Hausa Novels

GIDAN ARO hausa novel

Cikin k’warewa da sanin makamar aikinta budurwar mai kimanin shekaru 29 taci gaba da kwararo bayanai tana mai nuni da Farin allo wanda hasken k’wan wutan projector ya haskesa, Ko ba’a fad’a maka ba zaka fahimci cewa cikin d’akin gudanar da binciken manya manyan laifuka suke musamman irin laifin da ya shafi kisan kai, fyad’e, Garkuwa da mutane da sauransu..

Related Articles

Hoton wani matashi ne na’urar Ta hasko, kwance yake a k’asa tamkar bai numfashi, ga dukkan alamu babu rai tattareda shi.. Ko ina na wajen a kewaye ne da Doguwar igiya mai launin ruwan d’orawa, jikin igiyan an rubuta Restricted Area da manyan bak’ak’e…

Budurwar ta k’urama hoton idanu Wanda ya bayyana Babba gabansu kasancewar da na’uarar projector ake hasko hoton.. Ta matso sosai tana mai rage girman idanunta tana kallon hoton, a hankali take furta “Da hannun hagu ya rik’e bindigar, direction d’in da bindigar Ta kalla bai kamata harsashi ya samu k’irjinsa direct ba, ya kamata harsashin ya huda ribs d’insa kafin ya ratsa cikin k’irjinsa indai har da hannun da aka sami bindigar a ciki yayi harbin..”

Wani matashi mai kimanin shekaru 32 ya taso yana k’arasowa kusanta wanda shima d’aya ne daga cikin ‘yansanda masu gudanar da bincike da suke zaune a madaidaicin Zauren gudanar da binciken.. Hannayensa sakale cikin aljihun wandonsa, idanunsa naga hoton yake furta “Well done Agent Maleeka.. But wani hanzari ba gudu ba.. Baki tunanin idan mutumin nan ya kasance bahago zai iya karkata hannunsa har harsashin ta iso daidai tsakiyar k’irjinsa ta hudasa..?”

Karkatowa Maleeka tai tana duban wanda Yai maganar kafin ta d’an tab’e baki tace “Bani da tabbaci Inspector Assad.. Amma hakan nake tunani..”

Bata Kai aya ba wata murya ta katsesu da fad’in “Oh shut up.!”

Gaba d’aya suka juyo suna dubansa, kusan tun shigowarsu d’akin kansa a k’asa yana aikin murza zoben dake mak’ale yatsarsa guda wanda yin hakan kusan d’abi’arsa ce musamman idan yana nazarin bincike..

Ya d’ago kai yana dubansu, kallon da yake sanyata daburcewa ta rasa mai take ciki, tunaninta duk su sakwarkwace shi ya jefata dashi kafin yace “Tunani kikeyi.? Ko kuwa kin tabbatar..?”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button