Hausa Novels

GIMBIYA Balaraba – page 1

GIMBIYA BALARABA••••••••••{01}
🔰🔰🔰🔰🔰🔰🔰🔰🔰🔰🔰
a kajin komai a gurin sai busa gami da sarewa da sawun doki kowa a gurinshi kokari yake yaga wucewar sarki Almustapah ma Adalin sarki kenan Wanda Al’umarshi take jin dadin mulkinshi gami da Adalcin A tsakanin talaka da mai kudi babu Wanda ya ware a ciki kowa nashi ne ,Gurin ya karade da hayaniya can jama’ar dake gurin suka fara jiyo wata Murya cikin Lasifiqa Ana cewa jama’a Ku dakata Ku nutsu kafin fitowar mai martaba sarki mai Adalci yanzu Yarima Mai jiran gado zai fito tare da ta wagarshi Allah yaja da ran Yarima Almansor takawar ka Lafiya ,gaba salamin baya Salamun Dan sarki jikan sarki sarauta gadarta kukayi bata haya bace wannan tsantsan tace a jini takeBa fade sai faman zabga kirari yake yi har yanzu bamuga fitowar Yarima Al’mansor ba ni kaina na qago in ga waye wannan Yarima n ,da ake tai wa kirari haka lailai sarauta ikon Allah masu Abu da Abunsu!Bakin shi yaqi yin shiru har ila yau zabga kirari yake gami da banbadanci ga Yarima Amma shiru kakeji tamkar an shuka dosa Wanda a keyi dominshi babu Alamarsa,Wani mugun tsaki Balaraba taja A fili tace Aikin banza Kawai Mtsss gaskiya wannan ma Dan rainin hankali ne kawai ya fito shine sai ya tsaya bata mana lokaci dubi fa time tafada tana kallon Agogon dake daure a hannuta gami da kallon kawarta Bushira wacce suke zaune a tare A wata katuwar rumfa cikin “yan Uwansu dalibai da’Alama Saukar Alk’urani Sukayi ganin tarin Alluna gami da kyauttuka a zube a gurin,gefen maza daban na mata daban hakanan gurin zaman malamai daban ,gurin zaman iyayen yara daban gurin zaman manyan baki daban ,sai wani guri keban tacce Wanda a ka tanadar wa da mai martaba domin zama shida Mai jiran gado Wato yarima gurin yasha shinfidu iri iri na Alfarma ga wasu bayi biyu a tsaye a bayan kujerun hannuwansu riqe da wasu tafka tafkan mafitai suna fiffita tun kafin Masu sarautar su zauna a gurin,Bashira tace wallahi kuwa dama naji rade radin cewa ae mugun girman kai ne dashi Yariman

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button