Hausa Novels

HUSSAIN MIJIN ALJANAH HAUSA NOVELS

HUSSAIN
🌹 MIJIN ALJANAH 🌹
80K
An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Related Articles

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau – kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau – manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau – Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that – we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that – pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that – our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__
SHORT AND TRUE LIFE STORY

 *MALLAKAR*👇

FATIMA SUNUSI RABI’U
Ummu Affan

AREWA WRITER’S ASSOCIATION
💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Page 1-2

Zaune ya ke cikin mota ya bud’e murfin,ya zuro k’afafuwansa k’asa,hannunsa d’auke da wayarsa yana dannawa,zuwa cen naga ya kara wayar a kunne da alama kira yayi.

Zuwa cen naji yace”Hello,ina k’ofar gidanku”,sai naga ya ajiye wayar yana ci gaba da karkad’a keys d’in motar,yasha wani mur,kai kana kallonsa kasan bashi da fara’a,sai wani d’aga kai yake tare da murtuke fuska,sa’arsa d’aya yana da haske da ba k’aramin muni zai yi ba saboda sam bashi da fara’a.

Cikin yanga da yauk’i ta fito daga gate d’in gidansu,kai tsaye wajen motarsa ta nufa,cikin fara’a tace”sannu da zuwa”,a hankali ya d’ago ya kalleta cikin isa da miskilanci,(Ko da yake miskilancin nasa na ganin dama ne,sai wanda yaso yakewa🤪).

Yace”yauwa” yana sake tamke fuska,cikin sanyin murya tace”kazo mu shiga daga ciki mana” da sauri ya d’aga mata hannu yace”kinga Zainab ba wannan ya kawo ni ba,kinsan ba don Hajiya ta takura nazo na ganki ba,babu abinda zai kawoni don haka ki iya takunki.”

A sanyaye tace”amma Yaya Hussain mai nene matsalata anan ko don kawai nace ina sonki” yace”eh ita ce babbar matsalarki”,yana gama fad’a ya ja murfin motarsa ya rufe,ba don ta matsa ba da sai ya mugeta,yawa motarsa key ya bar gurin da gudu.

Bin motar tayi da kallo kafin taja numfashi cike da k’aunar d’an uwan nata tabar gurin tana waiwayen motarsa.

Kai tsaye gidansu ya wuce,yana zuwa yayi hune mai gadi ya bud’e masa ya zura hancin motarsa ciki,guri ya samu yayi parking tare da fitowa ya nufi ciki.

Hajiya zaune a parlour ya shugo,kai tsaye kujerar da take zaune yaje ya zauna kusa ta ita,cikin murmushi ta shafa kansa”my son ka dawo da fatan dai kun dai-daita,d’an turo baki yayi gaba da d’aga gira irin na ‘ya’yan gata yace”no Mum wannan yarinyar fa batayi tsari da ra’ayina ba kawai ki hak’ura zan sami dai-dai da ra’ayina” tace”haba my son mai nene matsalar Zainab yarinya natsatstsayi ga tarbiyya kai-dai kullum zaka sami dai-dai da ra’ayinka kuma har yanzu shuru” Zaiyi magana k’anwarsa Fatima tace”Rabu dashi Mum kullum maganarsa kenan ina ga fa baya son aure ne kawai,bari nazo na rigasa sai muga tsiyar kuma fa ya girme ni da kusan shekaru goma sha biyar” da sauri ya katseta cikin d’aure fuska yace”wallahi ki kiyayeni kafin yanzu kisha duka kin rai nani koni sa’anki ne?,ta 6e baki tayi dacewa”ni ina ruwana kar kayi basai kayi ta zama ba”,kanta yayi da duka da sauri ta tasha ta ruga sama data masa dariya,sosai ya shak’a da hakan yace”Mum kina ganin yarda yarinyar nan ta rainani ko?tace”barni da ita yanzu dai ya maganar Zainab yace”mum mubar wannan maganar ni zan kawo muku mata wacce zakuyi fahari da ni.”

To muci gaba ko mu tsaya?🤪🤪

HUSSAIN 80K MIJIN ALJANA idan kuna so naji ruwan comments hakan zaisa ku sami posting kullum.

More comments more typing,idan naji comments na k’ara muku yawansa akwai chakwakiya kuma labari ne na gaske aha🤣🤣🤣🤣🤣

Ummu Affan.✍️
HUSSAIN
🌹 MIJIN ALJANAH 🌹
80K

SHORT AND TRUE LIFE STORY

    *MALLAKAR👇*

FATIMA SUNUSI RABI’U
Ummu Affan

Dedicated to
Hajiya Maryam Sakatare
Aisha Galadima
Wannan page naku ne,kuyi yarda kuke so dashi 😂

Special Thanks
Ga masu goyan bayan ci gaba da suburbud’o wannan littafi,karku damu yanzu aka fara. 😂

Da k’yau ‘yan Fcbk gaskiya kun burgeni musamman MIJIN KWAILA FANS gaskiya iya wuya ana tare.

AREWA WRITER’S ASSOCIATION
💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Page 3-4

Hajiya ta kallesa tace”to Allah yasa haka dai” yace”hakan nema domin ni matar da zan aura sai kowa yayi mamakinta” Hajiya tace” HUSSAIN Ba dai cika baki ba kar azo ayi za6en tumun dare” yace”haba Mum fatan alkhairi dai.”

Murmushi tayi tace”a kullum muna cikin yi muku HUSSAIN“,Kamar mai tunani sai tace”kai amma nafa mance da d’auko Hafsat kuma kai nace zan aika” HUSSAIN Wanda har ya fara danna wayarsa yace”haba Mum wacece kuma hakan?,tace”bana son shashancin banza har ka mance da Hassu ‘yar wajen Baba k’arami dake k’auye?da sauri ya zaro ido kamar zasu fad’o yace”Haba Mum yanzu saboda Allah a rasa wanda zaije d’auko wannan mahaukaciyar yarinyar saini,bayan ga direba” tace”to ba direban da zashi kasan dai Baba k’arami da fad’a,idan ba kai kaje ba haka zai dunga mita ka sani” Kallon Mum yayi zai magana tace”kar kace komai kaje ka d’aukota duka tafiyar batafi awa guda ba zuwa KUJAMA.”

Ba don yaso ba haka ya tashi tare da mata sallama,yana tafe a mota yana tunani,sarai yasan halin yarinyar bata da hankali sosai,matsalarsa d’aya da ita ALJANUNTA domin tana da Aljanu abin tashin hankalin babu abinda Hussain yafi tsoro irin aljanu.

Haka yana tafe yana tunanin nan har ya kai Kujama,kai tsaye gidansu Hassu ya nufa,kafin ya kai ya hango wasu matasan mata biyu suna fad’a,parking yayi tare da fitowa yana masifa”Ke!Ke!!,bazaku bari ba?,wacce ke kimar d’ayar da alama tafi k’arfi da rashin kunya ta taso da cewa”to Malam ina ruwanka sa’ido sana’ar banza” k’arasowa yayi cike da bala’i yace”ke wa kike fad’awa magana?d’aga hannu yayi zai mareta,ai da ta kurma wani uban ihuww tuni jikinsa ya fara rawa,wani mutum ne ya k’araso da gudu sai da ya iso gurin Hussain ya gane ashe Baba k’arami ne,ita kuwa yarinyar nan tana ganinsa ta k’ara sautin kukanta tace”Baba k’arami kaga wannan mutumin ko?cike da masifa ya juyo yana cewa”wanne mutumin?sai ganin Hussain yayi tsaye kansa yana mazurai,k’ara bud’e ido yayi yace”wa nake gani kamar USAINI?da sauri bakinsa na d’an rawa yace”eh Baba k’arami ni ne.”

Baba k’arami ya fara tafa hannu yace” ehye USAINI kaine kake mugun Hassu,yanzu Hassun kake bugu?, Hussain aransa yace”kuji wannan tsohon kamar yaji ance ya daketa,nai sani ba ashe maganar zuciya ta fito fili saiji yayi Baba k’arami na salati yace”eh lallai USAINI ka girma ni kake fad’awa magana eh lallai wuyanka yayi kauri.”

Girgiza kai da Shafa sumar kansa yayi tare da fad’in “matsala”, muryar Hassu yaji tana cewa”Baba wai daman wannan Yaya WUSAINI ne?(Su wusaini manya😂😂🤣🤣🤪)yace”shine fa bakiga ya kawo girma ba abinda yake fad’a mini”,turo baki tayi tace”Baba dama kace zaizo mu tafi binni ko?bari na ruga gida Iya ta had’a min kayana a leda,kafin ya bata amsa tuni har tasa gudu har tana take k’afar Hussain saboda sauri,ina ta sani ita dai tayi gaba da gudu,da sauri ya janye k’afarsa yana gogewa da fad’in “wash kai-kai yarinyar nan bata da hankali fa.

Baba k’arami ya tasa shi gaba har gida,suna isa k’ofar gidan sai ga Hassu ta fito da leda hannunta da tsummokaran kayanta tace”mu tafi,daga Hussain har Baba k’arami suka bita da kallo.

MORE COMMENTS MORE TYPING

COMMENTS
AND
SHARE

MUJE ZUWA
FATIMA SUNUSI RABI’U.HUSSAIN
🌹 MIJIN ALJANAH 🌹
80K

SHORT AND TRUE LIFE STORY

    *MALLAKAR👇*

FATIMA SUNUSI RABI’U
Ummu Affan

Wannan shafin naki ne Maman Imam comment d’inki na burgeni matuk’a

Hahhhhh🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣 Yau ake yinta fa,wasu sunce wai ya zata kasance da Hussain da Hassu 🤣🤣🤣🤣🤣 Ku biyoni muje zuwa.

AREWA WRITER’S ASSOCIATION
💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Page 5-6

Hussain yace”wannan wanne irin hauka ne,ke haka ake tafiyar?. Da sauri Baba k’arami yace”tofa ni fa matsalata da kai rashin hakuri abun magana bai wuya agareka,yanzu ita Hassu me ta sani wallahi idan har masifa zaka dunga mata gara ma a hakura da zuwan.”

Hussain aransa yace”da hakan yafi” sai ji sukayi Hassu tace”a fasa zuwa ina taf wallahi sai naje,Kai Baba kasan yarda nake mafarkin binni kuwa tabbb”,Baba k’arami yace”tunda tana son zuwa ya zanyi,sai ka shiga ku gaisa da Talatu ka fito ku wuce” ciki ya shiga bayan sun gaisa ya fito,ya shiga mota Hassu ma ta shiga,Baba k’arami yace”uhmmm kai dai Hussain baka da halin k’warai yanzu kazo k’auyen nan ko ‘yar tsaraba nan babu sannan kuma zaka tafi babu ko kyauta,ni kam wannan rowa taka da yawa take”,sai lokacin yasa hannu aljihu ya zaro dubu daya yace”ayi hakuri Baba k’arami ga wannan” amsa yayi yana jujjuya gudar dubun yace”yanzu dubu guda zaka bani saboda tsabagen rowa irin taka to me ‘yar uwata tace ka kawo min” a hankali Hussain ya furta”wallahi mutumin nan ya cika matsala,a fili kuwa cewa yayi”tace zata aiko maka saboda ina sauri yasa ban tsaya amsar sak’on ba” Zaro ido Baba K’arami yayi yace”amma kai USAINI anyi shiryayye bazan fad’i d’ayan ba,yanzu saboda Allah ni kakewa bak’in ciki saboda tsabar bak’in ciki irin naka ka tsaya ka amsa shine kak’i saboda saurinka na banza da wofi to na gode kace mata zuwa jibi zanzo da kaina” yace”to” tare da jan motarsa yabar gurin yana mita.

Sam ya mance da Hassu dake rashe gaban mota yana da mita da cewa”Baba K’aramin nan matsala ne” Sai ji yayi an kece da dariya da sauri ya juyo Hassu ke dariya ba sassautawa kallonta yayi kafin yayi magana yaga ta kalli saman motar tana cewa”Eh mana haka ne fa” sai ta saki dariya,cikin d’aure fuska yace”ke lafiya?bata kallesa ba taci gaba da surutunta.

Sun shugo garin Kaduna,zasu wuce ta gurin wasu masu kayan marmari tace”Yaya Hussain don Allah tsaya ka sayamin” yace”ni ba mahaukaci bane irinki” ganin bashi da niyyar tsaya ta fara k’ok’arin rik’e sitiyarin ai da yaga tana niyyar sa su fara layi a titi ba shiri ya tsaya yada daka mata tsawa,ina ta sauraresa ai da gudu tayi ta fita sai gurin masu kayan marmari,tana zuwa ta zari ayaba ta 6are ta fara ci.

Mai kaya ya bita da kallo cike da mamaki,gani yayi ta zauna saman benci tana cinye waccar ta zari wata tare da d’aukar lemu wanda aka fere ta dasa masa hak’ora,yace”Malama lafiya?tace”ka had’a komai da komai na dubu d’aya” jin ciniki da sauri ya fara had’awa domin da farko ya d’auka mahaukaciya ce.

Hussain ya fito yana wani takon isa,ya k’araso ganin abinda take ya zaro ido yace”ke baki da hankali ne” wai lemu ya fara washe baki yace”ashe tare take da Yayanta wannan yarinyar da gani ‘yar gata ce” Mik’a mata yayi tace”yauwa ashe dai ka gane” gashi nan shi zai baka kud’in” ta nufi mota,mai lemu ya juyo da fara’a yace”oga na 1k ne kawai aka had’a” Zaro ido yayi yace”1k kai baka da hankali zaka bata kayan 1k ina laifin na d’ari biyu” yace”ranka ya dad’e ai ita tace a had’a mata” tsaki yayi yana mita ya basa domin shifa ya tsani kashe kudi ba gaira babu dalili.

Dawowa yayi mota,amma babu Hassu sai dai ga kayanta da lemukanta a ciki,yace”wannan mahaukaciyar kuma ina ts nufa” d’aga kan da zaiyi ya hangota gurin masu kaji,tana ci hannu baka hannu k’warya,da mugun tsoro ya zaro ido,ganin ana had’a mata guda uku cikin leda rik’e baki yayi da sauri tare da zaro ido.

Mota ya nufa da sauri domin ya yajin zai iya biyan wannan kudin sai dai idan basu gansa ba za amsa na ledar su yafe mata wanda taci ko su jibgeta babu ruwansa.

Yana k’ok’arin shiga har sun iso,amsar ledar tayi tare da cewa shi zai biyaku,ta shige ciki,suka ce”Alhaji dubu biyar ne” cikin masifa yace”ni kunga na muku kama da Alhaji ne?ko kuwa tsabar rashin mutumci?,mutumin yace”Allah yabaka hakuri Malam”,cikin tsawa yace”waye Malam?kai kafa kikayeni”,mutumin yace”koma dai menene fara biyana kud’in kazar na wuce” yace”ni naci da zakace na biyaka?,Hassu ta lek’o daga mota tace”wai Yaya Wussain ka basa mu wuce mana” wata harara ya buga mata tare dasa hannu aljihu aransa yana cewa Wallahi sai nayi maganin yarinyar nan tunda ta sani asara ba gaira babu dalili.

Biyansa yayi,mutumin na magana bai kukasa ba domin ji yaje kamar ya makesa wai ansashi asarar dubu shida lokaci guda me yakai wannan takaici🤪🤪🤪(Don a gurin Hussain dubu shida kamar Dubu dari shida take🤣🤣🤣🤣).

Shiga mota yayi yana mita da haka suka isa gida,yana parking ya fita cike da k’uluwa Hassu tace”Yaya WUSAINI kazo ka d’aukar min kayana mana.

🤣🤣🤣🤣🤣

MORE COMMENTS MORE TYPING🤸‍♀️🤸‍♀️

COMMENTS
AND
SHARE

MUJE ZUWA
FATIMA SUNUSI RABI’U.HUSSAIN
🌹 MIJIN ALJANAH 🌹
80K

SHORT AND TRUE LIFE STORY

    *MALLAKAR👇*

FATIMA SUNUSI RABI’U
Ummu Affan

Marubuciyar👇
UWANIN QAUYE
CIKIN WAYE?
NIDA YAYA LAMEER
KAINE SANADI
NAYI GUDUN GARA…
IZGILI
K’URUCIYAR SAPNAH
MAHAD’IN RAYUWATA
SANDAR MAKAUNIYA
AND NOW👇

    *HUSSAIN*
     _MIJIN ALJANAH_

AREWA WRITER’S ASSOCIATION
💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Page 7-8

Wani kallo ya mata da cewa”waye d’an dakonki?sakkowa tayi tare da dire basa ledar kayanta gabansa sannan ta d’auki ledar kazinta da su lemunta tayi gaba.

Tsuwww yaja tsaki tare da d’aukar ledar yace”wallahi Mum ta kawo mana matsala gida” domin shi fa gani ya ke Hassu ba kanta guda ba.

Kasancewar Hassu ta ta6a zuwa gidan yasa ta gane hanyar domin duk idan Baba k’arami zaizo wato mahaifinta tare suke zuwa,hakan yasa kai tsaye parlourn gidan ta nufa HUSSAIN na biye da ita.

Fatima da ke zaune parlour tana ganin Hassu ta tashi da murmushi tace”Laaaah Hassu sannu da zuwa” tace”yauwa tare da dire kayanta tsakiyar parlourn ta zauna,Hussain da ya k’araso ya jefa mata kayanta kusa da ita ya haye sama,yana mita,Fatima ta dunga dariya k’asa-k’asa.

Fatima ta jata zuwa bedroom d’inta,tana cewa”Hassu wannan kaji haka ba dai daga k’auye aka saki ki kawowa Hajiya ba?cike da shiririta irin tata tace”Yaya WUSAINI YA sayamin a hanya” sosai Fatima ta zaro ido tace”kai da gaske Yaya Hussain mai mak’o wanda d’ari biyar kafin yabaka aiki ne shine ya saya miki kazi har uku?Sosai Hassu tayi dariya sai-dai bata ce komai ba.

Fatima tace”bari na d’auka a sake d’umamawa lallai yau zamuci tafarrakin uban ‘yan mak’o,zata d’auki Kajin taga su lemu tace”wannan kuma fa?sosa kai Hassu ta fara tare da rank’washin kan kamar mai kwarkwata tace”duka duk ya sayamin. Fatima bakinta ya kasa rufuwa sosai take mamaki sai tayi murmushi ta had’a dasu tace”bari a wanko” sannan ta fita zuwa kitchen.

Ko da Hassu tayi wanka,wasu ko d’ad’d’un kayanta ta saka riga da zani da kallabi irin mai santsin nan,ta zana ja gira da wani jan gazar nata da ta taho dashi ta ranbad’a kwalli tayi d’igo-d’igo a kumatunta da goshi.

Sannan ta fito,lokacin Hajiya ta fito Hussain ma shugowarsa kenan ya dawo masallaci,gurin Hajiya ta k’arasa tace”ina wuni Inna” Hajiya tana murmushi tace”Hafsat lafiya k’alau,kun shugo ina sama na shiga sallah fatan kun sauka lafiya,ta washe hak’ora”lafiya k’alau Inna sai-dai Wallahi tallahi kinji na rantse kuwa wannan Yayan Wusainin yayi ta min fad’a wai zai dake ni”

Hussain wanda tun tahowarta yake harararta yace”nayi miki fad’an damma ban faffasa miki baki ba asarar da kika sani” da sauri tace”yauwa Inna kinji ko?,Hajiya da Fatima da babu abinda suke sai dariya Hajiya tace”kiyi hak’uri ‘yata Yayan ne naku da bak’ar zuciya kamar tsohon kuturu” Kallon Hajiya yayi fuskarsa babu walwala yace”abinda zaki ce kenan Hajiya bayan na sanar miki duk kan abunda ya faru tun zuwana Kujama har dawowarmu” Hassu ta d’aure fuska tare da zama tana harare harare.

Hajiya tace”ni kuna rud’ani na rasa bayan wa zanbi to duka kuti hakuri yarana”,tashi Hussain yayi ya wuce ciki Hajiya tace”Hassu haka yake da zuciya ga saurin fushi halinsa haka yake don haka ki iya zama dashi” Hassu aranta tace”ai kuwa haka wallahi zai ganene,bayana min kallon bagidajiya ba ‘yar k’auye da wannan zanyi amfani na gyara masa zama.

Fatima ta kawo naman sukaci gaba d’aya suka k’oshi suka sha kankana lemu da ayaba sannan suka kora da ruwa mai sanyi,Fatima tace”yau wace rana munci ta farrakin Yaya Hussain sarkin ‘yan mak’o.

Hajiya tace”wallahi babu ruwana idan yajiki ke da shine”,Ranar basuci wani abinci ba saboda sun k’oshi da naman nan.

Washe gari da safe,Hussain ne ya sakko cikin shirinsa na fita kasuwa,kasancewar babban shago ne garesu na sayar da atamfafo shadda yadi les kai duk wani abu da ya shafi kayan sawa suna sayarwa shagon Yayansa ne (HASSAN ATK)Kasancewar shi Hassan yana cen k’asar India to shi Hussain ke kula da shagon🤪🤪🤣🤣tare da sauran amintattun Hassan d’in.

Hassu wacce tun lokacin da ya fara bud’e k’ofa ta fito da sauri daman tun asuba da tayi sallah taje kitchen ta kad’a omo da ruwa da mai kad’an cikin k’aramar roba,jin yana bud’e k’ofa yasata saurin sakkowa tazo saitin k’ofarsa ta juye ruwan omon sannan ta shige cikin labule,

Fitowar da Hussain zaiyi cikin shirinsa ya d’au wanka sai tsantsi ya jamesa timmmm ya fad’i k’asan tass saboda wahala sai da ya saki k’ara,Hassu ta fito daga cikin labure tana shek’a dariya da cewa”wohwohwoh ya fad’i kuzo kuyi kallo,Fatima ce ta fito da sauri tana tambayar lafiya?ganin yarda Hassu ke tun tsura dariya ta kalli gurin da take kallo zaro ido tayi ganin Hussain 80k zube a k’asa ya kasa tashi,gaba d’aya jikinsa ya 6aci.

MORE COMMENTS MORO TYPING🤸‍♀️🤸‍♀️

Yasin,Yasin WhatsApp ku gyara ina son jin comments idan ba haka ba kuji d’if ato.HUSSAIN
🌹 MIJIN ALJANAH 🌹
80K

SHORT AND TRUE LIFE STORY

    *MALLAKAR👇*

FATIMA SUNUSI RABI’U
Ummu Affan

DEDICATED TO
My k’awar amana Rukayyat Ibrahim Lawal (Ummu Inteesar) Allah ya bar amana,Ya kaimu ranar bikin amin,Sannan ya bawa jinin jikinki lafiya mai d’aurewa yasa kaffara ne,ina yinki over my K’awata🥰

SPECIAL GIFT TO
Hauwa S Zaria
Anty Hauwa Mmn Uswan,Alkhairin Allah ya kai miki har gadon barcinki,ina yinki over my Antyna.🥰

AREWA WRITER’S ASSOCIATION
💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Page 9-10

Hussain wanda ji yake kamar ya karye k’ugu ya d’ago fuska murtuke yana dubanta,dai-dai fitowar Hajiya wacce ke cewa”K’arar me naji kamar abu ya fad’i?ganin Hussain k’asa warwas ta yi saurin k’arasawa da rik’esa”Hussain lafiya?saboda tsananin takaicin da yakeji ya kasa magana ma.

Tuni Fatima ta dena dariya,Hassu kuwa tasha wani mur kai ka rantse da Allah ba ita tayi ba.

Da k’yar Hajiya ta iya kaisa saman kujera,tasa Fatima ta d’aura ruwan zafi domin dole sai an masa gashi idan ba haba kuwa zaiji jiki,babu abinda yake sai hararar Hassu.

Zainab ce tayi sallama,rik’e da akwatinta a hannuta tana ja,duka suka zuba mata ido bayan sun amsa sallamarta,da sauri ta saki akwatin tare da k’arasowa gurin Hussain tace”Laaah Yaya Hussain lafiya?me ya sameka?,harara ya zuba mata murya ciki-ciki yace”me ya kawo ki gidanmu harda akwati?,k’asa tayi da kai tace”na cewa su Mama ni dai zan dawo nan gidan kuma sun amince” yace”amma baki da hankali” Hajiya tace”to meye a ciki don ta dawo nan gidan karka manta da mahaifinta da mahaifinku wa da k’ani suke don haka Zainab je kikai akwatinki d’akinsu Fatima”tace”to Hajiya na gode.”

Fatima ta kama mata zuwa ciki,Hassu ta bisu sa harara.

Bayan ruwan ya tafasa,Hajiya da kanta ta saka towul tana matsa masa bayan ya cire riga,me Hassu zatayi ba dariya ba ganin yarda yake rik’e hannun Hajiya da cewa”don Allah kiyi a hankali da zafi fa” tace”dole a gasa maka kar wajen ya suntuma. Zainab tace”don Allah Hajiya ki masa a hankali,wacce dawowarsu kenan da Fatima da tashiga da akwatinta ciki.

Cikin d’aure fuska yace”wai ina ruwanki ne?,cike da tausayi tace”Allah ya baka hakuri” tsuww yaja tsaki,ita dai Hajiya girgiza kai tayi tana ci gaba da matsa masa da haka har suka gama yana raki da cewa ta bari.🤪

Misalin k’arfe,shidda na yamma suna zaune a parlour dukansu,Hassu ta saka k’ara da ihu,kafin kace kwabo dukansu sukayi kanta da tambayar lafiya?ganin yarda idanuwanta ke juyewa yasa Hussain farayin baya aransa yana cewa”daga gani wannan ba ita bace gara na gudu”,ai saiji yayi cikin wata siririyar murya tace”karda ka sake d’aga k’afarka daga gurin” a mugun rud’e ya juyo yana dubanta tashi tayi ta kalli Hajiya Fatima da kuma Zainab tace”ya naga kun zuba min ido?da sauri dukansu suka maida idanuwansu k’asa cike da tsoro.

Tace”Yanzu abinda nake so shine dukanku ku runtse idanuwanku,babu musu suka runtse domin duk tunaninsu aljanin ne ke magana ita kuwa a gurin Hassu tsabar shak’iyanci ne irin nata take son basu tsoro da sunan aljanu,tace”Tana so Hussain ya hau bene da rarrafe idan ba haka ba kuwa yau za’ayi mamaki a gidan nan” Zainab tace”haba ke kuwa ya za’ayi kice hawa bene da rarrafe ai abun da kamar wuya,tsawa ta daka mata tace”ke dakata kinsan ko ni wacece kuwa?to nice Aljanar Hassu ba Hassu bace sannan wannan da kike gani shine HUSSAIN MIJIN ALJANA mijin aljanar Hassu,ai daga Hajiya har Fatima suka bud’e idanuwansu,batse baki tayi da zazzaro ido kai idan ka kalleta a lokacin tsaf zakace mai aljanu ce,tace”ko yayi ko yanzu na juya gidan nan,ai Hajiya da sauri tace”Hussain kayi don Allah,da sauri ya nufi bene gar yana tuntu6e,Hassu ta kusan sakin dariya ta dai daure,haka HUSSAIN yayi rarrafe ya hau saman bene,gwiwowinsa babu abinda suke sai rad’ad’i(Wayyo cikina🤣🤣🤣🤣).

Hassu tace”to kowa ya runtse idanuwansa Aljanar Hassu zata wuce” da sauri suka rufe idanuwa,kallon inda Hussain yake tayi wanda babu abinda yake sai numfashi ya jingina da garo tace”kaima ka rufe idanuwanka da sauri ya rufe.”

Dariya tayi k’asa-k’asa sannan ta koma gurin zamanta,saiji sukayi ta fara wak’a” Cikin raina na sanyoka ka bani guri kaima in shugo naka duka suka bud’e ido Fatima tace”Hassu” kallonta Hassu tayi irin bata san abinda ke faruwan nan ba tace”Yaya Fatima me ya faru” Hajiya najin haka ta tabbatar aljanar ta tafi sai tayi saurin isa gurin Hussain tana masa sannu haka Zainab.

MORE COMMENT MORE TYPING

MUJE ZUWA
FATIMA SUNUSI RABI’U.

COMMENTS
AND
SHARE

MUJE ZUWA
FATIMA SUNUSI RABI’U.HUSSAIN
🌹 MIJIN ALJANAH 🌹
80K

SHORT AND TRUE LIFE STORY

    *MALLAKAR👇*

FATIMA SUNUSI RABI’U
Ummu Affan

AREWA WRITER’S ASSOCIATION
💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Page 11-12

Ranar dai haka Hussain ya wuni a gida babu batun zuwa kasuwa,da ya kalli Hassu yaji kamar ya shak’eta saboda haushi gashi ba hali domin yanzu mugun tsoranta yake musammanma aljanarta.

Hassu kuwa tunda ta gane hakan ta tsiro da wulak’anci kala-kala da sunan aljanarta ce wacce tace”matar Hussain,sosai Zainab ke jin haushinta gashi da tayi magana yanzun Hassu ta tada aljanun,kamar jiya abinda ya faru,suna zaune bayan sun kammala breakfast sai Hassu tasaka dariya ganin yarda Hussain ke d’ingishi saboda fad’uwar da yayi,tace”ayya Yaya Wussaini na lura jiyan nan fa kaji jiki.

Tun kafin yayi magana Zainab tace”waike Hassu meye haka ? Wallahi zanci mutumcinki akan rashin kunyar da kikewa Yaya Hussain. Harara Hassu ta jefa mata tare da zaro ido tace”eh daman harda ke ciki. Sai Hassu ta mik’e ta nufi hanyar k’ofa sai kuma ta dawo sai gani akayi ta shak’e wuyan Zainab akayi-akayi taqi sakinta da qyar Hajiya ta qwaci Zainab ai kuwa tasha baqar azaba,tun daga lokacin ta dena sa mata baki a cikin abunta,sai dai ido da harara domin sosai take jin zafin abinda Hassu kewa Hussain.

Baba k’arami ne yau yazo gidan,Hassu tayi farin ciki da zuwansa haka Hajiya,Hussain yana ganinsa yace”yauwa Baba k’arami kazo tafiya da Hassu ne ?, wata harara ya banka masa yace”nazo tafiya da ita ko dai na kawo mata ragowar kayanta ai ita kuma ta sami gurin zama.” Hussain yace”a’ina ? ” Baba k’arami yace”kai bana son shaqiyancin banza fa yo a ina take ba cikin gidan nan ba.”

Hajiya tace”hakan na da k’yau daman ina son na mayar da ita makaranta naji dadi da kamar min ita ko ba komai zata san wani abu ilmi na da dadi sosai” yace”yauwa ‘yar uwata na gode sosai. Ya d’aura da cewa daman Hussain yace kin basa saqo ya bani saboda baqin cikinsa da rowa irin tasa bai amsar min ba wai saboda yana sauri shine nazo amsa.”

Hajiya ta kalli Hussain shima Hussain ya kalleta yana k’if-k’ifta ido,kai da ka kallesa kasan ya zubowa Hajiyarsa k’arya ne,tace”eh haka ne,bari na kawo maka” domin bata so tace”Hussain ya mata qarya ne a gabansa” tana shiga d’aki ta zage jaka dubu ashirin ta irga ta dawo ta basa,Baba k’arami ya dunga godiya da cewa”Allah ya raya miki zuria yaji k’an magabatanmu tabbas Hajiya ke ta gari ce” ita dai ba abinda tace”bayan amin.

Hassu wacce ke zaune kusa dashi tace”To Baba yanzu mai zakayi da kud’in nan?yace”ke kinci k’aniyarki ni sa’anki ne har tambayata zakiyi abinda zanyi da su. Tace”Allah ya baka hakuri Baba” cikin maqe murya yace”Hassatu sai-dai naga tunda nazo ko ruwa ba abani ba bare nasa ran abinci.

Hajiya wacce zurum a kunnanta ta kalli Fatima tace”ki kawowa Kawunku abinci” ta amsa da to ta nufi kitchen.

Hussain yana harararsa ya nufi sama,aransa yana cewa”uba da ‘ya duk halinsu guda” sai da Baba k’arami ya cika cikinsa harda guzurin wani aleda wai zai kaiwa Talatu sannan,Hajiya da Hassu suka rakashi har bakin gate sannan ya musu sallama ya wuce Kujama.

Su kuma suka koma ciki Hajiya na k’ara tunanin d’an uwan nata Hassu kuma na k’umsa abinda zatawa Hussain yau tunda har ita ce wai yake so tabar gidansu.

MORE COMMENTS MORE TYPING🤸‍♀️🤸‍♀️

MUJE ZUWA
FATIMA SUNUSI RABI’U.HUSSAIN
🌹 MIJIN ALJANAH 🌹
80K

SHORT AND TRUE LIFE STORY

    *MALLAKAR👇*

FATIMA SUNUSI RABI’U
Ummu Affan

DEDICATED TO
YUSUF NUHU Wannan page d’in naka ne kayi yarda kake so dashi,ina jin dad’in k’aunar da kake nunawa wannan littafin,ina godiya matuk’a,kana d’aya daga cikin masu samin k’warin gwiwa domin suburbud’o muku wannan labarin ina godiya Angon Fadeelah.

AREWA WRITER’S ASSOCIATION
💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Page 13-14

Suna shiga kuwa da ta kurma wata uwar k’ara ita kanta Hajiya sai da ta furgita,Zainab da Fatima da ke zaune parlourn suka tashi da sauri suna kallonta.

Muzurai ta fara tare da k’if-k’ifta idanuwa da zaro su,Hajiya ta kalli Fatima tace”Fatima ko dai zaki kira mana Malam Hadi ne,Malam Hadi malamin Islamiyyar su Fatima ne bashi da nisa da gidansu,Hajiya ta d’aura da cewa”abin yayi yawa kar azo a sata cikin wani halin gara a kirasa ya mata ruk’iyya.”

Hassu na jin haka cikinta ya d’uri ruwa tasan idan aka kira Malami asirinta ya gama to nuwa,don haka ta fara shawarar abinyi a zuciyarta domin in har ta bari aka kira Malamin kashinta ya bushe.

Cikin mak’ak’k’iyar murya da mak’e tace”ai duk wanda ya fita nan da bakin gate akwai matsala,abu guda kawai za’ayi aljanar nan ta tafi shine a kira WUSAINI ya kai Hassu gurin masu kajin nan ya sake saya mata,idan ba haka ba kuwa yau akwai daru” Hajiya wayarta ta ciro ta kira Hussain bai san abinda ke faruwa ba ya fito.

Hajiya ta fad’a masa,d’aure fuska yayi da kallon Hassu yace”da kud’in wa?Hajiya tace”bana son tashin hankali bari na baka dubu biyar sai ka siya mata” da sauri Hassu tace”ai idan har ba kud’insa ba to a kyau fa matsala don yasin-yasin yau d’akinsa zan kwana kuma zai gamu da gamonsa” Hussain najin haka yace”a’a baza ayi haka ba muje na saya miki”

Gaba yayi Hassu ko mayafi ta bi bayansa da Sauri Hajiya tasa Fatima d’auko mata hijabi ta kai mata.

Zainab ta cika tayi famm ji take kamar ta mak’ure Hassu saboda haushi,ita tazo gidan ne domin su k’ara kusanci da Hussain ko zai sakko daga dokin zuciyar da ya hau ya fara kulata har ayi maganar bikinsu,amma ta kula wannan yarinyar Hassu tana son kawo mata matsala dole tasan abinyi kuwa,domin ita ta fara k’aryata yarinyar nan gani take ko dai aljanun k’arya take fomin masu aljanu ai ba haka suke ba,amma idan ta tuno shak’ar da tayi mata sai jikinta yayi sanyi domin tasan mutum dai ba zai mata wannan shak’ar ba.

A mota kuwa Hassu babu abinda take sai murmushi da waqe-waqenta domin fagen rawar kai da son waqa tana sahun gaba.

Wak’ar mawak’inta UMAR M SHAREEF ce Hussain ya kunna ita kuwa tana son wak’ok’insa don tana da haddar wasu da yawa,hakan yasa take bin wak’ar tana karkad’a kai kamar kad’angaruwa.
Duk wanda yassamu gurin rabbi ya dace.
Samu rashi na rabbi ne karda ku mance.
D’auka kasa aranka ni taka ce.
In munyi aure na zarcewa tsarahhhhahhhh.
Tasa tafi da dariya kamar wata zararra,girgiza kai kawai Hussain yayi aransa yace”mahaukaciya kawai.

Sun iso gurin masu kaji,tun kafin ya gama parking ta fice da gudu,mai nama yana ganinta ya washe baki domin ya ganeta musamman da yaga Hussain na binta a baya yasan zayayi ciniki da su,”Sannu da zuwa” yace da ita cikin fara’a tace”yauwa” sannan ta sami guri ta zauna tana kallon gajin nan ta fara nuna wad’anda take so,manya guda biyar,da sauri ya kalleta yace”biyar kuma wannan cen karon ai uku kika d’auka,tace”eh wancen karon nasan mutum uku ne a gidan harda ni Hajiya da Fatima wannan karon kuma an k’ara Zainab kaima gaka ai ido guba ko” da sauri mai kaji ya amshe da cewa”wannan gaskiya ne ‘yan mata.

Haka ya biya ransa na suya sannan kuma tace”dole ya saya mata su lemu wannan karinma babu yarda ya iya haka ya biye mata amma yasan dole sai yayi zazza6in kud’ad’an nan da tasashi ya kashe,ransa 6ace yake tuk’i ita kuwa komai wasai sai cin Apple d’inta take tana kallonsa ta k’asan ido ta tuntsure da dariya.

MORE COMMENTS MORE TYPING

MUJE ZUWA
FATIMA SUNUSI RABI’U.HUSSAIN
🌹 MIJIN ALJANAH 🌹
80K

SHORT AND TRUE LIFE STORY

    *MALLAKAR👇*

FATIMA SUNUSI RABI’U
Ummu Affan

WANNAN page sadaukarwa ne ga duka masoyan wannan littafi,gaskiya ina jin dad’in yarda groups da yawa suke son wannan labari nima ina sonku FISABILILLAH kuji dad’inku page d’in nan naku ne.

AREWA WRITER’S ASSOCIATION
💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Page 15-16

Bayan sun isa gida,haka ya bita da dakon kaji yana wani kumbura kamar zai fashe,ita kuwa tana dariya k’asa-k’asa ta d’auki ledar su lemu tabi bayansa,har lokacin su Hajiya na parloun saboda ba’a kira sallah ba bare su tashi.

Da sallama suka shugo,suka amsa,gaban Hajiya ya ajiye ledar kajin,zaro ido tayi ganin da k’walan kaji har biyar tace”Hussain kana hauka ne. yace”to Hajiya ya zanyi tunda haka ta ke so” yarda yake maganar kai kanka da kaji kasan ransa a 6ace yake.

Kallon Hassu tayi wacce lokaci guda ta sauya fuska jin abinda Hajiyar tace,ganin yanayin da ta shiga yasa Hajiya tace”ok na gane hakan yayi” sai lokacin Hassu ta saki fuska tace”Hajiya kowa fa d’aya harda shi kinga daman mu biyar ne” tace”haka ne ‘yar albarka” Fatima da dariya ke cinta tana daurewa ta kasa,saiji akayi ta fashe da dariya,Hussain iya harzuk’a ya harzuk’a yace”ke da ubanwa kike?bakinta a hannu tana k’ok’arin ta tushe bakinta ko dariyar zata tsaya amma hakan ya fassakara dariyar tak’i tsayawa,kanta yayi ya kai mata mari Allah ya bata sa’a ta goce ya mari iska,wani marin yake niyyar kaima da ta gane da sauri ta ruga,sai da takai k’ofar d’akinsu tace”ayya Yaya Hussain sorry wallahi dariyar kud’in da ka kashe nake nasan ko ba komai yau sai ka kwana da zazza6i sanin halinka da nayi akan kud’i.”

Ai da gudu yayi kanta sai-dai kafin ya kai harta shige bedroom d’insu ta danno k’ofa,bugun k’ofar ya fara ransa 6ace da cewa”ba zaki bud’e ba sai na karya” Saman bed ta fad’a domin ta murza key tasan kuma babu yarda za’ayi ya bud’e bare har ya iya karya k’ofar,har lokacin dariya take tana cewa”gaskiya Hassu k’arshe ce,tasan salo da hanyar lagon Yaya Hussain” shi kuwa sosai ya k’ulu ji yake da zasu had’u da Fatima a lokacin zai iya karyata.

Ranar ma su Hajiya Fatima da Zainab sai oganniya Hassu haka suka sha bidirinsu na cin kaji duk kuwa cinsu kasa cinye kaji hud’u sukayi,domin an kaiwa Hussain tasa wanda saboda tsabar haushi kasa cin tasan yayi ko kallonta baiyi ba,Sai-dai kuma zuwa cen bayan ya dawo masallaci yaji k’amshinta ya isheshi kauda fuska yake kauda kai yake,amma zuwa cen dai sai gani nayi Hussain ya jawo plate da Fatima ta d’aura masa tasa akai harda su kabeji da albasa a sama sai tashin k’amshi take plate biyu ne d’ayan kuwa kayan marmari ne bayan an wanke aka yanka masa.

Yana wani tsuke baki da hararar k’ofa yace”ai idan ma naci kud’ina ne,gara ma naci na rage asara” haka yaci kazar sosai da kayan marmarin,Hassu ce tazo kawo masa abinci taga ya baje yana yagar cinya ji tayi kamar ta saka dariya ta dai daure tayi masa sallama,da sauri ya ajiye k’ashin dake hannunsa yana muzurai ta daure dariyarta tace”Yaya Wusaini ga abincinka”banci”yace da ita fuska d’aure baki duk maik’o,tace”ayya kace kazar ta k’osar da kai?yace”ban sani ba ina ruwanki kazar me ance miki ni irinki ne?,girgiza kai tayi da cewa”a’a tare da mik’ewa tana murmushi ta fita.

Washe gari Hajiya tace Hussain ya tafi da Hassu makarantarsu Fatima za’a mata jarabawa tunda tayi primary a k’auyensu sai a d’auketa JSS1 yace”Hajiya wannan k’atuwar yarinyar Jss1 ai ta wuce nan sannan kuma kin san dai babu abinda ta sani bazasu d’auketa ba” tace”Hussain mun riga munyi waya da shugabar makarantar nace yau zakazo da ita,haba ba don ransa yaso ba,yace suzo yana jiransu a mota,Zainab da Fatima ne a gidan baya Hassu a gaba,domin Zainab zata shiga Hassu tace ina bata isa ba ai idan zasu fita gaba take zama don haka yau don hardasu hakan bazaisa ta shiga baya ba,haka Zainab ta hakura ta shiga baya.

Zainab ya fara saukewa Poly inda take karatunta sannan ya wuce da su Fatima Capital School inda cen Fatimar ke karatu tana SS2,Har cikon harabar makarantar ya shiga da motarsa,bayan yayi parking Fatima ta wuce class d’inta su kuma suka nufi office d’in shugaban makarantar.

Don jin jarabawar Hassu mu had’e a page na gaba.🤣🤣🤣🤣

MORE COMMENT MORE TYPING

‘YAR SUNUSI JIKAR RABI’U WATO FATIMA

FATIMA SUNUSI RABI’U.HUSSAIN
🌹 MIJIN ALJANAH 🌹
80K

SHORT AND TRUE LIFE STORY

    *MALLAKAR👇*

FATIMA SUNUSI RABI’U
Ummu Affan

AREWA WRITER’S ASSOCIATION
💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

Page 17-18

Bayan sun shiga Office da sallama,gaisawa Shugabar sukayi da Hussain sannan ta basu izinin zama,yace”ga wacce Hajita tace na kawo miki” kallon Hassu tayi tace” ‘yan mata zauna mana” Hassu wacce take ta kallon Matar ta sami guri ta zauna.

Takarda ta mik’awa Hassu bayan tace”me sunanki ne?” Hussain Hassu ta kalla domin da turanci ta tambayeta,d’aure fuska yayi yace”ba tambayarki akayi ba?” harararsa tayi tare da ta6e baki tace”ai na sani Malam ko kaji nace maka wani abu ne,ko k’auyenmu za’aje ayi tambaya kowa yasan nafi kowa k’ok’ari a cen.”

Ga mamakinsa saiji yayi Hassu ta bata amsa kamar haka” My name is Hafsat Ibrahim” gyad’a kai shugaba tayi tana murmushi domin k’uruciyar Hassu ta burgeta.

Tambayoyi ta fara mata Hussain yasha mamakin jin yarda ta ke bada amsa duk da wani gurin dai sai a hankali amma sosai tayi k’ok’ari.

Takardar hannunta ta kalla wacce akace ta cike” shuru tayi tana bin takardar da kallo,kafin ta fara rubutu,kusan awa guda sannan ta bada,Hassu sai had’a zufa take,dubawa Shugabar tayi duk da wasu guraran ta fad’i wani gurin kuma taci kallon Hussain tayi tace”zamu d’auki HAFSAT kamar yarda Mahaifiyarka tace domin gaskiya yarda na kalli yarinyar da xata sami ilmi k’wak’walwarta zata bud’e sosai domin da alamar hakan.”

Yace”to muna godiya” Form ta basa tace”muna so ku cike wannan azo mana dashi gobe sannan ita ma tazo cikin shirin makaranta zamu bata class,yace”da kyau muna godiya sosai” sannan suka mata sallama suka wuce.

A mota kowa yayi shuru Hussain Hassu ta basa mamaki baiyi tunanin haka daga gareta ba,koda ya sanar da Hajiya tayi farin ciki matuk’a nan take tace zata je kasuwa sayo mata uniform ta bada d’inki da kuma littattafai.

Hajiya Balaka Sunan mahaifiyarsu Hussain macece mai matuk’ar ilmi da son jama’a tana da kyirki sosai,yaranta uku Hassan da Hussain wad’anda ‘yan biyu ne sannan Fatima Allah ya amshi rayuwar mijinta mutum mai dattako da fara’a yana da son mutane sosai mutum ne d’an kasuwa,bayan rasuwarsa Hassan da Hussain sukaci gaba da kasuwancin bayan dawowarsu k’asar India inda suka kammala karatunsu,ko da yake shi Hassan yana Abuja inda yake aikinsa Hussain kuma yana nan Kaduna yana kula da shagunansu.

Da mahaifinsu Hussain da mahaifin Zainab wa da k’ani ne uwa d’aya uba d’aya,ita kuma Hassu mahaifinta Baba K’arami k’ani ne a gurin Hajiya shima uwa d’aya uba d’aya suke ,wannan kenan.

Hassu ta fara makaranta boko da Islamiyya sosai ta fara natsuwa saboda ta had’u da wata k’awa Rahma wacce ‘yar gidan masu dashi ce akwai wayewa a tattare da ita duk da mata cika surutu ba amma tana koyar da Hassu abubuwa da yawa don tun farko ita ta fara shigewa Hassu tana sonta da k’awance,ita Hassu kowa nata ne don d’an banzan surutu ne da ita,duka class an santa,sune group na marasa jin magana a class d’insu ‘yan ajima basu ragawa ba bare malaman da suka raina kansu.

Rahma ce ta fara jan Hassu jiki inda take nuna mata abubuwa na wayewa,da farko ta fara jin Haushin Rahma amma daga baya sai ta aminta domin acewarta so take tafi Zainab wayewa da iya kwalliya domin gasa take da ita,ko gurin Hussain taga taje yanzu itama zata je ta faea surutunta na banza,ta dena aljanun k’arya amma tanama Hussain duk lokacin ta taso tsorata shi domin ta lura yafi kowa tsoran aljanu sunansa kuwa da ta sa masa MIJIN ALJANAH ya tsani sunan amma babu yarda zaiyi da ita.

Hajiya ce zaune da mahaifin Zainab yana mata magana akan su Hussain yace”ba zai yuwuba fa mu zubawa yaran nan ido sunyi karatun har sun k’oshi dashi Hussain na kasuwanci amma har yanzu baya maganar aire don haka ina mai sanar miki ki sanar masa ya fara shirin aurensa da Zainab” tace”ni kaina Alhaji ina so yayi auran nan sannan ina godiya da k’ara jajircewarka akansu xan fad’a masa yace”yauwa” sannan ya mata sallama ya tafi.

Koda ta sanarwa da Hussain maganar yace”bai san zancen ba shifa baice yana son Zainab ba.

Zainab zaune tana danna wayarta number d’in Hussain ta dannawa kira,lokacin yana kasuwa harta katse bai d’auka ba, Hassu dake zaune gefe tace”tusa kai inda ba asonka ai wahala ne,nan ta fara ‘yar waqarta wacce tagaji habaici take” Leliyar liye banyinsa la-la-la-la-lah son maso wani k’oshin wahala alalayyo.

Zainab tasan da ita take,sai bata kulata ba taci gaba da kiran number Hussain har lokacin dai bai d’auka ba.

MUJE ZUWA
FATIMA SUNUSI RABI’U.HUSSAIN
🌹 MIJIN ALJANAH 🌹
80K

SHORT AND TRUE LIFE STORY

    *MALLAKAR👇*

FATIMA SUNUSI RABI’U
Ummu Affan

WANNAN page d’in naki ne Bestiena Rabee’at Muhammad MAMAN KHALEEL kiji dad’inki dashi ina yinki over my bestie🥰🥰

My k’awar amana Rukayya Ibrahim Lawal UMMU INTEESAR kema kiji dadinki ina yinki irin sosai d’in nan,Allah ya bar so da k’auna🥰🥰

My K’anwata Maryam Ibrahim DR MARYAMAH kema kiji dad’inki ina yinki irin sosai d’in nan Allah ya bar zuminci🥰🥰

🔚🔚🔚 LAST PAGE

AREWA WRITER’S ASSOCIATION
💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

LAST PAGE
Page 19-20

Hassu tace”wallahi an daiji kunya babbar budurwa dake kin tsaya kina faman bin namijin da bai sonki,ko da kin auresa bakiji dadin zama da shiba tunda ke ke sonsa shi ba sonki ya ke ba sannan ina mai sanar miki MIJIN ALJANA ne,idan ma kika kuskura kika auresa wallahi kece a ciki domin Aljanar matarsa zata miki hukunci dai-dai da laifinki.”

Sosai Zainab ta zubawa Hassu ido,ita kuwa ganin haka ta sake wani zaro ido da d’aure fuska tamkar dai aljanarce ke magana,ta d’aura da wak’ar ” Sabuwa ta zuma nice ban zama aibuba dani da angona sam bazamu ware ba.

Zainab tayi shuru ta kasa magana,miqewa Hassu tayi tace”idan kunne yaji jiki ya tsira,tayi wucewarta.

Zainab sosai ta tsorata da yanayin Hassu a ranar ta had’a kayanta tace zata koma gida,Hajiya ta mata tambayar duniyar nan tace”ba komai kawai yana son komawa ne” haka Hajiya ta had’a mata sha tara ta arzik’i sannan tasa direba ya mayar da ita gida.

Hussain ko da ya dawo aka sanar masa d’aga kafad’a yayi da cewa tafi nono fari.

BAYAN SHEKARA SHIDDA.

Hafsat Ibrahim ce ta fito daga zana jarabarta ta k’arshe da sukayi na waec da neco.

Sai da na k’ara bud’e idanuwana sosai ganin yarda Hassu ta dawo wata k’atuwar budurwa ta cika sosai ta k’ara haske girma sosai,kallon Rahma tayi wacce suka fito tare tace”my Rahma Allah ya kawomu mun ida jarabawarmu Allah ya bamu nasarar samun sakamako mai k’yau” Rahma ta amsa da”amin my k’awa,yanzu sai yaushe?tace”sai mun had’u islamiyya kenan” Rahma ta shige motar direban gidansu tana d’agawa Hassu hannu,dai-dai tsayuwar wani d’an saurayi gabanta “yan mata barka da hutawa,ya fad’a,ko kallonsa batayi ba ta kauda fuska,yace”haba ‘yan mata magana fa nake” bata waigoba,tsayuwar motar Hussain yasa tayi saurin waigowa gurin saurayin tare da sakin fuska tace”ya kake?,sosai yayi mamakin kulasa da tayi,yayi saurin shanye mamakinsa da cewa”yauwa daman ina so na sanar miki wallahi ina sonki sosai,ina yawan ganinki Allah baisa na ta6a miki magana sai yau” murmushi d’auke a fuskarta tace”karka damu ka samu shiga don naji kaima ka burgeni matuk’a” Hussain wanda ya fito maganar Hassu karaf cikin kunnuwansa,binsu yayi da kallo bayan ya jingina jikin mota ya hard’e hannayensa saman k’irjinsa ya zuba musu ido,Hassu sai k’ara karairaya ta fari da ido da fara’a take gaban saurayin kuma duk saboda taga Hussain ne take wannan abun.

Shi kywa sosai ya k’ula da jin kalamanta,zuba musu ido kawai yayi amma ji yake zucitarsa kamar zata faso k’irjinsa saboda takaici.
Ransa ya 6aci matuqa da jin wannan kalaman nasu,juyawa yayi ya koma cikin mota,Hassu na ganin haka tama saurayin sallama yana tambayarta number wayarta da kwatance gidansu bata kulasa ba ta fad’a mota ganin har Hussain har ya tada,ai kuwa ko gama rufewa batayi ba,ya wani funciki motar da gudun tsiya abun har yabata tsoro matuqa,kallonsa tayi ganin yarda idanuwansa suka chenza kala tayi wani murmushi aranta tace”ana so ana kaiwa kasuwa,mutum sai miskilanci da girman kan tsiya to wazaka mawa?zanyi maganinka cikin ruwan sanyi.

Har suka isa gida ba wanda yayi magana cikinsu,yana parking ya fita a fusace zuwa ciki,girgiza kai Hafsat tayi da d’an murmushi a fuskarta tabi bayansa.

Hajiya zaune a parlour ita d’aya,shekaru biyu kenan da yin auren Fatima wacce ke aure acen Katsina itama Zainab tayi aurenta harta haihu domin rana d’aya akayi bikinsu da Fatima,tundaga habaicin nan da Hassu ta mata ta fara cire Hussain a zuciyarta tana kammala digirinta kuwa ta fitar da miji sukayi aure tare da Fatima ko waccensu tana zamanta lafiya da mijinta.

Hajiya tabi Hussain da kallo wanda yayi sama,Hafsat ta shugo da sallama ta mayar da dubanta gareta zaunawa Hafsat tayi kusa da ita “Hajiya sannu da gida” “yauwa ta amsa sannan ta d’aura da cewa”waccen uban ‘yan zuciyar kuma shida wa?naga ya shugo a harzuk’e?nace”ina zan sani Hajiya nima haka na gansa”

Cikin ikon Allah takardunmu suka fito kuma na sami abinda ake so hakan yasa na fara cuku-cukun zana jarabar jamb da lokaci yayi.

Hajiya ta sani gaba akan ya kanata na fito da miji sai naci gaba da karatuna a gidan miji,Hussain yace”hakan shine dai-dai.nace”to badamuwa insha’Allahu” Hajiya tace”hakan shine yafi domin kina ganin dai yarda a k’auye aka sa miki ido wai har yanxu kink’i aure gani ake ma nice na hanaki wai sa’anninki harda basu yara biyu” nace”haka ne”

Tashi nayi na nufi ciki Hussain ya kalli Hajiya yace”Hajiya nifa ina ganin da Hafsat za’ayi domin yarinyar ta shamma ceni matuqa” ya fad’a yana murmushi qasa-qasa,sosai Hajiya taji dadin batun cikin ranta matuqa amma saita ce”idan ma sonta kake ni babu ruwana kaje da kanka ka nemi soyayyarta idan ta amince to komai yazo gidan sauqi idan tace a’a to ni bazan takura mata ba” Shuru yayi baice komai ba domin shi a tunaninsa Hajiyar zata ce ta amibce zata mata magana da kanta.

Haka har sati biyu bayan nan ya kasa yi ma Hafsat magana gashi yana ganin yarda samari ke kawo mata hari,haka yayi k’undun bala wata ranar juma’a ya sanar mata,kallonsa take aranta dad’i tace”sosai amma a fili tace”zanyi tunani,ka bani lokaci” tun daga ranar har kusan sati Hafsat bata ce masa komai ba hankalinsa ya tashi matuqa nan fa yaxo ya sauke girman kan nasa ya dawo ya saki jiki da ita yana mata kalaman soyayya kai kace bashi bane,ita kuwa ganin haka take ta garasa.

Wata ranar Asabar ta dawo islamiyya bayan tayi wanka tayi sallah tana kan sallaya ya shugo d’akinta abinda bai ta6a ba,murmushi tayi ta dubesa bayan ta shafa addu’a tace”Yaya Hussain da kanka,yace”eh ai zuwa da kai yafi saqo Hafsat ganin na baki duka zuciyata shine kike ta garani kamar wata kwallo ko?,tayi murmushi tace”Yaya Hussain ina tunanin ko zaka iya da halina ne saboda nasan halinka,abu na farko ni dai kasan duk abinda nake so idan baifi qarfinka ba zaka sayamin kai kuma nasanka da maqo sannan kasan dai ina da aljanu sukan tashi lokaci zuwa lokaci to ya kenan kanajin zaka iya dani kuwa?”.

Yace”ni dai nasan ina sonki koma menene bai shafeni ba,maganar maqo dakike magana yanxu na dena” tace”to shi kenan ka bani kwana biyu zan sake tunani”

BAYAN WATA BIYU
Zuwa wannan lokacin soyayya mai k’arfi ta qullu tsakanin HUSSAIN 80K da Hafsat wacce yanzu har an fara maganar aurensu Hajiya da Baba K’arami sunyi farin ciki wanda har yanzu halinsa na nan amma yayi mamakin yarda yanzu Hussain ke masa kyautuka,haka ya taka har Kujama yaje ya gaishe su,tabbas yasan yanzu Hussain yanzu ya sauya sosai.

Hussain da Hafsat suna son junansu matuqa yanzu haka an bashi sauran saka rana da biki. Idan taso ta dunga tsokanarsa da MIJIN ALJANAH sai dai yayi murmushi kawai,idan suka tuna baya kuwa sin dunga dariya.

(TO MIJIN ALJANAH HUSSAIN 80K🤪🤪INA MUKU FATAN ALKHAIRI ALLAH YA KAIMU LOKACIN BIKI MUNA NAN ZUWA ‘YAN AREWA WRITERS DA KUMA FANS D’IN WANN NOVEL FATAN ALKHAIRI.)

SANNAN KARKU MANTA WNN LBR NE NA GASKE AHA.

GODIYA GA Allah da ya bani ikon kammala wannan d’an gajeren labarin da nayisa don nishad’i fatan alkairi gareku masoyana ina sonku sosai da sosai.

TAMMAT BI HAMDULLAH
ALHAMDULILLAH

An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya

Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,

Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490

A lura dakyau – kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,

Alura dakyau – manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu

Alura da kyau – Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC

Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku

This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services

Note that – we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us

Note that – pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it

Note that – our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
__
WhatsApp number 08104335144
FATIMA SUNUSI RABI’U

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button