara” Saif-wazir wanda hankalinsa bai kwanta da yadda Sheikh yabar motar ba, ya faɗa yana nufu wajan. Ƴan Fulanin suka tsaya ya kalle su sosai ya ce “Kuna hauka wanne irin fyaɗe mai yasa baku da tunani ne, yayi muku kama da wanda zai aikata haka?” Labo ya ce “Alkur’an sai na raɗeka da wannan sandan, ga jini nan muna gani ya kwantar da ita, dole kawai ya amshi hukunci” Saif-wazir ya ce “Wanne irin hukunci kuma?” Labo ya ce “Kai maza kira mana Giɗaɗo” abu kamar wasa kafin kace wani abu kusan gaba ɗaya ƴan Fulanin Rugar Bello suka zagaye Sheikh. Giɗaɗo ya kalli Sheikh kana ya kalli Labo ya ce “Zaro mana zoben hannunsa daka gani mai tsaida ne” Labo ya kama hannun SHEIKH tare da zare zoben, kusan mutuwar tsaye Sheikh ya yi yama rasa me zai ce, sai gumi dake yanko masa ya shigo ne domin tsinkar wani ganyen magani kalli yadda tsautsayi ya rutsa da shi. Kamar daga sama yaji Giɗaɗo na faɗin “Allhamdulillah mun riƙe wannan zoben matsayin sadaki” Saif-wazir ya ce “What sadakin me?” Giɗaɗo ya ce “Ai yanzu muka aura Wannan Balaraban aure da yarinyar nan, ni ne waliyin yarinyar Labo kuma waliyin Balaraban hakan shi ne hukuncin duk wanda ya yi wa wata fyaɗe a Rugar Bello, yanzu da shi da ita mata da miji ne halak ɗin sa ce….
Free pages yana gab da ƙare wa biya kuɗin ka domin shiga Paid book tuni sun yi nisa da karatu😂🤷🏾♀️…. Biya 500 ta Wannan account ɗin 6850917335 Na’ima Shu’aibu Sulaiman fidelity bank. Shaidar biya 08119237616. Ƴan nijar sun yi mini magana.
🌈 IDAN BA KE 🌈
Nimcyluv sarauta
15….
Saif ya ce “Aure kuma? waya ɗaura, dawa kuma?” Sheikh gyara tsaiwa ya yi zufa na yanko masa ta cikin naman jikinsa,kalmar auren ta gigita masa tunani dama lissafi baki ɗaya. Labo ya kalli Saif-wazir ya ce “Aradu aure aka ɗaura musu, babu wanda ya isa ya warware shi sai ikon Rabbi.. kai Giɗaɗo maza jawo mana su cikin Rugar Bello” cikin gargaɗi Saif-wazir ya nuna Labo da hannu ya ce “Saurara fillo kake kowa, an faɗa maka aure wasan yara ne? Kuma wanda kake cewa zaka aura masa ita already yana da aure wajan matar shi ma zamu, don haka babu wani aure idan ma kunyi sai ku warware auren yanzu nan” Labo ya ɗaga sanda sama gaba ɗaya sauran Fulanin suka ɗaga sanda sama tare da zagaye su Sheikh “ƙarya kake Aradu ina shemeka na sheme banza Alqur’anin Allah, aure kuma dole ne hukuncin duk wanda ya yi fyaɗe ko ya nemi lalata ƴar mutane ke nan, ku shige muje Rugar Bello” Saif-wazir zai magana Sheikh yaja numfashi da ƙyar yana girgiza masa kai domin sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi musamman da yake ɓangaren Fulanin suka shigo tsaf za su yi musu gayya. And he doesn’t want that to happen. “But Sheikh….,” Sheikh ya ware idanu wanda suke ɗaukan hankali kamar ba zai ce wani abu ba sai kuma ya yi ƙasa da murya kamar wanda aka ɗauke wa In-inar ya ce. “Saif-wazir” kallon Sheikh kawai Saif-wazir yake cikin mamaki.
Suna ƙoƙarin tsallake ta su shige Labo ya yi saurin faɗin “Waye zai ɗaukar maka matar ka? yadda ka kawo ta nan haka zaka ɗauke ta mu ƙara sa Rugar Bello” a fili Saif-wazir ya ce “Tab…” Domin yasan that’s the first thing da Sheikh can’t do it ba zai taɓa ɗaukan ta ba. A hankali Saif-wazir ya sunkuya zuwa inda take kwance zuciyarsa ta buga da ƙarfi lokacin da idanun shi ya sauka akanta. A ruɗe ya juya ya kalli Sheikh Aliyu haydar Aliyu wanda ya tattare Alkyabbar jikinsa idanun shi rufe lokaci guda jijiyoyin kansa suka fito hakan kuma tabbaci ne na zuciyar shi na kusa, tashin hankalin da Saif-wazir ya shiga lokacin da idanun shi ya sauka akan fuskar Halisa Danejo Rome yafi ƙarfin tashin hankalin da Sheikh Aliyu haydar Aliyu yaji akan batun auren nashi da suke ƙoƙarin ƙaƙaba mishi. Saif-wazir ya daidaita nutsuwarsa wani kuzari na zuwar masa mmkin abin da idanun shi ke nuna masa ya cika masa zuciya. Ɗaukan ta ya yi daidai lokacin da Sheikh ya runtse idanunsa yana juya baya da ɗan sauri bakinsa ɗauke da sunan Allah. Saif-wazir na gaba ɗauke da Danejo Sheikh Aliyu haydar Aliyu na binsa cikin nutsuwa da daddako haɗi da kamala yanayin yadda ya kame kansa yake tafiya zaka ɗauka sarki ko Hakimi ne. Gaba ɗaya ƴan Fulanin suka mara musu baya har zuwa Rugar Bello lokacin tuni saƙo ya isa wajan Arɗo gaba ɗaya sun fito tare da yin shimfiɗa a gaban wata bukka wacce ta cika da yalwar inuwa, tun daga nesa Arɗo ke kallon Sheikh Aliyu har cikin ransa bai na’am cewa zai aikata abin da Giɗaɗo ya faɗa ba, amma ya kasa fahimtar mene ya sanya yaji auren shi ne mafita a gare shi dama su baki ɗaya?. Saif-wazir na zuwa ya kwantar da Danejo wacce har lokacin bata farka daga suman da take ba, jini kuma bai daina zuba daga goshinta ba. Arɗo ya kalli Sheikh cikin mutumtaka ya ce “Ka zauna mana?” Ko inda yake Sheikh bai kalla ba balle ya ama shi, sai ma tsaiwa daya gyara yana ɗan duba time fuskar shi tai jajir. Arɗo ya jinjina kai yana ƙara samun ƙarfin gwiwar abin da zuciyar shi ke ayyana mishi. Cikin nutsuwa ya ce “Sannunku, an kawo ƙarar an kama wancan yana ƙoƙarin aikata abin da Rugar Bello ta hana, wasu sunce ya aikata ga yarinyar nan kwance, bisa doka duk wanda ya yi hakan muna ɗaura masa aure da ɗiyar wannan ya sanya zamu aura masa yarinyar nan a yanzu ba tare da ɓata lokaci ba” Sheikh dai jin abin yake kamar ta tsuniyar yara ko damuwa bai ba, auren Zahrah ba bai taɓa damunsa ba balle na wannan ƴar tayin yarinyar. Saif-wazir ya ce “Amma wannan kuskure ne, idan mutum baya so ba, kuma ai ba haka ake ɗaukan doka ba, shigowarmu garin kenan fa suka fara ihun ya yi me ne kamar wasu marasa ilimi?” Giɗaɗo ya ɗaga sanda zai makawa Saif-wazir Arɗo ya yi saurin cewa “A’a Giɗaɗo, ko ma dai yaya ne kuyi haƙuri aure babu fashi” Modibbo da tun ɗazo bai magana ba ya ce “Sai a karɓi sadaki wajansa ai babu lokaci” Labo ya ce “Ga wannan a wajansa muka amsa” ya miƙawa Modibbo zoben gold ɗin da suka amsa wajan Sheikh. Sai a lokacin Saif-wazir ya ƙara cewa “Ga kuɗi a bada zoben, yana da tsada sosai kuma yana da muhimmanci ga mai shi” Modibbo ya yi murmushin jin daɗi ya ce “Daman abu mai daraja muke buƙata ai” abu kamar wasa akan idanun Saif-wazir da kunan Sheikh aka ɗaurawa Sheikh Aliyu haydar Aliyu aure da Halisa Danejo Rome akan sadakin zoben gold. Modibbo ya zama waliyin Danejo Arɗo ya zama waliyin Sheikh. Mutane kusan ashirin suka shaida daga ciki harda Saif-wazir.
Shiru wajan ya ɗauka Saif-wazir ya rasa ta ya ya zai kalli idanun Sheikh ya ce da gaske Danejo matarsa ce? Zai amince da auren ne ko ya ya? Kamar gilmawar walƙiya haka Sheikh ya juya yana gyara Alkyabbar jikinsa kai tsaye baki n titi kuma ya nufa,ganin haka ya sanya Saif-wazir miƙewa da sauri Arɗo ya ce “Ina zaka baka ɗauki yarinyar ba?” Saif ya juya ya kalleta rauni ya bayyana a fuskar shi har baya son kallon yarinyar gani yake kamar idanunsa ke masa gizau da abin da yake gani ɗin. Da sauri ya ɗauke ta ya marawa Sheikh baya yana zuwa titi ya samu Sheikh zaune acikin mota ya dafe kansa da hannu bibbiyu hayaniyar duk ta sauya masa lissafi baki ɗaya, Saif na shirin saka Danejo cikin motar Sheikh ya ce “N…n.. No!!!!” Ya faɗa cikin tsawa da faɗa idanunsa na fitowa waje sosai da kyau, a tsorace ya ce “Jini na zuba a jikinta kada ta samu ƙarewar jini kuma ba zamu je da ita gida haka ba sai mun fara zuwa asibiti” kallon da Sheikh ya yi masa ya sanya Saif yin shiru yana ƙasa da ƙansa. “Please Yaa Lee Matarka….” Kafin Saif ya ƙarasa Sheikh ya yi wa motar key cikin wani irin azababban gudu ya juya kan motar tare da cillata titi ya nufi hanyar da zata mayar da shi Kano ba tare daya ƙarawa wajan Zahrah ba..
Baki Saif ya saka cike da mmkin zafin zuciya irin ta Sheikh Aliyu da alama za a sha fama kafin Sheikh ɗin ya amince da batun auren Danejo ɗin. Mota ya tsayar ya ce masa asibiti mafi kusa don Allah. Kai tsaye aka kai shi Specialist Yola dake Jimeta. Yana shiga reception yaci karo da wata cikin sauri ya ce “Oh sorry it was a mistake..” Tsaki ta ja ta ce “mistake ko rashin hankali Malam? Kana tafiya kai a sama” kallonta kawai ya yi shi bashi da lokacin ta ma, Saurayina ta ce “Banza kawai” Zahrah da hankalinta ya yi gida sbd zuwan wanda yake shirin zama mijinta ta ce “Wai Surayyerh har lokacin cacar baki gareki ne? Tunda muka zo asibitin nan ki ke neman faɗa” Surayyerh ta ɗaga hannu ta ce “Saurara Zahrah ke tunda kika samu cikin nan kike ji da masifa, daidai nake da ko wanne ɗan iska Wallahi” Saif-wazir ya kalli Zahrah da kyau kaya ne wanda suka kama jikinta sosai hannunta duk farce taci gashin doki, juyawa ya yi ya kalli Surayyerh ba tare ce komai ba ya juya zuwa cikin emergency. Kai tsaye aka bawa Danejo gado Dr ya kalli Saif-wazir ya ce “Suna?” Saif ya shafa kansa sbd sam bai sani ba sai kawai ya wayance da faɗin “Dr ka fara yi mata taimakon gaggawa, sai mu yi magana” Dr ya ce “Dole a buɗe mata file ai” “I knw, amma kulawa da ita ba zai hana buɗe file ba, a duba ta first buɗe file second” Dr ya miƙe tsaye tare da nufar ɗakin da suka kwantar da Danejo abun mamaki ba ita ba alamarta, cikin hanzari ya fito sukaci karo da Saif-wazir ya ce “Yarinyar nan ta gudu bata cikin room ɗin?” Saif ya ce “What?” Da sauri ya juya zuwa waje amma neman duniya babu Halisa Danejo Rome babu ko inuwarta “Innalillahi yau na shiga uku ko dai aljana ce yarinyar nan? Amma babban asibitin irin wannan ina zata?” Ganin bashi da wata mafita ya nemi abin hawa wanda zai dawo da shi Kano domin ba zai iya komawa Rugar Bello ba yace bai ga yarinyar ba, haka kurum su kashe sa a banza.
Ɓangaren Halisa ana kwantar da ita a saman gado A.c ta fara ratsa ta, ta farka da sauri tana dabe kanta, tsoro ya kamata tana mamakin yaushe tazo. Ita dai ta fito tallan Kindirmo ta ce bari ta biya ta Rugar Bello a hanya yunwa da jiri suka yarda ita, kanta ya daki wani dutse bata ƙara sanin inda take ba. Miƙewa tsaye tayi jikinta na rawa ta ce “Hande en boni gidan cire kai aka kawo ni wayyo Allah Dadata na lalashe, lalashewa ta sameni” kuka take sosai har da majina fuskarta tai jaa. Leƙewa tayi ta window taga ashe bayan asibitin ne, da sauri ta kama tagar ta dira baya duk da zafin da kanta ke mata amma haka ta dinga gudu kamar barewa a haka ta isa Rugar Rome. Shiri sosai Zahrah tayi ta tarbar Sheikh amma har dare babu labarinsa baƙin cikin duniya duk ya kamata ga ƙawayenta duk ta tara zata nuna musu haɗaɗɗan mijin da zata aura amma ya kwafsa mata.
Misalin 10:23 Abba Hakimi na zaune a Main parlour dashi da Momi kamar daga sama su kaga Sheikh ya shigo hannunsa guda ɗaya dafe da kansa, Momi zatai magana Abba Hakimi ya Girgiza mata kai alamar tai shiru,babu wanda ya kula ya shige part ɗinsa dake gidan, kai tsaye bathroom ya nufa bayan ya zame kayan jikinsa abin da bai taɓa yi ba shi ne, amfani da ruwan sanyi ya tsaya a shower na sauka akansa sanyi na ratsa masa tsakiyar kansa, sai numfashi yake fitarwa dan kansa ya kashe shower ɗin ya naɗe jikinsa a cikin wata bathroom mai ɗan kauri, idanunsa na rufewa sbd azababban ciwon kai a haka ya kwanta saman gado ya daɗe kafin barci ya ɗauke sa.
“Lafiyar Sheikh ɗaya kuwa?” Abba Hakimi ya ce “Kinga alamar bai da lafiya ne?” Momi ta ce “A’a, kawai yadda na shigo gidan ne” Apple ɗin hannunta da take miƙa masa ya amsa ya ce “Kada ki damu, duk sanda ya yi haka alheri ne ke bibiyarsa” tattaunawa sukai akan gobe za a kai kayan lefen na Sheikh ita ma zata a hankali ya ce “Allah ya kaimu” sai kusan 12 na dare Sannan Saif-wazir ya shigo ganin dare ya yi kai tsaye ya nufi part ɗinsa, motar Sheikh da ya gani ya bashi tabbacin ya dawo gida. Da batun Auren Sheikh ya kwana yana tunanin ya faɗawa Abba Hakimi ko ya yi shiru? Har barci ya ɗauke shi ba samu mafita ba.
Washegari da yamma wajan 5. Dr A’isha ta zabga tagumi Yaya Halima ta ce “Dr wai lafiya tun da muka dawo kike wata kala?” Dr A’isha ta ce “Wallahi Yaya tausayin Sheikh nake, ina zai kai wannan uwar matar? Na girgiza ban san rashin tarbiyyar ta ya kai haka ba, kalli da ita aka amshi kayan lefen fa?” Yaya Halima ta kalli Dr A’isha tana mmkin rashin control na bakinta da bata iya riƙe zance. “Kowa da tsarinsa fa Dr Allah dai ya sanya albarka” daga bakin ƙofa akace “Ba Amin ba, mugun ji da mugun gani ruɓaɓɓan baki ya kau daga kan Gadanga, yau ko ni ko uban Gadanga ya zaɓa” gaba ɗaya suka kalli bakin ƙofa, tana tsaye taci lace ɗauri har gaban goshi ta lafta uban Glasses a fuska wanda ya cinye rabin fuska. Cikin farin ciki Mother ta miƙe tsaye tana faɗin “Jadda” haɗe fuska tayi ta nemi waje ta zauna, Uncle Haroon ya shigo hannunsa riƙe da torelly ɗin Jadda ya zauna kusa da ita. Cikin farin ciki Mother ta ƙara cewa “Sannu da hanya Jadda ashe kina tafe” Jadda ta ɗauke kai sai da Mother tabar wajan, ta juya ta kalli Uncle Haroon murya can ƙasa ta ce. “Munafuka Algunguma duk masifa da yaƙin da ake a gidan fa bata sanar dani ba, shi ya sa na haɗe mata fuska na kame kai na, ba kaga jikinta ya yi sanyi ba, ai wlh yau sai sun bala’i ya sauka” murmushi kawai Uncle Haroon ya yi ta haɗe rai tana ƙanƙantar da idanu ta ce “Kaji masifa ko? Ba murmushi za kai ba cewa zakai nayi daidai” ya ƙara murmushi ya ce “Jadda duk abin da ki kai ai daidai ne” cikin ƙaramin lokaci Mother ta cika gaban Jadda da kaya kala-kala, Yaya Halima da Dr A’isha suka gaidata ta amsa a ciki. “Kinga ba kwaɗayi ya kawo ni ba, maza kira mini mijin naki” Mother ta haura sama yana zaune yana duba Invitation ɗin bikin Sheikh dana Zahrah Mother ta shiga a hankali ya ce “Barrister ya dai?” Kai tsaye ta ce “Jadda na kira” tana faɗin hakan ta juya, yabi bayanta da kallo da sauri kuma ya miƙe shima. A hankali yake sakkowa daga benen yana sakin fuska bayan ya zauna ya ce “Sannu da zuwa Jadda” banza Jadda tayi masa, ta zare Glasses ɗin idanunta ta miƙawa Uncle Haroon, ta cire mayafi shima ta miƙawa Uncle Haroon, fuskar Father cike da tsoro ya ce “Jadda lafiya me kike shirin yi haka?” Bata kula shi ba, ta buɗe rigarta tana nunawa father ta ce “mene wannan?” Kansa a ƙasa ya kasa cewa komai ta ce “Idan ba zaka iya ba, ai Ubangiji ya tsaga mini bakin magana nonon dana shayar da kai ne, kasan Allah tun nonon yana kwance ka lalata batun auren Gadanga da wannan gantalalliyar yarinyar, idan ba haka ba zan ɗaga maka nonon sama ka lalace kaje duk inda zaka…
Not edited
Masu tambayar yadda zasu biya kuɗin IDAN BA KE. Book 1, 2 ne. Mutum zai biya ₦500 har a gama littafin baki ɗaya. 6850917335 Na’ima Shu’aibu sulaiman fidelity bank. A tura shaidar biya ta nan 08119237616.
🌈IDAN BA KE 🌈
Nimcyluv Sarauta
16….
I am proud of my fans wherever they are, nayi mamakin yadda kuka amshi littafin IDAN BA KE fiye da ZAIN-ABEED. Masoya TSINTACCIYA, MOON, UNCLE NE duk ba a barku a baya ba🥰💋for the first time zanyi rubutu akan labarin zanan ƙaddarar soyayya zallah🫰🏿a shirya a gyara zama sosai yanzu aka fara…
TEAM SHEIKH ALIYU HAYDAR ALIYU
TEAM HALISA DANEJO ROME
TEAM EL-BASHIR AHMAD SARKI
TEAM ZAHRAH FAROUK
Jadda ta ƙara cewa “Kalle ni da kyau uwarka ce Jadda, Wallahi nono zan ɗaga maka kawai kabi duniya kaje duk inda zaka Aliyu tunda ka gagara, idan ya so ana nunaka da baki ana cewa gashi can uwar shi tai masa baki ta ɗaga masa nono shi ya sa yake ta galantuyi a duniya, duk wanda bai yarda ba, ni nai maka baki ba zaka iya kawo shi wajena na tabbatar masa” zufa ta dinga yankowa Father a hankali ya zame daga kan kujera zuwa inda take ya ce “Jadda don girman Allah kada kice haka, ki tsaya ki fahimci al’amarin nan I have a reason why I want Sheikh to get married with Zahrah.” Uncle Haroon ya ce “Mene dalilin naka? Uwar yaron nan bata so, I don’t agree either” Jadda dai kaɗa ƙafa take har lokacin tana riƙe da ƙirjinta cikin rarrashi Father ya ce “Jadda don ki fahimce ni Sheikh ba zai iya kula da dukkan al’amarin daya shafi kasuwancina da dukiyata ba, kullum ƙarfina ƙasa yake abubuwa na neman yi mini yawa, na bashi dama yafi sau goma akan ya kawo matar da zai aura amma yaƙi, Umar-khan yace tunda Sheikh yake magana bata taɓa haɗa shi da wata mace ba, kalli sharrin da akai masa tun daga jami’ar Madina, da ace yana da aure babu mai binsa da wannan sharrin shi ya sa na yanke hukuncin aura masa ƴar aminina tasan kan business sosai zata janye hankali Sheikh ɗin zuwa kasuwancin, Jadda ina son Sheikh Aliyu ban taɓa son wani abu kamar shi ba, kiyi mini uzuri ayi auren nan idan yarinyar ba tai miki ba sai ki ɗauki mataki” Mother ta girgiza kai cike da takaicin yadda Father yake tsara zan ce. “Aini duk bani da labarin haka, jiya jiya labari ya saman ana ta yaƙi a gidan naka, kuma yarinyar ƴar iska ce” Father ya kalli Jadda da kyau ya juya ya kalli Mother yana faɗin “ke kika faɗa mata Zahrah ƴar iska ce sbd ba ƴarki bace shi ya sa zaki ai bata musu ƴa?” Rai ɓace Mother ta ce “Ni na faɗa Engineer tunda haka zuciyarka ta shaida maka, kaga yaushe rabon da naje wajanka akan maganar Aliyu ko auren? Aje ayi aure lafiya nima zan zaɓawa Sheikh yarinyar da nayi niyya na aura masa ita” tana faɗin haka ta miƙe tare da nufar upstairs zuciyarta cike da tarin baƙin ciki. Baki buɗe Jadda ke kallon kowa kafin ta ce “Na amince ayi auren kuma na amince Maryam ta zaɓawa Gadanga yarinyar da duk tai niyya” Father ya ce “Amma Jadda daka aura masa Zahrah sai ya yi mata kishiya? Ba ai mata adalci ba” Jadda ta miƙe tsaye tana ƙanƙance idanu ta ce “Wai wacce ƙaniyar ce Zarra ko me? Ba ita ba ko uwarta ka aurawa Gadanga kwaranƙwasa sai anyi mata kishiya, Allah dai ya nuna mini ƴar banzar yarinyar da idanu naga abin da bai mini ba, maza ɓace mini da gani ko mene haɗina da kai dana tsaya shiga sabgar ka” Father ya miƙe tare da barin wajan yana faɗin “A huta lafiya Jadda” sai da yabar wajan Jadda ta sauke numfashi tana raɗawa Uncle Haroon ta ce “Ba gashi ba anyi sulhu komai ya lafa daman duk iskancin mutum ina zuwa shikenan, ai Alsulhu khair” murmushi kawai Uncle Haroon ya yi yana cewa sai Anjima zai dawo.
Sai a lokacin Jadda ta lura da Yaya Halima da kuma Dr A’isha kowa yana danna waya abinsa kasancewarsu masu ilimi da dukiya ya sanya suka kame kansu basu saka baki cikin abin da babu ruwansu ba.
Mother na zaune tana waya da wata friend ɗinta kamar daga sama Father ya faɗo ɗakin cikin faɗa ya ce “Burinki ya cika kin haɗani da mahaifiyata,she insulted me in front of people data hana auren Zahrah da naki auren ma sai ya mutu” tunda ya fara magana bata kula shi ba sai ƙafa da take girgizawa tana ci-gaba da yin wayarta hakan ya ƙona ran Father yaso ta tanka masa ya wanke ta tsaf.
Saif-wazir na zaune gaban Abba Hakimi ya kasa cewa komai. Abba Hakimi ya ce “Ya kai ne Saifuddeen?” Ya sauke numfashi ya ce “Abba ban san ya zaka fahimci maganata ba” Abba Hakimi ya ɗaga kansa tare da kallon Saif-wazir ya ce “Tunda ba zan fahimta ba ta shi kaje” da sauri ya ce “No Abba I’m sorry” shiru yai can dai ya ce “Daman akan zuwa Yola da mukai da Sheikh ne, tsautsayi ya faɗa masa na auren wata ƴar Rugar Bello” Abba Hakimi ya ƙara kallon Saif-wazir da idanun na fahimta a hankali ya ce “Uhm Aure dai?” In short, Saif told Abba Hakimi about everything that happened daga zuwansu Yola har fitar Sheikh mota da zuwan Fulanin har auren da aka ɗaura da zoben Sheikh ɗin matsayin sadaki, har maganar zuwa asibiti da ɓacewar yarinyar.
“Aiki jaa” Abba Hakimi ya faɗa a ransa wannan shi ne dalilin daya sanya Sheikh ya dawo a rikice kenan? “Kace yarinyar ta gudu? Zaka gane ita Rugar?” Saif ya ce “E, ta gudu Abba Rugar ma zan gane domin akan hanya take, amma bana ganin Sheikh zai amince da auren mata biyu lokaci guda” murmushi Abba Hakimi ya yi wanda shi kaɗai yasan ma’anar shi a nutse ya ce “Auren da ai masa na haɗi ne, wannan kuma Ubangiji ya ƙulla, Allah ya nuna mana zuwa Yola ɗaurin aure zamu je can Rugar” Saif-wazir ya jinjina kai alamar gamsuwa ta gefe guda kuma ya kasa faɗawa Abba Hakimi abin da ya gani a tattare da ƴar fillon wanda ya ruɗa masa lissafi ya hana shi bacci daren jiya. “Jirginsu Mai martaba ya tasu, zuwa ƙarfe huɗu zasu sauka yace Sheikh buƙatar ya je ɗakko shi, yanzu kuma lokacin barcin Sheikh ne” Saif ya duba lokaci ya ce “Yana barci tsakanin Zhur zuwa Asr jirgin kuma 4 zai yi landing akwai time Abba” Abba Hakimi ya ce “Mafi mushkila”
Bayan fitar Saif-wazir Momi ta ce “Amma bana ganin wannan auren ya ɗauro fa?” “Me ya sa A’isha?” Momi ta ce “Naga babu wani na Sheikh a wajan sai Saif” jinjina kai kawai Abba Hakimi ya yi yana ci-gaba da rubutun shi ta ce “kayi shiru?” Bai kalleta ba ya ce “Idan kika sake cewa I’ll do the same thing, aure ba shaidu da sadaki yake buƙata ba? Saifuddeen ya ce shaidu wajan 20 a wajan, Zoben da suka amsa kin san darajar shi kam?, Aure ya ɗauro kamar na ko wanne ma’aurata” Momi tai murmushin jin daɗi ta ce “To Allah ya sa albarka,ya sanya matar shi ce har aljanna sai a faɗawa Barrister” nan ma Abba Hakimi ya ce “A’a Maganar ta tsaya iya mu, bana son ko su Umar-khan da Ishaq-hakim suji, hatta Barrister Maryam da mijin nata bana son suji” hira sukaci gaba dayi.
Ƙarfe 4:5 daidai Sheikh Aliyu Haydar Aliyu ya fito sanye cikin dark blue ɗin shadda jamper da babbar riga, sai ƙamshin Roja yake wanda ya a cika parlourn. Ƙafarsa cikin Leather shoe sumar kansa wacce ya rufe da hirami ta sha Ginger Geminal Oil-hair daga sajansa zuwa gemu sai kyallin Luxury Beard oil yake. Bakinsa sai ƙamshin LB Breathe herbal sugar breath freshener spray. Fitowar shi cikin parlourn ya yi daidai da shigowar Abba Hakimi, Umar-khan da Ishaq-Hakim na binsa a baya. “Daman yanzu nake shirin zuwa sashin naka sai gaka” zama ya yi Sheikh yana gyara Babbar rigarsa yau ba saika Alkyabba ba, a nutse cikin kamala murya mai ɗauke da kwarjini ya buɗe baki ya ce “Barka da yamma Abba” kallon kallo akai tsakanin Umar-khan da Ishaq-Hakim jin yau Sheikh bai In-ina ba, Abba Hakimi kam murmushi kawai ya yi hakan bai wani dame shi ba ya ce “Yawwa Sheikh Dadynka Mai martaba ya sauka yanzu kai suke jira” Sheikh ya duba agogo ya riga yasan sai biyar jirgin zai sauka yana komai bisa tsari. Bai ce komai ba ya miƙe tsaye Abba Hakimi ya bisa da kallo yana mmkin sauyawar Sheikh da yawan lokaci kamar mai cin naman wahainiya yanzu zaka ɗauka yana da yara kusan biyar sbd yana yin kamalar shi, amma fuskarsa bata nuna shekarunsa ba kullum cikin kame ta yake.
Yana fita aka buɗe masa bayan mota, Umar-khan yaja Ishaq-Hakim da Saif-wazir suka shiga mota ɗaya sai airport. Zuwansu airport ɗin ya yi daidai da saukar jirgin har lokacin Sheikh na mota bai fito ba. Khalil Ahmad Sarki ne ya fara ɗakko daga cikin jirgin sai Mai martaba Ahmad sarki na uku ya shiga ɗakko cikin nutsuwa hannunsu riƙe da sanda, fari kyakkyawa da shi wanda zai iya yin shekaru wajan 65 da haihuwa. bayan sakkowar Mai martaba wani saurayi ya shiga sakkowa ganin saurayi ya sanya hantar cikin Saif-wazir juyawa, nan take kuma ya tuna da abin da idanun shi ke maza gizau. Zai iya yin shekaru 25 da haihuwa fari kamar mahaifinsa mai martaba har yari Mai martaba kyau da haske, Three-piece dinner suit a jinkinsa saɓanin Khalil Ahmad Sarki dake cikin shiga ta sarauta. Gaba ɗaya suka zube tare da gaida Mai martaba Ahmad Sarki. Khalil nata ware idanun ganin Sheikh can ya leƙa bayan mota ya ganshi zaune ya rufe idanun shi. “I expected to see you right here” Sheikh ya buɗe idanu ba tare da ya ce komai ba, cikin tsokana duk da Sheikh ɗin gaba yake da Khalil ya buɗe masa ƙofa yana faɗin “Ango kasha ƙamshi, Finally the Sheikh will get married, praise the couple’s line” har lokacin dai Sheikh bai kula Khalil ba sai fitowa da ya yi daga cikin motar a hankali ya ƙarasa Wajan Mai martaba ya ɗan sunkuyar da kansa Mai martaba ya ce “Yau gani ga Sheikh tunda yaƙi zuwa inda muke” ya lumshe idanunshi tare da buɗewa ya saki murmushi wanda ya sanya kyansa fitowa sosai.
Sheikh da Mai martaba suka shiga mota ɗaya, Khalil ya shiga bayan motar su Saif-wazir Mai martaba ya kalli matashin saurayin ɗan na shi ya ce “El-bashir…” Wanda aka kira da El-bashir ya ware ido murya a sake ya ce “Mai martaba zan zo” yana faɗin hakan ya juya yana tsayar da mai texsi…
Abu kamar wasa ɗaurin auren Sheikh ya rage saura kwana uku cif. Har lokacin da Sheikh da El-bashir ba a haɗu ba, Sheikh ba manta da wata Yola baki ɗaya balle Auren da yake kansa na ƴar fillo. A ranar aka kammala gina Bankunan Sheikh na Lagos da Abuja, tare kamfanin sarrafa shinkafa an zuba komai da komai ranar buɗewa kawai ake jiran Sheikh ya saka sai kuma ɗaukan ma’aikata.
Yana kwance a bedroom ɗinsa dake gidan father ya miƙe da sauri kamar wanda aka tsikara yana sanye da embrodiery Islamic jallabiya a hankali ya shiga duba contact ɗin wayarsa abin kunya ko number Maimoon bashi da ita, number mother ya kira aka ɗauka cikin dry akace “Yarona ya akai?” Muryar Dr A’isha ta sanya ya kwaɓe fuska ta ce “Ya akai? Ya kamata nazo na saka maka albarka” numfashi ya sauwaƙe “Uhm Maimunatu fa?” Mamakin maganar Sheikh kai tsaye ba In-ina ta cika Dr A’isha da sauri ta ce “Sorry who am I speaking with?” Kashe wayar ya yi gaba ɗaya. Dr A’isha ta juya ta ce “Maimoon kije part ɗin Sheikh wani yana kira” “wani kuma Aunty?” Dr A’isha ta ce “haka dai na fahimta” Maimoon ta miƙe tare da saka hijabi tasan tana zuwa haka zata ci ƙaniyarta. A parlour ta same shi hannunsa riƙe da Black tea wanda ya aka saka zuba a ciki. Jikinta duk rawa yake ganin yadda ya tsareta da idanun ya zame idanunsa ciki rashin tsammani ya ce “Kinga Aljani ne?” T ɗaga idanu da sauri ta kalle shi ta ce “A’a Yaa Lee kayi haƙuri” ya share zan can tana da zaune sai da ya gama shan tea ɗin son ran shi can ya ce “ki nemi number yarinyar nan” sai kuma ya yi shiru ta miƙe tana faɗin “na fahimta” waje tayi kai tsaye ta nufi upstairs part ɗin father lokacin ya gama raba Invitation baki ɗaya “Daughter ya akai ne?” “Father number Anty Zahrah zaka bani mu fara gaisawa kafin tazo” father yaji daɗin haka sosai ya bata number Zahrah ya ce “Baku fara shirin bikin babban yaya bane?” Ta ce “Father anjima zamu saloon gobe mai zana henna zata zo tai mana” waje tayi da sauri ta koma part ɗin Sheikh tare da kai masa number Zahrah.
Zahrah na zaune with her best friends ana musu henna sbd anjima suna da event. Wayarta tayi ƙarar da sauri ta duba text ɗin data gani ya girgiza mata lissafi ta miƙe da sauri ta nufi bedroom ɗinta ganin haka ya sanya Surayyerh bin bayanta ta ce “Wai what’s going on Zahrah looks so worried what’s up?” Zahrah ta ce “na shiga uku Surayyerh kinji abin da Sheikh ya ce” Surayyerh ta amshi wayar ta shiga karanta saƙon Sheikh a fili.
I agree to marry you, on one condition if you become a good woman like Hurul-in, idan na sameki a yadda ba zan taɓa a daren zan tsinke igiyar aure ukun nan…
“Tab ga ƙoshi ga kwanan yunwa, yaya za a yi yanzu?” Zahrah ta ce “Ba wannan ba Zahrah cikin dake jikina shi ne matsalar, kuma zan iya zuwa ayi mini ɗinki yadda Sheikh ba zai gane cewa na san namiji ba” Surayyerh ta ce “Ina da shawara kawo kunne kiji” ta raɗawa Zahrah a kunne Zahrah ta ce “Wow wlh na ɗauka jakar ƙwaƙwalwa gareki yanzu ta ina zamu fara nema, Kinga dai yanzu kira ya saman urgent” Surayyerh ta ce “Deen?” “Mtwss kina da matsala tsakani na da Deen sai after married, muje” shiryawa sukai Surayyerh na driving mota Zahrah na baya har zasu shige cikin Abti America idanun Zahrah ya sauka akan ƙwaryar Kindirmo nan da na kwaɗayi irin na masu yaron ciki ya tasu mata cikin sauri ta ce “Stop the car Surayyerh” Surayyerh taƙi tsayawa da sauri Zahrah taja burkin mota “Innalillahi zaki kashemu Zahrah are you at of your sense?” Zahrah ta fita da sauri tana zuwa ta ɗauki ƙwaryar kindirmon ya shiga sha ba tare da tunanin daga ina ya fito ba, sai ta gama sha kwaɗayi ya faɗa ta kalli ƴar fillon wacce kanta ke ƙasa tana rusa kuka da iya ƙarfinta bata san ma Zahrah ta zo wajan ba ta ce “ke nawa ne kuɗin ki?” Ta faɗa tana yatsuna fuska, Halisa Danejo Rome ta kasa magana sai kuka a hankali Zahrah ta ce “ke dallah riƙe kuɗin ki mtwss” Surayyerh ta ce “Zahrah yarinyar nan kamar zatai daidai da tsarinmu” Zahrah ta kalli Danejo da kyau sai kuma ta saki murmushi ta ce “Ƴar ƙanwata lafiya kike kuka?” Danejo ta ɗago kanta idanunta ya yi jajir cikin kuka ta ce “Dadata ce zata mutu bata da lafiya” Zahrah ta ce “Ayyah ki daina kuka to” ta ce “To ai mutuwa zatai bani da kowa kuma” Zahrah da Surayyerh sukai murmushi Zahrah ta ce “Kina son ta samu lafiya kuci gaba da rayuwa da ita?” Danejo ta ɗaga kai da sauri ta ce “Ina so Aradu ina so” Zahrah ta ce “Good, zan kaita asibitin kuɗi” da sauri Danejo ta riƙe hannun Zahrah ta ce “Da gaske kike? Hamma Yabi yace zai kaita asibitin burni shi ne aka kashe sa” Zahrah tai alamar tausaya wa ta ce “Wayyo ni zan kaita zan kashe kuɗi sosai har ta samu lafiya amma da sharaɗi guda ɗaya idan kin amince” Danejo tai shiru alamar tunani da sauri ta ce “Wanne sharaɗi” Zahrah ta ce “Kinga tunda zan taimake ki nima ki taimake ni taimako na rana ɗaya nake buƙata shi ne madadin alheri da nayi miki” Danejo tai murmushi wanda ya sanya zuciyar Zahrah bugawa sbd kyan yarinyar ta ce “Na yarda zan miki taimakon Adda” Zahrah tai murmushi tana ɓoye jin daɗin ta, ta juya suka kalli juna da Surayyerh ta ce “Tom shikenan idan kina so na kai Dadarki asibiti ta samu lafiya nima ina so ki kwanta da mijina na rana ɗaya ranar da akai kaini gidansa zai amshi budurcinki a matsayin nawa….
Last free pages
A nan na kawo ƙarshen free pages mu haɗu a paid group ga wanda suka biya, idan mutanan da suka biya basu kai 200 ba zan haƙura da sakinsa a whasap na buga shi zuwa kasuwa, ko kuma na sake shi iya AREWABOOKS…. Bugagge na takarda dubu ɗaya ne 1k… A whasap kuma mutum zai biya 500 (ɗari biyar har a gama labarin)… Ka tura kuɗin ka ta nan 6850917335 Na’ima Shu’aibu sulaiman fidelity bank. A tura shaidar biya ta wannan number 08119237616 ƴan nijar sun yi mini magana.
Sai mun haɗu a paid grp masoya💋❤🔥❤🔥 this time al’amarin daban yake salo wanda ban taɓa zuwa da irinsa ba.
Leave a Reply