Technology

Hanyoyin Da Ake Samun Kudi A Social Media.

Social media wata kafa ce da take dauke da mutane daban-daban daga kowanne bangare na duniya, sai dai yanzu zamani ya sa social media sun koma hanyoyin samun aiki, dogaro da kai da kuma ilimantarwa.
Wasu daga cikin hanyoyin da zaku bi idan har kunason samun kudade ta hanyar amfani da social media handles dinku sune:

  1. Affiliate Marketing; Abinda ake nufi da affiliate marketing shine dillanci a social media ma’ana idan wani company yana siyar da kayayyaki ko services misali kamar online stores haka ko kuma wani company a online da suke siyar da wasu services ko kaya, zaka iya zama affiliate marketer dinsu idan zaku kulla yarjejeniya dasu zaka ringa hadasu ko kawo musu customers su kuma suna biyan ka, haka shi ake kira da affiliate marketing akwai kamfununnuwa da yawa da suke bada damar zama affilate marketer nasu a koda yaushe.

2) Social Media/ Handle Manager; Zaka iya zama social media manager ta hanyar managing page din wani kamfanin ko wani celebrity ko dan siyasa ta hanyar kula da shafinsu kuma kana yi musu running ads ko da idan basu da lokaci, zakuyi yarjejeniya dasu suna biyanka, wannan hanyar ana amfani da ita sosai musamman ga mutanen da basu da lokacin yin social media kamar ‘yan ball, yan siyasa, celebrities, kamfanunnuwa da sauransu.

3) Influencing/Public figure; wannan itama hanya ce mai sauki ta hanyar amfani da yawan mabiyanka ko followers naka a social media handles, a inda ‘yan kasuwa ko wasu suna baka tallar kayansu kai kuma kana musu talla a shafinka na social media irin wannan zakuga yawanci celebrities ko wanda akasan suna da followers sosai ana basu talla suna sakawa a shafukansu ana biyansu wannan itama hanya ce ta dogaro da kai a social media.

4) Blogging/Youtubing: Wanna kusan kowa yasan ta hanya ce dasu kansu google zasu na biyanka kudade masu yawa ta hanyar dora talla a cikin website dinka da kuma youtube channels dinka idan ka bude kana dora videos ko tutorials ko film da sauransu, idan website ne kuma ta hanyar saka labarai da sauransu, google zasu duba su baka adsence suna biyanka kudade in dollars.

Wannan sune wasu daga cikin hanyoyin da ake samun kudi a social media, ba iya su kadai bane akwai hanyoyi da yawa amma iya wadannan na dauka kuma nakeyin wasu daga ciki, kuma zaku iya zabar wanda kukaga zaku iya domin ku gwada, har Allah ya taimake mu gaba ki daya, ina fatan kowa ya fahimta kuma an amfana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button