Gara kuwa hausa novel

YAHUNDE! Babban birnin ƙasar Cameroon.*
Cikin wani kekyawan rugar FULANI mai tarin al’barkatun duniya.
Kota wani sashi Allah yayiwa Rugar Arɗo Babayo, ni’imomi na musamman, makiyaye ne cikakkun Fulanin ƙasar Cameroon.
Ranar wata jumma da yammaci la’asar sakaliya, makiyaya nata dawowa gida yayinda kota ina. Shanu tumaki raƙuma awaki zabbi keta kai komo ko wanne na nufar garken ma-mallakinshi domin ko dabba tasan uban gijiyinta,
Garken Arɗo Babayo yana ɗaya daga cikin garken da babu kamarsa a nahiyar Afirka baki ɗaya,
Yanada MAKIYAYA a ƙala mutun arba’in.
Garin ya fara duhuwar sanire alamun yanayin sanyin damina da ake ciki ko ina yayi kore shar ga tarin tsirrai kana ga igiyar ruwa da yayiwa rugar Babayo ƙawanya,
Wasu dattawane a zaune bisa ƙarƙashin bishiyar ceɗiya dake ƙofar gidan Arɗo babayo Farin dottijon ne mai cikar zarra da mutun taka ke zaune a tsakiyarsu, kana sai wasu manyan mutane dake zagaye dashi.
A gefen damanshi kuwa wani Babban mutun ne mai cikar zarra da wadatar zuciya ga tarin alamomin mutuntaka da cikar imani da haiba, bisa dukkan alamu tattaunawa sukeyi kan abinda ya shafi rayuwarsu.
Da sauri Arɗo Babayo ya ɗago kanshi ido ya zubawa sashin damanshi, inda ya hango wasu ƴan saffa-saffan samari guda huɗu suna biye da ƙatuwar suntsuwar Boleru babban cikinsu ne a gaba wanda zai kai shekaru 15 sa mai binsa wanda zai kai shekaru 13 sai mai bin masa da zai kai shekaru 11 kana sai ƙaramin cikinsu da bazai gaza shara 9 ba, gudu sukeyi sosai da iya ƙarfinsu sun tasa tsuntsuwar Boleru nan a gaba wacce ta kasa firewa sai gudu takeyi da sawunta biyu, bisa dukkan alamu tsuntsuwar tanada tsohon ciki mai girma.
Gudun da takeyi gudune na ceton rai.
Arɗon Babayo daya buɗe baki kenan da nufin zaiyi magana sai kuma ya juyo ya kalli kekyawar yarinya ƴar kimanin shekaru 8 a duniya wacce take kan cinyar mutumin nan dake gefen damanshi.
Ta miƙe da sauri cikin tsananin azama da harshen fillanci da ƙarfi tace.
(“Acce mo) Ku barta”. Sai kuma ta juyo ta fuskanci mutumin da take zaune kan cinyarshi cikin kaɗuwa da firgici da alamun tsananin tausayawa tace.
(“Appa a vi’a ɓe acca tokkugomo nɓe naunanmo) Appa kace su dena binta zasuji mata ciwofa”.
Murmushi Arɗo Babayo yayi tare da cewa.
“Kai Gainako ku barta zaku kamata a hankali ai”.
Da sauri wanda aka kira da Gainako yace.
“Baffa Giɗaɗo ne yace mu kama mishi ita mu yanka mishi”.
Da sauri suka juyo kan ƴarinyar jin wani irin ihu da tai tare da cewa.
“Ku yankata kuma, Appa kajifa wai zasu yankata, wayyo Appa kace musu kar su yankata, gashifa tanata kuka gashi sun sa taji ciwo a hannunta yanata zunda jini”.
Da mamaki suke kallon ƴarinyar sabida furucinta na wai hannunta yaji ciwo yana zubda jini, ina tsunstsuwar Boleru ina hannu?.
Wanda ta kira da Appa ne ya jawota gabanshi tare da cewa.
“Parvina tsuntsu kuma tanada hannune?.”
Da sauri ta miƙe tare da ɗaga murya tace.
“Ba tsuntsu bane Appa wlh mutunce gata nan da ciki gashi ma tana kuka tana-ta kare cikin jikinta”.
Cikin mamaki suka zubawa tsuntsuwar Boleru ido su dai Allah ya gani gaba ɗayansu tsuntsuwa suke gani tana guduwa da kyar wanda kuma kowa ya ganta yasan tanada tsohon cikine.
Giɗaɗo ne wanda shine ƙarami yaron ɗan shakara 9 kuka yasa tare da cewa.
“Wayyo ya Gainako kayi sauri ka kamo min ita karta gudu”.