Hausa Novels

Gimbiya Balaraba page 2

GIMBIYA BALARABA•••••••••{02}
🔰🔰🔰🔰🔰🔰🔰🔰🔰🔰🔰
Bashira tace wallahi kuwa dama naji rade radin cewa ae mugun girman kai ne dashi Yariman shiyasa ban so Malam Idiris ya kawo saukar fadar sarkin ba yafi kawai dacewa sarkin yaro makaranta mu karbi Allunan mu sabida kin San sha’ani da masu sarauta a kwai matsala ,

Related Articles

Tsaki Balaraba tayi a karo na biyu cikin gadara tace wallahi Dan kar in tashi in yi tafiya ta Abin ya zama laifi gurin Malamai dama mutum yayi kaurin suna komai sai ace kai ,da tafiya ta zanyi babu wani banzan da zan tsaya batawa kaina lokaci a kanshi sauka ce dai nayi nasan nayi ae ba lailai bane sai na karbi Allon ba,

Ke Balaraba! Bushira tafada cikin mamaki tace kardai maimar taba kike zagi kin San dai nan ba gurin gadara ba ne gami da girman kai Dan haka ki iya bakinki,wallahi ,kasa kasa Balaraba ta karashe zancan tana waiwayawa bayanta domin dogarawa ne ke waye dasu ko wanne riqe da gora Kansu yasha tafka tafkan rawani idonsu ranbade da kwalli sai zarewa sukeyi

Babu wani tsoro ko kadan a Furucin ta tace ke rabu dani Dan Allah shikkenan sai in zauna a kan wani ina batawa kaina lokaci sanin kanki ne fa su Sadiya suna can na jira na kin san basu da kowa sai ni nasan suna can a takure ,shikkenan sai in zauna wani ya bata min lokaci,nifa ba da sarki nake ba,ke kin San da Wanda nake yi tafada tana wani ciccije baki!

Bushira tace wallahi balaraba ki rage wannan zafin kan naki sai ki riqa Abu cikin gadara tamkar wata “yar wani ki yi tunanin nan fa gidan masu mulki kika shigo wallahi ni dai babu ruwana to!!

Mtsss ke nifa wallahi babu Wanda zan ji tsoro uwata da ubana kawai zan ji tsoro sai Allah da Annabi Amma babu wani mahalokin da ya isa yana kashi ina kashi in ji tsoro ni babu ruwana da wani sarautarsa,

Shiru Bushira tayi ganin Balaraba tana faman daga murya dama dama tayi kaurin suna a makarantar ,bata karacewa mata komai ba,

Can suka kara jin busa gami da sarewa wannan bafaden dake tsaye bakin katowar kofar da Mai martaba za fito yayi sa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button