Technology

Hanyoyin Daza Kabi Ka Kira Ko Kayi Tracking Private Number

Hanyoyin daza kabi ka kira ko kayi tirakin lambar private

 A duk lokacin da wayarka tayi ringing, abu na farko da zaka duba shine wadda yake kiranka kafin amsa wayar. Sannan bugu da kari abu na biyu da zaka sake dubawa shine bayanin lambar, shin lambar tana dauke da bayanai; kamar bayyanar lamba, suna da sauransu. 

Amma a duk lokacin da kiran private number ya shigo wayanka, dukkan wasu bayanai na wannan lambar ba’a ganinsu. Zata iya bayyana akan wayarka a matsayin block, private, ko kuma ta bayyana babu wata shaida, Restricted ko kuma Unknown.

A lokuta da yawa mutane basa iya amsa wayar data kasance unknown ko restricted calls, amma idan baka amsa ba tayaya zaka san yadda zaka kira lambar daga baya? Amma abin burgewa anan shine akwai hanyoyi da dama ta yadda zaka gane wadda ke kiranka kuma ka dawo da kiran daga lambar private!

Yaya zaka/ki gane wadda ya kiraka ko kuma kiran lambar private daga baya

1. Dawowa da kiran private ta hanyar amfani da *69

Da yawa daga cikin mutane suna da damar rufe bayanan lambobinsu saboda sirri, amma kaima kana da damar da zaka san wadda ke kiranka da wannan lambar. Mataki na farko wajen sanin kiran unknown shine amfani da lambobin Last Call Return Code.

Zaka iya danna lambar *69 domin kiran lambar karshe data shigo wayarka, amma ga masu amfani da wayar tarho na landlines. A wani bangaren kuma, zaka iya danna lambar #69 ga masu amfani wayoyin hannu domin dawo da kiran karshe daya shigo wayarka na private number. 

Amma wannan ya dangantane da wayarka ko kuma sabis din da kake amfani dashi, saboda suna da qaidi na lokacin da zaka kira lambar private daga baya, wadda yake mintuna talatin suke bayarwa daga kiran daya shigo maka.

Lokacin da kake amfani da wannan tsarin, bazaka samu ainihin lambar layin da mutumin ya kiraka ba amma dai duk da haka zaka iya tuntubarsa. Hakan ma kuma babu tabbacin zai amsa wayar sai dai kayi amfani da voicemail wadda ke dauke da fasahar nuna bayanai.

A wani bangaren:

Shi wannan tsarin ya danganta da irin service din da wayarka take amfani dashi. Misali wani lokacin Kamfanin layi zasu iya kiranka da lamba wadda take a bayyane, amma wani lokacin kuma saisu kiraka da lambar private suki nuna maka lambar da aka kiraka da ita.

Bugu da kari, wannan tsarin yana da dan rikitarwa, yakan iya bada matsala sosai a mafiya yawan lokuta. Wani lokacin irin wannan kiran na lambar private ana dora shine akan tsarin na’ura me kwakwalwa domin tabbatar da cewa layin da kake amfani dashi yana aiki, 

dalilin irin wannan kiran kuwa shine domin suna sone su sayarwa da ’yan damfara bayanan layin naka, a sakamakon haka kiran lambar private daga bisani shike nuna tabbacin lambar layin tana aiki.

2. Nema ta hanyar amfani da lambar look-of

Shi kuma wannan tsarin yana nuna idan kana san ka bar wata alamar dake nuna an kiraka da lambar private, ko kana son sanin bayanai game da lambar da aka kiraka ta private zaka yi amfani da lambar look-of.

Zaka saka lambar ne akan Google search ko kuma ta hanyar Yellow Pages domin tabbatar da bayanan lambar shin lambar ta landline ce ko ta wayar hannu. Za kuma ka iya gano mazaunin wadda ya kira ka da kuma inda akayi rigistar wayar sa duk ta hanyar wannan shafin na yanar gizo.

A wasu lokutan kuma, zaka biya kudi ne domin karbar cikakken bayanan lambar. Kuma zasu iya dawo maka da kudaden ka idan sabis din na look-of ya gaza samo bayanan na unknown caller din.

3. Amfani da application wajen gano kiran lambar private

Yawan kiran mutum da lambar private akai akai bashi da dadi ga mutane sosai. Amma idan kana neman hanyar daza ka bude lambar private bayan wadancan matakan, sai kayi amfani da wannan application din me suna TrapCall domin bude duk wata lamba kodai unknown calls, private number ko restricted calls. Shima wannan tsarin ana biyan kudi kafin su bayyana maka lambar.

Shi wannan app din me suna TrapCall yana bude duk wata lamba data shafi block ko restricted, shi wannan application din zai baka cikakken bayanin lambar dama sunan me lambar da kuma wurin da akayi rigistar layin nasa, bugu da kari zai baka adreshin sa sannan ya baka damar in kanaso ka saka shi a jerin lambobin da zaka dakatar dasu daga shigo maka saboda kaucewa kiran gaba. Zaka iya sauke wannan application din akan android dinka ko kuma masu amfani da iOS.

4. Saita tsarin kiran tracing domin budewa lambar private

Shima wannan tsarin yana taimakawa wajen gano lambar private, shi wannan tsarin yana amfani ne ga wasu takaitattun wayoyin hannu, wadda wadannan wayoyin an saka musu wata na’ura ne daga kamfani wadda ake kira call tracing service domin dakatar da kiranye-kiranye na gaira babu dalili. Idan an kira mutum da private number bayan kammala kiran sai ka danna *57 idan kana amfani da landline ko kuma #57 idan kana amfani da wayar hannu sannan kabi dokokin da kamfanin suka fada maka.

Bayan ka kammala kiran su, zasu turo maka da sakon murya cewar kamfanin yayi sa’ar samun bayanan lambar da suka hada da suna, adreshi da kuma lambar wadda ya kira kan. Wasu kamfanonin wayar hannu suna bada wannan tsarin kyauta ne, amma a wani bangaren kuma wasun suna karbar kudi a wata domin dakatar maka da irin wannan lamarin.

Wannan shine a takaice yadda zaka kira, ko kuma bayyana lambar private, restricted ko unknown calls.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button