Hausa Novels

FITAR RANA HAUSA NOVEL

6:15pm Bunu: Shammo cluster,east language of kainji,toro L.G.A bauchi state.

Related Articles

Lokacine da almuru ya Æ™eto gab gabotawar sallahn magriba. wata Æ™ibabbiyar matace wacce a shekaru bazata haura sama da arba’in ba, kalar fatar jikinta É“aki kirin ta Æ™ife irin fallen zanin atamfar dake jikinta akanta tayi lullubi dashi har saman idanunta tamkar wacce bataso a kalli tsananin munin fuskarta, dauÆ™e take da man fetur da kuma ashana ahannunta, ta tsaya a Æ™ofar wani matsaikaicin gida ginin blo dayajima sosai duk ya balangwaje ya tsofe ginin ya karsashe wanda ana taÉ“a bangon Æ™asane kawai ke zuba.

Daga cikin gidan Babu abunda ke tashi acikin dan tsurkukun dakin nasu sama da zautaccen bugun sautin wahalallaleyar numfashin mace wacce amonsa tayi kama da kamar ranta ake zarewa acikin tukikin ciwon naƙuda mai azabtarwa da kuma radadi,ita kadai sai murƙususu takeyi acikin dakinta tana tauna laɓɓanta tana wayyo Allahnta amma kashh!! shiru kakeji babu wanda ya kawo mata doƙi.

Bisa Kallo daya kayiwa matar zaka fahimce cewa bazata wuce kimanin shekaru arbain da takwas a haife ba,murmurarreyar mace ce mai ginannen jiki wanda duk da alamun wahala da talauci dayayi mata naso ajikinta da kangon dakinta bazai taba hanaka kallon kyakkwar surar halitta da Allah yay mata ba.,ba kuma ina nufin tsantsar kyauna kwatantacin siffar ƴayan aljanu ba,a a, .ina nufin itama baqace sidik original melanin beauty, mai dauke da natural skin na matanmu na mutan _biu(a jahar maiduguri)_ tabbas matar nan ta mallaki sulbabben sheqin fatar su mai kyau da daukar ido,game da dirarren shape da baƙin suman kai dai dai cikon misali.

Har kwatankwacin Misalin tara na dare amma haryanzu shiru,iska ne ya cigaba da kadawa sakamakon yanayin damina ne duhun inya rufa har ba a iya kallon hasken tafin hannu.

Matar can tana waje,mai naƙudar nan itama tana cikin gida tana kkrin fidda nishi,kuma Dukkansu basu rusuna akan qudurorinsu ba.

Duk wani addua daya fixgo kanshi cikin bakinta da zucyarta yinshi kawai takeyi danta samu saukin azabar naƙuda datake sha ajikinta dan kuwa yau Shekarunta 30 kenan da yin aure a duniya amma bata taɓa samun haihuwa ba sai a wannan ƙaron da jiki ya riga ya ragwabe tsufa kuma yaxo mata rayuwa ya kuma musu tsanani ita da mijinta malam hassan(aliyu) denge a hannun muguwar amaryasa Anmuna.

Maimunatu garba,
wacce akafi sani da Anmunah mayya yar gidan garba maye ta kasance tamkar wata mujiya ce acikin alummar shammo ta kabilar ribinawa a jihar bauchi, kasancewar zargin da akeyiwa mahaifinta nacewa shi mayene Shekara da shekaru bacin duk wani alamu sun nuna hakan amma rashin Æ™wakkwarn shaidu shi ya hana a gurfanar dashi.Qaddara shiya janyo aure tsakanin anmuna da malam hassan mijin badiatu wanda tunda suka Æ™afa alÆ™almin tarihin zaman auren su basu taba sabawa juna ba,mutane ne masu tsantsar hkuri da juriya tare da takantsantsan da rayuwarsu gameda kyakkwar zuciya,a tunanin su kawo anmuna cikin zamantakewar su zai iya jawo musu albarkan haihuwa bayan tsawon shekaru da sukaja basu samu É—a ko Æ´a ba,anmuna takai shekaru sama da arba’in babu wanda ya taba taya aurenta sabida halin mahaifinta na maita,acikin tsangwama tay rayuwarta,malam hassan da badiatu ne kawai suka tausaya mata, amma sai abun yazo musu da sabuwar qaddara wanda basu tabayin tsammanin cin karo dashi ba.

Dan kuwa tunda anmuna ta shigo cikin gidan su da sunan aure yau shekaru goma kenan malam hassan da matarsa badiatu suke cikin tasƙon rayuwa mai tsanani.

Duk wani albarkan Rayuwarsu saida tayi fatali dashi,ta talautasu ta muzanta su,tayi zaman diris akan dukiyarsu sannan ta sassaka musu ciwuka kala kala ajikinsu.

Tunda badiatu ta same wann cikin yakasance malam hassan bayada wani kwanciyar hankli
Yaushine nan gobe shine can duk dan ya ƙare matarsa badiatu daga mummunan kaidin anmuna,ahakan ma da ikon Allah ne kawai sukaci nasara dan kuwa tasha alwashin dauƙar ransu duka inhar ya sake badiatu ta haihu mata acikin gida.

Yau tun safe ya fita neman taimako awajen wani babban malamin addini dake taimaka musu sosai wajen Æ™aresu awani dan kauye,duk hanklinshi baijikinshi, ya tafi yabar badiatu cikin ciwon ciki yasan izuwa yanzu ta galabaice,yana amsar magungunan da malam ya damÆ™a masa ya kamo hanyar gida cikin gaggawa,tafiya yake kamar zaici da baki tsabar sauri amma sai yaga kamar ana komar dashi baya, ko yayi lalume yaga ya É“ata a jejin,gaba daya saiyaga ya ruÉ—e hanyar ya bace mishi baiya fahimtar inda ya dosa,ko haka kawai yaji ya firgita,wani sa’in ji yake anai masa maganganu marasa ma ana masu kuma firgitarwa da tsaki mai Æ™auri acikin kunnen sa,Ahaka dai ya danne xuciyarsa bai karaya ko yaji tsoro ba,Adduoi ya dingayi har Allah ya kawo sauÆ™in abin sannan ya soma fahimtar hanyarsa harya gabato ixuwa gida.

Goma shaura dot na dare saigashi ya iso kusa da kofar gidansa inda baifi taƙu ashirin haka yakai inda matar can take ba,kirjinshi na tsananta bugu duk jikinshi na rawa cikin sauri ya hau warware kullin dake hannunsa kamar yadda malamin ya umarceshi daya shafa turaren dake ciki ajikinshi kafin ya gabatota hakan kuwa yay babu ɓata lokaci,shiyasa harya xo ya wuceta suduk cikin duhun dare bata ganesa ba..

Tari take tana zage zage ita kadanta “Durun uwa!!! wannan wani irin kazamin turarene haka?

Da addua abakinsa ya shiga gidan ya samu badiatu tana kwance cikin jikata harta fara É“arin jini,tana ganinsa ta soma kkrin miÆ™a mai hannunta dake rawa rawa cikin kakkalallen murmushi mai mugun rauni ta riÆ™osa tace “Aliyu”..Aliyu harka dawo?..raunatattun hawayensa ne suka soma gangarowa bisa kuncinsa yanamai gyadamata kansa yanacewa “eh”,agabanta ya durkusa bisa gwiwonsa duk gabobin jikinsa sun nakarkashe jikinshi baida wani sauran laka,wani malalaciyar numfashin tausayin kansu suka sakar ma junansu.

Rungumeta yay ajikinshi
Tsammm yana maida ajiyar numfashi muryansa can Æ™asa sann yace “sannu…kiyafe ni Badi’atuh na..kiyafeni daya kasance bana tare dake a wann lkcin dakike matukar bukata…sannu kinji..Allah ya sauÆ™eki lpya yar aljannata…kanta kawai ta iya gyadawa cikin ciwo…Ya dauÆ™i shauran turaren ya shashhafa mata ajikinta itama,yabi ya hada ruwan maganin daya amso awajen malam ya bata tasha wasu ya wanketa dashi dan malam ya gaya masa aljanu ke azbtar da ita ba zallan ciwon naÆ™udar ba,Aikuwa tana shan maganin gadan gadan saiga ciwon naÆ™uda ya tasomata babuji babu gani,da murÆ™ususu da komi haka badiatu ta sauka lpya cikin ikon Allah ta haifo lafiyayyar Æ´a mace
Wacce ta debo kamannin uwa da uba batada nakason komi.

Malam hassan(aliyu)tuni ya zauce wajen kallon yarinyar dake cikin jini rauntattun hawayensa na diga yuuuuuuuu akanta tamkar koramar datayi ambaliya,bakinsa dake karkarwa babu abunda yake furtawa sai Allahn sa “Alhamdullahi rabbil samawati wai al’ardi…ya rabbil alameen,anta noorul samawati wama fi hinn,Rabbil arshill azeeem.Allah maiyi duk yadda yaso a kuma lokacin dayaso,yah Allah nagode maka!!Allah nagode maka,ya rungume yariyar tsam ajikinshi yana mai fidda sautin kukansa mai cike da gamsuwa da ni’imar da Allah ya saÆ™a musu dashi daya azurtasu da haihuwa sakamakon hakuri da juriyarsu tsawon shekaru 30 da aure.

Cikin kalilin lokacin suka tsaftace kansu da diyarsu wacce taci sunanta..”WASIMÉ”
Ma’ana wani kyautar karramawa mai girma kuma ta musamman daga wajen ubangiji,
kalman “wasimé” yana nufin “the mercy of God”, as distinguished from His justice;a divine love or pardon,a state of acceptance with God.

Tare da dayar ma’anarsa dayake nufin “Sa’a,(fortune)or someone who helps odas selflessly,divine beauty or lets say graceful nd preety..

in greek philosopy wasimé is a historical name of 3 beautiful sister goddesses
(Aglaia,euphrosyne,and thalia) represnted by ancient writers for apollo nd ofteners of venus and are regarded as inspirers of good qualities like wisdom, love nd social spirits.Kalman wasimé har ila yau kalmace mafi daraja ga masarautar england as thy often refer to their dukes nd dutchesss with its kinds.

Sunan da suma suka zabarwa yarsu kenan sabida su nuna wa Allah godiyarsu,Saidai ciwon ciki da xubar jini shiyaci ƙarfin badiatu ayanzu,
babu yadda malam hassan baiyi dan subar wajen akan lokci ba amma ina duk kkrinsa yaci tura gashi malam ya gargadesa da suyi maza subar gidan kafun anmuna ta hankaro
,Saidai akowani dakikanln wucewar lokaci jikin na badiatu dada rakwabewa yake daÉ—ayi…”yarinyarsu wasimé da suka nannade acikin zani tana baiwa nono ta fincikota a hankli tana kallonta idanunta na fidda kwalla ta damka masa ita a hannunsa ,É“ari hannunta yake alamun ta jikata muryanta na fita a rarrabe cikin wahaliyar
Tace”Ali…Al…iyu ka tsira tare da wasimé,kayi sauri..sauri kuje kakaita matsera sann kadawo gareni…Aliyu ka..kkaje bamu da lokaci..kar mumm..mujefa rayuwar yarmu da batasan komi ba acikin ukubar maimunatu,kanaji na kuwa Aliyuhhhh?..Ya rasa abun da zaice mata sai kukan zuci dayake rabzawa,ahnkli ya rungume Æ´arsa a kafadun sa hannunsa saÆ™ale dana matarsa yana murzawa a hnkli
duk jikinshi na rawa,can ya miƙe tsaye kamar an tsakureshi yanata kallonta da raunatattun idanunshi wanda sukayi naso da kaunarta yanaji kamar zai hadiyeta,wani wawan shauki ya kuma yunkuro da shi ya gurfana ajikinta kamar sabon mahaukaci wanda baiya cikin hayyacinsa Tare da sakar mata wata shaukakkiyar runguma mai tsuna yanamai sumbatar koina ajikinta araunane
“..muryan sa a dishe yake cewa’..Badiatu kiyimin alkwarin zaki jirani kinji?…bazan daÉ—e ba wannan karon zan dawo gareki badi’atu..nayi miki alkwari rabin raina…kijirani anan kinji badi’atu na…ta gyada kanta a hankli tana sumbatar sa,wani
Murmushi mai taushi suka sakar ma juna sannan ya share fuskarsa ya share mata nata itama,nan yay ta maza ya saɓi jinjirarsu a kafadunsa ya shafa musu turaren sannan suka doshi hanyar yamma..,lkcin ana neman ƙarfe 2:00 na dare
Cikin murkususun ciwon cikin badiatu ta kasancel mai tsananin azabtarwa.

Malam hassan kuwa bai tsaya ba tafiya kawai yakey acikin jeji burinsa baifi yaga ya iso wani dan ƙaramin gari da ake ƙira Ringin gana ba.

yadda ya rungume jinjirar babu abunda yake jansa sai amon sautin murya matarsa dake yawo akansa yana ƙara ma zciyarsaa rauni da ƙarsashi.

Hudu da rabi shaura na dare ya iso ƙofar wani gidan ƙasa wanda ya samu kofar zaurenta a buɗe shiga yayi cikin sauri zuciyarsa tamkar zatay tsalle ta fice daga kirjinsa,direct kofar wani rumfa ya shiga ya kwankwasa sau daya sai gashi an buɗe kofar.

Wata matace sanye da hijabi dogo har Æ™asa,ta fito hannunta riÆ™e da carbi,da kuma fitilar obasanjo ya gaza tana mai Æ™are mai kallo cikin mamakin ganin yanayin sa..muryanta kamar na wacce zatayi kuka ganinsa da jaririya a hannu ta dada kwalo idanunta waje tace “Tubarkallahu masha Allah Aliyu har badiatu ta sauÆ™a? kun iso ne toh ina ita badia’atun take?
..gani tayi yay shiru dik ya kasa furta wata magana lkcin numfashin shi ma sama sama yakei kamar zai dauÆ™e ya rabu da jikinshi, da kyar maganan ya kufce masa bacin kuka mai tsuma da tsofuwar ta sakar ganin duk ya gigice. Aliyu lpya kuwa?a hnkli yace”umma na ki riÆ™e mana wasimé amana ni zanje in dauÆ™o badiatu a shammo!!
Umma nabar badiatu cikin ciwo…umma saina dawo!!!…”gyada kanta kawai take tana hawaye tanacewa toh toh toh Aliyu kayi maza ka jeka Aliyu Allah ya Æ™areku gabadayanku ya dawomin daku lpya.
Allah yay ma wasimé Albarka tana magana tana kuka sosai…harya juya zai bar wajen sai taga ya juyo ya riko hannayenta tare dana babyn Ahnkli yace “umma inbaki ganmu ba Wasimé takice har abada mun barmiki ita amana!!umma kiyafe min dukkan kuskuren dana aikata miki arashin sani ki kuma yafewa matata badia,!!kanta take girgizawa cikin kuka”zaku dawo Aliyu,kadena fadar haka kaje ka dauÆ™o badia insha Allahu zaku cinye wann jarabawar,baice komi ba ,tanata magana harya bar wajen bata sani ba sabida kuka mai taÉ“a zuciya da tausayinsu da ya mamayeta.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button