Gimbiya Balaraba page 3

GIMBIYA BALARABA••••••••••{03}
🔰🔰🔰🔰🔰🔰🔰🔰🔰🔰🔰
Can suka kara jin busa gami da sarewa wannan bafaden dake tsaye bakin katowar kofar da Mai martaba za fito yayi saurin zubewa a gurin kanshi a qasa gami da dunqule hannunshi Alamar jinjina, cikin banba danci yace Allah yaja da ran Yarima Almansur sarki mai farin baya baka fito ba sai da ka shirya mai takalmin karfe wannan haka yake sarautar ma suna taci in kana guri ,Dan gidan Fulani Dan gidan zainaba Dan gidan Fadim……

Tsitt! Bafaden yayi sakamakon da katar dashi da Wanda a keyiwa banbadanci yayi,

Nayi ta kokarin in ga fuskar sa Amma ina nakasa gani sakamakon tarin jama’ar da ta take masa baya da yawa daga cikinsu Abokannanshi ne sai “yan uwanshi da kyar da jibin goshi na hango bayanshi sakamakon sunkuyawa da bafaden dake take masa baya yayi domin tattare masa rigar da yake sanye da ita domin samun damar zama cikin kujerar Alfarmar da a katanadar dominshi.

Wannan bafade da yake ta zuba kirari yakara dawo wa kusa dashi fadi yake tuba nake yi Jimina A gafarci na Tuba!!

Wani Abokinshi mai suna Shahid ya kalle shi yace kaje ya yafe maka Amma ka kiyaye gaba kasan sarai ba ya son wannan Abinda kake yi masa saunawa naji yana hanaka”

Sunkuyawa yayi yace tuba nake ranka yadade bazan karaba ,In sha Allahu,

Daga Kai shahid yayi yayi masa Alama da ya tafi,

Tunda ga can nesa balaraba take ta faman daga kai domin hango Dan mulki sunan da tasa masa kenan ,Amma ta Gaza ganinshi, takasa daurewa sai tamike tsaye cikin wayancewa tana gyara daurin zaninta gami da gyara zaman hijab dinta,

Da kyar ta hango shi ba sosai ba sabida yadda fadawa suka kewayeshi kuma da a kwai taxara mai yawa a tsakaninsu da inda take zaune,

Idan ba’idonta ne yake mata gizo ba sai taga Yariman da a ke tawani zuzutashi yaro kankani, tabbas ko ita ta girmi wancan yaron tafada cikin zuciyarta gami da komawa ta zauna tana tabe baki,

~BINTA UMAR ABBALE~

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *