Hausa Novels

GIDAN Mu 1&2

GIDAN GANDU
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Related Articles

Wattpad username:SAKHNA03

       ** ❤ Gargadi❤**

Wannan littafin kirkirarrene,saidai zai iya cin karo da dabi’un wani ko halayyar wata,sannan ba a yarda wani ko wata suyi koyi da mugayen halayyar Wannan littafinba,anyine dan isar da wani sako.
Sannan game da marubuta idan kinga wani abu yayi kama da littafinki toh yanayin tunanine yakawo hakan,dan banida niyyar bata wa kowa rai,burina isar da sakon da littafin ya kunsa,wanda in akayi hakurin bani hadin kai har zuwa karshe toh kowa zai ga mai littafin ya kunsa.

           ❤Jinjina❤

Babbar jinjina ga proficient writer association,Ina godiya matuka.

❤01❤

………………Gidan gandu,gidane daya kunshi mutane fiye da 300 a muhalli daya banda wanda sukayi aure wasu suka tafi cirani wasu kuma tantirancin su ya hanasu zaman gida,tunda ga baki kofar gidan mutum yasan wane irin gidane saboda yawan kofofinsa tun daga kan kakanni,iyaye,jikoki,tattaba kunne da saurensu.
*

______lokacin safiyace dan baifi 9:30am na safenba,gidaje a kowa yana kokarin aikin gabansa inda masu himma kam yayansu sun dade da tafiya makaranta,maza kuwa wasu sun tafi gona.
Shiru cikin gidan kakeji babu wata hayaniya kowa yatafi harkarsa,bayan yasamu abinda ya sawwaka ya zuba a cikinsa,sai iya kofar kawu shehu wanda dama su kullum cikin fada suke,da inna larai da kuma inna karima.Dakin yan matan gidan ma bakowa sai wata matashiyar budurwa a kwance tana zuba bacci kaman ba gobe,ta dade batayi motsiba can kuma sai ta yi wata mika irin ta wanda ya more da baccinnan,gyara zamanta tayi a bakin katifar tata tana bubbuga kai da kuma jan majina da irin kaman mutum ya shaki kura,
“Kai shiyasa dadina da BURGU yasan DULAH (wiwi),mai kyau yanzu mutum zaiji shi a caji,duk wata gajiyarka saikaji ta tafi,inda ana samun mai kyau haka yaushe mutum zaice yayi asarar kudinsa kuma ai…………”
Katsewa tayi da zancen nata jin wayar ta irin yan nokia dinnan ta dau kara ta cika dakin,juyawa tayi tana yatsina fuska ta dauki wayar kafin ta saka a kunnenta,
“Menene??”
Shine abinda tace tana daga kiran,sai kuma tayi shiru danjin maganar da ake a daya bangaren,
“Hmm indai kaji kira a wajen alhaji sama’ila toh siyasah ce ta kariso yana so ayi masa aiki,toh wallahi kaji na fadamaka inhar ya hau kujerar nan yamanta da mu,to sai yayi dayasanin sanina a cikin rayuwarsa,dan saina masa abinda har ya mutu bazai mantaba,kuma kasan zan aikata,dan haka yanzu ka fada masa,inya amince kazo kadaukeni mutafi a san abin yi,yanzu dama nake maganar ka dan naji dadin dular jiyannan akwai caji baaaba,…………shikenan kazo ka daukeni sannan kace arnan yara su shirya ganinan zuwa yanzunnan”
Fitowa tayi a dakin tana wani garwaya hanya irin na iya shegennan can kuma sai ta dauki bokati dama da ruwa aciki da alama wani ne ya ajiye,
“Keee SAMEEMAH ruwa na ne na ajiye”
Juyawa tayi tana kallon mai maganar cikin daga ido,
“Toh so what dan nakine,ajiyewa zanyi dan naki ne,inkuma kinga a tawani sako na kwakwaiwarki ya nuna miki ina tsoronki ta kizo ki karba,kin manta ina da labarin guntun sabuluna da kikayi wanka dashi?koh an gaya miki bansaniba,dan dai munayin hankali ne kullum shiyasa muke barin koh ta kwana”
“Iyyyeee Ku zo ku jimin wata magana wai sameemah ceh tayi hankali,da kuwa anyi ruwan farin ciki a garinnan,kuma narantse kika shiga wanka da ruwannan saina miki abinda yafi na ruwana,dannima inada wajen zuwa da safennan”
“Keh sameerah ya isheki haka,maida min maganar inbaso kike daga ke har mazinacin bazawarinnaki dazaki wajen sa na juya rayuwarku ba,kuma inkin fasa daukar matakin banza shashasha”
“Kai lallai ma yarinyar nan,a haifeki a gaban mutane amma ki dunga yiwa mutum maganar da uwarsa bata isa yimasa ,shegiya yar daba kawai”
“Hhhhhhh gwanda dakika fadi abinda yake bakinki amma bari na fito nasameki a cikin gidannan yau wallahi mai rabani da ke koh…………..hmmm”
Sauri sameerah tayi tabar wajen dan yanda taga ran sameemah yabaci ba abinda bazata iya mata ba ,na rashin mutunci,takaicinta daya ma,yarinya karama ta takura musu ta addabesu,gashi sunyi waya da bazawarinta Saminu,yace zaizo yadauketa su tafi bikin abokinsa a Kaduna tana ta murna,yanzu tasan dole saidai ta tafi ba wanka, saboda gudun haduwarsu da sameemah a yau,dan tasan in ba hucewa tayiba,tsab zata aikata abinda tace.
Bata dade ba a bandakin ta fito,har yanzu fuskar ta ba fara’a saboda sabanin dasukayi da yayarta sameerah dazu wanda suke uba daya su da itah,dakinnasu ta shige ta nufi hanyar wajen kayanta,dan daki kawai suka hada da yan matan gidan amma kowa shirginsa daban ,gwanda su wani lokacin in wata tayi samuwa ana zama a ci ana dariya da yada zance,amma sameemah in ta shigo da abu a gabansu zata cinye in ya isheta ta bawa karanta BINGO.
Mayuka ta fitar lotion masu gyara fata ta mulke jikinta kafin ta dauko wasu kaya na saki irin na farauta amma anyi musu dikin irin na mata riga da wando.
Bayan ta gama saka kayanne kuma aka shafa hoda kafin aka dauko bakin jambaki wuluk ta shafe karamin bakinta dashi ,ga kuma kwalli da tayi masa saku kasa da sama,dan saida girar ta kusa hadewa da saman ido,juyi tayi a gaban madubinta kafin ta dauki gyalen ta nadeshi a kafada ta fito daga dakin.
A bakin hanyar fitarta daga dakin suka ci karo da wani dan anguwarsu yana rataye da yar gidan inna larai a kafadarsa,yarinyar sai kuka take bazata wuce shekara bakwai ba,Sameemah ce ta fara ganinsa tareda Tambayar “lafiya”
“Ahah seemah jar wuyah(haka kowa ke kiran sameemah a waje)wallahi a hanyar shagon ilu naganta a kwance jini yana binta hine dana tambayeta tacemin wai Labiru ne abokin yayanta Manu yayi mata haka”
“Ayyah Toh sannunka da kokari zaka iyah tafiya”
Bayan ya tafine sameemah ta dauki yarinyar tayi kofar su inna larai din da ita,
“Inna larai! inna larai!! Inna larai!!!”
Suna cikin habaici kowa yana kofar dakinsa ita da inna karima,sai ta zuyo tareda cewa,
“Ke miyene kike ta jundumamin kira kaman zaki cinyeni”
“Iyyeh hakanee abin(sameemah ta fada tana ajiye hanifan a gababan inna larai) toh gashinan,yar tatsitsiyar yar kice wani gardin ya fardeta ,kona ce yabudeta a ledarta,saiki zo ki dundumata da ruwan zafi ba masifa zaki tsaya yiba,itama alamu kwadayinnata ya kaita ta shiga sahu tun lokacin ta ba yiba”
“Lallai sameemah abinda zakice ma kenan,wanne dan tsinanniyar ne wannan?”
“Waye kuwa banda Labiru abokin danki Manu,bake kike manna masa itaba dan kinga yana siya mata shayi da safe,bakuda aiki sai kwadayin tsiya,saiki dundumata ta samu ta ware,ko tayi harkar da kwarin jiki,ni na tafi inna dawo da kaza na dan bata,kota maida jinin da yazuba,in kuma nima bandawo ba tacan tacan,ga wannan kisaya mata ibrofen saboda zafin jiki(tafada tana mikawa inna larai din naira hamsin).
Wani wawan tsalle inna larai din tayi tareda buge kudin dayake hannun sameemah,kafin tabita da wani ashar mai dumi.
Inna karima kuwa tana gefe tana zuba uwar dariya kamar makogaranta zai fito dan mugunta,komawa kanta zagin yayi,cikin haushi inna larai tayi kanta suka rukume da fada,tana zaginta tana kururuwa kan gari ya gari.
Ganin mutanen gidan sun fara sanin abinda yafarune,yasa sameemah zagewa ta fice daga gidan.
Tana fita ta samu Burgu a kan mashin yana jiranta,burgu yana ganin ta fito ya tada mashindin yafara diri,dalewa tayi suka fara tafiya,yana bata labarin yanda sukayi da alhaji Sama’ila,duk zancen dayakeyi bata kulashi ba saima umarni da ta bashi cikin karamar magana,
“Ka saka su dodon dawa su kama Labiru dan malam sule,su kaimin shi gidan karangiya,su dan tabashi kafin naje wanjansa gobe”
“Shugaba reza mai yayi haka?”
“Bai shafeka ba kayi yanda nace kawai”
“Wai yau labiru yaga ta kansa tabbbb”
Da haka har suka isa gidan kungiyar tasu burgu bai sake cewa komai ba saboda yaga yanda shugabar ta murtuke fauska.
Gidane da akayi wajen da langa langa saikuma,dakuna na bulo guda biyu da kuma dakuma dan tsakar gida.
Babu KO sallama haka suka saka kai ,inda kowa yatashi yana yi mata barka da isowa,dakin dayake farko ta shiga,tareda hakimcewa akan wata kujera wadda aka saka tebur a gabanta,sukuma suka zauna a sauran kujerun dakin,
“Uhm uhm,kaman yanda kuka sani wannan kungiya ta kafu bada iya taimakona ba harda naku,sannan muna abune bisa tsari,in munyi abu saida dalili toh dan haka,ba mason katsalandan da yan sanda,alhaji Sama’ila yaba mu aikin ragamar siyasarsa,dan haka zamuje yau ,amma iya mutum shidane zasu biyomu sauran nasaka burgu yabaku aiki,shi zai fadamuku mai na sakashi yasa ku aiwatar kuma kunsan banason ganganci,dan haka k kula,kai kuma ASUSU,(tafada tana nuna wani dan saurayi a gefen burgun a zaune),nawa muke dashi acikin bankinmu na kungiya?”
“Eh shugaba iyah dubu talatinne”
“Toh kabawa dodon dawa dubu goma yah,yasayo mana suyar kaji da lemo,sannan kuma ka tambayi burgu inda ake saida dulah mai caji ka sayo mana,dan wacce ka kawo wancan sati ta asarar kudi ce kawai,inna dawo daga wajen alhaji Sama’ila akwai shagali”
Ihu wajen kowa yadauka mai feduwa sunayi,
“Sai ogah kina abinda kika so,sai shugabar gidan gandu,da girman kujerarki,sai reza ki yanki wanda yasayeki idan ya kuskuren rikeki ba dadaiba,kuma dole ya gyara yayi aiki da ke,ehhhhhhooooool”
“Toh ya isa haka maza ayi haramar fita aiki kuma”
Kowa tashi yayi inda masu kamo labiru suka tafi bayan burgu yayi musu bayani,sannan masubin shugaba seemah jar wuyah kuma suka bita a baya da mashinan su,sai gidan alhaji Sama’ila.

Toh farkon farawa kenan a cikin littafin gidan gandu,daga taskar sady-sakhna,kuci gaba da bibiyar littafin da sannu zamu nishadantar daku yanda yakamata inshaallah,nagoda ga duk daukacin masoyan wannan littafin.

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤02❤

Labirune a zaune shida abokansa suna shan rake a baki rafi,kai kace ba abinda ya aikata hankalinsa kwance kaman tsumma a cikin randa,yana cikin zance sai waigawa kawai yayi yaga bakowa a gefensa kamar dama ba zaune suke shida mutane ba,tun kafin yayi magana yaji an toshe masa baki,yayinda wani duka ya jiyarci keyar sa ta baya,daga nan bai sake jin komai ba sai duhi daya lullube ganin sa.
Sun gumarsa sukayi suka sabashi a bayan mashin din daya daga cikinsu sai gidan karangiya.
Zefashi sukayi a kasa kaman kayan wanki yayinda daya daga cikinsu yace,
“Kai baaaba yanzun zamu dabashi kaman yanda shugaba reza tace kokuma kawai mubarshi ta ji dashi”
“Haha nayi dakon kawoshi a banza wallahi saina dan tabashi,dama inajin haushinsa sani ne bakayi ba,shine fah wanda yayi shunemu a wajen yan sanda lokacin da muka sato akuyar hajiya delu zamu babbake mu maida maiko,kasani ai dakyar muka sha,badan shugaba jar wuyah tananan ba da tuni sun tara mana jini da majina”
“Gaskiyarka arnan mazaje,dole mudan mauleshi koh kadanne,dan babu abinda na tsana kaman masu bakaken kayannan(yan sanda) yan banza saikaace cinnaku”
Dariyar yan daba suka sa baki dayansu kafin daya daga cikinsu yasamu daidai duwawun labiru ya narka masa sandar hannunsa,wani wawiyar zabura yayi ya mike yana rarraba ido akan kowane dayansu.
Daya daga cikonsu ne wanda shine ya daki labirun da alama shine shugaba idon sa ya dau kwalli kaman tsohon dan farauta,
“Heeege gama karemu da kallo yau uwarka zaka ci a wajennan dan ma bamusan mai kayi ba,amma tunda ka tabo shugaba yau kataryarka sai tayi jawur a wajen mu”
Yana gama magana ya hau tabkar labiru kaman an aikoshi wajensa.
Saida sukayi masa lilis kafin suka barshi yashe a wajen tareda rufo kofar suka bar wajen.
Basu wane dade su sameemah suna tafiya a hanyaba suka iso gidan alhaji Sama’ila,gidane sannane kowa yasanshi saboda siyasarshi,a bakin kofar get din gidan suka yi parking din mashinansu kafin suka tunkari mai gadin wanda yake zaune akan benci yana jin radio,burgune yafara masa magana cikin gadara,
“Kai dattijo maza shiga gidan ka sanar da mai gidan isowar mu”
Bai ce komai ba sai tashi da yayi ya shiga gidan dan aiwatar da abinda suka sakashi saboda tsira da mutuncinsa,bai dade da shiga kuwa ba saigashi yafito,
“Eh na Shaida masa isowarku yace kushiga daga ciki”
“Shikenan dattijo godiya muke”
A parlorn baki suka sameshi ya baje akan kujera tareda ware cinyoyi yana shan iska,saboda kibar da yayi irin ta yan siyasa,washe bakin nan yayi yana musu barka da zuwa.
Sameemah ceh ta kalleshi tana yatsine fuska bayan ta zauna akan kujerar daya daga cin parlorn,dora kafa daya kan daya tayi kafin tace,
“Kafin a fara komai alhaji hada wannan cinyoyinnaka waje daya tukunna,dan banji dadin zama ba da ganin yanda ka wani ware kafafu kaman mai jiran kaciya ta biyu”
Cikin kunya da kuma dariya irin ta yan duniya ya hade kafafunsa waje daya amma da gani baiji dadin yanda sameemah ta disga shiba a gaban yaranta,saidai babu yanda zaiyi tunda shiyake nema a wajensu.
Maganar abinda yatarasu suka farayi gameda campaign daya ke so suyi masa na mutane,Musamman matasa na birni da kauye,sameemah ceh tayi saurin katseshi tareda cewa,
“Dakata harda kauye kakeson muyi maka ko iya cikin gari,sannan kanason mukula da ta bangaren yan sanda ko kuma ba ruwanmu dasu?”
“Eh kowanne nakeso ayi nidai kawai na samu na hau zabennan shikenan burina yacika”
“Toh sharadinka shine;zaka bada rabin kudi yanzu sauran rabi kuma saika hau zabe,amma idan ka hau zabe ka manta da mu,toh kasani sanda ka sauka a mulki saidai kanemi wani garin ba dai nan ba,dan bana barin bashi ko ranka zaka sayar saika biyani kudina bai dameni ba,sannan idan wani yarona ya shiga hannun hukuma kai ke da alhakin fito dashi ,idan ka yarda da sharruda na,kayiwa burgu magana zai kawo maka takardar saka hannu”
Gilas ta fitar daga jin jakarta ta toshe fuskarta kana ta mike tsaye har ta juya zata fita can kuma ta dawo,
“Am karka manta,inada lawyer wanda ba’a siyansa da kudi,karkayi kokarin wani kuskure,dan ni ba irin sauran yan dabar bane,ku tashi mutafi yara”
Kowa mikewa yayi kaman dama umarninta suke jira,sun zo dadai kofar fitane suka hadu da wani gogygyen dan siyasa da alama yafi alhaji Sama’ila ma matsayi a siyasar.
Tsayawa yayi kaman wani gunki ya tsare sameemah da ido wanda ta bashi hanya tun dazu ya wuce,ganin shiru kaman bashida alamar wucewa ne yasata dagowa dan ganin mai yake kallo haka,wani dan isakan kashe mata ido yayi tareda lashe baki irin na yan duniyar nan,dayake itama shugaba ce a wajen cikin sakanni ta gano mai yake nufi,take kuwa ta mayar masa da martani ta hanyar daga masa girarta ta hagun,
“Kibani numberki idan bazaki damu ba mana”
Ba wani bata lokaci tafara karanto masa yaronsa yana copy akan wayar datake hannunsa,saida suka gama yace,
“Banjin sunan zazzakar kazar ba?”
“In min hadu zakaji abinda yafi suna ma”
“Shikenan idan kinshirya zamuyi waya “
Bata sake cemasa komai ba tafice daga cikin parlorn.
Bayan sun gaisane shida alhaji Sama’ila,sai yayi shiru kaman mai tunani yana ta murmushi shikadai,alhaji Sama’ila ne yakatseshi ta hanyar cewa,
“Amma alhaji BALA naji dadai kuwa harkar da kuka kulla kaida seemah jar wuyah”
“Au Ashe kajimu,gaskiya na samu dami a akala dan dagani zatayi dadin harka sosai”
“Hmm alhaji bala kenan,anya kuwa kadauki dami mai kyau kuwa,karfah ka dauki dan maciji ina……..,..”
“Kai kai alhaji Sama’ila menene kuma na wannan maganar,babu abinda yafaru kabar ma wannan zancen muyi abinda yakawo mu kawai”.
A wajen fita waje kuwa bayan sun zo hawa mashin,burgune yakalli sameemah da Mamaki abinda yafaru,
“Amma shugaba maganar da kukayi keda wannan alhajin anya ba matsala kuwa”
“Me nake Tunani,ka fara mantani ne,gaskiya yakamata ma na fara sabon aiki dan ina ganin nayi laushi dayawa tunda har kuke min wannan kallon kaman kuna gaban kannenku mata na gida”
Basu sake cewa komai ba sai burka mashinansu dasukayi kowa ya dale,dan da alamar sun jiyo gargadi da kuma fushi a cikin muryar tata.
Acikin gidan gandu kuwa tun safe ake abu daya har rana ta fara zafi lokacin daura abinci amma babu alamar zasu daina hayaniyar dasukeyi.
Inna larai kuwa tun ana jiyo muryarta da karfi harta fara dushewa saboda masifah,kawu shehu ne yayi sallama ya dawo daga gona,tun daga wajen kofar gida yakejin masifar da akeyi wanda inda sabo yariga ya saba,saidai daya shigo gidanne yakula da kofar tasa cike take da mutane kaman ana rabon kudi,karo sukayi da baba umaru (baban su sameemah)wanda shikuma gadin makarantar primary anguwar yake wanda antashi kenan ya dawo gidan,
“Ahah shehu yadai kana kallon gaban ka kuwa?”.a kokuma maganin abinda yafaru?,ai kin fi kowa dabbanci da irin wannan kwakwalwar taki,baku da aiki sai shege kishi da fada,shi kadai kuka iya kawai”
Baba umarune ya rike kawu shehu wanda yake ta zazzagawa larai masifa saboda tsabar ransa yabaci,daki ya wuce yadauko yarinyar wanda jikinta yayi zafi rau saboda Zazzabin daya hau Jikinta.
A hanyar fita suka hadu da mazan gidan guda biyu,da Sule dakuma Bashari wanda dukkansu yayan baba umaru ne,
“Yawwa kai sule bi bayan kawunka shehu ku tafi asibiti ,kai kuma bashari zo mu tafi wajen yan sanda”
Hakan kuwa akayi kawu shehu suka tafi asibiti,wanda ganin zasu tafi yasa inna larai dauko gyalenta tabiyo su har waje,saida baba umaru yasaka baki kafin kawu shehu yabar ta bisu asibitin,saida tayi ta rusa musu ihu tukunna aka barta ta tari mashin tabi bayansu.
A wajen su baba umaru kuwa,saida suka bi layi tukunna suka samu layin yazo kansu,dan sandanne yakalli su baba umaru amma idon sa yafi tsayawa akan bashari da alama yaganeshi,
“Malam muna tsaye amma bakace mana komai ba”
“Eh ina jinka menene yake tafe daku”
Saida suka tsara masa, abinda yake faruwa tas kafin ya yamutsa guska yace,
“Hakikanin gaskiya babu inda zamuje kamo wani dan ya taba wani mutum a gidan gandu,saboda kuma da wani a cikin gidanne ya aikata mukaje kamoshi da kyar zaku bari dan sandan yafito da ransa in ya fito ma to saikun sanja masa kamanni kuwa.
Toh fah yadai gidan gandu??

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

wannan shafin sadaukarwane kwacokam ga,@sumayya yarima,@Aisha dakuma @hajiya,allah yabar kauna ga duk masoyana,hakika ina godiyah sosai
Bari muga nagaba kuma😀😀😀😀

❤03❤

“Baba kayi hakuri fah dan yayan gidankune suka jawo,lokacin da mukaje kamo manjo dan gidan malam IDI a gidan ya saci mashin din wani saurayi kuma yayi masa duka,naga wannan shegiyar yar takace ta aiko mana arnan yaranta sukayi mana faca faca da ofishinmu,waima dan bata gari ba da kanta tazo ba,dan haka babu inda zamuje,in labiru kuke zance ma,dazu wasu samari suka kawomana kara wai sun nemeshi sun rasa a baking rafi lolacin da suke shan rake dazu,dan haka ku tattara naku ya naku kubar nan wajen tun wuri”
Cikin sanyin jiki na rashin sa’a suka bar wajen,wanda dama shi bashari baiyi magana ba,inda wajen tsara yan matane da bleaching toh ya rufe kofah,amma harkar yan sanda kam,matsoraci ne shi sosai na bugawa a taro.
Fitowa sukayi daga police station suka tari acaba wanda zai kaisu asibitin da aka kwantar da hanifan,nan ma saida akayi ja inja da mai adaidaita sahu kafin ya daukesu,suna cikin tafiyane bashari yagyara zama yafara magana wacce baiyi ba tun sanda aka shiga police station din,
“AI baba umaru in fada maka,mutanennen basuda imani,cewa muka cemusu anyiwa fah yarinya fyade amma ji yanda suke wani nuna halin ko inkula,hmmm abin duka babu sanda”
“Dallah can yimin shiru da fuska kaman ta sabuwar fatalwa,waiku adole yan gayu,duk kun shafa mai kun mele fuska kaman wanda aka bi da dutsin guga,zaka ce wani abin duka babu sanda in anbaka sandan uban me zaka iya idan an baka sandan,akwai abinda ka iya ne banda shegen zuwa wajen yan mata,duk wani dan kudinku anan yake karewa da kuma sayen tsukakkun wanduna”
“Kai baba umaru ku bakwa gane zamani,idan ta ganka baki babu wanka ai babu rabin zance,ai idan ta ga fuskarka fara tas ga kuma wandonka irin sabin gwanjonnan yanzu zakaga ana love wallhi in ba kaiba sai rijiya”
“Kai bashari zaman mu lafiya kayimin shiru anan wajen tammmm”
Shiru kuwa yayi da bakinsa bai sake cewa komaiba har suka iso asibitin da aka basu gadon.
A wajen cashier suka hadu dasu inna larai a tsaye suna jiran layinsu ya iso saboda ganin likata(kasar tamu kenan allah yah ya fiddamu cikin wannan hali).
Kudin wajennasu bai isa ba ,saida baba umaru yaciro guntun sanjinsa kafin aka bawa mai karbar kudin.
Bayan sun samu an basu gadone,baba umaru yah kalli kawu shehu yana mayar masa yanda sukayi da yan sanda a police station dazu,tun bai karisa jin mai ya faruba ya fara masifa saboda tsabar ransa ya baci,
“Hmm dama nasan za’a rina,wai an saci zanin mahaukaciya,duk sun bata yayannan basuda aiki sai jawo magana acikin gari,kowa acikin su bayason laifin dansa toh yanzu wa gari ya waya ,gatanan ina tatura yarinya kwadayi anyi mata aika aika tabar mutane da wahala”
Inna larai ce ta goge idanunta da yacika da hawaye ta dubi kawu shehu cike da masifa tafara magana,
“Kai shehu ya isheka haka,kawai zaka samu mutane da shegiyar masifa,zaka ce wani mun b’ata y’ay’a ,aikai suka iyo kaidin na allah ko kanace bamusan mai kake aikatawa,dama wanda yayi ai sai anyi masa,kuma dama kyan d’a yagaji ubansa,kai suka iyo,dan haka kadaina wani jingina laifin akaina eheee”
Kunyace takama kawu shehu ganin yanda inna larai tafere baki ta masa wankin babban bargo da masifa kaman d’anta gashi dakin Da’aka kwantar dasu da mutane.
Sallama baba umaru yayi musu ganin yanda abin yafara zama na tone tone maimakon zaman jinya,fatan samun lafiya yayi musu yai hanyar gida na fatan allah ya kyauta aransa.
Yana shiga gida inna RAMATU(matar baban SAMEEMAH ,uwar su sameerah )ta tari baba umaru da barka kaman ba itaba,da Mamakin sa yah kalleta saidai ya boye baice komaiba,ruwan sanyi ta kawo masa da shinkafa fara da mai da yaji da akayi da ranar.
Saida yah wanke hannun sa kafin yafara garwaya shinkafar dan dama da yunwa yadawo gidan ,kuma yayi arba da tsautsayin daya faru,dawowa tayi ta samu waje ta zauna tana gyara zaman dan kwalinta,
“Ah dama nace baban su ATIKA,(haka take cemasa),kaman dakai aka tafi da hanifa asibiti koh?”
“Eh dani ne ya akayi?”
“Meyafaru ne acandin?”
“Shiyasa kika tareni da fara’a harda ruwan sanyi da kawo abinci a kwano mai murfi dan kiji labarin abinda yafaru koh?”
“Haba baban atika ya zaka ce haka kuma naga dan ka fadamin ba laifi bane koh”
“A gunki kenan ba,toh bazan fada ba,waiku mai yake damunku ne bakuda aiki sai kowa buri yake yaga wani abu yasamu dan uwansa yadora agaba koh,haka kuke daga ku har y’ay’anku kamar an garwaya an raba”
“Kaga baban atika nifah ba cewa nayi kafara min wani zance na banza da wofi ba,kawai tunda bazaka fada ba shikenan,dadinta ma da su sule kaje,zan tambayesu su fadamin,kuma dama dazu na kara kudi an dad’o maggi na ashirin saika bani kudina na fasa yafewa”
Kade zaninta tayi tana cika kaamar kububuwa ta bar wajen,dan tsabar takaici daya shak’i baba umaru jijjiga kai kawai yayi yana rufe kwanon abincin,dan ji yayi duk abincin ma ya fita a ransa.
(Allah ya shirya matan mu a yanzu,musamman ma kauye koh babban gida wannan matsalar tafi yawa a irin wannan muhallen).
A kofar su larai kuwa kowa yah watse yakama harkar sa sai matan dasuke karkashin inna karima su kadaine a kofar ana maida abinda yafaru ana yada shewa,Hansai ceh matar dan baba umaru na farko manjo wanda yatafi cirani bayan ya saci kudin sarkin noman anguwar tasu ana nemansa,wanda yanzu y’ay’anta biyar kenan,duk suna gidan suma ana fama dasu.
“Hmm ke kiji sai mukaji abu yafaru kuma?”
Itama wata a gefensu ce ta cafe tareda cewa,
“Naga dama ita ke likawa labirun,yanzu gashinan ai yayi mata aika aika,maganinta”
Wata a can gefece tana bawa danta nono ta kalli MAIRO wanda ita ta gama magsna yanzu,
“Ke mairo yanzu kece mai cewa wani wai allah yakara dan anyiwa Y’arsa fyade?,ai gwara ita dole akayimata naga ke yar ki HAFSA,amai muka ga tanayi akaje aka dawo kuwa ashe cikine da ita,kuka shirya ke da ita da asuba kikaje aka zubar mata ,harda cewa wai shawara ce take damunta”
Kunya ce ta ishi wanda aka kira da mairon wanda tafara masifa cikin borin kunya itama ta fara maidawa wanda tayi maganar da nata laifin,
“Naji dai ina Y’a tace kawai tayi,kuma hakan bazata sake faruwa ba,amma ba’a kama uwata da makocinsu ba a daki ina”
“Ke dan kutumar ubanki mairo mutsaya iyah kan gidannan banda sako gidan kowa,dan wallhi inta hakane kowa bazai ji dadi ba in toza’afara’za’afara”
“Hehe dama in baki yasan mai zaice bai san mai za’a mayar masaba,kan me uwa da wabi duk uban abinda za’a fada a fada ba tsoro nakeba,abin kunyane kowa gaba yabashi anan wajen ba baya ba,dan babu wanda abin kunya bai lullubeshi ba anan wajen,dan haka kawai ayi sha’ani wai na birni ya cuci na kauye”.
Ganin abin zai bacine yasa inna karima korar kowa daga dakinnata ,kowa yayi hanyar kofarsa yana maida nasa zancen.
A wajen su sameemah kuwa lokacin da suka dawo daga gidan alhaji Sama’ila har sunyi hanyar gidan kungiyar tasu,ta bada umarnin a nufi hanyar gidan karagiya inda aka kai labiru dazu da safe,mashin din suka k’uza suna sakin hayaki a duk layin dasuka wuce kafin suka yanka cikin gari inda zai kaisu inda yake.
A zaune suka sameshi yana rarraba ido fuskarsa ta kumbura suntum saboda dukan dayasha,mamakine kwance akan fuskarsa daya ga sameemah a wajen,
“Yayah labiru kayi Mamakin ganina ne,nice dai y’ar kanwar taka”
“Amma mai kike a wajennan,ko dagskene da ake cewa kece shugabar yan dabar garinnan?”
“Kwarai kuwa gashi ka tabbatar da kanka,kafin mukai ga nan,ajiye wannan wasan a gefe muyi abinda yatara mu,miyasa ka aikata abinda nake zarginka dashi”
“Makike zargina dashi iyee,kaika jimin yarinyar nan”
Murtuke fuska sameemah tayi kaman ba itace take dariya yanzu ba,wani irin wawan mari ta sauke masa akan fuskar sa saida dungura jini yana fita ta hancinsa,komawa yayi ya gyara zamansa da Mamakin irin naushin daya fito daga hannun nata kamar wani babban majiyin karfine ya dakeshi,
“Yanzu zaka bani amsa koh kuwa,mai ka aikatawa karamar yarinya dazu da safe?”
Karkarwa jikinsa yafara yana rarraba ido ganin abun dagaske ne ba wasaba,
“Iyyeee na’am wai nnnni ………din”
“Oh tambaya kake,kai burgu ku dan taba lafiyarsa na dan minti talatin da alama bayason lafiyar tasa”
“Ahah su tsaya,kiyi hakuri wayyo,dama kullum tana wajena,ina yin hakuri shine har jiya nakasa toh yau dana ganta shine,na saya mata shayi da biredi bayan ta shanye najata shagon ilu dama bai bude ba,na biya bukata ta,shine kawai”
“Mesunan abinda ka aikata kenan?”
Saida yayi dan shiru ganin zata sake zabga masa wani marin yasashi saurin cewa,
“Fyade,fyade sunansa”
“Kowa yaji laifinsa ko baijiba?”
“Eh munji shugaba”
Suka amsa dukkansu a tare,
“Kai arnen dawa dakkomun abinda nasaka kamin dazu nasan yanzu yayi yanda nakeso,cikin sauri kuwa yabar wajen ,bai dade ba sai gashi da wani kwano abinda yake cikinsa yana turiri,
“Kai burgu kucire masa wando yanzunnan”
Aikuwa kaman jira suke cikin kankanin lokaci suka sutale masa wando,tun baisan mai zai faru ba yafara ihu yana rokonta,
“Shshshsshdh,katsaya da ihun tukunna bari nayi maka wani gargadi,idan ka kuskura nayi maka hukunci kaje gida aka tambayeka mai ya faru ka kira sunana…….,hmmm,saina rabaka gabadaya da abinda kayi amfani ka aikata laifin”
Tun bata gama masa gargadin ba,ta juye soyayyan mangyadan da aka dauko daga wuta akan gaban labirun,cikin kankanin lokaci kuwa fatar wajen tafara sutalewa tun daga kasan cibiyarsa har zuwa rabin cinyoyinsa.
Su kansu yarannata saida suka girgiza da hukuncin da sameemah tah aikata,
“Kuje kujefashi a bayan layin unguwarsu inda yan gidan zasu ganshi,uwarsa saitayi jinyarsa tunda ita ke daure masa kan macijin yake wasa da wutsiyar”
Tabbbnnnnnnn,lallai sameemah!!
Mucigaba dai mutane Nah🤣🤣😂🤣

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤04❤

Ihu yake yana jijjiga kai tun yanayi da karfi har yazamo baya iyacewa komai sai nishi dayake saukewa kaman mai nakuda tazo gargara dan wahala.
Burgune yakalli sameemah wanda har yanzu fuskar sa bata dawo dadai ba da laifin daya ga shugabar tasu ta aikata,
“Amma shugaba wannan hukuncin dakika masa baiyyi tsauri ba kuwa?”
“Toh ka rama masa mana,saina san kaji babu dadi da abinda na yanke,kai wai yaushe kuka fara ma wannan challenge dinnna wa,ne,banason wani iyayi da nuna tausayi na karyar banza a fuskarku,dan tsabar munafurci har kune masu cemin kuna tausayi,da Y’ar gidanku ya farde,ai bansan sanda zakuyi masa aika aika ba saidai naji anakirana a police station naje na fitar da ku,aikin banza kawai inzaku kaishi inda na sakaku ku kaishi in kuma bazaku jeba ku fadamin saina kaishi da kaina”
Sunkuyar dakai sukayi dukkansu suna bata hakuri a tare.
Dalewa tayi kan mashindin burgu saida ta burka yafara kara kafin tace,
“Zanje gida na dawo,ku tabbatar kun shirya shagalin kafin na taho,bayan kun gama cika aikin”
“Bakomai Shugaba bakida matsala”
Fisgar mashin din tayi ta bule kura kafin tayi cikin gari da mungun gudu.
Bayan ta bacewa ganinsune burgu yajuyo yah kalli su arnan dawa tareda cewa,
“Kai dauko buhu musakashi muyi saurin gama aikinnan,dan komawa wajen shagalinnan,kunsan idan harta gama abinda take tariga mu,zuwa toh wallahi bazamuci wannan ganimar ba,nikuwa yanda yawuna yatsinke da wannan gashsshun kajin inban samu na yaga ba akwai matsala”
“Hakane ogah burgu nima tawajennawa haka take yakamata mu hanzarta”
Daukar labiru sukayi wanda yake ta yada kai dan wuya suka zefashi a wani katon buhu,bayan sun dorashi a mashindin arnen dawa suka dau hanya sai anguwar su labirun,wanda sannan yamma tayi,bayan layin ya dauke sawun mutane. Saida suka samu wani rami gefen kwatar gidan kafin suka jefah shi suka tafi.
Parker mash in din tayi a kofar gidan ta shiga tana fed’uwa tareda yin wakar koroso,larai tasamu a tsakar gidan wato matar yayansu manjo wanda yatafi cirani ,wanke hatsin tuwo take a kwaryah,saboda neman magana sai kuwa tace,
“Mutum bashi da aiki sai halayyar maza hakanma a mazan tantirai,allah dai yah shiryah”
Tsayawa sameemah tayi daga shiga dakinnasu na yan mata,kafin ta jiyo ta kalli kulu din,
“Kehh mekikace yanzunnan,kuma Sannan kifadamin dawa kike?”
“Aikin banza Inna fadi da wanda nake ma uwar me za’ayi,karkarinta dai borin koro kunya ko za’a dakeni ne yanda akeyiwa yan dabar iyee”
Jijjiga kai sameemah tayi kafin tayi wani bolll da kwaryar hatsin a kasa.
Ihu larai tafara tana kururuwa tareda durawa sameemah ashar duk wanda yazo cikon bakinta.
“Yar bantan uba ni zaki zubarwa hatsi ko uwarki ceh ta sayamin dazaki zubarmin?”
Shiru ta hadiye wani yawu mukut,ganin yanda sameemah ta saita y’ar wuk’a a makogaranta,
“Kika sake saka uwata a zancenki saina maida y’ay’an ki marayu kuma na maida manjo gwauron karfi da yaji,ki kuma sake ki gani zaki ga ko karya nake ko a’a,banza karya mai bin mazan wasu kawai”
Kwalo ido tasake yi kafin ta ce cikin mamaki ,
“Dama kinsani?,dan allah karki fadawa manjo wallahi yankani zaiyi”
“Banza karamar y’ar iska ashema tsoronsa kike ji,shine ni harkika samu damar shiga harka ta ko?”
“Ahah kiyi hakuri bazan sake ba”
“Kima kara mana kiga aiki da cikawa,mtswww”
Wucewa tayi ta bar kulu tana d’ebe hatsin dake kasa har Sannan jikinta rawa yake saboda kashedin da sameemah tayi mata.
Bakowa a dakin sai salma tana ta danne danne a irin wayar zamaninnan ,daga ganinta kaga irin matan nanne masu ji da kansu duk da cewa kyakykyawace dan inka dauke sameemah duk matan gidan ta fisu kyau,hakanne yasa take harka da manyan alhazan ds yan gidan basayi.
Itah ceh y’ar larai ta fari wato yayar su hanifah,kwanan ta dawo daga bikin kawarta wanda akayi a abuja sune manyan kawaye.
Sameemah koh kallonta batayiba balle ta yimata sallama,kayan jikinta ta cire kafin ta fito daga dakin daga ita sai towel a jikinta.
Fitowartane yayi dadai da shigowar SULEH MAYEH (yayan labiru) gidan abokin manjo wanda tun bayan tafiyar manjo cirani bai daina shigowa ana gaisawa ba.
Lashe baki ya hau yi yana kare jikin sameemah da kallo,dawani gashin bakinsa buzubuzu ga idonnan yasha kwalli dakyar kake ganin kwayarsa dan rinewar idon ,saboda shan sholi.
‘Yawwa yau na taki sa’a gaskiya tunda idona yai arba da wannan d’anyar kazar yau,kai rabbana yayi hallitta a wajennan,kaiiii dolema naje nasamu tsohonnan wato baba umaru,na mika yan kudina a bani ke mushiga daga ciki tunda naga ke baka d’ebi romo ka wuce”
Koh kallon inda suleh maye yake bata kallah saima neman ruwa da take wanda zata watsa a jikinta saboda zafin da’ake.
Wani dan yarone yazo wucewa ta kirashi,
“Kai zo nan,jeka kofar uwarka ka d’ebo min ruwa kace injini neh”
Da saurin jikinsa kaman zai kifah da kasa ya karba yayi kofar tasu da gudu dan cika umarnin nata.
Suleh ne yadameta da magana,dan shi a ganinsa tana jinsa,wani shegen kallo ta juya ta watsa masa kafin tace,
“Kai kasan allah duk da nasan ba saninsa kai ba,toh ka tattara yan kafafunka kabani waje,koh kuma yanzu nayi maka wani naushi da saina bajeka anan wajen saidai a zo a daukeka,kaga tsohuwa sai tayi jinyar majinyata biyu”
Karbar ruwan tayi da yaron ya kawo mata ta shige bandaki tana jan tsuka.
Saida ta gama shirinta tsaf kafin ta nufi gidan kungiyartasu,lokacin ana shirin kiran magriba,wasu masallacin kam ma sun shiga amma itah koh a jikinta kaman ma an ce an yafemata sallahr.
Lokacin da ta isa su burgu sun gyara wajen tsaf kaman ba shiba,a kijerar da aka tanada ta hakimce tana wani shan kamshi ,kayan ganimar aka bajemata a gabanta.
Kajine sun sha suya mai kyau jajaye sai turiri suke,gakuma lemo masu sanyi dakuma duulah mesaka mutum ya jishi a sama,wata kururuwa su burgu suka buga dan dadin ganin irin abunda aka kawo.
Hannu tasa ta yagi cinya guda d’aya tasaka a baki kafin kuma kowa yafara yagar nasa rabon,kid’a akasa mai irin buga sautinan kowa yana rausaya wa yana cika bakinsa da d’i,
“Kai shugaba jar wuyah mufah tunda muna kungiyarki mun more fah,wace kungiyace zakaga ana siyan kayan dad’i ana cin wannan dad’in in ba kungiyar seemah jar wuyah ba.
Wani rausayah seemah jar wuyah tayi irin na wanda aka zigashi dinnan,
“Hmm aiku bari kawai saima idan an samu wata hanyar ta bud’e,harka tazo saidai kuji ana kungiyar seemah jar wuya sai ana cika form kafin a shiga”
“Heeeeeeehuuuuu sai seemah jar wuyah”
Dukkansu aka dauki ihu tareda shewa ganin irin kirarin da suka yi mata yah shigeta sosai.
Salame ceh a zaune ana ta tad’i itama a nasu gidan da yamma itada surukanta da kuma kishin balbali,
Hira akeyi wanda duk rabin hirar tasu gulmar gidan gandune, d’aya matarce wadda duk zancen da akeyi bata saka bakiba saida ga baya tace,
“Babar labiru wannan gulmar dakukeyi bata da amfani ko kadan,abinda yake faruwa a gidan abune daya zama tamkar ruwan dare a namu sauran gidajen musamman ma kauyukan mu da kuma iyaye masu san ransu wanda daka yiwa y’ay’an su fa’da gwara komai ka musu,addu’a yakamata mu dingayi ba wai mudinga yayata lafin y’an uwanmu bah”
“Kehh Wallahi kiyimin shiru banason wannan iyayin naki da kutufifi,zaki wani zo kina yimana wa’azi an fadamiki nasiha mukeso,toh muje masallaci mana………..,”
Wani yarone yah shigo da gudu yana kiran salame da karfi,
“Babar labiru babar labiru,wai kizo inji wasu a waje,wai buhu suka gani a bayan gidan can yana motsi,suna budewa sukaga labiru ne wai an konashi da wuta a cikin buhun”
“Kuntun ubah kai meka ce?,dagaske kake Kuwa,yau nashiga uku na lalace wane la’ananne a fadin garinnan ya yiwa labiruna haka wayyyooo na lalaceh”
Amma babar labiru kamata yayi kiyi addu’a ba ki dinga ihu ba”
“Dallah rufemin baki yar kan uwa shegiya wato bazaki barni da wannan wa’azinnaki ba koh,yanzu haka ma dake aka had’a baki inaga,dan dama duk bakin ciki kuke min dani da y’ay’ana”
Ganin fad’an na neman komawa kansune yasa kowa tayi kofarta ,ita kuwa ta rufa hijabinta batasan ko dadai ma tasaka ba,tayi waje har sannan bakinta bai yi shiru ba.
Saida su seemah suka kai wajen karfe dayan dare kafin kowa yayi tunanin hanyar tafiya gidan su,mashin din burgu ta dauka tayi gaba ,yana ta magana amma ko juyowa batayiba bare yasa ran zata dawo masa da mashin din.
Hanyar anguwar su sameemah ba kowa haka ta bi da wannan uban daren ga kuma duhun allah da annabi daya lullube sararin samaniyah,a wannan lokacin babu yanda za’ayi mace kamar kowacce ba irin sameemah ba tafito da irin wannan daren kuma a mashin ita kadai.
Tana cikin tafiyane taji alamun wani abu yah rike mata tayar mashin,tsayawa tayi cak da mashin din amma shiru bataga kowa ba,Murmushin gefen baki tayi da tagane mai hakan yake nufi,
“Tabbb gaskiya an rainani,yanzu harni wani zai rikemin tayar mashin,toh me akeso nayi ihu ko kuma zefar mashin din na barshi a wajen,kafin gobe wani yah lallab’o yasace koh?”
Tura mashin din tayi sai kuma taji tayar ta tafi,wani yunkuri tayi tasake tayar da mashin din kafin tace,
“Yadai fi muku,a saukake dan ni ba addu’a zanyiba dama tunda ba iya wa nayi ba,kuma ba ihu zanyiba tunda ba ganin ku nakeba,kunga bata lokacinku kueyi nima ku bata min nawa,saboda so nake naje nayi bacci kuma sai gobe,aga dame zatazo a tareta ana mika wuyah”
Har taje bakin kofar gidannasu batabar surutunba kaman wanda wani ne a kusa da ita yana jin me take cewa.
Alamun kamar mutum tagani a bakin gidannasu kamar mace tana firah,duba agogon hannunta tayi tana murza ido,karfe biyu ta kusa amma ga wata a kofar gidannasu tana hira,
“K’undun ubancan mai yarinyar nan take a waje a wannan Daren,mu manya ma mungama mun dawo gida amma ita tana waje,hmmmmm bari nazo na sameku”
(Toh fah kunji wai itace manya,su manya gatan wasa)
❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤05❤

A manne suke a jikin katangar sun lab’e itada dashi har baka gane me ake kullawa a wajen,sameemah ceh ta sharo mashin din da gudu,suna kallonta kuwa sukayi saurin bajewa da sauri,saida taje ta kafe mashin din kafin ta dawo wajenna su tana gyara zaman gyalen dayake wuyanta da kuma wandonta wanda rigar ta tattare saboda hawa mashin.
Kad’a key din tayi a gabansu kafin ta karewa saurayin kallo,
“Kai uban me kakeyi a kofar gidannan,har karfe biyun dare,duk wanda kasamu da ka lallatsa tun karfe goma bai isheka ba saika kai har karfe biyun dare dan zalama,kawuce ka bar wajennan ko saina saka karnuka sun sanja ma kamanni tukunna,da haka kam ai sai kajata ku shiga cikin gidan zuwa kan gadon baba umaru ku karisa tunda har yanzu bai isheka ba(wato ubannata ma bata barshiba kenan)”
Cikin sauri da alamar rashin gaskiya yabar kofar gidan yana sosa keyah,harara ta bishi da shi tareda cewa,
“Heeeege mai siffar mayu kawai”
“Wai miye hakan zakina wani zagin min saurayi kaman wanda yayi miki sata?”
Buge mata baki sameemah tayi cikin sauri kana ta dora da cewa,
“Har kina da abin cewa keda na kamaki dumu dumu da laifi,a kofar gidanmu saboda ki jawo mana abin magana koh?,nasake jin bakinki ,kin shige gida ko saina yi kwallo dake tukunna”
Cikin kunkuni khadija tafara cewa,
“Kuma wallahi saina gayawa ummah abinda kikamin,naga kema daga yawon ta zubar din kika dawo kuma daga gani shaye shaye kika iyo tunda ga nan warin wiwi a jikinki…..,”
“Mekikaceh wai?”
“Babu komai ba abinda nace”
Tana fadin hakan ta shige gidan da gudu dan ba karamin aikinta bane ta biyota ta kara mata wani dukan.
Sassafe masifar a gidan su labiru ta kare dan yanda salame taga rana haka taga dare ita da labiru da kuma mai maganin tofi ,wanda ta daukoshi saboda yayi ma labirun magani,dan batada arzikin kaishi ko chemist ne bare kuma asibiti.
Da safe har ya samu ya yi d’an bacci saboda maganin da aka saka masa,saidai fah su labiru babu saka wando zaman daki yakamashi kenan.
Saida safenne saleh maye yah shigo dakin uwar tasa duba labirun,salame ce takalleshi da takaici kafin tace,
“Yau ganshi bawan mace kawai,tun jiya ake ta maganar abinda akayiwa dan uwanka sai yanzu uwartaka ta biyu ta barka kazo ka dubashi kenan,wanda yarako maza duniya kawai”
“Haba Babar labiru yah kike yawa ne,ni ina can bansan ma me ake yi ba,dan sai yanzu na tashi a bacci,shine nace bari nayi hankali nazo na duba shi da jikinnasa,kuma ma dazakice LUBABATU ceh tahanani zuwa,ai kaunace idan ta hanani ma”
Kuka salame takawo ta kece tana fyace majina ga ciwon labirun ga kuma takaicin babban dannata wanda yanzu shida wanda suke turu babu wata maraba mai yawa,
“Dallah ni tashi kaban waje,yanzunnan ba sai anjima kaje ka dau matakin abinda akayiwa labiru dan bazan yadda ba wallahi”
Mikewa yayi da d’an guntun karfinsa yah ciro wata wuka a wandonsa wanda yafita acikin kalarsa saboda daud’a,
“Wannan dolene yanzunnan zanje na koma waye fad’a minshi saina fard’e masa wuya a yau ba sai gobeba,mu daman ai ta irin wannan harkar muka kware”
“Eh naji ana cewa wani a anguwar yaga yaran sameemah wannan shegiyar yarinyar mai kama da y’ay’an aljanu,wai sun ajiye buhun da aka samu labiru a ciki,ina da itace tayi wannan aika aikar ,dan kowa yasan zata aikata”
Suleh ne yajuyo ya kalli uwar tasa tareda cewa,
“Iyee inna banji mai kika ceba,ai seemah dai tawa kike nufi?,kai ba mai taba wannan cikar na kyaleshi ,yanda nakejinta a kashin raina ai koke banajinki,babar labiru itah ceh fah surukarki wanda za’a daura auran kwanannan,so kike idan naje na yanketa akawomiki suruka mai tabo”
“Inalillahi jama’a kuzo ku tayani bakin ciki,wannan d’a haihuwar banza nayi,yanzu nikake fadawa bawanda kakeso sama da ita a duniya,kuma wai harda ni,bayan irin aika aikar datayiwa dan uwanka?”
Turewa sulen tayi cikin bacin rai yah wancakala gefen labiru wanda yake zaune an saka zani an lullube masa gun da ya kone din,sai zazzare ido yake maganar ma wuyah take masa kaman wanda aka kone masa bakin.
“Dan banza ji yanda ka wani baje a kasa dan kawai na bugeka,dama uwar me zaka iyah idan kajedin duk kwaya ta gama hudaka tun daga baki har hanji,wannan masifah da mai tai kama”
“Inna gaskiya karkije gidanannan kiyi musu wannan masifar taki ,gidan surukanki ne fah “
“Innnnnnaaaa ba ita bace tayimin haka ba,karkije kice itace tayimin haka na rokeki innannnnaaaa”
“Yawwa inna kinji abinda labirun ma yace koh?,in ma itace cikin soyayya zan lallameta ta fad’amin”
Dawowa tayi tana karewa y’ay’an nata kallo,daga wanda yake kwance babu abinda zai iyah an nakasa shi sai wanda shida tab’ab’b’u basuda maraba dashi da su.
Cije baki kawai tayi dan takaici ta rasa ma mai zata ce,
“Shashashu kawai in ma asiri tayi muku yau zai karye dan ubansa,zuwa gidan gandu kuwa ba fashi inyaso idan naje ku hadiyi zuciya ku mutu,yau koni koh su a garinnan wallahi,dan bazan tab’a yarda ba,in ta kamama kotu zan maka su,muje ayi ta shari’ah daga nan har kotun k’oleee.
KO safiyah bata gama waye ba,dan wasu ma ko karyawa basu gama yiba salame ta doko sallama cikin gidan gandun,
“Salamu alaikum gafaranku dai,ko bakowa a gidanne”
Wani yarone ya fito daga kofar su larai din yace,
“Suna nan amma kowa yah kofarsu”
“Inane kofar su sameemah wannan shegiyar yarinyar”
Tun kafin yayi magana larai ta leko domin ganin wace bakuwar da safiyanannan,dan tun a jiya da daddare suka baro asibitin saboda yanayin sha’ani na kudi,
“Kutt dama kece,kin hutasar dani dama ina shirin zuwa gidannanki muyi duk wacce zamuyi dake amma tunda kinzo shikenan sai a fara”
“Mekike nufi da cewa muyi wacce zamuyi ,toh ni ba wajenki nazo ba ,wurin yar dabar gidannan nazo da ta lahantamin d’a yana nan a kwance kaman bazaiyi raiba”
“Ayyyirirri koma wa kike nufi tamin dadai duk da bashi zai hana na fasa abinda nayi niyyah ba”
“Kehh duk abinda yafaruma larai ki bari sai daga baya yanzu ba wajenki nazoba”
“Ohh kina nufin bakiji abinda dannaki la’ananne ya aikata ba,koda yake bazakijiba saboda ba y’arki yayiwa ba,yanzu dayake shi akayiwa aika aika aikin ji har kinzo neman ba’asin labarin.
Toh in ma baki sani ba kisani danki labiru y’ata hanifa ya farkata,kaman yasami fanko saboda tsabar tashanci kuma yayi gado,toh bazan yadda ba,yanzu dakike cewa yana jinya toh yana warkewa zan bawa gardawa sadaka su sake maidashi kwance,dan jinin y’ata billahillazi bazai tafi a banza ba”
“Ke wai dankinga nayi shiru ina jiran ki fadi abinda yake bakinki,aikin banza saboda gadon kwadayi yasa ina kuke lik’a masa ita,dama aka ce ai k’uda wajen kwadayi akan mutu,kuma dazakice wai gado dan ma abin kunyar kowa yana da shi a gidansu ,ko kin manta tsoho wanda baya saka wando sai babbar riga kawai saboda bin bazawaran kauye”
Hayaniyar ce tafara yawa inda matan kofa ko wacce take lekowa dan kashe kwarkwatar idon ta.
Da abin yayi yawa fad’ane ya rukume tsakanin salame da larai kowa yana tsinewa kowa albarka kaman wasu zakaru.
Saida mazajen suka fito kafin aka samu aka rabasu dakyar kowa tana huci kaman shanu.
“Kai kai mai yafarune haka,mu gidannan babu dama mu tashi a ji shru kaman kowane gidan saidai Koyaushe da masifar dazata kunno kai”
Kawu KAMILUNE,mai magana yah fito zai tafi gona,dama shi bai fiye zama a gidanba kl yaushe yana wajen neman kidinsa,matansa ma yahanasu shiga duk wata cakwakiyah da ake a gidan indan yakama wata kuwa da hannunta a ciki toh saidai ta nemi wani gidan badai nasa ba.
Jin muryarsane yasasu salame tsayawa fad’an sauran matan kuma kowa ta koma gefe ta kasa kunne dan taji mai za’a ce,dadai lokacin ne kawu shehu shida baba umaru suma suka shigo daga wajen mai shayi da alama wani yaronne yaje ya kirasu,
“Wannan yar rainin hankalince mana,dan tsabar su dangin marasa kunyane duk abinda danta yayi bai isheta ba hada zuwa tana wani kumfar baki wai an illah ta mata d’a a gidannan,kuma illatawa bata ga komai ba ma saina tashi yanke nawa hukuncin ehhe”
“Hukunci kin dade baki dau hukuncin ba abinda akayi masa ma na yanzu ba shiru zanyi ba barekuma kiyi tunanin daukar wani matakin”
“Kai ya ishemu haka wannan yarintar,kun girma ku ba yara bane amma baku da maraba da yaran kuma abin kunyar ma a gaban yaranku kuke wannan abun,ke salame mai akayiwa dannaki kikazo tada fitina da safennan”
Baba umaru ne yadaka musu tsawar cikin bacin rai da kuma k’osawa da halinnasu na yau da kullum,
Jin an tambayeta ne yasata fashewa da kuka tana shareewa da gefen zaninta kafin tace,
“Dan tsabar rashin imani bakuga aika aikar da akayi masa ba,tun daga kasan cibiyasa har zuwa rabin cinyoyinsa an konesu da man gyada mai zafi,babu komai sai fatarsa a waje kawai,kuma anfadamin wani marar imaninne a cikin gidannan yayi masa dan haka bazan yadda ba wannan ai niyyar kisan kai akayi ,yanacan katon saurayi a kwance sai abinda akayi masa tukunna”
“Allah ya kara baiga komai ba ma,in duninsa halin bunsuru”
Larai ce tayi sauri ta fada tareda d’ane baki kaman ba itah ce ta fad’a ba,
“Keh larai banason shiririta ana kwantar da wuta kina kara mata fetur koh?”
Baba umaru yana rufe baki kawu shehu yadora da cewa ,
“Laifinta Toh kagani yayan umaru,bayan abinda dannata yayiwa yar mutane kuma taxo tana fadan wai wani yah nakasa mata shi,ina ruwanmu toh,in zatayi hakuri tayi in kuma bazatayi ba ta kai kara ,muma saimu kao karar in yaso ayi ta shar’ar tunda ita take so ayi tayi,
“Ahah baza a kai har haka ba,ke salame tunda kinji mai danki yayi sai kije gida kiyi jinyarsa tunda kinga suma jinyar tasu yar suke,kowa sai yayi hakuri yaran zamanine sai hakuri ka haifesu baka haifi halinsu ba,muma kuma iyayen da na mu laifin ta wani wajen ,allah dai kawai yah shiryamu gabaki daya”
Dakyar su kawu kamilu suka kwantar da fitinar salame ta tafi gidanta tana kanana nan maganganu wanda allah ne kadai yasan ranar dazata bari.
Sameemah kuwa duk abinda akayi a gidan bata sani ba,saida wayarta tayi Ring ne kafin ta juya ta kalli screen din ,tareda tsuka saboda tashinta a bacci saboda tasaka wayar a kusa da kunnenta,
“Alhaji bala”
Shine sunan da ta fad’a cikin muryar bacci kasa kasa……….

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤06❤
“Heelloo alhaji bala yah hidima?”
Seemah ta fada cikin muryar barci,wani irin mika alhaji bala yayi jin yanda ta amsa masa cikin sanyin muryah kaman ba sameemah daya saniba,
“Lafiyah kalau madam yah hutu da jin dadi”
“Lafiyah kalau,wani abune yah faru?”
“Ahah babu abinda yah faru gimbiya kawai na kira ne naji lafiyar ki,sannan kuma na sanar dake inkin shirya ko yaushene to kiyi min magana zan aiko mota har kofar gidanku a dauke ,kizo mushakata muji dadin mu,saidai ina rokonki dan allah naji kiran shiryawarki da wuri,dan baki san yanda nake jinki a cikin zuciyah ta bane,akanki babu abinda bazan iyah ba,kawai hadin kanki nake bukata shine kawai cikar burina”
Saida ta tabe baki tukunna tace,
“Naji alhaji yanzu ina kwance banason a takuramin ka bari idan na tashi nayi tunani zaka ji mai na yanke ,kuma karka sake kirana sai na nemeka tukunna”
“An gama gimbiya,ai duk abinda kikace shi za’ayi kawai”
Sauke wayar tayi kafin ta kara danna wani kiran,ring daya aka dauka a d’aya bangaren,
“Allah yah taimaki shugaba me kike da bukata”
“Kai C.I.D(dan leken asiri),ka saurareni da kyau”
“Ina jinki”
“Ina son duk wani bayanai akan alhaji bala wanda muka hadu dashi a gidan alhaji Sama’ila,tun daga kan iyalansa sana’arsa har zuwa kan karfin siyasarsa,in takama inason bayani kaf akan gidan shata warsa,ka kawomin nan da bayan azahar,sannan kuma akwai abinda zakamin bayan hakan”
“Wannan mai saukine an gama shugaba”
Ta shi tayi daga kan gadon kafin tah zuba wata uwar feduwa wanda in kana bakin kofar tasu saika jiyota,
Wasu manyan karnukane guda uku suka shigo dakin suna karkada jelah,suna sakin yawu a bakinsu kaman zasuci babu.
Sameerah ceh wanda take kwance tah buga uwar tsuka tareda cewa,
“Aikin banza wai dan tsabar rashin mutunci kare har dakin mutane,su gasu abu kamar kuraye dan muni wannan ai walakancin yayi yawa”
“Kehh reza yaga mata kayan jinkinta yanzunnan sannan kiyi mata balli balli a cinya”
AI kuwa kaman jira farar karyar take tayi kan sameerah da sauri tana gyara baki,wani uban ihu sameerah ta buga cikin kankanin lokaci sai gata a waje,dakin uwarta ta nufah tana ihu tareda neman taimako.
Dakin inna ramatun ta shige tareda rufo kofah tana rafza ihu a ciki.
Mutanen gidanne hankalinsu yadawo kan abinda ake,dama kowa yana tsaye bayan an yi hayaniya tsakanin salame da larai,
“Wayyo baba umaru ku taimakeni kuna ganin zasu cinyeni da raina wayyyo inna”
Kowa yana jin ihun sameerah ga karnuka a kofar wajen amma babu wanda yayi gigin karisawa kusa dasu,bare su had’a dashi,
Baba umaru ne ya d’aga muryah yah kira sameemah wanda take daki a zaune kaman ba itah ce ta saka su ba,saida akayi kira kusan uku kafin tah fito a dakin tana mitstsika ido kaman ba itaba,
“Gani baba mai yafaru”
“Gaki kaman yah,ki debe wannan karnukannaki kina gani zasu yiwa yar uwarki illah ?,kuma sannan ki debesu a gidannan yanzunnan”
“Bazan Hanasuba har saita bani hakuri in ba haka ba kuwa wallahi sai sun mata balli ballin dana saka suyi mata,gobema ta sake zaginsu a gidannan in zamanta sukeyi”
Sameerah kaman jira take dama tanajin mai ake cewa,
“Kiyi hakuri bazan sakeba dan Allah ki hanasu karsu min fata fata”
“Shikenan allah yah ceceki,kehh reza zo ki tafi yawanki yanzunnan,saidai barin gidannan babu inda zasuje,inda wanda yake bani abincinsu ya daina daga yau,ai sun mafi bil’adaman dasuke gidan mutunci,tunda su basa yin tazubardin da y’an gidan sukeyi”
Tana gama fada tabar wajen ,batare da jira jin mai wani daga cikin wajen zai ce ba.
Kowa shiru yayi yah tafi harkarsa,ita kuma sameerah ta fito tana share hawaye tareda jan zuciyah,fitasari yana bin gefen cinyarta.
Zainab ceh (kanwarta wadda take binta saidai sameemah ta girmeta da kadan),tah kalli sameerah suna hada ido ta tuntsire da dariyah tana nuna fitsarin dayake bin kafar ta,itama sameerah fitsarin dayake bin ta takallah wanda sai a sannan ma ta kula da shi,
“Kuttt keh dan buhun ubanki ni sa’arki ce kikemin dariyah iyee”
“Hehehe niba sa’arki ba ce ina na isa,saidai ga wacce itama ba sa’arki bace ai ta saka ki fitsari a wando😄😄😄”
Sameerah ceh tabi bayan zainab da gudu a zuciye,sai kuma inna ramatu tayi saurin dakatar da itah,
“Keh dakata ina zakije da wannan fitsarin koh mahaukaciyah ta maida ki,bayan tura miki kare?,gashinan ai kin kaso aurenki kinzo yarinya karama tana miki yanda ta ga dama”
“Kai ji inna da wani zance,naga ke kika nace saina aureshi saboda yana kawomiki kayan dad’i,da kika gane yana dukana kuma d’an shaye shaye ne,sai kika shiga kika fita kika raba aurena dashi,kuma yanzu kizo kice na kashe aure na,sameenu ma kullum sai dad’in baki idan nace yah fito aure sai yacemin zai tafi,yoh ya kikeso nayi iyeeh”
“Toh yah isa haka ba tone tone nace kiminba wuce ki cire kayanki,dukkanku baku da wani ishashshen hankali kaman kuna cin k’asa”
Wayah C.I.D yayiwa sameemah akan cewa yana kofar gida hakan yasa ta fita domin karbar abinda yah kawo mata,
A zaune yake akan dakalin kofar gidannasu,yana ganinta ya taso tareda mika mata abinda tasashi yayi mata.
Wani abu tah mika masa baki sannan sukayi kus kus babu wanda yakejin mai suke cewa,
“An gama shugaba ranki yadade “
Baba umaru ne yadawo daga masallaci anyi sallahr azahar ya wuce ta gefensu ita da c.i.d.din,har yawuce kuma ya dawo,
“Kehh sameematu idan kin gama dashi din kizo ina san ganinki”
“Tohhh”
Lokacin da ta karbi abinda take bukata maimakon ta tafi kiran da mahaifinnata yayi mata sai wucewa daki da tayi kaman basuyi yace ta zo ba.
Sai can wajen la’asar ne baba umarun yasake aika yaro ya kira masa itah.
Nan ma saida ta gama sha’anin gabanta kafin ta tafi dakin baba umarun inda yake kirannata,
KO sallama batayiba ta nemi waje ta zauna tana kallon bangon dakin ,
“Baki iyah gaisuwa bane?”
“Na iyah “
“Toh miyasa bazakiyi ba,koh sai ance kiyi?”
“Banayine nasaba kowa gaisheni yake bana gaishe da kowa”
“Toh nima harda ni,ni zan gaisheki kenan,mai yasa kina girmane amma komai yana kara tabarbarewa”
Hade girar sama da kasa tayi da alama an tab’o inda yake mata kaikayi wato fad’a,
“Tun dazu ka kirani ,amma toh kayi hakuri mana wani abu nakeyine,ni kasan banason fadannan,banaso ana min fada kuma ka sani”
“Hmm mm allah yah shiryaki,toh naji kinji labarin alhaji babba(uban gidan gandu kenan,yah tsufah tukuf shine baban su baba umaru) bashi da lafiyah?”
“Eh naji su zainab suna fad’a”
“Toh kinje kin gaisheshi? Kokuma sai yah mutu ki leka gaisuwar sa”
“Haba baba yanzu akan wannan ne dama ka kirani ,kuma fah kunsan mutuwa zaiyi shine kuma za’a fatamin lokaci akansa,habba dan allah,a dinga yimin adalci mana”
“Keee sameematuh gyauton uwaki,nake ganin ki kamar kinada hankali ashe babu komai akanki kema sai wiwi din,ki tashi ki bani waje ,kuma ki tabbatar kinje kin dubashi,dan uwanki ma wani satin zasu taho ,sun samu hutun sati d’aya”
“Tabbb AI wannan mai zubin aranan,hmmm ashe nasake shirin taryarsa kenan,dan rashin mutuncin nawa yayi sanyi,kar naje yah zo ya sameni da wanda ya sanni dashi,gwanda na yi sabo fill”
“Innalillah yanzu koshi d’an uwannaki ma baki barshi ba,ashe ba iyah y’ay’an innarku ramatu kikeyiwa rashin mutuncin ba har shima baki barshiba”
Toh kai ma baba umaru………..”
“Karki sake cewa komai tashi kije yah isheni haka dan Allah,allah ya shirya ku kawai shine addu’a ta a kullum.
Tana shiga daki kuwa taji su zainab suna zancen zuwan yayannata,wanda suke uwa d’aya uba d’aya itada shi,su kadaine y’ay’ayan inna Hajara,wanda tah mutu tun sameemah tana shekara bakwai,shikuwa MAJOR SAMEER tun bayan mutuwarta da kwana bakwai yabar ma garin gabad’aya ,inda yabi wani Soja a anguwarsu.
A can yayi makarantar sojojin a wajensa sannan yah fara aikin sojan,saboda kwarewarsa da kuma zafin nama har yakai matsayin Major da kananun shekaru.
Yanzu shekarar sa biyar da aure,inda yah auri matarsa Saleemah y’ar gidan shugabansu,da d’ansu guda daya mai sunan baba umaru,(farouq),saikuma ciki ta saleemah take dashi dan karami a halin yanzu.
Babu wanda yasan wace wainar ake toyawa a gidan major sameer din saboda sai yayi shekara biyar ma bai zoba,dan tun sanda yayi aure yakawo matarsa bai sake dawowa ba sai wannan zuwan da zaiyi wani sati mai zuwa,suna can a porthacourt shida matarsa da kuma aikinsa.
“Kee salma sinji wai yayah sameer zaizo wani satin shida anty saleemah,”
Zainab ta fad’a tana washe baki,
“Toh miye dan zasuzo din ,ni wlh na tsani matar nan tasa ta wani makaleshi ko zuwa bayayi bare ya samu wata ya aura,sai ita kadai kawai”
“Heeehhehe yarinya kice kishi kike,koh kina cikine a yi y’ar hadi gida keda shi”
Sameerah ta fada tana turo daurin dan kwalinta gaban goshi,wanda tun dazu chatting take a WhatsApp batace komai ba sai yanzu “
“Kee sameerah banason iskanci kishin uban me kuma,mai zanyi dashi “
“Mai zai yi dake dai,kina nan guntun alhajawa sun lakace sun bar saura,kinga dan kyakykyawan matashi mai kudi kinaso ki shiga daga ciki”
“Kutumar Uba lallai sameerah sai yanzu nagane inda kika dosa,kinaso kice kishi kike dani dan kinga bakya kasuwa,babu kowa sai wannan kanjamemmen sameenun mai kama da biri,Wanda koh daura min shi akayi zan cire na zefar ke kuwa nan har durkusawa kike kina rokonsa kar yah tafi”
Wani wawan duka sameerah ta kaiwa salma a kumatu,ai kuwa suka hau kokuwa,zainab ceh ta tashi ta fice dan ganin abin yayi yawa,dama itah tsoron masifah ne da itah kamar farar kura.
Sameemah kuwa tana zaune tana kallonsu saima dauke kai da tayi kaman ba’a haliccesu a dakinba.
Wayar tah ce tayi ring ta zuya ta dauka,saidai batajin mai ake fad’a saboda surutun da su salma sukeyi,wata tsawa ta daka musu cikim bacin rai.Dukkansu shiru sukayi suna kallonta,
“Hello,burgu mai kake cewa waim”
“Had’uwa da BUBA JINI kuma ?”
“Shikenan zamuji da Wacce yazo saidai ka kaishi zuwa gobe dan yanzu akwai abinda nake shirin yi ne”
Saida ta ajiye wayar ta kallesu kafin suka kula da yanda ta basu umarni cikin kankanin lokaci kuma suka bi batare da sun sani ba(sameemah kenan).

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

GIDAN GANDU
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤07❤

Tashi sameemah tayi kaman mai kiwuyar tashi a wajen kafin ta nufi kofar da alhaji babban yake.
Yana kwance anyi masa shimfidi a tsakar dakin saidai idonsa yana kallon mai wucewa,kallon sameemah yake da son gano wacece,
“Wannan din wacece?”
“Sameemah ceh “
“Ohj sameematuh ceh,toh yah labarin mahaifiyar taki kuwa an ji labarin itah y’ar inace ?”
“Mahaifiyata kuma ,ita kam ai tah rasu”
“Yaushe amma banida labari. Koh?”
“Ina nasan maka ni zaka tambaya,ya jikinnaka?”
“Lah jiki da sauki yar nan kinsan tsufah ne “
“Eh AI naga alama kam”
Tafada tana kare masa kallo daga inda take zaune,
“Toh nizan tafi allah yasa kurigamu gidan gaskiya,ina haka ake cewa?”
“Ni zaki tambaya,toh kigaida ummartaki idan an ganta”
“Kai ni karka dameni da wani zancen na gaisheta,inaga ma kaine kake kallonta saboda ka kusa jona sahunsu,haka kawai zaka wani dameni da cewa in gaida wanda yah mutu,kai idan kaje kace ina gaisheta “
“Lallai yar nan allah yayi ja’irah”
“Ashe da sauran hankalinka kasan mai kake,to sai anjima allah yah sawwake”
Daga haka ta kade skirt dinta tabar wajen tana buga feduwa,tai hanyar waje,bayan tah gyara gyalen wuyannata(dan itah yanda maza suke ficewa daga gida sanda suka so fita haka take ficewarta sai sanda ta dawo).

Washagari da safe da wuri tabar gida saboda shirye shiryen haduwa da buba jini,dan kaff garin ba kungiyar dabar da ta kai tasa wajen kwarewa da kuma bud’adden ido.
Lokacin da suka isah ainihin inda sansanin yan dabarsa take saida burgu yayi Mamakin irin tsarin da akayiwa wajen kaman na yan boko haram.
A harabar cikin wajen suka samu anyi shimfid’a da kayan marmari duk na tarar seemah jar wuyah da yaranta.
Tun daga nesa kuwa buuba jini yah hangosu itahce a gaba suna biye da itah ,har Mamakin irin biyayyar da yaranta suke mata yake,saboda ko shi daya tara manyan yan daba,basa masa biyyayah yanda yaran seemah suke mata biyyayah.
Tana zuwa saida ta zauna a tsakiyar daddumar suna kallon juna ita da buba jini kafin sauran yaran ta,wato su burgu suka zauna a bayanta.
Murmushi yayi tareda dage girar hagun irinna yan iskannan kafin yace,
“Barkanki da zuwa”
Itama irin yanda yayi mata tayi kafin tace,
“Na amsa gayyatarka ,saika fadamin meyake dauke a bakinka da har ka nemi yin magana dani,kuma har cikin gidanka?”
“Ba komai bane ,inaso ne kawai ki had’e da kungiyata muzama d’ayah”
“Meyasa ka bukaci hakan”
“Saboda keh macece,nasan ba iyah dan kungiyah yan siyasa suke nemanki ba,harda wani kudurinsu na daban,kinga idan muka hade ,karfin izzarki da kuma tsaro zai karu,nikuma kinga saiki kawo mana hankalin yan siyasah su bamu aiki,nasan bazaki ki amincewa ba”
“Idan kuma naki amincewar fah mezakayi?”
Kallon idonta yayi yanda take maida martani kaman ba a gabansa take ba ,babu alamar tsoro a idonta,
“Tunda kika shigo gidannan dole ki amince da bukata ta “
“Idan naki fah mai zai faru”
“Toh bazaki bar gidannan da kafarki b…………”
Tin kafin yah karisa maganar,seemah ta yanka jijiyar hannunsa daya rike wukar dayake mata barazana da itah cikin kiftawar ido.
Kururuwa yah fara yana danne wajen da jini yake tah fitah,
“Kai din dama ba babban shege bane ,ya za’ayi wanda yake kiran kansa da suna jini kuma yayi ihu dan jini yah fito daga jikinsa?”
Yan dabar sa ne suka iyo kanta da sauri,sai kuma yah dakatar dasu ,cikin dauriyah da cije baki yace
“Karku yi mata komai,kuyi hanzarin shiryah motah yanzu mu tafi asibiti,banason kowa yayi mata hukunci,ni nan da kaina zan hukuntata,sai tayi dana sanin abinda tah aikata”
“Kai dakata da surutun haka,duk naji su,bana bukatar neman ayimin maimaici,saidai kai din kayi hanzari,domin in bakayi sauriba jininka zai kare a nan wajen,kaga sai muga wa zai baka ransa kazo daukar fansar dashi”
Mikewa yayi idonsa yayi jawur dan azaba,fadawa mota yayi tareda watsawa sameemah wani mugun kallo,na alamar zamu had’u.
Ita kuwa gogar ko a jikinta saima murmushi da tayi masa tareda daga masa hannu tana yimasa bye bye.
Duk abinnan da ake,su burgu mutuwar zaune sukayi lokacin da suka ga abinda sameemah ta aikata,dan sun saddakar yau kam kwanansu yah kare a wajen buba jini,dan duk fadin garin babu wanda bai sanshi wajen yanka ba da kuma aika aika,kowa tsoronsa yake babba da yaro.
Saida ta shuri burgu kafin yayi ajiyar zuciya yace ,
“Ma’am shugaba,sun yanka mu ne”
Zefah masa makullin mashin tayi kawai batare da tace komai bah.
Bayan sun hau mashi dinne suna tafiyah burgu yace,
“Amma shugaba bakya ganin yanzu muna cikin matsala”
“Dallah ni yi shiru ka rufemin baki ,bakuda aiki sai tsoron tsiyah,ni narasa meyasa ma nake tare daku har yanzu”
“Yi hakuri bazan kuma bah”
“Kudin hannuna yayi low,kaini gidan badariyyah,zan karbi bashina da tazo har gida ta karbawa mijinta a wajena,yau zanga mai hanani fitowa da kudina a cikin gidannan,in tareda uwar wani ake samosu”
“Gaskiya kam shugaba kiyimasu rashin mutunci ba shin fah ya kusa wata guda a wajensu,babu ma yah wannan mijinnata kullum yana wajen caca”
“Toh ina ruwanka,kai waye zaka zagi mijin yar uwata,ko cewa nayi ka tayani,kudinka ne koh nawa?”
“Kiyi hakuri shugaba an iso gidan “
Sauka tayi daga kan mashin din kafin tacewa burgu,
“Jirani na Shiga na fito,dan ko bayanan saita fadamin inda yake”
Langa langan kofar gidan tah buga da karfi,saida awakin gidan suka dungura suna d’aure,badariyyah ce ta fito da sauri,suna had’a ido da sameemah ta buda wani uban salati da a’uziyyah tana dafeh kirji.
“Eh zaki kori shedan mana tunda kinga nice,na rantse ko dujal zaki kora saikin fitomin da kudina,koh kuma ki fadamim inda lalataccen mijinnaki yake naje na karba”
“Haba sameemah babu koh Sallama,kuma ai saiki shigo mu gaisa koh?”
“Ba gaisuwa ceh ta kawoni ba,kudina nazo karba,saiki bari sanda nazo zumuncin saiki ce ga wajen zama,ki fitomin da kudina yanzu ,dan babu d’aga kafa yau,koh inna karime zaki sayar bai dameniba,ni kudina nasani,tunda ba da wani shege aka hadu aka tarasu ba”
“Kiyi hakuri sameemah,wlh ko kudin cefane nima bai baniba,kuma ai ni yar uwarkice”
“Hmmm ke kikasan wannan yaren,fad’amim inda yake yanzunnan,ko kuma na tattare y’an awakincan nayi kasuwar dabbobi dasu yanzunnan”
Tafad’a tana nuna awakin Badariyyahn,
“Ahah kiyi hakuri,indai baban iliyah neh,wallahi yana rumfar kofar gidan Ashiru mai shayi”
“Dama nasan ai duk munafurcine,ba sonsa kike na,indai akan kudinkine”
Juyawa tayi ta fice daga gidan bayan tayi boll da langar data gani a tsakar gidan miyar kuka ta bushe a ciki,
“K’azamai kawai,ai dole kuyi ta gudawa”
Bayan ta fitane Badariyyah ta sauke ajiyar zuciyah tareda cewa,
“Na rabu da masifar yau kam,saikuma wata ta gaba”
Ashiru mai shayine ya k’ara gyara zamansa zance yayi dad’i yace,
“Hmm AI baka saniba BALA,shi sha’anin kudi a bishi a hankali kawai”
Audu ne (baban iliyah mijin Badariyyah),wanda shine mai raba cacar yana tah juyata acikin hannunsa kafin yah raba,
“Shiyasa ni da kaganni nan,banason na ci bashi na mayar,dan ji nake kaman ana zarar hanjina”
Bayan angama rabawa ne,aka hau wasa,round din farko baban iliyah yah cinye wasa,tattare kudin yah farayi,yana washe baki tareda zuga kansa,
“Saini baban iliyah mijin Badariyyah,caca tah sanmu mun santa,nasars a jininmu take”
“Eh in ka gama kirarin saika kirgo kudina ka bani koh?”
Yana d’aga kansa sukayi ido hud’u da sameemah wanda take tsaye a kansa,kokarin maida kudin cikin aljihu yake burgu yayi Sauri ya warce kudin a hannunsa,
Haba sameemah ya zakiyimin haka,Wannan kudin…………”
“Yimin Shiru Dallah,kai burgu kirgamin kudin kaga nawane”
“Dubu bakwaine shugaba”
Mika masa hannu tayi tareda cewa,
“Miko sauran cikaton kudin?”
“Iyee na’am ni banida wasu kudin,haba ke kuwa,yah ina auren yayar ki dan kawai na ari bashinki ki dungamin irin wannan tijarar”
“An taba yimaka kaciyah tah biyu?”
“Kaciyah kuma?”
“Toh in baka daina nunani da yatsa ba saina yimaka kaciyah ta biyu yanzunnan,maza ka dauko kudia sauran dubu uku ka bani yanzunnan”
“Ni bani dasu kiyi hakuri,dan allah karki sakemin kaciyah,wallahi ta wanzamai akayimin mai kyau ,bana bukatar ta biyu”
“Toh shikenan,kai burgu ku bud’e gadon bayansa kuyi masa balli balli guda talatin,kowace nairah dubu balli balli goma”
Kowa a wajen dayaji mai za’ayiwa audu sai yacika wandonsa da iska yabar wajen,shikuwa haka suka danne shi yana ihu yana komai suka babballe bayansa da aska,
“Wayyyyyo wayyyyyo,dan Allah kiyi hakuri,wallahi zan baki kudinki wayyyoo”
“Mtswww aikiniki banza lokacin biyan kudin ai yah wuce,bari a gama maka kawai saika tafi gida,na yafe sauran dubu ukun ma,kaga yanzu ba zuwa caca sai an warke kuma😄😄😄😄😄”.
Nan suka tafi suka barshi yana ihu,saida yaji bayan yafara hucewa kafin yah lallaba yah tafi gida,Yana ihu yara suna binsa suna dariyah har yah shiga gida.
Tun daga bakin kofah da burgu ya sauketa a mashin takejin hayaniyah,amma da alamun ba na fad’a bane kaman yanda aka saba.

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤08❤

Tundaga daga tsakar gidan tayi arba dana miji mai kayan mata,yana ta wani rausaya kaman bishiyah.
Saida ya juyo kafin takula a she DAN LITI ne yayan bashari,wanda yanzu yah koma LITTY,da suna wanda rabonsa da gidan tun lokacin su sameemah suna shekara goma.
“Hay sister ya kike yah hidima”
“Wata harara ta watsa masa,tareda matsawa zata shige”
“Habadai y’ar uwa yah antynki tana miki magana kina wani shigewa kamar baki ganni ba,ni ba seemah bace bane”
Kare masa kallo tayi,yan da yah sha jan baki,ga hoda kaman zatayi magana,sai rausaya yake yana gyara attachment din dayake kansa wanda ya sakko har kafadarsa.
“Hmm kaine antyn nawa?”
“Eh mana kinyi mamaki ne ?”
“Ahah banyi mamaki ba,taya zanyi mamaki,amma kasani koma kai wayeh banason shishshigi ka fita a sabgata ,in kuma ba haka ba,ko kuma kana tantama ka tambayi y’an gidan suyi maka karatun zama dani in kuma ba hakaba,bazaka iyah jure hukuncina ba,in kunne yaji jiki yah tsira”
Tana gama fad’a masa tayi hanyar dakinnasu,dan liti ne (littty)yah juya yana kallon y’an gidan wanda kowa kallonsa yake da mamaki.
Sameemah tana shiga dakin su,taga kayan mata,akwatina da kuma kayan shafe shafe,batayi mamaki ba ,sai ma abinda yakawota da tayi ta fice a dakin.
A hanyar kofah zata tafi tasake haduwa da shi har sannan yana tsaye a wajen,suna ta tad’i shida su matan gidan,dan yanzu kowa yasake dashi saboda kayan daya kawo ya raba musu,masu shaddodi da masu atampopi,kowa sai washe baki yake yana murna(hmmm mutane da san banza).
Dan litine yah kulada fitar sameemah,cikin sauri yah sha gabanta yana tattaro zanin shaddar dayasa,shi a dole ga mace,
“Haba y’ar uwa,yah daga shigowa kuma zaki fice,tun safe fah ban ganiki a gidannan ba,kuma yanzu kice fita zakiyi?,gaskiya hakan bai daceba,ace kina mace kina fitah”
Yah karisa maganar yana shafa fuska da hannunsa sannan kuma yana kifta ido,takaicine yah isheta ta kasa cemasa ma komai,
“Kasan Allah Idan nasake ganin ka shiga lamarina saina b’atamaka rai,sannan kuma kaje dakinmu ka debe kayanka dan dakin matane ba na gardawa ba”
“Tabbb kijimin karamar yarinya,me kike nufi ai naje dakin maza gardawa?,bazan iyah ba,dakin mata zan zauna yan uwana,dole mu zauna daku karkuji komai,ni banason harkar kauyanci da rashin wayewa ehhe”
“Toh shikenan Allah yabaka sa’a,zakuwa ka bawa wani labari”
Fita tayi da sauri dan ta tuna da zasuje ita da burgu wasu yan kato da gorah sun kama yaronta guda d’ayah yasaci akuyarsu a wani k’auyeh.
Wanene dan liti?
Ainihin sunansa shine Shu’aibu ana kiransa dan liti.
Tun yana saurayi yabi yan tafiyah neman kudi can kasar kudu onitcha,tun daga can yabi masu tuwo tuwo.
Shima kwanci tashi yanzu yazama mai zaman kansa dan yanzu yana da gidan tuwo tuwo har guda uku,gashi yazamana rikekken dan daudu,mai gidan kansa na karuwai da kawalai.
Sai wannan lokacin yaga damar zuwa gida bayan barinsa gida na tsawon shekaru,sanda yazo sunyi Mamakin yanda yazama,amma daga lokacin daya fara rabon kaya,sai kowa yah sake yana godiyah,inna karime kuwa sai washe baki ake yi,dan ita kadai saida ta tashi da turmin atamfa har guda goma,ka kuma mayuka da sabulai,ba abinda kkeji sai guda da yada habaici.
Da daddare a zaune suke ana ta hira kaman ba su ba,dan liti yabayar an siyo nama an dafa kowa yana ta ci,ana zazzare ido.
Mazan gidanne suka shigo kowa saida yayi turus ganin bakon al’amari a gidan,
“Ku wace macen ce tazo da mangariba haka?”
“Lah baba umaru nice fah litty ,baka ganeni bane”
“Lah ha I’ll ah,kai dan liti,dama kana nan,menene wannan din zan gani haka”
Shi ma kawu shehun uban gayyar kama baki yayi,haka sauran mazan gidan ma,
“Meka gani,sabon salone mun tuna gidane shine muka zo,kasan ance duk wanda yabar gida toh gida yan barshi,gwara mudinga tuna gida saboda wataran”
“Eh zaka tuna gida mana,saboda in an tashi kawoka sanda kafara kashin ajali koh?”
“Haba shehu wannan wane irin fata kake wa danka daka haifah,in bazakayi faran alkhairi ba kayi shiru”
Inna karima ta fada tana tafa cinyah ta cuno baki,itah a dole an zagi d’anta mai k’ashin arzik’i,
“Lallai karima idonki yah rufe yanzu wannan ne d’an? Yanzu zai tattara yabar gidannan basai anjima na karya jawo mana abin magana,muji da wadda ta baibayemu ma yanzu”
“Oh Toh bishiyah ka gani?,kana ganin kayan arzikin dayah kawomin ,idan aka tara abinda kamin tun aurenmu bazai kai hakanba,zancen yabar gidannan kuma babu shi,in abun magana ne ai akwai wanda suka fishi abun magana ma,menene bamuda shi a gidannan,tundaga kan yan fashi,da yan daba,harda yan shaye shaye,toh babu inda zaije,kaima ai bana allah bane,ai kawai ayi sha’anine wai na birni ya cuci na kauye”
Kowa shiru yayi jin abinda uwar dan liti tace,wanda yaga dama yayi addu’a allah yah shirya wanda yaga dama kuma yah yi shiru ya bisu da hmmmm.
Baba kamulune yah shiga kofarsa inda yasamu amaryarsa wanda bai dade da aurota ba dan itah d’anta d’aya ,kuma jinjirine,uwar gidance hauwa mai y’ay’a guda goma,
“Baban su mustapha sannu da shigowa”
“Yawwa Sannu,Ina yayartaki ne,kiramin itah”
“Ohh ta zagaya bandaki bari tah fito”
Suna cikin magana kuwa saiga ta ta fito da buta a hannunta,
“Menene yafaru baban mustapha?”
“Hmm Ku bakujiba kenan,wai dan litine yadawo yazama babban dan daudu yan nan yana raba shaddodi da atamfa ,yayah shehu zai koreshi karima ta hanashi”
“Toh wata sabuwa kenan,allah yah shiryah”
“Ameen dan annabi”
“Ina su mustapha kuwa,yayinsu nagani a masallaci shi ban ganshiba”
“Hmm mustapha suna d’aki da fitila ta tunda dare yah farayi,wai malamar makarantar safece ta bada assignment kuma gobe zata karba shine sukeyi,tun yamma suke abu d’aya ,wai ance duka ne da itah sosai,ni gaskiya ma har karatun ya fita a kaina bakaga fah yanda suka tashi hankalinsuba kamar ba suba,aka ma d’an mutum a yita duka kaman jaki”
“Hmm matsalar damuke fama da ita kenan,allah yah kawomu zamanin da y’ay’a suke samun d’aurin gindi daga wajen iyayensu,yanzu mahaifah sun zama agwagi sai yanda d’a yakeso shi zasuyi,yaushe toh za’a gyara tarbiyyahr yara idan kowa yah boye laifinnasa d’an kuma yanaso ya fad’i laifin d’an wani.
Toh ki kiyayeni da zancen hanasu zuwa makaranta,wata rana ai sai labari,kin fison su zauna a gidan su zama irin sauran yaran koh?su da karnuka babu banbanci? Ko bayan raina ban yadda y’ay’a na su tashi sakaka ba babu nunawa yaro dadai kaman goyon gwauro”
“Shikenan malam amma da zuwa kayi kace a rage dukan yayi yawa”
“Ba inda zanje bazaki bar zancen nan ba koh?,maza ni shiga ciki ki dauko min tuwona,yunwa nake ji”
“Allah yah huci zuciyarka malam”
“Ameen”
Sai can wajen goman dare sameemah tah dawo daga yawonta,kowa yah shiga kofarsa bayan an gama shagalin cin Kayan dad’i Wanda litty yah kawo,tun daga baki kofar dakinnasu takejin shewa ana rangad’a gud’a kamar za a kai amaryah,dan liti ta samu a bakin gadonta a zaune ,sauran yan matan kuma wanda suke nan,suna zaune sun bashi duk hanlalinsu yana tsara musu yanda harkar jin dad’i take ,da kuma abubuwan da mace zatayi ta haska a dunga yayinta,sameerah ceh cikin jin dad’in bayanin da dan liti yayi tai caraf tace,
“Banza muke tah bulayi bara a kufai,ashe ga dan uwanmu nan yasan dawar garin koh yah kikace salmah?”
“Hakane kam ,ai zamu faso said dai kiji ana labarinmu”
“Eh Toh naji kuna so ku haska,amma bazamu shiryah ba idan kuna kirana da d’an uwanku,ku kirani da litty koh kuma sister,yanzudai ku gyaramin wajen kwanciyah said gobe muga yanda za’ayi,ke kuma miye kike tsayeh tunda kika shigo”
Dukkan su juyawa sukayi suna kallon sameemah wanda tayi tsayuwar sojoji ganin abinda yake wanzuwa a dakin,tab’e baki sukayi had’e da cewa,
“babu ruwanka da itah litty,wannan y’ar bakin cikice,bari mu gyara maka shimfid’in shema’u tunda bata nan satinta d’aya da tafiya har yanzu bata dawoba”
Har suka gyarawa dan liti wajen kwana sameemah tana zaune batace musu komai ba saima waya da take yi,kuma a wajen shema’un shine a kusada da itah,dan duk dakin tafi kowa saukin kai da daukar komai ba komai ba,yanzuma ta tafi garin su mamartane wanda bata gidan saboda an basu hutun makaranta,itah kad’ai ceh sameemah take yiwa maganar arziki itah ma kuma ta d’au sameemah tamkar y’ar uwarta ta jini,babu ruwanta da su salma wanda suke uba d’ayah.
Saida sameemah tah bari dare yayi sosai,tah gama abinda take,tana wajen tsakar gidan tana jan wiwi a kwarkwaro,saida ta tabbatar tah dau caji mai kyau,tana jinta a can kololuwar sama,inda babu wani shegen daya kaita kafin tah koma d’akinnasu.
Saida tah kare musu kallo,kowa ta kula da irin kwanciyar da yayi,kafin tah fito da wata zambad’ed’iyar bulala wanda tah bawa burgu aike yah kawo mata daga gidan horo.
Kakkad’ata tayi tak’ara juyata,kafin tayi wani Murmushin gefen baki na mugunta,

D’agawa tayi iyah karfinta kafin tah shek’awa dan liti wannan bulalar a gadon bayansa,wata irin mika yayi tareda mikewa tsaye yana k’andarewa,
” Shshshs, yimin shiru kuma kayi kneel down,idan kuma ba hakaba wallahi zansa karnukan nan suyi tah yagar naman jikinka”
Dan liti yana had’a ido da karnukan masu jajayen idanu wanda duhun dare yasa yake ganinsu kamar kurayeh.
Yawu yah hadiye mukut kafin yayi yanda tace,
Kara d’agawa tayi tah zambad’a masa iyah karfinta,lokacin data sauke masa tah uku kasa zama yayi ,dan azaba bai san sanda yah dungura ba yana kikkifta ido😂😂😂,(ga mari ga tsinka jaka,@rahama zo ki cece shi keda @chuchu,uhm irin su umma najma kam bazata iyah zuwaba).
Jambad’a masa bulalar take tayi gashi ta hanashi kuka ko kad’an ,ganin zata kasheshi kwanansa bai kareba ne,yasa shi takarkara ya zunduma wani uban ihu tun daga mak’oshinsa irin na ainihin gardawan nan (shege ashe yasan shidin na mijine).
Su sameerah ne suka tashi a firgice wanda ba iyah su ba ma duk yan gidan ma babu wanda baiji ihun dan liti ba saboda yanayin dare.
Samunsa sukayi a zaune sai karkarwa yake ya had’a gumi shirkif kaman anyi masa wanka da ruwa.
Ta shi sameerah tayi zata bar dakin domin kiran wani a cikin gidan,saidai cak ta tsayah daga dorah kafafunta a bakin fita daga d’akin,saboda wani mugun gargad’i da sameemah tah antaya mata,
“Kina fita daga dakinnan zaki zo kema ko jone dashi ,dan duk wanda ta min shshshigi da itah zan had’a”
Tofahhhh

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤09❤

Dukan tsiyah sameemah tayi wa dan liti,tun yana kuka a cikin d’aki har suka fito waje amma bata bar dukansa ba,kowa fitowa yayi dan ganin mai yake faruwa kaman ba dareba,
“Zaka sake Shiga dakin mata ka kwanta?”
“Ahah bazan sake ba kiyimin rai na tuba”
Tsayawa tayi da dukan ,wanda cikin daga muryah inna karima ta fara magana,
“Ehhh lallai yau kam abin yayi yawa,dan tsabar rashin mutunci daga shiga daki saiki masa wannan aika aikar,dan kawai kinga kashin arzikin da uwarki har ta mutu bata samuba koh?,toh bazan yadda da wannan rashin mutuncin ba kuma………..”
Tun bata rufe bakiba sameemah tasake zabga masa bulalar,tana sake magana ta kara sake zuba masa ita,ganin hakanne yasa inna karima tsuke bakinta tayi shiru,saidai takaici na duniya yah isheta,
“Keh karima kike ko ma waye?har yanzu bakisan halina ba koh?,a gabanki dazu da yamma nayi masa kashedin ya dauke kayansa a d’akinmu amma yayi kunnen uwar shegu da ni,ke kuma da kikasan abinda zan iya aikatawa idan na tarar bai d’aukeba kika kasa jamasa kunne.
Sannan na dawo nasameshi a dakinmu kuma ma saboda tsabar raini a kusa da gadona wa’ennan shashashan mutanennan suka yi masa shimfidi koh,ba laifinku bane ,laifina ne da na ke daga muku kafa.
Toh bari kuji billahillazi daga yau idan nasake kafa doka wani yah karyah ta a gidannan hmmmm,yayi kuka da Kansa koda kuwa bak’one idan yazo a sanar dashi.
Kai kuma”
Tafad’a tana kallon dan liti,
“Iye na’am ina jikinki madam”
“Idan nasake kamaka a hanyar dakinmu saina cire maka kafa guda d’ayah,kai koh a cikin gidannan na shigo naganka da kayan mata kana zaune a cikin mata ,saina yi maka hukuncin dayafi wannan,ku kuma zamu hadu daku ,zakusan kun sauke gardi a dakin danake kwana”
“Naji Ranki ya Dade kuma inshaallah bazan sake ba ,nidai karki sakemin irin wannan hukuncin,ni gobema zan bi motar sassafe na bar garin bazaki sake ganina ba”
“Yadai fi maka”
Kowa juyawa yayi ya nufi wajen kwanciyasa aka bar dan liti a wajen yana kakkarwa ,karshe dai a wajen yah kwana.
Da safe kuwa kaman yanda dan liti yafada gari yana wayewa ya kama hanyar tasha bayan yayiwa kowa sallama,dan baya fatan sake gamuwa da irin wannan hukuncin da tunda uwarsa ta haifeshi ba’a taba masa yau gashi seemah jar wuyah tayi masa.
Saida aka shafe kusan kwana biyu wata fitinar bata sake kunno kai ba tun wacce akayi da daddare tsakanin dan liti da sameemah.

PORTHACOURT:SOLDIER’S BARRACK.

SALEEMAH ceh a zaune akan kujera tana chatting ta nad’e k’afa d’ayah kan daya kaman wata yar basarake.
Kyakykyawace ajin farko ga tana ji da ilimi da kuma matsayi,kowa a cikin barikin shayin wani abu ya had’ata dashi yake,dan ko fita zatayi sojojin da suke rakata sun ninka wanda suke raka mijinnata idan zata fitah.
Itah kadaice a wajen mahaifinta wanda shine General a duk gabad’ayah barikin,yataka matsayi da dama Sannan allah ya jarrabe shi da son yar tasa wanda yake jinta a cikin ransa,baya kaunar duk wani abu dazai tab’a farincikinta bare kuma lafiyar tah.
Tun lokacin da tah dawo daga karatunta a Germany,suka hadu da sameer yah kawo wasu document wajen mahaifinta,tun daga wannan ganin taji duk duniyah babu Wanda takeso saishi.
Har daki tasami mahaifinnata ta fad’amishi ,cikin kankanin lokaci General Musa Funtuwa,yah amince dan shima yah yaba da hankalin sameer din,saidai yanada zuciyah da kuma tsayayyan ra’ayi,amma indai kyan haline yasamu lambar yabo kaf barrack din akan haka.
Cikin kankanin lokaci yah kirah sameer yasanar dashi bukatarsa,da farko yace yah bashi d’an lokaci,amma daga baya yah amince saboda mutuncin general din a idonsa,sannan kuma duk da saleemah bata had’a dukkan abinda yakeso ba,tana da wasu abubuwan,dan itah din macece da bakowa zai kalleta ba baiji ta burgeshiba.
Bayan yah amincene soyayya ta fara kulluwa tsakanin saleemah da sameer duk da ba wasu cikakkun masoyah bane ,saidai kowa yana daraja lokacin kowa. Saidai soyayyar da saleemah takeyiwa sameer din a gaban kowa take nunawa har da kuwa iyayenta.
Saboda soyayyar daya ga tana yiwa sameer ne ya sashi d’aga matsayinsa zuwa major general sannan yah aura masa itah.
Lokacin da aka daurah aure,gida guda yah basu tareda colony na sojoji guda akasa a area gidannasu saboda tsaronta da kuma yi mata hidima.
Masu aikin cikin gida ma part guda aka waremusu,saidai duk wadda tazo aiki saleemah tah nuna batayimata ba ,a ranar ake sanja ta a dauko wata.
Masu kulada kayanta daban,masu kulada abinci daban,masu kula da sashenta daban haka masu kulada sashen mijinta su ma daban.
D’anta kuwa suna ta haifeshi ne,dan said tayi kwana uku bata ganshiba yana wajen nanny,ita kuma tana harkar gabanta.
Duk inda ka wuce ba sunan dayake tashi sai madam,shi kansa sameer bai isa yasaka ta abinda batayi niyyah ba,sai idan taga ransa yana baci kafin tah aikata abinda yah ce.
Mai shara ce ta zo goge palourn amma tana tsoron yiwa madam din magana saboda kar a koreta kaman yanda ake yiwa sauran.
Kulada itah saleemah tayi a tsaye kafin tace mata,
“Ke kuma miye kika wani make a can lumgu,kafin kifara sharar jeki waje duk sojan da kika gani kice ina san ganinsa yanzunan”
Cikin sauri kaman ana turata da iska tafita domin cika umarnin nata,koh minti uku batayiba said gata da wani soja sun shigo.
Saida ta gama abinda take a wayar kafin tace,”
“kuje kaida driver gidan kawata Surayyah zata baka sak’o ka kawomin,yanzunnan”
Saida yah sankame ta sara mata kafin yace,
“Yes madam”
Ta shi tayi ta koma daki dan bawa mai sharar daman gyara wajen.
Tana cikin sharar ne sameer yah shigo daga wajen aiki,babu kowa sai kawai mai sharar tana ta aikinta,
“Saleemah tana nan”
“Eh ranka yah dade yanzu tah shiga ciki”
Bai amsa mata ba said wucewa da yayi d’akin saleeman,nan ma saida yah jera sallama uku bata jishiba.
Samunta yayi tah kure wakar Alan walker,ga kuma chat tanayi.
Jin an fisge wayar tane,yasa ta saurin d’agowa tana kallon sameer din,cuna baki tayi kafin tace,
“Honey ka dawo neh?”
“Ba zancen honey bah,ki amsa gaisuwar danayi tukunna,koh kina so ki cemin bakiji sallamar ba?”
“Ahah ni banjiba”
“Toh yanzudai ba wannan ba ina abbana yake? Nasan sun dawo daga school tun d’azu”
“Nima ban ganshiba,amma ai sun dawo yana wajen su nanny d’insa”
“Wai saleemah anyah kuwa ke uwace ta gari,yanzu haka iyayenki suka miki,d’an ki haifeshi a cikinki amma kuna gida d’aya yah dawo a makaranta koh bai dawo ba ke baki saniba,sai chat da friend shi kika iyah kawai”
“Kai honey fad’anka yayi yawa kwana uku baka gida,kana dawowa babu hug din kayi missing dina ,sai fad’a”
Ficewa yayi yah tafi d’akinsa bayan yah mata kashedin ta d’auko masa yaronsa kafin yah fito.
A haka badan taso ba tah nufi sashen da nanny din farouq din suke.
A zaune tasameshi yana cin abinci har sunyi masa wanka,yana kallonta kuwa yah taho da gudu yana kiran mommy.
Tsugunnawa tayi ta rungumeshi itah kanta tana son d’annata saidai rashin halin kulawa irin nata kawai,
“Mommy tun d’azu na dawo daga school,kuma anty tace wai gobe zamu koma sabon clash”
“Eh hakane ya kk,ka gama cin abincinne?”
“Eh mommy ni bana son abin abincin tsami yake yi(mayonnaise) “
“Shikenan muje abbanka yadawo yana nemanka”
“Hee I mish abba”
“Okay toh muje”
Sanda ta koma sashennasu har yah fito daga bandaki da towel a kansa yah watsa ruwa,yana kallon yaronnasa yah mika masa hannu yana dariyah,
“Oyoyo abbana ya kake yah makaranta?”
“Fine abba,na dad’e ban ganka ba abba,sai yanzu”
“Eh my boy Abba yah tafi aikine,amma yanzu yah dawo,zamuyi wasa koh”
“Eh Abba “
“Yawwa Toh yanzu kaci abinci sosai”
Saida yah yatsina fuska irin ta yara kafin yace,
“Ni Abba bana son mayonnaise indomie zanci”
“Shikenan kije mommy ta baka koh”
Har suka gama firar saleemah na tsaye ta nad’e hannayenta tana kallonsa,saida ta ji an sakota a zancen tukun tah mikawa farouq hannu akan yazo su tafi,had’e fuska tayi kaman mai shirin fashewa itah a dole yana magana da farouq banda itah.
Bayan ta gama hidima da farouq dinne tah sake turashi sashen su nanny din,sai tsuka take itah a dole ta gaji da yi masa aiki.
Fitowa yayi daga dakin yasha kananan kaya amma na kakin sojoji,sosai ainihin yarintar sa yah ,tundaga fitowarsa saleemah tah kafeshi da ido ganin yanda kullum kaman kara kyau yake,shima yah kulada irin kallon da take masa saidai yasan inda kallon nata zai nufah wanda in akaje shi zata bari a ruwa.
Kujera yah ja ya zauna a wajen cin abincin,kafin ta tashi tah zuba masa abincin,bai yi wani murna dashi ba saboda yasan ba itah ce ta dafa masa ba da hamnunta,duk da yah dade bai dawo ba bazata iyah yi masa girkiba ko d’okin zuwansa saidai tayi ta masa korafin baya yimata soyayya yanda ya kamata.
Bai fi loma biyar yayi ba ,yah rufe abincin tareda cewa yah koshi,
“Haba honey Har ka koshi mai ma kaci toh”
“Shine cin,bari na fitah akwai dan aikin dazanyi saina dawo”
Rike rigarsa tayi tana masa shagwaba irin ta sakalan yarannan,dan dama ta kware tah wannan fannin,
“Uhm uhm shikenan daga dawowa sai kace zaka fitah,gaskiya yau gabadaya lokacina ne ,kuma kasan nafi bukatarka fiye da kowa yanzu”
“Saleemah ba dadewa zanyi ba ,in anjima zan dawo daga nan koma miye kisaka ni a gaba kiyi dani har zuwa gobe”
“Shikenan promise karka dade”
“Yeah I am sure”
“Okay bye “
Toh nima bye😍😍😍

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤10❤

Sai can wajen karfe 9:00pm,kafin sameer yadawo daga inda yacewa saleemah zaije,batare da tambayeshi mai ya faru ba kawai tah fara zazzaga masifa dama tah cika tayi famm ,dan tun dazu take jiransa a falo bayan tayi sallah.
Takaicin halinnata ne yasashi wucewa daki kawai batare da yabata karin bayani ba,itama bata huceba binsa dakin,sanda tah shigo yajuyah bayansa yana fitarda wani huci mai cike da bacin rai,saleemah bata kulada yanayin dayake cikiba tah cigaba da ta cigaba da mitar da take,
“Amma abban farouq dakai fah nake magana shine ka shareni ka shigo daki bayan kasan………..”
Katseta yayi daga karisa maganar sanadiyyar had’e bakinsu dayayi waje d’ayah,yah dad’e kafin yabata damar jan numfashi.
Fatar bakinta har saida tayi ja saboda farmakin daya kai mata cikin zafin nama,kallon idonta yake kafin ya fara magana kasa kasa,
“Dama ina abinda yasa kika damu na zauna a gidan kenan,sannan dana shigo ma kika fara fad’an na dad’e?,ba damuwarki rashin dawowa tah ba ko halin danake ciki,burin ki shine wannan,toh zo na baki”
Cikin halin ko inkula da maganar da yayi mata cikin salon maganar halinka mai sanda kuwa tah cafke bakinsa tareda maida martanin kiss din.
Sun dad’e a tsaye kafin suka isa ga kan gadon,saidai gogan cikin zafin nama daya kuma had’u da halin dayake ciki na baci rai yake kaiwa duk wani sassan jikinta farmaki.
Tun tana jurewa har tah matsa daga inda yake tah koma gefe tana sheshshsekar kuka,(dama su saleemah sakalai).
Shikuwa kansa yasaka acikin filo yana cije lebe tareda sauke ajiyar zuciyah,yah dad’e a haka shikadai yasan halin dayake ciki. Itah kuwa saleemah tun yana jin ajiyar zuciyarta har yah fara jin numfashinta yayi nauyi da alamun tayi bacci.
Tausayinta ne yakamashi,danshi kansa a sanin dayayi mata yasan bazata jure yanayin daya zo mata dashibagashi kuma tana dauke da yaran ciki,saidai shikansa yana tausayin kansa domin yasan koh kusa zaman su da saleemah bazai dore da haka ba,dole yah nema wa kansa mafita ,duk da yasan fitina yake shirin kunnowa,dan saleemah da d’anta ma kishi take ina kuma ga wata matar idan yah auro?(tabb hmmm).
Yah dad’e yana tah Tunani kafin yah tashi ya shiga bandaki.
Saida yah yi sallahr dare da addu’o’i kafin shima yah koma ya kwanta.
Da safe har sameer yah tashi yah gama shiryawa amma saleemah bata tashiba,kare mata kallo yayi da takaici kafin yace bayan ya bubbuka gefen filonta ta tashi,
“Wai kinyi sallahr dana tasheki kiyi da asuba kuwa”
“Eh nay I”
“Toh shikenan ni na tafi,sannan na manta ban fad’amiki ba,ki shiryah a cikin satinnan zamuyi tafiyah,zanje na gaida iyayena sannan kuma kakanmu alhaji babba bashida lafiyah”
Mitstsikewa idonta tayi tareda tashi zaune kaman ba itah ce take muryar bacci ba,
“Gidanku kuma?”
“Eh gidanmu menene a ciki?”
“Amma bazaka tafi kai kadai ba,kasan fah ni ba lafiyah ce dani ba”
“Tareda Ku zamu tafi dan nagama yanke hukunci,saboda tunda na aureki baki taba zuwa garinmu ba ka kuma farouq basu sanshiba yakamata na kaishi gidan kakanninsa yagansu”
Bai jira amsar dazata bashiba ya yi ficewarsa yabarta a kan gado baki a sake,
Tabdijan garinsu kuma,toh wata sabuwa(😂 yarinya zakije gidan gandu ki more).

GIDAN GANDU PALACE(na su princess sameemah😂)

Koh kwana biyu ba’ayi da tafiyar dan liti ba saiga shugaba MANJO yah diro garin.
Koh sallama babu said ganinsa sukayi a tsakar gidan yana zazzare ido kamar anyi masa kwalli da barkwano,kowa idan yah kalleshi sai yah karewa dress din jikinsa kallo.
Saboda wata biri da wando yasamu yah mamuk’a hantsar da matseshi ,kafafun rigar kuma a iyah gwiwarsa suke,ga kuma hular sanyi daya tabka,sannan ya goyi wata uwar jaka a baya.
A takaice dai kana kallonsa kaga mahaukaci sabon kamu,yaranne suka tafi da gudu suka kirah kulu a kofarta,da sauri ta fito jin ance manjo ya dawo har tana tuntube da gyara zaninta,turus tayi ganin irin shigar dayayi ga kowa sai dariyah yake kasa kasa,haushine yakamata ita da inna ramatu saboda daga gani babu wani abin arziki daya kawo,saida yah juyo ne kafin yah kulada kulun,
“Lah kulunkulun din manjo bakya ganin na dawo ne,babu wani dan tarba ta irin miji da matar nanne?”
Duk maganar cikin shakyakykyiyar muryah yake yin ta,ga bakinnan jawur dashi kaman bakin tsoho mai cin goro,tab’e baki tayi kafin tace’
‘Wannan shigar fah daga iyo ta me cece?”
“Lah wannan suwaga ce,suwaga ba ,ai irinta ake yayi”
“Mtswww Toh naji,saika shigo ai muji dame kuma ka dawo”
Binta yayi kaman rakumi da akala suka yi kofar tata,dan idan suna dad’i itah dashi tana juyashi yanda taga dama,saidai idan kwayar tagaya masa ba daidai ba kokuma tayi masa laifi ,toh ba iyah ita ba ko yan gidan sai sunsan an tab’oshi ,dan manjo shima number one ne wajen rashin mutunci,gashi bayan manta tsiyar da akayi masa a sauki.
Suna isa kofarsu manjo yah akiye jakarsa yah shiga bandaki ,kulu ta dau jakar tareda zazzageta a tsakar dakin,zare ido tayi gsnin abinda yake dauke a cikin jakar,ba komai bane sai wasu shafta shaftan silifas da kuma wani tsohon bargo sai kuma kayansa guda uku,har sun sanja kama dan daud’a.
Manjo yana shigowa dakin kulu tace,
“Wai uban me toh ka kawo duk tsawon dad’ewa dakayi da tafiya ranin iyee?”
“Uban me nakawo kaman yah?,tsaya wai kema uban me yasa kika zazzagemin jakata,har zaki wani sakani a gaba mai na kawo,uwarki na kawo,kulu billahillazi ki kiyayeni ,tunda na dawo kikemin masifa kaman wani d’anki,dan kinga ina muss(missing) dinki,toh wallahi zan ajiye muss din nayi miki duka,kinga saiki tunoni mu zauna lafiya”
“Eh zakace zaka dakeni mana saboda ga jaka,karyah nayi uban me ka kawo,naga jiya dan liti daya zo rabon shaddodi ya dungayi da atamfofi nima har turmi biyu aka bani “
“Ke dan yah rasulu,sheege toh ina tawa shaddar nasan yah bayar a ajiyemin kinga saina dunka in za’ayi daurin aure a gidan mudunga sakawa muna fitowa a manyan yayu,kuma baki isa kicemin an baki ki ajiyemin kice kin sayar ba,dan saikin fito da itah yanzunnan”
“Kutt lallai ma manjo wai wannan wane irin zance kake ne haka,toh ko yah baka ma bazan ajiyeba sayarwa zanyi barema babu wanda yah tuna da wata halitta wai itah manjo,dan koni saida akacemin ka shigo kafin na tuno da kai,saidai bansaniba koh inna ramatu ta tuna dakai”
“Kulu kulu tam”
“Menene? Dukana zakayi yanda ka saba?”
“Ahah bazan dakeki yau ba saidai inaga gobe kam saina yimiki lilis yanzudai debomim abinci tukunna,idan naci kuma saina zaga gari domin asan na dawo garin”
“Ni ban dafa komai ba,saika jira in an gama na dare na karbo maka”
“Ke Wai ina wancan shedaniyar yar wiwi dinne,tunda na dawo ban ganta ba”
“Me kake ci nabaka na zuba zaka ganta ai,tsab zaku zone,nida kwanaki sauran kadan tah cire min wuyah”
“Kehh wuyah dai batason kece matar manjo,lallai zata gamu dani”
Tunani kulu tayi da ta tuna cewa sameemah tah san sirrinta,aikuwa cikin sauri tace,
“Kai manjo da gangan nake fah irin wasan nanne”
“Aiko wasane sai nayi mata masu warning (last warning) saboda gaba”
Daga haka ya kad’a ya fice waje,gurin abokansa su sule maye.
Ring wayar sameemah tayi,tana tsaka da cin abinci wanda tabawa wani yaro a gidan yah sayo mata,dan sam harka da miyar kukanne bazata iyah ba sam,miyah babu wake ba bu ishshshen kayan miyah sai uwar kuka kaman zatayi magana,kana sakawa a bakinka kafi zabuwa(ajino moto )zai yi cuuu a bakinka kaman zaiyi magana.
Saida tayi tsuka kafin ta duba wayar dan ganin waye ya takura mata a lokacin,saida tah daga kafin taga ashe alhaji bala ne,yah mutsa fuska tayi kafin tace,
“Uhm inaji miye?”
“Haba sanyin zuciyata yah ina binki kina nuna min halin ko inkula,kinsan fah da arziki nake nemanki”
“Eh nasani shine nace menene yah faru yanzun”
“Inaso idan bazaki damuba gobe da kaman hantsi zan turo mota a daukeki zuwa gidan shakatawa ta saboda inada free lokaci goben kinga saimu wuni muna shakatawa,koh yah kika ce?”
“Eh naji idan na shiryah goben zanyi maka magana”
“Yawwa kefah komai naki na musamman ne………”
“Idan ka dameni zan fasa zuwa,dan ba’a lallamata kamar wata yar yarinya saboda abinda naga dama nakeyi,bana bin ra’ayin kowa”
“Shikenan gimbiya tah ai girmanki ne”
“Toh naki koma girman waye kai yah shafa ni ba matsala bace,sainaga driver naka goben”
“Shikenan,gaskiya naji dad’in amin………..”
Kittt ta katse kiran kafin yakai ga karisah maganar sa.
Yau ba wata tsiyah koh busa hayaki ,ciki yana dauka tabi lafiyar gado.
Can wajen tsakiyar dare sameemah tayi zumbur ta tashi daga kwancen da take,ga jikinta sai rawa yake,saida ta rike kanta ta dad’e haka kafin ta sau kan tana maida numfashi,komawa tayi ta kwanta tana kallon silin da haka har gari yah waye bata koma bacciba.
Kaman yanda sukayi da alhaji bala kuwa,can bayan rana tayi sameemah tah fesa wanka kafin tazo ta Zauna a gaban kayannata.
Tah dade tana nazari kafin tafito da wani material anyi masa dinkin roba dinnan,irin wanda yake bin jiki,ga adon duwatsu da aka baza a jikin dinki,a takaice dai dinkin ba karamin amsar jikinta yayi ba gashi kalar pink.
Takalmi tasaka shima pink din kafin ta daurah gyale shima pink akan kafadarta. Batayi wata kwalliyah mai yawa a fuskarta ba ,sai iyah dan lip gloss da tasaka kawai dakuma ruwan turare a jikinnata,ita kanta da ta kalli kanta a madubi saida tayi murmushi saboda kyawun da tayi.
Cingam ta zefah baki tareda toshewa fuska da bakin glass,sannan tah zari jakarta itama pink tayi waje.
Tundaga bakin dakinnasu ake karemata kallo ganin yanda tayi shiga kamar ta sauko a jirgi,tana fita kuwa idonta yayi tozali da wata zazzafar bakar motah a kofar gidannasu,tana isa gaban motar wani yah fito a motar yah bude mata kofah tah shiga kafin yah mayar yah rufe.
Fiiiiii suka figi motar suka hau titi,sai alamar kurar inda suka tashine kawai yah saurah.
Mutanen anguwa kowa yah bude baki yah rasa abincewa sai an lafah tukun kowa ya fadi albarkacin bakinsa.

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤11❤

” Kai kai isiyaku ka ga abinda nagani kuwa”
Mai shayin kofar gidannasu ne ya fada yana jijjiga kai,
“Hmm nikuwa nagani dan ma kai sanda ta fito daga cikin gidan baka gantaba kana sunkuye wajen tattara kofunan ka,
“Gaskiya kam wai haka tah koma ne,itah ma ta koma bin mazajen kenan”
“Kai amma ita bin mazannata mai aji takeyi ,ka kallifah irin motar da aka dauketa a ciki,aradu tunda nake ban taba ganin an dauki wata y’ar unguwar nan a irin wannan motar,kai motar fah ta zo matuka”
Manjone yah karkace kai bayan yagama shan shayinsa ya ajiye kofin,
“Kai Wai wa kuke magana ne,kaman fah wannan kanwartawa nagani wato jar wuyah,ko ba ita bace”
Sule mayene shima yah gyara zama kafin yace,
“It ah ce mana,kai bakaji nayi shiru ba ai haushine ya isheni,yanzu ina zaune a wajennan tasan ina matukar santa Amma ta tsallakeni tah shige wancar motar “
Saida manjo yah gama kyakyatawa da dariyah shida mutanen da suke wajen ,har yana shirin fadowa daga tebur din,
“Kaii Baaba dama san ta kakeyi,toh ai ni bansaniba”
“Sule mayene yasake turbune fuska ganin yanda suka sakashi a gaba suna dariyah kaman sun samu mahaukaci,
“Eh mana ai na dade ina sonta,kana ganin mace har mace,kuma ita ma nasan tana sona sosai”
“Toh AI lefinkane abokina ,kasan ni babban yayantane kuma ance babban yaya uba,mai yasa baka zo kasameni ka fad’amin ba”
“Kai kaji min mutum,dan iska kana garinne,basai jiyah muka ganka ka bayyana ba kaman tsohon aljani?”
“Toh dai naji d’an heeege kai ,kana neman abu a wajena kana zagina,yanzu dai ka bani sadakinta nairah dubu talatin,kuma bazan rageba daga nan,Sannan dole ka ringa gaisheni duk inda muka had’u,idan kuma wani rashin arziki yah had’amu dakai toh rufe ido zanyi na kuma manta da ka bani dubu talatin nayi maka rashin mutumci”
“Ba za’ayi hakaba indai akan seemah ne babu abinda bazan iyah ba”
Motar bata yi parking a ko inaba sai gidan shakata war alhaji bala,budewa kofar tayi tana karewa gidan kallo tareda zare glass din idontah.
Yaron alhajin daya kawota ne ya katseta da kallon gidan ta hanyar cewa,
“Nan zaki biyo madam”
“Binsa kawai tayi batace komaiba har suka iso parlorn alhaji bala din.
Yana zaune yah baje akan kujera iskar AC tana kad’ashi,yana kallonta yah tashi da sauri yana washe hakora,kaman ance masa yaci zab’en shugaban kasa,
“Lale lale da zuwan gimbiya sarautar mata,samu waje ki zauna,bari a kawo abin motsa baki,kai IDI maza a kawo abin mak’ulashe yanzunan”
“An gama ranka yah dad’e”
Da sauri idi ya fice daga parlorn,yayinda shi kuma uban gayyar wato Alhaji bala yah dawo kujerar da take kusa da wacce sameemah tah zauna”
“Kallonsa tayi cikin yahtsina fuska irin ta tattatun shu’uman matannan kafin tayi masa magana tana yin bubble da dank’on cingam din da yake bakinta,
“Alhaji ka damu akan nazo nazo,toh gashi nazo saika fadamin menene dalilinka na kirana,kana ta zancen shakatawa gidan rawa zamuje koh gidan shaye shaye”
“Ah kina zuwa gidan rawane da dakuma shaye shaye?”
Yah tambayeta da mamaki,
“Hmm lallai kai karamin dan akuyane a cikin awakin,ai inaga nafi sabuwar bishiyah lokacin damina rausaya,sannan fidda hayaki kuwa,koh itacen murhu bazai nuna mini fitarda hayaki ba”
Maganar da sameemah tayi masa ta bashi haushi amma haka yah murkushe ta yah hadiye kaman wanda tayi masa asiri.
“Toh shikenan barina kira idi tun baiyi nisa ba yah had’o miki da taba”
“Ahah mai kake nufi banasha cigarettes,wannan kayan saka mutum baki,saidai dulah,itama karka wahalar da kanka dan ba kowacce nakeso ba “
“Toh shikenan ranki yah dade,yanzu dai mekike bukata”
“Kai me make bukata dai?saboda kai ka damu nazo ba nice na ce zanzo ba,yanzudai ina bukatar shiga bandaki nuna min dakinnaka zan shiryah tukunna”
AI kuwa cikin rawar jiki har murmushi yake ya nuna masa dakinnasa,dan shi a ganinsa koh irin dabarunnan irin na mata zatayi kafin azo kan harka.
Wuceshi kwas kwas tayi ta nufi dakin,har tazo bude klfar zata shiga sai kuma tazuyo tana kallon alhaji bala,
“Am yawwa nace ba,karka kuskura ka biyoni ka jirani na fito dan ba dad’ewa zanyi ba”
Saida yayi dariya irin ta yan duniya kafin yace,
“Ahhhhh karki damu wane irin shigowa kuma,ai ki gama shirinki tsaff yanda zakiyi zam zam najini a sama tah bakwai”
Wani Murmushin gefen baki tayi masa kafin ta bude dakin ta shiga,tana jijjiga kai,alamun zaka ci ubanka.
Tah dan dad’e a d’akin saiga ta tafito,tana gyara zaman rigarta wadda ta tattare saboda matseta da tayi,cire gyalen kafad’arta tayi ta ajiyeshi a kusa da itah,Alhaji bala sai binta yakeyi da wani mayen kallo yana lashe baki.
Duk abinda yake tana kula dashi har yah bude soyayyar kazar da aka nannadeta a takadda,cirewa tsokar yayi daban dakuma kashin yah ware a gefensa sannan yah tura gabanta yana cewa,
“Bisimillah hajiyata kici iyah cinki”
Kiran sallah akeyi a cikin anguwar na azahar,sameemah ceh tah kalli alhaji bala bayan tah cika bakinta da naman kazar ta cinye,
“Alhaji bala bala zuwa masallacine naga kana zaune ana ta sallah”
“U hmm na’am oh wai sallah zanje,ke kuma idan kin gama saiki shiga ciki kiyi sallahr”
“Karka damu ni banayi ai”
“Eh me kike nufi yanzun dama kinsan kina cikin rashin sallah kuma baki fad’amin ba har kika zo?”
“Ba wannan nake nufiba sallahr ce dama banayi ,daga azumi sai azumi nake sallah a rayuwata saidai kuma idan ansakani dole,wanda ita ma idan inayi bana cewa komai,amma idan akan ra’ayin kaina ne bana yin sallah”
Cikin jin dad’in zancenta alhaji bala yah tuntsire da dariyah harda buga kafa yace,
“Kai kefah kin had’a abinda nakeso,kuma dama ke bakyayin sallahr kike cewa ni naje nayi,toh nima yau kam sallah nayi mata yajin aiki,kinga idan muka shiga daga ciki bazamu fitoba har sai duhu yakawo kai ,koya kikace?”
Bata kulashi ba duk surun dayake yi saima antaya naman kazarta da take tayi ,saida taci tayi nak kafin tace masa,
“Zuba min lemon na Kora da sanyinsa kar yah huce”
“Hooo Bari a zuba miki lemo kisha kam,saboda kiji dad’in hawa service,nima ai na koshi da naman tunda kin koshi”
Kofi biyu yah fitar masu glass sabi fill a leda kafin yah zuba lemon a ciki,wasu kwayoyi ya d’akko da niyyar zubawa a cikin lemu kan,sameemah ceh tayi saurin dakatar dashi tah hanyar cewa,
“Ahah karka sakamin kwayoyin karin sha’awa”
“Ah ashe kin sansu kenan?”
“Me ka daukeni karamar yar iska?”
“Ahah nibance haka na,tunda bakya so shikenan,da alama yanda kike da karfinnan haka kike idan an hau gado”
“Eh ina ga kam,kai idan kanaso ma zaka iyah juye nawa kwayoyin ma akan naka,nafijin energy idan banyi amfani dasu ba”
“Hahaha ayi haka,kice nakara duk akan nawa danna
jini a sama kenan,ku ai yarane nikuwa saida su kwayar idan inason yin dogon aiki wanda zai d’auki lokaci,toh bari najuye su ma dukka kawai”
Aikuwa yana gama magana yajuye dukka kwayoyin sameemah acikin nasa lemon.
Yana dagawa saida ya shanye tas kafin yah ajiye kofin yana karewa SAMEEMAh kallo kaman zai cinyeta d’anya.
Saida tasha lemon ta tabbatar tah koshi sosai kafin ta dan kishingide akan cushion din kujerar,alhaji bala ne yayi saurin cewa,
“Haba madam da girmanki ki kwanta akan kujera,ai muje daki ki baje sosai ,amma kya kwanta akan kujera”
Batayi masa musu ba sai tashi kawai da tayi ta nufi cikin dakin,kaman jira kuwa yake da sauri yah bita yana had’a hanya kaman dan maye.
Tana zama a bakin gadon shima yah zauna yana narai narai da ido kaman anyiwa yaro kwacen alewa,ga idonsa yayi ja da alamun kwayar da yayiwa over dose ce tah fara tambayar sa.
“Menene yasa ka kirani nan wajen ,har yanzu baka ban amsata ba bayan tun dazu nake tambayarka?”
Ransa ne yah fara b’aci da tambayar ta ganin yanda tah ma raina masa hankali,cikin bacin rai yace,
“Bai kamata kina min haka ba seemah dan kinga ina binki ina lallabaki,ke kanki ba buk’uwace ba a wannan harkar kin fi kowa sanin abinda nake bukata daga wajen ki,tunda a gabanki na sha kwayoyin karin kuzari “
“Toh Idan kuma naki baka abinda kake nema kuma yah zakayi?”
“Hakanma bazai faruba dan nasan bazaki taba fadan hakan ba tunda kema da amincewarki za’ayi”
“Haka nace maka da amimcewata ?”
“Kee yakamata kima daina batamin lokaci dan baki isa kicemin kin fasaba saboda yanda na bata lokacina wajen lallamarki da kuma naman dana sayo,sannan kuma idan baki shirya ba saiki fadamin yunda farko ,amma kina ganin na sha kwaya a gabanki amma bakice komai ba sai yanzu kicemin wai idan kika ki yarda mezai faru?”
“Eh Toh mezai faru idan naki amincewar,ai tambaya ce nayi maka”
“Matseki zanyi nayi miki dole dan in kinki ta dad’i saka miki karfin maza zanyi tunda yan dabar taki basanan bare su kwaceki,Sannan kuma bazan baki koh sisi ba haka zan koreki a gidannan,inaga yarinyah bakisan halina ba ne,toh bari kiji na fadamiki a gidanna bansan iyah adadin yara nawa nayiwa fyade ba ,ko kuma na lalata,dukkansu kuma babu wanda nayi mata a san ranta,ke kadaice nake binki dan nayi miki da yardarki saboda bakaramin sonki nake ba,in kikayi sa’a ma harka ta goge dake zan dunga zuwa abuja”
“Duk naji bayanin ka amma ban amince ba”
“AI kuwa baki isaba yarinyah”
Yana gama fadar haka yayi sauri yah riko kunkuminta yah jawota kusa da shi. Bai ankara ba kuwa saijin mari yayi tasss a kumatunsa saida yah fad’a kan gadon tah baya yana kikkifta ido,saboda hasken ganinsa daya d’auke na wucin gadi.
Tashi tayi daga kan gadon tah koma jikin madubin dakin tah tsaya wanda yake kallon gadon,tsura masa ido tayi har yah gama juyinsa akan gadon yah tashi ya zauna,yana had’a ido da ita ya hadiye wani yawu tareda cewa,
“Kai kai dutsin guga kika manna min a fuska ko me”
“Au tambaya ma kake,zaka kuwa san me na manna mama,kuma kayi kuskure tabbas ka tsokano rina a gidanta,dan kayi min abinda tunda nake babu wanda yah taba gigin yinsa ,shine tab’a gangar jikina,duk duniyah babu wanda zanyiwa amincewar taba jikina,ba miji ba koh mai martaba ne bai isaba,saboda jikina ne nikadai kuma nikadai ce mallakinsa.
Kai kuma ka sab’a dokata dan haka a hukuncin danayi niyyar zartarwa akanka na rainani dakayi ta hanyar gayyatoni wannan matsiyacin gidan,saina k’ara maka da tab’a jikina ma dakayi,yau mai hanani hukuntaka a gidannan banganshiba a fad’in duniyar nan”
Tana magana muryarta tana fita da amo kamar muryah guda biyu ga kuma annurin fuskarta daya d’auke tass.
Tun kafin aje ko ina alhaji bala ya sau fitsari akan gadonnasa,ga jaraba tana cinsa na maganin daya antaya a cikinsa.
😄😄😄😄😄
Tab kashigesun ka (su alhazawa anji manyan mata).

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤12❤

Nufoshi tayi yana matsawa har sukaje karshen gadon,a lokacin jikinsa har karkarwa yake saboda tsoronta daya d’arsu a cikin zuciyarsa,dan a sannan koh qur’ani aka bashi zai iyah rantsewa akan ba sameemah daya sani wacce yah saka aka kawota bace a gabansa,duk da suna kama da itah saidai kamanninta sunsha banban da itah.
Wani marin tasake kifah masa ,saidah tah jerah masa kusan biyar,kan kace me kumatun alhaji bala sunyi luhu luhu kaman fanke sai shek’i sukeyi saboda kumbura da sukayi.
Tun yana daurewa har yah fara kuka wiwiwi harda majina shab’e shab’e. Komawa tayi inda take tsaye saidai sannan tah koma ainihin kalar ta,wani Murmushin tayi masa irin na muguntar nan kafin tace,
“Karka damu mucigaba daga inda muka tsaya a maganarmu,wannan hukuncin tab’a jikina dakayine na maka”
“Yanzu menene sunan abinda kikamin ina nemanki da arziki kina nemana da tsiya?”
“Yawwa gwanda da kace kana nemana da arziki ai haka nakeso Alhaji,kai ne shugaban kungiyar vigilantee na garinnan koh?”
“Eh nine amma bazan had’aki dasuba ai”
“Oh kana nufin cewa zanyi karka saka su su kamani?,lallai baka sanniba ina ga so kake na k’ara maka wani marin”
“Ahah kiyi hakuri na tuba ki yafeni”
“Kai Dallah ni kadaina wani rokona haka,sai kace wani sarki da bafade,so na ke shugaban kungiyar ka d’orani akai,zan baka nan da wata d’ayah daga nan bazan k’ara koh kwana d’aya ba,sannan yarana ma zan nad’aasu mufara aiki tare,dan garinnan yana bukatar gyara sosai,kuma na duba naga babu mai gyarashi sai ni nan jar wuyah”
Watstsakewa yayi daga marin da tayi masa yah yah gyara zama kafin yace,
“Lallai na yarda ke yarinya ce,yanzu marin dakika yimin ne kike tunanin zai sa na sauke yarona dayake kan shugaban kungiya na baki,kinsan irin wuyar dana sha kafin na kafa wannan kungiyar zuwa yanzu,lallai da sauran ki”
“Babu saurana alhaji kungiya kuma dole saika bani idan kuma ba hakaba zaka ga aikin yarinta kaman yanda kafad’a”
Tana gama fadar hakan ta matsa wajen television dinsa tah ciro wata y’ar karamar camera wanda duk nacin mutum bazai san da ita ba inba yasan sanda aka saka ba.
Zuwa tayi gaban alhaji bala tah tsugunna,
“Nasan kasan menene wannan ba sai nayi maka karin bayani ba ,kuma kasan wacece hajiyah kulu,(matarsa) dakuma wannan saurayin umaruje(babban d’ansa wanda yake karatu a UK),toh cikin minti talatin sakon dayake cikin nan zaije ga kunnensu ,sannan bayan sun gama ji sun more,saikuma mutanene garinnan suma su shaida wanene alhaji bala,ko ban tuna maka ba ,kasan wane irin fad’e fad’e kayi a dakinnan koh?,toh maza saka hannu a cikin takardar nan”
Tafad’a tana mika masa wata takarda,tsilli tsilli yayi da ido,ganin irin ruwan daya d’ebowa Kansas babu damar kuma fita daga ciki.
Mika hannu yayi yah karb’i takardar hannunta amma daga nan ko motsi bai sake yi ba kaman wanda aka sankare shi.
“Oh Ashe ban baka biro ba,bari nabaka”
Tafad’a tana mika masa biro,ya dad’e kafin yah karbi biron yah fara rubutawa kaman mai koyon rubutun,
Yana gamawa yah mika mata takarda fuskarsa d’auke da dana sani,fisgewa tayi tareda sake dubawa,
“Yawwa yaron kirki ashe kana jin warning,yanzu kuma saikayi shirye-shiryen d’orani saboda jama’ar gari su shaida,ko baka jiba?”
“Eh naji”
“Yawwa mutumina,ashe kasan abinda kakeyi,kuma yawwa bari na fadamaka,motar da aka kawoni d’azu gaskiya akwai dadi,kuma ta birgeni,dan haka da itah zan tafi ina sonta”
Alhaji bala bai san sanda hawayen takaici yah zubo masa a fuska,saboda tsabar irin fashin da sameemah tayi masa tunda yake a duniyah ba’a taba yimasa ba,ga kuma babu damar yayi magana.
Itah kuwa gogar key d’in motar ta d’auka akan kujera a palour,tah fita tana kakkad’ashi tana fed’uwa har ta bawa motar wuta tayi gaba abinda kaman babu abinda ta aikata.
Bayan fitar sameemah Alhaji bala ya dade a zaune bai motsaba ,can kuma yah kokarta yah tashi yana tafe yana had’a hanya gakuma rashin arzikin da sameemah tayi masa.
Itah kuwa gogar daga wajen gidan shakatawa ta wuce(club)inda kowane d’an iska yake baje nasa bidirin.
Tun a hanyah tah fad’awa su burgu akan su sameta acan,da murnar su suka isa wajen kuwa dan sunsan baza’a tashi banzaba.
A tare suka iso wajen su da itah,saidai sai waigawa suke koh zasu ganta amma babu wanda yah hangota,ita kuwa a nata bangaren tana kallon su daga cikin motar da take zaune,saida taga alamar bazasu gantaba kafin tah bud’e motar tah fito,da mamaki suke kallonta bakinsu a bud’e,burgu ne yayi karfin halin cewa,
“Shugaba jar wuyah wannan motarfah daga ina kika samotah,ta wayeh haka?”
“Tawa ce”
Daga nan bata sake cewa komaiba sai wucewa da tayi cikin club d’in suma suka bita a baya.
Shirya musu table akayi ita da yaranta kafin aka tambayi order,kowa shiru yayi yana jiran shugabar ta fad’i abinda takeso,d’aga yatsunta tayi sama tai kyass dasu kafin tace,
“Ki kawomin ruwa mai sanyi kawai,su kuma kowa ki kawo masa abinda ransa yake so”
“Sai ogahhhh suka fad’a cikin jin dad’i”
Kafin kowa yah fadi wane irin kayan maye yakeso.
Bayan an kawone kowa yah fara hawa caji,kafin sameemah ta kallesu d’aya bayna d’aya tana wani linshe ido kaman wanda akewa tausa,ajiye kofin ruwan sanyin tayi kafin tace,
“Kusha iyah shanku,daga yau duk kun daina shaye shaye”
Kallonta sukayi a zabure cike da Mamakin abinda ta ce,
“Eh Ai nasan kunjini,shaye shaye is enough from now,do you hear me”
“Kowa kallonta yayi kamar ba itah ba,jin yanda take turanci kaman wata yar gidan mongopark,
“Daga yau duk gyaraku zanyi na d’ora ku a hanyar gaskiya,saboda iyayenku basa son abinda kukeyi,kuma nayi tunanin dan inaso nayi iskancina bai kamata nasaka ku acikiba,bayan wannan shaye shayen dakuke zai iyah tab’a hankalinku dan na kula ni kuke biyewa bayan nidaku ba d’ayah bane.
Saboda haka wani watan zan zama shugabar kungiyar vigilantee na garinan,dukkan ku zan d’aukeku aiki,saidai bazan hana kowa yin muguntar daya ga dama na,amma shaye shaye na hanaku daga yau,ni kadai zan dungayi banda ku,saboda zai iyah yimuku illah.
Dan haka kowa yaje yah shirya kafin zuwa nan da wani watan,zaku tayani fara aikin rashin mutunci a garinnan,dan nakula kowa yah rainani,tun daga kan yan gidanmu har kan yan gari saina saita su na gyarawa kowa zamansa.
Da fari sun ji babu dad’i data hanasu shaye shaye,amma daga baya da sukaji zasu sami aikin vigilantee kuma kowa zai yi tsiyarsa yanda yaga dama ba mai hanashi,ai suka fara ihu,kowa yana tunanin wace irin mugunta zai shuka a garin saboda ya kafa tarihi.(Allah dai yah kaimu lokacin)
Suna cikin ihunsu ne,itakuma sameemah tana zaune kaman wata mai hankali tana jinsu,wasu y’an matane suka zo wajen table dinnasu guda biyu,sunyi shiga irin ta bariki amma daga ganinsu kasan bakaraman gogaggu bane a harka tsiyah,wani rausaya sukayi tareda sauke muryah kafin sukace,
“Uhm idan bazaki damuba seemah jar wuyah muna san muyi magana dake”
“Ku fad’i miye ina jinku”
“Am da mundan fita waje saboda yanayin hayaniyar wajennan da kuma gamu a gaban maza,sannan maganar mai muhimmanci ce”
Har su burgu sun hayyak’o zasu fara masifa ,sameemah tah dakatar dasu tareda cewa,
“Ahah ban as on hayaniyah,ku kuma ina kukeson muje muyi maganar?”
“Akwai wani lungu ta bayan gurinnan inaga muje can,saboda nan babu kowa”
Burgune ya hararesu kafin yace,
“Gaskiya shugaba bai kamata ki bisu ba ,ni kawai daga ganinsi naji ban yadda dasuba gaskiya”
“Kai ne gaba dani koh nice shugaba?”
“Kece shugaba”
“Toh bance kasake shiga maganar nan ba,sannan kar kowa yah biyoni ku gama abinda kuke ku tafi gidanku”
Tana gama fadin hakan ta tashi ta bi bayan matan suka bar wajen.
Saida sukayi tafiya mai nisa amma babu wanda yah ce komai daga itah harsu,dan a yanzu sun bar wajen hasken club d’in sun fara shiga cikin duhu,tsayawa tayi tana karemusu kallo,yayinda suma itah suke kallon ganin ta tsayah,murmushi tayi tareda kama kunkumi ta gyara tsayuwarta,
“Wai har yanzu bamu iso gun wanda suka aiko kun ba,koh suna tsorone basu fitoba,yanzu kam ai munfita a cikin haske,kafar mutane ta d’auke a wajen ,duk abinda zasumin ma babu wanda zaiji su”
Zaro ido matan sukayi da Mamakin yah akayi tasan abinda suke niyyar aikatawa,kallon kanannan yara tsyimusu kafin tak’ara da cewa,
“Lallai Ku yarane,a tunanin ku bansan me kuke nufi ba,toh tun a hanya nakulada ku kuna bibiyata,har na shiga club din kuma kuka kama table,bayan kunyi waya da wanda yasakaku kafin kuka nufo inda nake”.
Fezar da iska tayi daga bakinta irin na takaicinnan sannan ta d’ora da cewa,
“Lallai wanda yah aikoku bai sanni ba har yanzu,ku kuma ba laifinku bane,amma idan muka gama da wannan cakwakiyar ku tabbatar kunnemi inda nake kunzo ,domin inason yin magana daku”
Bata gama maganar ba tajiyo karar fed’uwa a bayanta anabin kid’an wakar naira maley,koh kuyawa batayiba har me wakar yah zo ta gaban ta,da wata wuk’a a hannunsa ya sak’alata a wuyansa.
“Yau wata tazo hannu babu yaranta,ina dasu kike takama har kika aikatawa shugaba haka(buba jini).Toh yau saidai uwarki ta haifi wata,dan saimun farke cikinki mun cikashi da kasa,mun jefar a hanyar dabbobi”
Duk maganar cikin larabci yakeyi irin na sudan,dan shikansa mutumin baiyi kama da mutanen nijeria ba.
Farine sol yahsha rawani ,amma koh a duhu mutum yah ganshi yasan ba karamin tantiri bane.
Wani ne daga cikin mutanensa yah matso kusa da itah tareda fassara mata abinda ogannasa yace,saidai har yah gama fassarar babu alamar tsoro a fuskar sameemah,dan ko motsawa batayiba daga inda take.
Mutumin ne yah kalli yaronnasa tareda tambayar,
“Ka fassara mata duk abinda nace kuwa?(yah kara fa’da cikin harshen larabcin)”
“Eh shugaba dukka na fassara mata”
Fusata yayi da yanda tah wani tsaya babu alamar tsoronsa,bayan duk kasar dayaje kowa tsoronsa yake,cikin zafin nama yah d’aga wukar hannunsa yah shaftawa sameemah a hannunta na hagun inda rigarta bai rufeba,wanda kuma yayi dadai da isowar su burgu wajen da gudu.
Ihuu suka fasa dukkansu ganin abinda akayiwa shigabar tasu,burgune yah isa wajenta da sauri,saidai tsayawa yayi cakk a gabanta yana karewa wajen da’aka yanketa ido,jijjiga kansa yayi tareda murza idonsa,anya kuwa yah gani dadai,saidai lokacin daya d’ago idonsa yah kalli Mamakin dayake kan fuskar kowa har shikansa wanda yayi aika aikar sai hakan ya tabbatar masa da abinda yah gani gaskiyah ne ba gizo idonsa yayi masa ba.
Wajen da aka yanki sameemah ne yake komawa yana had’ewa dakansa,kaman yankan wuk’a bai tab’a wanzuwa a wajen ba,shikansa jinin daya fito a wajen k’onewa yayi ya b’ace b’atttt.😲😲😲.

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤13❤

Ganin kallon da burgu yake mata yah isheta ne yasa ta tureshi daga kusa da itah kafin tace,
“Kai miye kazo kusadani har haka kaman zan maida ka cikina,wato dana ce karkuzo saida kuka biyoni koh,banzaye taron matsorata,ji idonku kaman kunga aljani da tsakar dare”
Har tagama masifarta bayan ta tureshi bai ko motsaba,saima kallonta yakeyi kaman yah samu hoto.
Wuceshi tayi taje har gaban shugaban,wiwi din da take hannunsa tah karb’a saida tayi masa zuk’a mai kyau kafin ta fesar tah hanci da baki,jefarta tayi take a kasa kafin ta mayar masa da martanin maganar da yayi mata cikin harshen larabcin da babu inda akeyinsa sai ainihin cikin kasashen larabawa.
“Oh da kana tunanin banajinka d’azu koh,hmmm lallai kana cikin duhu a gameda sanin koh ni wacece,saidai yanzu zan nuna maka wani misali”
Tana gama fad’ar hakan tayi masa ruk’o tareda kafa hakoranta a akan wuyansa,babu wanda yasan mai yah faru sai ganin sa sukayi dukka yah fad’i a kasa kaman wanda yah mutu.
Kare masa kallo tayi tana goge jinin dayake bakinta,tana kuma tofar da yawu,
“Ka tursasani yin abinda banida niyyah,ku kaishi asibiti aka ra masa jini yah mori lokacin sa kafin su biyo nemansa kwanan sa yak’are”
Juyawa tayi ta bar wajen,har ta yi nisa amma su burgu basu biyota ba kamar wanda suke jin tsoron ta a yanzu,kallonsu tayi harda matan da aka aikosu gurinta,kafin tace,
“Duk wanda yake wajennan yaga abinda yah faru inason gobe da safe yah sameni a office din kungiyata ,wanda bai san wajenba yah samu yarana su rakashi,kunji ina?”
“Eh munji muka zamu dole”
Kowa a wajen yah amsa jikinsa har rawa yakeyi tun daga kan yarannasa har yarannata.
Tana komawa gida ta shige dakinsu kan gadonta tareda rike kanta wanda yake barazanar fashewa dan azabar ciwo,da haka har bacci barawo yah saceta.
Da safe gidan da shirye shirye aka tashi na zuwan major sameer wanda zasuzo shida matarsa da kuma d’ansa,zuwan gobene amma tun yau ake shiryawa saboda cewar matar tasa yar shugabansu ce.
A bangaren sameemah kuwa da ta tashi ma batasan wace wainar ake toyawa ba saboda wankan ta tayi ta fice babu wanda tayi wa magana.
Motarta ta nufa wanda ta ajiye a kofar gidan,abin mamaki babu yaro ko d’aya a kusa da motar,saboda da wanine koh mashin ya ajiye sai an jefar dashi barekuma sabuwar motah

Direct gidan kungiyar tasu ta nufa inda take kiransa da office dinta,saboda a makare ta zo ,gidan a cike yake kowa yah hallara ana jiran isowarta.
Tana shigowa kowa yayi tsitt kaman ruwa yah cinyeshi saboda ganin fuskarta a murtuke kaman ta boss din y’an indiyah.
Zama tayi akan kujerarta yayin da kowa yah zube akasan wajen yah zauna kaman wanda akayi musu wahayin su zauna a lokaci d’aya,kallonsu tayi da mamaki ganin harda su burgu ake mata kallon dodanniya ko mayyah,wanda ko kadan bata ga laifinsu ba saboda ita kanta tasan ta dace a kirata da dodanniyar,domin tun tashinta lokacin data fara maida martanin abinda ake mata ,yazamana kowane halitta yah rabeta sai yaji tsoronta,”lallai akwai aiki”ta fad’a a ranta.
Gyaran muryah tayi kafin daga baya tace,
“Kowa yah ga abinda yah faru jiya daddare ko?”
“Eh kwarai kuwa mun gani sosai”
“Toh inaso daga nan wajen kar kowa yah tuna cewa yah ga abinda ya faru barekuma yabawa wani labari,idan kuma ba haka ba,…………”
“Baza akai ga hakaba babu wanda yah tuna abinda yah faru ,koba haka ba yan uwa”
Burgu yah fad’a yana kallon kowa a wajen,cikin sauri kuwa suma suka amsa da cewa,
“Hakane babu wanda zai tuna da abinda yah faru”
“Shikenan naji abinda kukace,saidai nasan a yanzu kunsan koni wacece,kowa a cikinku zai dunga kallona a matsayin dodanniya,kaman sauran mutanen dana yi rsyuwa dasu a baya,saidai bazan ga lafinkuba saboda nasan dagaske hakan nake”
Sukunyar dakai tayi alamun hakan yah tabata,saidai cikin sauri tamayar da fuskarta wanda babu wanda yasan mai yake cikin zuciyarta.
Burgune yah d’ago kaman zayyi magana sai kuma yayi shiru,kallonsa tayi ganin yanda magana ma yanzu yakasa yi mata,ganin yanda a lokacin baya har kyaleshi take idan yah isheta da surutu,
“Karamin shigaba wace magana kake da itah?
“Eh dama shugaba,mun ji kinyi yaren larabci kaman wata balarabiyah,ga kuma abinda yah faru wanda gaskiya yah shige mana duhu,toh kafin kizo kowa yah ce na taimaka na tambayeki ,idan bazaki damuba munason jin tarihinki”
“Shine bukatarku jin labarina”
“Eh Ranki yah dade”
“Toh shikenan bari naga koh bazai d’auki lokaciba,saidai inaso kusani bawai zan fad’amuku saboda ku kai wa wasu labariba,saidan inason yin aiki daku,kuma naga yakamata kusan ni danjin da wa kuke zaune”
*** *** *** ***

Da farko kaman yanda kukaji sunana SAMEEMAH,saboda tunda nayi wayo haka na tashi naji ana kirana,abinda yha faru kuma kafin nayi hankali toh banida masaniyah akai.
Mahaifiya ta hajara batada lafiyah,kullum tana daki kafafunta suna ciwo,ko yau she nice nake gyara kaya idan tah bat’a sannan na kai mata abinci idan kuma taci na fito dashi,shikuma yayanah wanda shima muke uwa d’aya dashi wato yah sameer,shine yake wanke kaya idan tah b’ata saboda ni sannan ban yi wayon yi mata hakanba.
Watarana da safe na tashi daga bacci da safe lokacin banfi shekara shida ba,saboda tun bankai shekarun yin wasu abubuwan ba nake koyah,duba da halin da muka tsinci kanmu nida ummah tah,shikuma yah sameer namijine kuma yayi girma koyaushe suna gona shida baba umaru ,don su manjo ko me za’ayi bazasu jeba,kuma haka inna ramatu take d’aure music gindi suyi abinda suka ga dama.
Bayan na yi shara da kuma gyarah dakin da muke,inna ramatuce tah shigo d’akin tana ta zage zage wai ummah tah bata iyah aiki kuma ta hanani ni na gunga tayasu aiki,ummah ceh takalleni bayan ta d’auke idonta daga kallon inna ramatu wadda tah kama labulen kofar ta rike tana ta masifa kaman tanayi da y’arta ba kishiyarta ba,
“Seematu tashi kije ki tayasu wanke wanken kinji keda su sameerah kuyi”
Inna ramatuce tayi saurin cewa,
“Su sameerah bazasuyi ba itah kad’ai zatayi ,ai su jiyah su sukayi lokacin da kika aiketa karb’o maganin munafurci,yanzu haka ma na cutar damune mu da y’ay’anmu”
Ummah bata kulataba saini ce,da abin yah k’ona min rai nayi magana,saboda maganin da take magana akai,manjo fah ummah tah aika a wani kauye kusa damu amma yak’i zuwa,saboda yah sameer yah tafi aikin kud’i shida yaran unguwarmu,amma haka inna ramatu tace bazaijeba saini ta aika naje na karb’o duk da aikan yayimin girma,amma ji abinda take cewa kaman batasan mai ake cikiba.
Tun kafin nayi magana ummah tah katseni tareda cewa,
“Seematu maza je kiyi wanke wanken allah yayi miki albarka”
Kallon ummah nayi da takaicin yanda take bin duk abinda sukace kaman wasu iyayenta bayan itah ce duk babba a gidan idan ka d’auke IYAH MAI KALWA(mahaifiyar su baba umaru,matar alhaji babba,kakarmu kenan).
“Amma ummah kince fah nayimiki tausa lafafunki suna ciwo?”
“Eh ba sosai bane kije kiyi inyaso saikimin daga baya”
Dan takaici haka badan nasoba na bi bayan inna ramatu ina zobara baki.
Na dad’e tsaye a gaban wanke wanken ina kallonsa saboda bala’in yawansa kuma wai ni zanyishi,kwallar da ta fito a idona na share kafin na tsugunna na fara shirye shiryen farawa.
Na shafe kusan awa d’ayah inayi duk kayan jikina sun jik’e jarab da ruwa,ban kulaba sai ganin Badariyyahn nayi ta watsomin kwanuka tun daga sama,har saida wani kwanon silver yah bigeni a kan goshina,kallonta nayi amma ko nuna alamar mutum yana wajen batayiba sai kama hanya da tayi tah juya,tana karairaya itah a dole ta fara k’irgen dangi.
Ihun yara na faraji wai ankawo gyad’ar baba shehu ,da gudu nabar wanke wanken na zura da gudu domin nima kar ayi babuni.
Kan gyad’ar muka hau nida su salma da manu muna tah tsina,karar duka naji akaina kaman saukar aradu,ihu nafaryi tareda tashi daga kan gyad’ar dan ganin waye,inna ramatuce take dukana wai ta bani aiki bangamaba kuma na tafi kan gyad’a.
Dakinmu na shiga dasauri na tsugunna a gaban ummah ina kuka,kad’e kurar da take jikina tafayi saboda birgimar danayi a tsakar gida.
“Toh kiyi shiru haka”
Ta fad’a tana duba inda yah tsage a jikina yana had’ewa da kansa,nima kalon wajen nayi har sannan ban daina kukan ba,
“Nasan kuka ne irinnaki amma ina babu zafi?”
Jijjiga kai nayi ban bata amsa ba,
“Ni abinda nake tsoro seematu banason kina lalfi suna dukanki,idan wata rana kikayi laifi suka gane cewa ciwo a jikinki Yana mannewa da kansa bansan mai zance ba,maganganune zasuyi ta fitowa wanda bazasumin dadiba sam”
D’aga mata kai kwai nayi alamar naji,kafin ta bingire a wajen na fara bacci.
Na manta ma da tausar danace zanyi mata itama kuma bata tasheni ba ,saboda dukkan mu tausayin kanmu mukeji.
Abubuwa da dama sun faru a satin ciki harda zafin da rashin lafiyar ummah yah k’ara,yanzu har yah kai koh tashi tah zauna bata iyah yi sai an taimaka mata,shikansa yah sameer ko yaushe yana d’akin,nukuma nakan fitah wasa,wajen yara a waje,saidai in anyimin abune zan dawo gida kokuma in dare yayi ,dama masu iyah magana suna cewa sai gida wai an doki kare a kayi.
Fitowa nayi daga dakinnamu aikuwa cikin rashin sani na shambe kalwar IYAH,wacce tah shanyah a Rana tana jiran ta dan sha ta curata dan taci kasuwar gobe,tsayawa nayi nai shiru dannaji ta ganni koh bata ganniba,cikin daga muryah kuwa irin ta masifaffunnan muryarta ta doki dodon kunnena.
“Keeeh dan kusun uwarki uwarkice tace kibimin takan kalwa koh kuma tashen rashin hankalin danaji dama ana shedarki dashi,dazaki zo ki takamin kalwar yanzu idan nace uwarki tazo tayi zata minne,tana nan da itah ba gurguwa ba itah ba mai kafafuba,bata tsinana komai saidai a zuba abinci a kai mata ta cinye.
Cikin yanayin dama na saba da masifarta nayi ficewata wajen wasa,dama ana ta jirana nice nake acting din boss a wasan.
+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤14❤

Tun lokacin dana fita bani na dawoba sai wajen la’asar,muna had’a ido da yah sameer wanda yake gefen ummah a zaune yah watsamin wata uwar harara tareda cewa,
“Ke dan ubanki daga ina kike iyee”
Shiru nayi ina mitsitstsika ido,saboda kogi muka bi malam sule yaje kamo kifi,kuma nasan sarai an hanamu zuwa,kawai rashin ji ne irin nawa,ummah tayi saurin fansata daga amsar dazan bashi,saboda a duniya ta tsani a dunga dukana domin guje tsoron a gano yanayin yanda jikina yake,ni kuwa ko a jikina itah ce take rawanta da kid’anta ita kad’ai.
Saurin rab’ewa nayi na koma gefenta na zauna,can gefe dashi saboda kar yah bugeni dan nasan halinsa sarai,mungun yaro ne shi,kama hannun ummah nayi na rike tareda cewa,
“Ummah ya jikinnaki kinji sauki koh?”
Tun kafin ta bani amsa yah sameer yayi saurin cewa,
“Zaki tambayi yah jikinta mana bayan tun safe kika fitah gidannan bance da rana ba,sai yanzu aka ga k’eyarki,saboda shegen yawo irinnaki”
“Kai kai sameer,nikam banason kana hamtararta kaman ba kanwarka ba,idan batayi wasaba mai kake so tayi,yaro ai dole sai yayi wasa,kayi addu’a ma da ta dawo lafiyah”
Tabb yah sameer dinner zaiyi wata addu’a wai na dawo lafiyah yo na mutu mana,na fad’a a raina,ummah ce tah katseni da tunanin danake musamman da taga ina hararar yah sameer din tagefen idona,tasan sarai yanzu zai bugeni idan yah kula da mai nakeyi masa,
“Ke seematu tashi ki d’auko abincin ki a gefen daki can,har yayi sanyi baki ci ba tun rana”
Toh na amsa dashi kafin na tashi na d’auko ,ina budewa na saka hannu na fara ci,lomar farko dana kai muka had’a ido da yah sameer,ya mutsa fuska yayi tareda cewa,
“K’azamar banza ,ji yadda take ci babu wanke hannu kaman ba yanzu tah dawo daga wasan k’asa ba”
Juyawa nayi na kalli bongon d’akin ina nuna musu k’eyah,dan gaskiya yah sameer din yah takuramin magana ce kawai banyiba.
Tun daga lokacin zama kusada ummah yakemin wuyah saboda Koyaushe yah sameer yana makale da itah,gashi yanzu babu damar tah koreshi ta kirani saboda yanzu babu abinda takeyi da kanta,sai sameer din yayi mata,nikuwa bana shigowa dakin sai kwanciyah ko kuma zuwa neman abinci,duk sanda na je dakin sai ummah tasaka min albarka tareda yimin kashedin zaman duniyah,duk da ina ji amma babu damar aiki dashi a lokacin saboda yarintata nakeci a lokacin babu babbaka.
Bayan wata d’ayah da kwanciyah jinyarta mai tsanani,sai yazamana ciwon dayake kafarta yah fara shiga har cikin jikinta,tashin hankali kam babu irin wanda su baba umaru da yah sameer basu ganiba,idan kaga yah sameer a zaune yah zuba tagumi toh tunanin jinyar yakeyi.
Babu yanda baba umaru baiyi da ummah ta barni na dinga kwana a dakin inna ramatu,amma haka firr taki yarda,komin halin ciwo da ta shiga tana dawowa hayyacinta zata nemeni,nikuwa yanzu tunda naga haka jikina yayi sanyi sosai,saboda nasan idan mutum yana ciwo sosai mutuwa zayyi kuma in yah mutu bazai dawo ba,har kuka nake idan naga tayi shiru ,sai yah sameer yace min bacci takeyi kafin nayi shiru,dan saina ga kaman tah mutune.
Yauma a kwance nake a gefenta saina ji tana riko hannuna,tashi nayi na rike hannun tareda tambayar tah,
“Ummah mai kikeso na miko miki?”
“Babu komai inaso ki bani hankallin ki ne yanzu”
Jijjiga kai nayi alamun ina sauraronta,Murmushi tayi irinna dauriyah kafin tace,
“Inaso da farko seematu ki kasance mai hakuri,sannan duk rintsi karki watsar da ahalinki duk da sun kasance masuyin san ransu amma ki barsu watarana sai labari,ki kama mutuncinki a matsayinki na y’a mace,ban yadda kibawa wani namiji dama yah yaga mutuncinki ba,saboda kudi,wahala,koh kwadayi,idan kikayi haka bazan yafemikiba,duk wata huduba daza’a doraki a bayana ban yadda kibita ba sai yah kasance huduba mai kyau ce,in abune baki ganeba ko yah shige miki duhu ki tambayi dan uwanki kinji,sannan duk rintsi ki guji abinda za’amiki wanda zai ji miki ciwo,saboda boye yanayin halittarki daga idon mutane.
Allah ya tsare ki daga sharri,yah inganta rayuwarki sannan yah yabaki miji nagari”
Duk abinda take fada ina jinta saidai na gagara bata amsar komai saboda bansan mai zance ba.
Yah sameer ne ya shigo shima idonsa yana hawaye da alama yaji duk abinda take fadamin,shima tana kallomsa ta rike nasa hannun tareda cewa,
“Nasan kai kasan mai kake,Toh inaso kacigaba da bin hanyar dana doraka,sannan ka kulamin da rayuwar seematu domin tata rayuwar zata fi shiga hatsari fiyeda naka,karka bari wani mungun abu yah faru da itah,sai abu na karshe munyi magana da babanku,na bashi wata wassiyyah wanda nakeson yah cika min itah,koda bana duniyha wata rana yah baku wannan wasiyyar inaso ku zama masu cikata,sannan ku kasance masu min addu’a bayana,sann…………nan………..uhhh ……..uhh
Tarine yah sarketa jini yana fitah ta bakinta,amma duk da haka tana rike da hannunsu,cikin dauriyah ta hada hannunsu waje d’ayah,kafin tace cikin nishi
“Na baku amanar kanku,kar d’ayah yabar d’ayah cikin halin wahala shikadai,kuzama tsintsiyha madauri d’aya”
Tana gama fadan hakan ta sau hannunsu da alama jikinta yasake,suna kallo tana fadan wani abu wanda basajin mai take cewa har kuma suka ga idonta yah rufe.
Kallon yah sameer nayi ganin yanda yayi wani shuri kaman an daskareshi,
“Yah sameer yanzuma ina bacci tayi koh,kace min zata tashi idan anjima,kaji yah sameer”
Kallona yakeyi kawai fuskar sa da alamar tausayawa idonsa yana zubar da hawaye,batareda y ace komai ba yah rungumeni a kirjinsa,nima a sannan babu abinda nake bukata sai naji wanda zai saurari kukana,hannuna nasaka na zagaye bayansa tareda sake kankameshi,mun dad’e a haka kafin ya dago fuskata muna kallon juna,saida yah share fuskata kafin yace,
“Kiyi Shiru haka,ummah batason kina kuka ,sannan muma watarana zamuje inda ta tafi ,kidaina kuka haka bari na kira su baba yanzu “
Saida yaja numfashi tukun cikin yanayi na juriyah da alama yana cikin mawuyacin hali shima,jijjiga masa kai nayi ina jan majina kafin shikuma yah fita ya barni dagani sai gawar ummah nah.
Tsura mata ido nayi ina ayyana abubuwa da yawa a raina,ciki harda maganar da mukayi da ita nida yah sameer mintuna kadan da suka wuce,d’aga kaina nayi ina kallon baba umaru wanda suka shigo shida yah sameer da kuma inna ramatu,wani irin ihu inna ramatu ta rantab’a tana tsugunnawa a wajen,baba umarune ya wuceta tareda zama a gaban gawar inna hajara,
“Ke matace tah gari hajara mai sunan matar annabi ibrahim,kuma kema kin gado mai sunanki wajen yin biyayya ga mijikinki cikin dad’i da rashinsa,indai a lahira shedar mai mijice ke saka mata su shiga aljanna toh na shedeki matata,allah ubangiji yah yafemiki duniya da lahira sannan yayi miki rahama daga cikin rahamarsa😭😭”
Saida yah kare mata kallo yana zubar da kwalla kafi yah ja mayafi yah rufe mata kanta,shiru inna ramatu tayi tana sauraransa daga ji kasan ranta bayason yanda baba umaru yake yaba halayen ummah na kirki.
A zaune muke a tsakar gidan munyi zugum bayan an tafi kaita gidanta na gaskiya,har sannan zuciyata ta kasa gaskatamin cewa na rabu da ummahn tawa farincikin raina.
Mutanene suke ta shigowa wasu na fita wasu na shigowa,har babu inda wasu zasu zauna.
Wasu mutanene suka fara shigowa gidannamu bayan anyi kwana uku da rasuwar ummah,wanda ranar ne yakama ana sadakar uku,tun daga yanayin jikinsu mutum yasan ba y’an garinmu bane,baba umaru aka kira yazo yagansu bayan an kaisu d’akin da ummah take a da.mamaki ne ya isheni ganin yanda baba umaru yake gaisawa dasu kaman yasan su,toh yaushe yaje wajensu har yah sansu haka,oho.
Sum dad’e dan saida suka kai har wajen la’asar kafin suka sauke buhun shinkafa dana sugar dakuma jarkar manja suka tafi.
Mai hali baya fasawa inna ramatu tana cikin kukan munafurcinta,tana ganin wannan kaya ta share idonta tana washe hakora,(Allah yah shirya).
Yanzu ummah tayi wata guda da rasuwa mutane kowa yah manta da itah inka d’auke ni da yah sameer sai kuma baba umaru,nikam ma nice wadda mutuwa tafi bankad’a saboda cin zarafi tun ba’a kai ko’inaba nafara ganinsa a cikin gidan,su kuwa si yah sameer in suka fita aikinsu sai dare nagansu,toh dama shima rashin lafiyar ummah ne yake sakawa yana shigowa gidan,Amma yanzu tunda babu itah dare yake dawowa.
Dakin ummah shiya zama na yan matan gidan,kowa anyi mata shimfid’i,amma nikuwa sai dare yayi na tura kofa na kwanta a wajen,saboda duk sun saka shirginsu su Badariyyah da kuma manyan yan matan gidan irinsu hafsa,shukura,da kuma lami,dukkansu yayan kannen baban mune mata wanda sun kasa zama a gidamsu sunzo suna takura mana,saidai babu wanda zaiyi magana sai an tab’a d’ansa nikuwa wazayyi magana tunda babu tawa uwar.
Tun abin baya damuna saboda yarinta yamzu har ya kai na fara ganewa,sau daya na je wajen yah sameer na fadamasa cewa ba a bani abinci na koshi,yah tsina fuska yayi yana juya kansa,da alamar na takura masa,
“Kee bafa zan yadda kina takuramin ba ,dan kawai ummah tace na dunga kula,fisabilillah kina ganin dawowata kenan fah amma kina cemin wai ba’a baki abinci kin koshiba,nima kina ganin d’an kad’an suka bani amma nayi shiru nake ci haka,kiyi hakuri kawai kisha ruwa ki kwanta”
Kallonsa nake da mamaki kaman wanda aka sanjashi tun daga mutuwar ummah,takaicine yah cika zuciya tah ganin wanda zan ji sanyi a wajensa ma kallon na takura masa yake,yana kallon na takura masa,dole na sanja tunani na tsaya da kafafuna kawai.
Tashi nayi cikin sanyin jiki na koma d’akin na kwanta,
Jeji ne wajen mai cike da duhun dare da kuma ban tsoro,idan walkiyah ta haska babu abinda nake gani sai wasu halittu a tsaye,matswa nakeyi jikina yana rawa had’e da karkarwa,ji nayi na dungura da wani abu kaman bishiya alamun babu inda zan sake matsawa kenan,saidai abubuwan basu fasa matsowa inda nakeba shiru kawai nayi dan na saddakar da sake rayuwa a lokacin.
Rike fuskata daya daga cikinsu yayi yana hada kallona dashi,cikin wata irin murya yake magama mai cike da amo wanda nakejin ta har cikin jikina ba iyah kunnena ba,
“Hakika dole watarana zaki sallama ki dawo inda yah dace dake,kedin mallakinmu ce,duk da busan inda kike ba har yamzu amma dole muna hade dake,dole zaki dawo inda ya dace dake watarana,sakin fuskata yayi wanda saida wajen yah faramin zafi saboda rikon dayayi min,wata kwaryah suka mikomin mai cike da wani abu kaman jini,kin karba nayi ina kallonsu kawai,dannima gwana ce a taurin kai insu suna gadara da iyah shege,yah mutsa fuska nayi tareda kawar da kai,
“Bazan saha ba”
Shine kawai abinda nace,
“Hhhjhh babu dole a harkar musamman ma ke kinada muhimmanci a wajen mu muna jiram amincewarki”

Tun daga lokacin na ga kamar an wayemin wani duhu sai kawai na ganni a dakinmu,toh mafarki nakeyi ?ko kuma gaskiyace ni kadai nayiwa kaina tambaya sannan na kasa bada amsa.
Tashi nayi naje na sha ruwa na dawo,har sannan mafarkin danayi yana tsaye a raina,yau kusan kwana uku kenan kullum sanayi irin mafarkin,duk da ina shakkar daukarsa a matsayin gaskiya amma nasan yanada alaka da wani abun,saidai banida wanda zaikula da halin dana ke ciki bare yatayani yaki da abinda yake shirin tunkaroni,zama nayi akan gadon duk abin duniya yah isheni,da kuma wane irin aiki zan samu na dungayi saboda magance lalurin rayuwata,tunda nagane abinci ma baza’a bani mai yawa ba ina kuma ga sauran abubuwan bukata na rayuwa.
Da safe ina tashi bayan na cinye d’an dumamen da’aka bani nayi wanke wanke sai na fita waje wajen abokaina su wanda yanzu suke zuwa gonaki aikin gona,ina zuwa kuwa na samu suna jirana saboda munyi dasu nace nima zanje.
Gonar da nisa sosai haka muka tafi a kafa,dayake tafiyar yarace bamu damu da nisan ba haka har muka isa.
Gonace mai girma sosai babu komai a ciki sai wake,yah nuna yayi kyau,roro muka fara cikin buhu naira d’ari d’ari,da murna na fara jin zan samu kud’i nima na sai abubuwan danake bukata.
Saida muka kai har lokacin wajen azahar kafin kowa yaje yah faracin dan tuwon daya zo dashi,nikam ban tashiba saboda nasan idan naje wajenma babu abinda zanci tunda banzo da komaiba,su iliya ne sukai takirana nazo muci amma naki,saboda banason a yanzu dogaro da abin wani koyaya yake kuwa. Kafin a tashi saida na cika buhu guda biyu,ko su dasuka saba zuwa buhu daya sukeyi,mamaki na bawa shikansa mai gonar inda yah bani dari biyu da hamsin saboda dagewa danayi,karba nayi tareda godiya muka kamo hanya muka dawo gida.
Ina shigowa gidan naji karar karan dawa a bayana,tun kafin mai dukan yayi magana nasan inna ramatu ce,aikuwa bata gama sauke karan ba tabini da uwar ashar tana fadin,
“Yar kusun uwa shegiyah,gidan uban wa kikaje tun safe sai yanzu kika dawo ina ta neman ki ki iyo markad’e”
Babu alamar kuka na kalleta raina a bace nace,
“Aikin kudi nabi yara wata gona”
“Eh lallai wuyanki yayi kauri nawa kike harkin fara wani neman kudi,ke yanzu har kinkai a barki da kudi?,bani kudinnan naga naira nawane,wuyarki danake sha duk wani kudi kika samu dama ki kawomin su”
Kallonta nake da Mamakin jin furucinta,su kuwa su inna larai suna gefe suna zigata kaman in anamin azabar cetona sukeyi,maida hannuna nayi baya alamun bazan bata kudin ba,wata wawiyar cafka ta kawowa hannuna na yi saurin gocewa saiga ta tashsh a kasa tayi zaman yan bori,daga kai tayi tana kallona da mamaki,saidai babu alamar tsoro a idona saima kallonta nake kaman zan kai mata duka,hakika in idona yagani dadai kaman na ga alamar shakka a idonta,wuceta nayi na nufi d’akinmu,na tona rami na boye naira d’ari,kafin na d’au hamsin na tafi wajen mai shayin unguwarmu domin nasiya.
Daga ranar tunda nagane da aikin gona ko yan anguwarmu bazasu je ba saina je,dan yanzu nagane da zamana babu kudi hatsarine tunda babu wanda zai kula da rayuwata.
Yauma tafiyah mukeyi nida su iliyah kaman kullum,saida mukayi kusan rabin tafiyar,mun bar gari a baya,turus muka tsaya ganin wani maciji a gabanmu,abin yara da tsoron macijj cikin sauri muka koma da baya zamu koma,saikuma cikin rashin sa’a yah sareni saboda nice a gaban tafiyar dan yanzu nazama shugaba,dan a jinina yake koh cikin yara yawanci nike jan ragamar abubuwa.
Kallona sukeyi da Mamaki kaman idonsu zai fito saboda ganin abinda yah faru,saurin kawar da mamkinnasu nayi tareda cewa,
“Kai Karku damu nasha maganin maciji babu abinda zaimin”
Ganin sun yarda da abinda nacene yasa hankalina ya kwanta saboda kullum ina kula da gargadin da ummah tayimin game da halittata,alama nayi musu akan suyi gaba ina zuwa,yarda sukayi da abinda nace kafin sukayi gaba,saida naga sun bace babu alamarsu kafin na bude inda macijin yah sareni.Wajen ciwon ya warke sai wani abu daya fito daga cikin ciwon baki kirin da alama dafin macijinne,irin yanda ya tabayi sanda kunama ta harbeni lokacin ummah tana da rai,rude kafar nayi kafin nabi bayan hanyar da macijin yabi bayan ya sareni.
A kwance naganshi a jikin wata bishiyah,yah murde kaman igiya yayi baki,tsugunnawa nayi ina kare masa kallo tareda Mamakin shin wane irin jini ne dani,duk wani abu inya dandana shi sai yah mutu.
Tunani na tafi lokacin baya,idan na tashi da safe sai ummah ta kade shimfidina saboda duk sauron daya cijeni mutuwa yakeyi,kafin safiyah sun taru a gefen shimfidina,haka kunamar ma itama mutuwa tayi ummah ta zefar da itah ,toh gashi macijin ma ya mutu.
Tun lokacin da ummah tana raye ban taba tunanin tambayar taba saboda yanayin yarinta,amma yanzu na gano cewar nidin dabance da sauran mutane kaman yanda dodannin mafarkina suke fadamin,amma har yanzu zuciyahta taki yardar cewar nidin dabance har yanzuina ji a jikina nima mutumce kaman kowa,tunda yah sameer ma mutumne yaza’ayi kowa na gidan mutum kuma niba mutum ba,hakan ba mai yiwuwa bane .
Da haka na kawar tunanin a raina na tashi daga tsugunne a gaban macijin na kade rigata na bi bayan su iliyah wanda sunyi nisa yanzu.
Ina zaune a tsakar gidan a gefe kowa yana ta harkarsa yau banje ko ina ba saboda an kare amfanin gona saidai muna tunanin tafiya wani gari aiki,saboda yanzu mun kware a wajen aikin kodago sosai musamman ma ni ,wani yarone yah shigo da sallama tareda cewa wai nazo inji yah sameer,gyara dan kwalina na nayi nabi bayan yaron,a zaune na sameshi akan benchi gefen dakinsu,samun waje nayi na zauna banyi magana ba,
“Ke Bali I yah sallama bane bare kuma gaisuwa”
Shiru nayi ina jinsa dan ina akwai wanda nakejin haushinsa toh ya biyo bayan yah sameer saboda su inna ramatu idan basu kulada rsyuwata ba banu komai saboda ni ba dolensu bace,amma yah sameer shi aka bawa alhakin kulawa dani,kobai min komai ba a kallah ya tambayi wane hali nake,amma babu ruwansa saima wata masifa daya dauki yi kaman wani shine uban mutane,
“Duk abinda kika ga dama ma kiyi tayi,kowa a gidan zancen rashin muncinki yakeyi dama ummah ce take daure miki gindi gashi yanzu babu itah”
Katseshi nayi da masifar dayakeyi kafin nace,
“Uhm akwai abinda zanyi idan ka fadi metasa ka kirani”
“Dama ba kiranki nayi na dunga kallonki ba inason na fadamiki gobe zan bar garinnan da asuba zan tafi aikin soja,ogah soja na anguwarnan ya min hanya,saiki fadamin mai kike bukata”
Kallonsa nayi kawai na ya rainamin hankali dan yaga ni yarinya ce ,banda haka yaushe rabon dan ganshi sai yanzu zai cemin wai me nake bukata?
“Babu abinda nake bukata ni,saboda duk abinda nake bukata,ina yiwa kaina dan haka kaje allah yah bada sa’a,idan shikenan nizan tafi cikin gida”
“Eh shikenan dama dan karkiji na tafine baki saniba kice ban fadamiki ba,”
KO magana ban sake yi masaba na bar wajen saboda wani abin bakin ciki daya tasomin dan takaicin halin yayannawa na rashin kulawa.
Dakinmu na shiga da sauri ,ina shiga kuwa na fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya,saboda duk abinda yakemin ma na halin koh inkula,koba komai in ina ganinsa ko ina tuna cewa yana cikin gidan hakan kan karamin sanyi a zuciyahta,musamman kama da yakeyi da ummah kaman an tsaga kara,irin kyau na anihin fulanin asali,naso ace nima na iyota saboda na dunga kallon fuskata a madubi duk lokacin dana yi kewarta,saidai yanzu shima zai tafi yah barni a cikin wannan halin na kunci ni kadai,wanda kullum cikin kalubalen rayuwa nake.
Saida nayi kukana na koshi kafin na fito daga dakin,ina mitstsika ido.
Yah sameer kuwa kaman yanda ya mafadamin da asubar yabar garin yah nufi jahar porthacourt,domin cikar burinsa dayayi niyyar cikawa,nima kudira nayi a raina saina cika nawa burin na tafiyah babban gari aiki nemam kudi,wanda zamubi irin manyan motocinnan da suke wucewa idan sanyi yazo.
Haka rayuwar take ta garamin da dadi da babu dadi,har muka fara shiga sanyi sannan an gama duk aikin gona,shiri mukryi sosai da wasu tsofaffi wanda suma dasu zamu tafi,inyaso idan lokacin aikin can yakare saimu dawo,dama suna zuwa duk shekara nice dai sai wannan shekarar zan fara zuwa,zancen makaranta kuwa dama ba zuwa nakeyi ba tun daga mutuwar ummah na daina zuwa dama itah ce take korani zuwa makarantar ba a son raina nake zuwaba,dan haka koh hanyar makarantar bana zuwa,idan kanason rawar jikina toh aikin kudine zanyi a biyani toh zakaga aiki har sai ka kama baki.
Tun kafin saura sati dayah da tafiyar nake ta shiri kaman ance zamje makkah,nayi wanki da sabulun dana siyo duk da ma kayan sun tsufah kyakykyawan mutstsika su kayi saidai kaga garinsu a cikin hannunka. Shagon dan anguwarmu naje na sayi garin kwaki rabin kwano dakuma k’arago a wajen a wajen masu tallah,a takaicedai na hada kayana kiciff saboda tafiyah.
Acikin akwatin ummah na karfe na jera kayana a ciki ina kuka ina komai haka na dauko kayan na fito daga dakin,wanda bantaba tunanin zan barshi a kwana kusaba,kkda na kwana dayane bare na watanni.
Dakin inna ramatu na shiga suna zaune ita da baba umarun,tsugunnawa nayi daga gefe tareda gaisheshi,maganar sa ta farkoce tah batamin rai sosai,
“Ahh sameemah dama kina nan yaushe rabon dana ganki a cikin gidan,yanzun wani abune yah faru ?”
Daga masa kai kawai nayi tareda cewa,
“Eh dama inaso zanbi su iyar shehune aikin gona zuwa cikin babban gari”
Shiru yayi yana tunanin maganar tawa,har zai ce wani abu inna ramatu tai caraff tace,
“Ahh Toh ai dakyau kije allah yah tura keyah”
“Ahah ramatu hakan bayyiba tafiyah mace neman kudi hakanma har wani garin?”
“Ahh ba ita tace zatajeba ina ba kai ka tursasa mata ba,ai babu alhakinka koda wani abune yah faru,taje kawai allah yah tsare hanaya”
Daga kai kawai yayi alamar yah ji,nikuwa koh na jira yace wanj abu na kama hanyata na fita a cikin gidan,koh sauran kofofin ban shigaba nayi musu sallama,shima abinda yasa na fada masa dan yah amsa sunan uba ne,badan hakaba saidai yaji labarin tafiyata,dan hakan kamar halin gidannamune in kaga da hanya kawai saidai aji baka nan kayi wata hanyar.

** tan uwa mukula musamman ma mata,saboda daga majority matan mu na yanzu daga an saki kishiyarki koh kuma ta rasu sai yah zamana duk wani aiki su za’a dinga sakawa ko kuma shikenan sun daina zuwa makaranta saboda dama uwarsu ce take kokarin rakasu makarantar.
abinda matanmu basu saniba shine idan yaron yayi karatum watakil ke zai fara amfana saboda ke yatashi yagani ba uwar tasaba,mu kula dan Allah,d’a na kowane idan da hangen nesa.

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤15❤

Lokacin danaje gidan su iyar shehun ban samesuba sai sallahu suka bari akan na bisu da sauri sun tafi neman motar dazasu hau,akwatina na dora a kaina na yanki hanya ina ta gudu burina karsu bacemin bangansuba,ina haki ina komai kaman raina zai fita amma ban dakata da gudunba saida na fara alamaun ganin bakin hanyar dasuka ce na samesu tukun.
A jiye kayana nayi a gefe,lokacin dana isa. Bamu muka samu wata motar ta daukemu ba har wajen karfe 8:00am na dare,saboda lokacinne suke wucewa mu kuma said mu sauka a bakin garin su kuma su wuce garin dazasu je.
Hawa mukayi dukkanmu kowa da kayamsa,nikam samun waje nayi na kwanta tareda yin filo da kayana saboda gudun sata,su kuwa kowa yana bayanin idan an sauka,mai zai farayi,masu lissafin wajen da zasu sauka daban haka masu lissafin irin aikin kudin dazsuyi daban kafin lokacin yah kare mudawo.
Na dade ina bacci saboda lokacin dana tashi duhu yah lullube sararin samaniyah ga kuma duhu hazo da kuma azababben sanyi dayake hurawa kaman an saka mutum a cikin fridge.
Kallon sauran mutanen bayan bodin motar nayi ,suma duk sun takure a wajen daya kaman sardines,hmm neman kudi da wuyah na fada a raina.
Karar salatin da mai motar yah fara yine yah dawo dani daga duniyar tunanin dana tafi,inda kowa a cikin motar shima yah tashi zaune dan jin mai suka gani,hantar cikin mune da duri ruwa tun kafin mu san abinda yake faruwa,tsofin cikin said salati sukeyi wanda suk da banyi karatuba kuma banason yi nasan ba dadai suke fadaba.
Wani daga cikin yaran dirabannne ya leko ta gefen glass din gaban motar yake cewa,
“Toh jama’a saidai fah kowa yayi ta kansa saboda,yan fashine a gabanmu kadan”
Iyar shehu ce tayi saurin cewa,
“Yan fashion kuma,a wannan hanyar amma bamu taba jin labarin yam fashi a hanyar nan ba duk wushewar mu”
“Hakane I yah muma bamu taba gamuwa dasuba gaskiya akwai abinda yake faruwa,gashi babu damar mukoma da baya ,domin suna dauke da bindigogi a hannunsu kuma basuyi kama da kananan yan fashi ba”
Duk abinda suke fada ina jinsu,saidai bana gane mai suke hasasowa saboda ni ban taba ganin yan fashinba sai labarinsu dana keji a nayi kawai.yaran cikin motar kuwa su iliyah da bazasu wuce shekarunmu ba sai kuka suke suna kiran sunan iyayensu sai kace wani shegenne yace su taho.
Motarmu ce tafara sloww a hankali har muka tsaya cak da tafiyah.
Wata muryah ce marar dadin ji ta doki cikin dodon kunnena daga jin muryar babban mutumne kuma ba yaran hausawa ba,masifa yake yiwa direban akan ya fito daga cikin motar. Fitowa yayi yana gaishesu,saida suka kwala masa wani abu kafin daya daga cikinsu yace,
“Kudi ka bamu kudi koh kuma mu dauka rai”
“Ogah babu kudi yamzu muka debo kayan”
Wani ne daga cikinsu yace kai wannan ka barsu kawai basuyi kama da wanda zamu samu kudi a wajensu ba”
Har sun barshi yakoma cikin motar mu fara tafiyah,wani yaro daga cikin mu yayi atishawa saboda murar dayake yi,hantar cikinmu ce tah kada dan dagani kashinmu yah bushe yau.
Tun kafin na gama Tunani naga sun yaye tampol din da muke ciki sai gamu gasu lokacin da suka dallemu da wata fitila mai haske.
Wani daga cikinsu ne ya duro cikin motar yana daukar mu yana mikawa wanda yake waje shikuma yana diremu a kasa,kallon mu sukeyi da mamaki ganin yara a motar kayah.
“Kai driver kenan sato yara kayi baka fadamana ba”
“Ahah ogah ba sato su nayi ba,zan ajiyesu a babban garine na wuce”
“Taya zamu yarda dakai lallai dole kayi bayani”
Dukansa suka farayi yana ihu tareda rantse musu,nice nayi saurin cewa,
“Ba sato mu yayi ba mu ka ce yarage mana hanya zuwa cikin babban gari”
Tun kafin na rude baki wani daga cikinsu yah yadak’i dan kwalina tareda gashina da karfi,wata kara na sake mai kara saboda azabar danaji,zefarni yayi a gefe tareda cewa,ku kama yarannan dukka ku saka min su a motah.
Su iliyah suna jin haka suka fara ihu,babu abinda na tuno a raina sai yanda dukka yaran iyayensu suke matukar nuna musu soyayya,yah zasuji idan suka ga cewar yaran su sun bata kenan har abada,musamman mahaifiyar iliyah shikadai ta haifa a rayiwarta ,dole na ceci abokaina in ba hakaba zasu illatar dasu,sannan koda na saukar da rayuwata babu komai tumda idan na mutu a sannan babu wamda yake sona bare yah tuna Dani,da haka na samu karfin gwiwar tashi daga wajen nace,
“Bazaku tafi dasuba,saidai ku tafi da ni kadai, in ma tafiyah zakuyi da wani daga cikinmu,sukam dole su koma wajen iyayensu cikin koshin lafiya”
Dariyah ogannasu yah fashe da itah ganin yanda na wani murtuke fuska kaman wadda zata iyah masa wani abu,tahowa yayi wajena yah kamani tareda hade hannuna waje daya yana kallon fuskata,cizo na garya masa a hannunsa na kusa da fuskata,aikuwa cikin sauri yayi min duka mai karfi wanda saida hankalina yah gushe.
Cikin juyawa da kaina yake na ga lokacin da motar yan sanda tah fara tahowa daga nesa,yayinda ogannasu yace su daukoni su sakani a cikin motarsa,ina ganin lokacin da motar dana ke ciki tana ta tafiya cikin jeji hoton motarmu kuma yana karayin nisa a cikin idanuna har wani duhu yah lullube ganina.
Bude idona nayi na ganni a wani daki mai dauke da yara da yawa,dukkansu tsiramin ido sukayi kaman sunga dodo,nima a vangarennawa kallonsu nakeyi da tunanin a wane waje nake haka,babu wanda zai amsamin tambaya ta da alamu saboda yaran dukkansu a tsorace suke taya zasu amsamin wata tambaya.
Daga idona nayi ina kallon wani mutumi wanda shigowarsa dakin kenan,kama yayimin dana daba ganinsa awani waje,saida nayi Tunani kafin na tuna da yana daya daga cikin yan fashin da muka hadu dasu a hanyarmu ta zuwa babban birni,cikin kankanin lokaci hankalina yah fara tunanomin abinda yah faru dallah,saboda hankalina ya gushe lokacin baya saboda dukan da shugabannasu yayimin a kai.
Daga ido yayi yana kareni da kallo sannan yana daga gira,nima kallonsa nayi saidai ban dade ba na dauke ganina daga Kansas ina sunkuyar dakai kasa,wani ne daga bayansa naji yana tambayar sa cikin gurbatacciyar hausa.
“Wace yarinyace wannan kuka kawo jiyah”
“Mutumiyar ogah ce yana bukatar hukuntata ne,idan yah warke,dan yanzu haka yana can daki hannunsa ya shanye saboda cizonsa datayi,nazo yin magana da itah kuma naga kaman da alamun hankalinta yah gushe saboda mummunan duka da ogah yayi mata akai”
“Wai dagaske kanayi shine abinda yah faru”
“Eh babu karyah akan hakan,yanzu bari na kaitah dakin ogah doctor yana nemamnta”
Duk maganar dasuke inajinsu,saidai koh daga kai banyiba,amma batun hannunsa daya shanye nasan dama hakan zata faru dan yadda jinina yake da guba haka ma bakina,nikaina ina Mamakin hakan.
Fizgata yayi ta kayi saidai da alama shidin a tsorace yake dani,domin duk yah daure hannunsa da wani karfe,duk da halin ciwo da nake na rikeni dayayi saida nayi dariyah da abinda yayi din.
Dakin babu nisa daga inda yah fito dani saidai kuma yanayin surkukiyar wajen daga gani anyi ne domin samun damar tserewa idan rana ta baci.
Ni kaina saida abin yah tsoratani ganin yanda hannun nasa yayi wani baki musamman wajen da cizon yah fara,kamar wanda maciji yasareshi,sunkyar da kai nayi har ya sakko daga kan gadon ya iso wajen danake,kama kumatuna yayi kafin yah dago da fuskata dan dole.
Nima kallon mummunar fuskar tasa nake mai,cike da takaici a cikinta,
“Ke me kika saka min acikin jikina mai azabar ciwo wanda inaji yana kone jinin jikina sannan kuma yana rubar da fatar jikina?”
“Ni babu abinda nayi maka,kawai wata cutar ce dakai”
“Ke kewaye da har zakice haka,zaki fuskanci hukuncina dole,ku daureta a cikin cell,sannan ku fara shirye shiyen tafiyarmu,kasar da zamuje ta boyayyiyar hanya”
Komawa sukayi dani daga amma yanzu wani daki ne daban mai matukar duhun gaske.
Tun daga bakin kofar mutum yake jiyo kukan beraye da kuma warin datti dana mushe,tunkudani ciki sukayi tareda maida,kofar suka rufe.
Tafiya nake a hankali a wajen saboda bana ganin gabana har na isa jikin bangon dakin,samun waje nayi na zauna dan ganin mai zai faru kuma yanzu.
Mutanen da suka saba zuwamin ne yauma suka zo,saidai yanzu sun sanja kaya daga jajaye zuwa bakake wuluk,kara mikomin kwaryar sukayi yauma dauke da wani jan ruwa a ciki,har nayi kokarin kawar da kai mutumin yace,
“Karki dam u wannan ba ruwan dawowarki cikinmu bane,wannan na biki ne da mukeyi,kuma yah zama dole shikin sha wannan domin a wannan lokacinne zaki fara taka mataki na gaba”
Sake mikomin yayi bayan ya gama bayani,abinda yah ban mamaki shine na kasa yimasa,musu akan hakan saima karba nayi na kai baki,dandanon gishiri naji dakuma karni daya ziyarci hancina,cikin sauri na sau kwaryar ta fafi kasa ina mai cewa,
“Jini jini kuka bani na sha ,meyasa”
“Saboda shine nasararmu zaki sani daga baya watarana,yanzu zamce yakare tunda kin dandana a bikinki,duk wanda kika dandana jininsa a nan gaba zai kasance namune,ki saka wannan acikin kwakwalwarki”
Tun daga wannan maganar na farka daga baccin danake yi,yau banyi Mamakin ganinsu ba saidai abinda yabani mamaki shine abinda suka bani nasha,kuma tun daga lokacin nakejin kaman ana zigani na ciji mutane.
Bamuyi kwana uku a wajen ba na ga wani yazo wajen kejinnawa amma ba wanda yasava kawomin abinci bane,budewa yayi tareda yimin alama na biyoshi,saboda hasken daya ziyarci idona karo na farko bayan kwana uku,bansan lokacin dana rufe idona ba,saida nasaba da hasken kafin na bude ina kallon sararin samaniyah,da sauri na bishi ganin yanda yamin nisa kafin na isoshi.
Samun su nayi kowa yayi shiri,dukka yaran an saka su acikin mota ,nima ina zuwa suka iza keyata cikin motar muka fara tafiyah.
Tafiyar mai nisa mukayi,tun muna ganin rana har ta fadi mukayi bacci gari yah sake wayewa amma duk muna cikin tafiya,dukkan mu idan ka ganmu mun yi laushi lukwui saboda tsabar gajiya.
Bude ido mukayi kawai sai ganinmu mukayi a bakin wani tafkeken ruwa,sai shiga jirgin ruwa ake ana wucewa.
Mu ma cusamu akayi a wani jirgin ruwan saidai a kasan cikin jirgin ruwan inda babu wanda zai kuladamu.
Nan ma munyi tafiyah mai nisa kafin muka ji ana mana alamar mu fito ,kallon inda muka nake da mamaki.
Toh kuma nan ina ne ???

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤16❤

Da mota aka daukemu zuwa masaukinmu wanda shima cikin lungunne kaman wanda muka fito a ciki,duk da bansan a wani abu ba lokacin amma nasan wajen ba kasarmu bace,saboda duk mutanen da muke wucewa fararene tass kaman zabiyah,kallon hanya mukai tayi har muka isa inda zamu zauna din.
Washarin saukarmu a sabon wajenne muka tashi da cewar ogan su yah mutu,saboda cizon danayi masa sati d’aya daya wuce,zuwa sukayi suka sake daukata zuwa dakin dayake inda likitoci suke ta zirga zirga,
Yaron oganne wanda shine mataimakinsa,tsaye yake akan gawar yana kallon yanda yayi bakikkirin kaman an shafeshi da gawayi,rufeshi yayi da wani farin kyalle idonsa yana zubar da hawaye,juyo da kallonsa yayi i zuwa gateni wanda nima kallon gawar nake.
Tun daga fuskarsa zaka san ransa yah baci matuka saboda hatta naman jiknsa rawa yakeyi.
Wata wukace a hannunsa mai masifar kaifi yake nufoni da itah,wani bugu zuciyata takeyi ina matsawa da baya domin nasa hukuncin ba mai dadi bane,magana yafara cikin dacin harshe,
“Dolene kema ki mutu kuma kisan wulakanci tunda har kikayi sanadiyyar mutuwar dan uwana”
Damkar wuyana yayi yah dagani sama yana kallon cikin idona,har sannan wutar bakin cikin dake huruwa a cikin ransa bata daina ruruwa ba,daga wukar yayi yah shaftata min wuka a makogarona,wani irin zafine ya ziyarci wajen inda nayi sautin saka hannu ina tari,tsorone ya kamani jin yadda iska ke fitowa daga makogarona a maimakon tah hancina ko baki,ina jin yadda iskar ke daina fita har yah zamo ta koma fitowa daga inda dama ya dace da ita wato hanci.
Dauke hannuna nayi daga kan wuyana ina,kallon yanda jinin dake hannuna yake konewa,a lokacin dana kai kallona kan mutanen dake dakin dukkan su kowa ni yake kallo bakinsa bude,ni kuwa ko ta kansu banbi ba saima,fita da nayi daga dakin ,saboda idan Mamakin abinda yah farune ni na dade da gama wannan Mamakin,kawai na mika wuyah da duk ma wace halittace ni shikenan komai yah banjama banjam.
Tun daga lokacin babu wanda yasake tunkarata da wani zancen komai kaffah kaffah sukeyi kowa yana tsoron zuwa kusa dani,tun abin yana min dadi har yafara damuna saboda yanda sukeyimin kallon dodo abin babu dad’i,sai a sannan na tuno illar da ummah take nunamin na gujewa nuna ainihin ni wacece a gaban mutane,musamman ma wanda suke kusa dani,dan saina budi ido na rasa kowa a DUNIYA TA.
Washagari da safe lokacin dana tashi babu kowa a dakinnamu,abinne ya dauremin kai saidai ban ce komaiba,tashi nayi na fito waje nan ma ban hadu da komaiba,
Wasu mutane nagani da alama kaman yan sanda ne danna gansu da kayan tsaro,suna kallona suka iyo wajena tareda sakamin wata sarka a hannu,nidai kawai kallonsu nake har muka dau wata hanya bayan mun shiga wata mota mai budadden baya.
A bakin wani get muka tsaya saida wani mutum yah duba kafin muka shige.
Gidan yana da bangarori da dama,gashi babban ginine wanda tunda nake ban taba ganin irin wannan gininba.
Iza keyata sukayi har wani bangare wanda yake can karshen gidan,muna shiga naganshi kaman gida saidai,da gani wajen da tsaro sosai,a wani daki suka sakani bayan an cire sarkar da take hannuna.
Wasu yarane a dakin guda hudu dukkan su suna sanye da kaya kaman uniform din makarantar garinmu irin wanda,aka bani bayan shigowarmu wajen,biyu daga cikinsu bazasu kaini ba,amma dayar da take gefe ita kam zatayi sa’a ta daga ganinta,dukkansu fararene tass da alama basuyi kama da kalar fatataba,duk da cewa nima farace amma baza’a hada nawa farin danasu ba.
Samun waje nayi na zauna a gefe duk da yanda nakejin fitsari babu damar na tambaya tunda bansan da wane yare zanyi magana ba,saura kiris fitsarin yah zubo kafata har rawa takeyi naga daya daga cikinsu ta tashi ta shiga wani dan daki shima a cikin inda muke dinne. Bayan ta fitone nima na shiga saidai ja nayi na tsaya ganin wani katon baho a bandakin da kuma wani dogon karfe a tsaye sai wani abu kuma mai dan kai shima a kasan dogon karfen,tsugunnawa kawai nayi na tsula fitsarina koma dakin waye shiya sani.
Bayan na gama ne zan tashi sai santsi ya debeni,kama bakin dake jikin dogon karfennayi gam,amma sainaji yah juya ruwa kuma ya fara zuba,tsayawa nayi ina kallon ruwan da mamaki ganin daga inda ruwan yake fita,kunnawa na farayi ina kashewa nayi yafi goma kafin na tsaya dayi,fita nayi da sauri na dauko wannan kayan da suka bani masu kyau kalar ruwan omo,zuwa nayi na wanke jikina kafin nasaka su na fito ina bubbudawa nima na saka irin kayansu.
Yanzu nayi sati daya a wajen,kullum za’a kawo mana abinci mai dadi,su kam na dakin kaman basa son zaman wajen da kullum cikin tagumi suke abincin ma basaci da yawa,nikuwa saina cinye nawa na side kwanon wani lokacin ma saina hada da nasu na cinye tass,ga wanka yanzu nasan yanda ake amfani da komai na bandakin sainayi sau uku ma a rana,sannan idan rana ta dan fito sosai za’a kaimu wajen karatun su larabci da kuma su litattafai na addini.
Cikin lokaci kankani nayi bulbul dani fatata har sheki tajeyi saboda tsabar dadin danake ci,abu daya na tsana wanda yake cimin tuwo a kwaryah,shine duk lokacin sallah sai anzo an tafi damu zuwa cikin masallaci ran juma’a kuma zasu bamu abaya da gyalenta musaka mu tafi masallaci,ga karatun asuba dole sai kowa yayi,wannan shikadai yake hadamu dasu,idan kuma mutum bayyiba ayi masa duka lilis,kuma sai ka wanke dukkan kayan yan dakinku da kuma wankin bandaki.
Yanzu nafara sanin wani abu idan yan dakinmu sun fada ,dan yanzu nasan sunansu suma sunana,khairah da hairah,su yan biyune,matar babansu suka yiwa wankan soyayyan mai shiyasa aka kawosu,ita kuma shaheedah guduwa tayi daga gida tabi yan iska,shiyasa yan uwan babanta suka kawota nan,tambayar su nayi nikuma meyasa aka kawoni wajen,cewa sukayi wai sunji ana cewa an kamani ne da hodar iblis(cocaine)a cikin wani gida da ba’a amfani dashi,da alama wai abokan aikina ne suka gudu saini kadai,cikin kankanin lokaci nayi tunanin cewa,da gangan suka gudu suka barni a kamani saboda tsorona da sukeyi.
Tun daga lokacin muke dan magana da,su shaheedah duk da cewa banajin yaren larabci sosai amma ina gwadawa,har take fadamin sunan kasar su palastine. Abin bai wani ban mamaki ba tunda ba wani sanin mai take nufi nayi ba,kawai dai naji ta ne,ni dai ina rayuwa kawai naci na koshi kuma nayi abinda nakeso idan masu kuladamu basu ganiba,dan yanzu har wajen bangaren maza nake jan shaheedah muje hira dayake itama jar wuyah ce tasan takan rayuwar air,saimunsha hirarmu da su munajin mai sukayi aka kawosu suna fadamana,harda labarin yanda area su take.
Haka kawai idan ba zancen rashin arzikba bana jin raina yanaso don duk lokacin da’aka zo karatu tun daga na turanci har na larabci yi kawai nake badan raina yanaso ba,duk da ina kokari sosai na iyah kowanne amma raina bayaso,kawai dannasan horon dazai biyo baya bazaimin kyau bane,gashi tsoron malamin addinin nan nake kaman raina zai fita,dan koda da kuskure ya zangamin carbinsa ji nakeyi kaman yana kona jinin jikina,shiyasa ni nake fara bada hadda idan yazo karba,sai yaga kaman nafi kowa san karatun ,nan kuwa ba haka abin yake ba sam.
Wata ranar juma’ane aka daukemu zuwa makabarta,munsha abaya bakake dukkanmu matan,su kuma mazan sunsha fararen kayah,bayan mun shiga motane kuma naga wasu matan suma sunsha bakaken kaya amma su da nikaf a idonsu suna shiga wata motar,tabo shaheedah nayi wanda take gefena a zaune,dagowa tayi tareda tambayar menene,nuna mata nayi tunda har sannan ban iya larabcin sosai ba sai kalmomi kadan kadan,ganin ta kallesu ne nace mata suwaye?
Murmushi tayi kafin tace,
“Masu laifine amma sun haura shekara goma sha takwas shiyasa aka kaisu wancan kurkukun,muma da mun yi shekara sha takwas da can za’a kaimu,kuma su suna aiki sosai ga kuma horo ga wanda yah aikata laifi mai yawa”
Jijjiga kaina kawai nayi har muka ja muka tafi idona bai dauke daga kan motar tasu ba.
Mun dade muna tafiyah kafin muka isa zuwa cikin makabartar,ba mu muka dawoba har sai wajen magriba ,naji dadin fitar sosai koba komai nayi kallon waje dayawa.
Bayan munyi sallar isha ne nazo na kwanta ba bacci nayi ba tunani kawai nakeyi na gida ,tareda yiwa kaina tambayoyi yanzu suna can sun manta Dani babu wanda zayyi tunanin an saceni kowa zai dauka na tafi babban birni neman kudi kaman yanda na fadamusu,hawsyene ya fito a idona dansn tuna da ummah na,lallai mutuwa mai yanke kauna ce,nasan da tana.nan da yanzu ina gefenta a kwance tana yimin tatsuniya,saidai wani bangare na zuciyah ta yana cewa,gwanda da bata nan,domin da tana nan da hankalinta sai ya tashi matuka da haka na gama tunanina har bacci ya dauke ni.
Kwanci tashi shakuwa ta shiga tsakanin mu ba iyah yan dakinmu ba hatta bangaren maza babu wanda bai sanniba musamman ma shaheedah wadda kullum tare muke da itah,dan ni da itah har wiwi mike sha wanda mazan suke bamu suna siyah a wajen amintattun mutanensu masu gadi,saidai duk abinda mukeyi babu wanda yasani hatta yan dakinmu ma basu saniba,gashi babu inda na fita naje amma zallar rashin mutunci koh shaheedah bazata gayaminba duk da ita ta dade a cikin yan iska amma saida na nuna mata iyakarta wajen rashin tsoro da kuma aikata abinda nayi niyyah,saboda ni bayan rashin mutuncin danakeyi har jinake ana,zugani a cikin kaina idan kuma nakiyi sainaji kaman ana son azabtar dani,gashi duk sanda mukayi fada da wani sainaji babu abinda nakeso sai shan jininsa,tun kafin aje ko ina na kula cewa wannan abinda zuciyata takeso yana da matukar hatsari,shiyasa idan hakan ta faru saina shiga bandaki na rufe,saina huce kafin na dawo,yanzu kuma in ba wiwi na zukaba banajin dadai kwata kwata.
Muna cikin tsaka da shuka tsiyamu nida shaheedah kwatsam saiga iyayenta sunzo tafiyah da itah,a da lokacin baya kafin zuwana babu abinda takeso sai tabar wajen amma yanzu bata kaunar abinda zai rabata da wajen,dan yanzu ta gane tsiyar danake jan ragama anayi a cikin wajen koh inda take ba’a irinta.
Tun safe take kuka nake rarrashinta akan wata rana zamu hadu,sai can wajen rana kafin motar kawunta yazo,wata takarda ta mikomin da number a jiki,kafin tace.
“Ni zan tafi amma ki tabbatar kin kirani duk lokacin da kika dawo,zanyi kokarin na gyara number kuma ina jiran kiranki duk ranar da kika fito,bazan taba mantawa dakeba,yimata alama nayi da karta damu,dan ni a yamzu tunda na rabu da mahaifiyata to kowa ma zan iyah rabuwa dashi ko waye shi kuwa.
Bayan naga kulewar motarsu ne na kade rigata tareda shigewa dakinmu ko a jikina ,wasan ma yanzu aka fara bugawa.
Toh fahh.
+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤17❤
Ina Shiga naji su nairah sunyi tsit da alama gulmata ma sukeyi,dan kwanannan naga wuyahnsu nema yake ya isa yanka,kallon kowaccensu nakeyi cikin kankanin lokaci suka shiga taitayinsu,shigewa nayi bandaki nayi wanka kafin na fito na kwanta sannan ana ta kiran sallah,gyara filona nayi na kwanta,khairah na kalla wadda take saitina a zaune itama daga idon tayi tana kallona tareda cewa ,
“Menene anty sameemah?”
Murmushin jin dadi nayi yanda ta kiranin kafin nace,
“Idan muallim yace ina nake a wajen sallah kuce bana sallah ne”
“Ahh amma fah yau kwananki uku da yin tsarki,kuma muce masa bakya sallah a cikin mutane”
“To Karku fada ku hadu dani,ina ruwanan dan kowa yaji bana sallah iye,dolene said nayi sallah ni ya takuramin dan yaci sa’a babu wanda nake tsoro duk duniyah sama dashi da wallahi saina koya masa hankali,kuma saura karku fada ku gani,hmmm”
Komawa nayi na kwanta,dan wannan shine period dina na farko a duniyah,tinda yanzu naji a kwai excuse din rashin sallah ai kuma shikenan ta zo gidan sauki kuma,na samu abin cewa har sai yaganoni da Kansa.
Komawa nayi na kwanta su kuma suka fita suna tura baki jin irin aikan danayi musu,gashi dole said dun fada ,dan yanzu ba karamin tsorona suke jiba,tun lokacin dana danna kan khairah a cikin ruwan toilet na ploshing dan ta zageni suka mungun tsorona kaman mala’ika,gashi kuma shaheedah bata nan dama itace take taremusu hukuncina idan suka shoga gonata.
Ban ta shi a bacci ba sai wajen magriba,ina tashi na dauki abincina na ci,nasake wani wankan kafin kuma nafara shirye shiryen bin barauniyar hanya zuwa cell din maza,ban samu su hairah a dakinba sun tafi sallah dan haka har na bar dakin basu dawoba,
Wajen babu nisa da inda muke dan haka dama sun san da zuwana kawai kofah suka budemin na shige,zama nayi a tsakar dakin ina kallon kareem wanda zaikai shekara sha biyar a duniyah,yarone amma shegen kansa ne,murdaddiyar wiwi yah mikomin na karba ina busawa,take wani sanyi yah ziyarci zuciyata naji duk duniyah babu wanda yafi burgeni sama dashi,hira aka shiga yi ta labarin duniyah da kuma yanayin yanda kasar take.
Bani na dawo dakinmu ba said sha biyun dare,aikuwa ina dab da shiga dakin na hadu da nannyn mu mai kulada wajen,saurin juyar da fuskata nayi ina kallon kasa,
“Ke seemah me kike a wajen”
Shine abinda tace da Mamakin ganina a wannan lokacin,dayake nidin shigaba ce Cikin sauri nace mata cikina ne yah baci shine na fito domin nayi tusa a waje kar na damu su hairah,alamar kin kyauta tamin tareda yimin addu’a allah yah kara shiryamu,ni kuwa a raina nace,aida zanyi tusa dari wallahi duk sai sun sheka dan banga shegiyar dazan fito waje dan kartaji tusa ba,saidai ta mutu a kaita da safe.
Bugo kofar nayi bayan nashiga wanda yasa dukkan su suka tashi a razane suna kallona,nima kallonsu nayi batare da nayi musu magana ba na koma na kwanta.
Bayan shekara daya da tafiyar shaheedah mukayi sauka a makarantar mu’allim nafi kowa kokari da kuma kaifin hadda,kuma dama duk wanda yafi kowa ilimi toh za’a tambayi wanda yake zaune dasu shaidar halinsa idan an ga yah shiryu sai a sallameshi.
Da sassafe muka shiryah domin zuwa wajen walimar,cikin kaya iri daya,na maza daban na mata daban,mu’allim na zaune akan kujera duk sanda muka hada ido said yayimin Murmushi,nikuwa kallonsa kawai nake,wai fah yanace danna shiryune na ke bada haddar,baisan carbinsa nake tsoro ba,dan duk sanda ya dakeni dashi kwana nake ina jin azaba,kaman ana kwaramin wuta,shiyasa nake binsa kawai a rabu lafiyah.
Tunanin na katse lokacin dana ji ankira sunana,SAMEEMAH UMAR,tashi nayi zuwa wajen karatun na fara.
Da karfi nake cikin kwarewa,saboda burina shine su sallameni a wajen nima naje naga me akeyi a cikin garin.
Kabbara naji yah dauka lokacin dana gama wajen da aka bani,da ni watace dadi zanji amma maimakon haka saima gani nake bata lokacin su sukeyi.
Da haka aka gama walimar da kuma karatun kowa yah kama gabansa,da niyyar gobe za’a ji wanda yayi na daya a bashi kyautukansa da kuma sallamarsa zuwa gidansu.
Bamu muka dawoba sai tab ana kiran magriba,bayan munci abinci mun yi komaine,na kira,sunan su khairah ina gyara zama akan katifa ta,dukkan su nutsuwa sukayi,dan sunsan hankalinsu nake bukata a lokacin,
“Yawwa inaso na gargadeku,idan aka tambayeku ni wacece naji wata tayi zancen abinda nake aikatawa,har kukasa aka ce bazan tafiba hmmmmmm,basai na fadaba kawai”
Khairah ce ta cuna baki kafin tace,
“Toh dama ko kin hanamu ai shaidar karyah zamu bayar a kanki dan ki tafi muma mu huta”
Hairah ce tayi saurin gwabe bakinta tareda yimata kallon ta shiga hankalinta,
Nikuwa tunda naji abinda tace nasan banida matsala tanan bangaren sai kuma a ji da gobe kuma.
Da sassafe na tashi yau saboda zumudi mai zai faru,cikin sauri muka shiryah domin zuwa jin sakamako.
Bayan anyi taro kowa yayi shiru yana sauraran mai gabatarwa can naji sunana yana amsa kuwwa kaman a cikin mafarki,dagaske fah ni aka kira wai na lashe gasar karatun qur’ani da kuma litattafan addini,tab lallai sunyi kuskure,tsinke tunanin nayi na tashi ina tafiyha cikin nutsuwa har naje gaban mu’allim,Murmushi yayi min tareda mikamin kyautata yana cewa,
“Hakika nay I miki murna sameemah ke yarinyace mai hazaka da kuma dagewa,allah yah albarkaci rayuwarki sannan ina muki albishir da cewa a yau an sallameki daga gidan horo na yara zakije wajen danginki ki cigaba da rayuwa kaman ko wane da mai yanci”
Banyi murnar karatun ba da kuma addu’a abinda na sani shine fita waje domin neman shaheedah shine kawai a raina,amma a fuskata murmushi kawai nayi tareda nuna masa na ji dadi sosai.
Haka taro yah Kare kowa yah karbi kyautukansa mukuma nida sauran guda ukun da aka sallamemu kaya masu kyau suka bamu ba uniform dinmu ba.
Tun kafin na shigo dakinmu su nanny sun hada min kayana uniform kuma sun dauke abinsu,su hairah nagani a,zaune ko kallon inda nake basuyiba,nima ban kallesuba,lokacin danazo fitane nace musu sai wataran,su ma toh suka bini dashi, na kama hanyata nayi hanyar waje inda za’a daukeni a mota.
Bayan mungama sallama da kowa muka dauki hanyar tafiya,sauran mazane suna ta murna zasu je gida. Daya daga cikinsu aka sauke sai shima dayan da akayi tafiya mai nisa dashi aka saukeshi.
Ni kuwa tafiya muke tun suna hakuri har suka gaji sukayi magana ganin nayi shiru bana da alamar nuna musu hanyar gidanmu,
“Keh sameemah a ina zamu saukeki ne?”
“A gidan dayake farkon hanyar dazaku shiga”
Toh kawai sukace,a bakin wani gida mai baki get suka saukeni,kayana na dauka na shige cikin gidan kaina tsaye ina daga musu hannu,saida naga wucewarsu da wasu mintina kafin nafito daga cikin gidan ina lellekawa ko wani yah ganni a cikin gidan,saidai cikin sa’a babu wanda yaganni harna fito na tari taxi.
A cikin taxi dinne na rokeshi yabani aran wayarsa, da farko bai niyyar baniba amma dana marairaicemasa akan gidanmu zan kira sai yah bani.
Number wayar shaheedah na saka,cikin sa’a kuwa sai ta dauka,da farko tayi Mamakin ganina saidai ban barta ta cikani da surutuba na tambayeta address din gidansu,tana fadamin in fadawa driver da haka har muka isa kofar gidansu kafin nabashi kudinsa ina yimasa Godiya.
Da murna ta rungumeni tana tsalle kaman zata cinyeni,cikin gidan muka shiga gashi mai kyau saboda babanta yana da kudi sosai.
Mahaifiyar tace ta tarbeni cikin mutunci da ta fadamata ni kawarta ce ta makaranta.
Satina daya a gidan su shaheedah komai yana tafiyah normal amma kuma matsalar daya shine yayanta yah takuramin waishi sona yakeyi ,saidai abinka da dan iska ina ganinsa nasan jirgi daya ne mudashi amma da alama ita shaheedah bata fahimci hakan ba,kuma duk matsalar daga wajen mamarsu ne domin itah ce take sangartasu batareda sanin mahaifinsu ba.
Yau ma a zaune muke a falo nida shaheedah mamarsu batanan ta tafi shopping,sai shaheedah ta shiga wanka nikuma ina zaune da waya a hannuna,banzata na kawai naji hannu yana bin cinyata ina daga ido naga yah shaheed ne,abinne yaban mamaki ganin abinnasa har ya kai haka. Matsawa nayi gefe batareda nace komaiba,shima sake matsowa yayi yana wani bina da mayen kallo,fuskarsa ya matso domin yah sumbaceni bansan lokacin dana zuba masa wani gigitaccen mari ba akan fuskarsa,wanda yayi dadai da shigowar mahaifiyar su ta dawo daga kasuwa.
Zubar da kayan siyayyar tayi tana bina da kallon mamaki,dan a duniya babu abinda takeso yah yayannata guda biyu ,shiyasa ta tsani jinin abinda zai tabasu ko miyeshi.
Lokacin da aka kai shaheedah gidan horo ma itace tayi kutun kutun aka dauko mata yar ta.
Matsowa tayi inda nake har sannan idonta bai dauke a kaina ba,ganin haka ne yasa shaheed yayi saurin cewa,
“Ummeeh dama ban fadamikiba wai fa dan kawai ina yimata wa’azine saboda itace take hurewa shaheedah kunne lokacin da suna gidan horo”
“Gidan horo kuma,amma naga shaheedah tacemin kawarta ce daga makaranta”
“Karyane it’s ce shugabar tantirai a gidan”
Kallon su kawai nake batareda nace komai ba,dan ko mamaki banyiba tunda hakan ba bakon abu bane a wajena.
Bayan sun gama zancen sune ummeeh ta kalleni tareda cewa na bar mata gidanta ,daga kai kawai nayi alamar naji,juyawa nayi domin komawa dakin shaheedah domin tattaro kayana,kicibis mukayi ta idah a bakin kofa da alama taji duk abinda mukace,bance mata komai ba sai rabewa danayi na wuce dakin ina tattara kayana.
Rike hannuna tayi tana jijjiga kai alamar karna tafi,dafa kafadarta nayi ina cewa,
“Ahah shaheedah dole na tafi amma ba rabuwar kenan ba,nima tunda akayi haka yanzu nafison nayi zaman kaina ba nawani ba”
“Amma sameemah……….”
“Karkice komai dan kinsan ba sauraronki zanyi ba”
“Shikenan amma zan baki number BINLAD,saiki nemeshi nasan zai baki inada zaki zauna dan suna neman irinki,nima ina zuwa cikin satinnan dan akwai wani patrol da zasu je”
“Shikenan hakan yayi ni bari na tafi saikin shigo,kuma sannan ki fadawa yayanki kar ya bari na hadu dashi a hanya ko kadan,ke kinsan mai zai faru dan haka ki sanar dashi”
“Zan fadamasa ogah seemah”
Bansami kowa a farlon ba da alama ummeeh da shige dakinta shikuma gogan yah fita,shaheedah ce ke biye a bayana fuskarta tayi narai narai da alama bata son tafiyahta,saidai ni kuma a nawa bangaren tunda naga abinda yah faru naji banason zama a karkashin wani ba iyah gidannasu ba ma,address din wajen na karba da kuma numaber wayarsa kafin na tari taxi.
Bayan na shiga ne na juya naga shaheedah tana matse Kwallah,hakika nima banso mu rabuba saboda ita kadaice kawa mace dana tava yi a rayuwata,amma ni nafita juriyah badai mutum yaga raunina ba kama,ta inda muka banbanta da itah kenan,duk da ta iyah tsiyah amma tanada rauni gakuma shagwaba.ni kuwa wa yaga dutsi.

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤18❤

Tafiyah mukeyi a cikin birnin har muka shiga wajen da babu gidaje sosai sai jeji,ga kuma garin yayi duhu sosai da alama cikin kowanne lokaci ruwa zai iyah kwacewa.
Driver ne yakalleni ganin muna ta shiga cikin jeji har munzo inda babu wani gida amma bance mun iso ba,
“Gaskiya kiyi hakuri amma daganan zan ajiyeki duniyah babu yarda karnaje ke mai cutarwa ce ki cutar dani,kiyi hakuri bazan sake yin gaba ba gashi kuma hadiri ya hadu inason komawa wajen iyalai na ni…………..”
“Yah is a haka zaka iyah saukeni,banason dogon zance”
Bayyi musu ba kuwa yah fara fitomin da kayana daga cikin motarsa saida yagama kafin na bashi kudinsa yayi gaba.
Samun wani wajen kiran waya nayi na zauna saboda wayata babu charge.
Tun daga nesa nake ganin hasken fitilar har yah fara isowa inda nake,ban matsa daga inda nake ba bare na tashi saidai kallon mai tahowa danake duk da bansan wayeba.
Lokacin da suka iso wajena ne nakula ashe mazane guda uku sun saka rain coat bakake,zagayeni sukayi da bindiga kafin daya,daga cikinsu yasa,
“Ke wacece,sannan kuma waya aikoki”
“Bai shafeka da sanin ni wacece ba,saboda ba matsalarka bace”
Kallon na raina musu hankali suka faramin saboda jin amsar dana basu,
“Dolene ki amsa tambaya a wajen ogah binlad,ku daureta yanzunnan,sannan ku rufemata ido,sai iyayenta sun kawo kudi tukun”
Tashi nayi daga zaunen danake ina kallon su,kayana na dauka na rike kafin nace,
“Wanene wanda zan hau mashin din nasa,yazo mu tafi kar dare yayi ga kuma ruwan sai karuwa yakeyi”
Nafada ina kallon hadarin a sama,ko ban kalli fuskokinsu ba amma yanda nayi magana nasan sunyi Mamakin action dinane,hakan a jinina yake bawa mutane mamaki da halina.
Dukkansu tada mashin dinsu sukayi,ni kuwa saida naje gaban ogannasu mai barazanar kafin na dale mashin dinsa ina gyara zaman jakata.
Kara nausawa cikin dajin muka kara yi,munyi tafiyah mai nisa kafin muka iso wani gida da aka yi katangarsa da karfe,masu tsaron bakin wajenne suka bude mana,dukkansu kowa yana rike da manyan bindiga a rataye,kana ganin su kaga manyan yan iska.
A bakin wani babban d’aki muka tsaya,wanda yafi dukkan dakunan wajen girma,shiga sukayi nima nabi Bayan su.
Wani farin balarabene a zaune yasha askin tankwal sai uban gemu kaman zayyi magana,bakar jallabiyace a jikinsa ga idonsa yasha kwalli,a takaice dai jan wuyane kawai.
Sallama yamin na amsa kafin yace,
“Sunana Binlad”
“Nasani basai ka fadaminba”
Yayi Mamakin yanda nayi masa magana babu tsoro amma kuma sai yah basar,
“Baki fadamin sunanki ba”
“Kaima baka tambaya ba”
“Miye sunanki karamar yarinya”
“Sunana sameemah “
“Yayi barkanki da zuwa”
“Toh”
Daga nan na katse maganar tamu ta hanyar zuyawa ina kallon wajen,shima bai sake cewa komai ba sai kareni da kallo kawai dayake wanda inajin yanayin kallonsa a jikina,maganar sa na jiyo yana cewa,
Akwai dokoki a wajennan sannan kuma saboda ke macece akwai matsayin dazaki tsaya bakomai zamu sakaki ba kar shirinmu yah wargaje”,
juyowa nayi Nima ina kallonsa kafin nace,
“Ka barni a tsaye haka ake taryar sabon member ,toh ina jin bacci kuma sannan nagaji dayawa,inayaso koma mai za’a cemin sai gobe kuma”
Daga haka na kalli wanda mukazo tare ina tambayar sa inda zan zauna,binlad ne yayi masa alamar ya kaini kawai inayso sai goben.
Da safe kuwa wata tsohuwa ta shigo hannunta dauke da tea da kuma gurasa,karba nayi na ajiye kafin naje gyara jikina tukunna,saida na shiryah na karyah tukun naji dan aike na shaidamin kiran Ogah,wani dan gyale nasaka, a kaina bayan dogon wandon dayake jikina da kuma riga iyah gwiwa.
Ya u ma kaman jiya yana zaune saidai yasaka rawani,samun kujera nayi na zauna tun baice na zaunaba,
“Ke Baki iyah gaisuwa bane”
“Na iyah amma banayi,kayi hakuri”
“Keee,………..”
“Kana Bata lokacin ka,bayan na fada maka ra’ayina,muwuce wannan shafin kawai,kafadamin menene abinda zanyi kawai”
Buga bencin dake gabansa yayi idonsa yayi jaa,da alama furucina yah bata masa rai,
“Tabbas ke baki sanniba kina bukatar a horar dake,inaso yanzunnan,samad kuyi mata bulala hamsin da dorina”
Matsowa sukayi da niyyar kama hannayena ciki harda wata mata jikinta a murde,dakatar dasu nayi kafin na wuce inda mai bulalar yake,kwanciyah nayi akan table din hankalina kwance.
Saida naji yah irga hamsin tukunna na tashi daga wajen na dawo na zauna akan kujerar danake zaune dazu,
“Yanzu shugaba zaka iyah cigaba da bayaninka tunda hankalinka ya kwanta ka horani din”
Bude baki yayi yana kallona,duk da yana kokarin boyewa amma alamun tsoro ya bayyana a fuskarsa,komawa yayi yah zauna tareda cewa,
“Zaki fara koyon sand’a ko wuce waje batareda wani yah gankiba,sannan nagaba kuma harbi da bindiga saikuma koyon fada”
“Saikuma me?”
“Banson musu ki koyi wannan din tukunna”
“Shikenan and gama ogah”
Tun daga ranar na fara koyon harbi da kuma fada babi dare babu rana,nikadaice mai koyon saboda babu sabon shiga a lokacin shiyasa masu horon ni kadai suke yiwa.
Cikin sati daya na kware wajen harbin bindiga da kuma fada,hatta wanda suke koyamindin sai sunyi dagaske su yi abinda zan aiwatar,labarine ya isa kunnen ogah binlad na himmata da kuma rashin tsoro.
Saboda yanayin nasarar dana taka a cikin wata daya sunana yah fito a cikin wanda zasu je fashi,da farko su Samad sunyi bakin ciki ganin yanda nake taka matakin da saida sukayi shekaru kafin su taka,nikuwa harka ta nake ni kadai ,saidai idan aikine yasamu muke zuwa in group,shima wani lokacin Samad ya jagoranci shirin wani lokacin kuma ni,kuma duk aikin dana jagoranta ba a samun cikas,saboda koda harbi ake nice na ke tarewa saina zo gida kafin na cireshi,idan wani yayimana cikas kuwa cizo kawai nake masa kafin bayan sati daya mutanen mafarkina sun zuk’e jininsa,dan dama abinda suke so kenan,su kuma ko yaushe cikin karamin karfin jiki sukeyi idan nakai musu jinin da suke so.
Bayan kwana biyu shiru banji labarin shaheedah ba duk da tacemin zatazo wajennamu,abinne yabani mamaki hakan yasa na shiga cikin gari da b’adda kama,mai gadinsu na tambaya a gefen gidansu nan yake shaida min kanin babanta yah tafi da itah gidansu wai zayyi aurenta a can,da farko nayi bakin cikin bamu sake haduwa ba,,amma nayi mata murna domin hakan shiyafi dacewa da itah,sama da rayuwar damuke,dan irin wannan rayuwar nikadai yakamata da dungayi tunda hakane kaddarata.
Komawa nayi jikina da sanyi jin bata gidansu ta tafi inda rayuwarta zata inganta,tun kafin na isa na watsar da tunanin ta dan yanzu banason saka wani abu a raina har ya dameni.
Maida himma nayi akan aikinmu ba dare ba rana,dan yanzu nice nake kulada da kowanne shiga da fita,saboda ogah Binlad shida Samad sun tafi kasar Brazil,binciken wani sirri,yanayin yanda abun yake tafiyha har yafi in ogah yananan,saboda sun fi tsorona fiye dashi yamzu,dan kowa yasan halina idan yah aikata abinda banceba.
Ina cikin bincikene na gano wani aiki a gidan sarkin malamai,saboda yanada kudi sosai,sannan duk wani kudi a gidansa yake tarawa.
Shirye shirye muke ba kama hannun yaro,kullum muna cikin binciken yanda zamu aiwatar da shirin.
Tun da yamma,na zabi wanda zasu bini da kuma wanda zasu kulada gida kafin mudawo,babu wanda yayi magana bare musun abinda nace,bindigoginmu muka cika da bullet,duhu yana farawa muka shiga motocinmu sai cikin gari,a bayan gidan muka tsaya muna ganin shige da ficen gidan,wasu motocine suka,fara shigowa zasu kai wajen bakwai,har wajen karfe sha daya amma babu motar da ta fito hakan yasa na bada umarnin mushiga kawai.
Wani daga cikin yaranne yace,
“Amma ogah seemah akwai fah mutane a ciki”
“Nasani ai ko makahuwa ce ni,ubanme mutanen zasuyi mana,idan tsoro kake ka zauna acikin mota,banza lusari kawai,idan kuma suka fito da kudin suka tafi fah,mu mai zamu samu”
“Afuwa Ranki ya Dade”
“Dallah yimin shiru,ku mazaje maza a kafta”
Cikin sanda muka fara dosar gudan,har muka shiga babu wanda yah kulada mu,cikin gidan babu kowa sai haske daya gauraye gidan,ina biye suna bina a baya har muka haura stairs din benin,acan wani daki karshen corridor muka jiyo maganar mutane,da alama suna cikin dakin kenan.
Alama nayiwa na baya su tsaya kafin nayiwa nagefena su biyoni,a bakin kofar muka tsaya sai kuma muka banka kofar da sauri.
Falone mai girman gaske an jereshi da kujeru,manyan malamaine a zaune amma shigarmu kowanne ya tashi ya tsaya yana kikkifta ido,jerin malam na bi da kallo inda idona yasauka akan mu’allim,”dank’ari” nace a raina.
Daga bindigar nayi sama kafin nace wa yaran,
“Maza Ku bincikemin sako da lungu na dakinnan,karku bar ko ina”
“Angama ranki yah dade”
Zagawa nayi ina kallon malaman wajen,tsawa na daka musu cikin sauri suka zube a kasa suna karkarwa,tafiyah nake saida nazo saitin mu’allim kafin na tsaya,sunansa na kira inda yah dago da mamaki da alama yasan muryar,dadai lokacin yarana suka dawo da cewar basuga komai ba,.
Cire hular fuskata nayi ina kallon mu’allim din da shima kallona yake da Mamakin.
“Kayi mamaki koh,nicedai sameemah,wannan itace hanyar danake kai ba wacce kake kokarin dorani ba,inayine saboda tsoronka badan ina so ba,tunda kai ka sanni inaso ka fadawa shugabanku yabani kudi na tafi bana bukatar taba kowa a nan wajen,idan kuma ba hakaba,karkayi tunanin,zaka iyah kallon wannan sameemar”
Tun kafin mu’allim yayi magana na nuna masa yayi shiru saboda ina kallon sanda shugaban yah mikawa yarona kudin ta gefen idona.
Tsayawa nayi a gabansa,bayan ya mika kudin nace,
“Mu zamu tafi saika musu bayanin irin kodar yaran daka siyar kafin ka samu wannan kudin,saboda su sanjaka da wuri kafin lokaci yah kuremusu,muma kuma su daina zargin mun sace kudin marayu kamar yanda ka fadamusu”
Ina gama fadamasa na tunkuda keyarsa da karshen bindigata zuwa gaban sauran malaman nayi gaba.
Sai wajen karfe biyun dare 2:00am,muka koma sansanin mu.
Ogah binlad nasamu a kan kujerarsa a zaune har sannan bai kwanta ba yana jiran isowa ta,kallona yayi da alamar tuhuma na fitar aikin danayi bayanan.
Nima banyi masa magana ba sai mika masa jakar kudin danayi,karba yayi yana zugewa dan ganin menene a ciki,
Dagowa yayi da alamar neman karin bayani,nima shiru nayi banyi magana ba ,dannaga alamar da miskilanci yadawo,
“Baki fadamin wane aiki kukayi aka samu wannan kudin ba”
“Toh ogah kaima baka tambayeni ba ai”
“Hmm kina nan da rashin mutuncinki toh yanzu na tambaya”
Labarin inda muka samu kudin na bashi tun daga farko har karshe,jijjiga kai yayi tareda mikamin alamar jinjina da hannunsa,
“Yayi kyau gobe akwai maganar dazamuyi daku,akwai wanda za’a zaba zasu je Brazil wani aiki,amma sai gobe tukunna,kowa tafiyah yayi ya kwanta,kafin muji mai ogah yake tafe dashi bayan tafiyar tasu.
+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤19❤

Tunda safe ogah Binlad yah taramu domin yanda lavarin yake cinsa kaman arai.
Faraway yayi da cewa,
“Yawwa kaman yanda kukaji nace akwai wani abu,nasan kunga munyi tafiyha nida Samad zuwa kasar Brazil mun hadu da wasu yan uwanmu na can,suke fadamin akwai training daza a yiwa sojojin kasashe na horon hacking,kwarewar harbi da kuma sneaking,(sanda),.
Za’ayi program na tsawon shekara uku,duk wanda yayi nasarar gama wannan horo yah fito da mataki mai kyau toh ba karamin aiki zayyiba,a yanzu haka maganar dananke mun gama yin information na badda kama ga yaranmu guda uku;Na farko Samad ta biyu sameemah sannan kuma da hakeem,saboda shi yayi karatu dama a kan na’ura,sukuma sauran kowa yasan jarumtarsu da kuma boye sirri.
Jin kaman ya gama bayaninsa ne kuma gashi banji gamshashshan bayani ba yasa ni cewa,
“Amma ogah munji abinda kace,saidai munaso kayi mana bayanin a wane irin yanayi zamuje wajenne?”
“Kinyi tambaya mai kyau,ke zakije a matsayin RAUDAH ABDULSALAM,mahaifiyar kice yar najeria babanki kuma dan palastine,zamu baki password akan raudah dakuma fuskar dazaki na sakawa saboda kar a ganeki.
Kai kuma Samad zakaje a matsayin SULAIMAN BIN HUD,sai hakeem kuma a matsayin ABDULHAKEEM BIN MALEEK,na gama bayani kowa za’a bashi information akan sabon sunansa,dakuma training da ogahna zai muku kafin yasaka ku cikin sojoji ta barauniyar hanya,saboda kar a samu matsala ko kadan.
Da farko abinne mukaji shi banbarakwai ,wai zuwa kasar Brazil kuma zama na shekara uku,har mun juya zamu tafi ogah Binlad yakirani,juyowa nayi da alamar ina jinsa,
“Da farko inaso karkiyi wata yarinta a can,tunda har yanzu bakiyi shekara sha bakwai ba,girmanne kawai da kuma zallan kwarewa a harkar teranci,toh kikula sosai karsu gano ke karamace”
Abin mamaki yabani jin yadda ogah Binlad yazageni hankalinsa kuma kwance,nima karkakce kaina nayi kafin nace,
“Toh in hakane shi tsohon yaje mana tunda yana tsoron kar yara suyi shirme idan yah turasu,sannan kuma……….”
Katseni yayi ta hanyar cewa,
“Bana bukatar jin komai,tunda kinji mai na ce kuje allah yah kaimu wani watan”
Tun daga lokacin muka dukufah yin training din yanda zamu boye kamanninmu a cikin ainihin sojoji,ta hanyar sanin abubuwan daya shafesu,lokacin da results wanda zasu tafi yazo kowa mamaki yayi ,domin a cikin wanda zasu tafi candin,a cikin mu dari kowa yah taho daga sansaninsu an zabeshi da kuma wasu sojojin daga wani waje a cikin kasar,dukkan mu iyah mutum goma suka dauka wanda zasu tafi kasar Brazil,abin mamaki babu sunan Samad a ciki.
Bakin cikine kwance a kan fuskarsa ganin zamu tafi nida hakeem banda shi,da farko nayi niyyar hakura nima,amma yanda naga yana bakincikin hakanne yasa nace zanje,dan naga ya zaiyi,kuma zama waje daya ma ai hatsarine inji kifi,gwanda muje muga mai duniyah take ciki a dayah bangaren.
Shiri aka gama mana tsabb muka kama hanya cikin taron sojojin palastine,bisa kasada irin tamu na rayuwa.
Lokacin da muka dira a kasar wani iri naji saboda tsawon shekarata shida nafi sabawa da kasar palastine,a air Port suka saukemu mota tazo daukarmu zuwa masauki.
Tun daga washa gari muka fara aiki ba dare ba rana,wanda cikim saka abu a rai da kuma kwazo banyi wata shida ba saida ya zamo ko ina sunan RAUDAH ne yake zagawa har na fara mantawa da Sunana sameemah in ba Hakeem yakirani muna mu kadai ba.
Sukuwa sojojin palastine har murna suke saboda a cikin tawagarsu nake,shikanasa ogahn duk abinda ban saniba shiyake nunamin domin burinsa na fito da tauraro wanda zai daga kasarsa.
Lokacin da muka shiga shekara ta biyu aiki yah fara tsananta,domin har wajen kaiwa a hari ake turamu,ni ina a cikin rukunin yan hacking amma wani lokacin idan naga yannamu zasu kasa yi,bansan lokacin danake shiga cikin filin ba,da haka ta nan ma nafara koyon aikin sojoji na shiga filin yaki,dan idan na bisu mukanyi sati biyu har wata bamu dawo sansaniba.
Wani lokacin wasu su mutu,wasu kuma su dawo a wahale,mune yan basu taimako da kuma cigaba idan wasu sun gaza.
Tunda nake binsu fili ban taba dawo wa da ciwo ko dayah ba,domin a wajen yake warkewa da kansa cikin yan mintuna,duk da babu wanda ya taba yimin magana nasan kowa na mamaki,saidai suka barshi a matsayin kwarewa ta ce kawai.
Bayan mun shiga shekara ta uku sannan kam na kware a ta bangarori da dama ciki harda abubuwan da ban taba tunanni zan gansu ba ,irin tuka egwuwa,da kuma harba bombs.
Kowa hankalinsa ya tafi yanda zaici gasar karshe saboda yakoma kasarsa cikin abin alfahari da yabo.
A cikin wata na takwas kafin shekarar ta kare muka fara shirye shiryen tafiyah wajen gasa tah karshe,wanda zamu shiga cikon wani bakin dajine mai cike da arna duk wanda yah fito da rai cikin kwana goma toh sune wanda za’a bawa tutar yabo.
Mukuma masu hacking wani mission aka bamu wanda zamuyi bayan wata daya,akan wasu gogaggun barayin hacking a kasar Canada,duk wanda yayi nasara shima shine da tutar yabo.
Shiga nayi cikin yan zuwa daji muka tafi,ko ba komai zan kashe kwarkwatar ido,aikuwa naga abin mamaki,nan akayi ta artabu aka kashe mutane da dama,mu wanda muka fito babu fi mu dari ba,dan ma na taimaki wasu da yawa.
A wajen hacking kuwa kwana muke a gaban computer sai bacci ya kama mu muyi,idan mun farka mu cigaba,mun fi sati muna abu dayah kafin wani yaro a cikin mu yagano lagonsu,muka afakamusu.
Idan aka sakawa abu rana toh sai yazo,yau mune a tsaye a fili da kayan sojoji muna kiran karbar sakamako,tun waccen satin aka fara sallamar wanda sukayi nasara,dayake mune Batch C,muna kasar Brazil,yayinda Batch A suke America,sai Batch B a Canada.
Nice na karbi numaber yabo ta uku,bayan wasu guda biyu a kasashe daban daban sun karba.
Daga kyautar nayi a hannuna,ta silver sai sheki take,anyi alamar soja mace a jiki da kuma sunana wato RAUDAH, yayinda a daya bangaren kunnuwa na suke jiyomin karar sauti tafi rafff rafff da kuma harbin bindiga,kuma duk ni akeyiwa.
Kowa murna yakeyi acikinmu zai koma gida da irin nasarar daya samo,wanda suka mutu kuma saidai muce Allah ya jikansu da rahama.
Shugaban tawagar palastine ne ya taramu murna a cikinsa kamar ba gobe,bakinsa yaki rufuwa saboda murnanar nazo tah uku,a cikin kasashe da dama,magana yah faracikin harshen turanci maimakon larabci,wanda yasan kowa yah iyah saboda zamanmu cikinsu.
Kowa zuwa yayi yah kwanta da niyyar gobe za’a fara shirye shiryen komawa gida jibi kuma mu tafi,
Wani duhu nake gani saidai duk da bana gani sosai nasan gidanmune na Nigeria,wutace take cin cikin gidan amma kowa yah ki kaiwa taimako,gani na nayi a tsaye a gefen gidan mutanen cikin gidan suna ta ihuu amma babu wanda ya kulada ni,wani mutum ne naga yazo wucewa na ja rigarsa,tsayawa yayi yana kallona kafin nace,
“Bawa allah baka ganin suna neman taimakonka ne?”
“Nagani amma ke da kike yar gidanma aikin barshi ina kuma yani,ke mai zai hana kidawo ki taimakesu hannunka a baya rubewa kayanke ka zefar,saidai kayi masa magani koda kuwa maganin akwai wahala har ka samu yah warke……..kidawo gida,saboda wanda yabar gida ,gida ya barshi.


Da sauri na tashi daga kan katifata jikina duk gumi,mafarkin danayi kuwa har sannan yana ta dawomin cikin kaina,babu abinda nakeson gani sai kasata Nigeria,zaman kasar wasun yah isa haka.
Filin jirgi muka iso kowa yasha kayansa yana jan trolly a kasa,tafiyah muke cikim tawagarmu tah yan palastine kowa ka ganshi murna yake saboda nasarar da aka samu.
A waiting room muka zauna muna jiran sunanmu yazo layi zuwa jirgin palastine din,shugabanmu ne yah fita shida wani daga cikinmu zuwa dubo wani abu wanda bamu sani ba.
Sunana ne yake amsa kuwwa a jirgin da zai tafi Nigeria,wato SAMEEMAH UMAR,tashi nayi hankali kwance na maida glass idona tareda jan trollyn na nufi hanyar jirgin,Hakeem ne yah ankare dani tunda dama yasan sunana,hakan yasa sauran ma suka farga da jirgin danake kokarin hawa,saurin riko hannun doguwar rigata yayi tareda cewa,
“Kee sameemah mai kike kokarin yine,wannan fah ba jirgin kasarmu bane”
“Eh ba jirgin kasarku bane,amma ni jirgin kasarmune ai,koh baka ganine”
“Hankalinki d’aya kuwa,kinsan mai kike shirin aikatawa,idan ogah Binlad yagano mai zakice,kinfi kowa sanin ya matsu ki dawo saboda nasarar da kika ciyo”
“Toh so what Ubana ne shidin,kuma ta ina zai hadu dani din,daga yau babu wanda zai sake ganina a cikinku saidai tarihina,dama shine abinda nake barwa duk wanda muka zauna,ni zan tafi kasarmu nasara kuma kai ta shafa bata shafenba,daga nan ma bazan sake maganar ta ba”
Har na fisge hannuna na tafi,sai kuma najuyo,har sannan yana tsaye kaman kungi da Mamakin abinda na aikata,Murmushi nayi masa tareda cewa,
“Ka gaidamin kowa idan ka isa lafiyah,musamman ogah,kace ina yi masa missing😘😘😘”
Karfe biyu na rana dadai na sauka a kasata wato uwa Nigeria,tundaga yanayin mutanen nasan Nigeria ce kam,a garin abuja muka sauka,ana tah hayaniya wai wani dan sanda sai yah caje wata mata a airport din,duk da ba hausa nakeji sosai ba a wajen saboda dadewa da nayi banyiba,amma na cafki wasu kalmomin kuma nasan shine baida gaskiya.
Rike hannunsa nayi wanda yake kokarin dorawa a kugun matar,wanda hakan yasa fadan yah dawo kaina,matsowa kusa dani yake wai nima sai ya cajeni,banyi tsammaniba kawai naji hannunsa a kan kirjina,bansan lokacin dana sauke masa dukkan training din danayi ba na tsawon shekara uku akan fuskarsa ta hanyar zabga masa mari.
Tun kan na sauke hannuna na nemeshi na rasa ashe yah zube kasa sumamme,karfe naji a hannuna saida na duba ashe ankwa ce suka sakamin dan zuwa police station,banyi musu ba na bisu muka tafi inda suka bukata,saboda koda zanyi magana ba zasu gane so sosai ba hausar tawa sai a hankali.
File suka fara cikewa akan nayi attemp din kashe dan sanda ,nidai ban ce musu komai ba har suka gama rubuce rubucensu suka gama,a raina nace mai hali baya fasawa,wato mutanenemu na Nigeria sai a hankali wajen san kai sa kuma yin hukuncin zalunci,wannan kam sun rufe kofah a kai.
Prison a ka turani kasancewa babu wanda zai min beli na tsawon wata shida,banji komai a raina ba,allah na tuba nayi shekara shida ma a prison ai ,menene kuma wata shida ,kaman gobene,kuma wallahi tunda a prison din duke aiki dukkan su,zasu ci ubansu a guna sai sun kwammaci sun sallameni yah fiye musu,bari kawai a dan buga wasan kafin yah kare ………………….muje zuwa😀😀😀😀😀😀

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤20❤

Tun daga bakin kofar prison din nake yah mutsa fuska ganin yanda wajen yake duk babu tsari ko kadan,wani daki aka kaini wai shine na mata,babu kowa a ciki sai wasu mata tula tula guda biyu a gefe suna zaune da kayan prison din a jikinsu.
KO magana banyi musu ba na kade wani waje na zauna ina kallon wani gefen daban,muryar dayar naji tana min magana cikin wata hausarta da duk yare ya gauraya da itah.
‘Ke baki ganin mutanene da bazaki kulasu ba”
“Toh miye saina kulaku,tare mukazo daku,ko kuma zamanku nakeyi a wajen”
Dayar ce ta matso tana wani hura kirji itah ga yar iska,nima gyara zamana nayi domin naji mai zata ce,cikin rashin sani naji ta kamani da kokuwa mun dungura kasa,matsawa tayi tana huci itah a dole ga karamar yar iska.
Da farko takaici abin yabani ganin yanda tah batamin kayana da datti,dagowa nayi ina kallonta dadai da isowar wani ma’aikacin tsaro wajen,kallona yakeyi tareda dariyah yana cewa,
“Bake yar iska ba hada marin ASP,yanzu zaki fadawa yan garinku a cikin wannan masifaffun matan,dama ba’a saka kowa a cikinsu,saboda karyah mutane sukeyi,yanzu zamuga bakin rashin kunyarki yarinya”
Haushi maganar tasa ta bani,kafin nace masa,
Kana nufin kenan koh karyani sukayi babu wanda zai dau mataki?”
“Kwarai kuwa”
Murmushin jin dadi nayi kafin nace,
“hakan babu matsala ,bari a fara buga wasan”
Tun kafin na gama magana na dauki buleliyar cikinsu na duma tah da kasa,dimmmm saida cell din yah Amanda wani vibrate,koh motsi batayi ba sai wani nishi da tayi na wahala,nufar dayar itah ma nayi fuskata dauke da wani evil murmushi,ihu ta fara tana neman taimako,wanda shima ganin abinda yah faru kaman yah daskare haka yayi shiru.
Labari ne yaje kunnen DPO,inda aka kiramu nida su,tsura mana ido yayi da alamar neman karin bayani.
Cikin sauri kuwa suka zayyane masa,hadda cewa wai ni ce na fara bugata da sumunti,nidai bance komai ba har naji DPO yana cewa a kaini cell din maza,kallonsa suke da mamaki,jin ina mace yace a kaini cell din maza,sannan laifinna ya nunku zuwa shekara guda ciff.
Jana sukayi muka nufi wajen mazan har sannan ko kala banceba.
Wajen mazan yafi girma sosai saboda suna da yawa a wajen,ni hakanma yafimin saboda ba fiye son zama da mata nake ba,sun faye rainin hankali.
Cikin sati biyu muka saba dasu,saboda duk abinda suke tsoron yi ninake aikatawa,zuwa lokacin hausata ta fara dawowa normal saboda yanda nakeyinta akai akai.
Masu shaye shayen cikinsu kuwa in sujjada nace sumin zasuyi,saboda dare nake bi na tsallaka fence cikin sauki (saboda training danayi a Brazil),na sayo musu a cikin gari,yan iska kuwa harka ta bude saboda sun samu jagorancina,kullum dare za’a raba ana hira kafin kowa yah tafi yah kwanta,daki daban na ware nace musu nawane,babu musu kuwa suka barmin shi,wasu yan kusan yankinmu na hadu dasu a wajen,suke bani labarin yanda garinmu yasanja,suma an kamasune bayan sunyi laifi a garin abuja.
Mikewa nayi da sauri,kkwa saida yah kalleni dan ganin mai yah ke faruwa,hade fuska nayi babu alamar wasa nace,
“Wayake son yabini garinmu?”
Kusan mutane ashirinne suka daga hannu,ina ganin haka nace,
“Shikenan an gama ,gobe zamu kama hanyar tafiyah da safe bayan an sallamemu,dan tunda naji labarin gida toh nafasa karisa wata goman,tafiyah zanyi kawai”
Kallona suke da mamaki,musamman yanda na hade rai sun san da gaske nake,tsallakesu nayi na wuce,har nayi nisa na juyo na kallesu,
“Kowa yah me yah kwanta kafin gone mu tafi,zanje wani waje sai na dawo”
Ina fita ta fence ban same KO ina ba sai gidan DPO,dayake police quarter da wuta,haske ya garwaye ko ina,wata sanda na fara cikin kwarewa kamar mage na shiga cikin gidan.
A falo na tsaya babu kowa a wajen amma ina jin hayaniyarsu shida matarsa a cikin daki,wasu kuloli na gani a akan dining table,ai kuwa idona yayimin tozali da wasu kaji a ciki sun sha farfesu,zama nayi na fara ci hankali kwance kaman ina cikin gidanmu.
Ban kai ga cinyewa ba DPO yah fito daga cin shida matarsa suna min kallon mamaki,nuna ni yakeyi da yatsa yana kokarin fito da waya a aljihunsa,dagatar dashi nayi tah hanyar daukar wuka na yanka hannuna na hagun,
Jikinsa ne yah fara karkarwa ganin yanda wajen yake komawa yanda yake,komawa nayi na zauna bayan na maida wukar inda take,
“Karka daga hankali nka ka dagawa matarka ma,naga kaman kudin sabin aurene,koda ka kira wannan karnikannaka (yan sanda) babu abinda zasuyimin,dan haka ka saurareni da kyau,……….inaso gobe idan kaje aiki,abinda zaka farayi shine bugamin takardar sallama nida yarana guda goma,idan kuma ka barshi sai gobe,toh wallahi daga kai har matarka a duk fadin Nigeria banga mai hanani juya rayuwarku zuwa yanda bakwa tsammaniba,hmmmmmm kai karma kayi mana”
“Zanyi wallahi zanyi,ni daman daga ganinki nasan ba mutum bace ke”
“Nidai na fadamaka”har na fita daga gidan na dawo nace wa matar tasa,
“Abincin ki yayi dadi sosai,kiyi hakuri na raguza miki miji,nagode sosai”
Da safe kuwa tun kafin na karya saiga yan sanda guda biyu sunzo kirana,tashi nayi na bisu muka tafi office din.
Tun daga shigowa ta da muka hada ido da DPO,yah dauke fuskarsa da sauri,nima bance komai ba har yah mikomin takarda ta,sunayen dana bashine su “burgu”naga an buga tasu sallamr ma.
A ranar bamu kwana ba a garin abuja sai garinmu kuma gidan mu wato “GIDAN GANDU”.
Tun daga shigowata garin nake ganin sanji da dama,saboda tsawon shekarata goma bana garin sai gashi na dawo. Da wata yarinya muka fara haduwa a bakin kofah,bansanta ba amma daga gani yar gidan inna larai ce saboda yanda suke kama sosai,itam kallona take da mamaki kafin ta ruga kofarsu da sauri,mutanen gidanne suka fara fitowa ciki harda inna ramatu,wanda ta dan fara manyanta saboda shekaru.
“Kuttt sameemah dama kina raye baki mutuba?”.
“Ga shi kuwa kin ganni,inso kike na mutu sai ki kasheni yanzu ma lokaci ai bai kuremikiba”
Kowa shiru yayi yana bina da mamaki,gashi na wuce duka bare su dakeni su huce,dakin mahaifiyata na tafi wanda nasan shine yan matan gidan suke,matsar da kayan wata nayi a wajen danaga yafimin kafin na ajiye jakata a wajen.
Tunda nafita bani na dawoba sai dare dauke da kayan amfani,wanda na siyo da kudina,su burgune suka shigomin dasu dayake shima dan garinne,biyar ne a cikinsu ba yan garinmu ba kawai.
Sannu a sannu na fara kafa kungiyata harda su iliyah wanda suma suka zama yan iskan kansu,mika wuyah sukayi ga kungiyata saboda basu manta ceton rayuwarsu danayi ba shekara goma da suka wuce,hakanne yasa yan kungiyata suke bani daraja,saboda babu wanda na jawoshi da kudi saidai sadaukarwar daanyi masa ko kuma wani taimako.

**** ****** *****””
DAWOWA CIKIN LABARI.

Kowa tsayawa yayi yana kallon sameemah,ciki harda wanda yawu yah bushe a bakinsa saboda mamaki.
Ta shi sameemah tayi daga kan kujerar da take tana kade rigarta,
“Toh yanzu kunji labarina,kuma saura naji zancen a bakin wani,ban yadda wani ya fitar zancennanba,sannan munyi magana da alhaji labiru zan hau kan kujerar shigabar vigilantee ta garinnan,dukkanku za’a debeku aiki,kuma banason shashanci ku kiyaye,ku kuma (tafada tana nuna yaran da suka ganta lokacin da sukayi fada da yaron bubu jini da kuma dukkan yarannasa),tunda kun ji labarina toh kun dawo yan kungiyar nan,daku za’a fara aikin vigilantee,musamman matan kune masu kamomin wani idan yah shiga Gidan su,daga wani satin za’a fara koyar da horo wanda zan dauki nauyi a gidan horona dayake cikin jeji”
Dukkansu amsawa sukayi da cewar,
“Mun ji shugaba kuma mun mika wuyah”
“Yadai fi muku,sauran naji wani yayi abinda ban saka shiba kuma”
“Babu wanda zayyi ma ranki ya dade”
Motarta ta nufa tana kakkada key,saida ta zauna na dan wani lokaci kafin ta ja motar tabar wajen,sai kurar tashinta me kawai yah saura.
Wata bakar motace tah faka a gaban gidan gandun,baka mai sheki amma ba wacce sameemah ta iyo kwacenta a wajen alhaji bala bace.
Saleemah ceh takalli major sameer ganin ya faka a wani waje kaman gwalalo,shima kallonta yayi amma baice komai ba,
“Honey naga ka tsaya koh motar ce ta baci kai?”
“Ahah ba motace tah baci ba anzo gidanne”
“Gida kuma honey wannan fah kaman ba gida bane,baka ganin yanda yaje ne”
“Saleemah ya fah isheki haka,tun kafin mu taho kike wani bata rai,miye nufinki,bazaki zo gidanmu ba kenan,saidai ni nayi ta zuwa gidanku,toh bazai yiyu ba wannan shine gidan mu kuma sai munyi sati guda kafin mu tafi,dan haka kima shirya zaman cikin gidannan”
Hawayene yafara zubowa a cikin idonta tana wani cuna baki,
“Nikam bazan iyah zama a cikin gidannan ba,mai laifin ka kaimu hotel sai mu dunga zuwa,gaskiya d’ana zayyi gudawa a cikin gidannan”
“Eh Kat d’anki yayi gudawa ko?,toh ni na mutu mana kafin ki ganni,kuma sai yanzu kike son dan”
“Eh KO ma menene ni bazan zauna ba”
Ganin abinnata bazai kareba ne yasa yah fito daga cikin motar yah barta itah kadai tana ta mita da shagwabarta,tsayawa tayi da mitar da take ganin wata mota mai irin tasu bak’a ta shawo hanyar layin da suke,saleemah ceh ta fito daga cikin motar tareda tsayawa a kusa da sameer din,tambayar sa take saboda tsabar gulma tana cinta,
“Honey dama akwai irin wannan motar acikin garinnan ne,tunda muka shigo ko karamar mota ban ganiba amma ji wannan motar kuma a hanyar gidanannan?”
“Kin isheni da surutu ki tsaya ki gani mana”
A bangaren sameemah kuwa tunda ta shawo hanyar gidannasu tah kulada motar kofar gidan ,kuma ta gane sarai suwaye a cikin motar,tana zuwa fakawa tayi a gefensu tareda fitowa daga cikin motar tana feduwa.
Dukkansu kallon ta sukayi da Mamaki harda saleemah wanda bata santa ba,ina kuma ga uwar gayyah yayannata.
Tahowa tayi tah gabansu zata wuce sameer din yayi saurin shan gabanta tareda cewa,
“Ke ubanwa ya baki wannan motar haka”
“Uban wani ne yabani itah mana”
“Akan wane dalilin,wane irin aiki kike masa haka”
“Akan dalilin na bashi budurcina ne,batun aikin danake masa kuma,irin aikin da matarka take maka duk dare shi nake yi masa nima,har yah bani itah”
…………,.😲😲😲😲

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤21❤

Baki yasake yana bin sameemah da kallon mamaki,wanda ta shige gidan tana feduwa da karfi.
Sun fi minti goma a,tsaye kafin yayi karfin halin jan hannun saleema suka shiga gidan.
Tun daga bakin kofa ake tah muranar isowarsu,yayinda saleemah take tah makewa a jikin sameer kaman taga kashi,lura da hakan da yayi ne yasa shi tureta daga jikinsa yana aika mata kallon tah shiga hankalinta,itama wayancewa tayi tana aika musu murmushin.
Cikin kankanin lokaci aka shimfida musu tabarma a tsakar gidan suna gaisawa,shima baba umaru yana gida saboda yasan da zuwan dannasa bare kuma su baba shehu kodan gulmama ai,kowa shiru yayi da zancen sa ganin shirga shirgan karnuka sun shigo gidan suna d’aga jela,saleemah ceh tayi tsalle ta haye kan sameer tana kikkifta ido,dan dama kaman akan kaya haka take ji,wucewa sukayi tareda nufar dakin da sameemah take ciki,sameer ne yayi karfin halin cewa,
“Karnukan fah,kuma a cikin gida haka”
“Uhmmmm”
Shinen abinda kowa yace tareda kawar da zancen.Sameemah ceh tah fito daga dakinsu daga itah sai wata vest da dogon wando,ledar nama ce a hannun ta karnukan sai binta sukeyi har suka je wajen kejinsu.
Ganin koh kallon inda suke sameemah batayi bane bare kuma gaisuwa tah hada su,yasa Baaba umaru cewa,
“Keh sameemah baki ga dan uwanki da matarsa bane,kika tsaya baki zo kun gaisaba”
“Mun gaisa mana dashi a waje,wace gaisuwar kuma yakeson kara ji daga wannan”
Sameer ne ya mike tsaye cikin zuciyah irinta sojoji yace,
“Ke anya kuwa hankalinki daya dazu kin yimin rashin kunyah yanzu kuma kina yiwa harda yan gida,ana miki magana hankalinki yana kan karnuka,wai tukunnama menene na ajiye karnuka a cikin gida,in kinyi wasa yanzu zansa a fita dasu kuma bazaki kara ganinsu ba”
Inna larai ce tah tashi cikin jin dadi tace,
“Yawwa gwanda da kazo ko zakayi maganin ta,wlh ta addabemu matuka”
Kowa fara fadan albarkacin bakinsa yayi.
Duk abinda suke sameemah bata koh motsaba ,saida kowa yagama fadan abinda yake bakinsa kafin ta tafa hannunta raffffff,tsitt kakeji kaman anyi ruwa an dauke,takawa take a hankali har ta kai gaban sameer numfashin su yana bugar na juna,
“Wace rashin kinyar na maka,fadamin itah naji,amsar dana baka dazu bayan ka tambayenine rashin kunya ko kuma dan naki zuwa na gaisheku kaida matarka,wanne ne daga ciki?,sannan kuma da kake cewa zaka batar da karnukana bazan sake ganinsu ba koh?,dan allah bismillah kada ka fasa,kaima kuwa kai kadai zaka koma inda ka fito batareda danka da matarka ba,dan nima saina batar dasu”
Kowa zaro ido yayi tareda shan jinin jikinsa jin abinda sameemah tace,musamman ma saleemah da taji ana cewa za’a batar da itah,cikin kankanin lokaci tah tsure.
Kallon kallo aka fara tsakanin sameemah da sameer,shi yana mata kallon Mamakin yanda ta zama ita kuma tana masa kallon zaka san koni wacece.
Katse kallon da suke ita da yannata tayi sanadiyyar karar da wayar ta tayi a cikin aljihun wandonta,saida ta danyi yar karamar tsuka kafin tah daga kiran tana hade girar kasa da sama,
“Kai miyene wai kuka dameni,naga yanzunnan na dawo gida ko hutawa banyiba”
Dayake wayar tana handsfree kanajin abinda ake fada a daya bangaren,
“Ogah Ranki ya Dade wallahi duk bayanin da mukayi masa akan kece kika turomu yaki bada hadin kai,yanzu haka muna wajensa ma”
“Okay inason information gameda komai nasa nan da dare,sannan ina sabin yan kungiya suke,dafatan kun fara nuna musu aiki kaman yanda nace”
“Eh shugaba,matan sun bi su uban dawa wajen campaign din alhaji Sama’ila,sauran kuma har yanzu jikinsu a mace yake tunda sukaga abinda kikayiwa ogahnsu wanda yake asibiti”
“Karka dam u dasu zasu ware ,ka kawo min information kafin dare ina jiranka”
“Shikenan ogah allah yaja da ranki”
Sauke wayar tayi tareda yah mutsa fuska ganin yanayin reaction din fuskar su ya nuna duk sunji abinda aka fada a cikin wayar.
Barin wajen tayi ,ko a jikinta maganar da tayi.
Su sameerah ne suka dauki kayan saleemah wanda suke kira da anty saleemah zuwa dakinsu,binsu takeyi a baya kaman anyi mata dole,su kuwa sai shige mata sukeyi ganin yanda tasha kaya na girma da alfarma.
Shikuwa sameer dakin mazan gidan yah tafi da kayansa.yah ajiye jakarsa kenan yana kallon dakin saiga manjo yah shigo yana kirga kudi a hannunsa,sai wuriwuri yake da ido da alama baya son wani yah ganshi,sameer ne ya katseshi daga diridirin dayake ta hanyar cewa,
“Ah MUSA dama kana nan ,na shigo ban ganka ba tun dazu”
“Lah wa nake gani kaman sameer,shege kace kaine dai nake gani,wallahi daka ganni nan wani abun arzikine yasameni,da banso na fadamaka ba amma tunda kaima babban yayantane,toh bari a yi zancen dakai”
“Menene yah faru Musa(manjo)?”
“Ai in fadamaka abokina ne sule maye yake son seemah jar wuyah kaman ya maida ta cikinsa,toh shine nace yah kawo nairah dubu talatin casss ba ragi ba kari na bashi itah,ni zan shige masa a daura aure,kagansu nan ya bani su cifff,ai ni kam yau kakata ta yanke saka,irin wannan kudi haka inba sata nayi ba har saina kai ga filo da kasa ban sami kamarsu ba”
Mamakine yakama sameer jin abinda manjo yake fada,
“Amma Musa Kaman naji kace na neman aurenta ne,kuma yanda naga fuskarka kaman so kake ka rike kudin,kuma kana tunanin yanda nima iyah yau na hadu da itah zata bari ka aurarta a haka kuwa?”
“Kaga tsaya sameer shiyasa fah dama nake tah buyah kar a ganni,toh gashi kaima kana cikin yan bakin cikin ashe,kudi babu mai hanani cinsu ,batun kuma karta yarda ai dolenta ma ,ina yayanta ta kawomin iyah shege”
Daga haka sameer bai sake cewa komai ba sai jijjiga kai kawai da yayi.
A dakin su sameemah kuwa,iyah sameerah ce sai zainab a zaune suna ta zubawa saleemah labari,wani ta amsa wani ta gwalesu ko kuma ta tayi shiru,amma da yake basuda zuciyah kkh a jikinsu,suna cikin hirar ne salma ta shigo itama tana wani yatsina fuska dan kana ganinta kasan haushin saleemah takeji ,koh miye dalilinta oho.
Sameerah ce ta washe baki bayan saleemah tah yabawa zainaba wata magana ta rashin mutumci,
“Amma anty saleemah gaskiya kina burgeni dazan samu dama ai da nabiku porthacourt koba komai zan tayaki ayyuka acan,tunda a nan din na rasa miji kinga acan din watakil saina samu mai dan romo nima,nasan yah sameer din ma bazai hanaba”
Saida saleemah tayi mata kallon mamaki kafin tace,
“Lallai kam ki bimu,waya ce miki ina bujatar yar aiki,nida nake sanja yan aiki sau kusan goma ma a sati daya,sannan sashe guda aka warewa masu yimin hidima,kinga kuwa bana bukatar yar aiki,sannan dakike cewa yaynki bazai hanaba,dama bashi keda ikon wannan ba nice nan,sai wanda na yadda kafin yah zauna a cikin gida”
Dariyah sameerah tayi cikin jin kunyar maganar ta da kuma irin amsar da aka bata,saidai bata da ikon nuna cewa taji haushi.
Duk maganar dasuke sameemah tana jinsu dan shigowarta kenan daga waje.
Tsayawa tayi akan katifarta ganin jaka da kuma gyalen saleemah akan gadonnata,daukarsu tayi ta wurgawa saleemah akan fuskarta kafin ta zauna a bakin katifar.
Binta sukayi da kallo ganin abinda tayiwa saleeman,sameerah ce tayi karfin halin cewa,
“Kefah sameemah bakida mutunci,yanzu a gaban bakon ma saikin nuna halinki,toh akan gadonnaki zata kwanta in yaso saiki kwana a shimfidin wata,haka inna ramatu tace”
“Saboda ubanta ne yasiyamin katifar kome,ko kuma itah inna ramatun ce ta saya mun iye?”
Cikin bacin rai saleemah ta fara yiwa sameemah magana,
“Ke na kula tun sanda na shigo garinnan bakida mutunci kina ji da tashen rashin mutunci,toh bari kiji na fadamiki ke baki kai ki ganni ba ina dan dalilin nazo gidanku ba,bare har kiyi misayar miyau dani,ke kinsa inda nake rayuwa kuwa da har kike takama da wata katifa”
“Hmm lallai kina bukatar na koya miki hankali,da farko uban me yakawoki gidan namu da har naganki,koh nice na take Naje inda kike,sannan idan harkin isa yanda kikace da sai kice bazaki zo garin ba mana,kodai kina tsoron mijinnaki ne kar ya sakeki?,toh ki bude kunnenki kiji,daga ke har shi a tafin hannuna kuke,ke inkinyi wasa saina shiga har Gidan ubannaki na saka masa wuka a wuyah ,kuma idan kina musu ki bani lokaci da kuma address ki gani”
Tsayawa tayi da maganar ta furzar da iska idonta yayi ja,dan daga gani dama a cikin fushi take,wiwi ta,dakko a cikin kwarkwaro ta banka mata wuta ta fara zuga tana fesarwa ta hanci da baki.
Karkade tokar tayi kafin ta zawo wata leda da ta shigo da itah,kaza ce a ciki taji jar suyah da dakuma lemo mai sanyi.
Saida taci tayi nak kafin tah koma kan katifar ta zauna tana daddanna waya. Duk abinda take suna kallonta amma babu wanda yayi tunanin magana saboda abin yafi karfinsu sosai.
Kirane ya shigo wayar tata inda ta daga tana cewa,
“Eh yah kawomin information din dazu sannan nagani sosai,kah saurari abinda zan fadamaka,inaso ku satomin kanwarsa a gida ku kaimin itah gidan horo ,amma ban yadda kuyi mata komai ba ,har abinci ku bata kafin naje wajenta,ba lallai naje da wuri ba saboda zanje karbar kudina a wajen alhaji Sama’ila gobe”
Gyara shimfidin tayi taja bargo sai bacci,abinda ta iyah kenan.
Sameerah ceh ta kalli su Salma lokacin da sameemah taja numfashi bacci na farko tace,
“Tabbbb yanzu ku gani,toh ni ko a tarihi ban taba ganin mai irin halin Sameemah wlh ba karamin tsoro take baniba”
Basuja hirar da yawa ba suma suka kwanta dan kar tsautsayi yasa ta jisu su shiga uku.
Fitowa tayi daga dakinnasu cikin shiri zata je wani waje,babu kowa a kofar tasu saboda yanayin lokaci daya tafi sosai.
Baba umarune ya tsayar da itah har takai bakin kofa ,juyowa tayi kafin kuma yam hankalin suka ce ta dawo da baya,
“Ina kwana “shine kawai abinda tace daga nan kuma tayi shiru,
“Lafiyah kalau saidai ba dan gaisuwa na tsayar dake ba,wani waje zakuje dake da yayanki da kuma iyalansa,saiki shiryah tunda ba yau zaku dawoba”
“Wani waje kuma ina kenan”
“Dangin mahaifiyar ki ko shima bazaki jeba ne”
“Ahah zanje amma ba yanzu ba,akwai abinda nake idan na gama saina je daga baya ai nasan garin sosai,kuma nafison tafiyah ni kadai”
“Hungo naki(yafada yana bata yatsu biyar),dasu zaku tafi kuma a mota daya saura kuma naji kince bazaki jeba kumadu,kije maza ki dauko kayanki koh guda biyu kizo ku tafi”
Daga ido tayi tana kallon sameer wanda yake ta zabga mata harara shikadai,itama ramawa tayi tareda mutstsika baki kafin kuma tah cije lebe alamar zasu kwala.
Komawa dakin tayi da dauko wani dan karamin trolly,na irin tafiyah kwana biyu,ficewa tayi zuwa wajen ko sake kallon baba umaru batayi ba,tun a hanya take hango saleemah a gaban motar sameer din,itama itah take kallo ido cikin ido.

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤22❤

Budewa motar tayi ta shiga tareda maida kofar da karfi kaman zata cireta,itah dai saleemah bata kuta ba,dan abinda ya isheta yah isheta na zuwa kauyen da za’ayi na su inna hajara,tana ganin an kawota lungunan cikin zariyah a she ga kauye can za’aje.
Shigowa yayi cikin motar suka fara tafiyha a cikin motah,sunyi tafiyah mai nisa amma babu wanda yace wani abu,saleemah ce ma ta kalli sameer da alamun shagwaba tace,
“Honey fushi kake da ni?”
“Haka nace miki,abinda kike yi ne banaso bawai fushi dakeba,bai kamata ki dunga kushe gidanmu a gabana ba”
“Toh na DA in a”
Takaicine ya isheta tana bayan mota,ga an katse mata aikinta na rana guda an hada ta da wayannan shashsashun waje daya a cikin motah,ganin abin yayi waya ne yasata daka wata uwar tsuka kafin ta fuske ta kalli window,dukkansu juyiwa sukayi suna kallonta amma babu dama sanin mai ya sameta tunda ba magana zata musu ba.
Tin daga bakin kofar shiga garin yara suke ta shafa motar saboda yanayin kauyene sosai.
Wani gida suka shiga wanda aka zagayeshi da dangar kara,tun daga cikin gidan suke jiyo murnar yara suna fadan isowarsu.
Irin tabarmar karauno aka shimfida ga kuma kindirmo(nonon shanu)da kuma kaji da aka dafa saboda taryarsu,dan kowa yasan mutunci irin na inna hajara shiyasa komai idan daga wajenta ne toh yan uwanta basa kyashin nuna tasu bajintar,saidai marar nuna godiyah ya kushe musu,irin su saleemah dan fafur kin saka wani abu a cikinta tayi,itah a dole wai jagwalgwalone,sukuwa su sameer zama sukayi suka ci abincin sosai.
Dan duk duniya sameemah babu wanda take ganin mutuncinsa badan yah tursasata ba ya mahaifin ummah ta wato Malam Mansur,saboda ya nuna mata soyayya matuka,musamman idan suka zo da inna hajara a wajensa take zama har su tafi yana mata labarai da kuma jan kunne,duk da bata so amma tana kokarin ce masa zata gyara.
Mahaifiyar su inna hajarance ta zauna ana gaisawa Sannan wani lokacin idan ana tadi sai a dunga sako irin abubuwan da inna hajaran tayi a baya,sameemah ce tayi kuncin da fuska can kuma da taga abin bazai yiyu ba said tace,
“Nikam iyah in san samu ne kidaina sako ummah in kina yin zanjenki kiyi zancenki kawai,bai kamata zance marar amfani a dunga saka ta ba gaskiya”
Baki ta sake tana kallon sameemah wanda ta hade fuska tana wani bada umarnin a daina zancen ummahn tah,
“Iyeee lallaima yarinyar nan toh kinci gidanku,bazan daina zancennata ba idan yar kice ke kika haifeta”
“Toh ina ummah tace koh,to nace a daina haka kawai sai a dunga zancenta a kan abu marar amfani,ko kuma a dunga bada labarinta ga mutum marar amfani,hakan bai daceba”
Sameer ne ya kalli sameemah wanda ta wani hade rai tana zuba tijara,sai a sannan ya gano meyasa take fadan,dan kawai an fadawa saleemah labarinta ne yasa take wannan tsiyar,jijjiga kai yayi yana Mamakin yanda yarinyar ta zama bayan tafiyarsa,kwata kwata ta koma kaman an sanja ta.
Malam mansur ne ya shigo daga gona da fartanya a rataye a kafadarsa,
“Lahh baki mukayi a garin,wa nake gani kaman sameer,ko dai gizone yake min kai?”
Iyah ce ta amshe da cewar,
“Ba gizo bane shine yazo da matarsa gashi nan,wata sabon gani a garin zariyah”
“Toh madallah sannunku da zuwa yah iyalai tunda naga an fara tarawa koh?”
Sunkuyar dakai sameer yayi yana sosa keyah kafin yace,
“Iyalai alhamdulillah,mun sameku lafiya dai ko”
“Lafiyah alhamdulillah,yah iyalinnan ka bata magana ne”
Kunya ce ta kama sameer da halin saleemah na rashi girmama mutane,dan duk abinda ake idonta akan malam din amma gaisuwa ta kasa hadata dashi,shikuwa irin mutannene masu nuna wa mutum kuskurensa sannan bayason raini ko kadan shiyasa ko wasan kaka baya yi.
Jungurarta yayi yana mata alama da ido,saida taga ransa ya baci kafin ta gaisheshi tana wani yah tsina fuska.
Shima dayake baya daukar raini amsawa yayi ciki ciki kafin yayi hanyar dakinsa.
Iyah ce takallesu tareda cewa,
“Zaku kwana mana ne koh kuma akan hanya kuke kaga saimuji mai za’ayi”
Saleemah ce ta washe bakinta dan dama tun dazu take so taji anyi zancen tafiyah,tun kafin ta bude baki sameemah tayi saurin cewa,
“Eh iyah kwana zamuyi mana ba yau zamu tafi ba”
Takaicine da mamaki ya cika saleemah lokacin da taji abinda sameemah tace,shikuwa sameer a bangaren sa bai damuba duk yanda akayi dayane,saidai shima yayi Mamakin sameemah amma yasan da biyu tayi hakan,dan saleemah taji haushine.
Dakin dayake gefen iyah aka gyara musu domin su kwana shikuma sameer ya shiga dakin malam din.
Katifa dayace a dakin ta bunu saikuma tabrmar karauno,a tare suka shiga dakin su biyu kowa yana karewa dakin kallo,saleemah ce ta bude baki tana kallon itacen da akayi rufin dakin dashi ga kuma yayi kasa kaman zai kifo a kanta,hannu ta kai tana taba plastar kasar da akayiwa daki da kuma wanda akayi a kasan dakin.
Bata ga komai ba saida aka zo kwanciya ta dora hannunta akan katifah taji wani tauri kaman buhun siminti,ja tayi da baya tana zare ido tareda cewa,
“Nikam gaskiya bazan kwanta akam wannan abunba ,wannan ai saina tashi da ciwon jiki gobe”
Jin abinda ta fadane yasa sameemah kara matsawa ta baje akan katifar sosai yanda babu wamda zai iyah sake kwanciyah akai idan ba jinjiri bane,wata uwar hamma taja tareda juyawa da alamar bacci zatayi.
Saleemah tafi kusan awa daya a tsaye itah bata kwanta ba itah bata zauna ba,ganin yanda kafafunta suka fara gajiyah ne yasa ta zaunawa dabas akan tabarmar tana karewa sameemah kallo da take kwance a akan gadon cikin takaici.
Kwanciyah tayi akan tabarmar saidai koh minti uku batayi ba ta tashi ta zauna,saboda yanda taji kaman a saka ta a kabari,bubbuga katifar take akan sameemah ta tashi amma tayi shiru kaman dutsi.
Har ta juya zata kwanta kuma sai taji motsin wani abu a dakin,bata kawo komai a ranta ba ta gyara kwanciyarta da niyyar yin baccin kawai.
Wani katon abu taji akanta amma bai kai kuliya ba saidai katone,ihu tasaka tana kakkade jikinta,shikuwa beran tuni ya fice a dakin.
Jijjiga sameemah take tana hawaye amma shiru babu alamar ma zata motsa,da haka tana kukan bata san lokacin da bacci ya dauketa ba.
Da safe da ta bude idonta a kasa ta ganta kayanta sunyi futu futu da kura saboda artabun da sukayi da berayen dakin,sameemah tah kallah wanda ita ma tashinta kenan tana mike hannu babu ko salati,saleemah ce ta kalleta tareda cewa,
“Jiya kika tare katifar ina tashinki amma baki jiba ga kuma wasu abubuwa a dakin koh”
“Ina jinki rass ba bacci nayi ba,dariyah ma nakeyi har kika gama kukan kikayi bacci”
Da sauri Saleemah ta zabura daga inda take zaune kafin tace,
“Dan tsabar iskanci dama kina jina ina tashinki kikayi shiru?”
“Toh uban me zan miki,goyonki kikeso nayi ko me?”
“Amma dai ……………..”
“Kinga karki dameni da surutu da sassafe nan,ajiyarki aka bani mtsewwww”.
Tun daga haka babu wanda yasake magana acikinsu har suka fito karyawa wajen iyah.
Anan ne suka hadu da sameer wanda shima ya fito daga dakin malam.
Gaisuwa aka farayi itah kuwa saleemah sai shagwaba take yiwa sameer ko kunya bata ji.
Kaman mai zargin wani abu sai sameer yace,naga dakinku shiru kunyi bacci mai dadi koh?”,iyah ce itama tace,
“Lallai kam dan naji da asuba ma shiru basu fitoba”
Kunyah ce ta kama saleemah amma sameemah koh a jikinta saima kokon da takai bakinta a karo na biyu,fada sameer ya fatayiwa saleemah ta inda yake shiga ba ta nan yake fitaba,wanda yana cikin fadan ya kalli sameemah da niyyar bata itama nata kason,sauke kofin tayi kafin tayi saurin cewa,
“Karka tambayeni komai ,saboda ba’a tambayar mace tayi sallah,yanzu zaakji kunya da jin amsata kuma ba abinda ya dameni ehe,(kiji maman najwa mutumiyar taki koh,dan ma naga su yah kubrah suna yi mata nasiha,da kuma su zuzunmasta,batayi sallar ba kuma fah?🙄😲,gashi kalau take rasss).
Malam ne yayi gyaran muryah ai kuwa kowa yayi shiru aka cigaba da cin abinci.
Bayan sun yi wanka sun shirya saida suka shiga gidan kawunsu wanda suke uwa daya uba daya da inna hajara kuma kaninta.
Surfe sukeyi a tsakar gidan matannasa lokacin dasu sameemah suka shiga,gidane mai fili sosai saidai sun shareshi kall abin sha’awa,iyah matannsa suka gaisar basu sameshi ba ya tafi cikin gari cin kasuwa,kudi sameer ya rabamusu sai godiyah sukeyi da saka albarka.
Shikuwa malam mansur lokacin da suka zo tafiyah kayan gona ya hada musu irin su wake da gyda ,da yake lokacin kaka’a ce,amfanin gona ya dawo gida.itama iyah tayi kokari,dan jarkoki ta cika musu da kindirmo da kuma shima man shanu ciki leda,godiyah sukayi sosai dai kafin suka kamo hanyar dawowa gidan.
Wayar sameemah ceh tayi kara inda tafara magana cikin tsare gida,
“Bance kuyimin shirme ba ina dawowa in anjima dinnan,ka saka wani yah wankemin motar nan kafin na dawo dan akwai aikin da ban kammala ba na shekaran jiyah,sannan ku tabbatar yarinyar nan kun kula da itah yanda ya kamata,idan har nazo naga ba yanda nace ba duk ranku zai baci………………yadai fi muku,ina zuwa yanzunnan”
Tana sauke wayar suka hada ido da sameer tah madubi yana kallonta da alamar tambaya,itama dayake tasan yau kawar da idonta tayi kaman bata san yana kallonta ba.
“Wace yarinya kike magana akai,yar gidan uban waye?”
“Yar Gidan uban wani ce mana”
Tsayar da motar yayi yana huci jijiyiyin jikinsa sun tashi sunyi wani rudu rudu,saleemah ceh ta make a jikin kujerar ta ganin yanayin daya shiga,sake kallon sameemah yayi ta cikin madubi har idonsa sunyi kala,
“Me kike nufi,bayan abinda nakeji na dabanci har kidnap din yara kikeyi ashe?”
“Yanzu idan kidnap dinne ina ruwanka dan farouq na dauke ko me,ni banaso ana min katsalandan a rayuwata,akwai wanda yake daukar dawiniya tane,ko kuma kayanka na taba kake tada jijiyar wuyah,saika bari idan na taba naka sai kamin abinda ka ga dama mtseww”
Tun kafin ta gama tsukar yah kifa mata mari a fuska,abinda ba’a taba yimata na tunda take bayan ta girma,kallonsa take da idonta wanda suka fara canja kala zuwa jawur,saurin rufesu tayi dan tasan a lokacin idonta sun fita daga kalar dasuke,sannan tana koarin saita rawar da jikinta yakeyi.
Shikuwa juyawa yayi ya tashi hanyar suka cigaba da tafiyah,har sannan bai daina masifa da kuma kirafin halayyarta ba na raini da kuma rashin kamun kai.
Tana jinsa duk abinda yake fada saidai a lokacin ba tashi takeba tukunna ta hucin da zuciyarta takeyi take tukunna.

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤23❤

Suna isowa kofar gida tun kafin yah tsayar mota sameemah tayi saurin ficewa daga motar kaman ana harba ta ceàudirect zuwa kan gadonta,ta dade a kwance kafin ta dago saboda ringing da wayarta tayi,saida ta ga mai kiranne kafin ta tuna da cewar ashe tana da wajen zuwa fah.
Cikin yanayin daga mutum yagani yasan tana bukatar hutu amma hakan bai hanata tashi fita wajen ba.
A bakin kofar gidan suka hadu da burgu ya kawo mata motar da ta bayar a wanke,karbar key din tayi ta su ka shiga sai gidan horonta inda ta bayar a ajiyemata yarinyar.
Kofar wajen a bude suka ganta hakan yabawa sameemah mamaki saidai bata ce kkmaiba sai shiga gidan da tayi kawai .
Su mungun dawa ne a zaune sun baje suna karta,saikuma wata yarinya a tsakiyarsu itama da katin wasan a hannunta,wani saurin bugawa tayi tareda tsalle tana murna saboda nasarar da taci a wasan.
Babu dan kwali a kanta sai dogon gashinta madaidaici wanda ya baje saboda rashin daureshi da ribbon,dogon wando ne a jikinta da kuma riga t-shirt bak’a anyi mata adob fari.
Dukkan su surutu suke basu damu da tsayuwar sameemah a wajenba wacce ta kama kunkumi tana kallon ikon allah.
Saida burgu yayi magaana kafin kowa yah nutsu ciki harda yarinyar da take tsalle da murnar cin wasan,mungun dawane yah gyara murya kafin yace,
“Eh wato dama shugaba abinda yafaru shine,itah yarinyar ce wai gwanda da muka daukota kuma zatayi vidion anayimata azaba ma kodan yasaka hannun,wai dama ya takura mata”
Dakatar dashi sameemah tayi tareda cewa,
“Banason wani shashancin zance,ba abinda na daukota dan nayiba kenan,tsakaninta da shi bai dameniba”
Matsawa baya yayi jin mai tace,matsawa kusa da yarinyar tayi tareda cewa,
“Menene sunanki inason jin takaitaccen bayani game da tarihinki”

true life story ne na yarinyar wanda yah faru da gaske,saidai zan kara wani abu ba kaman yanda aka bani labarinba,amma zan sanja suna saboda yanayin tsaro

“Sunana Surayyah kuma ni kadaice a gidan mu y’a mace,sannan kuma nice ta karshe a gidan wato y’ar auta,Saida mafi yawan yayuna suka girma har suka zauna da kafarsu kafin aka haifeni,Akwai soja ,yan sanda,morpol custom da sauransu,kuma dukkansu yawanci aikin d’amara sukeyi.
Mahaifiyar mu bata yimin fada dukkan abinda nakeso shi nake,gashi allah yah yini da rawar kai kuma da farin jinin mutane,sanadiyyar rashin mutuncin danake yi a gari ina jawomusu abin magaan yasa suke yimin horo mai tsanani,amma duk a banza ina warkewa zan koma.
Haushinsu nakeji kaman na kashesu,inaso naga suna bani kudi sosai amma babu wanda yake bani komai,dan haka ni koma menene zanyi idan ta kama ma kuce saceni kukayi,suna da kudi sosai kuma nasan su abba zasu tashi hankalinsu har sai an bada kudin.
Nima saiku dan bani nayi harkata”
“Toh naji labarinki saidai ban daukoki dan nayi kudi dake ba,na daukoki ne dan nasa yayanki yayimin saigning akan wata paper game da wani aikina.
Batun kudi kuma zaki iyah yi dakanki,saidai abu daya zanyimiki ,nayi niyyar dan taba lafiyarki dan yasan da gaske nake,amma tunda naga kema da hannunmu ce zaki iyah yin pretend a matsayin mun dakeki saboda abin ya tafi miki a sauki”
“Toh shikenan naji shugaba,amma inaso na zauna a cikin kungiyar nan,saboda nima nayi zama a cikin yan daba a unguwarmu”
“Ahah ban karbekiba ,baki cika abinda nake bukata ga yan kungiyata ba,saboda ke kina da yadda zakiyi wato bin maganar yayunki,amma idan har kika karbo saka hannunsu a paper toh wato sun amince toh zan karbeki,yanzu zan kira creator yah sanja mikk kama irin na wanda yasha duka,zamu fara buga wasa da yayanki tunda naji shima dan taurin kai ne”
Bayan wasu mintina kuwa mai kwalliya yazo,inda surayyah ta zauna aka gama kirkirar ciwo kala kala a jikinta,kai kace dama ciwon gaskene.
Lesson na dramar dazatayi aka fara bata kafin lokaci n action din yah fara.
A can gida kuwa su mahmood in hankalinsa yayi dubu toh ya baci,saboda batan layar zanar da surayyah tayi tun shekaran jiya,babu kuma labarin ta ko kadan,tun abin suna zaton karamine har yazama babba,kuma shi kadaine babba wanda yake garin,sauran dukkansu suna garin aikinsu.
Karin abun ma kuma mahaifiyar su da ko abinci taki ci sosai dole sai an kawo mata yar ta.
Yanzun haka yana tsaye a cikin gidansa itama matarsa tana nata korafin na kudin ankone ya ga kiran waya,da bazai daukaba saboda bakuwar lamba ce,kuma layinsa na gida aka kira ba na aiki ba amma duba da yanayin aikinsu ga kuma dama kanwarsa wanda yakeji kaman yah hura wauta yasaka ta ita ma ta bata.
“Salam wa yake magana”
Muryar wanda yajine yasa shi sauke wayar na yan sakanni,saida ya dan washe da Mamakin kafin yamayar da wayar kan kunnensa,
“Eh nine ,kina magana da mahamood ne”
“Dama nasan dashi nake magana ai,basai nayi maka bayanin waye yake magana ba,dan daga yanda ka sauke waya na wani kankainin lokaci nasan ka ganeni,dama nakira na fada maka ne cewa;kanwarka da kuke ta wahalar nema tana wajena tun shekaranjiya,idan kuma ta cika adadin danake jira banji kayi abinda nakeso ba,toh har Iman(yarsa)da kuma uwarta zan hada na yi gaba dasu,saika zaba koh su kokuma takardar wajenka”
Komawa statue(gunki) yayi kafin yah saita saboda yin magana,
“Uhm naceba amma taya zan san……….”
“Karka damu ga vedion ta nan yana shigo maka,gobe nakeson kayi saigning din,saboda akaita wajen manya da wuri,mukwan lafiya a ci gaba da rarrashin tsohuwa”
Sauke wayar tayi tana kallon surayyah wanda ta daina kukan karya da rausaya jikin lokacin da aka dauke camera daga kanta,saidai kuma akwai alamar bataji dadin maganar da akayi ba,saboda ta so a tambayi kudi masu yawa ko ta samu kasonta,amma ji yadda aka tsaya akan wata paper ta banza,cuna baki tayi tana kukkumbura fuska itah a dole ga sakaliyah.
Tsawa sameemah ta daka mata duk da bawani finta tayi da yawa a haifeba,amma yanda takeyi kai kace itah ta haifeta,
“Banason shashanci,nariga na fadamiki abinda nake da bukata karki sa nayi magana biyu,kodan kinga ina miki gentle,toh wallahi sa’a kika ci,dan koh shi yayannaki banason sakashi dole ta wata hanyar ne da tuni an wuce wajen.
Ki shirya gobe watakila zaki koma gida,dan nasan zai yi signing ko daga jin yanayinsa”
“Amma nace miki inasob shiga kungiyar nan fah”
“Saikin kawo saka hannun yayunki ko iyayenki,idan ba haka ba karki bari musake haduwa dake,bazaki ji da dadi ba kwata kwata “

Tana fita daga gidan horon bata zarce ko ina ba sai club,dan yau yanda yayannata ya bata mata rai tanajin idan dai ba shaye shaye tayi na fitar hankaliba toh akwai matsala babba,dan shedanun kanta babu abin da suke bukata sai jinin wanda yah bata mata rai a lokacin,saidai idan har ba babbban kuskure mutum yayi ba toh bata yimasa irin wannan hukuncin.
A table din dayake karshen club din ta Zauna tayi shiru kaman mai nazari,muryar wani gaye taji yana yi mata magana,amma ko daga kai batayiba har ya gaji ya zauna dan kansa.
Bartender (mai kawo odar)ce ta zo da book list a hannunta,tambayar sameemah ya shigayi akan mai takeso,itadai bata kalleshi ba sai nunawa da tayi da hannunta kan abinda takeso,dayake tasan mai sameemah tace ,wucewa kawai tayi domin isarda bukatar customer dinsu.

“Yan mata ina ta magana amma bakice komai ba,gashi da alama kina cikin damuwa,koh zamu dan yi dance ne ina ganin zakiji kin dan sakko,ko kuma bari nayimana oder wata zazzafar giyah yanzu zakiji kin daina jin abinda kike ji,”
Har yayi surutun yagama sameemah bata dago tackalleshi ba,saima wasa da farcen hannun ta na dama da takeyi,abinne kaman yafara isarsa hakan yasa ya cigaba da magana,
“Beb bakice komaiba,bai kamata ki dunga jin haushiba da irin wannna kyawunnaki ya kamamta kiji dadin rayuwarki gashi kuma…….”
“Kai bakone a cikin garinnan?”
“Eh nazo wani aikine meyasa kika tambaya”
“Saboda nasan da kasanni bazaka zauna anan ba,dan haka ka bace ka bani waje tun ban huce a kanka ba gaye”
“Amma beb hakan bai miki kyau ba sam,sunana Tukur ana cemin TK,ke ya sunanki”
“Dama ni na tambayeka sunanka ne ,bare ba fadamaka nawa sunan”
Suna cikin hakanne matar ta dawo da wata yar karamar kwalba an nade samanta da leda said kumu murdaddiyar wiwi suma kusan goma a kan wani plate,tun kafin ta ajiye Tk yake Mamakin wanene yake shan irin wannan giyar mai karfi anan garin.
Saida yaga an ajiye a gaban sameemah kafin hankalinsa yakoma kansa dukka.
Yar karamar kwalba ce amma babu wanda zai iyah shanta haka ba tareda ya sirka ba,idan kuwa ba haka ba mutum zai iyah shiga coma ko kuma yayi akallah sati daya bai tashiba idan yayi sa’a.
Mantawa tayi da wani jarababbe a gefenta saima bude kwalbar da tayi tana zubawa a cikin bakinta har zuwa makogaranta.
Shikuwa gogan kaman television haka ta KO ma masa,koh A bai sake cewa ba har ta sauke kwalbar ta kuma dauki kwarkwaro daya na wiwin tana kyasta masa lighter.
Busawa take hankali kwance saidai duk wanda yake kallon idonta yasan akwai sauran bakin ciki a cikinsu.
Sun dad’e a wajen a zaune har sannan bai gaji ya tafi ba saima kallonta dayake tayi har takusa tashi da wiwin itama,lokacin dare yayi sosai dan a kalla shabiyu zata kusa gotawa,tashi yayi ya bar wajen koh sallma bai mata ba,itama kuwa bata kukashiba har ya fita a cikin club din da Mamakin ganin ko layi bata faraba bare kuma bacci ya dauketa na giyar.
Sameemah bata tashi daga kujerar da takeba har saida ta ga babu ala mar wiwin da gama da su tukunna,fitowa tayi ta nufi motarta tana wani rausaya idonta har wani sanja kala yakeyi.
Figar motar tayi duk da darene amma hakan bai hanata fara rage haushinta akan motar ba.
Wata kwana tayi ta shiga layin gidannasu babu kowa sai filin wajen,a gefen motar sameer ta faka motar kafin ta fito tareda rufeta.
Har takusa shiga cikin gidan said kuma taji kaman alamun mutum a bayan ta,tsayawa tayi domin jin menene zai faru,gyaran muryarsa taji amma duk da haka bata juya ba,shima kuma zo gabanta ba din ,duk da yasan ta gane waye yake bayannnata.
“Daga ina kike da wannan daren,wanda in namijine ma yanzu yah koma gida,tun dazu kowa ya shiga gida har mazan amma ke sai yanzu zaki dawo?”
Juyowa tayi suna kallon kallo itah dashi babu alamar maganar dayayi mata ta shigeta saima haushi da maganar tasa tayi mata,
“Daga club nake,shiyasa kaga nayi dare ko kana da business akan hakan ne”

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤24❤

“Daga club nake ko kana da business kan hakan ne,har yanzuna sai wani ya fadamin abinda zanyi,abinda naga dama nakeyi sannan banason wani yah dunga shiga lamarina,lokacin da wasu zasu fadamin mai zanyi yah wuce yamzu nice da alhakin jan ragamr rayuwata saboda nikadai nasan yadda nake fiye da kowa”
Duk da karamar riga ce a jikinsa amma kana ganin yanda tsokar jikinsa ta murde saboda maganar da sameemah take yimasa,cikin zafin na ma kuwa yasake kifa mata wani marin har saida tayi baya amma ta tirje da kafafunta,
“Ke Wacce irin yarinya ce,har ana cemiki daga inakike kina cewa wai daga club kike,gani kike abinda kike na arzikine,ko kuma rashin hankali,dakike cewa kinada hankali toh ko dabba bazayyi abinda kikeyi ba ,sannan nasake ganin kina mayar min maganar son ranki tana fitowa daga bakinki kina fadamin,idan bakiyi wasaba saina karyaki a gidannan kafin na tafi shashasha kawai”
Saida ta bari yah gama fadar duk abinda yake bakinsa kafin ta dago da idanuwanta wanda farin cikin idon ya koma jawur kaman garwashin wuta,saida ta cije bakinta har fatar bakinta tana fashewa saboda bakin cikin dayake cikin ranta kafin tace,
“Sameeeeeer!
Sameeeeer!!
Sameeeeer!!!
Idan har kanaso ka cigaba da tunanina a matsayin kanwarka da kake da ita guda daya cikin kaunar rai toh kadaina shiga rayuwata ,bare har hannunka yasake taba fuskata,kayi na farko dazu yanzu kayi na biyu toh karka sake na uku,saboda hukuncin dazai biyo baya bazai yiwa kaff yan gidan gandu dadiba,har ummah da take makwancinta bazata yafemin ba.
Dan haka tun ina iyah rike kaina duk da hakan yana cutar dani toh karka kara,kaci albarkacin umma dan haka karka sake shiga sabgata na fada maka,ka dauki matarka ku tafi kuna cikin koshin lafiya. Wannan gargadine idan kaji da kyau idan kuma ba haka ba …………………hmmmmmm”
Dunkule hannunta tayi jikinta har rawa yakeyi ta shige cikin gidan ta barshi a wajen yana wasiwasin abinda tayi.
Gogar kuwa tana zuwa ruwa ta diba tafara tuttulawa a cikin bakin ta tana jijjiga kai,saida ta gama ta fada kam gado tana ritse ido da karfi,dahaka can wani lokaci bacci ya dauketa mai nauyi sosai.
…………kallonta take a wata duniya daban mai duhu,sadai daga ganin idonta dama tah saba zuwa wajen ba yau ne na farko ba,kayan jikinta ta kallah jawur da su ,saida ta daga ido taga suma wanda suke wajen haka kayansu yake,saidai itah nata anyi masa hoton wani katon tattoo a tsakiyar rigar irin na jikin kayan shugaban dayake kan kujerar,
“Koyaushe cikin saba doka kike,babu wani ruhi daga cikin mu dayake saba doka saike,kuma kedai ce a tarinhimu kike saba dokar shugaba amma yake kyaleki dan haka ki shiga hankalinki”
“Idan naki fah ,wai me hadina daku ne wai,akan uban me zan dunga bin umarnin naku,shidin yayanane kufurinku shine kusakani kashe duk wanda ya bata min rai ciki harda ahalina,to kun makara dan yanzu na koyi control din hankalina ba kaman shekarun baya na lokacin ina Brazil,sannan ai bance ina cikinku ba ai”
Tana gama fadin hakan ta kama rigar da take jikinta da karfi ta cireta,aikuwa cikin kankanin lokaci hankalinta yah koma iyah cikin bacci kawai,da haka baccin gaske ya dauketa bayan ta bar wajennasu.
Kwana sameer yayi yana tunanin yamda sameemah tayi masa magana,abin haushi ya bashi ganin yamda take taka kowa san ranta.
Tun kafin kowa ya tashi saleemah ta tashi ta gyara danta saboda tafiyah,dan itah gidan ya isheta musamman sameemah da tsoronta takeyi yanzu tun sanda akayi dramar mota a gabanta,kuma ta dau kudurin babu ita ba garin zariyah har abada,musamman wannan yankin nasu da babu komai sai yan daba,ta tashi a cikin sojoji amma bata tashi a cikin mutanen da babu wanda yake ganin mutuncin na gaba dashi ba.
Shima sameer bayan yah karyah fitowa yayi suka gama sallama da mutanen gidan ya kama hanya.
Gogar kuwa sai wajen bayan azahar kafin ta tashi tana mutstsika ido,hada ido sukayi da karen ta bingo yana saki baki,hannu ta mika masa yazo yana shanshanata,
“Oh Baku ci abinci bane,bari na tashi dama akwai wajenda zanje na manta kwatakawata”
Sakkowa tayi ta fito daga dakin tana hamma da kuma mika,da baba umaru suka hadu a tsakar gidan yah dawo daga gona,kallonta yayi tareda jijjiga kai,koh gaisheshi batayi ba kuwa tayi hanyar bandaki,dan dama idan ba yan muyuncinne suke kusa ba koh gaisuwa bata hadasu da yan gidan,
“Ke sameemah ni kun yi sallama da yayannaki ne?”
“Ahah “
“Ya tafifa dazu da hantsi kuma bakuyi sallmaa ba”
“Sallama kuma,saikace wasu yara,yafi masa ma dan wallahi daya ga yanda ake iyah shege,kuma hankalinku yah kwanta”
“Tabbbdi lallai yarinyar nan,yanzu dan uwannaki kiyi shekara da shekaru baki ganshi ba saida ya tafi bakuyi sallama na kike cewa yafi hakan”
“Baba bazaka ganeba ne a bar zancen kawai”
Shiryawa tayi cikin atamfa anyi mata dinki simple na doguwar riga,sai daurin ture ka ga tsiya da kuma gyalen rigar a kafadarta,tayi kyau sosai dan ba karamar kyakykyawa bace (kyan dan macijiba)kuma tafi saka abaya,ko kuma riga da wando,haka in bata ga dama ba sai tayi sati bata daura dan kwaliba sai gyara gashi kawai takeyi ta daureshi.
Hanyar waje tayi su bingo suna biye da itah a baya,kicibis sukayi da manjo yana shigowa,yah saka wata babbar riga wanda takusa ta yadi goma,a ina ya samota oho,dan dama manjo ba dai shigar hauka ba,taba ce a hannunsa tana hayaki ga kuma wani kwalli dayasha kaman dan farauta,
“Yawwa ke dama ina nemanki zamuyi wata magana”
“Wacce maganar ka bari saina dawo akwai wani abu dazanyi manage yanzu”
“Ke ni zakice zakiyi wani mange(manage),maganar muhimmancin nima nake tafe da itah”
Har zatayi magana saikuma ta gyara tsayuwa tareda cewa,
“Ina jinka manene”
“Ehe yawwa zancen soyayyarki keda sule maye,inaga maganar zatayi karfi tunda ni yayanki nashiga ciki,yanzu hak nace yabani sadakinki dubu talatin,kuma yabani duk da ma na dan ci dubu biyar a ciki,kinsan sha’anin rike kudi abinka da mutum mai dan uzuri,hhhhhhh amma tunda naga yana sonki sosai nasan zai karo cikaton kudin.
Kai dole ma ya ce yanason ki duk da irin tantirancin da kikeyi ,akwai kyau ne musamman idan kikidau wanka”
“Toh yanzu dai kagama magana mai muhimmancin ko kuma da saura har yanzu kai”
“Ke kina rainani fah,dama sanda na dawo kulu tacemin kin mata rashin kunya kyaleki kawai nayi saboda sule abokina yana sonki”
“Allah koh,haka akayi kenan,duk zancennan ka barsu idan na dawo sai muyi shi”
Jijjiga kai kawai tayi tana Murmushin mugunta ta shiga mota suka tafi itada karnukannata.

Wajen da ta ajiye surayyah ta tafi domin jin yanda ta kaya,yauma a zaune take saidai dayake su mugun dawa sun tafi aiki daga itah sai C.I.D shikuma bashida magana sai leken asiri koh bera ya sara masa.
Sameemah tana shigowa surayyah ta tashi tana gaisheta duk da a gida koh uwarta sai taga dama take gaisheta.
C.I.D ne ya matso tareda yimata bayanin abinda yah faru dazu,mika mata wata takarda yayi yana cewa,
“Ranki ya dade ga wannan paper burgune ya kawota dazu wai yayan surayyah ne yabayar,yayi signing din yaan neman a sake masa kanwarsa,tun dazu muje jira ki iso gashi kin ce kar wanda yakiraki shiyasa na zauna ko zaki zo”
“Okay shikenan babu matsala,zaku iyah maida ta gida,amma ban yadda tasan wane waje take ba,na gama da wannan shafin”
Saida ta gama kallon signing din ta tabbatar shine kafin ta rufe paper cike da murnar nasarar da ta samu.
“Amma shugaba nafadamiki cewa nima fah a nan wajen zan zauna”
“Eh kuma nima na fadamiki idan baki kawo signing din yan uwankiba bazan daukeki ba ai,koh kin mantane?”
Sunkuyar da kai surayyah tayi cike da jin haushi saidai ta kudiri aniyar karbo izini dan itah taga wajen zama inda yayi dadai da ra’ayinta.
Wani bakin kyalle aka saka mata a idonta har sannan sai cuna baki takeyi wai sameemah bata yadda da itah ba,ita kuwa ko kallonta batayiba har su ka isa kofar gidan yayannata a mota,C.I.D yah fito ya budemata kyallen fuskarta da kuma motar kafin ta fito,cikin gidan yayannata ta shige koh kallon sameemah batayiba.
Suna ganin shigewarta gidan suka bar wajen.
Mahmoud ne a zaune shida matarsa haka ma iyayennasa suna zaune a daya kujerar kowa yayi jugum sun rasa ma me zasuyi,ko sallama surayyah batayiba haka ta shigo tana wani cika,dukkansu tashi sukayi suna kallonta da mamkin ko kwarzana babu a jikinta,bayan hoton da aka turomusu duk jikinta ciwone.
Mahmoud ne yafara cewa,
“Ke ya na ganki kaman babu abinda yasameki baayan jiya video da suka turomin nishi kike yi kaman zaki mutu”
“Ba abinda suka min,duk nice nayi saboda su saka ka bada kudi,dan cewa nayi zan taimakesu,amma wannan shugabar tasu ta ce wai bazata karbi kudiba saka hanunuka kawai take bukata a wannan paper”
Da bakin ciki sir Mahmoud bai san lokacin daya zabga mata mariba da kuma yin boll da itah,kuka ta rusa tana kallon ummahn ta,itama kawar da kai tayi da a wannan fadan babu dama tayi magana dan surayyah ce bata da gaskiya.
Haka ya dak at a saida tayi lis tukunna ya barta.
Cikin sheshshekar kuka tace,
“Kuma an taimakesu din,naga inna ce ka bani kudin hanani kakeyi,ka bawa su yaya Najeeb,kuma koh kasheni zakuyi saidai kuyi,ni yanzuma idan nasamu dama wajenta zan koma aiki.
Dan takaici shigewa daki yayi kaman zai tashi sama,itakuwa mahaifiyar su ce tazata daga kwancen da take tace,
“Gaskiya bakyaji surayyah,duk wuyar dayasha ganin kin fito ashe da hannunki a ciki,saiki tashi mutafi gida ai kafin ya karisa ki”
Da haka uwar ta jata suka tafi nasu gidan,shikuwa uban dama dayajj abinda yafaru tun da farko yabar gidan.
A cikin mota kuwa sameemah ce ta kalli C.I.D,tace,
“Kafadamin inda zan ajiyeka dam akwai wajen da zanje daga nan”
“Ahh KO Ina ma kika ajiyeni duk dayane”
Fakawa tayi gefen hanya ta saukeshi kafin tayi hanyar gidan alhaji bala direct,tun kafin ta kai ga shiga cikin gidan tayi wani murmushin migunta.
Da shirinta tazo dan jiyah C.i.d ya fadamata duk wani shiri da alhaji balan yakeyi akanta,kuma dama tayi tunannin hakan,dan a rashin muyumci irin nasa,da kuma itama irin tsiyar da tayi masa tasan bazasu kare iyah hakaba.
Shi bazai fasa daukar fansaba itama kuma bazata daina yaki ba har sai ta hau kan kijerar shugabar vigilantee tukunna,saboda tarihin da takeso ta kafa bazai tafiba saida wannan kujerar tukunna.
Danna kai tayi cikin ainihin gidansa kuma tasan yanannan. Mai gadine ya bude mata kofa ta shige kafin yamayar da get din yah rude.
………..hmm mm D’an sa ma yadawo yana nan.😂🤣😂

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤25❤

Saida ta gama saitawa kafin ta fito daga cikin motar,hanyar dazata kaita cikin gidan ta nufa tana wani shekar iska.
A bakin kofar tayi sallama wata mata da alama mai aikice ta amsa mata,
“Matar Gidan tana cikine?”
“Eh hajiya tana nan bari nayimiki iso da itah “
A kujera ta zauna kafa daya kan daya,wasu samarine suka shigo guda biyu suna ta magana,har saida sukayi wata hanya kafin daya daga cikinsu ya kula da itah.
“Lah umar wallahi wannan zazzafar yarinyar danake fadamaka na hadu da itah a club toh wannan ce”
Yafada yana nuna sameemah,itama kallonsa tayi sau daya dan taganeshi sarai,shine yace mata sunansa tukur. Cigaba yayi da magana tareda tsayar da ummaruje a waje daya.
“Kai ban gane ba fah ko yar uwarkuce,naga ta sake a falon daga gani ba zuwanta na farko ba kenan”
Da yayi niyyar share abin amma daga kallonta dayake shima dan duniyar ne,cikin sakanni yaji ya fola mata shima.
Komawa falon sukayi suka zauna,ummaruje ne ya daga girar barin dama yana lashe baki kafin yace,
“Yan mata me ne sunanki,abokina yace kun hadu a club daga gani kema yar hannunce wato ta hannun damanmu”
“Like father like son”
Sameemah ta fada a ranta,dayake ta sha kansu iyah rashin mutunci,kara daga kafarta tayi tana wani jijjiga ta irin ta shegun matannan,saida tah ciji lebenta ta gefe da hakoranta kadan kafin tah kashe murya tana cewa,
“Uhm Wai ni sunana sameemah saidai banji sunan gwarazan mazanba kuma?”
Ummaruje ne yah washe baki har kunne kamar gonar auduga kafin yace,
“Sunana umar,ina karatu a abroad sannan nan gidanmune kuma nikadaine a namiji a wajen babana sai kanwata da tayi aure”
Yah karisa magana yana kafafa,shikuwa a bangaren Tk mamaki abin yabashi domin yasan haduwarsu ta baya da itah batayi kama da wannan da take zaune ba,shikansa badan yagane fuskar ba zaice sanja ta akayi,waccer fuskarta banu annuri ga kuma uban shaye shayen da tayi,amma wannan idan ka ganta saika ce ai batasan menene fushi ba,dan fuskarta sai murmushi takeyi da annuri.
Hada ido sukayi da Tk da kuma sameemah,wani kallo tayi masa na alamar gargadi,cikin sauri kuwa yah sauke idon tareda wayancewa yana dariya.
Suna ta tadi dukkansu babu wanda yah kulada zuwan alhaji falon shiga hajiya Mairo,jerowa sukayi ko wannensu kaman zai fashe dan kiba,musamman ma hajiyah mairo sai huci takeyi.
Tsayawa su sameemah sukayi da tadi ita da ummaruje wanda ya zare sai surutu yakeyi kawai dan yaga wannan kyakykyawan Murmushin a fuskar sameemah.
Hajiyah mairoce ta tambayi ummaruje tareda cewa,
“Kai daddy wannan kuma fah a ina kuka samota?”
Sameemah ce ta hada ido da alhaji bala wanda yake feso gumi a akan fuskatarsa ta kyasta masa ido batareda kowa yah kula ba,
“Ahh mommy nima anan na ganta ,nayi zaton fah kin santa,tana jiranki ne ki fito”
“Ahah ni bansantaba kwata kwata”
Tun kafin sameemah ta bude baki zatayi magana alhaji bala yayi sauri ya rigata saboda yaga niyyar ta kenan ta tona masa asiri,
“Ahh hajiyah sai yanzu nagane ta ,ai yar gidan aminina ce,yayi min zancen tana neman kudin makaranta toh shine nace ta zo ta karba”
“Ayyah to ai bazata tsaya anan ba sai tayi magana kuma”
Wani Murmushin sameemah tasake yi masa mai nuna alamun ka ceci kanka,shikuwa ummaruje jin abinda akace gameda sameemah cikin sauri yace,
“Lah Ashe kema student ce,allah ya taimaka,amma da kin bani number ki ko zamu sake gaisawa dan yanzu fita zanyi foot ball ba lallai na dawo na sameki ba “
Yana gama fadan haka yabawa sameemah wayarsa,itakuwa kodan taga yah alhaji bala zayyi cikin innocent smile ta karbi wayar ta saka masa number tah.
Tun wajen yayi tsallen samun nasara kafin yah fita aka bari daga alhaji sai hajiyah,itama hajiyah mairon Murmushin takeyi ganin abinda dannata yayi,
“Yarinya ki saki jikinki kinji,idan da wani abunma kizo kanki tsaye,babu wata matsala”
Sunne kai tayi kaman yar arziki tace,
“Nagode hajiyah allah ya jikan mahaifa,yasaka muku da alkhairi”
“Ameen ameen diyar albarka,menene sunanki”
“Sunana sameemah hajiyah”
“Kai suna kuwa mai dadi,yah dace dake sosai”
Da haka hajiyah ta koma sashenta tabar Alhaji bala a tsaye wanda yayi simmm kamar gunki.
Sameemah ce ta tafa hannunta kafin yadawo hankalinsa,
“Amma seemah menene wannan kikeyi da iyalina,musamman umaruje wanda ba hanunsa a komai kike son ki cutar dashi”
“Ka ga dakata cutarwa kuma bashi numbar ta shine cutarwa,cinyeshi kaga nayi komai,sannan abinda nakeyi sunansa wasa”
Ta gama maganar tana kyalkyalewa da dariyaar mugunta,
Takaicine yakama alhaji bala yarasa ma mai zaice,ganin tsayuwar ta gagareshine yasa ya samu kujera ya zauna wanda take facing din sameemah.
Yanzu dai mudawo zancen gaskiya,duk abinda zakiyi kar ki taba iyalina,kowa yah ajiye iyalai a gefe,idan kuma ba haka ba kinsan kin fi kowa iyalai sama dani,zan iyah daukar mataki”
“Lahhh alhaji bala gwanda da kafadi abinda yake bakinka,toh bari kaji in fadamaka,ba abinda zai shafeni dan ka taba wayannan mutanen,koh zai dameni ma ba sosai,saboda wadda naso a duniyah sama da komai ta tafi ta barni kuma na rayu,dan haka uban kowa ma yah mutu,idan aka jajanta na sati daya kowa ya koma harkarsa.
Bar ganin na fadi hakan kuma,allah yasa naji ko mura wani yayi a cikin gidannan ace da hannunka………..hmmmm danka zan dauke mubar kasar dashi muyi rayuwa,sai yagama makancewa akaina na nuna masa video ka sanda kake kokarin yin lalata dani,idan ciwon zuciyah ya kamashi sai na dawo na barshi a can😎”
Tun daga jin bayanin irin ta’asar da sameemah zatayiwa dansa yasa yasha jinin jikinsa,saidai bai kai ga komawa hankalinsa ba yaji ta cigaba da cewa,
“Kai maganar da kayi ma,ka karawa kanka yanzu bayan na siye zuciyar hajiyah mairo da kuma danka,saina saka yarka taji batada wata kawa mai shirin zama kuma yar uwa a zuciyarta sama dani,saina ga yanda zakayi dani idan sukaji ka illatar dani,kuma kana kokarin keta min haddi a video”
Saurin toshe kunnensa yayi tareda cewa,
“Yah isa haka mai kikeso ne kika zo gidannan iye?”
“Abu kadanne,naji labarin shirin da kakeyi a kaina,Toh ka daina banaso sannan batun bani kujerar vigilantee tana nan babu inda zaraje,dan har na karbi takardar ixini a wajen shugaban yan sanda,dan haka ka shiryah zuwa wani sati,in kuma kak ji baza ka ki ganiba.
Ina nan a kan bakana babu inda zanje”
Saida yasauke ajiyar zuciya na babu yanda zayyi kafin yace,
“Shikenan naji,amma batun d’ana please karkiyi wasa da zuciyarsa kinga baisan komai akanki ba”
“Zai sani a hankali karka damu,ai yanada hankali ba mahaukaci bane shi,dan haka in yayi kuskuren hanya zan saita muku shi,sai kuyimin godiyah na cigaba da aikin da iyayene ya kamata su dinga yi,kun sakaltashi da yawa yana bukatar gyara daga irinmu”
Zaro glass dinta tayi daga cikin jaka ta toshe fuskarta dashi,har ta isa bakin kofah ta dawo tana cewa,
“Ahh alhaji zan tafi amma bakazo kun gaisa da motarka ba,ko ka daina santa ne bansaniba”
Ganin dan bakin ciki bai kulata bane yasa ta fita tana Murmushin mugunta.
A can Gidan su surayyah kuwa yau sati daya kenan kullum tana cikin aiki,ko an saka ta ko ba a sakata na zata tashi tayi,tunda ta dawo daga hannun sameemah kaman an sanjata haka ta zama,ummanta sai murna takeyi.
Yauma zaune hajiyah Sa’aden take bayan sun gama aiki dan d’anta dayake aiki da sojoji yau zai dawo garin,Kwallah mata kira takeyi amma babu itah babu labarinta sam,abu tun safe har wajen yamma,lokacin yayannata har ya iso yah huta,shima daya tambaya cewa akayi bata nan.
Shigowa tayi tana sanda hanyah,bata ankaraba saijin maganar mutum tayi a bayanta,
Juyawa tayi taga ashe yayantane da zaizo yau,
“Daga ina kike haka tun safe,kuma ke ba makaranta kike zuwaba,yansu surayyah kina nan da halinki na yawo da rashin kamun kai koh?”
“Iyah Gidan kawata fah naje,ni ba wajen wasu najeba yau din”
Jijjiga kai yayi kawai ya wuce shima cikin gidan,itama binsa tayi a baya har ta wuce dakinta,tanajin kowa yana fadar abinda takeyi ita kuwa tura dan kwali tayi tana bubble din chewing gum.
Sallamar yah Mahmoud ce ta fito da itah daga cikin dakin tana lekawa ta window,
“Miye kike lekoni kizo ki karba abinda kikace na baki”
Fitowa tayi kanta a sunkuye kamar wata wanda kwai yah fashe mata a ciki.
Mahmoud ne ya mikawa kaninnasa takardar tareda cewa gashi kaima kayi sign tunda kazo,
Har zai tambayi ta mecece amma Mahmoud ya hanshi,hakan yasa yah karba shima yayi sign din.
Mikawa surayyah takardar yayi kafin yace,
“Abinda kika tambayeni sati daya daya wuce ne,wanda nace miki saikinyi hankali shine kika dauki yin aiki na karyah ga ummah,ganin ban baki ba kika tafi wayo inda zan ganki koh?wato koma menene nayi din,shikenan na cika miki sharadinki,gashinan mun amince kiyi aiki da sameemah jar wuyah komai yah faru da amincewarmu”
Ba iyah surayyah ba har su ummah su da suke wajen saida sukayi Mamakin abinda yake faruwa,itah kuwa karbar takrdar tayi tareda komawa dakinta tana Murmushin jin dadi,kaman anyi mata albishir da kujerar makkah.
Uwar ce takasa hakuri tace,
“Amma mahmuda wannan wane irin danyen hujunci kayi,yarinyar da ake nema ta shiryu”
Saida yayi murmushi da alamun shi ya hango mai yah faru tukunna yace,
“Ummah karki damu babu abinda zai faru sai shiriyah,dan ina mai tabbatar miki kwananna surayyah zata shiryu a wajen seemah,dan nayi bincike nagano cewa duk yaranta yanzu ta hanasu shaye shaye da kuma aikin banza,dalilim da yasa tayi kidnap din surayyah dan na yi mata sign din takrdar neman izinine na zama shugabar yan vigilantee,kuma duk yaranta tace zata sakasu aiki,wanda zasuyimata iyah itah kadai,kaman yamda kuke ganinta ba haka takeba,tana kula da duk wanda yake karkashinta sannan yanda kikasan uwa akan yayanta haka take akan duk wanda ya yadda yah zama acikin kungiyarta,zata iyah bada ranta akansu.
Yamzu haka idan wani abu yasamu surayyah,ko bamuyi komaiba zatasan yadda zatayi ta tabbatar ta kubutar da itah,kuma ina mai tabbatar miki zata hanata yawon dare da kuma shaye shayen da take ganin tanayi,kuma dole ta daina dan dole,saboda zataji maganarta fiye da yanda takejin taku.
Kudai kuzuba idon ku gani,itah bata san yah sameemah takeba shiyasa take rawar kafar shiga kungiyarta ai,kudai ku zama yan kallo,sannan ku kwantar da hankalinku kaman kun kaitah gidan horo…………….mai zakuje zai faru tsakanin surayyah da seemah😂😂😂😂😂😂.

Please wanda basayin comment sai dai thank koh liking,ku dunga yin comment mai kyau,musamman Facebook da telegram,naga yan wattpad sun dan fara dagewa. Amma WhatsApp kune akan gama ina ji daku sosai

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤26❤

Kwanaki sunja sameemah ana ta shiryen zama yar damara,duk wani abinda take bukata ta gama hadawa,dan yanzu koh lokacin yan gidannasu bata da shi bare kuma akai ga tsayawa ana saida dan hali.
Suma yan gidan nasu bidirin sukeyi an kawo goron tambayar auren Zainab,wannan jarabbabbeb saurayinnata da suke kaiwa dare a wake,sukuwa manyan gidan wato sameerah salma da su sameemah kaman anyimusu asiri babu wacce tayi aure har yanzu,dan gwara ma sameerah ta tabayi ta fito.
Su inna ramatu sai kafafa akeyi y’a zatayi aure,su guzuma ana zaune wato su salma.
Babu laifi yayi mata kaya masu kyau dadai karfin sa,inda aka saka bikin nan da wata biyu.
Duk abinda akeyi sameemah batasan anayi ba dan idan ta fita bata dawowa sai dare,sai shirye shiye sukeyI.
Yau ma da sassafe tah tashi kaman abin arziki akayi su wanka da shigar mutunci tafito,babu kowa a tsakar gidan dayake safiyah ce amma rana ta fito,manjo ta samu yana alwala a bakin kofarsa ko kuma nace wanke ido,hada ido sukayi koh eh bata cemasa ba haka shima bai kulata ba,yan miskilancin suna kusa.
Gidan su burgu ta fara zuwa tah daukeshi suka tafi ainihin babban office din dayake birini,dauke da takaddar da Mahmoud yayi mata sign da kuma ta Alhaji bala.
Saida ta dauki lawyer tah saboda tsaro kafin suka dauki hanyar tafiyar.
Zainab ce a zaune tana shafa kurkur a fuskarta tana wakar habaici saboda taga yayan kawu shehu mata a wajen da kuma sauran yan matan gidan,
“Lokacinki ne yayi amarya yar amana sai kize ki zauna da miji aure ibada ne…………”
“Hee amaryah manya,amaryah da yin kurkur,kir ayi mai na kanti mana,kuma a wane shegen saurayin kowa yasan halinsa da bin yaran mutane”
Wata ce itama ta sake cafkewa bayan salma ta yi shiru,
“Ke ma kya fada,dan dai an rasa wani ne sai shi,in ba hakaba mai za’ayi da Uzairu a rayuwa”
“Eh haushin rashine makaho yace ido da wari,inma mai danne iyayene wata ta fito da nata mana,aurene nima zanyi na bar gidan gandu nafara girka nawa abinci wanda nakeso na barku da tuwon masara miyar lami”
“Dan ma tuwon masara kikaci kika girma ,kuma shi uwarki zata shigaba da ci har kasa ta binne idonta”
Salmace cikin yatsina fuska tace,
“Ke zainab ya isheki haka kuma,bamuson raini,a wane shegen saurayinaki naga saida nace bana sonsa kafin yah dawo wajenki,kuma shi banzan bazarane a cikin masoyana wallahi”
“Eh naji banzan bazarane shiyasa naga baki auri wannan tula tulan alhazan nakiba ai kika makale da soyayyar yah sameer har kike zagin matarsa,kuma duk jarabarki ma zaki barshi ki auri daya daga cikin tsofinnaki,dan anty saleemah ba sa’arki bace ehhe”
Cikin rashin daurewa da zancen salma tah kaiwa zainab wani uban naushi a bakinta,abinka da brush bai ishi bakinba sai jini yace yah samu wajen fita shikuwa.
Kururuwa ta hada itama ta kamata suka fara fada sai ga sameerah ta shigo da leda a hannunta da alama daga wani waje take,wajen su tayi tana rabasu tareda cewa,
“Ku hakan menene mai kuma yah faru kuke wannan kokuwar,ke salma bakiga aure zatayiba kike dukan ta a fuska?”
“Ke sameerah kema banason iskanci,auren yaci kundun ubansa,haukane auren dan zatayi ta dunga yadawa mutane magana,toh gobema ta kara saina zubar mata dukkan hakoranta,saidai inna ramatu ta akaita a saka mata na roba”
Tana gama fadan hakan ta bar dakin tana huci,sukuwa binta sukayi kawai da kallo.
Ita kuwa sameemah tun safe suke bakin kofar shugaban amma basu samu shiga ba schedule dinsu bai zoba har dare yafarayi,tun suna saka rai har suka hakura suka dawo,gashi sai wani satin su koma kuma.
In ran sameemah yayi dubu toh yah baci a wajen dan ko magana batayi sosai,haka ga gajiyah ga komai tah tuko motar suka taho.
Saida ta fara sauke barr.Kamal kafin ta sauke burgu shima a gidansu,yana mata godiyah da huta gajiyah ko kulashi batayi ba saima kara hade fuska da tayi.
Tun da ta shigo layin gidansu takejin muryar yan gidannasu gashi darene dan 9:30pm ta kusa,takaicine ya isheta tasan ba lallai ta shige Kalau na.
Ai kuwa hakance tah faru dan inna karimane da inna larai suke fada akan marar tuwo guda biyu.
Babu wanda yah kulada da itah a wajen dan manya da yara an tsatstsaya kowa wasuma hadda torchlight a hannunsu saboda su gani da kayau dayake an dauke nepa.
Baba umarune ya dawo ana tsaramasa yanda akayi,tun kafin su gama tsarawa sameemah tah fisge kwanon tuwon ta wullawa su bingo wanda suke biye da itah sunga ta shigo.
Kowa mamaki yayi tareda yin shiru amma banda inna larai dan masifah ta farayi kaman makogaranta zai fashe,
“Kinsan allah inna larai ko kiyiwa mutane shiru da darennan ko kuma na tura karennan yah ciromin mamanki na hagun idan kina bacci,kinsan sarai zan aikata yanda kofar dakinki kuwa ta baci babu sakata,dan haka saiki zaba yanzunan”
Kowa inna larai yake kallo da jin wanne zata zaba maganar sameemah,aikuwa cikin sauri tayi kofarsu tsitt kakeji kaman ruwa ya cinyeta.
Kowama dayaga hakan kofarsu ya nufa yana dariyah da tsoron inna larai,ga tsokana ga fada dakuma rashin gaskiya, aka bar filin wajen,sai gobe kuma.😂
Yanzu dakinnasu iyahsu kadaine babu zainab saboda tah koma dakin iyah mai kalwa(kakarsu da ta rasu )ana mata al’ada na aure,kaman su tsimi na tsugunne da sauransu,hakanma sai yafi musu,domin indai zasu zauna da itah da salma toh fadane zai biyo baya tsakninsu da itah,ita kuwa dama sameemah babu wanda take shiga shirginsa saidai idan ka shiga nata shirgin ku kwashi yan kallo.
Misalin karfe 12;00pm rana tayi ga kuma zafin rana saboda yanayin lokaci na rani,surayyah ce ta shigo gida da sauri sai hada gumi takeyi,babu ko sallama bare ta kula mutanen gidan ta dau buta tayi bandaki da gudu,saida ta fito ta sha ruwa kafin ta zube a tabarma a tsakar gidan nasu wanda take karkashin bishiyah.
Saida ta gama hakin da fifita kafin ummansu ta tambayeta,
“Mai Sunan uwata ya na ganki haka kaman wanda aka zefoki daga sama”
“Hmm ai bari kawai ummah,muna kan tsallaka siradi ne,da yawanmu shugaba ta saka a training kuma duk wanda bai fito da matakin nasara ba sallamarsa zatayi,gashi bata afuwa,idan tana yimana training dinannan kaman fah soja haka takeyi,gwanda ma ogah burgu yana mana da sauki.
“Ahh kikce aiki kukeyi babu kama hannun yaro”
“Hmm ni ummah kuwa anya kungiyar yan daba ce kuwa?”
“Me kika gani?”
“Naga an Hana shaye shaye,an hana yawon dare sannan ba’a yin shagali,kullum ana cikin training da kuma fita aiki,ni gaskiya gani nakeyi kaman ba kungiyar dana ke jin labari bace”
Dariyah ce ta kama ummah amma haka ta kunsheta kar surayyah ta gane,kwata kwata satinta daya tana zuwa wajen sameemah amma har ta fara sanjawa,babu shegen wayon club,babu shigar rashin mutumnci sannan babu wannan baccin safen har zuwa azahar.
“Uhm ummah bani abinci naci,nayi wanka dan in anjima shugaba tana neman mu akwai abinda za’ayi,naji tace wai zata sakamu a wajen koyon computer wasu kuma a turasu wajen training na police da yan sojoji,nikam kungiyar tamu har ta fara bani tsoro,yanzu ko samarina nagani tsoton kulani sukeyi wai tunda na shiga kungiyar seemah”
Narai narai tayi da ido kaman zatayi kuka,amma tunanin abinda zai faru idan bata koma ba yasa ta mike tana wani lankwashewa kaman wanda ta fito daga labor room,itadai ummah bata kara cewa komaiba sai dariyah da takeyi ciki ciki tareda fadin madallah.
Aikuwa la’asar nayi tun kafin tagama cin abinci saiga kiran burgu,da sauri ta tura sauran lomar da cokali ta mike zuwatt,badan tsoron burgu ba saidan tsoron wanda tasa burgu ya kirasu.
Da gudu gudu tayiwa ummah bye bey ta fita,sai a wajema ta karisa saka gyalen a wuyanta.
Tun da sameemah ta dawo gida sanda su inna larai suke fada da daddarenan take ta bacci har bayan azahar,su kansu yan gidan su zata ta mike ta can zuwa makwancinta na gaskiya,wanda da hakan yah faru da sunfi kowa farin ciki,saidai kash!!! Daidai wani lokaci ta bude idonta tareda yin wata mika irin ta wanda babu abinda yah dameshi.
Fitowa tayi tsakar gidan tana rarraba idon neman yaro dan ya debo mata ruwa,ita wannan rashin ruwa da suke fama dashi yana ci mata tuwo a kwaryah ba kadan ba.
Dan Gidan manjo ne yah yazo wucewa zai fita waje,sai sameemah ta kirashi,da sauri yah taho wanda koh uwarsa ce albarka,saboda yasan bata wasa dasu ko kadan.
Bayan ya tafi debo ruwanne tah koma dakin jin wayarta tana ta ringing,gashi dama bata saka volume kadan,kuma da saninta takeyin hakan.
Ganin number ummaruje saida tayi jimm kafin ta dauka,
“Allah ya taimaki gimbiya sameemah,yah gida da kuma jin dadi”
“Lafiyah kalau yah hajiya”
“Lafiyar ta Kalau,dama inaso naji in kina gida yau zan zo miki mu gaisa baby”
“Kaman wane lokaci”
“Kowane lokaci kika saka duk dayane”
“Ka Bari sai anjima zanyi wani aikine”
Ajiye wayar tayi tah shiga wanka domin zuwa wajen yarannata.
Bayan surayyah tayi wannan gudunne gashi bata samu abin hawa da wuri ba hantar cikinta sai kadawa takeyi kaman zata fito waje,abin haushi kuma har saida ta yi kusan wata awar kafin sameemah ta zefo hancin motarta wajen cikin takama.
Dukkansu tashi sukayi duk da ba itah ta saka masu dokar hakanba su suka sakawa kansu.
Ajiyar zuciyah ta sake bayan taga dukkansu hankalinsu ya dan koma jikinsu.
“Yawwa nasan kowannenku Yaga yanda ake saka ku aiki sosai,wasun ku sunsan dalili wasu kuma basu sani ba,toh kaman dai yanda kuka sani,daga rana i ta yau,wato wani satin ina so sunan kunhiyar nan ya tashi daga marar lasisi zuwa mai lasisi,wato zan mayar ta zuwa karkashin gamnati ta hanyar shiga kungiyar vigilantee.
Duk abinda zamuyi zai zama babu mai kaimu kara bare kuma ya dau mataki,walau tah hanya mai sauki koh ta hanya marar sauki ina so mu saki ruwan rashin mutunci a garinnan ban daukeba har cikin gidan gandu domin kawo sauyi a cikin garianan sannan kuma muma mu kafa namu tarihin da wanda za’a dunga tuna mu dashi”
Surayyah ce ta daga hannu tace,
“Amma shugaba muma aikin vigilantee zamu dungayi mata damu,baza’a dunga aikin daba ba kenan”
“Ke surayyah ke fah dama nakula duk da horon da aka baki har yanzu kina cin kasa,toh ki kiyayeni in dan auta kike ji nima nan itace,dan haka banson harkar lalaci duk wanda kika ganshi anan wajen walau mace koh na miji sonake ya zage dantsensa wajen nuna kwazo,banason abinda zai kawomin nakasu gameda burin danake son ai watarwa sam.

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤27❤

“Ina su Lubna da Kubrah”
Dukkansu daga hannun su sukayi dan dama duk cikin su babu wanda tayi magana amma daga ganinsu kaga mata masu kirar karfi da kuma zarrah(ina baku mantaba sune wanda suka kira sameemah lokacin da yaron buba jinI yakeson zanta cikin jeji).
“Yawwa ina so aikinku yahada da surayyah,duk wani wanda yayi Rashin mutunci yashiga dakin uwarsa toh ku nakeson ku shiga ku daukoshi sannan ku mikashi ga mazan su kawomin shi,saboda bai kamata muna gyara kuma mu bar maza su dunga shiga gidan mutane ba any how,jibi zanje mu sake zama da shugaban tsaro a cikin babban birini,idan abu yah tafi normal za’ayi bikin saka ni akan kujera,ku kuma za’a baku uniform bayan lokacin.
Kowa zai iyah tafiyah,akwai training daga karfe bakwai na safe,sauran kuma burgu ya cemin wani bai zo da wuri ba hmmm”
Ta shi tayi ta fita saboda ta gama isar da sakon da tazo isarwa dama.
Inna ramatu ce zaune a daki itah da yayanta sameerah da zainab,wanda babu wanda ya kaita rawar kai itah a dole zatayi aure,sai wani rangwada takeyi tana cuna baki,
“Yawwa ummah kikace zaki kaini wajen malaminki ta yanda zan mallakeshi kk uwarsa bata isa ta fada masa yajiba koh?”
“Hmm ke harki na ganin zan manta da wannan zancen nne,ai kwantar da hankalinki ni kaina malam shine dogarona shine dalikin dayasa na kai yanzu a wajen ubanku,da badan haka ba da yanzu nasan inda dare yamin”
Sameerah ce ta yah tsina fuska kafin tace,
“Nikam da ina baki shawara karki bi ummah wajen wannan mutumin,idan ta kama taimakone ta karbo miki basai kinje ba kawai”
Saurin katseta inna ramatu tayi tareda cewa,
“Ke sameemah banason shashancin banza,dan ubanki ba shine dalilin dsyasa kikayi auren farin ba,sannan kuma shine yabaki sa’a kika Rike bazawarinki a hannunki kinsan da haka”
“Eh ni dama bance ba shine yake bani sa’a ba ,kawai tun sanda yah turmusheni bana sha’awar komawa wajensa da dadin rai”
“Kiji sameerannan wallahi ke yar bukulu ce,kina zagewa yana baki sa’a amma ni kice bazanyi ba koh,bana san shawarar taki toh,idan ba da neman taimako ba ai mazan sai a slow”
Haka suka cigaba da zancensu har daga karshe aka yanke lokacin da za’aje wajen bokan(malami in jisu da fada).
Yauma sameemah da wuri ta tashi saboda tafiyar dazasuyi tana cikin ranta sosai.
Duk da sammakon su saida suka samu mutane a wajen sun rigasu wanda hakan ya bata mata rai sosai,akan layi suke amma hankalinta baya kan wajen kwata kwata,bata ankaraba sai jin hannun wani tayi akan bayanta wani Yana shafawa,zuyawa tayi da niyyar magana sai ta hada ido da wani saurayi ya sha askin wizaye da kuma sabullalen wando,lashe baki yakeyi yana binta da wani dan iskan kallo,
“Yadai yan mata kinaso a cigaba ne ko yah?”
Karisa juyawa tayi sosai tana kallonsa,dauke da dan iskan Murmushi,
“Eh mana ina so a cigaba amma yanzu kamata yayi ya zama layina ne,nice zanyi koh”
Wani washe baki yayi jin abinda tace tana wani kashe muryah.
Cikin lokaci kadan sameemah ta rike ta rike kaciyar sa ta cikin wando da karfi kaman zata cireta,ihu yasaka iyah karfinsa amma hakan bai sa ko motsi tayi ba,saima wani daskarewa da tayi duk kuwa da dukan da kuma kokarin zanyeta da akeyi.
Wani ne yah shiga da gudu ya fadawa shugaba abinda ake ciki,saboda yaron da ta rike dan sane,dama haka yake yi idan mata suka zo wajen neman wani abu,idan kika ki yin abinda yake so sai yasa a koreki,wai ana cewa yana da ciwon zuciyah da kuma dan dabin hankali,idan ba’a barshi yayi abinda yakesoba zuciyarsa zata buga.
Security ne suka rike hannunta ta kowanne bangare kafin cikin saka karfi suka cire hannunta daga inda ta rike,sannan har ya galabaita koh ihu baya iyawa da kyau sai haki.
Duk da hakan idonta yana kansa saima kokarin nufarsa da tskeyi tana huci,shikuwa ganin hakan da gudu yayi bayan wani security na miji kaman yaga aljani.
Ganin tsaida itah zai musu wuyah ne yasa secretary yi mata magana akan ta shiga da bujatarta duk da lokacinta bai yiba,saboda a samu ta rabu dashi da ransa.
Su burgune suka bi bayanta shida lawyer ta wanda idonsa yayi tsuru tsuru.
A office din secretary suka tsaya itah kuma ta shiga office din da takardu a hannunta.
A zaune yake yana zuyawa akan kujerarsa duk da yadan manyanta saidai zama a cikin AC,bazai bawa mutum damar ganin hakan ba.
Itah ma zama tayi a kujerar guess wanda take fuskantarta tun kafin ya bata izini,karemata kallo yake na kurullah kafin ya karbi takardun hannun nata.
Saida yagama dubawa tass kafin yah sauke dan glass dinsa yana kallonta,
“Mekike nufin,cewar bansan labarinki ba,da irin abinda Kika yiwa alhaji bala,saboda ki karbi kujerar aiki daga hannun yaronsa,ko kuma dan kin ga kina juya wasu yan yara a yankinku shi zai sa na yimiki sign sannan na doraki akan kujerar tsaro.
Sannan kuma kin daki yarona a waje,duk da nasan akwai abinda yayi miki amma baki da shaidar hakan,saboda yana da takardar asibiti na cewa bashida cikekken hankali,kinga yanzu dole ki amsa kiran kotu”
Karishe maganar yayi yana shafa gemunsa tareda tsira mata ido dan yaji mai zata ce.
Murmushi tayi mai kayatarwa kafin tace,
“Dama inada wannan halin na barin mutane su gama fadar abinda yake bakinsu,kace kasan labarina,amma bayaninka ya nuna baka sani ba,saboda da kasani da bazakayi furucin da kayi yanzu ba”
Fitowa tayi da dan kunnenta wanda yake yin yar danjar wuta ta ajiyemasa a gabansa,ido ya zaro yana kara karewa abin kallo,tabbas Camera mai recorder yake gani.
Kasheta tayi kafin ta gyara zama,wasu takardu ta mika masa tareda bashi damar dubawa.
Gumine ya yanko masa lokacin daya gama karantawa,(ba komai bane sai taksrdun ban girma da aka bata a kasar Brazil lokacin da suka je horo).
“KO baka fada ba na karanta abinda yaje kan fuskarka,kuma nasan kasan labarin Raudah da take jikin paper,idan naga dama zan iyah neman kujerarka da takardun kuma na samu.
Yaronka kuwa karamin alhakine,dan zan iyah kutse cikin yanar gizon asibitin na sanja information dinsa kaf,zuwa abinda naga dama,kuma babu wanda zai gane.
Dan haka umarnine kasa ka hannu a takardun nan,ka taho dasu gobe zuwa garin mu ka dorani akan kujerar dana ce maka ina so,idan kuma ka kiyin hakan,………….hmmmm toh zaka sauka akan taka kujerar ka bani,sai ka zabi abinda kaga yafi maka”
Tana gama fadar hakan ta fice a office din ta barshi yana goge gumi da handkerchief .
Bata yiwa su burgu wata doguwar magana ba,sai kawai alama da ta musu akan su zo su tafi.
Da gajiyah amma dauke da farincikin samun nasara ta isa gida,sabani wancan zuwan da bata samu abinda takeso ba.
Yau tayi akan zata hadu da ummaruje dan haka tun yamma yake shiri kafin ma rana ta danyi sanyi,dayake ya fadawa mahaifiyar sa inda zaije wato hajiyah mairo,itama sai murna takeyi dan haka kawai take some sameemah din.
Itama sameemah a bangarenta shiryawa tayi,duk da bata arziki bace dan kwalliyar wandunan nata tayi amma tayi kyau sosai.
A motarsa yazo dan haka tana zuwa gaban motar ta shige.
Kowa zai wuce sai yah kalli motar saboda kyanta,kuma ga hasken allah dan kowa yana kallonsu a gaban motar kasancewa ba mai tinted bace.
Tunda ta shigo motar ummaruje yaje murmushi wanda ita kuma hakan ne yasa taji ta takura,dan ta tsani taga mutum yana ta murmushi ko dariyah,shiyasa zama da mata yake mata wuyah,saboda basu da aiki daga gulma sai dariyah da shewa.
“Barka da fitowa baby”
“Wacece babyn wai ni?”
Mamakin tambayar da tsyi masa yayi amma sai daure yah cigaba da magana,
“Gaskiya nayi farinciki da har kamarki wannan kyaky kyawar ta bani izinin nazo ganinta”
Surutunsa yake tayi amma bata sake cemar komai ba saima cewa da tayi,
“Uhm Idan ka gama nizan shiga ciki a gajiye nake sosai,ka gaidamin hajiya “
Baiji dadin abinda tace ba amma haka yah daure tareda mikamata wata bakar leda a kusan cike da kaya.
Kallon ledar take taredashi kafin tah yunkura zata ba motar,saidai tsyawa tayi jin abinda yace,
“Dan allah karkiyi haka,wannan kyautar ba daga hannuna bane ummah ce tace na kawomiki,idan na koma dashi bazata ji dadiba,koda bazakiyi amfani dashi ba at least ki tafi dashi.
Fizgar ledar tayi ko sallama batayi masa ba,shima a nasa bangaren Murmushi kawai yayi tareda cwwa,
“Farkon farawa ne” a ransa.
A can gida kuwa tun kafin sameemah ta shigo har zance ya baza cikin gidan har da makwantai cewa sameemah tana hira da dan gidan alhaji bala a mota,bakin ciki idan yayi dubu toh ya taru a cikin ran matan gidan gandu,dan tsohuwar gaba ce tsakaninsu da jinin inna hajara wanda suna ganin babu ranar dazata gushe a cikin ransu.
Musamman ma uwar gayyar wato innna ramatu,cikin hade fuska taja su sameerah daki daomin taji ainihin tushen zancen,duk da tah leka amma hakan bai isheta ba.
Zama tayi akan gadonta mai rumfa yayinda su sameerah suka zauna a kan kujerar dakin kwallo dayah kaman rai.
“Wai ummah mai kike fadane ban ganeba”
“Bazaki ganeba sameerah amma indai har asirin dayake kan sameemah yah karye toh akwai matsala,dan haka basai gobe ba a yau komin dare zamuje wajen malam domin yimana sabon shiri,tsugunne bata kama mu ba,ba iyah ni kadai ba har da sauran matan gidannan”
“Toh Wai ummah ina ta magana amma kin saKa mu a cikin duhu”
Masifah ta darara musu tareda cewa,
“Dallah ni kuyimin shiru,maza kowa taje ta dauko mayafinta mu tafi,har ke sameerah dake,saboda akwai tsumin danake so ayimiki,dan babu shakkah ina jiyo tashin hankali yana tunkatowa”
Duk su ukun tare suka fito daga dakin,inda sukayi kisibiss da sameemah tah dawo daga waje da leda a hannunta,wanda kowa yah gani yasan ba abune na harkar karanta a cikiba.
Wucesu tayi tana waka ta shige dakinsu,inda sai a lokacin dukkan su suka dauke idonsu daga kanta suna jijjiga kai tareda cewa……..uhmm!

Toh nima uhmmmm………😀😀😀😀

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤28❤

Duk da dare yayi amma haka inna ramatu ta dage akan dole sai sun tafi waje malami,dakyar suka shawo kanta aka bari akan sai gobe da hantsi sai suje.
Can Bayan isha kowa yana kofarsa saiga inna larai da dan mayafi ta shige dakin inna ramatu.
Sun Dade suna dan kuskus dinsu kafin ta fito ta koma kofarta.
Kaman hadin baki kuwa tana komawa itama inna karima ta shiga kofar,itah kam sai can wajen dare kafin ta tafi.
Gabadaya gidan shiru yah koma banda munafurci babu abinda yake zagayawa a gidan,ko na menene oho…….
Da safe gidan da wani yanayi daban yah tashi,
Sameemah tah shiryah ta tafi wajen shirye shiryen hawa kujerar ta
Sukuwa su sameerah sunyi hanyar zuwa wajen malamin sa’ar su.
Yayinda innna larai kuma tace tah tafi gidan su in jita da fada.
Itah kuwa inna karima dayake gidan su babu nisa tun a jiyan taje gida,dawowarta ne ta shiga kofar inna ramatun.
Sauran kofofin kuwa kowa yana fama da tasa matsalar,musamman ma kulu habibiyar manjo🤣🤣🤣🤣.
Shigowa yayi daga wajen mai shayi yana daga wata babbar riga ko waye yah bashi ita oho,kulu ce ta kalleshi da kallo mai kama da harara kafin tace,
“Kai manjo sai ka cemin wai ka tafi shan shayi saina ce ka kawo kidin sabulu da abinci rana kacemin kai baka dashi,wai a ina kake samun kudinne,dan nasan mai shayi ba kanin ubanka bane da zai dunga baak kullum a kyauta ai”
“Ke kulu wallahi ki shiga hankali ki,na hana ki yimin magana kaman dan ki bakyaji koh,toh ba kudina bane ,kudin sadakin sameemah ne nake dan tabawa a matsayina na yayanta”
Tsayawa tayi da hurar wutar da takeyi tana kallonsa da alamar neman karin bayani,ganin bazai sake magana ba gashi kuma ta matsu ta ji mai yake faruwane yasata sake tambayar sa,
“Manjo wace sameemah kake nufi”
“Sameemah dai ta gidannan akwai wata sameemah a garinnan ne bayan itah,shegiya mai suna mai wahalar samu,anayin kwatance mutum yasan ita ce”
“Amma waye yabaka sadakinnata ne”
“Waye kuwa banda amininna sule maye,kinsan irin kaunar da yake mata kuwa”
“Ahah bansaniba amma daga ganinka baka da labarin abinda yah faru a kofar gidannan koh?”
Matsowa yayi kusa da kulu yana baza kunne kaman wata mace a wajen son gulma,
“Ke fa dam in mai yake faruwa kinsan daga ni har sule bama gida mun tafi karkashin gada”
“Ohh dama karkashin gada kaje,shine kacemin wai kana wajen abokanka,toh bari kaji na fada maka dan gidan alhaji bala ne yake son seemah,dan jiya ma yini sukayi suna hira a cikin wata dan kareriyar motarsa,baka ga yanda innarku ta dau fushiba saboda basu sameerah yakeso ba,Nima da zai soni tun yaushe na fige wannan auren masifar ga……….”
Bata kare maganar ba manjoya zabga mata mari tareda cewa,
“Shegiyar yar kundun uba kai,ina tsaye kike cewa zaki je wajen wani saboda kinga yanzu na fara girma bana dukanki kullum”
Bata bari yah karisa fadanba ta ture kujerar da take kai tayi dakinsu da gudu.
Daga rigarsa yayi ya share gumin da yake tsatstsafo masa,dan yasan idan sule yaji labarinanna bai san yanda zasu kare ba sam,da haka ya samu kwarin gwiwar fita wajen, saidai zuciyarsa bata daiNa dukan tara tara ba,dan kudi kam ya cinyesu babu dalikinsu a wajensa.
Saida su sameerah suka hau mashin kusan sau uku kafiin aka kawosu dadai inda saidai su isa da kafarsu saboda duhuwa da kuma matsin wajen,zainab sai ware ido takeyi dan dama ita kadai ce bata san wajen ba su sunsani.
Wata hanyar suka nufa wanda zata kaisu wajen bokan da suka zo dominsa.
A wajen wata bishiyah suka tsaya saiga dariyar sa ta na amsa kuwwa a wajen.
Lokacin daya bayyana a gabansu saida zainab da saka wata uwar kururuwa dakyar inna ramatu ta riketa tana mata alamar gargadi da ido.
Kara rikicewa tasake yi jin muryar sa mai kama da aradu tana dukan kasar wajen (hmmmm sumayyah kiji ta fah,amma take raina kawarki dan tana kallonta kullum).
“Ki Shiga hankalinki ba a yimana yarinta a nan wajen,kinzo karbar sa’a ne ba nuna tsoroba,madubinmu ya nuna mana cewa idan akayi aiki zaki mallakeshi yanda kikeso har sai abinda kikace shi zaiyi,uwarsa data kawoshi duniya ma bata isa ba”
Ai zainab daga jin haka ta gyara zama tana washe baki,zuyawa yayi yana kallon inna ramatu kafin yace,
“Ke kuma ki tashi tsaye,domin aikin da mukayi akanta lokacin ta dake yarinya ba mai karfi bane,domin uwarta duk da mun nakasata tana kokarin yin ibada akan yayanta,toh sihirin dayake saka ta rashin mutunci da kuma jin batason kowa yah matso inda take da sunan yana sonta toh ya karye”
Inna ramatu kaman zatayi kuka tace,
“Malam kayi wani abu akai,naga alamar har tafara yin samari masu kudi,dan ina zaton morar nan ma yaronne yabata”
“Bashine yabata na mahaifinsane ya bata ,dukkansu sonta sukeyi,saidai akwai aikin da za’ayi idan kun amince”
Cikin sauri suka fara jijjiga kansu a tare,
“Zamu maida soyayyar yaron zuwa kan babbar yarki sameerah,duk da bazawara ce amma haka zai nace yace duk duniyah itah yakeso,saboda soyayyar da iyayensa suke yimasa haka zasu amince da hakan,ita kuma zamu kara yin wani aikin a jikinta wanda zai kara saka kiyayyarta a cikin zuciyar mutane kaman yanda kuka fada”
Sameerah wanda tunda aka fara magana tayi shiru,amma jin ummaruje da ko kallonsa bata san zatayiba ance zai sota har ya aureta ai tuni ta jita a wata duniyar daban.
“Yawwa boka dama inaso idan da hali,a rabata da duk abinda ya shafi gidan alhaji bala,saboda kar idan nayi auren ta kawomin cikas,saboda naji kace uban ma yanasonta”
“Eh kin fad’i wani abu,za’a nesanta ta da duk wata kaunar namiji a zuciyar ta indai da niyyar aurene,saidai ke anan zaki zauna akwai turaren da za’ayimiki wanda zai sa shi kwarewa cikin kogin sonki”
Duk da bata son zama a wajen bokan tunda ta san halinsa,amma yau kam bata damuba saboda babban shirin da za’ayi mata,itama zata faso cikin manyan mata.
Wani dauri yabawa inna ramatu wanda za’a saka wa mijin zainab din,sannan da wanda zatayi matsi dashi idan aka zo auren.
Haka inna ramatu ta karba tana godiya suka taho itada zainab din,babu alamar damuwar barin yar ta da tayi wajen bokan
kai wa iyah zubillahi duniyah ina zaki damu,allah yakara tsare mana zuri’a,ya hana mu dogaro da wani bayan shi.
Kaman yanda sameemah ta fadawa shugaban yan vigilantee kuwa,karfe tara ma a garin nnsu tayi masa tareda shi da tawagarsa,duk da a fuskarsa kasan baya farinciki da abinda zai aiwatar saidai babu yamda zaiyi,farillah ne tusa ga mai bacci.
A wani babban hall akayi taron wanda sameemah ta dauki nauyin komai,kama daga tarar baki har zuwa shirya waje da sauransu.
Sai wajen karfe goma kafin ta shigo da kayanta na damara anyi masu dinki mata sun amshi jikinta sosai,dayake dama ta iya tafiyar sojoji sai hakan yabada wani style mai zaman kansa.
Su kansu manyan bakin basu san sanda suka lume a kallonta ba har ta ison kan presentation floor din.
Rigane da wando irin na kayan vigilantee sai wani babban belt daya zagaye hips dinta,ga kuma takalmi mai kaman na sojoji amma na mata,kitsone a kanta amma ta sau jelar ta kasan hular da take kanta.
Babu kwalliyah a fuskarta banda dan lip gloss din da ta shafa,saidai fuskar nan babu alamar fara’a,dan dama bata dariya,a ganinta zubar da girma ne.
Shikansa speaker saida yayi dan gyaran muryah har sannan yana satar kallomta kafin yafara abinda ya kawoshi wajen.
Ba wani bayani sosai yayi ba saina yamda take gwagwarmayah a garin,sannan kuma yah kara da nasa aji moton irin na yanayin aikinsa,wato da abinda tayi da wanda batayiba,sannan da dalilinta na karbar aikin dan san kawo cigaba a garin.
Tafine ya dauka raff raff a wajen musamman ma yaranta wanda suke cikin audience.
Shugannne ya fito shima da kayan aikimsa a jikinsa saidai akwai yana yi tazarar ster tsakanin nasa da na sameemah.
Godiyah yah fara mikawa kafin kuma yayi nasa dan takaitaccen bayanin.
Yaransane ya miko masa takardu da kuma file wanda suke dauke da cewa ya yarda da zaman sameemah akan kujerar aikin,wanda zata zagoramci garin karkashin ikonsa.
Mika mata fike din yayi da hannu daya itama ta miko hannun da niyyar karba,wani kallo yake binta dashi na allamar kinyi kuskure,yayinda itama take aikamasa kallon ina daidai da kai.
Mutanen da basu san mai yake faruwa na gani suke kaman tausaya mata yake akan aikin.
Alhaji bala da kuma Mahmoud dukka sun halarci taron,saidia alhaji bala ko kallon inda take bayyi ba,saboda shi kadai yasan takaicin da ta kunsa mar.
Alhaji Sama’ila kam har taya murna yayi mata,yana wani cusa kai saboda idan bukatar alfarma ta zo,su samu da rangwamemi.
Mic aka bawa sameemah domin tayi bayanin nuna godiyar ta gameda irin nasarar da ta samu.
Karba tayi tana gyara tsayuwa,inda gun yayi tsitt kowa yana jiran yaji mai zatace,
“Da farko dai ina godiyah da duk wanda yah halarci wannan taron,sannan ina yiwa kowa fatan komawa gidan lafiyah,gameda nasarar dana samu kuwa tabbas nayi farinciki,saboda ni kadai nasan dagewar danayi akan hakan,dan haka aiki sai inda karfina yakare.
Sannan bazan yadda da shigowar wani gabana ba ba tahanyar da ta daceba,kowaye shi koda kuwa uba nanne sai na dau mataki akai,Shirina akan aikin nan kuwa nikadai na santa sai kuma idan wanda yayi abin da bai daceba zai gani,da kuma lokaci idan yah ara mana.
Nagode sai anjima”
Dukkan maganar cikin tsare gida da gargadi tayi ta gama,hakan yasa ko tari babu wanda yayi har ta gama maganar tayi shiru.
Sallamatr kowa akayi saboda taro yah kare an bar wanda yah sauka da cizon yatsa shida mutanensa da kuma kudirin daukar fansa.
Yayinda aka bar kuma yan kungiyar sabuwar tawaga da murna da kuma kudirin yin aikin su cikin nasu tsarin.
Dadai lokacin sallah azahar ne manjo ya fito daga masallacin unguwarsu,har sannan wannna rigar gadon ce a jikinsa bai cireba.
Yah karyo kwanar gidan kenna yayi turus ganin sule maye a kofar gidansu yana jiransa,kokarin komawa yakeyi amma babu dama saboda sun riga sunyi ido hudu shi da shi.
Ga shi ba dama yakawo masa wani uxirin dan da alama bai yi shaye shayenba idonsa tar yake,maitar karban kudinsa tah motasa.
Cikin sanda manjo yah isa har gaban sule mayen yana wani sunne kai,tun kafin yayi magana sule maye yace,
“Karkace komai manjo billahillazi kudina zaka bani,dan nima daka gsnni nan ba kudina bane sato su nayi,kuma masu kudi sun ganoni dasu ma muke tare,dan haka ka bani na basu ,ko kuma na nuna ka nace kudi yana wajenka ehe”

Toh manjo ka shiga uku,za’a manjeka kenan😀😀😀😀.

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤29❤

Wuri wuri da ido manjo yayi jin abinda sule maye yake fada.
Gabadaya jikin sa rawa yakeyi,ganin yamda wasu mutane suka zagayesu da alamar sun fi su manjo iyah shege.
Bakin manjo sai motsi yakeyi amma ya gagara fidda ko kalma daya,wani daga cikinsu ne yah kinsa masa duka a ciki,aikuwa ya hada kururuwa yana neman taimako.
Ganin da sukayi manjo babu kudin a wajen sa cikin kankanin lokaci suka fara dukansu kaman sun samu kayan wanki.
Tun manjo da sule suna ihu har sukayi shiru suna karbar ruwan dukan dayake Ziyartarsu.
Karar motace da hayaniya ta tsayar da su daga jibgar su manjon suna kallon waye yake tahowa.
Motar sameemah ceh a gaba sai wata mai bodi an cikota da mutane kuma anyi mata paint irin na uniform din jikinta.
Fitowa tayi daga motar ta mutane suna binta a baya harda yan kungiyarta,a wajen su manjo ta tsaya wanda sukayi futu futu da rairayin wajen,saboda burburwar da sui tayi.
Kallon masu dukannasu tayi tareda tambayar su abinda yah faru,
D’aya ne daga cikinsu ya zayyane mata abinda yah faru,kuma ta yadda da hakan dan sunyi maganar kudin kuwa ita da manjo,sannan tasan ko za’a kashe sule maye bashida inda zai samo dubu biyar ma bare har dubu talatin,dan matarsa ma da shi kansa innarsu ce take ciyar dasu.
Hakuri ta basu inda suka ce,dama tafiyah zasuyi tunda sun daki na kudinsu,saida suka bace daga layin kafin Sule ya karkace baki yace,
Dama nasan har yanzu kina sona kawai zancen mutanene,gashi kin cece………….”
“Kai Dallah yimin shiru marar hankali kawai,duk da dukan daka sha hankalin ka bai dawo ba koh?,kasake magana a wajennan in ban kirasu sun karisa ka ba yanzunnan”
“Kai kuma (tafada tana nuna manjo wanda fuskarsa tayi buleliya koh magana bayayi),kasake karbar kudi ka kashe kai a dole ga mai son banza,kaga yamzu sai kulu tayi jinyarka koh?”
Tana gama fadar hakan ta yiwa wasu gardawa guda biyu magana akan su kinkimi sule zuwa gidansu,yayinda wasu guda biyun kuma suka shiga da manjo shima gida,sai nishi yakeyi saboda tsamin jiki.
Tsitt kakejin gidan babu hayaniyah saboda kofar kawu shehu innna karima ce kawai a ciki,abokiyar fadannata wato inna larai bata nan bare a jisu ,ita kuma inna ramatu har yanzu itama bata dawoba.
Kofar kulu tah nuna musu akan su kaishi,dan bazata iya da kuma hayaniyar kulu ba a lokacin,idan ta huta koma menene sai ayi,dan dama an saba ba yaune farauba.
Kwanciya tayi ta kashe wayoyinta saboda kar a dameta.
Baccine yayi gaba da itah har sai wajen isha kafin ta tashi,domin shirin tafiya dinner da za’ayi na samun kujera da sukayi.
Wanka kawai tayi dan babu batun sallah,kafin aka zo fara shiri,rigar da akayi domin zuwar ranar ta dauko mai masifar kyau,daidai ciff jikinta rigar ta kama,ita kanta saida ta juya tayi Murmushi a gaban madubin kafin ta zauna domin yin hira.
Dadai misalin karfe tara ta gama shiri saiga kiran umaruje,dan dama cewa yace tayi masa izinin ya kaita wajen dinner,da har taki amincewa amma ganin yanda ya damu yasa tace babu komai.
Toh kawai tace kafin ta fita tana tafiya a hankali saboda takalmin da ta saka mai tsayi.
A bakin kofar shigowa ta hadu dasu sameerah zasu shigo,tun safe da suka fita sai yanzu suka dawo,kallon kallo sukeyi da sameemah ganin kayan alfarmar daya ke jikinta.
KO ci kanku bata ceba ta nufi motar umaruje wanda yah ke tsaye a kofar gidan.
Yana ganin tahowarta ya fito tareda bude mata kofa ta shige,shima ya koma ya ja motar suka bar wajen.
Duk abinda yake faruwa akan idon su inna ramatu wanda suka fasa shiga cikin gidan suna kallon Ikon Allah.
Sameerah ce ta hade fuska gameda dunkuke hannu tace,
“Ummah kin Gabi koh,wallahi yau zan fara amfani da maganinnnan basai gobe ba,tunda boka yace matukar tashi tsaye mukayi ba toh abin sai ya fi karfinmu”
Hall din da za’ayi dinner ya dau haske da kida ga dare kaman ba shiba.
Sameemah suna shigowa aka dau ihu da tafi,ita kuwa dan Murmushi kawai tayi na gefen baki alamun ta ji dadin abinda sukayi mata.
Wajen da aka tanada dan zaman ta ta nufa kafin salon kidan ya sauya.
“Kai aboki dan Allah ganemin lady din can,gaskiya duk wanda ya sameta yah more,ga kyau ga kuma zarrah,kai da ganinta kaga zazzafar manyan mata wanda ake shiga taro dasu”
“U hmm saidai ka gani daga nesa,ita cefah aka zo taron dan itah,sabuwar shugabar yan vigilantee ceh toh,kai ma daga gani kasan za’a sha dabi,mace da shugabancin yan kato da gora,ai abin Akwai show billahillazi”
“Hmm Bari kawai,ni ina ga da gangan zanyi laifi dan akaini office din ta na dung a Ganinta kawai”
“Saika DA ur a niyya,idan naga ta wanye lafiya dakai toh nima sai nayi,dan ba a shaidar mutum a fuska,tsaff sai ta baka mamaki ina fada maka”
Hakadai abin yakasance kowa yana fadar albarkacin bakinsa,shikuwa umruje duk yanda yayi da sameemah tazo suyi rawa kin amincewa tayi,iyah yanka cake akayi aka danyi serving abinci kafin kowa yah kama hanyar sa.
Watsewa akayi saura iyayen gayyar wato sameemah da tawagarta,direct gidan kungiya suka wuce za’a fara sabon shagali,dan dama ta ayyana a ranta ita da gida kuma sai gobe.
Da daddare da kyar su sameerah sukayi bacci saboda tunanin mai zai faru,dan maganar boka na cewar indai har ba rabata akayi da maza ba toh bazasu taba auren miji mai maiko ba,hakan sukayi ta jiranta bata dawoba har sukayi bacci.
Zainab ce ta shigo sauri tareda fadawa inna ramatu sameemah tana shigowa cikin gidan.
Cikin gudu gudu sauri sauri suka gama abinda zasuyi kafin ta karaso.
Shigowa tayi amma kayan dayake jikinta ba na jiya bane da alama tah sauya kaya,babu sallama bare bisimillah haka ta zefa kan ta dakinnasu,wani abune taji ya coki tsakar kanta har saida kanta yah sara lokaci guda,sannan idan bata manta ba tah taba jin irinsa lokacin da ummah tana da rai.
Basarwa tayi tareda shigewa cikin dakin kawai,duk da kannata bai bar sarawa ba amma bata kawo komai a ranta ba sam.
Uniform din aikinnata ta dauka tana kallo hade da murmushi ita kadai tasan mai take rayawa a cikin ranta.
Wayar ta ce tayi kara tana dauka taga surayyah ce,kayan hannun nata ta ajiye kafin ta daga kiran.
“Hello Allah ya taimaki ogah”
Aka fada a daya bangaren,
“Dama Bayan an gama shagali munga ogah burgu yah bamu kayan uniform ne na aiki,dama ogah abinda wurine haka”
“Me kike nufi baku shirya bane”
“Ahah min shiryah ogah allah ya bamu sa’a toh”
“Yau Ku tabbatar kun gyara office din da duk wani abu daya kamata,ran monday kowa yasa uniform yah fito aiki,idan kuma naga mutum yasaba lokaci zai fadawa yan garinsu,kafin lokacin zan tsara wa kowa aikinsa da inda yakamata ya yi aiki,sannan zan duba tsofin maikata idan sun cancanta kuma zasuyi aiki dani toh zan barsu amma wasu dole zan sallamesu.
Dafatan kin saka a speaker kowa yana jin abinda nake fada koh”
“Eh kowa yana jinki shugaba,bari muje gida mu shirya saimu tafi gyaran office din,kuma ran Monday da asuba zanje,ai mun fi kowa jin dadin aikinnan”
“Ya is a haka ban as on surutunki nan surayyah,kudai kuyi yanda nace kawai”
Tana jin surayyah tana surutu amma ta shareta ta kashe wayar ta,shiyasa wani lokacin shirinsu da surayyah sai a slow,akwita da surutu da kuma lalaci,kubra da lubna sun fita nesa ba kusaba,saboda koh a maza ma sai an tona a samu kamarsu.
Tun daga bakin kofah umman su surayyah take jiyo feduwarta a zauren gidan har ta iso tsakar gidan. Ummah bata kulata ba sai cigaba da tsinar shikafarta da tayi,shima nazeef dayake zaune suna hira da ummah kallonta kawai yakeyi,
“Gaskiya umma ke yar gata ce fah”
“Da akayimin me mai sunan uwata?”
“Duk yayanki aikin damara sujeyi,nice ma babu wanda yayi zaton zanyi koh goge gogene sai gani da dankareren aikin vigilantee,ran monday dinnan mai zuwa za’a fara kwatance damu a garinnan,kuma wallahi babu mutunci kan ta ko uban waye,tunda shigaba ta bamu lasisi”
“Dallah rufema na baki,a wane aikinnaki da bai taka kara ya karyah ba”
“Kai ji nazeef dinnan,yo ba gwara namu ba da wannan shegen aikin sojojinnaku da mutum bai isah yayi abinda yaga dama ba,kullum hannunsa yana gefen kansa shi a dole ga mai biyayya”
Haushi ne yakama nazeef inda yah tashi zai maketa,ummah ce ta hana tareda cewa,
“Mai kake ci nabaka na zuba,ni bakaga kyaketa nakeyi ba,ai baza’aje ko ina ba zaka jita da ogar tasu,ina wannan yarinyar ce,kyaleta da ita kawai”
Ahah ummah albarka zaki saka mana zamu fara aikin damarar muma muji mai wasu suke ji a ciki,har suke tada mana jijiyoyin wuyah”
“Allah yasaka albarka”
Shine kawai abinda ummah tasu tace,aikuwa daga jin haka surayyah ta hau wani kirkirar doron da da bata dashi,
“Shikenan ai tunda kika saka albarka ummah to kowa ma yah kushe,kuma gyara gariannan sai inda karfin mu ya kare,sai mun kafa namu tarihin”
Tana shiga daki kuwa bata wani dade ba sai gata ta fito da uniform dinanta ta janjame belt dinnan kaman zata miyar shi cikin cikkinta itah a fole tayi damara.
Kallon su nazeef sukeyi suna boye dariyarsu dan karta gani,
“Yawwa ummah kallifa uniform din yanda sukayi min”
“Eh nagani kam,sunfi wannan tsukakkun wandunan naki,yau kam babu cin abinci da sauri ne,ko kuma yau baza’a koma ba ne?”
Zaro ido tayi sai sannan ta tuna ashe zasuje shiryah office,komawa dakin tayi da gudu tana cewa,
“Wayyo na manta Ashe fah ance mukoma,yau inaga tsire shugaba zatayi da nama na idan taji,ummah hada abincin gani nan fitowa yanzu nan”
Jijjiga kai nazeef yayi dan ganin ahirmen kanwar tasa,
“Wai ni ummah yau ban jita da safe ba,ko yau ma bata kwana a gida bane?”
“Eh amma ta fadamin wai dinner zasu je na shugabar tasu ta samu kujera sanann kuma suyi shagali nasu daban,har gari ya waye,kasan shahshancinsu ai,tun wancan satin take lissafin shagalinnan,mudai addu’a zamuyi tunda yanzu ta daina zuwa kwana a wani wajen ma a nemeta a rasa,amma wannan sai da ta fadamin su da sameemah ne da kowa,kaga ba lallai ne ayi badala a wajen ba,saidai sharholiya kam wannan wajibine”
“Toh shikenan Allah yah kara shiryawa ,indai zuwa wajen seemah alkhairi ne ana ganin sanji ai sai aiyi ta yimusu addu’a gaba dayansu”
“Hakane abinda muke fata kam”

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤30❤

Manjo ne a kwance akan wata katifa wanda da ita da babu ma duk daya ,sai nishi yakeyi yana daddaga ciki,ga fuska tayi suntum kaman yan mata zasuyi kwalliya sai sheki takeyi.
Haushine ya ishi kulu ga wutar da take kokarin hurawa taki kamawa ga kuma dawainiyah da manjo.
“Kulu zo ki gyara min wuyannan nawa yayi tsami”
“Kai Dallah kaima ka rabu da ni,dame zanji wai,da wannan shegiyar wutar ko kuma da kai daka dameni,aikin banza lokacin dakake cin kudin ai bansaniba saida wahala tazo za’a zibgemin yau ga jaka”
“Yanzu kulu ni kike fadawa haka ,ina mijinki”
“Miji ? Muna miji dai,ai nayi kokari ma yini gudan da aka kawoka wane shegen ne ya leko a cikin yan gidannaku ya ga ya jikinka,har uwar da ta haifeka ma bata san me kake cikiba,ta dorawa kanta bakin kishi akan wacce ko yawo take da bakin jaki bata isa da itah ba(sameemah),daga ganinta da mai mota ta kwallafa wa ranta sai y’ay’an ta sun aureshi,sai kace itah nata dan motace dashi ake zaune dashi”
“Yanzu kulu ni kike zagi dan kinga ina kwance kuma harda uwata”
“Eh an zage kam,mai zakayi iyee?,kai ba gwanda kowa ma a cikin gidannan da kai ba,kafi kowa rashin amfani ,dan mugunta aka tashi aka hadani da kai,kuma duk inna ce ta bataka itah a dole ga mai da bata san laifinsa,gashi nan ta cuceka ta cuceni nima da nake ta fama”
“Haba habibiyata share hawayenki wallahi ina sonki sosai,kuma na miki alkawari kodan farin cikinki zan zan shiryu idan na warke na fara sana’a”
“Babu wani dadin baki ne dan nayi jinyarka saika warke ka koma gidan jiyah”
“Bazan komaba kulun majatan uwar gida sannan kuma amaryar manjo”
Murmushi tayi najin dadi kafin tazo ta gyara masa kwanciyar,sai nishi yakeyi babu dauriyah.
Sameerah ce zaune a bakin katifarta sai tadi takeyiwa sameemah wanda take danne danne a waya,
“Uhm naceba yar uwa mai yah farune naga kwanannnan sai zirga zirga kikeyi,koh wani abune yasamu”
Dan tsabar mamaki lokaci daya salma da sameemah suka dago suka kalleta jin yamda ta kira sameemah din,da farko kam ma saida sameemah ta kalli salma dan ta zata da salman take magana,amma sai taga ita take kallo.
“Uhm wani abu nakeyi,na riga ma na kammala sai kuma fara aiwatarwa”
“Ayyah allah yah taimaka,yah saurayinnan naki dana ganku tare kuwa”
Murmushin gefen baki sameemah tayi dan ta dago sameerah din,bare kuma salma wanda itah dama kar tasan kar ce itada sameerah,
“Yana nan kalau shima”
“Uhm amma yaushe zaki hadani dashi mu gaisa kuwa”
“Banida iko da rayuwarsa duk sanda kika ga dama kika nemeshi zaku iyah gaisawa banda business da hakan ni”
Shiru sameerah tayi daga haka dan taga babu alamar samun nasara a zancen.
Zainab ce ta shigo dakin tana rusa ihu kaman ranta zai fice,sameerah mai karfin gwiwar tambayar ta menene,amma sauran mutanen dakin koh kallo bata ishe su ba,
“Ba……..ba shine ba wai an zanye yin auren sai ya dawo daga service din aikin dan sanda ,yace wai sai bashida kudi toh sunansa ya fito a cikin masu tafiyah service,kuma dama wai bai gama giniba yana so dama a daga auren”
“Koh so yake yah gudu dama ba”
Salma ta fada tana dariyar mugunta,wani ashar zainab ta nana mata kafin suka rukume da fada kaman karnuka.
Itah kuwa sameerah da dakin mahaifiyar su ta nufah da sauri domin jin tushen bayanin.
Da wuri ta tashi yau babu baccin safe,wanka tayi ta ruwan sanyi amma ba ta sanyin take na burinta kawai taje inda yake ranta.
Kayan uniform ta dauko na vigilant ta saka,dan karamin hijab din kayan ta saka tareda dora hular a kansa,hoda ta shafa kawai sai mai kafin ta feshe jikinta da turare,glass ta saka baki wanda yayi match da wandon jikin ta ga kuma kalar fatarta ta fito a cikin coffee rigar tasu,jakar ta dauka da kuma key din motarta kafin tah fita daga dakin.
Duk abinda takeyi su salma suna kallonta,dukkansu mamaki suka dungayi da ganinta cikin kayan,dan babu wanda tah fadawa zata fara aikin.
A tsakar gida kuwa bata hadu da kowa ba har ta isa wajen motarta ta shiga.
Su surayyah kuwa an fi kowa d’oki dan rana ma acan ta fito ta ganta,dukkan su kame wa sukayi tareda sarawa lokacin da sameemah tah iso wajen,dan labarin sauyin shugaba dama yazo musu,kuma sunyi farincikin da hakan dan dama babu wanda yake somsa,shiyasa da tace wanda yake bukata zai iyah tafiya babu wanda yah tafi,suna fatan dai kar ayi gudun gara a tadda zago.
Fitowa tayi a motar tana gyara zaman glass dinta fuskarta babu alamar fara’a bakinnan a d’ane.
Hanyar office dinta ta nufa koh kallonsu batayi ba,wata bazawara ce wanda anan suka zo suka samesu tah kalli surayyah tareda sauke murya kasa kasa tace,
“Hmm kika ce shugabarku tanada mutunci?,amma yanzu ji yanda tazo ta wucemu koj kallonmu bata yiba bayan wannan shine zuwanta na farko”
“Ke me kike ci na baka na zuba yanzu fah aka fara wasan,ki tsaya ki gani mana”
Itah kuwa sameemah batayiwa kanta a ko ina waijiba sai kan kujerar ta office din,saida ta zuyah ta sake juyahwa kafin ta saki wani dan iskan Murmushi.
Wasu takardu aka kawomata da alama sauran aikine da tsohon shugaban bai gamaba.
Zare glass din idonta tayi ta ajiye a gefe kafin ta daga takarda tah farko,case ne akan yanda karuwai da yan daudu sukayi yawa a gidan kara,yan hisba sun kawo case din akan za’a hadu dasu ayi amma babu wanda yayi magana.
Sai kuma na gaba yanda sane yayi yawa a kasuwa sannan idan an kama su yan sanda basayin komai akai,da kuma wani saurayi dayah kama wani tsoho a unguwarsu yayi masa duka,dan kawai yakaishi kara yah sace masa akuyah.
Dariyah sameemah tah fashe da itah saida mai kawo takardun yah ja da baya,daga ganin dariyahr kasan ta mugunta ce zallah,
“Irin wannan kujerar dama nake nema,inda zan baje tawa baiwar,kai inaso ka kiramin duk wani maikaci yasameni a waje yanzunnan”
“Angama Ranki yah dade”
Da gudu yah fitah kaman zai kifah.
Bayan mintu kadan yadawo tareda shida mata kowa ya hallara.
Fitowa tayi ta tsayah a gabansu,kowa yah kame kaman an daskarar shi,yaranta ta kallah acikin tsofin maikatan dukkan su sun sha kaya kaman ba suba,koba komai taji dadi da ta sama musu sana’a.
“Inaso kijini da kyau,wanda suke wajennan dayawa dama yarana ne nasan halinsu,su kuma sauran na duba bayanansu wanda ina fata muyi aikin daya kawomu banason shashanci.
Abinda yasa na kiraku shine,akwai casr kuda uku wanda sune suka fi girma kuma ina so yau dinnan basai gobe ba a gama dasu”
File din ta Bude tareda kiran suna,saida ta tabbatar ta raba wani rukuni gida uku tukunnan tace sauran su koma aiki.
Su burgu tah nuna da wssu suma biyar tace su je kasuwa,duk wanda yayi sata su kamo mata shi kafin ma yan sanda du sani,sannan wsu ma guda uku tareda surayyah da kuka shamsiyyah(bazawar nan),su kamo mata yaton da yayi duka ga tsohon anguwarsu.
Sai kuma wanda tasaka akan aje gidan kara kamen karuwai,amma kar a tabasu har sai taje tukunnan,kawai suyi kaman ba wajen suka jeba su yi shiru har zuwa yamma.
Nuna lubna tayi da kubra kafin tace su biyota zuwa wani waje.
Direct office din hisba ta nufah,tana isa ta nemi iso zuwa office din shugaban,shiga sukayi ta zauna su kuma su kubra suna tsaye a bayanta sun kame,dan dama matan sun ji karfi da kuka kira,bare suka samu training daga wajen sameemah na salon fada daban daban,shiyasa itama take ji dasu ta wannan fannin.
Dagowa yayi daga rubutun dayakeyi yana kallonsu,ganin sun shigo amma babu wanda tayi magana,
“Eh ina jinku mai ke tafe daku”
“Da baka tambayi mai ke tafe damu ba shiyasa nayi shiru domin baka daMa ka gama,amma yunda yanzu ka taambaya sunana sameemah sabuwar shugabar kungiyar vigilantee. Gameda abinda yakawomu kuma ba kkmai ba ne illah akan zancen case daka rubutah na gidan karuwai ne yakawoni saboda na ganshi a office”
“Eh anyi haka amma wannan case din yace bazasu damar yiba,ku kuma muma muna wani aikin har yanzu gashi bamuda wasu ma’aikata masu yawa,idan muka ce zamuje irin wannan aikin mu kadai,mukan samun barazana,toh shi kuma yace mana wai ogansa ya hanashi irin wannan aikin”
Numfasawa sameemah tayi dan tasan wa yake nufi da ogan,
“Shikenan karma damu dama akan case din nazo,Inaso kasaka hannu akan takardar Ta yajejeniyar ni zan ajiyesu a wajena ba ma kune zakuyi ba, nikuma a yau basai gobeba zan kamasu”
Hankalinsa ne kaman bai dan kwanta da zancneta ba dan da alama bai wani yarda ba,ganin hakanne yasa tace,
“Idan wata matsala ta faru ka dora laifin a kaina sannnan karka sake bani wani hadin kai anan gaba”
Karbar takardar yayi yai mata sign din kaman yanda ta bukata kafin yabata.
Tana fitowa direct gidan karuwan suka shige,acan nesa da wajen suka hadu da sauran yarannata inda itama ta fito daga motar ta suka shige.
Gidane mai fili sai dakuna dayawa,kaman dai gidan haya,da wasu yam daudu suka fara cin karo a tsakar gidan suna wasan karta,aikuwa suna ganinsu suka rufah da gudu kowanne yana zefar da zanin daya rufe kirjinsa dashi.
Dakuna dakuna suke bi suna fito da mutanen ciki,mutane kala wasu da attach wasu saikace fatalwa dan fari.
Duk tarasu akayi a tsakar gidan masu ihu suna yi masu roko sunayi.
Wata kujera sameemah taja ta zauna tanan kare musu kallo,wai yau itah ake roko kartayi rashin mutunci,gashi kuma gangar rashin mutuncin nata ta riga ta kada sauti.
Wani dan daudu ne yakalle ta tareda cewa,
“Haba ke kuwa sister ai andaina zamanin kame tun wancan karnin,ki fadi kawai nawa kike so a baki a wuce wajen”
“Ahah mai kake ci na baka na zuba dama ai za’ayi ciniki,har saikayi cinnki ka kaji,yanzudai bari muje a gyaraka ka koma ainihin siffarka tukunna koh?”
Shiru yayi jikinsa yafara tsima jin abinda tace,wata ce a cikinsu tace,
“In gaskiya ne naga ba’a je chamber su yar sheelah ba idan iskanci ne ma ai sun fimu,kawai dan dai suna lungune”
Tashi sameemah tayi tareda iza ketarta tana cewa,
“Ina ne muje ki nuna min wajen,wayaki k’aari kuma”
Wani lungu suka bi sai gasu a wani gidan irin wanda sukayi kame a cikinsa,dakin dayake farko sameemah ta bankada tah shige,zare ido tayi dan ganin da wanda suka hada ido.
Shima zare idon yayi da yai kulu kulu a duhu,gashi yah hada gumi shirkiff.
Da kyar bakinta ya samu damar tattaro harafin kafin ta furta….
“Kawu sheeeeehu!!!”

Toh lokacinku yah kare sai wani jirgin yazo zai dibeku yanzu dai ku sauka a nan wajen…………..

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤31❤

Tunda suka hada ido da sameemah duk wani motsinsa yah dauke saura kawai rawa da jikinsa yakeyi,musamman daya ganta da kayan da duk masu hali irinnasa suke tsoron su rutsasu.
“Miye katsaya ka tsaya kana kallonna koh so kake nazo na saka maka wandonnaka harda wani rawar jiki,ai na karya kakkeyi zakayi bayani ne yau”
Har sannan bakinta dauke da murmushi dan taan son irin haka dama,Kallon matar tayi wanda ta ja bargo tah rufe jikinta tana sunkuyar da kai.
“Hmm ji munafuka dallah ku tashi ku fito inason ganinku a waje yanzunnan”
Tana gama fadar hakan tah fice daga dakin tareda nufar sauran dakunan.
Babu kowama a cikin su saboda tuni sauran ma’aikatan suka rarrako su zuwa wajen sauran.
Dukkan su maza da mata yara da tsofi kkwa yah Zauna yayi shiru domin yaji abinda zai faru,mai gidan hayar ne ya shigo da sauri wani yaronsa yana biye da shi,da waya hannunsa koh takalmi bai saka ba,daga ido sameemah tayi tana kallonsa domin jin shikuma da me yake tafe,
“Ina gida naji ance gidan hayata ba lafiya,wai masu kamen karuwai sunzo,toh ke kuma wayah aikoki saboda yanzu ma muka gama waya dashi bayuimin cikyakykyen bayani ba,dan idan kudinharaji ne nariga na bayar hada karin danakeyi a shekara,amma waka a bakin mai ita tafi dadi bari kiyi magana dashi.
Yana gama fadar hakan ya mikawa sameemah wayar dake hannunsa,dauka tayi kafin ta saka hands free,
“Hello……..hello.sameemah bai kamata daga hawa aikinki har kin fara saba dokaba,kamata yayi idan zakiyi abu toh ki nemi shawara mana,yanzudai komai yah wuce ki baro Gidan zamuyi magana kawai sannan………..”
“Alhaji bala KO nace Bala,kadaiji yanda na kira sunanka koh,toh billahillazi idan na sake jin hannunka a cikin aikina koda dan kadanne,kai ko wani nakama yafada maka kabashi koyon baya,toh wallahi idan muka dunga buga chakwakiyay dakai saina yi maka kaca kaca,hatta zaman garinnan ma kai har cikin yan uwanka ma sai yayi maka wuyah a rayuwarka,idan kuma kana tunanin ban kai nayi hakan ba toh bismillah mu zuba ni dakai”
Daga wayar tayi ta kwankwatsata da kasa tun kafin ma taji mai zaice daga daya bangaren,jiki na rawa mai gidan hayar yaja da baya yana kallonta.
“Kai kuma idan baka bace a wajennan ba ,toh idan na tashi dakai zan hada harda mataimakinnaka”
Tun kafin ta rufe bakinta yah yayi waje da sauri yana baza rigarsa.kallonta ne yah koma kan wanda aka kama din wanda idonsu zuwa yanzu yah raina fata,
“Ku kiramin wanda na aikesu kuma na ce su tsaya a waje yanzunan”
“An gama ranki yah dade”
“Wani dan gajere daga cikin yan vigilantee dinne yah fita da gudu zuwa waje,basu dade ba sai gasu sun dawo da wasu garada guda biyar,kowannensu dauke da dorina mai kai biyu,
“Kubisu KO wanne kuyi masa bulala goma goma,sannan ku saka su a mota zuwa office”
Ihu suka fara da kururuwa saidai babu yanda zasuyi tunda tafada toh fah lallai sai anyi musu.
Bayan angama round Donne kowa sai nishi yake yi wasu kuma suna tah soshe soshe,masu ragwanta kam harda kukansu.
Har an tashi za’a tafi sai sameemah tah dakatar dasu tareda cewa,
“Tun daga ina akeson shugaba yayi adalci idan ya hau kan mulki?”.”
Had’a baki sukayi tareda cewa,”daga gidansu”
“Toh Indian hakane a matsayina na shugaba mai adalci sannan mai nuna yakamata,zanyi adalci ta hanyar karawa kawuna dayake wajennan bulala ashirin kacal,kunga tah kama talatin kenan anyi masa ninkin nasu sau uku”
Dama tun lokacin da sameemah tafara wannan maganar muguntar kawu shehu ya fara tara kwallah a idonsa saboda yasan bazata barshi ya tafi haka banza ba.
Tana nuna yatsanta akan sa garsawannan suka tattagoshi dama basu gaji ba,taleshi sukayi aka fara tsula masa sabon wani lissafin.
Saboda tsabar wuyah kasa ihu yayi sai nishi kawai kaman balamar tunkiya tazo haihuwa,kusan za’a kai karshe kawai gani sukayi wandonsa ya rine da fitsari yana zuba.
Duk da zafin dukan da’aka yimusu saida wasu sukayi dariyah ganin yanda kawu shehu yake fitsari.
Kowa tashi yayi yana dingisawa har wajen motar tasu,shikuwa kawu shehu saida aka tattageshi saboda lagabewa da jikinsa yayi.
Suna zuwa office suka samu su surayyah sun dawo,kuma sunyi nasarar kamoshi kaman yanda aka fadamusu,saidai masu sata a kasuwane ba’a kama ko daya ba.
Wajen da’aka kaishi sameemah ta nufah tareda tsugunnawa a gabanta.
Dayake dan duniyah ne kallon cikin idonta yake yana cewa,
“Dama barin zancen nan kikayi yah wuce yan mata,dan babu abinda zaki iyah a kai,dukane na riga na dake shi”
Tashi tayi daga kusa dashi dan bai isheta ma kallo ba a yanda yake,wani na gefe ta bawa umarni akan yayi masa hukunci kafin a kai shi wajen yan sanda yah bada tara.
Marinsa ma’aikacin yayi amma yah zuyah fuskarsa yah tofar da yawu yana Murmushin taurin kai.
“Ashe Baki cika sunan ki ba na jar wuyha sannan baki cancanci gwagwarmaya da irin mu ba,nayi mamaki da aka cemin yanzu macece shugabar yan kato da gora,amma yanzu na gane kawai daurin kafa kika samu har kika hau kan kujerar,kuma kina daga gefe kina saka mutane aiki suna yimiki,kir idan kin isa ki kiyi dealing da mu mana da kanki”
Har sameemah tah taka kafarta zata bar cikin wajen amma ta tsaya cak saboda jin maganar dayake fesa mata,jijiyoyin wuyanta ne suka tashi lokaci daya,damke hannunta tayi da cije baki,ba wanda bayyi mamaki ba ganin yanda takoma gabansa tah tsugunna.
“Bazan ce komaiba akan abinda kace,saidai daga ni har kai zamu buga wani wasa sai aka ya zai in ma dorani akayi akan mulki saboda inada daurin gindi koh kuma matsayina yakai nasamu.
Wasan mai sauki ne idan ka fahimata,zamu bada filin daga tsakaninmu,kowa zai fita babu wanda zai saka hannu,sannan idan har kayi nasarar yimin dukan da bazan iyah tashiba toh zan baka duk abinda ka bukata kuma za’a sallameka anan wajen,kuma babu ruwan shari’a a ciki.”
Murmushin jin dadi yayi dayaji abinda tace,shikuwa wanda aka Bashi ajiyarsa kallon sameemah yayi da alamar gargadi na batasan yan iskan zamani ba fah.
Nuna masa tayi ba matsala tareda cewa,
“Karka damu babu abinda zai faru ,kawai ka bamu waje sannan kace ban yadda koh wani abune yah faru wani yah shigo ba”
“Shikenan tunda kince haka amma duk da haka zamu tsaya a kusa saboda tsaro”
Jawo musu kofar yayi tareda nufar su burgu dan yasanar musu abinda yake faruwa saboda yasan su zasu iyha yi mata magana,amma yana gama bayanin yaga kowa yah cigaba da abinda yakeyi.
Kallo akeyi tsakanin sameemah da saurayin,saurin mike wa yayi yana gyara wuyansa wanda ya bada kara kakkkk,dantsensa ya daga yana murdawa domin bata tsoro,ba karyah kam namiji ne majiyin karfi wanda zai iyha firgita duk wanda yaga dantsennasa amma babu alamar hakan daga wajen sameemah,saima kara matsawa da tayi tana bashi waje ya gama motsa jikin.
Cikin sauri yah shammaceta ya kinsa mata naushi a fuska saida ta juya,dago da fuskarta ta tayi tareda yimasa murmushi kaman babu abinda yah faru,wani naushin yakara kawo mata inda tayi saurin rike hannunsa da nata hannun,jijjiga hannunsa yayi da niyyar janyewa amma yayi yayi yakasa kwacewa,mitsitstsikawa tayi sai ji kake kururrs kurus.
Wata kara ya sake yana kallon yanda yatsuna hannusa suke kokarin tashi a aiki,amma duk da haka yah kara kawomata daya hannun,wannan karon ba iyah Yatsun ta karya ba harda tsintsiyar hannun,sannan ta kara masa da wani duka a akan gwiwarsa hakn yasa
Ya zube a gabanta akan gwiwoyinsa,
“Yanzu mai zaka ce game da aikina,koh kana da wani saurin bayanin da kake son isarwa gareni,idan kuma karaya uku bata isheka ba saina kara maka wani ,hadda wani kawo naushi da karfi kuma wai ga mace koh kunyah bakaji ma”
Saboda ranar ba wani bacin rai takeji ba dan ma taji furucin da yayi ne,gashi a aikin banza yah jawo wa kansa duka.
Dakin da aka kai su kawu shehu ta nufah,suna hada ido da shi yayi saurindauke kai,
“Zaku Zauna anan za’a dan yimuku horo kafin kowa yah tafi gidansu,wanda kuma suke a wani garin za’a saka su motar garinsu”
A wajen park din motarta suka hadu da wanda yake kula da saurayin da yah sha dukan,
“Yawwa kaje ka duba shi ayi masa dorin karayarsa zuwa gobe zamu kaishi wajen yan sanda”
“To shikenan sai gobe toh”
Daga haka ta bar office din ta nufi gida.

Tun a bakin kofar shiga gidannasu da hangi sameerah suna fira da ummaruje sai wani sunne kai takeyi itah a dole ga mai kunya,shikuwa har wanj lekata yakeyi yaan dariyah.
Tun kafin ta fito daga cikin motar ta karemusu kallo tass,duk da abin yabata mamaki amma kawai tah watsar abin aranta dan bata ga dalilin sake tunawa dashi bama.
Kashe motarta tayi kafin tazo bin ta kusa dasu zata wuce,hakan bai ishi sameerah ba ko tana tunannin bata gansu bane,?oho
“Lah sameemah kin dawo ne,ga ummaruje ku gaisa mana,tun dazu nake cemasa bari kizo ku gaisa amma yace wai na daina yimasa zancenki amma bari kiji daga bakinsa ma”
“Ahah basai najiba nima ban nemeshi ba ai,dama kece kike neman na hada ki dashi nacemiki idan kika nemeshi kuka gaisama babu abinda ya shafeni gashi kuma kun gaisa din na gani,kuci gaba da gaisawarku kawai”
Har sameemah ta saka kai zata wuce kuma sai sameerah ta sake cewa,
“Naji ummaruje yace wai dama ke kika je har gidansu wajensa koh?”
Abinne yabatawa sameemah rai dan rainin hankalin yakuma fara isarta ga kuma gajiyah da ta kwaso yau din,komawa tayi har wajen, kafin ta kankance ido ta fara cewa,
“Ke sameerah wallah in baki rabu dani ba ranki zai baci,me kike nufi shidin daya fadamiki yana tunanin wajensa najene?toh ki fadamasa duk da naga kaman wannan bashine a gabana ba tunaninsa yana wani wajen daban,wannan gangar jikice,toh idan yadawo hankalinsa kice masa ba wajensa najeba,wajen ubansa naje domin yi masa gargadi,kuma dama koda bai fita a rayuwata ba zan fitarda shi,dan ko a farcen kafar mutum din da zai iyah rayuwa dani bai kaiba,sannan ke kuma ………..hmmmm ban ma yi hakuriba ki shigo gida kisameni kawai idan banyi bacciba.
Kwafah taja babba saida sameerah taja da baya kafin ta bar wajen zuwa cikin gidan.
Yawwa shirin yayi aiki akan ta hankalina ya kwanta tunda yanzu baya ranta kaman yanda bata ransa itama yanzu,shikenan zan wataya saboda nasan nawane ni kad’ai. Fadin sameerah kenan acikin zuciyarta.

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤32❤

Tana shiga gidan yara suka fara kallonta har da manyan,ganin kayan dayake jikinta wanda basu saba ganinta dashiba,saboda lokacin data fita da safe basu tashiba bare suga fitarta.
Duk da yanda suka kewayeta amma bata kula kowanne daga cikinsu ba,domin abu ne mai wuyah mutum yaganta tana kula wani daga cikin yaran gidan.
D’aki ta shiga ta cire kayan kafin tah kwanta,ta dad’e tana tunanin yanda rayuwa take gara mata,amma kasancewarta mace mai nuna juriya yasa babu wanda yasan halin da take ciki.
Kiran sallah akeyi amma koh a jikinta ,gashi yanayin lokaci na magriba ba’a son kwanciyah,amma baga sameemah ba kam,wanda sallar ma batayiba bare kuma ta kiyaye lokacin kwanciyah.
Fiiiiiiifiiiii kake jin feduwa daga zaure,saida ta bayyano kafin ummah tata ta rike baki,itakuwa zata so taga ranar da surayyah zatayi hankali,da kuwa tafi kowa farinciki.
Duk da kallon da umma take yi mata bai sa taji wani koh dar a ranta ba saima kokarin zama da takeyi zata nada labarin abinda yah fafu a wajen aikinnata zuwan farko.
Dakatar da itah tayi kafin tace,
“Kai mai Sunan manyah,wane zama kuma zakiyi bare bada labari,bakyajin ana ta sallah a masallataine,ki tashi kije kiyi sallah ina yaso koma mainenee zanji daga baya”
Kobare fuskar tayi tana dadare da buga kafah a kasa,sai ka ce ba itah ce ta shiga har gidan wasu tah kamo mai laifiba dazu.
Da haka dai ta wuce badan taso ba ta tafi yin sallah.
Idarwar ta keda wuyah taji wayarta taNa kara,kaman mai kiran kuwa yasan sanda zata sallame sallah.
Duba screen din tayi inda sunan burgu ya bayyana a gaban wayar ,dauka tayi tareda murmushi saboda tuna alkhairi dayake mata a kwanakinnan ba dare ba rana.
“Aslm yar ummah ya kika shiga gida lafiyah”
“Lah lafiyah kalau karamin ogah,yah gajiyar aiki”
“Tabi jiki sosai,ki mikamin godiyh a wajen umma mana”
“Zataji sosai”
Da haka suka cigaba da hirarsu suna ta wasa da dariyah,har zuwa wani lokaci.
Tun kafin kowa yah tashi sameemah yau ma tabar gidan.
Saidai yau babu wani aiki sosai saboda jiyah kusan suka kammala ayyuka da yawa daga zuwansu.
Can wajen rana tana aiki a takardu aka cemata ana sallama da itah,bada izini tayi akan a shigo,bata daga kai tah kalli wanda suka shigo din ba har sai da sukayi gyaran muryah tukunna.
Baba umaru ne da Manu da kuma baba munkaila,dayake bayau ta fara rashin mutumci ba fuskewa tayi tana kara daure fuska tareda kishingida akan kujerarta tana juyawa.
“Uhm ina jinku mai yake tafe daku?”
Baba munkaila ne ya harzuka dayake dama yah fisu zuciyah,
“Ke seematu kinci gidanku,wajen ogah daya kama mana dan uwa mukazo bakeba sannan dan rashin tarbiyyah kina kallonmu ko gaisuwa babu ko,wai tukunna ma uban me kikeyi a cikin wajennan dakuma kayan ma’aikata”
Duk fadan da yake yi bata cemasa komai ba har yayi yah gama,
“Toh malam duk naji bayaninka ,shugaba da kake nema nice shugabar wajen,batun kuma kama dan uwanku da akayi tabbas anyi haka kuma bazan sake shi ba sai yayi kwana uku kaman kowanne masu laifi da muka kama jiyah,ina fatan ka gama jin amsar tambayoyinka,idan kuma basu gamsheka ba zaka iyah tambayar daya daga cikinma’aikatan,”
Tun kafin ta rufe bakinta kuwa saiga wata yah shigo,da sauri yah duka yah gaisheta tareda mika report zai fitah,Sunan sa ta kira tareda cewa,
“Am zo zaka dan yimin wani aiki mana,wannan zaka raka zuwa dakin da muka ajiye yan kamen jiyah”
“Okay ma’am,”
“Ku bishi ku kalleshi na baku wannan alfaramar”
Dan tsabar mamaki duk cikinsu babu wanda yayi magana,sai kawai tashi da sukayi domin bin wanda tace musun.
KO a jikinta kuwa tah cigaba da abinda takeyi ,kaman dama dai duniya bata san suba.
Bayan tafiyarsu da kusan minti talatin mutane da dama zunzo karbar yan uwansu,dan office dinnata yah cika har wasu suna tsaye,duk maganr da sukeyi bata ko dago kai bare basu amsa.
Su baba umarune suma suka dawo office din bayan sunje sunga baba shehu,wanda bayansa yayi burd’i burd’i da dukan bulala,bakincikine kwance a ransu,musamman ma Manu wanda shi ubansa ne,kuma sa’anni suke da sameemah din ,buga table din yayi har saida takardun wajen suka zube,
“Ke Wacce irin halitta ce wai,tum dazu muke magana amma koh amsa mana bakiyiba,wane irin laifi ubana yayi miki kika yimasa wannan hukuncin,kuma dan zabar ke baki imani kika yimasa dukan dayafi na kowa a wajen,magana nake yi nima amatsayin bansanki tunda naga dan kin sami matsayi tun ba’a je ko ina ba kin watsar da yan uwanki,sun zama sune abin farautarki,butulu kawai wanda bata san zafin iyaye da yan uwa ba”
Cikin zafin nama sameemah tah zabga masa mari dama a tsaye yake a bakin table din ta,wanda hakaan yasashi hadiye sauran maganar dayake shirin amayarwa,tashi tayi ta tsaya lokaci guda tah sauyah daga kamannin da take,nuna shi takeyi da yatsa kafin tace,
“Kai waye da har zakazo office dina kana fadamin magana,koh dan kaga kana dan uwana?,toh baka da wannan ikon kuma bazaka samu ba,a ganinka bansan mai nakeyi ba ne,har zaaka fadamin bansan zzafin iyaye ba kasan mai kai ubannaka yayi da kake jin zafinsa”
Rintse idonta tayi tareda kokarin control din jijiyoyin dasuke kwance akan goshinta,
“Ban so fada maka abinda yah faruba har da mutanen gidan ma banso su sani ba amma shiahhsiginka yasa saina fadamaka inayso duk abinda zaka ji ma kai yah shafa,………..a kwance na ganshi akan karuwa a dakinta suna aikata masha’a ,mai kake tunanin zanyi,dadi zanji kenan,iyah fadaamka danayi nasan zaka ji zafi,amma bazaikai nawa ba tunda kai kwantance zan yi maka amma ni zahiri nagani……”
Tun kafin ta gama fada baba munkaila ya daga mata hannu,dan shima ba kdan ba abin ya bugeshi sosai.
Jan Manu sukayi suka bar office din wanda yazama tamkar gunki,kallonta ta mayar kan sauran mutanen office din wanda yawancinsu daga wanda tazo karbar danta sai mai karbar mijinta ,wata yar ta wani kuma kanwarsa koh kuma yar yayanka da sauransu,
“Ku kuma mai kuke jira da bazaku bacemin daga ni ba,babu wanda zan saki saina ganan masa azaba kaman yanda yaganawa zukatan jininsa,da kuma masu sonsa,dan tsabar baku da hankali wai su bijiremuku su tafi shashahnci amma kuzo kuna yar karamar muryah a sakesu,yaushe duniya zata cigaba a samu raguwar yan banza idan har zuciyoyi bazasu tsaya su kawar da so su hukunta masoyinsu ba.
Ban yards da irin wannan son ba ni “
Da sauri kowa yah fita daga office din babu sauran magana tunda aka ga yamda tayiwa dan gidansu ma,wasu suna cewa ta kyauta wasu kuma suna cewa zaluncine,amma duk da haka babu mai magana wai an ce fadan dayafi karfinka saika mai da shi wasa.
Kaman yanda tayi alkawari kuwa saida baba shehu da sauran masu laifin suka cika kwana uku kafin ta sake su,office tace akawo mata baba shehu wanda har saida ya rame a iyah kwana ukun,rigar jikinsa duk tayi wani iri,kansa a sukunye aka shigo dashi saboda kunyar da yake ji.
Wasu kaya na maza yadi ta wullah masa tareda nuna masa bandakinta na office din,
“Ka Shiga nan ka yi wanka akwai ruwa sannan ka sanja kayan jikinka”
Ba uhm ba uhm uhm,sanna babu musu yah dauki kayan yah shiga bandakin.
Ya dan dsde da alamun gasa jikinsa kayeji kafin yah fito.
Abinci tah bashi mai rai da lafiyah yah ci yah koshi,tukunna tace,
“Ina fatan kaga yanda ta kasance koh?,idan har kuna cin kasa ku kiyayi tah shuri,yanzu ba da bane an sauya tsarin kungiyar nan,sauran ma nayi musu gargadi,idan har kuka kuskura nasake kama wani a wannaa wajen ba ma iyah nan ba,toh ba iyah bulala zanyiba,wallahi kawu shehu dandakeka zanyi yanda akeyiwa Akuyah,ai ka tara y’ay’a da sun isheka,toh idan baka kama kanka ba zaka mutu babu mazakutah,ni nan ni zan rabaka da itah,idan kaji kayiwa kanka,yanzu idan ka shirya muje na kaika gida,sai a gyara hali kuma”.
Shidai har ta gama abinda zatayi bai ce komai ba har ta fita a office din yabi bayanta shima.
Mota tashiga suka tafi,duk da lokacin tashi ba yyiba amma tabar aikin a wajen mataimakinta kawai.
Suna shiga gidan kowa kallo yah bisu dashi,shikuwa baba shehu kofarsu yazo zai shiga,inna larai ce tayi tsallae ta tare bakin kofar tana masa wani kallon nasan mai yake faruwa.
Bayyi mata magana ba sai tsayawa da yayi. Yana kallomta.
Sameemah ceh da haushi yakamata ganjn zasu fara fadannasu a gaban yara tace,
“Wai kekam inna larai meyasa kike hakane,ke har kina da karfin gwiwar dazaki yi wata magana akan laifin wani,hakan ma mijinki,nagan daman kin san yana aikatawa ba wai baki sanj ba,kawai yanzunne akka kamashi hannu dumu dumu,kaman yanda kema yasan halin dakike aikatawa.
KO kin manta lokacin da kike bin manyan anguwa akan zaki dawo dakinki lokacin da shima ya ganki da malam mai gani har hanji na anguwar kan tudu ya sakeki idan kuma…………”
“Ke kinga dakata haka yah isa haka naji ,banason wani tone tone,shegiyar yarinyah kai,sai kace kedin allah da annabi kike bi yanda yakamata,naji zan barshi ya shiga amma ba dai ya tabamin kayan amfani ba sai yah tsarkake tukunna”
Shidai wucewa yauyi ya barta a wajen tana ta sababi kaman aikota.
Can wajen isha ne bayan anyi magriba,baba umaru ya aika a kiramasa dukkan yan matan gidan.
Har bakin turakarsa suka je kowa ta samu wajen zama ta zauna.
Gyaran muryah ya fara tareda godiyah ga Allah tukunna.
Nasan kunyi Mamakin tara ku danayi ,badan komai bane saidan na gargadeku sannan na baku umarni,a gaskiyah na gaji da ganin masu hira a kofar gida,kaman ku su sameerah,sannan kuma da jawo magana wato irin su sameemah.
Saurayi zainab ya bada uzirin cewa bai gama giniba,ga kuma wani aiki daya samu yana bukatar zuwa service,dan haka ina mai baku umarni kowa a cikinku ta fitar da miji,dan duk tareda za’ayi auren babu wadda zata sake zama na gaji haka sai na jj da masu tasowa.
I’d an kuma baku fitarba toh in lokacin yayi koma waye zan aura ma yarinyah,zabi yarage gana ku.
Ku ta shi Ku tafi na sallame ku.

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤33❤

Kowa tashi yayi yah nufi harkar gabansa masu surutu sunayi,ita kuwa sameemah hakan bai dameta ba dan duk cikin zancensa babu wanda ta saka a mizanin gaskiyha bare har yah dameta,ai zancene ma ace wai itah ce zatayi aure.
Da haka zancen yah wuce kowa yah cigaba da abinda yake gabansa.
Harkar aikinta kuwa sai abinda ya cigaba,dan koh wata bata cikaba amma suanan ta ya zagaya inda mutum baya tsammani a fadin garin.
Da dare suna kwance dakin shiru kowa yana harkarsa sameemah kamma aiki takeyi a cikin system na wajen aikinta,sameerah ce tah shigo dauke da leda a hannunta sai wani daga kai takeyi,dagargajewa tayu a tsakar dakin tana fito da duk abinda yake cikin ledar.
Da biyu takeyin abinda take dan kawai su salma su gani,
“Kai koh a tarihi ban taba ganin yanda masoyi yake kulada masoyiyar sa kaman umaruje ba,gaskiyah na yarsa ba kyau ne da kwallaiyah yake sa mace tayi farin jini ba,idan itah mai sa’a ce shikenan,saboda bakin jini har ana binsa gida amma ba’a sameshi ba har yah tako har wajena yah zabi sarauniyarsa”
Haka tah cigaba da surutunta da zarar bunu, amma babu wanda yah tanka mata,dan gwara ma salma taja tsuka amma sameemah kam koh daga idonta daga kan system din batayi ba,
“Salma bisimillah ga kayan dadi,wanda ba’a ci a gida fah”
“Ke sameerah iskancin ya isheki haka kodan kinga mu zuba miki idone iye,ta bamaci a gidan kedin ci kikeyi,banza sabun shiga kawai a cikin hakrkar”
Dari yah sameerah ta sheke da itah dan dama so take wani yah tanka mata a cikinsu,
“Sabun shigar shiyasa naga daga shigata da kamo babban kifi dan gidan manya saboda na cika mace”
“Wacce macen kika cika,koh kinace babu wanda yasan asirin da kukayi masa ne keda uwarki,kuka karkatar da hankalinsa daga kan sameemah zuwa naki,ai kowa ma yaga kallon dayake miki yasan ba a hankalinsa yake ba,idan har kina ji da ke macece ai saiki kallameshi tah kissa ba ta asiri ba”
Bakin cikine yah kama sameerah jin abinda salma take fada mata,bata san lokacin da ta kaimata raruma suka fara fada ba,cikin kankanin lokaci duk suka tumurmjshe naman kajin a da lemon a kasa.
Feduwar da sameemah tayi ne yasa su tsaywa sai a sannan suka ga irin ta’adin da sukayi da abincin.
Karnukan ne suka shigo da gudu,dan yanzu harda wani karami ma a cikinsu wanda sameemah tah samoshi a hanya yana halin jinyah,yanzu watansa daya kenan har koma kaman ba shi ba.
Dan dama itah haka halinta yake,yawancin abubuwan da suke karkashinta taimakone yake hadata dasu,shiyasa koda kudi babu wanda yah isa ya sayi yardarta a wake abinda yake nata.
Hannu tah mika tareda nuna musu naman dakaye kasa a babbaje. Sukuwa dama jira sukeyi kare da nama,ai babu batun jira.
Sororo sameerah ta tsayah tana kallon sameemah wanda tah bawa karnukanta naman da saida tah hada da bada jikinta kafin ta samu duk dan tazo tayi burga a gabansu,dan kallon yamda yake mata mutane suke gani,amma har yanzu bata wani mallkaki zuciyarsa yanda take so Ba,kawai idan tayi magana ne yaka aiwatarwa amma dan shi a karan kansa baya yi mata abu dan racayinsa kawai,
“Me kika aikata haka sameemah, nama nawa dana shigo dashi kika bawa karnukanki suke cinyewa”
“Yanzu yah tashi daga naki ai,tunda kin gama dashi ta hanyar zubar dashi a kasa,kinga yah zama na karnuka tunda dama abincin kasa su ake bawa,dan karna wahalar dake ne kawai na basu,menene lafina a ciki Toh?”
Har ta bude baki zatayi magana sameemah tasaka hannunta a baki shshshs da alamar tayu mata shiru .
“Banason dog on surutu aiki nakeyi,kuma nariga na fadamiki dalili,idan har kika sake cewa takk kuma a kan maganar toh umarni zan basu suna gamawa da naman su koma kan naki naman,in kuma kin musa ki gwada”
Ga kwadayi yana cin sameerah ga kuma haushin yanda ta samu naman amma bata ciba,ga kuma takaicin bata da ikon yin komai akan abinda sameemah tayi mata,,dan haka hadiye wani yawu kawai tayi tah fice a dakin,duk da tana ganin salma tana mata dariyar mugunta amma bata,kulata ba.
Dakin inna ramatu ta shiga ta sameta tana ta nade kayan wanki akan gado,daga ido tayi ta kalli sameerah din wanda sai kumbura takeyi dan bakin ciki,
“Ke kuma miye kika tsaya min a kai kaman kububuwa”
“Ummah da na fasa amma yamzu ina so a zartar da aikin kawai,sona ke yanzu duk wani aiki da zai rikitah kwalwalwar sameemah tah haukace to ayi mata,umma idan da dama ma tah daina yin komai a rayuwarta tazama tamkar mutun mutumi”
“Hmm kindawo hankalinki kenan,lokacin danake nuna miki gabar ai yamma kike dosa,dama na fada muku matukar tana numfashi sannan babu wani abu na dauri da akayi mata toh babu wanda zai yi rayuwar farin ciki kaff a cikin gidannan”
“Ummah harda salma ma inaso ayi mata wani abu”
“Keee rabani da taba salma uwarta maba a zaune takeba,sannan itah ba itah ce mataalarki ba a halin yanzu,su kansu mutanen gidan indai akan sameemah ne toh suna cikin tashin hankali idam asirin kanta yah karye,ke kina tunanin iyah ni kadaice kawai mai hannu a cikin aikin? Hmm akwai abinda yafaru wanda iyah mu muka sani kawai,yamzudai a bar wannan zancen tunda kince kin amince shikenan dama tun farko kece kika yimin gardama.
Boka yace baya bukatar kudinmu shidai burinsa kawai ki kwana a wajen sa toh duk wani abu da muke bukata zai tabbata,kinga koma menene sai ki tambayeshi kawai,saidai daga yanzu ki daina tuntubarta da fada,saboda kar ta gano mai yake faruwa”
“Toh shikenan ai gobe ma zan tafi,sai kicewa baba umaru na tafi kauyen kawunki saboda kinsan bayason fitarmu kwana a wani wajen,ai yamzu na tsani sameemah dinnan,dan idan muna zaune da umaruje har kirana yake da sunan fah”
“Yanzudai mungama magana ,kuma sannan ki fada masa yah turo a da maga ba tansa idan kuna hira,saboda da wurwuri ake dukan karfe kafin yayi sanyi”
Yau da safe kasancewar weekend ne babu zuwa wajen aiki,kowa yana gidansu,sallama akayiwa sameemah ana nemanta a waje,sai kace na miji babu alamar wani tambayar wani kafin ta fitah haka ta yafa gyalen abayar da take jikinta ta fita zuwa ganin mai sallamar.
Mamaki tayi da taga burgune da surayyah a bayan mashin dinsa suna kallnta fuskarsu dauke da murmushi,itama karisawa tayi kusansu saidai sabaninsu itah fuskarta babu alamar nuna wani reaction a ciki,
“Menene yah faru na ganku da ranar nana haka?”
“Shugaba alkhairi ne amma ga surayyah nan zaku shiga ciki tayi miki bayani,nizan je wani wajene idan na dawo zan maida ta gidan”
Kallon surayyah tayi tareda cewa,
“Ke Har yanzu kina yawon banzar koh baki dainaba,ba na gargadeki da bawa kowa lokacinki a araha ba,koh baki karanta takardar agreement din mu ba”
“Ahah shugaba wallahi na karanta,kuma ba na bin kowa yawo yanzu,kawai wannan din wanj abune daban kuma zanyi miki bayani”
Daga kai tayi kawai alamar taji kafin ta maida hankalinta kan burgu,
“Kai kumaa dama dazu nake shirin kiranka akN batun taron daza’ayi na senatoci ran Monday,ku tabbatar kun shiryah wajen kulada zirga zirgar mutane da cike hanya saboda kae a samu matsala”
“Shikenan zan samesu muyi maganar”
Sauka surayyah tayi daga kan mashin din tana kallon sameemah da idanuwanta so innocent kaman ba itah bace mai filllah rashin mutunci,itama sameemah kallonta tayi sau daya tareda zuyawa cikin gidan.
Ganin ta tafine yasa surayyah sake kallon burgu da alamar tambayar tabi ta kuma ta tsayah,
“Ki bi bayanta kawai kinga tayi mikk nisa,tunda Kika ga tayi haka tana nufin ki bi bayanta ne,saboda kimsan ba magana zatayimiki ba kaman sauran mutane”
Dahaka surayyah da dan gudu gudu saboda tayi mata dan nisa,tana yiwa kuma burgu bye bye wanda yah tada mashin din yana shirin barin wajen.
Tun daga shigarsu take ta kalle kallen cikin gidan,wanda yakeda kofofi da yawa a ciki,tana jin labarinsa amma wannan shine zuwanta na farko.
Wata kofah taga sun nufah sai gasu a dakin su sameemah,a bakin gado tah zauna yayinda sameemah ita,kuma tah fita waje sai gata da pure water a plate.
Ajiyewa tayi a gaban surayyah wanda ta hade jikinta waje dayah tana ta kalle kallen wajen ,
“Ke Kallon mai kike ne tunda zu,kincemin akwai abinda zaki fadamin kuma naga kinzo kinyi shiru baki ce komaiba”
“Ah Toh dama shugaba,ko na ce anty sameemah dama nida Ahmad(burgune )muke soyayya toh shine bamusan yanda abin zai faruba,sai muka yanke shawarar fadamiki tukunna duk yanda kika yanke akai”
“Nikuma nice mai yamke wa abinda yake cikin rayuwarku,ni babu ruwana da hakan saboda babu wanda nakeyiwa dole a cikin tsarina bare kuma saka shi dole sai yabi tsarina,saidia idan har ya yarda da cewa zai zauna dani toh wannan kuma daban”
“Eh dama ba haka bane anty sameemah,nice ma nace dole sai mun fadamiki,saboda iyayena sun amince da zamana a wajenki,duk da sunsan ba abune mai kyau ba nake niyyar yi amma kuma sun yarda dake ba niba,sannan tunda dukkanmu nidashi a karkashinki muke inaga ke yakamata ki shige mana gaba wajen hada kan iyayenmu da yimusu bayani,dan allah karkice a’a,ke kadai nake ganin zan samu goyon baya,wani abin a rayuwata rashin yar uwa mace da kuma rashin samun abokiyah ta gari mai hankali shiya fara saka raywata cikin hakan,saidai a yanzu ni ba ganinki na ke a iyah shugabata ba harda ma yar uwata,dan allah inaso ki daukeni a matsayin hakan”
Numfasawa sameemah tayi kafin tace,
“Shikenan inshaallah zanyi kokarin hakan tunda kin saka yardar ki a gareni”
“yawwa nagode anty sameemah Allah ya biyaki”
Daga haka suka bar zancen akan zata yi musu nata kokarin amma suma su sanar da iyayenna su akwai meeting dazasuyi da itah.
Dadine yakama surayyah har bata saN lokacin da ta rungume sameemah dan farinciki.
Tad’i suka dan fara yi bayan wannan zancen wanda kusam rabin maganar surayyah ce takeyi,dan itah bata iyha a zauna ana tadi ba irin na mata.
Sai wajen la’asar kafin burgu yazo yah dauketa suka tafi,wanda duk zamanta a dakim su salma basu kulata ba itama kuwa da ba baya bace a rashin mutunci sai abin yatafi a balance dan itahma kaman bata samu mutane a dakinba haka tayi.
Tun yinin ranar sameemah takejin faduwar gaba ga kuma wani nauyi da kirjinta yake yi mata wamda bata san daliliba,ta dawo daga raka surayyah zata shiga daki taji kamar alamar ana kiranta da karfi,bata wani bada reaction akan hakan ba duk da cewa zuwa sannan tah tabbbatar wani ne yake turomata wani abun,kasancewar ba wannan ne farko ba da ake mata,kuma tanada masaniyah akai.

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤34❤

“Haba manjo ka gyara hannun mana na gyara maka rigar,wallahi hadda ragwancinka ma yamzu kam tunda ciwon ya warke ai sai ka barni na ji da y’ay’anka ma”
“Wai ni kulu meyasa kika sanjane kullum cikin fada,nikam bana cemiki bazna kara shaye shaye ba,zan nemi sana’a na dungayi”
“Yah rage naka kuma,in kanaso ma ka cigaba”
Shiru yayi yana jinta shidai bukatarsa ta zubo masa wainar da takeyi ta rana yah ci tukunna komai ma sai ayi.
Hakan kuwa akayi tana zubowa yah yagyara hannun yanan dandanar miyar ganyen masar yana antayawa a bakinsa,koh maganarsa ba kaji,
“Hmm Gaskiyah nayi sa’a dana sameki dan naji ance sule har yanzu baya tashi.

~~~wani bakin tsuntsune yake ta bita mai kama da hankaka a wani waje mai surkukiyar gaske,dubawa tayi taga babu komai a jikinta sai wani farin yadi an yane jikinta daahi.
Ganin babu mafita ne yasata furmawa da gudu shikuwa ya bita a baya yana wata irin kara mai ratsa cikin kunnuwa.
Sun dad’e suna gudu har suka iso wani waje da hanyar bazata bulle ba sai wata babbar katanga wanda iyah ganin mutum baya iyah ganin keshenta.


A can kuwa cikin sukukiyar daji da kuma tsohon dare,mutane biyu ne a zaune wanda saboda maita da kuma san abin duniyah basa da niyyar kwanciyha bacci irin na kowane san adam.
Sameerah ce ta kalli bokan da yake mata aiki tace,
“Toh yanzu kana ganin aikin zai yiwu kuwa?”
“Eh zai yiwu mana,yanzu haka tana can tana mafarki saboda munyi nasarar kama kuruwarta tun dazu,yamzu wancan tsuntsun da kike gani wanda muka tsireci da allurah uku bayan mun saka masa gashinta a cikin bakins kafin mu kasheshi,toh ruhinsa zai bayyana a cikin mafarkinta duk inda kuma yah ji mata ciwo toh bazai warkeba saidai ciwon ya cigaba da yaduwa irin na uwartah”
Leka kwaryar da take gaban bokan sameerah tayi dan ganin menene a ciki,idonta ne yayi tozali da video abinda yake afkuwa a cikin mafarkin sameemah,dadai inda bokan yasaka wani abu mai kaman katanga a gabanta saboda hana ta damar wucewa.
~~~,duk da gudun da tayi amma babu alamar gajiyah ko haki a cikin jikinta,saidai rashin ganin hanyar dazata cigaba da gudun yasa ta juyah tana kallon bakin tsunstun dayake nufowa wajen ta cikin saurin gudu da yafi na karfin tsuntsaye a gaske,saisa yazo daff da itah kafin tah mika hannunta tareda cewa,
“Tsaya Haka angama wasan. Yakai wannan BAKIN RUHI,(littafin marubuciyah oum hairan). Kayi kuskuren biyonin har wannan wajen,daga inda kake in jiyowa wani bangare na jikina a tareda kai,dan haka in umarninka daka tsaya a inda kake,idan kuma kayi gangancin matsowa toh mutuwar ma sai ta fimaka sauki”
Cak ya tsaya a wajen yana daddaga fuka fukansa kaamn yaga uban gidansa, masawa tayi inda yake tareda cewa,
“Yaron kirki ace dai kana jin magana”
Daga idonta tayi wanda yayi za kaman jini tana kallon sama,dadai wajen da su sameerah suke kallonta,gashin kanta ma yana dagawa a iska tamkar fatalwar data fito daga sabon kabari.
“Kinyi kuskure daga ke harshi din,a tunaninku bansan duk abinda kukeyimin bane?,nasani dukka kuma ba barku zanyiba ku tafi a banza,tunda yanzu har kun fara yin bakin asiri da kuma ruhin ba bayyi muku komai ba,duk da nakan dauki ruhi amma bana taba ruhin da baida laifi koda kuwa naso hakan,amma ku kunsaka kanku ciki saboda ku azzalumaine masu cutar wa.
Hhhhhhahhha kana nan yan iska kuna tunanin zaku iyah yimim wani abu a duniyar mafarkine wanda take itama duniyata ce?,kai daga nan inaso ka kayanka hannunka har sai jininka ya gama zubewa,ke kuma bazan yimiki komaiba kinci albarkacin yan uwantaka amma zaki karbi naki hukuncin koh ba yau ba kuwa,idan na barki da halin da kike shirin shiga ma ya isheki,sannan idan kin dawo ki gargadi uwarki abinda na fada miki
cewa karta kuskura ta sake shiga gonata,idan kuma wani ya ji a binda yafaru anan wajen toh sunanki matacciyah”.


Abin bai kara bawa sameerah mamakiba saida taga yanda bokan yah dauki wuka ya yanka wuyahsa da itah,sannan jinin yana tafiyah direct zuwa cikin kwaryar wajen da sameemah take.
Ko motsi kasawa tayi har jinin bokan yah kare yah fadi a wajen,itah kuma kwaryar ta fashe,wani dogon numfashi sameerah taja kafin tah tashi ta furma da gudu zuwa cikin gari a kafarta duk da tsohon daren.
Tashi tayi daga baccin duk da har sannan gari bai wayeba dan koh assalatu ba ayiba,hankalinta kwance ta tashi ta debo ruwa ta sha kafin koma ta kwanta,saidai babu alamar bacci a idonta dan haka kallon rufin dakin kawai takeyi,idan ta tuna wanj abu sai tayi Murmushi wani kuma tah jijjiga kai.
Tana bude idonta sukayi tozali da sameerah wanda ta dawo da asuba tah zo daukar wani abu dakin,dan tunda ta dawo ba yanda ba’ayi da itha na amma daga ta doso dakinnan su sai jikinta yafara karkarwa saboda tsabar tsoro,sannan an tambayeta mai yah faru tace kuma babu komai,sai aka barshi da inaga gamo tayi a hanyarta ta dawowa,itama da taji mai suka ce sai ta amsa musu da cewar hakanne.
Toh yanzun ganin rana ta farayi amma sameemah bata fitoba ne yasakata shiga dakin da sanda domin daukar kayanata dan wancan din duk sun yage a hanyar dawowa daga jejin cikin hali na fitar hankali.
Saidai kashh rashin sa’a,tana shigowa itakuma sameemah tana tashi,karkarwa kafafunta suka farayi har sun gaza daukarta gabadayah,bajewa tayi a tsakar dakim har sannan idonta bai bar kan sameemah bah.
“Ke miye kike min kallo kaman kinga aljani”
“Bbbbbba bbbbbbu shhshshugabata dama kaya nazo dauka kuma banaso na tashaki a bacci,kiyafeni dan girman allah kiyimin rai”
“Hmm banace miki kar naji ba maganar nan a bakin kowa ba,toh ciki harda bakinki,gobema ki sake gigin yin shashancinki akai,dalla jita kaman kinsan allah ke,da kike hadani dashi nayimiki rai”
“Ahah na tuba kiyimin rai,in da san samu ma ki daukeni aiki a karkashinki koh kuma ki hadani da mai miki wannan aikin nasan tabbas babane a harkar”
Wata harara sameemah ta watsa mata kaman idonta zai fita tace,
“Lallai dan adam kayan allah ,wato baki daddara ba koh?,toh wallahi idan kika sakemkn wannan zancen koh kika fadawa wani toh zanjiji sarai,kuma hukuncin bazai miki dadi ba kkh kadan”
Tun kafin tabari ta karisa sameerah ta yunkura da sauri tah fice a dakin har sannan jikinta rawa yakeyi kaman tasha tsimin yan farautan.
Saboda maganar da sukeyi da sameerah har sameemah tah manta davzuwa gidan su surayyah da zasuyi itah da kawun burgun saboda tambayo masa izini,daga wayar tayi domin kiran burgu dan taji koh kawunnnasa yah shiryah dan itah bata son zuwan daren ta fiso ta gama da wannan babin kawai.
Tashi tayi tah fara shiryawa jin zuwannasu yana nan ba’a canja ba.
Dayake Surayyah ta sanar da zuwan su sai aka fara shirin taryarsu tunda wuri,dan haka lokacin da suka shigo kowa yana gidan harda babanta shima yau bai je aiki ba.
Toh wata sabon gani surayyah ta fada a ranta ganin yanda sameemah tasha wani uban hijabi mai alkyabba kaman ba itah ba saboda koh a tairihi babu wanda yah taba ganin tasaka,”gaskiyah koba komai na samu matsayi a ran shugabrtawa alalmu ya nuna ta karbi tayin zamana kanwa a wajenta”
Har suka wuce falon baki inda akayimusu shiri bakin Surayyah bai rufuba dan farincikin ganin su sameemah,koh yaushe suka hada ido sai tayiwa sameemah Murmushi itakuwa koh sau daya bata sau fuska ba bare kuma tayi mata magana,hakan bai damu surayyah ba koh kadan saboda tasan haka take,kuma itah haka kawai sameemah take burgers Kodak bata yimata komaiba.
Maganar abinda yah tarasu suka farayi bayan kowa yah kammala abinda zaiyi.
Babantane yafara magana bayan yah bude taro da addu’a.
“Toh da farko tun banji abinda yah taraku anan wajen ba hankalina a kwance yake,don yanayin da kukazo da kuma yamda kuka sananr damu zuwanku akan wata muhimmiyar magana nasan abin alkhairi ne,dan haka zamuso muji abinda yake tafe daku”
Alhaji isah yayan mahaifin burgu shiya fara jawabi kafin yah fara magana da jawabi duk da bai fito fili ya fadi abinda yake ransaba.
Haushine yakama sameemah ganin yanda suke tah jan magana guda daya ana ta bata lokaci ,dan dama tun sanda shigo bata ce komaiba,katsewa kawun burgun tayi tareda numfasawa tana kallon agogonta tukun kafin tafara cewa,
“A takaice dai a daina wani bata lokaci,ni sunana sameemah nasan kunsan sunan koda fuskata zatayi muku wuyahr sani,sannan kuma nice shugabar kungiyar da yaranku suke ciki kafin yanzu kuma suna karakshi kuwata ta kungiyar vigilantee,kuma dukkanku saida kuka amince kafin na fara aiki dasu,wanda hakan ya nuna kun yarda dani a kusa da yaranku.
Sun zo sun sameni akan nayi magana da ku amatsayin iyayensu saboda su basuda karfin gwiwar tunkararku saboda abubuwan da suka faru,abayah.
Sun ce su na son junansu kuma kuma burunsu shine hakan yakaisu ga aure,shin kun amince???.
Shiru wajen yayi kowa yana nazari,ganin hakanne yasa sameemah cigaba da cewa,
“Ni nazo a matsayi guda hudune,na farko amatsayin shugabrsu na biyu a matsayin yar aikar sako,na uku a matsayin abokiyar Ahamd(burgu)na hudu kuma a matsayin yaya ga Surayyah kuma yar uwa,wanda jiyah ta rokeni akan na zamo tamkar yaya a gareta kuma na amince,dan haka ni na amince da kasancewarsu tare saboda hakan abune mai kyau wanda ake fatan yah dore”
Kowa ma dayaji abinda sameemah ta fada kuma sun san dagaske takeyi sai kawai suka amince har aka fara shirye shiyen yanda abin zai kasance,daga haka taro yah kare kowa yah tafi nasa harkar.
Dadai lokacin da sameemah tazo fita daga zauren gidan taji an rungumeta ta baya,ko bata fada ba tasan mai aikata hakan,muryar surayyah tah tsinkayo tana cewa,
“Nagode sosai da kokarin da kikayimana anty sameemah,ina lekawa duk naji abinda kika fada,hakika ko kowa bazai alfahari dake ba ni ina alfahari dake antyna.
Har cikin ranta sameemah tah ji dadin abinda surayyah ta fada,amma a fuskarta iyah karamin Murmushi tayi tareda cewa “nagode”atakaice kafin ta fice.

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤35❤

Wata biyu aka saka biki surayyah da burgu,babu a binda suke sai murna da hakan saboda ganin burinsu zai cika,dan yanzu ko a wajen aikima soyayyar su suke sha,dan ma sameemah tana taka musu burki ganin abinnasu yana nema yah wuce gona da iyahka.
Kwanaki haka ma watanni sun shiga,yanzu sameemah tana neman shekara guda akan kujerarta,inda yazamo cewa burunta na yin suna a garin yah fara cika saboda duk inda ka shiga babu abinda ake labari sai gwarzuwar macen da tayiwa maza zarrah barekuma mata,ta kawo cigaba da kuma gyara da dama,amma idan muguntar tazo ma ana tabata kuwa.
Maganar da baba umaru yayi musu na aure tana cigaba da matsowa,saidai koh kadan hakan bai damu sameemah ba dan tasan zancen bai shafeta ba ta kowacce siga.
Su kuwa wanda zancen yah shafesu wato su inna ramatu ana ta shirin hidimar biki,dan saurayin zainab yah turo akan yah shiryah shima yanzu.
Wata motace a tsaye a bayan gidan su sameemah tah faka a cikin duhu dan kar a gane me suke a wajen,salma ce cikin yatsina fuska tace
,”alhaji yakamata idan sona kake toh ka fito,dan nima tunda naga sa’annina a gida zasuyi aure gaskiya nima auren zanyi,idan kuma kaga bazaka aureni ba toh gaskiyah karka sake zuwa kofar gidannan”
“Haba salma baby meyasa kike haka,yanshe zan bari ki subucemin yanda na sameki dinnan,dudu watam mu biyu amma kin sace zuciyata,ai irinku mutum yasaka a cikin gida yah boye hankalinsa kwance yana sakawa a gaban motah”
Murmushin jin dadi salma tayi jin yadda alhajinnata yana gwadata da kuma yaba kyanta,
“Toh shikenan alhaji,nima kaine a raina ai idan har kaga kana ciki toh ka turo gidanmu,idan kuma ba haak ba na bawa wasu dama”
“Ahah baza’ayi hakaba indai aurene ai abune mai sauki”
Da haka kuma bayan zancen auren suka fara tabe taben su har wajen karfe dayan dare kafin tah fito ta shige gidannasu .
Kulu ce tah kalli manjo wanda zamansa a gida baya zuwa wajen shaye shayen har yayi dan hankali saboda bata gara masa badaidai ba din,
“Yanzu manjo kai baka ga hakan yafi maka ba,ji na lokaci daya har ka dan sanja abinka”
Kara gyagygyara kayan yakeyi yana jijjiga kai shi a dole yayi abinda aka yabeshi,
“Ai nake fadamiki yanzu haka idan na fita neman aiki zanje saboda nima a dunga ganina da kamala,ko yah kikace”
“Eh hakan yayi,toh ni ai gwanda da akyi maka dukan gashi ai ka nutsu kana shirin bin hanya”
Harararta yayi yana cewa,
“Kefah dadina dake kenan ba’a abin arziki dake,toh in fadamiki makasudin kara shiriyahta saboda taron da za’a yi a gidannan ne,dan naji labarin duk yan matan gidan aurensu za’a yi lokaci daya,kinga idan mazajen suka ganni a haka,kuma aka nuna ni akace nine yayansu na karamin kyauta zasuyimin ba koh?”
Dariyha kulu ta kece da itah tareda cewa,
“Lallai manjo har yanzu da saura,kaidin yanzu jira kake ajo auren kannenka mazajensu su tara maka dukiyah ?”
Kai mata duka yayi tah shige daki,sai kimbura fuska yakeyi ganin yanda take masa dariyah dan yayi mata tadi zasu samu abin alkhairi.
Dukka yan matan kowa hidimar aurenta takeyi banda sameemah wanda hankalinta gabadaya akan aikimta yake,tah wani wajen ma dadi takeji zasu tafi subar gidan ta maida dakin iyah itah kadai kawai.
Yanzu sameerah duk wani abu da zai shiga tsakaninta da sameemah gudunsa takeyi tumda ta gano sameemah tafi karfinta,saidai mai hali baya fasawa ,bayan mutuwar tsohon bokanta yamzu ta samu wani,wanda yafi na da yimata aiki,saidai koda wasa bata yarda wani tayi maganar sameemah a wajensa balle kuma yimata asiri.
Ummaruje zaune a falon mahaifiyar tasa bayan isha,shiru yayi baiyyi magana ba ita ma kuma hankalinta bai kai Kansba dan ko dauke kanta batayi daga kan shirin da akeyi a gidan television na bolly wood,ganin bazata kula da sunkuyar da kan dayake yi bane yasashi cewa,
“Ummah! Ummah ummah!”
Saida yakirata wajen sau uku kafin tah juyo ta kalleshi,
Na’am son me ake ciki?”
“Dama Idan abba yana nan inaso zamuyi magana ne daku”
“Ahh wannan ba matsala bace bari na kirashi sai yah shigo”.
Suna zaune kuwa sai gashi ya shigo, shima zama yayi akan kujerar tareda daukar wani apple akan pilate yana ci.
“U hmm mahaifiyar ka tace kanason magana damu,ina jinka”
“Eh ……eh damaaaa abbba akwai wacce nakesone a gidan gandu shine nakeson aje nema min ,dan tah cema na turo,gashi babansu yace zuwa nan da karshen shekarar nan kowa a cikinsu tah fito da miji”
“Toh naji dadi da ka fadi haka kuma munyi farin ciki,dan dama shi namiji cikar mutuncinsa shine aure,toh amma yar ina ce waye babanta”
“Eh a Gidan Gandu take sunan babanta umaru,yayar sameemah ce ma”
Hajiyah mairo ce tayi saurin cewa,
“Ayyah Kaga nifi na allah,ni da da farko ma nayi zaton da sameemah za’ayi ashe kuma da yayrta ne ashe,toh allah yasanya alkhairi inshaallah za’a bincika sai ajen tambayowa”
Duk maganar da akeyi alhaji bala bai ce komai ba sai wani shiru da yayi kaman wanda ya tafi wani nazari,maganar da ummaruje yasake yi ne ya dawo dashi daga tunanin daya tafi.
“Amma ummah bazawara ce dan ta taba aure,amma koh shekara batayiba ta fito,dan ko da bata dashi”
“Toh gaskiya my son bazaka auri bazawara ba ban aminceba sai ka nemo budurwa,ga mata nan birjik a gari……”
“Meyasa kake haka alhaji,wannan wane irin zamcene haka,bawani dan zancen bazawara tunda aka fadi yar wacece ka wani hade rai baka ce komaiba,kuma naga annabi ma yana saurayin yah auri bazawarar,ai abin farin cikine dan ka zai dabbaka sunna,ni dai bazan hanashiba duk da banso ba amma tunda yana son shikenan bazan haanshi ba,saidai kuma idan akwai abinda kake boyewa?”
“Ahh ha m………….ahahha babu abinda nake boyewa mai zan boye,shikenan za’a san yamda za’a yi kaje allah yabada sa’a”
Shidai mamakin ubannasa yayi ganin yanda yake wata rawar muryah ta rashin gaskiya.
Manjone a zaune a unguwar su kulu dayake nanne inda yah samu sana’ar had’a bulo,sumyi dan hutune dan kowa yaci abinci yah koma aiki.
Wata kanwar kulu ce take ta fad’a da wata sai zage zage sukeyi an rabasu sunki su daina.
Budar bakin wani a wajen sai cewa yayi,
“Hmm ai wanna yarinyar bata da mutunci,dukkansu yaran gidan haka suke,naga kana ganin itah kanta yayarta wacce tayi aure a gidan gandu,duk da aurenta amma duk sanda tazo gidansu raba dare zasuyi suna hira da tsohon saurayinta har sai sukai dayan dare a wajennan,gashi babu dama a fada sai uwarta tace karya ne”
Wanine shima yah cafke tareda cewa,
“Toh laifinta zaka gani,naga shima mijin shashashane,inba marar hankaliba ka tafi rani har kayi kusan shekara biyu babu labarinka,idan ma ba irin su kulun ba wace matarce zata yadda,ni banga laifinta ba sai nasa laifin gaskiya,ai aure ba hauka bane koh”
Duk maganar da akeyi a kunnen manjo wanda yayi mutuwar tsaye,banda juyawa babu abinda kansa yakeyi,dan jinsa yakeyi kaman a wata duniya yake.
Tun kafim wani yah ganshi ya dauki rigarsa daya cire yah bar wajen siyarda abincin tun kafin wani ma ya ganshi.
Shirye shiye ake tayi dan yau masu kawowa kayan auren su sameerah zasu zo itah da zainab,sai wani rankwada kai sukeyi,za’ayi aure watan gobe.
Dare yafayi dan wasu kanma sun kwanta,alhaji balane ya shigo dakin hajiyah mairo wanda har tasaka kayan bacci,
“Alhaji lafiyah na ganka da darennan babu alamar kwanciyah allah yasa dai lafiyah”
“Eh lafiyar ce tah kawo haka,dama inaso muyi magana da kene saboda in fitah hakkinki”
“Toh wace maganace haka inajinka”
“Dama inasone na kara aure,kuma badan kin gazamin ba kawai ra’ayin hakkanne ya taso”
“Aure! Aure!! Fah kace alhaji?,wacce shigiyar ce zaka auromin ka kawomim cikin gida yau shekarar mu talatin da takwas da aure?”
“Haba hajiyah ki kwantar da hankalin mana,yarinyace ba lallai tah baki matsala ba dan koh kanwar ummaruje bata kaiba”
“Kutumar ubancan,alhaji mai kake nufi,dan kaga kwaanannan nayi sanyi shine har ka samu kwarin gwiwar fadamin wannan maganar?,kuma ma dankayi mungun rainamin hankali hadda wani cemin yar yarinyace,wato ni na gama zama dakai da haifamaka yara,ka gama ragwargwajeni bari ka auro sabuwa dall ku more nikuma na zauna na zuba muku ido koh?”
Hmm …..alhaji dani kake zancen kawai,kuma banson sake jin wata magana daga bakinka ka fice kabarmin dakina tun kafin raina yafi haka baci,hawan jinina ya hau ka kasheni da dalili kayi auren ka hankalin ka kwance”
“Aurene kuma kayi mugani,amma daga kai har amarayar zaku san kun tabo hajiyha mairo hmmmmmm”.
Alhaji bala yana ficewa ta daga wayah ta fara dannawa babu ruwanta da yanayin daren da gari yah fara.
“Hello hajiyah Lailah kina jina”
“Eh ina jinki hajiyah mairo,amma lafiyah kika kirani da tsohon darennan ?dan ma nayi sa’a mai gidan baya nan yana dakin shegiyar”
“Hmm kedai bari kawai,dama kina fadamin halin maza nake cemiki alhaji bala dabanne,toh yanzu kam na gano halimsu duk dayane tamkar an cakudasu an raba su”
“Wai meyah farune hajiyah mairo ki kaini ganuwa mana”
“Alhaji ne fah wai zai kara aure nan da wata daya,ke inda irin nakine ma da sauki a auro maka wanda bata wuce sa’arka ba ta yanda babu abinda zata nuna maka,amma bakin cikin shine budurwa zai auromin mai jini a jika koh yusrah bata kai na a haife,ina so ki fadamin abinda za’ayi dan bazan zauna haka ba kam”
Ashar hajiyha lailah ta durah kafin tace,
“Ai bazai yiyuba kam dolene ayi wani abun,kinga irinta koh dama ina fadamiki ai kike wani yabashi gashinana ya zefar miki zani a kasuwa”
D’urum manjo yah buga kofar dakinsu shida kulu yah shiga ,kallonsa takeyi tareda tambayar lafiyah,bai cemata komai ba sai maida kofar dayayi yah rude idonsa yayi jawur da shi dan bakin ciki.
Zare wani tsohon belt a kungunsa yafarayi,yana wani kakkadashi tareda nufar gunda kulu take tsaye a dakin.

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤36❤

Matsawa takeyi da baya yana nufarta,bata amkara ba sai jin duka taji a jikinta zuwattt,ihu ta saka tana soshe soshe,tareda da dadare,
“Dan ubanki saboda kin maidani mutum mutumi wawa soko,shine wato inacan na tafi rani kike zagewa wajen kwartonki koh,toh yau allah ya toni asirinki naji komai,kuma mai rabani dake sai Allah”
Kulu tanajin abinda yafada tah daina ihun tareda tike belt din dayake dukan ta dashi da hannunta,
“Ohh dama akan hakane kake dukana,toh bari kaji na fadamaka dama tun ranar dana gane cewa wani yasam abinda yah faru na shiryah wa zuwan hakan,wato sameemah ceh tah fada maka koh,dama nasan sai ta fada ai kuma ……”
“Dallah rufemin baki munafuka,toh ba sameemah bace ta fadamin a unguwarku naji wasu suna fada,ai dama abin duniya baya buya indai anyishi”
“Eh nasan na aikata amma sau dayah nayi kuma daga lokacin ban sake ba,shima kansa na yi masa gargadin kar ya sake kirana tun rananr,kuma koma mai yah faru ai lefinka ne,naga tun ina da cikin mai sunan baba ka tafi ka barni,bakasan halinda nake cikiba har na haifeshi na yayeshi yayi wayo baka nan,sannan daka dawo babu abinda ka bani bakasan mai muka ci ba bare kuma muka saka,komai ma a lokacin ne yah faru,ai nayi kokarima da ban tafi gidanmi na,shidinma jugani yayi akan bazaka dawoba,na kashe aurena na aureshi,nayi nadama nace yadaina kulani”
Zuwa yanzu kuka takeyi amma bana dukan da manjo yayi mata ba,na halin dasuke ciki takeyi,durkusawa tayi akan gwiwarta tareda cewa,
“Duk da nasan banda mutunci a idonka,saidai ina kwadayin muyi zama irin na ma’aurata na gari badan muba saidan yayanmu,banida ilimi na arabi dana boko haka kaima duk dayane dani,sannan dagani har kai munsan hanyar da muke kai bamai kyau bace,mai zai hana mu gyara,ko makarantar yaki da jahilci mushiga domin musamu ilimin bawa y’ay’an mu tarbiyyah,ni dama ina zuwa wajen matar kawu munkaila tana doramum,rayuwarsu tana burgeni,sannan har yanzu manjo ina sonka wallahi,soyayyar ka ita tasa na kasa kashe aurena na bishi badan wai dan ina tsoron Allah ba a lokacin.
Dan allah kadaina shaye shayennan sannan karka sake zuwa cirani dinnan da bashida amfani,ka zauna tareda damu iyalanka mugina rayuwa mai kyau tun kafim lokaci ya kure”
Tana gunjin kuka tana fada iyah karfinta,matsawa tayi tah kamo rigarsa da hannunta ta rike gam kaman wanda zai fita yah barta.
Shima ganin hakanne yasa ya jefar da belt din tareda tsugunnawa yana rungumeta a jikinsa,
“Shikenan kuluna na yafemiki kuma na fahimceki,nima inso ki yafemin,hakika laifinane kam babbba a ciki,inshaallah zan gyara halayya tah,amma ina ga zanje wajen mai gidana nace masa na yarda zan je Kazaure na rike masa aikin bulonsa nacan,inyaso sai mu tafi daku gabadaya na kama mana haya na sakasu a makaranta,dan wannan wajen zayyi wuyar sanja mutum zuwa na gari koda kuwa yayi niyyah”
Kara rungumeshi tayi cike da jin dadi,jim abinda manjon yace ,kuma cikin muryah irin ta mutum mai hankali,fito da kudin dake cikin aljihunsa yayi wanda yake tunanin zuwa siyan kwayah dasu yah mika mata tareda cewa,
“Ka wannan ki sayi abinda babu kiyi abincin rana,kuyi hakuri da rashin ciyarwar dana yi muku a baya”
Da farinciki ta karbi kudin tana yimasa godiyah da kuma fatan neman budin allah.
“Yanzu inna haka za’a kawashe duk wannan ubam kayan kayan akaimata,wanda akayi shekara ana tarawa,saikace wata diyar sarki,naga ko mu ma akwati daya aka kawomana shine ita sai ankaimata har akwati uku,gaskiyah bazai yiyu ba”
Sahura ce take fada yayar Yunusa saurayin zainab,Iyah Larabace mamar su yunusa wadda aka kira da inna itama tace,
“Kema dai kya fada y’ar nan(bata fadan sunan tah na farine)sai wani rawar kafa yakeyi akanta,duk wani dan kudinsa yah kashe a kanta tun kafin tazo,ni wannan tun kafin tazoma na fara zargim inaga farar kaface da itah”
Wata ce a gefe tah jijjiga kai ,saboda kaff garin babu wanda bai san inna laraba da kishi da matan y’ay’an ta ba,ga masifa da kuma saka ido,kuma su kansu yaranta mata halinta suka gado a jaraba.
Kanwar inna larabance tace,
“Gaskiya yaya karkiyi haka,wannan ai sai aji kunyah,ki bari koma menene idan tazo ai sai ayi koh amma ba a nan ba gaskiyah”
Dahaka badan tasoba ta bari amma bahakan yana nufin tana son akai kayanba.
Tun kafin yamma gidan gandu yah fara cika kasancewar za’a kawo kayan yan mata har guda biyu ,na salma kuma sai gobe.
Inna ramatu sai shiga ake ana fita saboda hidimar tarar baki.kasancewar al’adarsu da yamma ake kawowa shiyasa mutanen dazasu karbi kaya daga bangaren amare har sunzo.
Guda aka fara rangadawa tun daga zaure saboda masu kawo kayan zainab sun iso,kowa sai san barka yake sakawa ganin akwatinan ta har guda uku.
Wata kawar zainab dince wacce suke zaune a dakinsu tace,
“Gaskiya zeeey kinyi farin jini a wajen yunusa kuma yana sonki,ji fah har akwati guda uku aka mikk”
“Hmm dama an fadamiki so dan karami yake min ai komai yah mallaka ma zai iyah kashemin ga ………….”
Katsewa tayi da maganar suka leka waje da gudu jin wata gudar wanda tafi tah farko,
Zare ido sukayi ganin yanda aka kawo akwati har guda shida kuma ainihin designer.
“Kutt wannan duk kayan sameerah ne,tabb to a aiko a auren farko bata samu rabin na zainab ba ma,amma ji akwatinan ta”
Ihu da tsllen sameerah suka jiyo a bayansu da alama itama ta ga kayan da aka kawo gidannasu a matsayin nata.
Haka aka gama hidimar kawowa kayan aka gama kowa yah watse.
Ita kuwa sameemah dama ba ta gidan bare tasan mai akeyi dan da gangan tah tsiri aikin patrol na dare a hanyar masu cin kasuwa dan kawai kar tah dawo gidan,aikuwa ba itah ta dawo gidanba sai shabiyun dare.
Tayi mamaki ganin har sannan su sameerah basuyi bacciba sai tadi sukeyi kaman ba darene yayiba,haushine ya isheta ganin dukkansu babu wamda yayi bacci gashi tana bujatar hutu.
Sameerah ce takallesu cikin ji da kai,harda fada da karfi saboda sameemah da batasan mai yah faruba itama da ji me ake cewa,
“Ai ko yanzu na cire tuta a tarihin gidan gandu,dan tunda ake auren yan mata a gidannan ba’a taba kawo irin kayama ba,har akwati guda shida kuma masu tsada”
Haushine yakama zainab dan duk da uwar su daya amma ba karamin kishine da haushi yah turnuketa ba ganin yamda kayan yar uwar tata ya kere nata.
“Toh nidai anga kayana saikuma muka wane kaya gobe tsoho zai kawo ,shin zai taka rawa ko kuma karyar ce kawai”
Salma tanajinta amma bata ce komaiba saima murmushi kawai da tayi da alamun zan baku mamaki ni kadai na san abinda na tanada.
Duk zancen da suke babu wanda yayi gigin saka sameemah acikin zancen dam tunda kowa yaga yanda sameerah duk da rashin mutuncinta take kaffah kaffah da itah kowa ma fita harakar ta bare yimata abinda ba daidai ba.
Washagari da yamma dadai lokacin da aka kawo kayan su sameerah itama salma aka kawo nata,saidai nata yaci uban nasu sameerah,dan akwati shidan itama aka kawo amma kuma hadda wata jaka ta takalma dackuma jakakkuna,banda kuma uban kudin da aka hado dashi a cikin takrda,kofar kawu shehu babu abinda kakeji sai tashin guda da kuma hayaniya.
Tunda ganin kayan bakin sameerah ya mutu tah daina cewa nata yafi yawa,wanda hakan yabawa salma damar cewa,
“Toh yamzu mai farin jini kayan waye yafi na wani kenan?”
“Eh naji idan kayanki yafi yawa ma amma aikin banzane tunda tsoho zaki aura kuma bai kai dai saurayi ba koh?”
“Eh naji tsoho zan aurah,amma ki sani babu boka babu malam da kissata na kamashi a hannu,ke kuma fah saida aka hada dana gindin tsamiyah tukunna,saboda baza’a iyah ba.
Fada sukayi tayi har saida aka rikesu tukunna suka daina.

Kwanaki sun matso na auren su sameerah,dan dama abinda aka sakawa rana toh fah lallai sai yazo,ko ina na gidan shirye shiye akeyi dan an kula auren na manyam mutanene,babu yadda yan uwan su inna hajara basuyi da sameemah ba amma fur tace koh tsefe kai ma bazatayi a watan ba bare ace na Niki tayi,haka dole suka kyaleta,kowa yana shirin bikii ita kuwa tana tafiyah wajen aikinta.
Ana sauran kwana uku daurin aure ta dawo daga aiki cikim kayanta na damara,dan ranar koh dan karamin hijab dimma bata saba,daga itah sai hular aikim kawai.
A bakin kofar gidan suka hadu da sameer wanda shigowarsa kenan garin,wani aiki aka turoshi yankin toh yah gama shiyasa yah zo idan aka daura aure sai yah wuce,dan dama yah fadawa shugabansa.
Kallon kallo sukayi da itah ta dauke kan ta tana shirin wucewa cikin gidan,
“Ke sameemah zonan”
Tsayawa tayi kaman bazata zoba sai kuma ta taho ta tsaya a gabansa tareda cewa,
“Gani”
“Kina Ganina amma kika saka kai kika wuce koh,wai yaushe zakiyi hankaline kam iye,su inna Rabi(kanwar inna hajara),sunce sunyimiki magana akan kiyi dan shiga irin ta mata saboda yanayin biki amma kika cemusu bazakiyi ba,sannan baba yace dukkanku kowa tah fitar da miji,amma ke kikace bazakiyi aureba,so kike a jikaki a sha,yanzu fadamin wanne Kika fitar a cikin samarinki”
“Ni yah sameer banda saurayi,kuma batun kwalliya indai kainane toh nace banaso dolene,kuma aure ai ba wajibi bane mutum yana iyah cewa bazayyi ba,dan haka karabu dani karka saka daga zuwanka mufara fada da kai akan abinda bai kai ya kawoba”
Tsayawa yayi sororo yana kallonta da mamakin abinda ta fada duk da ba yau yafara jin tijararta ta ba.
“Ke yamzu sameemah abinda kike kinga yana dacewa,kinsan dai bazan ji dadi ganin ki haka ba koh,kalli aikin da kikeyi fah,babu wanda yasani sai gainki sukayi a ciki,kuma dam tsabar ke kin iyah tarar aradu da ka wai kece mai hukunta kawu shehu dan yayi laifi,kina tunanin sunji dadin abinda kikayi ne duk da basu fadamikiba”
“Toh suzo su rama masa mana,ko kuma su turoshi ya rama idan zai iyah koh …….,…….”
Tun kafin ta gama surutun sameer yayi buge mata baki da hannunsa yana cewa,
“Rashin kunyarki shiyake hadaki da mutane,kawunna ki da iyayenki kike cewa suzo su rama?”
Saurin rufe bakin tayi tana hade rai itah a dole taji haushi,shikuwa bai kulada yanayin dake ba sai wucewa da yayi yah tafi masallaci jin ana kiran sallah.
Sauke hannunta tayi a wajen tana kallom dan jinin dayake hannunta yana konewa kaman ruwa akan karfe mai zafi,wanda dama dalilin dayasa tah rufe wajen kennan.
Shigewa tayi cikin gidan kan ta tsaye ko kallon wanda suka tsura mata ido bata yiba.
*** *** ***
Fatiha allah yabawa SAMEERAH UMAR &UMAR BALA ZAINAB UMAR&YUNUSA SHEHU, SALMA SHEHU& ALH BALA………………..SAMEEMAH&……………..😂😂😂😂😂,kujirani zuwa gobe inshaallah,wannan wajen daga kasan ster duk shortcut ne..😀😀😀😀💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼.

+__________+
ABIN YABO BOOKSHOP
Kasuwar Rimi Kano
Tel:📞 07038339244

❤❤SADY-SAKHNACEH❤❤

Kar ku manta da

comment

share

like

follow.

** GIDAN GANDU **
❤❤By sadi-sakhana❤❤

Wattpad username:SAKHNA03

❤37❤

Tun wayewar gari na ranar da za’a daura aure kowa yana ta shiri,su sameerah sai rankwada kai akeyi za’a yi aure.
Karfe takwas na rana bakin kofar gida yah fara cika da mutane masu daurin aure.
Yau sameemah bata tashi da safeba saboda rashin bacci jiyah da batayiba saboda yanayin surutu na gidan,dan duk matan da’akayi aurensu nagari da ba na gari ba dukkansu sunzo,wanka tayi kafin tah dauko kayan aikinta zata saka,inna rabi ce tah ganta aikuwa ta hada mata kwaredede,
“Yanzu diyar nan mai kike shirin yi haka?,za’a yi aure a gidanku amma ke kina kokarin fita wannan shegen aikinnaki,toh ko namijima yau kam bazaije ko ina ba”.
Hakadai tah rinka yimata fada har saida aka hada da sameer tukunna kafin ta ajiye kayan.
Amma kayan anko kam na daurin aure kin sakaawa tayi,bare kuma lalle da kitso.
Baba umaru yah sha farar shadda sai sheki takeyi ga kuma hula ya kafa,duk inda yazaga murmushi kawai yakeyi kaman gonar auduga.
Motocin su umaruje ne suka fara shigowa kofar gidan da abokannansu,can kuma saiga na alhaji bala ma shida abokansa su alhaji Sama’ila,ummaruje bai tashi mamaki ba sai da yaji abinda mai shela yake fada na daurin auren,baki yasake jin wanda yah auri salma,sai a sannan ya tabbatar ba iya wajen daurin aurensa na ubannasa yazo,shima nasa aurenne yakawoshi ashe………
Fatiha allah yabawa SAMEERAH UMAR &UMAR BALA ZAINAB UMAR&YUNUSA SHEHU, SALMA SHEHU& ALH BALA……………..allah basu zaman lafiyha.
Har bayan an gama daurin auren mutane har sun fara tafiyah saiga kira daga wajen uban amare biyu wato wato baba umaru kan cewar yana kara gayyaar wani sabon daurin auren na y’ay’an sa. Dawowa aka farayi angwaye harda ma abokan angon da kuma yan uwansu,su alhaji bala sai washe baki sukeyi kaman bai san tashin hankalin dayake jiransa a gidaba.
Mamakine yakama mutanen gidan kan cewar wane aure za’a daurah bayan kuma angama,sannan nawa kuma wanda ba’asan dashiba sai yanzu?.
Surutun da’ake a cikin gidanne yatsayah cak,yayinda kwanon dayake hannun sameemah yah fadi a kasa ta koma kaman gunki wanda bashida digo rai a cikinsa sakamakon abinda kunnuwanta suka jiyo mata a waje daga bakin mai shelar:
Toh jama’a ga wani aurem ma wanda yazo a bazata saidai muyi fatan Allah yasa a samu zaman lafiyah tsakanin amrayah SAMEEMAH dakuma angonta SAMEER.
Kowa ka kalli fuskarsa a cikin gidannan yana cikin firgici saboda abinda yah ji,yam uwan inna hajarane basu ce komai ba dan kaman dama sunsan abinda yake faruwa musamman ma inna rabi.
Ba ga iyah cikin gidanba hatta mutanen dasuke waje saida suka shiga cikin rudu akan abinda yake faruwa.
Shikuwa sameer sunkuyar da gansa kawai yayi dan ji yake kaman kunnuwansa basu jiyo masa dadai ba na auren da ya jiyo sunan sa mahaifinsa yah daura masa da yar kanwarsa kwayah daya tall wacce yake da itah,kuma yake tunanin jininsu yah kusa fiye da kowa a gidan.
Su burgune suka kamashi tareda shiga dashi cikin kidan dan koh kafarsa baya motsawa sosai,banda numfashi babu abinda yake fitarwa da kyar,shidinma barazanar karewa yake a makogaransa,babu abinda yake sakawa a ransa sai tambaya guda dayah.
“Tsakanin nida sameemah shin wanene wanda ba dan gidan gandu ba kenan?”
Gangar jikintane gameda tunanintah suka tsayar da itah a da’irah guda daya,tareda hanata damar sake motsawa tun bayan lokacin dataji BAK’IN SAK’ON,dayah jiyarci cikin dodon kunnwanta,dan ji takeyi da zasuyi arba da manzon sakonnan da sai ta raba kan sa da gangar jikinsa nan take batareda da nadama koh danasaniba.
Idanuwanta ne kawai suka samu karfin gwiwar bijirewa sakon da kwakwalwarta suke basu na su tashi suma a aiki,saidai suna iyha kokarinsu naganin suna dakkomata hoton mutanen dasuke kallonta da ido a zare kaman itah ce wacce ta isar da sakon.
Tafi dakika sittin a wajen bata san inda kanta yakeba,dan ta rasa ma mai yahanata barin wannan duniyah a yanzu mai cike da zallan rudani,
Itama tambaya tayiwa kanta cewa,
“Tsakanin mu wanene wanda ba ummah na ce haifeshi ba, NI KOH SHI???.”
Saida tasamu tah yiwa kanta wannan tambayar kafin komai na haske a idonta yadauke ya barta da bakin duhu mai cike da zullumi da rudani.
Ganin tah fadi ragwaf a wajenne bayan sandarewarta na tsawon awa guda yasa akayi kanta tareda daukarta zuwa dakin baba umaru,dan shine kadai dakim da babu kowa a cikinsa a lokacin.
Haka aka cigaba da biki saidai ba kaman da ba,kowa kuzarinsa ya ragu sannan kuma yana dauke da tambaya idam za’a amsa masa amma kowa yasan babu wanda zai zauna yayi masa bayani a lokacin.
Dare yanayi aka zo daukar amare domim kaisu gidan aurensu,kawacce tasha kwalliya dadai yamda jikinta zai iyah dauka.
A wajen daukar amaryah iyaye sunzo daukar salma yayinda su kuma y’ay’a suka zo daukar sameerah,dukkansu gida dayah aka kaisu saidai kowacce da part dinta.
Part din salma a cikin gidane yana kallon na hajiyha mairo,yayinda na sameerah kuma yakewani bangare daban,dan sai an shiga wata kofah ma tukunna,sannan kuma za’a iyah fita ta ainihin get a kofar sameerah iyah karamar kofah ce tah hada ta cikin Gidan.
Tum kafin a kawo salma da sameerah bayan daurin aure wata mata ta shiga dakin hajiyah mairo babu klwa sai su kadai,ta zayyane musu duk wani abu dayake faruwa,kama daga alakar salma sameerah har zuwa yanda rayuwar gidannasu take.
Numfasawa hajiyah mairo tayi kafin kankamce ido tana cewa,
“Lallai wato abin hakane koh,sun auri dana saboda su mallakeshi sannan kuma sun auri mijina saboda nima su gajeni,to kuwa hakan bazai yiyuba dole saina dau mataki da kuma fansa,wato dukkansu a siri sukayi musu bada son ransu suka auresu ba,ni nan ina nan zaune gahotar bansa mai ake cikiba,tabbna ai dole ma na dau mataki”
A can Gidan surukan zainab kuwa wani daki aka kaita guda dayah sai dan wani waje na bandaki,hakanma inna laraba sai surutu takeyi wai an mata giinin bulo da bulo an sakata sauran matam y’ay’an ta da kuma itah kanta suna giinin kasa…………hmmm toh fah.

A rigingine yake yana kallon rufin dakin,dan tunda aka gama daurin aurennan aikinsa kenan koh magana mai karfi bayayi sai dauriyah kawai irin na mazajen sojoji,shi da yake zancen ana gama daurin aure zai tafi sai gashi har ana shirin kwana uku da aure amma har yanzu bai tafiba,bashida aiki sai tunani da neman mafita wanda har yanzu ya gaza samowa amsar ma,babu abinda yake ji aransa sai tausayinsu daga shi har sameemah wanda tun ranar yau tana cikin kwana na uku kenna amma koh mosti batayi ba .
Manjone yashigo dakin tareda tsugunnawa a gaban sameer din,karakto da fuskarsa yayi yana kallon manjon.
“Yanzu sameer kana ganin wanannan rayuwar zata kai ka,inaga mafitah shine kaje ka samu baba yah fitar dakai daga cikin zullumin daka ke ciki”
Dan murmushi sameer yayi wanda daga gani na yakene kafin yace,
“Ni bansan ma mai zanyiba a halin yanzu,nakasa samun mafita”
“Dama bakaine zaka samu mafitaba kamata yayi kaje kasamu baban”
Kimanin kwana uku da daurin auren,zuwa lokacin mutum duk san sa da jin abinda yake faruwa na auren su sameer sai da yah hakura yah tafi badan yasoba.
**
Wata irin jan iska tayi mai karfin gaske,saida ta gama gauraye duk ilahirin jikinta kafin tah fesar da itah ta karfi kaman tayar trailer tah fashe.wani mikewa tayi daga kan gadon tana karewa dakim kallo kaman mai son tuno wani abu daya shige mata duhu.
Wani irin huci tayi kwayar idonta tah koma tamkar jini na yan sakanni kafin suka koma yamda suke.
Inuwar mutum ta gani yana shigowa dakim wamda hakan yasata kawar da kanta,dan a halin yanzu bata bukatar kowacce irin halittace tah kusanci inda take,bata dago taga waye ba har gama abinda yah ke shima yah fice,da alamar mai shigowar yah fuskanci yanayin da take ciki na rashin son ganin kowa a tareda itah.
Tun safe tah tashi har wajen la’asar tana zaune bata motsaba,inna rabi ce ta shigo dauke da kwanon abinci a hannunta,
“Yar nan yakamata kici abinci,yau fah kwananki uku bakici komaiba”
Har ta gama surutuntah sameemah batace ko juyo da fuskarta ba bare ta kalleta.
Matsala tayi da niyyar dafa kafadarta,aikuwa da sauri ta ja da baya ganin yanda sameemah ta buga mata wani arnen kallo mai kamada na karashiyah.
Saurin barin dakin tayi jikinta har rawa yakeyi dan tsoro.

Baba umaru ne yashigo dakim tareda cewa,
“Sameemah yakamata zuwa yamzu ki kwantar da hankalinki ki rungumi kaddara,dan shima kansa yayannaki yaui tawakkali ba kaman keba,kashi har kwana uku sunyi da auren ki ya,kamta akaiki dakinki kema kaman sauran yan uwanki”
“Aure ,dakina, yayana, tawakkali,toh duk nabisu da azababben gudu babu wando tsirara dan malafar ubansu,kuma kaima idan baka fita a harkata ba inban hadaka da duk munafukan da akwai hannun su akan danyen aikin dakuka mini ba na saka ku a daki daya na kona ku ba,harda shikansa dan banzan da kake kira da mijinnawa,duk abinda kuka aikata ma dole zaku amayar dashi yai basai gobeba,koda bazai amayuba billahillazi saikun amayo da hanjin da gurbatacciyar garkiyar lamarin yah taba…………..”

TAMMAT BIHAMDULLAH!!

Ananne na kawo karshe litaffin gidan gandu,sannan duk wata cakwakiyah da za’ayi a cikin gidan gandu takare,yanzu sai a gidajen yan matan gidan, littafin zai cigaba………………Tambayoyinku dazasu samu damar amsuwa a littafi na gaba sune:

shin wace irin hargitsatstsiyar gaskiyah ce da su baba umaru suka boye akan rayuwar su sameemah?

wace irin rayuwa su sameemah zasuyi da sameer har ma saleemah a gida dayah?

shin saleemah zata yadda ta zauna da sameemah kuwa bayan tana ganin ubantane yake da ikon komai ,gashi bata yi tsammanin kishiyah a rayuwarta ba barekuma irin kishiyah kaman sameemah?

Da farko ma sameemah zata yadda da auren da’aka daura mata kuwa?

wace irin cakwakiyah za’a buga a gidan alhaji bala da amaryarsa salma sannan da surukarsa sameerah,ga kuma hajiyah mairo?

ina kuma rayuwar gidan zainab da surikarta inna laraba kuma?

yah rayuwar sameemah a barikin sojoji na porthacourt?

ina kuma halittarta wanda har yanzu ba’asan menene ba?

~***~~~~

DUK WANNAN AMSOSHIN TAMBAYOYINNAKU SAI A CIKIN LITTAFIN………..

WASA FARIN GIRKI (cigaban gidan gandu)

Wanda zaizo nan da sabuwar shekara akan farashin Naira dari biyu kacal (200).

……….AFUWAN……..

Nasan wasu zasuga na ce musu littafin kyautane amma kuma na shiga na kudi ta cikinsa.
To dan Allah kuyi hakuri wallahi ina bukatar kudin dazan dunga saka data ne,saboda kudina duk ya kare a saka data na littafin gidan gandu,dan haka nasaka dari biyune domin samun kudin data,idan kuma baka fajimceni ba to shikennan.

Domin neman karin bayani ku tuntubeni a numaber wayata kamar haka:
09035784150.

Ina yiwa kowa fatan alkhairi sannan kuma ina godiyah Sosai ga duk wanda suka bani goyon baya a littafinnan tah hanyar bani support da ku nuna soyayyar su ga littafin.
Uwa uba kuma wanda suka taka rawar gani wajen yimin cover.
ABIN YABO BOOKSHOP &KING AIIMAR GRAPHIC.
Ina godiyah sosai.

……….JINJINA ……..

Ga mahaifiyata allah yakara yiwa rayuwa albarka.

………GODIYA……
Ga daukaci masoyana ina godiyah sosai,Allah yah biyawa kowa bukatarsa tah alkhairi. Musamman yan group din WhatsApp kun fi taka rawar gani wajen comment,sannan Facebook,sai wattpad sai kuma telegram.
Dukkanku ina godiyah.

Wasallalallahu ala muhammadin wa ala ali Muhammadin,wasallama tasliman kasserah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button