FINA-FINAN BATSA BLUE FILMS

Idan ka karanta ka turawa sauran yan uwa domin su amfana.
Blue films fina finai Ne da wasu tsageru daga cikin Yahudawa suke shiryawa wanda Yana da Illa sosai.
Domin Yanzu anyi ittifakin cewa ba abin da Yake saurin rufta mutum zuwa zinace-zinace kamar shi kallon blue films din wanda zamani Yazo da shi baga namiji ba ba kuma ga mace ba.
Babban abin takaici Yanzu Yan mata sunfi kowa kwarewa wajen iya kallon wannan lalaci na blue films.
HUKUNCIN SA:
Kallon tsaraici haramun ne a shari’ar musulunci in banda na matarka kona mijin ki ballantana kuma kallon saduwa tsakanin mazinatan wannan abune mai matukar muni sosai.
Allah Yana Cewa:
“Ka gayawa mumunai maza su rintse idanuwansu daga kallon haram kuma suki Yaye farjinsu daga Yin zina.
‘Yan uwa mu kiyaye, duk wanda Yake kallon irin wadan nan abubuwan to lallai Yayiwa Allah Tawaye.
A Wani Gurin Alkah Yana Cewa:
Kada Ku Kusanci Zina hakika ita zina Alfasha ne kuma mummunan hanyace.
Kunga sabo da halakan da take cikin zina, sai Allah Yace kada mu kusan ceta, shi kuwa irin wannan kallon Yakan sanya masu Yinsa su afka cikin zina kai tsaye.
Manzon Allah (S.A.W) Yana Cewa;
” Allah ka tsinewa mai kallon tsaraici da kuma wanda ake kallon tsaraicin nasa.
Daga karshe ina kara jawo hankalin masu Yi su tuba su daina…..!!!
Don Allah Daure ka rubuta Ameen Bamusan tawa za’a karba Ba…
Sannan kallon fina-finan batsa yana kai mutum zuwa ga aikata mummunar dabi’ar nan ta istim’nai wacce ita ma tana da illoli ga lafiya.
Ya Allah Ka Tsarkake Mana Zukatan Mu, Ka Kare Zuri’ar Mu Daga Afkawa Cikin Mummunar Bala’in Dake Tattare Da Kallon Blue Films.🙏🙏🙏
Like & Share.
Dr-Nuraddeen katsina
08068962793