Hausa Novels

DOCTOR HASSAN – COMPLETE

🩺DOCTOR HASSAN🩺

Related Articles
            💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

Love and romantic and funny story

Writing by

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*

Marubuciyar nan taku ta INDO A BIRNI

Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a duk inda kuke da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni yanzu ma gani tafe da Hatsabibiyar da tafi INDO sheɗanci.

Bazan taɓa manta alherin ku gareni ba masoyan Asali waɗanda suka kasance dani a cikin littafin RUƊANIN ZUCIYA BIYU gaskiya naji daɗin ƙaunar ku gareni, domin kuwa kun sayi wannan littafin fiye da yanda nake zato to yanzu ma gani tafe da sabon labari mai rikitar da mai karatu.

Ku dai ku kasance dani mu tsunduma cikin wannan labarin.🖊️📖

بسم الله الرحمن الرحيم

________________________

🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼
🇦SSOCIATION🤝🏻
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

      *Book One*

Page 1 to 2

_________________________

Alhamdulillah ala kulli halin, na godewa Allah daya bani damar sake dawo muku da sabon book ɗina, wanda nake da tabbacin zaku samu nishaɗi a cikin sa, tare da tsantsar darasin zamantakewar Rayuwa mussaman zama irin na babban gida Soyayya tausayi cin Amana ban dariya, ɗan uwa ƴar uwa ina kike maza taho mu haɗe dake cikin wannan labarin mai matuƙar zaƙin zuma tare da garɗin madara taho domin kema a dama da ke nidai fatana na kawo muku Abunda zai amfane ku.

Wannan labarin yana tafe ne da salo na mussaman .

Please idan kina da interest akan wannan book ɗin ki fara binsa tun yanzu kar sai nayi nisa kice min daga farko.

Sharhin ku shi nake buƙata.

Mu kafta ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️

BABBAN BIRNIN MAIDUGURI BARNO STATE

Jihar da ta tara Barebarin Asali birnin kanuri.

Unguwar GRA

____________Fitowa yayi daga tollet ƙugunsa ɗaure da towel, ɗaya kuma ya ɗaura a kansa yana tsame ruwan jikin sa, dressing mirro ya ƙaraso ya jawo table ɗin dake wajen ya zauna yana cigaba da tsame ruwan jikin sa, sanda ya tsame ruwan tas sannan ya ajiye towel ɗin a hanun bed, lotion ya jawo mai ƙamshin gaske ya fara mulke jikinsa dashi, sannan ya hau gyara gashin kansa shima da mayuka masu ƙamshi sanda ya mulke ko ina na jikin sa da lotion sannan ya ɗauki body spray ya dinga feshe jikinsa dasu sanda ya fesa kala uku kafin ya miƙe tsaye ya je drower ya buɗe ya ɗauko set ɗin kayan sa Blue Black ɗin wandon jeans ya saka tare da rigar suit fari yasa tare da ɗauko ribin dark blue ya ɗaura a wuyan rigar gyara kwalar rigar yayi sannan ya ɗauko suit ɗin ya saka , komai cikin nutsuwa yake yinsa sannan ya ɗauko takalmi sau ciki zama yayi bakin bed ɗin ya sunkuya yana ɗaura igiyar takalmin.

” Assalamu alaikum”

Yaji sallamar ta, shuru yayi ba tare daya amsa mata ba ya cigaba da ɗaure igiyar takalmin, Sau uku take sallamar amma yayi banza da ita kamar baiji ta ba ya cigaba da abunda yake yi, sai a na huɗun ne ya amsa mata can ciki kamar wanda baya son Maganar nan ma sanin darajar Sallamar yasa ya amsa mata idan ba kana kusa dashi ba bazaka ji ya amsa sallamar ba, ita kanta ganin da tayi bakin sa yayi motsi ya sata fahimtar sallamar ya amsa mata, ƙarasowa tayi har gaban sa ta tsaya jikinta a sanyaye ta sunkuya tare da saka hanu zata karɓi igiyar takalmin ta ɗaure masa, yayi saurin bige hanunta yana cigaba da ɗaure wa, cikin sanyin jiki ta masa magana da Sweet voice ɗin ta tace.

” My Doctor breakfast is ready.”

Shuru Yayi Still bai kulata ba, kuma sarai yana jinta sai ma ƙara haɗa fuskar sa da yayi tamau babu alamar annashuwa cikinta, ɗagowa yayi tare da ɗaukar agogon sa ƙirar gucci ya fara ƙoƙarin ɗaurawa a hanunsa, a karo na biyu ta ƙara cewa.

” I Say Doctor breakfast is ready please jiya ma fa haka ka kwana babu abunda kaci ko ruwan tea baka sha ba, haka ka kwana ya kamata kafin ka fice kasa ko da ruwan tea ne a cikin ka bana son kana fita da yunwa bana jin daɗin hakan.”

Ɗago lumshashshun idanunsa yayi masu kama dana mai bacci fuskar sa kuma a matuƙar ɗaure ya dubeta sannan ya fara magana cikin Slow VOICE ɗinsa da kuma faɗa faɗa.

” Wai meyasa ke mayya ce kam FALMATA!!!!, Meyasa kika addabi rayuwata ce, nace miki na tsaneki ki daina damun rayuwata ki daina shiga Cikin lamari na, Wallahi Falmata na miki tsanar da ban taɓa yiwa wani ɗan adam shiba, na tsaneki na tsani iyayen ki ina Zaune dake ne a dole Saboda kin zamo min ƙarfen ƙafa ba yanda zanyi dake, Banza ƴar Mayya, dan Allah ki fita a cikin rayuwata, nace bazan ci abincin ki ba ko ana dole ne Get Out of my room Mayya!!!!.”

Ya ƙarasa maganar yana nuna mata ƙofa, hawaye ne suka gangaro daga daradaran idanunta, ta ɗago tana kallon mijin nata cikin matsanancin damuwa da tashin hankali, sunkuyawa tayi ta durƙusa da gwiwowin ta ta fara magana cikin rawar murya mai cike da alamun kuka.

” Karka min haka mijina Please ka daina hukunta ni da laifin da ba nawa ba, asali ma bani da hanu ciki, kana azabtar dani da yawa Doctor, kaine duniya ta, bani da wani farin cikin daya wuce naka, meyasa sanda ka koya min Soyayyar ka sannan zaka juya min baya, Ka ji tausayi na ka cire ni cikin LAMARIN GABAR CIKIN GIDAN MU TABBAS AN ƁATA ZUMUNCI amma ni meye nawa ciki da zaka juyawa Soyayyar mu baya, INA SOYAYYAR DA KACE KANA MIN, KAINE FA KA ƊAUKA MIN ALƘAWARIN CEWA BAZAKA TAƁA RABUWA DANI BA, KOMAI TSANANI KOMAI WAHALA KANA TARE DANI MEYASA YANZU KA TSANENI LOKACI GUDA ina sonka MIJINA kaji ƙaina?”

Ta ƙarasa maganar cikin matsanancin kuka, tunda ta fara Maganar ya zuba mata Lumshashshun idanunsa yana mata kallon tsana da kuma tausayi sanda ta dire maganar tukunna Yaja tsaki mai sauti sannan ya sunkuyawa ya ɗebi wayoyinsa dake bedsite drower da key ɗin motar sa ya juya da niyar ficewa ba tare daya tanka mata ba, yaji ta riƙe ƙafafunsa, Runtse idanunsa yayi sanda yaji hanunta a jikinsa, Yana jin wani abu na yawo tun daga babbar yatsar sa har cikin kansa tsayawa yayi cak.

” Please My Doctor ka taimaki Rayuwata ka tausaya min, Ka dawo da Soyayyar mu ka ji ƙaina, Wallahi zuciyata ciwo take min, karka bari na mutu ta sanadiyyar ka kaine gata na, kaine rayuwata ina sonka DOCTOR.”

Cin jin wani ƙarin tsanarta ya saka ƙafarsa ya naushe ta da ƙarfi sanda ta bige kanta da jikin bed ɗin, da sauri ya saka kansa ya fice daga cikin bedroom ɗin, kanta ta riƙe tana jin yana mata zafi, hawaye kuwa wani ne yake bin wani saman fuskar ta, sosai take kuka harda shashsheƙa, takurewa tayi a gefe tana cigaba da kuka zuciyarta kuma cike take da baƙin ciki, Duniyar gabaki ɗaya ji take ta isheta, kullum baƙin ciki shine abokin hirar ta, ta rasa farin cikin ta tun sanda wannan mummunan ƙaddarar ta afku tsakanin mijinta d iyayenta, mijinta mai tsananin ƙaunar ta wanda ada baya son ɓacin ranta wanda kullum shine abokin hirarta shine amininta, shine mai share mata hawayenta amma yanzu shine mutumin daya fi kowa tsanar ta, shine ya maida ita ABOKIYAR GABAR sa, Tabbas rayuwa ta juya mata ba tunda har ta shiga tsakanin ta da mijinta, sanda taci kukan ya isheta sannan ta tashi ta goge hawayenta, ta faɗa saman bed ɗin nasa tana ajiyar Zuciya, rigarsa daya cire ta rarumo ta rungume a ƙirjin ta, tana shaƙar ƙamshin turaren sa, ji take tamkar shi ta rungume, sai famar ajiyar Zuciya kawai take, tana nan rungume da rigar har bacci ɓarawo yayi nasarar sace ta tana sauƙe ajiyar zuciya.”

Shi kuwa yafi 30 minute yana zaune cikin motar ya ɗaura kansa jikin matuƙin motar pictures ne ɗan ƙaramin elagment a ajiye cikin motar, Sosai yake ƙarewa pictures ɗin kallo kafin yasa hanunsa ya shafa sa hawaye ne yake tsiyaya saman fuskar sa, AUNTY JALILA DA UMMAN SA sune kawai suke masa yawo a cikin zuciyarsa shikenan ya rasa AUNTYN SA DA ABBAN SA anbar UMMAN SA kuma cikin jinya, taya zai iya yafe musu bayan ya rasa farin cikin sa duk ta sanadiyyar su, ya daɗe zaune cikin motar kafin ya ɗago kansa ya goge hawayen sa, motar yayiwa key, ganin tahowar sa yasa mai gadin saurin wangale masa makeken get ɗin gidan, Yana ɗaga masa hanu, shima hanun ya ɗagawa Baba mai gadi ya ciro kuɗi dubu goma ya miƙa masa cikin sanyin halinsa yace.

” Gashi Baba kuɗin da na maka alƙawari jiya kayi hkr 20k nayi niyyar baka, so yanzu babu kuɗi a gida gaskiya dole sai na biya bank na ciro, so kayi hkr da wannan sai kaje ka fara Siyan maganin kafin na ƙara maka wani abu.”

Yana godiya baba mai gadi ya amsa yana cewa.

” Mai yawan kenan ranka shi daɗe na gode sosai Allah ya ƙaro zumunci ya tsareka ya bawa Umma lafiya na gode.”

Murmurshi kawai ya masa tare da amsawa da Amin kafin ya fice daga cikin gidan rufe get ɗin Baba yayi sannan ya zauna saman tebur ɗinsa yana cewa.

” Oh ni iro har yanzu wannan yaro yaƙi sakin jikinsa tunda wannan al’amari ya faru kullum yana cikin damuwa, babu walwala kwatakwata a fuskar sa, duk da shi ba ma’abocin dariya bane amma ai kullum fuskar sa ɗauke take cike da haiba da kuma murmurshi, Allah ka daidaita lamarin waɗannan bayin naka, Allah ka kawo ƙarshen wannan lamarin ka bawa Mahaifiyar wannan bawan naka mai tausayi da jin ƙan na ƙasa dashi lafiya ka bayyana masa ƴar uwarsa da mahaifinsa, itama Hajiya ko zata samu farin cikin ta ya dawo kamar da mace mai tausayi da kyauta tana cikin damuwa.”

Ya ƙarasa maganar yana ajiyar Zuciya..

Shi kuwa doctor titi ya harba yana dreving a hankali, zuciyarsa kuma cike da ƙunci kwatakwata ya tsani dosar family Hause ɗin nasu sai dai babu yanda ya iya dole ya kamasa yaje tunda akwai Umman sa kwance babu lafiya, ringine ɗin wayar sa ne ya dawo dashi daga tunanin da yake, kallon sa ya kai kan screen ɗin wayar yaga sunan IB ya bayyana hanu yasa ya ɗaga wayar tare da cewa.

” Ina sauraronka IB.”

Murmurshi IB Yayi daga can kafin yace.

” Kana ina ne yanzu Doctor.”

A taƙaice ya basa amsa da cewa

” Ina hanya zanje family Hause wani abune yake faruwa.”

” Okay to shikenan idan ka fito daga Family Hause sai ka samu ka biyo Hospital domin kuwa akwai matsala wacce jiya doctor Saif ya mata oppretion sun bata ruwa tasha daga farfaɗowar ta cikin ya ɗan hau.”

Da ƙarfi Ya furta.

” What!!!!! Suka bata ruwa tasha mahaukatan inane su, bayan sanda na gargaɗe su da cewa karsu bata komai tasha idan ta farfaɗo mtssssss!!! Ka bani 30 minute ina zuwa insha Allah bari naje na duba Umma amma ka kira DOCTOR Saif yanzu maza ku shige da ita ɗakin operation nima ina zuwa.”

” Okay ba damuwa Allah ya kawo ka lafiya.”

Kashe wayar doctor Yayi yana tsuka tare da furta ” wasu mutanen sam basu da hankali” a haka ya shigo cikin unguwar tasu ta BULUN KUTU TSALLAKE dake cikin Local govt na MAIDUGURI, jihar BORNO wani ƙofar gida na gargajiya yayi parking ƙofar gidan cike yake da Dattawa suna zaune a babbar taburma sai wani Dattijo dake zaune a saman farar kujerar roba da alamu dai wannan gidan na sarauta ne irin sarautar cikin unguwa, fitowa Doctor Yayi ya tako zai shige cikin gidan, sai ya hango Kawu Dauda, da har zai wuce ba tare daya nufi wajen da dattijan ke zaune ba, sai kuma ya dawo yazo ya sunkuya cikin sanyin muryar sa yace.

” Kawu Dauda sannu da hutawa”

Tare da miƙa masa hanu sukayi musabaha gaisawa yayi da sauran dake zaune bai ɗaga kai ya kalli wannan dattijon dake zaune a saman kujerar ba, wanda fuskar sa take naɗe da rawani, ya miƙe zai shige cikin gidan yaji muryar kawu, Dauda yana ce masa.

HASSAN baka da hankali ne, baka ga BAFFAN KA bane baka gaishe sa ba,ko ka manta dashi ƙanin ubanka ne kasa kai zaka wuce, rashin ɗa’a fa ba halin ka bane naga yanzu ka ɗauko wani halin banza wanda a baya baka dashi.”

Shuru Doctor Yayi yana tsaye yana sauraran Kawu Dauda, sai da ya ƙarasa maganar tukunna sannan ya saka kai ya shige da sauri ba tare daya tankawa Kawu Dauda ba domin kuwa bazai iya gaishe da wannan baƙin azzalumin ba, Kawu Dauda duban wannan mutumin yayi yace.

YALLAƁOI kayi hkr na rasa ya akayi Hassan yafi kowa ɗaukar wannan lamarin da zafi, duk da nasan yana da zafin zuciya, amma abun nasa yayi yawa insha Allah zan masa faɗa komai zaizo ƙarshe zai gyara.”

Gyara zaman sa yayi wanda aka kira da yallaɓoi ɗin, sannan ya fara magana.

” Karma ya gyara dan ubansa idan sunga dama su cigaba da gaba damu daga su har yan uwan nasa har duniya ta tashi, ɗan banza wanda ya yi gadon tsiya a wajen uwarsa kuma wallahi idan sukayi min iskanci sai na kore su daga cikin gidan naga uban da zai dawo dasu.”

Gabaki ɗaya dattawan dake wajen kallon sa suke cike da mamaki, wai zai koresu daga gidan nasu gidan da aka haifesu gidan ubansu ikon Allah lallai ZUMUNCIN wannan gidan ya lalace, Kawu Dauda baice komai ba.

DOCTOR da bai ƙarasa shigewa bane yaji Abinda yake cewa ya dawo cikin sauri da ɓacin rai.

Jin muryar sa sukayi yace.

” Idan ka fasa korar mu daga cikin wannan gidan ka raina Allahn daya halicce ka, idan ka isa kai mai iko ne da faɗa aji dan Allah karka barmu mu kwana a cikin gidan nan ya idan kuma ka barmu mun kwana baka ci sunanka ABUBAKAR ba mtsss, shasha…….

Yana ƙarasa maganar yayi shigewar sa cikin zafin rai gabaki ɗayan su kallon mamaki suke bin DOCTOR HASSAN dashi Lallai ɗan zaki ya girma.

Kawu Dauda ya furta tare da tashi ya bar wajen, yana Allah ya kyauta, shi kuwa wannan bawan Allah zuciyarsa takai har wuya domin kuwa gani yake Hassan ya tozarta shi amma babu damuwa sai yayi maganinsu kamar yadda yayi na ubansa.

To fa ina kake/ina kike maza biyoni mu ninƙaya cikin wannan labarin mai matuƙar daɗi cike da nishaɗantarwa tare da tsantsar Soyayya kudai ku kasance da.👇🏻

ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻

(Ummu Nasmah ce)

            🥰

[8/27, 9:27 AM] Ummu Nasmah❤️❤️❤️❤️: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

            💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

Love and romantic and funny story

Writing by

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*

Marubuciyar nan taku ta INDO A BIRNI

Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a ko yaushe, da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.

Special Gift to

Masoyan Asali waɗanda suka kasance dani a cikin book ɗina na kuɗi wanda ya gabata wato Ruɗanin Zuciya biyu kun sayi wannan book ɗin fiye da zato na Tabbas kun nuna min ƙauna domin kuwa hakan ya gwada min kuna tare dani ako yaushe koda kuɗi ko babu nima dai Ummu Nasmah ina ƙaunar ku🥰

Waɗanda suke buƙatar Complete document na Ruɗanin Zuciya biyu ƙofa a buɗe take zaku samesa akan farashi mai sauƙin 200 Naira only ku tuntuɓeni ta 08147537180.

بسم الله الرحمن الرحيم

________________________

🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼
🇦SSOCIATION🤝🏻
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

     *BOOK ONE*

PAGE 3 to 4

_________________________

✍🏻_________Shigar sa tsakar gidan ya samu sai famar dambarwa ake, tare da cacar baki, MAI KANTU ta dage sai famar lailayo ashar take tana makawa yayin da FANNA take maida mata da zagin, da yawa daga cikin mutanen gidan sun fito sunyi carko-carko suna kallon faɗan, Doctor tsayawa yayi turus yana kallon su cike da ɓacin rai, wani irin mungun kallo yake jefawa ƙanwar tasa FANNA da ta tsaya harta biye wannan Yar barikin marar mutunci Iya mai kantu, cikin tsawa yace.

” Keee!!! FANNA maza zoki bar nan ko kuma na ƙaraso na taka miki wuya a wajen, ban hanaki faɗa da JAHILAI BA oya shige daga wajen.”

Ya faɗawa FANNA Still Yana jifanta da mungun kallo bakin ta FANNA ta tura sai kuma idanunta suka ciko da hawaye cikin rau rau da ido tace.

” Yaya Umma na fa suke zagi tun ɗazu ita da KALTI YA GANA (KALTI yana nufin Umma ƙanwa ko kuma yar Mahaifin ka) shikenan yaya sai nayi shuru na barsu suna zagin Umma sai kace wanda banda Zuciya.”

Runtse idonsa kawai yayi cikin ƙunar rai da kuma tsanar family ɗin nasu, ya tsani zuwa gidan saboda, gutsiri tsome da baya karewa a cikin gidan, cikin sanyin muryar sa yace.

Shifa jaki duk yanda akayi dashi sai yaci kara sannan kuma ai shi jahili bazai taɓa yin aiki irin na masu hankali ba dan haka wannan ya daina damunki duk wanda ya zagi uwar wani uwarsa ya zaga shige mu tafi.”

Wani raɗaɗin Maganar Doctor Hassan YA GANA DA MAI KANTU suka ji, cikin takaici ta tashi ta dinga surfawa Doctor magana, wanda shi bai san ma tana yiba tuni yasa FANNA a gaba sun shige part ɗin mahaifiyar tasu.

” Ka faɗawa Uwarka YAMURAN tana can tana kwance naɗe baƙin ciki ya kusa kashe ta itace jahilar ba muba, ɗan iska marar kunya, ina matsayin ƙanwar ubanka ko kunyar kira na jahila bakayi ba, marar mutuncin banza.”

Yagana ce tace.

” Kinga fa kumfar bakin banza kikeyi Mai kantu, shifa ya shige sashin Nakassashiyar uwar tasa, dama kin rabu dasu baƙin cikin su shine zai kashe su, kinga ni kizo ma ki rakani wajen Uwar marassa Zuciyar nan Falmata akwai maganin da Aunty YANA ta bani na kai mata, ko zata samu ɗan Iskan mijin nata Hassan ɗin ya sassauta mata jeki ɗauko mayafin ki mu tafi.”

Taɓe bakin ta Mai kantu tayi, tare da cewa.

” Ni babu inda zani, Waye zai sassauta matan wannan ɗan Iskan mijin nata mai zuciyar fir’auna shine zai sassauta mata, wanda muma da muke ƙannan Ubansa bai ɗaga mana ƙafa ba bare kuma Matar sa kina gani yanzu fa ya gama faɗa min magana, ita dai Falmata ta gamu da Wahala tunda tace ita bazata rabu dashi ba, tana kuma tare da Wahala dan ubanta, idan Soyayya zata biye haka zata ƙare cikin nadama da zubda Hawaye saboda ta gamu da ɗan iskan miji, dan haka ku ƙyaleta wannan Uban Yan taurin kan tsiyar ma, Asiri ba kamasa yake ba, dan haka kuma daina wahalar da kanku a banza ni ba inda zani na wahalar da kaina da yawun baki na a banza ita ba ganin laifin mijinta take ba kina mata magana zata fara karesa tana ɓata rai ita a dole bata son ana zagin mijinta, shegiya wai ita SOYAYYA a zamanin yanzu ana daka ta soyayya ne, Soyayyar banza Soyayyar wofi yanzu ina Soyayyar take da zaki taɓa tunanin zai wulaƙanta tane, gashi yanzu wahalar take famar kwasa kullum yana gasa mata gyaɗa a hanu ita kuma marar zuciyar banza sai famar liƙe masa take kamar ruwan gam.”

” Himm!!! Kinga Aunty Yana ba yadda zatayi ba, domin kuwa ta rantse da Allah sai ta, dawo da Hassan tafin hanunsu tace shiɗin ma da yake tausayin uwar tasu, nan gaba koda kallon inda take bazaiyi ba, kinga nifa ƴar aika ne, ganan laya dai ta bani tace naje a saka masa ƙarƙashin katifar sa, kuma kinga yanzu ne dai-dai sawa baya cikin gidan kinga bari ma kiga na tafi tunda ke bazaki ba.”

Yagana ta ƙarasa Maganar tana tashi, taɓe bakin ta Mai KANTU tayi tare da cewa.

” Hmm!!! Sai kuje kuta fama da sassaƙar da babu ranar gamata su dai iyayensa kunyi nasarar ganin bayan su, amma shi kam abune mai kamar wuya domin idan juninki sammako ne, to kuwa da alama shi a hanya ya kwana, kinga tafiyata.”

Ta ƙarasa maganar tana barin wajen, Yagana kafaɗarta ta ɗaga sannan ta shige part ɗin Yana mahaifiyar Falmata.

Doctor da Sallama ya shiga ɗakin mahaifiyar tasa, AJIRAM ne ta amsa tana cewa.

” Sannu da shigowa Yaya.”

” Yauwa sannu AJIRAM Umman bacci take ne.?”

” Ehh yaya Bacci ne ya ɗauke ta, amma gaskiya yau tana fama da Matsalar Numfashi, jiya munyi magana da BELLO yake sanar dani akwai wani Dattijo mai bada magani a ƙauyen BINISHED ance yana bada magani sosai akan matsalar ciwon da aka rasa kansa, shine nace ko za’aje a gwada ko Allah zaisa a dace, tunda ciwon nata ba na asibiti bane, sannan ance yana bada taimako sosai mussaman ga mutanen da suka ɓata aka nemesu aka rasa, kaga sai mu masa zancen ɓatar Baba da Jalila ko Allah Zaisa mu dace.”

Shuru Doctor Hassan yayi yana kallon Umma dake kwance tana jan Numfashin ta da ƙyar, sosai yake jin tausayin Mahaifiyar tasa wani sa’in idan ciwon ya tashi mata kamar ciwon hauka haka zata dinga fisgar gashin kanta tana ƙoƙarin ciresa daga kanta ko kuma ta dinga ƙoƙarin zata cire kayan jikinta, wani sa’in kuma numfashin tane yake ɗaukewa, ajiyar Zuciya ya sauƙe yana duban AJIRAM yace.

” Okey zan tuntuɓi bellon naji yanda abun yake, idan har malamin Allah da Annabi ne bana shirka ba, to zamuje mu gwada, zamu kai Umma koma inane muddun zata samu lafiya, Allah ya baki lafiya Umma yasa ƙaffara ne, Allah ya yassare miki wannan ciwon Umma na.”

Ya ƙarasa maganar cike da tausayin halin da mahaifiyar tasa take ciki sannan ya jefawa AJIRAM tambaya.

” AJIRAM yaushe zaki koma gidan ki ne, dan ya kamata ki koma kar mijinki ya ga kamar mun masa rashin adalci, zan ɗauko HAJJO zata zo ta zauna da Ita kafin Allah ya bata Lafiya tunda ita tana zaune a gida babu aure mijinta ya rasu ina ga hakan zaifi ko, ni dama HAJJA MERO ta bani izini tuni da na mayar da ita gidana, to ta hana na rasa me wannan tsohuwar take nufi.?”

AJIRAM duban ɗan uwannata tayi cike da tausayin kansu tace.

” Yaya idan banyiwa Mahaifiyata jinya ba, waye zai Mata, shima idan har ya kasa min uziri akan mahaifiyata, bai min adalci ba, mu Huɗu ne kawai ƴaƴan data haifa daga Aunty Jalila sai kai saini sai kuma FANNA kai namiji bazaka iya mata jinya ba, domin ba komai bane zaka iya mata a matsayin ka na namiji, FANNA kuma tayi ƙanƙanta ga ɗaukar ɗawainiyar jinyar mahaifiyar mu, kaga dole ne a kaina, na jinyace ta, Amma babu damuwa idan har HAJJO zata yarda domin kuwa duk ɗaya muke, tunda itama hajjo Ƴace a wajen Umma, ƴar ƙanwar Umma ne, kaje ka tuntuɓeta idan ta amince sai na koma gidan nawa amma dole kullum nazo na dinga duba umma.”

Numfashi Doctor ya sauƙe yace.

” Hmmm!!! Ba damuwa insha Allah Hajjo bata da matsala zata amince, mu cigaba da addu’a Allah ya kawowa Umma sauƙi cikin gaggawa.”

” Ameeen yaya, FANNA tashi ki ɗauki tsintsiya ki share cikin gidan nan.”

Da to FANNA ta amsa sannan ta tashi ta ɗauki tsintsiya ta hau shara, Doctor Hassan tashi yayi tare da ciro kuɗi masu yawa ya bawa AJIRAM yace.

” Gashi ki riƙe a hanunki ko akwai Abunda zaku buƙata koda bana kusa, munyi magana da malam Sani ga wannan kuɗin kuma ki basa, yace zasuyi sauƙar ƙur’ani gobe suna so zasuyi yanka sai ki basa idan ya aiko, sannan ki tabbatar kin bata maganinta da zarar lokaci ya cika, Bari naje na gaishe da HAJJA daga can zan wuce Hospital insha Allah zuwa dare zanzo naga jikin nata.”

” To yaya a dawo lafiya Allah ya tsareka.”

” Ameeen AJIRAM.”

A tsakar gidan ya tsaya tare da kamo kunnen FANNA ya murɗe, ɗan ƙara ta saki sakamakon jin zafin da tayi, cemata yayi.

” Ke ba!!! Ina baki jin magana ta ko, nace ki daina biye musu kuna hayaniya baki ji ko, to daga yau na sake jin kunyi faɗa da wani cikin gidan nan, ko ranki sai ɓaci, kinji ko bakiji ba.”?

Ya mata Tambayar yana zaro mata Ido tare da sake mata kunnen, bakin ta ta tura tace.

” Naji yaya bazan sake ba.”

Ficewa yayi, FANNA ta tura baki tana cewa.

” Allah bazan ƙyale duk wanda ya zagi Umma na, ba sai dai ka kasheni yaya amma duk wanda ya zageta nima sai na zagesa ehe.”

Sashin su matar tasa ya nufa wajen kakarsu mahaifiyar Baban su, wanda take zaune sashin su matar tasa, AUNTY YANA tana zaune ita da Mairama tana tankaɗen garin tuwo, ya shigo ko Sallama babu, kansa tsaye zai shige ko inda suke bai kalla ba, ɗago kanta Aunty yana tayi ta dubesa cike da jin haushin rainin daya mata, kamar ba Uwar matar sa ba, ɗafa tayi tare da girgiza kai ta tashi tare da tare gabansa tana cewa.

” Tsaya ƙaramin marar kunya, marar mutunci”

Tsayawa Doctor Yayi ba tare daya kalleta ba, nan ma ya tsaya ne saboda ta tari gabansa, hanu ta miƙa masa tare da cewa.

” Bani Takardar sakin ƴata, mun gaji da Auren tsiya Auren da babu mutunci Auren tarkace dan haka sakar min ƴata idan kana da zuciya nacaccen banza kawai marar zuciya.”

Runtse idonsa Doctor Yayi yana jin wani irin tsanar surkar tasa yana ƙara shiga cikin zuciyarsa, gefen ta ya matsa zai raɓe ya shiga ta ƙara matsawa ta taresa tana cigaba da cewa.

” Nace ka Sakar min ƴata ko, kai wani irin marar zuciya ne kam, ka saketa, ta fara gajiya da ganin baƙin cikin ka, dan wallahi bazan tsaya na zuba ido ina kallo ka kashe min yarinya ba, Dan haka sakar min ita.”

Dariya maganar ta, taso bawa Doctor, idanunsa ya ɗago da suka sauya kala ya fara mayarwa Surkar tasa magana son ransa kamar wanda yake magana da sa’arsa, wannan shine karo na farko daya fara kiranta da sunanta darect ba tare daya lulluɓe ba.

YANA ya kamata zuwa yanzu ace kin fita a hanya ta, ki daina garajen tare min gabana domin kuwa daf nake dana tureki ki faɗi har ƙasa muddun baki fita cikin rayuwata ba, ƴarki kuma nace bazan saketa ba, sai randa ta yanki jiki ta faɗi hawan jini ya kayar da ita ko kuma ciwon zuciya ya kamata, a wannan ranar sai kizo zan baki takaddar ƴarki, sannan ina miki Albishir da cewa yanzu ma FALMATA ta fara ƙunsar baƙin ciki a cikin gida na.”

AUNTY YANA sake baki da hanci tayi tana kallon Doctor, wai yau ita HASSAN yake kallon tsabar idonta yake faɗa mata maganar da yake so, mutumin da a baya yake mata biyayya tamkar uwar da ta haifesa yau shine yake neman zaginta haushi ne yasa ta cakwami wuyan rigarsa tana cewa.

” Idan ka fasa yasar dani a ƙasa ka raina Uwarka YAMURAN kuma wallahi dole sai ka sakar min ƴata ko kaƙi Allah.”

Murmurshi yayi yana duban hanunta dake riƙe da rigarsa, zuciyarsa tana tunzurasa daya tankaɗeta kawai ta faɗi ƙasa, HAJJA dake cikin ɗakinta ne taji hayaniyar AUNTY YANA ya sata fitowa da sauri, tsayawa tayi tare da riƙe baki ta rafka salati tare da tafa hanu.

” Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un!!! Ni Mero yau kuma ina ganin wani baƙar lalacewa wai Surukace ta riƙe wuyar rigar Mijin ƴarta, Lallai Yana baki da ta ido, ta sakesa kafin na ɓata miki rai shashancin banza kawai.”

Aunty YANA ƙin sakar masa riga tayi tana jijjiga tace.

” Allah HAJJA bazan sakar masa riga ba sai ya Bani takaddar FALMATA tunda ba ƙanwar uwarsa bane sai ya Rabu da ita ai, akan me zai zauna yana wahalar min da yarinya dan ubansa shi wayee.”

Doctor leɓen bakin sa ya cije yana kallon AUNTY YANA kallo na tsana da kuma wulaƙanci, kafin ya dubi HAJJA yace.

” HAJJA idan wannan matar bata sakar min riga ba ko, to wallahi za’ayi mummunan abun kunya yau a cikin gidan nan domin kuwa zan hankaɗa matar nan hankaɗar da idan ta faɗi wallahi sai ta karye sannan ta daina zagin ubana yafi ta ita da wannan shashashan mujin nata daraja da mutunci.”

HAJJA cike da haushi da kuma fara gajiya da masifar iyalan gidan nasu ta taho tana cewa………..

Tirƙashi akwai ƙura fa cikin wannan book ɗin, tare da cakwalkwalin cakwakiya ku dai ku biyoni mu jone tare⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️

Please my fan’s Share and comments

08147537180

ALƘALAMIN RASHEEEDAT USMAN✍🏻

(Ummu Nasmah ce )
[8/27, 9:30 AM] Ummu Nasmah❤️❤️❤️❤️: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

            💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

Love and romance story

Writing by

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*

Marubuciyar nan taku ta INDO A BIRNI

Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a ko yaushe, da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.

Special Gift to

Masoyan Asali waɗanda suka kasance dani a cikin book ɗina na kuɗi wanda ya gabata wato Ruɗanin Zuciya biyu kun sayi wannan book ɗin fiye da zato na Tabbas kun nuna min ƙauna domin kuwa hakan ya gwada min kuna tare dani ako yaushe koda kuɗi ko babu nima dai Ummu Nasmah ina ƙaunar ku🥰

بسم الله الرحمن الرحيم

________________________

🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼
🇦SSOCIATION🤝🏻
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

     *BOOK ONE*

PAGE 5 to 6

_________________________

✍🏻__“Sakar masa riga, wai ke meyasa sam baki da hkr ne kam yaƙi ya Saki Falmatan nace yaƙi ya Saki Falmatan ko kuma ke ki rubuta mata sakin idan kin isa marar mutunci ɓace ki bani waje kafin na ɓata miki rai.”

HAJJA ta ƙarasa Maganar tana bige hanun Aunty yana dake cakwame da rigar Doctor, sakin rigar AUNTY Yana tayi ranta a matuƙar ɓace ta juya tayi ɗakin ta, tana kuma jin takaicin wulaƙanta mata ƴa da yakeyi, Doctor juyawa yayi da niyar ficewa ma daga sashin gabaki ɗaya domin kuwa ransa yayi matuƙar ɓaci, Muryar HAJJA yaji tana ce masa.

” Ina kuma zaka daka juya, ai duk baƙar zuciyar ta ka zaka tsaya mu gaisa dai ko dan ubanka, to maza ka dawo muje uwar ɗaka dama ina neman ka.”

Babu musu Doctor ya juyo ya dawo, har cikin ɗakin HAJJA suka shiga a bakin gadon ta Doctor ya zauna tare da gaishe ta, ta amsa tana cewa.

” Hassan na fara gajiya da wannan masifar gabar taku ta fara yawa, Abunda ya faru ya riga ya faru, meyasa kowa bazaiyi hkr ba, duk kaima zargi kake bawai kana da tabbacin abinda kake zargi a kai ba, kana gani fa mutanen unguwa har gulmar gidan nan suke, haka bai dace ba sam gidan sarauta ne fa Babban gida amma a zauna ana abu na rashin mutunci, to na fara gajiya da wannan abun kunyar da kuke jawo mana, dole ne kowa ya ajiye gabar nan, a dawo da ZUMUNCI kamar da ko kuma duk na ci ubanku, Sannan ita MATAR KA meye laifin ta, da zaka dinga mata rashin imani, nan fa ka zauna a gabana nida Marigayi Sarki Allah ya jiƙansa ka dinga kuka da mukace bazamu baka aurenta ba, duk saboda tsoron lalacewar Zumunci, Amma kuka daka tsalle kuka dire kai da ita ku lallai kuna son junanku haka muka hkr muka yarje muku akayi Auren nan, amma shine yanzu zaka dinga wulaƙanta yarinya, kaji tsoron Allah Hassan ka kasance namiji mai kyautatawa iyalin ka, ka daina wahalar da wannan yarinyar idan ƴan iska na suka juyo kanka Hassan zanci ubanka kun sanni kaf ɗinku kun san halina bawai sanyi nayi ba ido kawai nayi shuru na zuba muku to ka kiyaye ka gyara kafin na juyo kanka.”

Shuru Doctor Yayi yana sauraran HAJJA sai da ta gama maganar tukunna yace.

” HAJJA kinfi kowa sanin baƙin zaluncin da aka mana a cikin gidan nan, wannan gabar da ake yinta mu bamu da laifi dan mun ƙauracewa alaƙa tsakanin mu dasu, HAJJA ko kene a halin da muke ciki iya abinda za kiyi kenan, HAJJA sune sanadiyyar Ɓatar Babbar yarmu AUNTY JALILA, suka ƁATAR DA ABBAN MU, suka KWANTAR DA UMMAN MU, jinya duk inda muka kaita cewa ake SAMMU AKA MATA waye zaiyi mana wannan aikin idan basu ba, Saboda kawai tsananin son sarautar su ta tsiya haka kawai su tarwatsa mana farin ciki, sannan kuma ace a zauna lafiya wallahi HAJJA yanzu muka fara gaba dasu, ai tun farko na sanar dake cewa zan sake musu yarsu kikace baki yadda ba, dan haka FALMATA bazata ƙara samun farin ciki a gida na ba, dole itama sai ta ɗanɗani baƙin cikin da muma iyayen ta suka ɗanɗana mana, HAJJA bazan ɓoye miki ba, Ina son Falmata sai dai a yanzu nafi jin zafinta fiye da Soyayyar da nake mata, zuciyata bazata iya bawa Falmata farin ciki ba a yanzu Saboda ƙiyayyar da nakewa AHALIN TA yafi Soyayyar da nake mata tasiri a cikin Zuciyata Soyayyar ta ta fara fice min a raina ki gafarce ni HAJJA bazan iya dawo da farin cikin mu kamar daba a cikin gidana bazan iya ba, saboda ina ganin baƙin Falmata da Iyayen ta hajja koda kasheni zakiyi bazan taɓa sassautawa Falmata.”

Ya ƙarasa maganar idanunsa sunyi jajajur yana kuma duban action ɗin HAJJA, HAJJA ma kallon sa take cike da tausayin sa, da kuma tausayin jikarta Falmata wanda bakin fentin da babu hanunta a ciki ya shafeta, tasan har yanzu Hassan zuciyarsa tana tafasa game da rashin Ƴar Uwar sa JALILA da yayi da kuma Ɓacewar Mahaifin sa, ita kanta HAJJA har gobe cikin tashin hankalin ɓatar ɗannata take, cikin faɗa hajja tace .

” To ita FALMATA meye laifin ta da zaka sakata a cikin wannan lamarin Hassan ka dawo hankalin ka fa.?”

” Hmmm!!! HAJJA idan ita bata da laifi, Iyayen ta ai suna dashi, dan laifin iyayenta shiya shafeta, kinga HAJJA kifa daina zare min Ido kinsan dai anmin rashin adalci ko, kinga ni na tafi domin kuwa bani da lokacin zama ina ɓata yawun bakina akan waɗannan mutanen marassa imani, Kuma HAJJA ki faɗawa wannan shashashan ɗannaki Abubakar ya fita a harkata ya daina zagi na, idan ba haka ba wata rana sai na cire masa haƙorin gaba saboda babu mutunci yanzu tsakanin mu dashi bare kuma girmamawa.”

Hajja kwanon da yake gabanta ta ɗauka tare da wurgawa Hassan saurin sunkuyawa yayi kwanon ya bigi bango cewa Hajja tayi.

” Sai kazo aini ka fara zubawar haƙwaran tunda nice a gabanka, Hassan ka kiyayi duniya wallahi, komai tsiyar Abubakar dai ƙanin ubanka kuma ƙanin uba shima ubane hanu bazai goge ba haka kuma ruwa bazai wanke baa.”

” to Hajja ni dai ba ubana bane shi, Allah ya kiyaye ya zamo ubana”

ya ƙarasa maganar yana ficewa daga cikin ɗakin salati HAJJA tayi tana cewa.

” Tafiya zakayi Hassan bamu gama Maganar ba, cap lallai Zumunci ya lalace wai yau ɗan ADAMU ne yake cewa Abubakar shashasha, na shiga Uku ni Maryam, Allah ka kawo min ɗauki ya daidaita min tsakanin Zuri’a ta, Allah karka bawa sheɗan damar nasara akan su.”

Ta ƙarasa addu’ar tana rafka tagumi, shi kuwa doctor da ya fito a inda ya samu su Aunty YANA yanzu ma anan ya gansu wannan karon harda YAGANA a wajen, kansa ya ɗaga ya fice ba tare daya dubesu ba, AUNTY YANA tsaki taja bayan ficewar Doctor tace wa YAGANA tashi muje na baki saƙon, tashi Yagana tayi tabi bayan ta suka shige ɗaka YAGANA ne ta dubi Aunty YANA tace.

” Oh ikon Allah Aunty YANA dama haka ashe wannan yaron Hassan ya miki mungun raini, hmmm lallai abu ya girmama sai kace ba Surukarsa ba.”

Aunty YANA cewa tayi.

” Kedai Yagana bari kawai, kin san tunda wannan shegiyar ƴarinyar munafuka tayi Aljanu ta tona mana asiri cewa mune muka musu Sihiri, ta dinga faɗe faɗe shikenan yaron nan ya tasomu a gaba kamar zai kashe mu kuma wallahi bai isa yaga bayan mu sai dai mu muga bayan sa.”

” Hmmm!!! Aunty YANA aini yau Abunda ya miki ya bani tsoro, koda yake kina dai-dai dashi nasan zuwa kwana kaɗan ne zai dawo hanunki sai yanda kikayi dashi, ki ci ubansa iya son ranki.”

Dariyar Aunty YANA tasa tare da cewa.

” Aikuwa bazan taɓa ƙyale yaron nan ba, muddun bokaye basu kare ba a duniya, sai na sashi shida kansa ya wulaƙanta uwar tasa da yake wannan gabar a kanta, kinsan yanda ake juya masa a tanda, nan gaba kaɗan haka zamu juya Hassan a hanun mu nida ƴata Falmata, kinga YAGANA yarda dake yasa nake sanar dake sirri na, kuma kema ina sanar dake ne saboda ina da naki sirrin a tafin hanuna, yanda kina fallasa nawa zan fallasa naki, dan haka ki riƙe min nawa nima sai na riƙe miki naki, yanzu ki tashi ki tafi gidan Falmata ki kai mata wannan LAYAR kina tsaye ki tabbatar kunsa a ƙarƙashin katifar sa, idan kin min haka kin gama min komai.”

” To amma Aunty YANA ni Matsalar bata waje na, tana wajen Falmata domin kuwa cewa zatayi bazata yiba, kinsan ta da shegen Ustazancin tsiya, cewa fa take shirka muke aikatawa, sannan Aunty YANA Ina tsoron kar Falmata ta sanar dashi, kinsan halin sa zai iya zuwa har cikin gidan nan ya shuka min tsiya.”

Shuru Aunty YANA tayi tana nazarin Maganar YAGANA domin kuwa tasan halin ƴarta sarai zata aikata Abunda yafi haka indai akan Soyayyar wannan ɗan Iskan yaron ne, duban Yagana tayi tace.

” Kijeki Yagana kice mata nine na aiko ki, idan ta miki musu ki kirani a waya dan ubanta ai ƴancin ta nake nemar mata shegiya marar zuciya kamar ba nono tasha ba.”

Yagana da to ta amsa mata sannan ta tashi ta fice.

Cikin mintuna ƙalilan Yagana ta isa gidan Doctor sanda ta ƙwanƙwasa ƙofar kafin mai gadi ya leƙo ya buɗe mata kasancewar ya san daga gidan su Uban gidan nasa take, gaishe ta yayi ta amsa babu yabo babu fallasa.

Darect Part ɗin Falmata ta shige babu kowa cikin falon sai mai aikin ta, taɓe baki tayi tare da duban mai aikin tace.

” Ke!!! Ina uwar gijiyar taki take Falmata?”

Sunkuyawa Ladiyo mai aiki tayi tare da cewa.

” Ina kwana Aunty.”

Tsawa Yagana tayi mata tace.

” Keeee!!! Bana son shashancin banza, gaisuwa na tambayeki, cewa nayi ina Falmata ko kurma ce ke.?”

” Kiyi hkr Aunty, Aunty Falmatan tana ɗakin DOCTOR tun ɗazu ta shige.”

Tsuka Yagana taja tare da cewa.

” Shi Hassan ɗin yana nan ne.?”

” A’a baya nan tun safe daya fice bai dawo ba.”

Yagana bata sake cewa komai ba ta wuce bedroom ɗin Doctor Hassan, tana kwance idanunta biyu tayi shuru alamun tana cikin matsanancin damuwa sai bushashshen hawaye dake kwance gefen fuskar ta, tunanin da ta shiga baisa tasan da zuwan Yagana ba, harta zauna sai da ta taɓa ta tukunna, tayi firgit git ta farka cikin tsoro duk a tunaninta, DOCTOR ne ya dawo, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da dafe kanta tace.

” Aunty Yagana, yaushe kika shigo.”

Bakinta Yagana ta taɓe tare da cewa.

” Ina zaki ji shigowata tunda kin saka kanki a cikin duniyar tunani kina neman kashe kanki akan namiji guda ɗaya tal wanda ina da tabbacin a yau kika bar gidan sa zaki samun wanda ya fisa komai, kin zauna kina neman sawa kanki Hawan jini a banza akan wanda bai damu dake ba.”

Gyara ɗaurin ɗankwalinta tayi Falmata cikin sanyin halinta tace.

“Ina son mijina Aunty Yagana bazan iya rabuwa dashi ba, kuma duk abinda yake min bana ganin laifin sa, domin kuwa iyayena sun cutar dashi da yawa, Aunty Yagana na rasa me zanyi na daidaita lamari na da mijina wlh ina sonsa amma shi ya tsaneni yanzu kwatakwata bashi da lokaci na ko kallo na baya son yi.”

Tsuka Yagana taja tare da cewa.

” Ai kuwa tafe nake da yadda zaki gyara zamantakewar ki da Shi romio ɗin naki uwar marassa zuciya.”

Gyara zaman ta Falmata tayi tare da matsowa kusa da Yagana tace.

” Aunty me zanyi Doctor ya daina Wulaƙanta ni.”?

Layar Yagana ta ciro tare da nuna mata tace.

” Da wannan zaki dawo da hankalin mijinki kanki .”

Falmata cike da jin haushi take duban Yagana tace.

” Aunty Yagana laya ce fa wannan.”

Yagana cewa tayi ” eh laya ce itace maganin matsalar ki, da zarar kin saka masa a ƙarƙashin wannan katifar tasa yana kwanciya magana ta ƙare sai yanda kikayi dashi, Aunty YANA ce ta karɓo ta jiya a wajen malamin ta.”

Tunda Yagana ta fara Maganar Falmata ta zuba mata ido sai da takai aya sannan Falmata tace .

” Bana buƙatar maganin matsalata daga wajen boka, ba tun yau na fara faɗa muku haka ba, a wajen Ubangiji nake neman maganin matsalata kuma insha Allah zai kawo min ƙarshen ta, Aunty Yagana na rasa me yasa kuka nacewa mushirikin Mutum keda Mama gaskiya bazan iya cutar da mijina ba, ki mayarwa mama layarta kice mata bana buƙata ta tayani kawai da addu’a Allah ya kawo min ƙarshen matsalata.”

Yagana cikin jin haushin Falmata tace.

” Abinda yasa kike shan wahala kenan wannan tsoron Allahn naki, ke ga wacce kika fi kowa tsoron Allah ai kuwa kina nan kina shan wahala, an faɗa miki kowa kika gansa yana zaune a gidan sa lafiya da mijinsa to ba haka ya zauna ba, sai da ya haɗa da malami, bari na kira Aunty YANA na sanar da ita kince bazaki karɓa kiyi amfani dashi ba idan yaso sai ki mata musun ita “

” Aunty Yagana, dan Allah ba sai kin kira Mama ba, ni fa bazanyi Amfani da wannan layar ba koda na karɓa jefar da ita zanyi, kinga time dawowar DOCTOR yayi yanzu haka nayi imanin ya na hanya ki tashi ki tafi kar yazo ya sameki rai ya ɓaci kinsan halinsa.”

Falmata ta faɗawa Yagana hakane kawai dan ta samu ta tafi badan Hassan zai dawo ba domin kuwa dawowarsa babu lokaci sai sanda yaga dama.

Taɓe bakinta Yagana tayi tare da miƙewa ta zari jakarta tana cewa.

” Bani kuɗin nafef ke kika sani da wahalar ki jiki magayi ai.”

Falmata ɗago kanta tayi tace.

” Wallahi bani da ko sisi Aunty kiyi haƙuri dan Allah.”

” Kuɗin nafef da zaki bani ma baki dashi, hmmm!!! Cap Lallai akwai matsala, to sai anjuma.”

Ficewa tayi tana sababi ita dai Falmata jingunuwa tayi da jikin bed ɗin tana jinjinawa rashin tsoron Allah na mahaifiyarta ayi mutum baida tawakalli da yarda da ƙaddara shi boka ne kawai zai yi masa maganin Damuwar sa, tsuka Falmata taja tare da tashi, tollet ɗin DOCTOR ta shiga ta wanke tas sannan ta fito ta gyara masa shimfiɗar gadon nasa, ɗakin ma mopping ɗin sa tayi sannan ta fito falo, Ladiyo ƴar aikin ta ta samu zaune ta zubawa tv Ido tana kallon tashar Mbc Bollywood inda suke series mai taken ZAUJIZ ZAUJEN da alamu kallon yana mata daɗi, zama itama Falmata tayi tare da sakin murmushi Falmata a Kwaita da son mutane sam bata nuna ƙyama ko banbanci tsakanin ta da Ladiyo tamkar ƙanwar ta haka ta ɗauki Ladiyo Falmata cewa tayi.

” Ladiyo har kin gama aikin kenan kin zauna kallo, kedai kina son wannan series ɗin.”

Murmushi itama Ladiyo tayi tare da cewa.

” Ai Aunty tun dazu shigar Aunty Yagana na gama aikina, kuma Aunty ai series ɗin yana da ƙyau fa sosai saboda akwai soyayya.”

Dariya Falmata tayi tace.

” Ikon Allah Ladiyo sarkin son Soyayya, to Allah ya kawo miki miji na gari wanda zaku sha soyayya, yauwa idan kin gama kallon zan aikeki Monday market ki sayo min ganyen alayyaho, yau gwate zamu sha cikin gidan nan.”

Da to Ladiyo ta amsa sannan suka mayar da hankalinsu ga tv sai dai ita Falmata sam tunanin ta yana kan matsalarta ne idanunta ne kawai suke kan tv, ajiyar zuciya ta sauƙe tana jinjinawa girman matsalar dake gabanta, haka ta kasance cikin wannan yanayin.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Shi kuwa Doctor bayan ya fito daga cikin gidan nasu Darect Asibitin sa ya wuce dake unguwar Gwange Sabon Layi Babban privat Hospital ne wanda akayi rubutu da manyan baƙaƙe a makeken get ɗin AJIRAM MALA SPECIAL HOSPITAL shigewa ciki yayi, parking yayi a gefe kafin ya fito cikin izza da isa ya nufi cikin Hospital ɗin, nurse gaishe sa suke yana ɗaga musu hanu harya ƙarasa ciki, office doctor Saif zai wuce, sai ya jiyo wani sauti mai kamar hayaniya a woman word, har zai shige sai kuma ya fasa ya nufi word ɗin jin hayaniyar tayi yawa, koda ya shiga turus ya tsaya yana kallon ikon Allah, domin kuwa wata ƙaramar yarinya ce ta gagari kusan nurse Biyar, sai famar magana yarinyar take da ganinta kaga cikakkiyar ƴar ƘAUYE ko da yanda kake jin tsantsar zallar ruwan Barbarci a bakinta babu mis ko kaɗan da Hausa haka kuma yanayin jikinta ya nuna daga ƙauye ta fito duk da babu wata ƙazanta a jikinta.

” Na rantse da Allah babu wanda ya isa a cikin ku ya min allura azzaluman banza kawai baku da aiki sai cin zalin Mutane kunsa farin kaya kamar wasu Gawawwaki sai famar allure mutane kuke saboda zalunci to wallahi nikam uwar kuturu ma tayi kaɗan ballan tana ta makaho babu ubanda ya isa ya min allura a cikin ina ji ina gani da idanuna.”

Haushi da takaici ne ya cika wani tsohu dake zaune gefe da sandar sa a hanu cikin jin haushi yace.

” Ke dai AI’SA kin shiga Uku da wannan shegen bakin naki da baya mutuwa, baki da lafiyar ma bakin ki bai mutu ba, to ko kiyiwa mutane shuru ko na tashi naci ubanki da wannan sandar kin dai san halina yau naga tsiya a wajen yarinya, na kawo ki domin na sama miki lafiya shine xaki zo nan ɗin ma ki sai da mana da hali kina min iya shege to baki isa ba dole sai anyi wannan allurar ko zaki mutu.”

Nurse ɗin gabaki ɗayan su sun jiƙe da zufa tsabar uwar kokuwar da suke da yarinyar da aka kira AI’SA ita kuwa bakinta yaƙi mutuwa wannan dattijon yana dasa aya ta ɗaura da mayar masa da martani.

” Ni dai wallahi BA’KURA ban shiga Uku ba tunda ban mutu ba nida bakina ina ruwan ka dani, Ni nace ka kawo ni wajen waɗannan azzaluman ina cewa kawai kayi magani zaka saya min a cikin garin mu koma, to wallahi Allah ko zaka kasheni bazanyi wannan allurar ba, yanzu fisabilillah shikenan sai na tsaya ina kallo a soke ni da wannan kifiyar wallahi bazan yadda ba babu ruwan ka da ciwo na ka ƙyaleni idan mutuwa ma zanyi na mutu, ai dai ba nice ƴarka ba, ya’yan ka sunan kana kallon su ni sai kaga dama kamin addu’a, eheee.”

Ta ƙarasa maganar tana murguɗa masa baki DOCTOR dake tsaye ya harɗe hanu yana kallon dramar ce ya sashi murmushi mai sauti, ” Lallai wannan yarinyar ba dai daru ba, sai famar magana take tsau-tsau bakinta ko gajiya bayayi” cikin zuciyarsa yake wannan zancen ƙarasawa yayi ya taka har cikin word ɗin tare da cewa nurse ɗin dake riƙe da AI’SA ɗin.

” Ku saketa wannan ai ta fiku lafiya ma, yanda ta gagare ku.”

Sakinta sukayi Nurse Khadija tana cewa.

” DOCTOR wallahi bata da lafiya koda sukazo sanda aka musu gwajin maleria da typort kuma duk tana dasu a jikinta yanzun ma allurar typort ɗin zamu mata shine duk taƙi sakin jikinta sai famar dambe take damu.”

Carap AI’SA tayi tace.

” Kaji masharranta, meye kuma materia, to aniyar ku ta biku babu ƙatuwar matar da ta isa ta min wannan allurar komai girman ta koda kuwa ta kai bishiyar kuka girma ba………..”

Tsawa DOCTOR HASSAN ya daka mata tare da cewa.

” Shut’up, karna ƙara jin maganar ki cikin word ɗin nan, shegen Surutu cau-cau ko gajiya bakya yi” kallon BA’KURA DOCTOR yayi tare da cewa.

” Baba Amma dai wannan yarinyar tana da matsalar aljanu ko, ko kuma ta taɓa samun matsalar ƙwaƙwalwa ne, naga kamar babu saiti a kanta.”

” Likita Babu aljanu a jikinta ko taɓin ƙwaƙwalwa, kawai tsabar sheɗanci ne da kuma rashin kunya ya mata yawa, yanzu haka da kaji tana wannan bakin wallahi a hakan ma bata da lafiya ne da abinda zatayi sai yafi haka.”

Ajiyar zuciya DOCTOR HASSAN ya sauƙe, ita kuwa sai famar murguɗa masa baki take, ficewa ma tayi daga word tana harare harare tare da riƙe ƙugu, DOCTOR HASSAN duban Khadija yayi yace

” Ki rubuta musu magani kawai ki bar allurar.”

Yana faɗa musu haka ya fice abinsa, Khadija maganin ta rubuta ta bawa BA’KURA tace yaje ya duba chemist ya saya karɓa yayi tare da basu hkrn abinda AI’SA ta musu sannan ya fito, dube dube ya fara babu AI’SA a wajen sandar sa ya dogara, ya fito daga cikin asibitin a waje ya same ta zaune a bakin wani dakali sai famar kalle-kalle take, sandar sa ya ɗaga ya kwaɗa mata a bayanta, a razane ta tashi tare da rarumar dutse ta juyo a fusace zata zabgawa BA’KURA, Allah ya rufa asiri sukayi ido huɗu dashi ta sauƙe hanunta ƙasa tana huci.

” Wallahi Allah ya rufa maka asiri BA’KURA ban rufe idona wallahi da yanzu na lotsa maka kai, to wai ma me na maka da zaka ci zalina yanzu idan ban yafe maka ba fa ka mutu mai zaka cewa Ubangijin ka, ni dai Allah idan baka daina duka na da wannan sandar ba wata rana nice ajalinta sandar nan sai dai kuma ka sake nemo wanda zaka ɗingisa wannan gurguwar ƙafar taka dashi…………….”

Dariya BA’KURA yayi tare da ƙofa kawai suka shige cikin wani madaidaicin Chemist ya miƙa musu katin maganin suka basa kuɗin suka faɗa masa 2k ya cire ya basu sannan ya sakata a gaba suka wuce ƙauyen su………

08147537180

ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻

(Ummu Nasmah ce)
[8/27, 9:31 AM] Ummu Nasmah❤️❤️❤️❤️: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

            💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

Na

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*

Marubuciyar nan taku ta INDO A BIRNI

Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a duk inda kuke so da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.

Waɗanda suka ce Document ɗin Ruɗanin Zuciya biyu suke so, to ga dama ta samu na gama na kuma haɗa Complete document idan kina so zaki samesa a 200 Naira only 08147537180.

بسم الله الرحمن الرحيم

________________________

🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼
🇦SSOCIATION🤝🏻
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

   *Book One*

Page 7 to 8
________________________

ƘAUYEN BINISHED

__✍🏻 Motar da suka hau tafiyar 40 minute ne ya kaisu mashigar ƙauyen nasu, a bakin ƙauyen aka sauƙe su, sannan suka kama hanyar shiga cikin ƙauyen, ƙauye ne sosai wanda bashi da yawan mutane, jejin Allah, idan kinga gidan kara ɗaya kafin ki sake ganin wani gidan sai kinyi tafiyar minti 15 mutane ɗaɗɗaya zaki dinga haɗuwa dasu, da haka har suka ƙarasa nasu gidan AI’SA da gudu ta ƙarasa cikin gidan sai kuma ta fashe da kuka tana ƙwalawa KAKA kira.

KAKA KAKA KAKA !!!!”

Kaka dake zaune cikin bukkar ta ta jiyo kiran jikar tata, amsawa ta hau yi itama tana washe jajayen haƙwaranta da ta rinasu da gwarango.

” Lale maraba da dawowa ƴar albarka yarinyar kirki shigo gani a cikin bukkata zoki sanar dani wani shegen ne ya saki kuka, yanzu na tashi muje naci ubansa.”

Ƙarasowa cikin bukkar tayi tana kukan munafurci ta zauna ta hau shure-shure da ƙafa tana cewa.

KAKA KAKA KAKA!!!!!”

Matsowa Kaka tayi kusa da AI’SA ta dafa mata kafaɗa tana cewa.

AI’SA wai ko dai kin makance ne da kika je cikin garin nan gani ina kallon ki kina kallo na amma tsabar shashanci kita ƙwala min kira yuwa wata makahuwa me aka miki a cikin garin.”?

Kuka AI’SA ta fara tana mutstsike idon ta na karya tare da gyara zama ta fara shiryo ƙarya.

” Kaka an cuceni a cikin garin nan da mukaje, BA’KURA shima ya cuceni, kaka kinsan me yacewa wani koɗaɗɗen likita, suka dinga zagina wai cewa fa suke waini nake da shafar aljanu wai mahaukaciya ce ni Allah kaka idona idon wannan koɗaɗɗen likitan sai na shuka masa tsiya wallahi, sai ya gane Ruwa ba sa’an kwando bane, kuma kaka tsabar mungunta irin ta BA’KURA ba cewa yayi zamuje ya saimin nagani ba, to wallahi kaka ƙarya ya miki, mungunta yamin ya kaini su min allura.”

Salati kaka ta tafka tana tafa hanu tace.

” Haka BA’KURA zaimin, na ɗauki amanar ki na basa amma tsabar tsiya yace Ke ɗin ce mai shafar aljanu, to ƙarya suke kinfi ƙarfin aljanu, domin kuwa kina da Ni, ni ɗin nan da kike gani na san manya manyan aljanu guda bakwai, kuma yanzun nan zan baki addu’ar su, aljani ko wuta suka hura kibi ta ciki ki wuce, kuma shima BA’KURA zai san ya ci amanata, kinga AI’SA buɗe kunnenki na baki addu’ar aljanu karma bakin su ya kamaki kinsan wani mutum bakin sa guba ne.”

Tura baki AI’SA tayi tace.

” Kaka akwai wata addu’a ne bayan wanda Baba ya bani ta surorin baƙara da Falaƙi da nasi.”

Kaka cewa tayi

” Ke dallah wannan addu’ar da zan baki itace tafi komai korar aljanu su aljanun sune suka bani addu’ar da kansu, ke kinsan waye ni kuwa to bari kiji addu’ar, SHUKURAJU MANGA GINNI, SHURƁANJO MANGA GINNI, MAHALFINI GA ALLAH GA SURATUL WALIYIL GINNI.” kinga wannan addu’ar dana baki sahihiyace sunan manya manyan aljanu ne idan kika yita to karkiji tsoron aljanu na faɗa miki ko wuta suka hura shige ta ciki ki wuce sanyi ƙalau zakiji babu zafi.”

Fanta ƴar AI’SA dake kwance kan gadon kaka tana jin duk abinda suke faɗi ne, ta saka dariya dama dariyar cinta take tun sanda aka fara addu’ar cikin dariyar Fanta tace.

” 🤣lallai kuwa zaki ƙone ƙurmus babu mai ciro ki, yau naji wata addu’a a wajen kaka to waima ke kaka a ina kika gamu da aljanun har suka baki addu’ar😄”

Ta ƙarasa maganar cikin dariyar domin kuwa sosai kaka yau ta bata dariya ” su SHUKURAJU MANGA GINNI manya manyan Aljanu😄 cikin zuciyarta ta yi maganar, AI’SA kuwa kallon kaka tayi ta kalli Fanta tare da dakawa fanta harara cikin rashin kunya tace.

” To ke kuma uwar gulma da saka ido waye ya saki cikin zancen mu da kakata, to wai kina nufin Kakan ƙarya ta miki, kuji ƴar shishshigin tsiya dai”

Zaro ido Fanta tayi ganin lokaci guda Ai’sa tana neman tada mata da fitina a wajen kaka to ma idan banda raini Ai’sa ce zata ce mata shegen shishshigin tsiya Fanta za tayi magana Kaka ta rigata da cewa.

” Barni da ja’ira Ai’sa to dan ubanki buɗe kunnenki kiji inda muka haɗu da MANGA GINNI ya bani wannan addu’ar”

Taɓe baki Fanta tayi tare da jefawa Ai’sa mungun kallo, kaka labari ta fara basu.

” A kwai wani lokaci munje jeji da Ba’na muna tsaka da tafiya cikin jejin nan kawai sai naji an kira sunana ance.

” Ke YA KWALO zoki karɓi goro, kinsan dana juya kawai sai nagan su aljanun sai bikin suna suke yanda muke bikin sunan mu suma fa haka suke nasu harda maroƙa da makiɗa , na cewa Ba’na bakaji ana kirana bane sai cemin Ba’na yayi Ke Ya KWALO ki kiyayi kanki me zakije kiyi a wajen Aljanu, nace ni sai naje yana tsaye na ƙara wajen su, suka bani goro mai yawa sannan MANGA GINNI ya bani wannan addu’ar, kinji inda na samu munafuka uwar gulma, ni nayi zaton ma bacci kike ashe shuru kikayi kina mana gulma.”

Tashi Fanta tayi tana dariya har tana riƙe ciki ta fice da ga ɗakin Kaka, domin kuwa wannan ba addu’a bace surkullen kaka ne kawai da kuma gigin tsufa daya fara cimmata, Tsuka Ai’sa taja tare da cewa.

” Kaka kina kallon tana miki dariya, tana fa nuna alamun ƙarya fa kenan kike mata, hmmm bazaki tashi ki bita har wajen Maman ba ki hukunta ta shine kika zauna kina kallon ta, duk zuciyarkin nan kaka wannan fa raini ta miki.”

Ai kuwa kamar wanda ta tunzura kaka ta miƙe tare da sandarta tana cewa.

” Ai kuwa gaskiyar ki ne Ai’sa tashi muje, naje har wajen Ferebuwayen naji idan itace ta sata ta dinga mai da min da zance.”

Tsalle Ai’sa ta saka tare da tashi tabi bayan Kaka, Fanta suna zaune da ita da Mama da kuma wansu Kacalla, sai dariya suke fanta tana basu labarin addu’ar kaka, basu ankara ba sai ji sukayi kaka tana cewa.

” Umhum ƴar Albarka Kinji zancen ki ya dawo ko AI’SA ashe da gaske Uwar taku ce take sawa a rainani a cikin gidan nan to dake wato Ferebuwaye Ni kika raina ko to bani kika Raina ba, uwarki AI’SA Wanda kika laƙabawa wannan yarinyar sunanta ita kika Raina bani ba, sandarta ta ɗaga ta kwaɗawa Kacalla a kansa tana cewa, kaikuma munafukin Allah kana namiji kana shiga cikin mata gulma to tashi kabar wajen.”

Kacalla idonsa ya ɗaga yana yiwa Ai’sa alamun zan riƙeki, kafin yace wa kaka.

” Ban tashi ba kizo ki ɗagani idan kina da ƙarfi kuma kinga wannan sandar da kika kwaɗa min akan wannan tujajjiyar mai kama da bulugari zan rama na lahira sai ya fita jin daɗi ga ta nan babbar munafuka tana biye dake kina kiran wani munafuki kaji tsohuwa da jaraba haka kawai kizo ki samu a gaba akan wannan shashsheƙar ta sakoki gaba.”

Mama doge bakin Kacalla tayi tana cewa.

” Karna ƙara jin bakin ka tashi ka fice Kaltin abokiyar wasan kane (dake haka take kiran kaka dashi), ɗauki abincin marar lafiyar da aka kawo ka kai musu kafin mahaifinku ya dawo daga gona.”

Tashi Kacalla yayi yana hararar kaka ya ɗauki abincin ita kuwa kaka ƙwafa tayi sanda yazo fita da gangan ya jide ƙafar AI’SA ji kake gum ta faɗi ƙasa, dariya Kacalla yasa tare da saurin shigewa yana cewa.

” Gobe ki sake munafurci ina dai-dai dake.”

Kaka salati tasa tana cewa.

” Ferebuwaye kina kallon baƙar muguntar da Kacalla ya yiwa wannan yarinyar ko, kina kallo ko, bari uban nasu ya dawo zai shiga tsakaninki da waɗannan baƙaƙen mugayen tashi kinji.”

Tana callara kuka ta tashi tare da riƙe kanta da ta bige, tana tsalle.

” Na rantse da Allah bazan yadda ba sai na rama wallahi bazan yadda ba, da gudu ta juya zata bi Kacalla Mama ta daka mata tsawa.”

Dawo nan karki yadda ki bisa wallahi idan kuma kika bisa bayan ya dako ki nima ƙara miki zanyi, tunda baki da mutunci baki da kunya, ba yayanki bane da………..”

Kaka ce ta dakatar da Mama tana cewa.

” To ya isheki haka zaginta, sai ku daketa tunda jaka ce ita, to naga ɗan iskan da zai daketa a wannan gidan Ferebuwaye ki kiyaye ni Allah zan iya sawa BA’GAJI ya sakeki kibar gidan nan akan wannan yarinyar muddun baki fita harkarta ba.”

Hanun AI’SA taja suka bar wajen tana sababi.

Mama dai shuru tayi bata kula Kaka ba amma cikin zuciyarta tana jin takaicin yanda ta lalata AI’SA yarinya duk ta zama marar kunya babu wanda ya isa ya mata faɗa daga ni har ubanta bamu isa da ita ba ya Allah ka shirya min AI’SA.

Mama tayi Maganar tana ƙwafa tare da cigaba da iza wuta, Fanta ma tashi tayi bata ce komai ta ɗauki garin tuwo ta fito waje ta fara tankaɗe itama tana jinjinawa Rashin Kunyar AI’SA.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨

CIKIN MAIDUGURI

DOCTOR shine bai dawo cikin gidan sa ba sai misalin goma na dare, lokaci ne ya ƙure masa a Hospital ko gidan nasu bai samu ya koma ya duba jikin Umman sa ba, tsap ya sami falon sai tashin ƙamshi yake ita kuwa Falmata tana zaune ɗaya daga cikin kujerun falon tasha kwalliya cikin wandon jean three cutter da kuma wata ƙaramar best wanda tasha mata jiki, gashin kanta kuwa ta ƙullesa da Ribon ko ɗan kwalo bata sa ba sosai tayi kyau, Ganinta cikin falon yasa DOCTOR ya fasa yin sallamar da yayi niya, kansa ya ɗauke tamkar bai ganta ba ya wuce Bedroom ɗinsa, wani irin tuƙuƙun baƙin ciki Falmata taji a cikin ranta duk wannan kwalliyar tayi ne ko zata samu ta burgesa amma ko arzikin kallo bata samu ba a wajensa wannan wacce irin ƙiyayya ne haka, wani irin girman laifi na masa haka “anya kuwa iya ƙiyayyar iyayena ne yasa DOCTOR yake gwada min wannan tsanar ko dai na masa wani laifi ne mai girma wanda ni ban sani ba, Allah gani gareka kana kallon halin da nake ciki Allah ka sauƙaƙa min wannan baƙin cikin dake damun Zuciyata” duk cikin zuciyarta take wannan zancen, hawaye ne ya gangaro mata daga idanunta hanu tasa ta goge tare da jingina kanta jikin kujerar ta rufe idanunta tana jin ƙirjinta yana mata ƙuna.

Shi kuwa DOCTOR wayar sa ya ajiye da kay ɗin sa a bedsite drower sannan ya hau cire kayan jikinsa towel ya ɗauka ya ɗaura a ƙugunsa sannan ya shige tollet wanka yayi, bayan ya fito daga wankan ne ya tsane ruwan jikinsa da ƙaramin towel body spray kawai ya fesawa jikinsa sannan ya ɗauki wasu blue ɗin sleeping dress ɗinsa na maza ya sanya a jikinsa, wayoyinsa ya ɗauka ya fito falo, darect daining table ta nufa, Falmata dake zaune har yanzu a inda ya barta ne ta zaro idanunta ganin DOCTOR ya nufi daining domin kuwa ko a mafarki bata taɓa tsammanin zai ci abincin gidan ba, saboda ya juma baya cin abincin ta, gashi ƙwate tayi ɗan kaɗan bata dafa dashi Bama, “yau kuma na shiga Uku ta furta a zuciyarta” cike take fal da tsoro, shi kuwa zama yayi a daining ɗin kawai ba tare daya ce mata komai ba, danne danne kawai ya hauyi da wayarsa cike da tsoro Falmata ta tashi ta nufe sa tsayawa tayi tare da cewa.

” Kayi hkr DOCTOR banyi tunanin……..”

Tsuka mai ƙarfi yaja tare da ɗaga mata hanu.

” Please leave me alone, ki daina shiga rayuwata fa, wai dole ne sai kin haɗa rayuwarki da tawa, ko dole ne sai kin min Magana Mtsss!!! Duk sanda Allah ya haɗa ka rayuwa da Maye ka shiga Uku ni kuma tawa jarrabawar kenan Auren irin tsiya, mema zai hana ba za kiyi maita ba, kinsha nonon Yana mtsss!!!.”

Ya ƙarasa maganar cikin tsaki, yana maida idanunsa kan wayarsa, Falmata wani irin raɗaɗi taji yanda DOCTOR yake zage mata iyayen ta babu ko kunyar idanunta, idan ba kunnenta ne suka jiye mata ƙarya ba kamar ma kiran sunan mamanta yayi babu ko sayawa, bata so magana amma dole sai tayi koda kuwa kasheta DOCTOR zaiyi.

” Kana kirana da mayya banajin zafin sa sosai, amma sai dai yau da ka danganta maitar da Mahaifiyata sai naji yamin ciwo sosai a cikin Raina, Doctor Sunan mahaifiyata ka kira fa baka saya ba, karka manta da komai lalacewar iyaye ɗansu yana sonsu, bai kamata ka ciwa iyayena mutunci a gabana ba, tunda ko ba komai surukan ka ne, baka kyautatawa zuciyata ba, DOCTOR.”

Ta ƙarasa Maganar cike da rauni hawaye na zuba daga idanunta, tunda ta fara Maganar doctor yake sauraron ta ba tare daya dakatar da ita ba, sai da takai ƙarshe tukunna kafin ya ɗago ya kalleta yana sakin murmushin gefen baki kafin yace.

” Hmmm!!!! Ai daman zafin shi nakeso kiji, Idan na kira sunan mahaifiyarki sunan mahaifiyata na kira, ko kuma ni ta haifeni ne, ƙarya nayi ba YANA ake kiranta dashi ba, ko dan bakiji na kira asalin sunan nata ba, YAHANASU, komai lalacewar iyaye tabbas ƴaƴan su suna sonsu amma ba irin lalacewar iyayenki ba na rashin albarka, tir da iyaye irin naki, sannan tunda naci mutuncin iyayenki ai sai kimin hukunci, bana ɗaukar iyayenki a matsayin surukai na, ina ɗaukar sune a matsayin wanda aka zalunta da wanda yayi zaluncin ma’ana dai ina ɗaukar su ne a matsayin azzalumai maha’inta waɗanda bazasu gama da duniya lafiya ba Mtsss.”

Ya Kawo ƙarshen maganar tare da buga table ɗin dake gabansa ya miƙe ya bar Falmata tsaye cikin tashin hankali da munguwar damuwa, bakinta nauyi ya mata ta kasa magana jin mugayen kalaman da DOCTOR yake faɗa mata, kuka ta saki tare da shigewa Bedroom ɗin ta da gudu ta faɗa saman bed ɗin ta tana sakin kuka mai cin zuciya, sosai take kukan tana Allah wadarai da halin iyayenta da suka ja mata tsana idan har sun aikata abinda DOCTOR yake zarginsu dashi me zatayi ta dawo da DOCTOR hayyacin sa domin ta fara zargin cewa DOCTOR baya cikin tunanin sa, anya kuwa wannan abubuwan da suke faruwa basu sashi ya fita daga hayyacin sa ba kuwa…………………..”?

Vote.
Share.
And comment.

08147537180

ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻

(UMMU NASMAH CE)
[8/28, 5:34 PM] Ummu Nasmah❤️❤️❤️❤️: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

            💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

❤️ Love and romantic and funny story ❤️

Na

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*

Marubuciyar nan taku ta INDO A BIRNI

Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a duk inda kuke so da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.

Waɗanda suka ce Document ɗin Ruɗanin Zuciya biyu suke so, to ga dama ta samu na gama na kuma haɗa Complete document idan kina so zaki samesa a 200 Naira only 08147537180.

بسم الله الرحمن الرحيم

________________________

🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼
🇦SSOCIATION🤝🏻
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

     *Book One*

Page 9 to 10

________________________

_✍🏻sosai Falmata take sambatu cikin kuka daren ranar Falmata baccin ta kaɗan ne, washe gari da ciwon kai ta tashi mai zafin gaske koda wanka ma daƙyar ta iya yinsa ta dawo ta kwanta shuru tayi tana tunanin rayuwarta ta baya har yanzu hawaye bai daina gudu a fuskar ta ba, ina ma ana tariyo Rayuwar baya tabbas da ta tariyo tata ko zataji sauƙin damuwar ta.

Shi kuwa DOCTOR ƙarfe tara ya fito daga Bedroom ɗinsa cikin shirin sa na fita aiki, breakfast ya gani jere saman table da alamu dai Ladiyo ce tayi, daining table ɗin ya nufa domin kuwa yunwa yake ji sosai jiya babu abinda yasa a bakin sa, plast ya jawo ya haɗa tea mai kauri bread ya ɗauka tare da ƙwai, ya fara ci a hankali, sanda ya gama sannan ya goge bakin sa da tissue jakarsa ya ɗauka sannan ya fice ba tare daya duba Falmata ko lafiya ba kasancewar bai ganta ba kuma ya saba kullum ta saba shigowa ta gaishe sa koda kuwa bazai amsa ba, ita kuwa tana kwance taji tashin motar sa alamun ya fita wasu hawayen ne suka ƙara sauƙa mata masu ɗumin gaske, wato ko mutuwa tayi sai dai idan ta ruɓe aji warin ta DOCTOR bazai shigo ya duba halin da take ciki ba.

Cikin wannan yanayin ta kasance, har kusan ƙarfe 12 na rana tana nan kwance cikin Bedroom ɗin ta bata fito ba Ladiyo ce ta shigo Bedroom ɗin da Sallama, amsa mata Falmata tayi muryar ta adashe kasancewar kukan da tasha, ƙarasowa Ladiyo tayi ta gaishe ta tare da cewa.

” Aunty Lafiya tun safe baki fito falo ba.”

Murmushin da yafi kuka ciwo Falmata tayi tace wa Ladiyo.

” Kaina ke ciwo Ladiyo”

” Ayya sannu Aunty Allah ya baki lafiya dama baƙuwa kikayi Ƙawarki Aunty MAJI shine nace fa nazo na sanar dake.”

” Kice mata ta ƙaraso.”

Tashi Ladiyo tayi taje ta sanar da Maji, maji ƙarasawa tayi cikin Bedroom ɗin Falmata, a bakin bed ɗin ta zauna tana ƙarewa ƙawar tata kallo tace.

” Falmata lafiyar ki kuwa kinga yanda kika rame kikayi duhu, idanunki duk sun zurma, Zaki kashe kanki Falmata akan ɗa namiji da bashi da tabbas, ki dawo hankalin ki ki cire damuwar DOCTOR a ranki idan ba haka ba zaki sawa kanki cuta kin daina zuwa makaranta anyi lectures da yawa babu ke gashi har ana daf da fara test abinda ya kawo ni kenan na sanar dake gobe ki shiryawa zuwa school idan ba haka wallahi za kiyi rippit.”

Tashi Falmata tayi ta zauna tare da goge hawayen dake bin fuskar ta tace

” Maji damuwa ai ta zama dole a gareni babu ta yanda zan iya gogeta a zuciyata muddun ba farin ciki na bane ya dawo, nida banza ɗaya nake a wajen DOCTOR baya son koda gani nane Maji, ban san mena masa ba, shi yana ɗaukar laifin iyayena ne yana ɗaurawa a kaina, Ban taɓa jin inda aka ɗaura laifin wani a kan wani ba sai DOCTOR, wallahi maji bana jin daɗin zaman gidan nan duk yanda naso na fahimtar da DOCTOR mu samu masalaha yaƙi fahimta Maji ba dole damuwa ta dameni ba, shiyasa komai na duniya naji ya fita a Raina, makarantar ma naji bana son zuwa saboda koda naje babu abinda zan gane, sai da nutsuwa ake gane karatu Maji, ni kuma bani da nutsuwa.”

Shuru Maji tayi tana jin tausayin ƙawar tata, hanu Maji tasa ta gogewa Falmata hawayen ta .

” Hakane ƙawata tabbas akwai ciwo ace mijinka ya juya maka baya, ni lamarin mijinki yana bani mamaki wai duk Soyayyar da yake miki kamar zai haɗiye ki yanzu babu ita ta juye ta koma tsana, kai gaskiya DOCTOR baya ƙyautawa ko kaɗan, amma ƙawata ki cigaba da hkr insha komai yayi zafi zaiyi sauƙi babu abinda bazai wuce ba sai ikon Allah, ki cigaba da masa biyayya kamar da karki fasa, koda yana hantarar ki, bautar Ubangijin ki kike yi, sannan abinda nake so dake ki rage yawan damuwa karki sawa kanki hawan jini, sannan ki koma makaranta shima zai ɗebe miki kewar wata damuwar domin yafi zaman da kike ke kaɗai a gida, insha Allah farin cikin ki zai dawo kuma nima zan tayaki da addu’a .”

” Hakane Maji na gode insha Allah gobe zanzo school, Ya Mama.”

” Mama lafiyar ta ƙalau tace ma na gaishe ki.”

” Ina amsawa.”

” Kawata da alamu dai bakici komai ba tun safe Ko naga kamar kinyi yanayi da mai jin yunwa.?”

Ajiyar Zuciya Falmata ta sauƙe tace.

” Wallahi kaina ke ciwo ban fita falon bama tun safe ina nan kwance wanka kawai nayi.”

” To ai kuwa ya kamata ki tashi muje kici abinci sai kisha magani idan yaso ki dawo ki kwanta nasan baza’a rasa magani ba a gidan likita.”

” Akwai a Bedroom ɗin sa.”

To tashi muje ki ɗauko kizo kisha koda ruwan tea ne sai ki kwanta nima ba jumawa daman zanyi ba, zan shige shagon saloon ne zan wanke kaina “

Tashi Falmata tayi tana cewa.

” Nayi zaton fa wuni zaki min har ina murna, kice kuma tafiya zakiyi gaskiya ban so haka ba.”

” Kinga Hajiya tashi muje kisha magani ina kallonki kafin na tafi.”

Murmushi Falmata tayi tana tashi tare da cewa.

” To Mama Maji muje.”

Dariya Maji tayi sannan ta tashi suka fito falon tare, Falmata Bedroom ɗin DOCTOR ta shige ɗauko magani ita kuma maji ta shige daining table ta haɗawa Falmata tea, Falmata na zuwa maji ta miƙo mata tea ɗin tana cewa.

” Gashi karɓi kisha.”

Karɓa Falmata tayi tana kallon Maji cike da ƙauna, domin kuwa ƙawarta ce tun na yarinta tare suka girma komai tare suke yi, Babu wanda yake son yaga ɗaya daga cikin su yana cikin damuwa, suna ɗaukar damuwar ɗaya daga cikin su damuwar su duka, Falmata tea ɗin tasha haɗe da maganin sannan ne maji tace.

” To Allah ya baki lafiya ni zan tafi sai mun haɗu gobe a school dan Allah ki rage yawan damuwa da tunani saboda kare lafiyar ki.”

Murmushi Falmata ta saki tare da cewa.

” Ameen insha Allah zanyi ƙoƙari wajen ganin na kiyaye, ki gaishe da Mama.”

” Za taji” Maji tace tare da ficewa, Falmata ma Bedroom ɗinta ta shige ta kwanta, bata juma da kwanciyar ba bacci ya ɗauke ta.

Zaune yake a office ɗin nasa, bayan ya ɗan samu nutsuwa na duba patient ne ya ɗaga wayar sa, My dear sister na gani a rubuce, jikin screen ɗin wayar ringing ɗaya AJIRAM ta ɗaga.

” AJIRAM ya jikin Umman dai, yau ban samu na shigo ba, na fito a ƙurarren lokacine gashi kuma ina da wanda zan duba a wannan lokacin ya jikin nata.”

Daga can AJIRAM tace.

” Eh to da sauƙin musulunci amma yau tun safe bige-bige take tun ɗazu hankali na yake tashe, gashi ni ɗaya ce Fanna bata nan.”

Cikin tashin hankali DOCTOR yace.

” Subabanallah yau kuma bige-bigen ne ya tashi, yanzu ya kenan ko nazo ne.”

” A’a ba sai kazo ba da sauƙi domin da na mata hayaƙin maganin nan bacci ya ɗebeta.”

Ajiyar zuciya DOCTOR ya sauƙe tare da furta.

” Alhamdulillah, ina zuwa da yamma naga jikin nata ki kula da ita sosai idan kinga abinda bazaki iya ba kiyi kirana.”

” Shikenan to sai kazo.”

Kashe kiran DOCTOR yayi, yana jawo wata farar takadda gabansa, Nocking ɗin ƙofa yaji anyi.

” Yes come.”

Buɗe ƙofar Maji tayi ta shigo da Sallama, murmushi DOCTOR yayi ya amsa sallamar tare da cewa.

” Yau babbar baƙuwa ce kenan nake da ita.”

Dariya Maji tayi tana zama tace.

” Ga dai ƙaramar baƙuwa, Ya aikin.”

” Aiki Alhamdulillah amma ba daɗi, kwana biyu kin ɓuya bana ganinki ko a online ne.”

Murmushi Maji tayi tace.

” Dama aini ba gwanar hawa online bane, amm DOCTOR wajen ka fa nazo Allah yasa na samu lokacin kasancewar nazo maka lokacin da bai dace ba lokacin aiki.”

Murmushi DOCTOR yayi yace mata.

” Aikuwa kin iya zuwa a Sa’a domin kuwa yanzu ina Free ne aikin yayi sauƙi.”

” To Alhamdulillah haka nake so, amm DOCTOR nazo ne game da Case ɗinku da Falmata, a gaskiya DOCTOR baka kyautawa Falmata domin kuwa kana zaluntar ta da yawa kaga kuwa yanda Falmata tayi baƙi ta rame ta fita hayyacin ta, sai kace ba Falmata ba, wai dan Allah DOCTOR na tambayeka ashe dama laifin wani yana shafar wani? Taya dan iyayenka sun haifeka sai ace halinku ɗaya ko ka manta da cewa nacacce yana fitowa a cikin rayayye haka kuma rayayye yana fitowa a cikin macacce, idan har mukace zamu dinga hukunta yara da laifin iyayensu, to wallahi mu jira sakamakon Ubangiji, dan Allah ka gyara zamantakewar ka da matarka, domin kuwa Allah ya baka mace ta gari wacce ko wani namiji yake neman irinta domin kuwa irinsu wuya suke yanzu bako wace mace bace take iya juran wulaƙanci daga ɗa namiji, dan koni nan bazan iya jura ba, dan Allah DOCTOR karka bari Falmata ciwo ya shigeta bata cancanci wulaƙanci daga gareka ba.”

Shuru doctor yayi yana sauraron Maganar Maji, sanda ta gama kafin ya kalleta yana sakin murmushi yace.

” Gaskiya Maji son kanki yayi yawa wato nine ma na zalunce ta, ba su bane suka zalunce mu, hmmm !! Baki san yara suna gado halin iyayensu ba kenan, to ki sani yau yaro yana gadon halin iyayensa, kinga Maji Nifa bazan iya kyautatawa Falmata domin kuwa idan na kyautata mata dole iyayenta zasuji daɗi ni kuma Bana buƙatar jin daɗin su, nafi buƙatar na gansu cikin ƙasƙanci da tashin hankali tabbas macacce yana fitowa daga cikin rayayye haka kuma rayayye yana fitowa daga cikin macacce, wannan faɗin Ubangiji ne, amma ana gadon hali, bazan miki karya ba Maji bazan iya dawo da farin ciki na da Falmata ba kiyi haƙuri kawai lokaci kawai nake jira da zan bata takaddar sakinta kowa ya kama gabansa.”

Maji wani irin haushin DOCTOR taji danne ɓacin ranta tayi tace.

” Saki fa kace DOCTOR, to ina soyayyar da kace kana mata a baya ina wannan soyayyar da kuke yiwa juna tamkar ɗaya zai haɗiye ɗaya, ina take, DOCTOR baka da tabbacin cewa iyayen Falmata sune suka ɓatar da Baba da Aunty Jalila Zargi kawai kake yi, baka da tabbas, DOCTOR na zo nan ne na faɗa maka gaskiya ka dawo hayyacin ka kafin lokaci ya ƙure maka Falmata tana maka biyayya tana kuma shanye wulaƙancin da kake mata kabar ganin tana sonka , wallahi duk sanda ka cikawa Falmata ciki DOCTOR zata bushe maka ta daina jin tsoron ka, kazo kuma kana neman tanƙwarata ta kasa tanƙwaruwa, kashi ma yazo ya fika daraja a gareta, ka dawo hankalin ka kasan me kakeyi kafin lokaci ya ƙure maka bana so kazo kana danasani.”

Dariya DOCTOR yayi yana ƙarewa Maji kallon baki da hankali kafin yace.

” Kinsan Hausawa sukace so tsuntsu ne yakan tashi daga wannan reshen ya koma wata, to haka nima babu soyayyar Falmata a cikin zuciyata, bazan taɓa danasani ba danna rabu da Falmata irin tsiya.”

” Duka ai irin naku ɗaya ne da ita domin kuwa jini ɗaya ne yake yawo a jikinku, idan irin tsiya ne ita kaga kuwa ai irin kune, idan har haka soyayya take da juyawa masoyinta baya to tabbas soyayya hatsari ne, DOCTOR ka sani cewa idan ka ci amanar Falmata Allah ba……….”

Dakatar da Maji DOCTOR yayi yace.

” Ya isa haka Maji ina ganin mutuncin ki bana son mukawo matakin da zan gaya miki maganar da bata dace ba, mubar maganar haka idan ita kaɗaice ta kawo ki, kina iya tafiya.”

” DOCTOR korata kake daga office ɗin ka saboda na faɗa maka gaskiya.”

” Saboda kin faɗa min son ranki dai, ba gaskiya ba.”

” Okay to na gode sai anjuma Allah ya baka hakuri idan har a cikin maganganu na akwai masu zafi.”

Ta ƙarasa maganar tana nufar hanyar fita DOCTOR dakatar da ita yayi yana zaro kudi daga aljihun sa dubu biyar ya ƙirgo yace.

” Ga wannan kiyi kuɗin adaidaita, Ib baya nan ya fita dana basa kay ya mayar dake.”

” Na gode bana buƙatar kuɗin ka, ina da na nafef, ka riƙesu zasu maka amfani.”

” Haushi na kikaji da bazaki karɓi kyautar dana baki ba.”

Murmushi Maji tayi tace.

” Akan me zanji haushin ka?”

” Akan kina zargina da zaluntar ƙawarki.”

” Wannan ba zargi bane abinda yake a zahiri ne.”

Tana faɗin haka ta fice da sauri, DOCTOR SAIF da zai shigo office ɗinne suka ci karo da Maji, ko kallon sa batayi ba ta shige, shi kuwa kallon mamaki ya bita dashi a ransa ya furta lafiya, yarinyar da duk inda ta ganni sai ta gaishe ni munyi wasa da dariya kafin a rabu, shigewa office ɗin yayi da Sallama ya zauna yana cewa.

” Me yake faruwa.?”

Ɗago kansa DOCTOR yayi a taƙaice yace.

” Meka gani.”?

DOCTOR Saif amsa ya basa da cewa.

” Abinda idona ya gani, kai Malam meya sami Maji naga ta fita daga office ɗin nan cikin ɓacin rai.”

” Baka tambayeta daka ganta.”

Tsuka DOCTOR Saif yaja tare da cewa.

” Bana son rainin hankali malam ya ina tambayar ka kana ƙoƙarin mai dani shashasha……………..”

08147537180

Kuyi hkr yau ban samu nayi Editing ba, sannan ku sani cikin adduar ku zan shiga axam.

Vote
Share
And comment

ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻

(UMMU NASMAH CE)
[8/29, 8:59 PM] Ummu Nasmah❤️❤️❤️❤️: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

            💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

❤️ Love and romantic and funny story ❤️

Na

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*

Marubuciyar nan taku ta INDO A BIRNI

Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a duk inda kuke so da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.

Waɗanda suka ce Document ɗin Ruɗanin Zuciya biyu suke so, to ga dama ta samu na gama na kuma haɗa Complete document idan kina so zaki samesa a 200 Naira only 08147537180.

Bari nayi rawa da girgiza son so nake muku my FAN’S gaskiya naji daɗin yanda kuka amshi wannan book ɗin hanu biyu, ko wani group na shiga ruwan sharhi nake gani gaskiya naji daɗi sosai😘😘😘😘

بسم الله الرحمن الرحيم

________________________

🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼
🇦SSOCIATION🤝🏻
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

     *Book One*

Page 11 to 12

________________________

_✍🏻 Murmushi DOCTOR ya saki yana kallon DOCTOR SAIF kafin yace.

” Kaima dai kasan tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, wai tazo min da wata banzar magana ne akan wannan yarinyar Falmata, wai nine nake zaluntar Falmata kai kaji wata banzar magana da son kai irin na Maji.”

Taɓe bakin sa DOCTOR SAIF yayi yana hararar DOCTOR yace.

” Sai ka mata rashin mutunci ko nasan amsar bazata wuce haka ba.”

” To akan me zan mata rashin mutunci meta min, amsa kawai na bata daidai da Maganar ta.”

” Hmm!!! Haba DOCTOR halinka ne ban sani ba wannan maganar kuma ai wanda bai sanka bane zaka faɗawa, shakka babu ka mata rashin mutunci, Kuma koda bansan abinda tazo maka dashi ba, nasan gaskiya ta faɗa maka tabbas kana zaluntar matar ka DOCTOR, kuma Falmata bai kamata ta samu wannan mungun sakamakon a wajen ka ba ka mata yayi ace kana riritata kamar ƙwai, ka sani Falmata fa ta soka a lokacin da baka da komai, sisin da zaka kashe, baka dashi sai an baka, a wannan lokacin idan baka manta ba samari ne masu kuɗin gaske suke zuwa wajen ta, amma taƙi su tace lallai kai take so, duk da a lokacin kakan nunku basa son Auren zumunci saboda gurɓacewar zumunta, haka Falmata ta dage sai da aka muku Auren, sanda gomnati ta ɗauki nauyin karatun mu haka yarinyar nan tayi haƙuri tana kallo ka tafi India ta jiraka a ɗakin mahaifiyar ta har tsawon shekaru bakwai ka gama karatun DOCTOR ɗin ka, ka dawo kayi sati ɗaya rak ka koma sakamakon aikin da suka ɗauke ka acan, nan ma kayi shekara biyu sannan ne ka dawo ka ɗauke ta kuka koma tare kafin daga baya ku dawo gida Nigeria, yanzu DOCTOR wannan matar data yimaka wannan soyayyar itace abar wulaƙantawa a wajen ka, ya kamata kafin ka yanke mata hukunci ka dinga tunanin baya, wallahi kaji tsoron Allah, ka daina azabtar da baiwar Allah.”

DOCTOR ɗago kansa yayi yana duban DOCTOR SAIF yace.

” Gori kake min kenan, to naji tamin halacci sai kuma akace su cuceni ko, to ban riritata kamar ƙwai ɗin ba, kaga DOCTOR SAIF dan Allah tashi ka tafi office ɗin ka, kaima idan wannan maganar zaka min na gode.”

” Gaskiya ne ai baka so, shiyasa zaka koreni, Allah ya shirya ka, amm jiya ka iso kuma na fita bamu haɗu ba, Ib ya sanar dani cewa wai a mayar da matar nan opression room.”

” Eh nine nace a maida ta saboda ya sanar dani cewa, sun bata ruwa tasha wai har cikin nata ya kumbura.”

” Kai Ib ma dai wani lokacin shashasha ne, bafa tasha ruwan ba, sun dai ɗauko zasu bata sai Allah yasa na shigo na hana su bata, kuma matar tana da tunbi ne shiyasa ina ga zaiga kamar cikin ya kumbura.”

DOCTOR cewa yayi.

” Ehh ya faɗa min jiyan dana zo, harma naje na duba ta DOCTOR SAIF bari na gudu ina son zanje na dubo jikin Umma.”

Tashi DOCTOR SAIF yayi tare da cewa.

” Okay nima bari na shige office ɗina.”

Tare suka fito DOCTOR SAIF ya wuce shima DOCTOR ya shige parking space ya ɗauki motar sa ya fice daga Asibitin ya shige family Hause ɗin nasu, kamar ko yaushe ƙofar gidan cike yake da mutane musamman dattawa, shi kuwa SARKIN yana zaune a tsakiyar su, taɓe bakin sa DOCTOR yayi ya ƙaraso wajen tare da sunkuyawa suka gaisa da dattawan ɗaya bayan ɗaya, sai dai Sarki ko YALLAƁOI zance bai samu kallon mutunci a wajen DOCTOR ba bare kuma gaisuwa, haka shima bai kulasa ba gudun ya tsinkasa a cikin talakawan sa, yau dai tsakar gidan babu taron gulma domin kuwa babu kowa sai yara dake famar wasansu, sashin su ya wuce da Sallama ya shiga, Hajjo dake tsaye bakin randa tana ɗibar ruwa ne ta amsa masa da.

” Ameen wa’alaikumussalam , ɗan halak kaƙi ambato, yanzu nake tambayar BULAMA kai yake cemin shima yanzu yake tambayar BELLO kai.”

” Kice kamar yadda nima nake neman ki kenan, Ina kuka haɗu da Bello shima nemansa nake.”

” Yana cikin ɗakin ka ƙarasa bari na kaiwa AJIRAM ruwa bayi, ina zuwa.”

Shigewa DOCTOR yayi cikin ɗakin Umman, bata nan da alamu sun Kaita tollet ne wanka, zama yayi gefen katifa tare da miƙawa Bello hanu yana cewa.

” Bawan Allah jiya na kiraka shine baka ɗaga ba kuma baka biyo kira na ba.”

Dariya Bello yayi tare da cewa.

” Bana kusa ka kira nazo kuma zanbi kiran taƙi shiga, ya aikin.”

” Aiki Alhamdulillah, jiya AJIRAM take sanar dani cewa kunyi magana akan wani mai magani da yake ƙauyen BINISHED ko.”

” Eh tabbas munyi magana, kuma gaskiya ana samun dace sosai a wajen sa, dan akwai wani mutum a bayan layin mu, shima shigen irin ciwon Umma ne, wallahi da aka kaisa can ya warke sosai.”

” To amma Bello ina dai ba ɗan tsubbu bane dan gaskiya bana son muje wajen boka.”

Dariya Bello yayi yace

” A’a wallahi ba ɗan tsubbu bane malami ne na gargajiya sannan kuma ruƙiyya, babu tsubbu a tattare dashi.”

Numfashi DOCTOR ya sauƙe tare da cewa.

” Okay ba damuwa insha Allah zamuje, kamar Ranar asabar tunda ranar ce weekend, to amma waye zai mana jagora kasan dai ni ban taɓa shiga cikin wannan ƙauyen ba.”

Bello cewa yayi.

” Zamuje tare nasan ƙauyen Saboda tare mukaje dasu, kuma malamin ya sanni sosai, wannan ba matsala fatan dai Allah yasa mu dace.”

” Ameen ma je Asabar ɗin, Ina BULAMA ne kam kwana biyu bana ganin sa.”

” Ai kuwa yanzu kikayi saɓani, dan bai juma da fita daga gidan nan ba ka shigo.”

” Okay.” Doctor ya furta a taƙaice, AJIRAM da Hajjo ne suka shigo riƙe da Umma sun mata wanka kwantar da ita sukayi, DOCTOR duban mahaifiyar tasa yayi da idanunta suke buɗe kamar zaka mata magana ta amsa sai dai ina babu baki, hanunta ya riƙe tare da cewa

” Sannu Umma Allah ya baki lafiya.”

Duban Hajjo yayi yace.

” Hajjo alfarma nake nema a wajen ki, ina son zaki dawo ki karɓi AJIRAM jinyar Umma, ita ta koma gidan mijinta ta kula da yaranta, tunda kinga ke kina zaune a gida ba aure.”

Murmushi Hajjo tayi tace.

” Haba Hassan har sai ka nemi alfarma a wajena dan kawai na yiwa Umma jinya nima fa uwata ce Umma babu abinda bata minba a rayuwata, dan haka babu komai AJIRAM ta koma gidan ta, ni zanyiwa Umma jinya.”

Ajiyar zuciya DOCTOR ya sauƙe cike da jin daɗi yace.

” Hakane na gode Hajjo, to ke Kuma AJIRAM, gobe zaki koma gidan ki, idan Hajjo ta ɗauko kayan ta, sannan ranar Asabar zamuje wajen mai maganin da Hajjo zamu tafi karki ce zaki zo ki zauna a gidan mijinki idan yaso daga baya sai kije ki dubata.”

Nisawa AJIRAM Tayi tace.

” Shikenan yaya Allah ya kaimu goben.”

Da ameen ya amsa, Hajja ce ta shigo da Sallama, amsawa sukayi DOCTOR ya ɗaga ido ya kalleta yana sakin murmushi, Hajja kusa da DOCTOR ta zauna tana sakin masa dundu a baya tace.

” Ja’iri jiya da ka gudun yanzu bamu haɗu bane.”

Dariya DOCTOR yayi tare da cewa.

” Kinga Malama Hajja, ni bana son yawan Magana karki dameni.”

Dariya Hajja tayi tana duban Umma tace.

” Sannu Yamuram kina fama da bautar Ubangiji, Allah ya baki lafiya Allah ya sa zakkar jiki ne” kallon DOCTOR Tayi tace.

” Hassan yanzu babu inda za’a kai Yamuram haka za’a barta a gida, nifa gaskiya bana jin daɗin zaman ta haka ba tare da annemi wani me magani an Kaita ba , duk da kuna karɓowa amma dai ya kamata a ƙara dagewa.”

DOCTOR cewa yayi.

” Hajja yanzu ma maganar da muka gama kenan munji labarin wani mai magani a ƙauyen BINISHED zamuje can Ranar asabar zamu kaita.”

” Yauwa to Alhamdulillah hakan yafi ai”

Hajjo ce tace.

” Sannu Hajja ina kwana.”

Murmushi Hajja tayi tace.

” Hajjo lafiya lau ya uwar taki Merama”

” Lafiyan ta lau tana gaishe kuma.”

” Muna ansawa da kyau,”

AJIRAM ma gaida Hajja tayi tana cewa.

” Ina zuwa haka Hajja naga kinsha sari, unguwa ne.”?

” Gidan wannan ja’irin wannan wannaki zanje na dubo Falmata, kwana biyu shuru babu labarin ta, tashi ma mu tafi ka sauƙeni.”

Hajja ta ƙarasa maganar tana jan kunnen DOCTOR, doctor bai kalli Hajja ba yace.

” Da banzo ba kuma waye zai kaiki.?”

Dariya Hajja tayi tace.

” Kuɗina ne zasu kaini.”

DOCTOR cewa yayi.

” Yanzu ma kuwa sai kuɗin naki su kaiki domin kuwa ni ba gida na nufa ba asibiti zan koma.”

Hajja cewa tayi.

” Baka isa ba wallahi dole sai ka kaini idan yaso ka juya asibitin.”

Juyowa yayi ya fuskanci Hajja yana ƙare mata kallo yace.

” Zaro min idanun da kike ne zaisa naji tsoron ki na kaiki, ke dai malama bini a hankali kawai na kaiki.”

Tare suka saka dariya Hajja tace

” To naji angon Hajja, ka dai san bama faɗa ko, tashi mu tafi uban masu gida.”

Dariya DOCTOR yasa tare da miƙewa yana cewa AJIRAM.

” Ina FANNA taje ne ban ganta ba.?”

AJIRAM cewa tayi.

” Na aiketa gida na, amma ina ga tama kusa dawowa.”

Okay ya amsa yana cewa Bello.

” Sai Asabar ɗin ka shirya zan kiraka, Hajja muje na sauƙe ki na wuce.”

Tashi Hajja tayi suka fice mota DOCTOR ya buɗe mata ta shiga sannan shima ya zaga ya shiga yaja motar suka tafi.

DOCTOR hom ya danna a ƙofar gidan mai gadin ya fito da sauri ya buɗe get ɗin, a compaunt ɗin gidan DOCTOR ya tsaya tare da buɗewa Hajja yace.

” To Bismillah fita ni juyawa zanyi.”

” Kai!!! Wai dama da gaske asibitin zaka koma.”

Dariya DOCTOR yayi yace.

” Au dama kinyi zaton wasa nake miki, asibiti zan koma ban gama aikina ba yaushe zaki koma na turo azo a ɗaukeki.”

” To Allah ya tsare a dawo lafiya, eh to ina ga zuwa ƙarfe biyar.”

Ta ƙarasa maganar tana fita da Allah ya kaimu DOCTOR ya amsa sannan ya juya ita kuma Hajja ta shige cikin gidan……….

Vote
Share
And Comment

ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻

(Ummu Nasmah ce)
[8/30, 7:26 PM] Ummu Nasmah❤️❤️❤️❤️: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

            💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

❤️ Love and romantic and funny story ❤️

Na

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*

Marubuciyar nan taku ta INDO A BIRNI

Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a duk inda kuke so da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.

Waɗanda suka ce Document ɗin Ruɗanin Zuciya biyu suke so, to ga dama ta samu na gama na kuma haɗa Complete document idan kina so zaki samesa a 200 Naira only 08147537180.

Bari nayi rawa da girgiza son so nake muku my FAN’S gaskiya naji daɗin yanda kuka amshi wannan book ɗin hanu biyu, ko wani group na shiga ruwan sharhi nake gani gaskiya naji daɗi sosai😘😘😘😘

بسم الله الرحمن الرحيم

________________________

🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼
🇦SSOCIATION🤝🏻
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

     *Book One*

Page 11 to 12

________________________

_✍🏻 Murmushi DOCTOR ya saki yana kallon DOCTOR SAIF kafin yace.

” Kaima dai kasan tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi, wai tazo min da wata banzar magana ne akan wannan yarinyar Falmata, wai nine nake zaluntar Falmata kai kaji wata banzar magana da son kai irin na Maji.”

Taɓe bakin sa DOCTOR SAIF yayi yana hararar DOCTOR yace.

” Sai ka mata rashin mutunci ko nasan amsar bazata wuce haka ba.”

” To akan me zan mata rashin mutunci meta min, amsa kawai na bata daidai da Maganar ta.”

” Hmm!!! Haba DOCTOR halinka ne ban sani ba wannan maganar kuma ai wanda bai sanka bane zaka faɗawa, shakka babu ka mata rashin mutunci, Kuma koda bansan abinda tazo maka dashi ba, nasan gaskiya ta faɗa maka tabbas kana zaluntar matar ka DOCTOR, kuma Falmata bai kamata ta samu wannan mungun sakamakon a wajen ka ba ka mata yayi ace kana riritata kamar ƙwai, ka sani Falmata fa ta soka a lokacin da baka da komai, sisin da zaka kashe, baka dashi sai an baka, a wannan lokacin idan baka manta ba samari ne masu kuɗin gaske suke zuwa wajen ta, amma taƙi su tace lallai kai take so, duk da a lokacin kakan nunku basa son Auren zumunci saboda gurɓacewar zumunta, haka Falmata ta dage sai da aka muku Auren, sanda gomnati ta ɗauki nauyin karatun mu haka yarinyar nan tayi haƙuri tana kallo ka tafi India ta jiraka a ɗakin mahaifiyar ta har tsawon shekaru bakwai ka gama karatun DOCTOR ɗin ka, ka dawo kayi sati ɗaya rak ka koma sakamakon aikin da suka ɗauke ka acan, nan ma kayi shekara biyu sannan ne ka dawo ka ɗauke ta kuka koma tare kafin daga baya ku dawo gida Nigeria, yanzu DOCTOR wannan matar data yimaka wannan soyayyar itace abar wulaƙantawa a wajen ka, ya kamata kafin ka yanke mata hukunci ka dinga tunanin baya, wallahi kaji tsoron Allah, ka daina azabtar da baiwar Allah.”

DOCTOR ɗago kansa yayi yana duban DOCTOR SAIF yace.

” Gori kake min kenan, to naji tamin halacci sai kuma akace su cuceni ko, to ban riritata kamar ƙwai ɗin ba, kaga DOCTOR SAIF dan Allah tashi ka tafi office ɗin ka, kaima idan wannan maganar zaka min na gode.”

” Gaskiya ne ai baka so, shiyasa zaka koreni, Allah ya shirya ka, amm jiya ka iso kuma na fita bamu haɗu ba, Ib ya sanar dani cewa wai a mayar da matar nan opression room.”

” Eh nine nace a maida ta saboda ya sanar dani cewa, sun bata ruwa tasha wai har cikin nata ya kumbura.”

” Kai Ib ma dai wani lokacin shashasha ne, bafa tasha ruwan ba, sun dai ɗauko zasu bata sai Allah yasa na shigo na hana su bata, kuma matar tana da tunbi ne shiyasa ina ga zaiga kamar cikin ya kumbura.”

DOCTOR cewa yayi.

” Ehh ya faɗa min jiyan dana zo, harma naje na duba ta DOCTOR SAIF bari na gudu ina son zanje na dubo jikin Umma.”

Tashi DOCTOR SAIF yayi tare da cewa.

” Okay nima bari na shige office ɗina.”

Tare suka fito DOCTOR SAIF ya wuce shima DOCTOR ya shige parking space ya ɗauki motar sa ya fice daga Asibitin ya shige family Hause ɗin nasu, kamar ko yaushe ƙofar gidan cike yake da mutane musamman dattawa, shi kuwa SARKIN yana zaune a tsakiyar su, taɓe bakin sa DOCTOR yayi ya ƙaraso wajen tare da sunkuyawa suka gaisa da dattawan ɗaya bayan ɗaya, sai dai Sarki ko YALLAƁOI zance bai samu kallon mutunci a wajen DOCTOR ba bare kuma gaisuwa, haka shima bai kulasa ba gudun ya tsinkasa a cikin talakawan sa, yau dai tsakar gidan babu taron gulma domin kuwa babu kowa sai yara dake famar wasansu, sashin su ya wuce da Sallama ya shiga, Hajjo dake tsaye bakin randa tana ɗibar ruwa ne ta amsa masa da.

” Ameen wa’alaikumussalam , ɗan halak kaƙi ambato, yanzu nake tambayar BULAMA kai yake cemin shima yanzu yake tambayar BELLO kai.”

” Kice kamar yadda nima nake neman ki kenan, Ina kuka haɗu da Bello shima nemansa nake.”

” Yana cikin ɗakin ka ƙarasa bari na kaiwa AJIRAM ruwa bayi, ina zuwa.”

Shigewa DOCTOR yayi cikin ɗakin Umman, bata nan da alamu sun Kaita tollet ne wanka, zama yayi gefen katifa tare da miƙawa Bello hanu yana cewa.

” Bawan Allah jiya na kiraka shine baka ɗaga ba kuma baka biyo kira na ba.”

Dariya Bello yayi tare da cewa.

” Bana kusa ka kira nazo kuma zanbi kiran taƙi shiga, ya aikin.”

” Aiki Alhamdulillah, jiya AJIRAM take sanar dani cewa kunyi magana akan wani mai magani da yake ƙauyen BINISHED ko.”

” Eh tabbas munyi magana, kuma gaskiya ana samun dace sosai a wajen sa, dan akwai wani mutum a bayan layin mu, shima shigen irin ciwon Umma ne, wallahi da aka kaisa can ya warke sosai.”

” To amma Bello ina dai ba ɗan tsubbu bane dan gaskiya bana son muje wajen boka.”

Dariya Bello yayi yace

” A’a wallahi ba ɗan tsubbu bane malami ne na gargajiya sannan kuma ruƙiyya, babu tsubbu a tattare dashi.”

Numfashi DOCTOR ya sauƙe tare da cewa.

” Okay ba damuwa insha Allah zamuje, kamar Ranar asabar tunda ranar ce weekend, to amma waye zai mana jagora kasan dai ni ban taɓa shiga cikin wannan ƙauyen ba.”

Bello cewa yayi.

” Zamuje tare nasan ƙauyen Saboda tare mukaje dasu, kuma malamin ya sanni sosai, wannan ba matsala fatan dai Allah yasa mu dace.”

” Ameen ma je Asabar ɗin, Ina BULAMA ne kam kwana biyu bana ganin sa.”

” Ai kuwa yanzu kikayi saɓani, dan bai juma da fita daga gidan nan ba ka shigo.”

” Okay.” Doctor ya furta a taƙaice, AJIRAM da Hajjo ne suka shigo riƙe da Umma sun mata wanka kwantar da ita sukayi, DOCTOR duban mahaifiyar tasa yayi da idanunta suke buɗe kamar zaka mata magana ta amsa sai dai ina babu baki, hanunta ya riƙe tare da cewa

” Sannu Umma Allah ya baki lafiya.”

Duban Hajjo yayi yace.

” Hajjo alfarma nake nema a wajen ki, ina son zaki dawo ki karɓi AJIRAM jinyar Umma, ita ta koma gidan mijinta ta kula da yaranta, tunda kinga ke kina zaune a gida ba aure.”

Murmushi Hajjo tayi tace.

” Haba Hassan har sai ka nemi alfarma a wajena dan kawai na yiwa Umma jinya nima fa uwata ce Umma babu abinda bata minba a rayuwata, dan haka babu komai AJIRAM ta koma gidan ta, ni zanyiwa Umma jinya.”

Ajiyar zuciya DOCTOR ya sauƙe cike da jin daɗi yace.

” Hakane na gode Hajjo, to ke Kuma AJIRAM, gobe zaki koma gidan ki, idan Hajjo ta ɗauko kayan ta, sannan ranar Asabar zamuje wajen mai maganin da Hajjo zamu tafi karki ce zaki zo ki zauna a gidan mijinki idan yaso daga baya sai kije ki dubata.”

Nisawa AJIRAM Tayi tace.

” Shikenan yaya Allah ya kaimu goben.”

Da ameen ya amsa, Hajja ce ta shigo da Sallama, amsawa sukayi DOCTOR ya ɗaga ido ya kalleta yana sakin murmushi, Hajja kusa da DOCTOR ta zauna tana sakin masa dundu a baya tace.

” Ja’iri jiya da ka gudun yanzu bamu haɗu bane.”

Dariya DOCTOR yayi tare da cewa.

” Kinga Malama Hajja, ni bana son yawan Magana karki dameni.”

Dariya Hajja tayi tana duban Umma tace.

” Sannu Yamuram kina fama da bautar Ubangiji, Allah ya baki lafiya Allah ya sa zakkar jiki ne” kallon DOCTOR Tayi tace.

” Hassan yanzu babu inda za’a kai Yamuram haka za’a barta a gida, nifa gaskiya bana jin daɗin zaman ta haka ba tare da annemi wani me magani an Kaita ba , duk da kuna karɓowa amma dai ya kamata a ƙara dagewa.”

DOCTOR cewa yayi.

” Hajja yanzu ma maganar da muka gama kenan munji labarin wani mai magani a ƙauyen BINISHED zamuje can Ranar asabar zamu kaita.”

” Yauwa to Alhamdulillah hakan yafi ai”

Hajjo ce tace.

” Sannu Hajja ina kwana.”

Murmushi Hajja tayi tace.

” Hajjo lafiya lau ya uwar taki Merama”

” Lafiyan ta lau tana gaishe kuma.”

” Muna ansawa da kyau,”

AJIRAM ma gaida Hajja tayi tana cewa.

” Ina zuwa haka Hajja naga kinsha sari, unguwa ne.”?

” Gidan wannan ja’irin wannan wannaki zanje na dubo Falmata, kwana biyu shuru babu labarin ta, tashi ma mu tafi ka sauƙeni.”

Hajja ta ƙarasa maganar tana jan kunnen DOCTOR, doctor bai kalli Hajja ba yace.

” Da banzo ba kuma waye zai kaiki.?”

Dariya Hajja tayi tace.

” Kuɗina ne zasu kaini.”

DOCTOR cewa yayi.

” Yanzu ma kuwa sai kuɗin naki su kaiki domin kuwa ni ba gida na nufa ba asibiti zan koma.”

Hajja cewa tayi.

” Baka isa ba wallahi dole sai ka kaini idan yaso ka juya asibitin.”

Juyowa yayi ya fuskanci Hajja yana ƙare mata kallo yace.

” Zaro min idanun da kike ne zaisa naji tsoron ki na kaiki, ke dai malama bini a hankali kawai na kaiki.”

Tare suka saka dariya Hajja tace

” To naji angon Hajja, ka dai san bama faɗa ko, tashi mu tafi uban masu gida.”

Dariya DOCTOR yasa tare da miƙewa yana cewa AJIRAM.

” Ina FANNA taje ne ban ganta ba.?”

AJIRAM cewa tayi.

” Na aiketa gida na, amma ina ga tama kusa dawowa.”

Okay ya amsa yana cewa Bello.

” Sai Asabar ɗin ka shirya zan kiraka, Hajja muje na sauƙe ki na wuce.”

Tashi Hajja tayi suka fice mota DOCTOR ya buɗe mata ta shiga sannan shima ya zaga ya shiga yaja motar suka tafi.

DOCTOR hom ya danna a ƙofar gidan mai gadin ya fito da sauri ya buɗe get ɗin, a compaunt ɗin gidan DOCTOR ya tsaya tare da buɗewa Hajja yace.

” To Bismillah fita ni juyawa zanyi.”

” Kai!!! Wai dama da gaske asibitin zaka koma.”

Dariya DOCTOR yayi yace.

” Au dama kinyi zaton wasa nake miki, asibiti zan koma ban gama aikina ba yaushe zaki koma na turo azo a ɗaukeki.”

” To Allah ya tsare a dawo lafiya, eh to ina ga zuwa ƙarfe biyar.”

Ta ƙarasa maganar tana fita da Allah ya kaimu DOCTOR ya amsa sannan ya juya ita kuma Hajja ta shige cikin gidan……….

Vote
Share
And Comment

ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻

(Ummu Nasmah ce)
[8/31, 12:50 PM] Ummu Nasmah❤️❤️❤️❤️: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

            💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

Love and romance and funny story

Writing by

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*

Marubuciyar nan taku ta INDO A BIRNI

Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a ko yaushe, da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.

Special Gift to

Masoyan Asali waɗanda suka kasance dani a cikin book ɗina na kuɗi wanda ya gabata wato Ruɗanin Zuciya biyu kun sayi wannan book ɗin fiye da zato na Tabbas kun nuna min ƙauna domin kuwa hakan ya gwada min kuna tare dani ako yaushe koda kuɗi ko babu nima dai Ummu Nasmah ina ƙaunar ku🥰

بسم الله الرحمن الرحيم

________________________

🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼
🇦SSOCIATION🤝🏻
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

     *BOOK ONE*

PAGE 13 to 14

_________________________

Sanda na faɗa nace dan Allah duk mai interest akan wannan book ɗin ya bibiya tun daga farko, shine kikayi kunnen uwar shegu dani, da zarar na buɗe data na ina samun saƙo sama da 150 mutane da kuma na group, ana tambayata DOCTOR HASSAN daga farko dan Allah da wanne zanji da typing ko da turo muku daga farko😩

__✍🏻 Hajja a ƙofar falon ta tsaya tare da Sallama bakin ta kusan Uku tana sallama Falmata dake zaune tana dogon tunani bata jiyo ta ba, Hajja haɓa ta riƙe tana cewa ” ikon Allah gida ata sallama babu mai amsawa sai kace ba gidan Musulmai ba” ƙofar Hajja ta tura ta shigo kanta tsaye turus ta tsaya tana bin Falmata da kallo, “ashe dama tana falon ina sallama shine tamin shuru tsabar iya shege” ƙarasawa Hajja tayi tana cewa.

” Wato tsabar iya Iskanci shine ina sallama kika min shuru ko.”

Ta ƙarasa maganar tana zama kusa da Falmata, shuru nan ma Hajja taji Falmata bata amsa mata ba, Hajja cike da tsoron ko ta mutu ne yasata girgiza Falmata sai yanzu ta dawo hayyacin ta, cike da tsoro a firgice ta dubi Hajja sai kuma ta sauƙe ajiyar Zuciya tare da kwantar da kanta jikin kujera, tace.

” Kin tsorata ni wallahi Hajja, yaushe kika shigo banji ba.”

Taɓe bakinta Hajja tayi tana cewa.

” Ina kuwa zakiji shigowata Fatuma, kin sawa kanki tunani kina neman kashe kanki, wai ma tukunna Fatuma kin dubi kanki a madubi kuwa yanda kika rame kika ƙwanjame kika fice cikin hayyacin ki, ko dai ciki ne dake Fatuma.”

Ajiyar zuciya Falmata ta sauƙe cikin sanyin jiki domin kuwa Hajja yau itace ta biyu da tace ta rame, duban Hajja tayi tace.

” Hajja bani da wani ciki, kin san dai matsalar da nake fama da ita ta matsalar mahaifa kinga kuwa ai Hajja babu ni babu saka rai ga samun ciki, ku dai min addu’a Allah yasa na samu maganin da zai sa na samu sauƙi.”

Cike da tausayin jikar tata Hajja tace.

” Hakane Fatuma Amma ai shi ɗan adam baya fidda rai ga rahamar Ubangiji, kiyi haƙuri Insha Allah kema zaki goya ɗanki a bayan ki, har kuyi wasa da dariya dashi.”

” To Allah ya amsa wannan addu’ar taki.”

Hajja ameen tace tare da cewa.

” Amma Fatuma, yanzu na fuskanci matsalar da tasa kika yi wannan bak’ar ramar wato HASSAN shine matsalar rayuwarki ya zamo miki barazana ko, yanzu Fatuma duk wanda ya kalleki tabbas yasan kina cikin tashin hankali, abinda na guda kenan a baya na ƙi yadda da ki Auri Hassan saboda shi Mutum ne mai zafin zuciya da rashin haƙuri sannan kuma bashi da fahimta, sannan shi idan ya tashi zartar da hukuncin sa idanunsa rufewa suke baya tantance fari bare kuma baƙi babu wanda ya isa ya dakatar dashi da aiwatar da nufin sa nafi ki sanin waye Hassan a hanuna ya taso tun yana ɗan yaye, ke kuma macece mai haƙuri nasan zaki cutu da Auren sa, koda wannan al’amari bai faru ba tsakanin sa da iyayen ki, dalilin kenan da yasa naƙi wannan Auren tun farko, Fatuma soyayya ta rufe miki ido kikace lallai ke shi kike so, wannan halayyar tasa ta zafin rai da rashin haƙuri yasa Hassan yake hukunta ki da laifin da babu hanunki ciki, yanzu sanar dani wani irin mungun abu Hassan yake miki yasa har kikayi wannan ramar!!!!.”

Falmata duban Hajja tayi tana tuno da hanyar da Hajja ta nuna mata kafin Auren ta da DOCTOR, ajiyar zuciya ta sauƙe tace.

” Hajja babu komai tsakanina da mijina babu wani mungun abinda yake min, kawai Hajja wannan ramar da kike gani nayi, Allah ne kawai ya kawo ta bawai dan bana jin daɗin Aure na bane, mijina yana kyautata min iya ƙarfin sa bai rageni da komai ba, Hajja karki zargesa domin kuwa bai sani cikin faɗansa da iyaye na ba.”

Murmushi Hajja tayi tana duban Falmata cikin faɗa da tsawa tace.

” Karki maidani shasha wacce bansan me nakeyi ba, kinsan dai ni ba yarinya bace ko na haifi ubanki na haifi Uwar ki, dan haka baki Isa ki ɓoye min matsalar Auren ki ba domin kuwa ko bakin ki da zuciyarki sun ɓoye to tabbas fuskar ki ta nuna, dan haka ki sanar dani me Hassan yake miki, dan ubanki dole auren ki yazo ƙarshe da Hassan ko yaƙi Allah, domin kuwa bazan zuba ido ina kallo ana cutar da rayuwarki ba!!!.”

Cikin mungun ɓacin rai Hajja take wannan maganar, Falmata idanunta ne suka zubo da hawaye cike da tashin hankali tace.

” A’a Hajja karki shiga tsakanina da igiyar Aure na, wallahi Hajja ina son mijina bazan iya rayuwa idan babu shiba ba, Hajja kimin rai ki ƙyale wannan maganar, kije ki cigaba da min addu’a Insha Allah Ubangiji zai kawo min sauƙin lamura na kashe min Aure bashi bane masalaha a cikin wannan lamarin, tabbas DOCTOR Yana cutar dani amma Hajja ina son mijina a haka.”

” Wallahi baki isa ba Fatuma bazan zuba ido rayuwarki ta lalace ba, Fatuma ki daina biyewa soyayya domin kuwa tana gabda kaiki lahira, ki dubi ya rayuwarki zata inganta ki samu farin ciki, ki tashi ki ɗauko mayafin ki mu tafi gida kinbar Auren Hassan kenan daga yau har gaban abada, zan Kuma ci ubansa yau zaisan ya wulaƙanta ki yau naga zalunci, shiyasa YANA ta dage lallai sai ya sakeki ina hanata ashe ita ta gano abinda ni ban gani ba, ki tashi ki ɗauko mayafinki mu tafi “

Falmata cike da damuwa take duban Hajja, muryar ta na rawa tace.

” Babu halin na saka ƙafa na biki Hajja ba tare da izinin mijina ba, saboda idan na biki bada izinin sa ba, zan fita ne cikin tsinuwar Mala’iku dan haka kiyi haƙuri Hajja bazan iya barin gida na ba, kije kimin Allah ya daidaita tsakanina da mijina, zanfi jin daɗin haka fiye da kashe min Aure da zakiyi, ina son HASSAN Hajja bazan iya rabuwa dashi ba .”

Hajja riƙe haɓa tayi tana tir da Soyayyar da Falmata take yiwa Hassan domin kuwa tana Soyayyar wahala ne Soyayyar da zata Kaita ta baro ta, Hajja sosai ranta ya ɓaci cewa tayi.

” Bazaki bini ba ko, kin gwammace ki zauna cikin wahala da kibini na sama miki farin ciki, wai wannan wata irin soyayya kikewa Hassan, ke fa Soyayyar ki bata da riba, anya kuwa akwai zuciya a ƙirjinki Fatuma ki zauna namiji yana taka ki amma a hakan kina nan maƙale a gidan sa kin gwammace wahalar da yake baki ta kashe ki idan yaso sai a fito da gawarki ko, to kinyi ƙarya dan uwarki da ubanki, na yadda bazaki bini yanzu ba, amma zaki taho idan ya baki takaddar ki.”

Hajja tana gama faɗin haka ta juya a fusace, Falmata kuka tasa mai cin rai tana tsoron abinda zaije ya dawo domin kuwa tasan halin Hajja sarai kamar yunwar cikin ta.

Hajja kuwa adaidaita ta hau, ta shige gida cike da ƙunar rai sosai yau ranta ya ɓaci taji baƙin ciki sosai da ganin halin da Falmata take ciki, mai adaidaita yana sauƙe ta Hajja ta basa kuɗin sa, shigarta cikin gidan part ɗin su DOCTOR ɗin ta shiga AJIRAM na zaune ita da Hajjo suka ga Hajja ta shigo cikin matsanancin ɓacin rai ko sallama batayi ba, AJIRAM ce tace.

” Hajja lafiya me yake faruwa.”?

Hajja bata bata amsa ba sai cewa tayi

” Ki kira min Hassan a waya, kice yazo yanzun nan ya sameni duk abinda yake ki ya barsa yazo dan ubansa.”

Tana faɗin haka ta juya ta fice daga part ɗin.

Cike da mamaki AJIRAM take duban Hajja matar da suka fita tare da Hassan ɗin suna wasa suna dariya yanzu kuma ta dawo a haka, AJIRAM wayarta ta ɗauka ta dannawa DOCTOR kira ringin ɗaya ya ɗaga tare da cewa.

” Lafiya kuwa meke faruwa yanzu fa nabar gidan.”?

AJIRAM ce masa tayi.

” Lafiya, Hajja ce tace kazo yanzun tana jiranka duk abinda kake wai ka ajiye kazo ka sameta.”

” Hajja kuma, yanzu fa muka rabu da ita, lafiya.?”

” Wallahi yaya ban sani ba, tace dai kazo yanzun nan.”

” Okay gani nan zuwa yanzun nan.”

Katse kiran DOCTOR yayi cike da mamaki, tashi yayi ya ɗauki kay ɗin motar sa, ya fito daga office tare da cewa nurse fatuma ta cewa DOCTOR SAIF yazo ya rufe masa office ya ƙarasa maganar yana ficewa, motar sa ya shige ya mata kay, cike da tunani harya iso ƙofar gidan, parking yayi tare da shigewa cikin gidan part ɗin Hajja ya shige Darect, bata tsakar gidan, ɗakin ta ya shige yana cewa.

” Wai Hajja meke faruwa ne kam, har kin dawo ne wai “

Ya ƙarasa maganar yana ƙarasawa kusa da Hajja dake tsaye tana riƙe da kunkumi, mari Hajja ta ɗauke DOCTOR dashi, a firgice DOCTOR ya dafe gefen fuskar sa, bai gama dawowa hayyacin sa ba Hajja ta ƙara ɗauke sa da wani marin kafin ta fara Magana cikin ɗaga Murya

” Ubanka ne yake faruwa!!! Nace ubanka ne yake faruwa, ɗan iska marar mutunci, azzalumin banza, me kake ɗaukar kanka, nace me kake ɗaukar kanka, banza a banza, to bari kaji na faɗa maka dan ubanka bazan saka Ido ina kallon ka ka kashe Fatuma wallahi ƙarya kake, me ta maka kake neman kashe ta wani irin baƙin azzalumi ne kai, kana da tabbacin cewa iyayenta sune suka ɓatar da ubanka, waye shaidar ka, ka saka yarinya a gaba kana azabtar da ita, hmmm, yanzu idan Ubangiji shine ya ɗauki ran magaifinka aka ajiye maka gawarsa a gaban ka, zakayi gaba da Ubangiji ne ko kuma zaka daina Bauta masa saboda ya ɗauki ran ubanka, to bari kaji, idan ka fito ɗan halak a cikin uwar ka da ubanka ka bani takardar sakin Fatuma, ka saketa dan ubanka, banza azzalumi wanda baka san darajar ɗan adam ba.”

Tunda Hajja ta maresa har zagin da take masa DOCTOR a tsaye yaƙe ƙyam yana duban Hajja, cikin mungun ɓacin rai idanunsa sunyi jajur kamar gauta ajiyar zuciya kawai yake sauƙewa yana jin kamar ya haɗiyi zuciya ya mutu tsabar baƙin ciki, sosai zuciyarsa take tafasa tare da sake rura wutar tsanar falmata da iyayenta a cikin ransa Magana ya fara cikin ɓacin rai shima.

” Hajja marina kikayi akan Falmata, Hajja nine banza a banza kike kirana kuma azzalumi akan Falmata, Hajja duk zalunci da aka mana baki gani ba mune ma kike kira da azzalumai, kin fifita Falmata akaina Hajja.”

” Na fifita a kanka!!! Nace na fifita ta akan ka dan ubanka, wawa marar lissafi da tunani, idan ka cika mai Zuciya ka saki fatuma, zuciyarka ta banza da wofi da kana da zuciyar ai bazaka zauna da ita ba baƙin mungu wand……….”

Cike da murɗar ɓacin rai da baƙin ciki DOCTOR ya dakatar da Hajja.

” Ya isa Hajja!!! Ya isa ba dai akan Falmata kike min wannan zagin ba hmmm!!!.”

Ya ƙarasa maganar yana cije yatsa.

Itama Hajja cikin tsawar tace.

” Bai isa ba ubana zuwa zakayi ai ka dakeni ba tsawa zaka min cikakken tantiri marar mutunci azzalumin bawa to ko ubanka bai isa ya dakatar dani ba idan ina magana bare kuma ƙaramin ɗan iska.”

DOCTOR hanunsa yasa da ƙarfi ya daki gini cike da haushi, tare da hura isa mai zafi a bakin sa wani irin mungun Sabuwar tsanar falmata ne yake ji a cikin ransa, ficewa yayi da sauri, saura kadan ya bige Aunty Yana dake tsaye tun sanda ta juyo hayaniyar su tazo wajen, Aunty YANA murmushi ta saki cikin farin ciki ta ƙara cikin ɗakin Hajja tana cewa.

” Abinda nake faɗa miki kenan kika kasa ganewa, Hajja yanda yake zaluntar yarinyar…………”

Hanu Hajja ta ɗaga mata tare da cewa.

” Rufe min baki, keɗin ma kanwar lasa ce, duk abinda ya sami ƴarta ki ai laifin kune ya shafe ta, fice min daga ɗaki munafukar banza, ƙulle ƙullen ne bakya yi dukkan ku a tafin hanuna kuke, kallon ku nake tar da idanuna kuma duk na kusa maganin ku, fice bana son munafurci “

Aunty YANA fita tayi siɗi siɗi tana tura baki, tana ƙunƙuni.

” Ai kuwa baki san ina ƙulle ƙulle ba tunda ƙulle ƙullen nawa ban taɓa biyo dashi ta kanki ba, da yanzu baki da bakin zagina, ko tsintsiya na baki nace ki share tsakar gidan nan sai kin share, ayi masifaffiyar tsohuwa ta addabi mutane.”

Ta ƙarasa maganar tana shigewa ɗakin ta, Hajja kallon Yagana dake kwance tayi a gefen ta tayi shuru tana kallon su tace.

” Tashi kema ƙaramar munafuka kinje kin kashe Auren ki, kinzo kin sani a gaba, kema na kusa dawowa kanki muddun baki fitar da miji kin bani waje ba, ki tashi kije ki kira min Yayanki Bukkar acan fadar.”

Yagana tashi tayi ba tare da cewa Hajja komai ba gudun kar masifar ta dawo kanta, ta shige kiran YALLAƁOI wanda Hajja ke kiran sa da bukkar.

Yana zaune Yagana ta samesa, ta sanar dashi sakon Hajja, kusan tare ya tashi suka shigo da Yagana, amma ita Yagana bata koma ɗakin Hajja ba tayi ɓangaren Yalwa matar baffan ta, yallaɓoi da Sallama ya shiga ɗakin mahaifiyar tasa, waje ya samu yana cewa.

” Sannu da hutawa Hajja.”

Wani irin mungun kallo Hajja tayi masa tace.

” Saboda kun barni nayi hutun, nace kun barni nayi hutun ne, munafukai waɗanda sam baƙwa ƙaunar zaman lafiya a Rayuwar ku.”

Ta ƙarasa maganar tana zama yanda zata fuskance sa, yallaɓoi cike da mamaki yake duban Hajja yace.

” Allah ya huci zuciyarki Hajja laifin mena miki.”

” Au!!! Tambayata ma kake laifin ka, to bari kaji na faɗa maka, bazaku kashe ni da baƙin ciki ba, Bukkar duk inda ka kai ɗan uwanka MALA kayi gaggawar dawo dashi idan kuma kashesa kayi ka binnesa babu wanda ya sani, to ka sanar dani a tono sa YA’YAN sa suga gawar sa, sai a samu zaman, dole ne ku gyara zamantakewar ku dan haka faɗa min ina kakai MALA DA JALILA.”

Da sauri yallaɓoi ya ɗago idanunsa a kiɗime yace.

” Wani irin Magana kike nine zan Hallaka ɗan uwana Hajja, Allah ya rufa min asiri banyi wannan lalacewar ba Hajja, taya zan Hallaka ɗan uwana wanda yafi kowa ƙaunata a duniya, wallahi wallahi wallahi ban san komai game da ɓatar Ya Mala ba, ki yadda dani Hajja.”

Hmmm!!!! Kaji munafukan Asali to ban yarda da kai ba, Bukkar nasan yanda kake son sarauta babu abinda bazaka iya aikata wa dan haka na ƙara baka umarni a karo na biyu kaje ka fito min da Ɗana da Jikata, idan kuma kaƙi na tabbata Hassan bazai taɓa ƙyale ku ba, zai fara kashe ƴarku da baƙin ciki ya kawo muku gawarta ya ajiye muku, sannan ya hanaku zaman lafiya kaga daga ni kuma sai na tattara kayana na bar muku gidan na koma gurbin gidan ubana, idan yaso sai ku kashe kanku.”

Hankalin yallaɓoi sosai ya tashi da kalaman mahaifiyar tasa, ya rasa ta ya zai fahimtar da ita bai san komai game da ɓatar ɗan uwansa, cike da tashin hankali yace.

” Hajja……….”

Dakatar dashi tayi tace.

” Bana son na ƙara jin komai daga bakin ka na gama baka umarni sakamako nake jira, tashi ka barmin ɗaki”

Tashi yayi ya fita cikin sanyin jiki da kuma damuwa, shi a ina yasan zai samo YaMala………

Ɗakin matar tasa Yana ya shige ya zauna tare da riƙe kansa yayi shuru cike da damuwa, yana dake zaune ta dubesa tace.

” Abban Falmata meya sameka ka shigo haka rai ɓace.”

Ɗago idanunsa da sukayi jajur yayi yace.

” Yana wai Hajja ni take zargi da ɓatan ɗan uwana, kamar yadda ƴaƴan sa suke zargina, Hajja ma tabi sawun su, wai naje na nemo mata Yamala duk inda na kaisa hmmm!!! Sunƙi su yarda cewa bani da hanu cikin wannan al’amari.”

Ya ƙarasa maganar cike da ƙunar rai Aunty YANA bakin ta taɓe tare da cewa.

” To sai me tunda basu yadda ba, sai su kasheka tunda suna zargin ka, kaga karka wani saka damuwar su cikin ranka bare kuma ya dameka.”

Tsuka YALLAƁOI Bukar yaja ba tare daya kuma cewa Yana komai ba domin kuwa ita ba fuskantar damuwarsa za tayi ba, ganin haka da Yana tayi itama ta watsar da zancen.

Shi kuwa DOCTOR ransa a matuƙar ɓace ya hau motar sa, ya figeta da ƙarfi, tsabar ɓacin rai idanunsa ko gani basa yi sosai, burin sa kawai shine ya gansa gashi ga Falmata, da wannan mungun tunanin yake dreving.

Allah Sarki baiwar Allah ita kuwa Falmata tun fitar Hajja daga gidan take cikin tashin hankali, tasan halin Hajja sarai yau bazata ƙyale DOCTOR ba, muddum Hajja ta sami DOCTOR ita kuma ta tabbata yau kwanan Auren ta ya ƙare, ta kasa zaune ta kasa tsaye sai kaiwa da kawowa take, ai kuwa kamar wanda aka tsikareta da sauri ta ɗauki wayar ta, numbern Maji tayi kira cikin Sa’a kuwa ta ɗaga Falmata cike da tashin hankali tace.

” Maji ki taimake ni kar Aure na ya mutu idan Aure na ya mutu nima mutuwa zanyi.”

Maji cikin ɗaurewar kai tace.

” Auren ki ya mutu, kuma, me Kuma ya ƙara shiga tsakaninku dashi.”

” Ba dashi bane Maji Hajja ne, yanzu tabar gidan nan cikin ɓacin tace lallai yau sai DOCTOR ya sake ni, na tabbata indai suka haɗu tabbas saki sai ya wajaba a kaina ki taimakeni ki dakatar da Hajja kisan yanda zaki hanata yiwa DOCTOR Magana.”

Maji tsuka taja tana cewa.

” To wai ma sai me idan ya sakeki meye amfanin Auren kin nan idan banda cutuwar da kike yi, da zakiji shawarata da kin bar Hajja ta ƙwata miki ƴancin ki, ta hakane DOCTOR zai fara fahimtar mahimmancin ki daga Ranar da kika kauce masa, Soyayyar da kike nuna masa tayi yawa itace take ƙara hura masa kai wajen ganin ya wulaƙanta ki, yana ganin koma me zai miki ai bazaki iya rabuwa dashi ba, wai ina zuciyarki take ne Falmata ki tashi ki ƙwaci yancin ki mana, meye amfanin Auren mutumin da baya ganin darajar ki da na iyayen ki da suka haife ki har ya ganki ya Aura, ki dawo hankalin ki Falmata.”

Cikin shashsheƙar kuka Falmata tace.

” Maji ba wannan maganar nake buƙata daga gareki ba yanzu, so nake ki dakatar da Hajja, ina son mijina bazan iya rabuwa dashi ba, koda kuwa naman jikina yake yanka kullum, zan zauna dashi a haka, ki taimakeni Maji karna rasa igiyar Aure na.”

Cike da jin haushin Falmata Maji tace naji zan dakatar da Hajja amma tukunna ki kira DOCTOR SAIF ya fara raba DOCTOR da wayoyin hanunsa tukunna, gudun kar kafin na isa gidan ku Hajja ta rigani kiran sa idan har kinyi haka to Tabbas zan dakatar da Hajja.”

Falmata da to ta amsa cikin sauri ta kashe kiran Maji, ta fara neman numbern SAIF sau uku tana kira zai shiga amma baza’a ɗauka ba, cikin tashin hankali Falmata ta yasar da wayar hawaye na gudu saman fuskar ta, shikenan ta shiga Uku yau zata rabu da farin cikin ta, tana cikin wannan tunanin taji wayar ta yana Ring saurin dubanta ta kai kan wayar Doctor Saif ke kira cikin sauri ta ɗaga, ko Sallama bata amsa ba tace.

” Saif kuna tare da DOCTOR ne.?”

Tambayar da ta jefa masa kenan, jin muryar ta cikin damuwa da alamun kuka yasa DOCTOR Saif cewa.

” Bama tare dashi ya fita tun ɗazu, lafiya Falmata meke damunki.”

Da ƙarfi Falmata ta furta “na shiga Uku……………..”

????????????????????????
Tabbas akwai ayar tambaya a cikin wannan cakwakiyar family……..

Shin mai zai faru, DOCTOR zai sake FALMATA?

Ina labarin AI’SA wata irin gudummawa zata bayar cikin wannan labarin ?

Shin Umma zata sami lafiya?

Shin mahaifin DOCTOR da ƴar uwarsa suna raye ko sun mutu?

Shin idan ba YALLAƁOI BUKAR bane da YANA sukayi sanadiyar rasa iyayen DOCTOR to waye ne?

Sannan su wannan family kansu ya suke rayuwarsu kafin faruwar wannan mungun al’amarin?

Amsar ku tana tattare cikin wannan littafin amma ta hanyar 👇🏻

Kuna iya nuna min soyayya ta hanyar siyen littafinan na DOCTOR HASSAN akan Naira 300 kacal,zaku iya biya ta wannan account ɗin 0006064512 RASHIDA USMAN JAIZ BANK ko kuma ku tura katin MTN ta wannan number 08147537180,sannan ku tura shaidar biya a ita ko a 08147537180 Nagode masoya,ina maraba da masu sayan ɗaya ko sari

Kumin adalci dan Allah kar wacce ta zageni dama bance free book bane, idan ya miki ki saya idan bai miki ba ki barmin kayana, amma dan Allah karki zageni ina maraba daku masoyana kiyi ƙoƙarin ganin kin biya naki domin kuwa tuni har an fara biya

Akwai waɗanda suka bani kuɗin su a cikin group ɗina na Ruɗanin Zuciya biyu so dan Allah kumin magana ta pc sai nayi adding ɗinku a paid group.

Vote
Share
And Comment

ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻

(UMMU NASMAH CE)
[9/1, 6:24 PM] Ummu Nasmah❤️❤️❤️❤️: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

            💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

Love and romance and funny story

Writing by

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*

Marubuciyar nan taku ta INDO A BIRNI

Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a ko yaushe, da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.

Special Gift to

Masoyan Asali waɗanda suka kasance dani a cikin book ɗina na kuɗi wanda ya gabata wato Ruɗanin Zuciya biyu kun sayi wannan book ɗin fiye da zato na Tabbas kun nuna min ƙauna domin kuwa hakan ya gwada min kuna tare dani ako yaushe koda kuɗi ko babu nima dai Ummu Nasmah ina ƙaunar ku🥰

بسم الله الرحمن الرحيم

________________________

🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼
🇦SSOCIATION🤝🏻
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

     *BOOK ONE*

PAGE 15 to 16

_________________________

__✍🏻 Yasar da wayar Falmata tayi cikin tashin hankali ta zauna rasa ya zatayi da kanta tayi, idan har Hajja ta sami DOCTOR bata san wani irin abu bane yau zai faru tsakanin ta da DOCTOR, hawaye ne sharshar yake zuba daga ƙwayar idanunta yayin da hankalin ta yake matuƙar tashe kafin kice me har idanunta sunyi jajur, tana nan cikin wannan halin ta jiyo dirin motar sa, wani irin tsinkewa zuciyarta, tayi da sauri ta miƙe tsaye tare da zuwa window ta ɗaga labule, a yanayin yanda taga ya fito daga cikin motar tabbas yana zuciye, runtse idanunta tayi cike da tsoro ta sake labulen jikin bango ta koma ta jingina hawaye na ƙara gudu daga idanunta.

DOCTOR kuwa da ƙarfi ya turo ƙofar falon idanunsa jawur, ya shigo ba ko Sallama, a tsakiyar falon ya tsaya cak yana ƙare mata kallo yanda take rakuɓe jikin bango sai famar zubar hawayen munafurci take, a hankali yake takawa inda take yayin da ita kuma zuciyarta take ƙara tsananta bugawa a duk takawar da yayi domin nufo ta, sanda yazo daf da ita har kamar numfashin su na haɗuwa, idanunsa da suka koma kamar gauta ya haɗa da nata yana jefa mata mungun kallo mai cike da zaki gane kurenki, saurin sunkuyar da kanta tayi ƙasa, cike da tsoro,shi kuwa DOCTOR cike da mungunta ya saka hanunsa ya fisgo gashin kanta, runtse idonta tayi cike da azaba ɗago kanta yayi tare da cewa.

” Ɗago kanki ki kalleni baƙar munafuka, uban waye ya baki shawarar ki kai ƙarata wajen Hajja, Hajjan uwata ce ita ko kuma zata hanani na miki abinda naga dama ne, bari kiji abinda baki sani ba, na tsaneki fiye da yadda na tsani mutuwa ta, bazan taɓa ƙara sonki ba a cikin Rayuwata, dan haka ki daina kai ƙarata domin kuwa bazaki ƙara samun wata kulawa daga gareni ba, dan haka kije na……………”

” Ka dakata!!!! Ka dakata!!! Karka aikata babban kuskuren da bazaka taɓa iya gyara sa ba Malam Hassan.”

Daga DOCTOR har Falmata kallon su suka mayar inda sautin muryar ta fito HABEEB ne tsaye ya zuba hanunsa cikin aljihu kyakkyawan mutum ne fari sol tamkar bafulatani sai dai KANURI ne shi murmushi HABEEB ya saki tare da cewa.

” Abokina kayi mamakin shigowa ta cikin gidan kane akan lokaci, nazo gyara maka kuskuren kane a karo na farko, kuma na ƙarshe, kana kuskuren rabuwa da ita, ni kuma a lokacin ne zan Aure abata dama tawace ƙaddara yasa ka ƙwace ta, sam bata ma dace da miji irin ka ba damu ta dace waɗanda zamu riritata tamkar ƙawai mu bata kulawa yadda ya dace, domin Falmata matar hutu ce, ka kiyaye idan kuma baka kiyaye ba, ina nan ina jiran fitowar ta, karka manta da har yanzu akwai Soyayyar ta a zuciyar HABEEB.”

Yana gama faɗin haka ya juya ya fice da murmushi ɗauke saman fuskar sa, gagara Magana DOCTOR yayi har HABEEB ya fita daga falon wani irin baƙin ciki ne ya murɗi DOCTOR HABEEB a cikin gidan sa uban waye ya basa izinin shigo masa cikin gida, Okay wato dai har yanzu bai cire Soyayyar matar sa Falmata a cikin ransa ba, ashe har yanzu yana bibiyar ta, cikin haushin ya ƙara damƙe gashin Falmata sanda tayi ƙarar azaba, haɗa kanta yayi da bango, tare da saka ƙafarsa ya mutstsike ƙafar ta, hawayen azaba sune suka gangarowa Falmata, ita kanta ta razana da shigowar HABEEB cikin gidan nan, to wa ya turo sa? sakin ta DOCTOR yayi ba tare daya ƙara furta mata komai ba ya shige Bedroom ɗinsa cikin mungun ɓacin rai, har yana jin kamar jiri, Falmata kuka tasa tana riƙe kanta dake sara mata ga yatsun ƙafarta da take jin kamar zasu fice daga jikinta riƙe ƙafar tayi cikin kukan take furta.”

” Na shiga Uku wai me nayiwa Ubangiji ne yake jarabtar Rayuwata, wani irin laifi na aikata, ya Allah na tuba ka yafe min idan har akwai wani laifin dana maka kake hukuntani dashi, ya Allah ka daidaita tsakanina da mijina, Allah kana gani ina son mijina bazan iya rayuwa ba tare dashi ba, ya Allah ka dawo min hankalin mijina gareni, Allah ka kawo min sauƙi cikin wannan baƙin cikin da nake.”

Ta ƙarasa addu’ar tana kuka mai cin rai.

Shi kuwa HABEEB cike da tausayin Falmata ya fito daga cikin gidan motar sa ya shiga, duban sa ya kai ga Maji dake zaune cikin motar tana jiran fitowar sa tambaya ta jefa masa.

” Ya akayi Allah yasa ba dukanta yayi ba naga ka fito kamar jikinka a sanyaye.”

Ajiyar zuciya HABEEB ya sauƙe tare da cewa.

” Meyasa kika sa na dakatar da Hassan daga sakin Falmata, anya kuwa kin mata adalci, dama haka take shan wahala a gidan Auren ta, da wannan mungun zaman da Falmata take a gidan Auren ta, gaskiya ina ga mutuwar Auren ta shiyafi, tabbas Hassan ya ci amanar Falmata, Soyayyar da ta nuna masa sam bata cancanci sakamakon azabtarwa daga garesa ba, komai tsananin girman laifin da ta aikata masa, amma meyene ya jawo musu wannan zafin ƙiyayyar? Ina ku ji a jiki na kamar zuwan da nayi bai dace ba.”

” Hmmm!!! HABEEB duk wanda yasan rayuwar su a baya abinda zai faɗa kenan wanda kuma bai san rayuwarsu ta baya ba, cewa zaiyi Auren ƙiyayya sukayi, duk abinda kaga DOCTOR yana yiwa Falmata bata ganin laifin sa, sai ma ƙoƙarin da take wajen ganin ta masa biyayya, sanin matsalarsu kuma wannan family essur ne, HABEEB nima dole tasa na sanya ka cikin wannan lamarin, domin samowa Ƙawata farin cikin ta, sanin kanka kaine kaɗai mutumin da DOCTOR yaƙe shayi a cikin samarin da suka nemi Falmata domin kuwa yasan kafi sa komai kuɗi matsayi da kuma iko, hakan yasa yake mungun shakkar ka tare da kishin ka, nasan koda yayi niyyar sakin Falmata, yasan cewa kana nan kana jiranta na tabbata bazaiyi gangancin rabuwa da Ita ba, na GODE daka taimaka min wajen dakatar da DOCTOR.”

” To Allah ya sauwaƙa, nima nayi hakanne kawai domin Soyayyar da nake yiwa Falmata, har yanzu Zuciyata babu macen da take so sama da ita Soyayyar ta a jinina take bazan taɓa daina sonta ba har ƙarshen Rayuwata, sai dai na ɗauki ƙaddarar rashinta a yanda tazo min domin kuwa Ubangiji ya ƙaddara Falmata ba matata bace. yanzu ina kika nufa na sauƙe ki na wuce.”

” Gida zaka mai dani, domin kuwa ina shiga gidan nan yanzu DOCTOR zai fuskanci nine na turo ka, na ƙara jaza mata wata matsalar muje kawai da yamma zan dawo.”

Kaɗa kansa HABEEB yayi tare da jan motar suka bar ƙofar gidan.

Shikuwa DOCTOR Tunda ya shiga Bedroom ɗinsa ya kasa nutsuwa ya manta ma da zagin da Hajja ta masa, kawai yanzu tashin hankalin sa HABEEB daya shigo masa har cikin gida, sannan yake masa barazanar cewa har yanzu yana nan yana jiran matar sa, a fili ya furta, ” cap lallai mace muminar kare ce mai cizo, anya kuwa Falmata basa tare da HABEEB suna Soyayyar bayan fage idan ba haka ba uban waye ya kirasa cikin gidan sa.” Kwalaben da suke shirye kan dressing mirror yasa hanunsa ya watsar dasu ƙasa, hakan bai ishesa ba, sai da yasa hanunsa ya naushi mirrorn da ƙarfi, wani irin mungun yanka glass mirror ya masa tare da tarwatsewa idanunsa sunyi jajur kana ganinsu zaka hango tsantsar kishi a cikin su da ɓacin rai.

DOCTOR SAIF ne ya shigo cikin gidan shima da sauri, Falmata ya fara cin karo da ita a inda take zaune tana famar disgar kuka kamar wacce ranta zai fita, nufota yayi cikin sauri yana cewa.

” Subabanallah!!! Falmata lafiya meya sameki.?”

Bata kai ga basa amsa ba sukaji ƙarar wurgar da abubuwa da ake a cikin Bedroom ɗin Doctor, kusan tare suka nufi ɗakin da DOCTOR SAIF, doctor Saif cike da tsoro ya zaro idonsa yana bin Bedroom ɗin da kallo, ga baki ɗaya yayi kacakaca da kayan ɗakin, harta dressing mirror ma sai da wurgar sa ƙasa hanunsa kuma sai famar tsiyayar jini yake, Falmata hanu tasa a kanta ta ƙara sakin wani sabon kuka, kansa tayi da gudu zata riƙo hanunsa wanda yake zubda jinin ya dakatar da ita yana nunata da yatsa.

” 👉🏻 Karki kuskura hanunki ya taɓani macuciya maciya Amana wacce bata san darajar Aure ba da Auren ki amma kina Soyayya da wani namiji a waje ko kunya bakya ji, shine zaki turo min ƙato ya shigo min har cikin gida ko?, To karki kuskura ki taɓa ni idan kuwa kika taɓa ni sai na miki mungun illa.”

Falmata a razane take kallon DOCTOR tana girgiza masa kai alamar bata da masaniya da shigowar HABEEB cikin gidan, DOCTOR Saif kuwa dariya ce taso ƙwace masa yanda yake hango kishi ƙiri-ƙiri a idanun DOCTOR Amma a hakan yake furta wai ya tsani Falmata bayan gashi yana kishin ta, Falmata ya duba tare da ce mata.

” Waye ne ya shigo cikin gidan nan.?”

Cike da tashin hankali tace.

” HABEEB ne kuma wallahi bani da masaniya akan shigowar sa rabona dashi tun Ranar Aure Na, da yazo ya min murna, ban ƙara sashi a cikin Ido na ba sai yau daya shigo cikin gidan nan.”

Murmushi DOCTOR SAIF yayi, tare da ce mata.

” Okay ki share hawayen ki ki daina wannan kukan kije ki wanke fuskar, karki kanki yayi ciwo, zanyi Magana dashi.”

Falmata fita tayi tana share hawayen ta sai ajiyar zuciya take, DOCTOR Saif cikin Bedroom ɗin ya ƙarasa drowarn doctor ya ƙarasa ya buɗe, first aid box ya ɗauko ya dawo kusa da DOCTOR, zama yayi bakin bed tare da buɗe box ɗin kayan wanke ciwo ya ɗauka tare da kama hanun DOCTOR ya fara wankewa yana cewa.

” Me zai dameka dan HABEEB yazo wajen Falmata, a zatona matar da ake so ita ake kishi, ba matar da aka tsana ba ina tunanin ya fara zuwa zawarci ne, tunda ka kusa sakinta kaga kuwa ai dole shi kuma HABEEB ya fara zuwa kamun ƙafa.”

DOCTOR ƙwace hanunsa yayi daga DOCTOR SAIF cikin masifa da zafin rai yace.

” Inji uban waye yace ina kishin ta, karka kuskura ka ƙara ƙiran kishi tsakanin mu naji zafin keta wa SUNNAR Annabi haddi da yayi ne, tunda duk tsiya dai akwai Aure a tsakanina da ita ko?, sannan kuma bari kaji bazan taɓa ƙyale HABEEB ba, sai na ɗauki hukunci a kansa na keta min haddi da yayi ya shigo min har cikin falo, ƙato dashi ya shigo min falo yana kalle min mata, haka addini yace ka faɗa min.”

Saif bakin sa ya taɓe tare da miƙewa tsaye yace.

” Abokina meye a cikin idanunka idan ba kishi ba, meyasa kaji zafi dan HABEEB ya shigo cikin gidan ka ya kalli matar ka meyasa kaji zafin maganar sa, DOCTOR ka dawo cikin hankalinka domin kuwa kana son matar ka, matar da ake so ita ake kishi, gashi kuma naka idanun sun nuna kishin ka, ka gane cewa matar ka tana da daraja, duk wani abu mai daraja kuma adana sa ake, duk sanda ka sake matar ka ta kufce maka, abune mai matuƙar wahala ta dawo maka, babu yanda ka iya da HABEEB domin kuwa yafi ƙarfin ka, ko shara’a ne bazaka iya dashi ba, dan haka abinda ya kamata kayi shine ka dawo da farin cikin gidan ka ka riƙe matar ka da kyau, sannan ka rage wannan Zafin zuciyar taka, ka kuma cire zargi cikin zuciyarka, shine kawai abinda zaiyi katanga tsakanin matar ka da HABEEB.”

Zama DOCTOR yayi tare da dafe kansa sai ajiyar Zuciya yake sauƙewa idanunsa ya kai kan hoton Abbansa da Aunty Jalila hanunsa yasa ya ɗauki pic ɗin, yana ƙare musu kallo, hawaye ne ya zubo masa daga idanunsa, ɗago kansa yayi ya dubi SAIF yace.

“SAIFUDDEEN taya kake tunanin zan iya gyara alaƙata da Falmata bayan iyayenta sun zalunce mu, sun mai damu marayun Dole, bazan Rayuwar farin ciki da Falmata ba, duk sanda na kyautata mata ji nake Tamkar na kyautatawa iyayen ta, bazan iya ba SAIF.”

” DOCTOR meyasa idanunka suke rufewa kake biyewa zuciyarka take tunzura ka, kake yankewa matar ka hukuncin iyayenta a kanta, dan Allah DOCTOR ka sawa zuciyarka haƙuri ka bawa matar ka farin ciki, kasan Falmata macece ta gari sai son zuciyarka yasa ka yanke mata hukuncin da ba nata ba.”

Shuru DOCTOR yayi jikinsa sosai yayi sanyi yasan dukkan maganganun da DOCTOR SAIF yake faɗa masa gaskiya ne, sai baya jin zai iya bawa Falmata farin ciki saboda yana jin zafin iyayenta…………

Ku biya domin cigaba da karanta wannan labarin mai matukar tausayi soyayya faɗakarwa tare da ban dariya ga yanda zaki biya kuɗin ki 👇🏻

Kuna iya nuna min soyayya ta hanyar siyen littafinan na DOCTOR HASSAN akan Naira 300 kacal,zaku iya biya ta wannan account ɗin 0006064512 RASHIDA USMAN JAIZ BANK ko kuma ku tura katin MTN ta wannan number 08147537180,sannan ku tura shaidar biya a ita ko a 08147537180 Nagode masoya,ina maraba da masu sayan ɗaya ko sari

Vote
Share
And Comment

ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻

(UMMU NASMAH CE)
[9/2, 9:28 PM] Ummu Nasmah❤️❤️❤️❤️: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

            💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

Love and romance and funny story

Writing by

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*

Marubuciyar nan taku ta INDO A BIRNI

Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a ko yaushe, da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.

Special Gift to

Masoyan Asali waɗanda suka kasance dani a cikin book ɗina na kuɗi wanda ya gabata wato Ruɗanin Zuciya biyu kun sayi wannan book ɗin fiye da zato na Tabbas kun nuna min ƙauna domin kuwa hakan ya gwada min kuna tare dani ako yaushe koda kuɗi ko babu nima dai Ummu Nasmah ina ƙaunar ku🥰

بسم الله الرحمن الرحيم

________________________

🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼
🇦SSOCIATION🤝🏻
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

     *BOOK ONE*

PAGE 17 to 18

_________________________

_✍🏻 “Zuciyata bazata iya daurewa ɗaukar haƙuri ba, WUTAR FANSAR mahaifina itace kawai take ruruwa a cikin zuciyata, SAIF duk sanda na kalli fuskar Falmata ji nake tamkar fuskar mahaifiyar ta na kalla, Sorry bazan iya doguwar rayuwa da Falmata ba, dole ne zan rabu da ita.”

DOCTOR SAIF girgiza kansa yayi cike da haushin DOCTOR, ya rasa wani irin Mutum ne shi sam bashi da fahimta bare kuma ɗaukar shawara, abinda yasa a gaban sa shi kawai yake aikatawa duban sa SAIF yayi yace.

” Shikenan kaje ka yankewa kanka hukunci tunda kaine ka haifi kanka, babu wanda ya isa ya faɗa maka tunda kaine kafi kowa sanin gaskiya, amma ina mai tabbatar maka akwai ranar da zaka zo kana nadama kana neman taimako amma ka rasa samun mai taimaka maka, saboda masu taimakon ka ka watsa musu ƙasa a ido sanda suke taro ka suke nuna maka Hanyar gaskiya, ka sani Ubangiji sai yayiwa wannan yarinyar sakayya abisa cutarwar da kake Mata, DOCTOR anya kuwa saboda matsalar iyayenku kake walaƙanta Falmata, ko dai Saboda bata haihuwa ne kake walaƙanta ta.”

Ɗago kansa DOCTOR yayi da ya kaɗa yayi jajur, ya dubi SAIF tare da girgiza kai yace.

” Karka kai zarginka zuwa ga rashin haihuwar Falmata, domin kuwa bawai kwatakwata bazata taɓa haihuwa bane a rayuwarta matsalace kawai take dashi, kuma muna saka ran zata sami sauƙi kuma koda Falmata bazata haihu a rayuwarta ba ni zan iya zama da ita a haka, saboda kafi kowa sanin yanda nake son FALMATA, sai dai ƙaddara ta shiga tsakanina da Soyayyar ta, matsalar da aka samu nafi son iyayena a kanta Soyayyar su tafi ƙarfi fiye da wanda nake mata, dan Allah Saif mubar wannan maganar haka.”

” Hmmm!!! Ko baka ce dama Dole zan barta tunda ba son gaskiya kake, amma ina son kasan abu wanda kowa yake kallon ka da ita, TUN CAN DAMA BA SOYAYYAR GASKIYA KAKE MAWA FALMATA BA SHIYASA KA JUYA MATA BAYA A LOKACI GUDA.”

Ya faɗa masa maganar tare da tashi ya bar Bedroom ɗin.

DOCTOR binsa yayi da kallo cikin sanyin jiki harya fice, kwanciya yayi a bed ɗinsa tare da yin rigingine yana kallon slip muryar HABEEB ne kawai take masa yawo cikin kunnen sa, runtse idanunsa yayi yana jin wata sabuwar tsanar HABEEB cikin ransa KA ADANA MATARKA DOMIN KUWA HAR YANZU INA SONTA tsuka yaja still pictures ɗin Aunty Jalila yana hanunsa, rungume shi kaɗai yasan zafin da yake ji na rasa iyayen sa da yayi, tashi yayi yana sauƙe ajiyar zuciya ya ajiye pictures ɗin tare da ƙwalawa Ladiyo kira, cikin sauri kuwa ta shigo da Sallama, nuni ya mata da ta tattara kayan da ya zubar a ɗakin, da to Ladiyo ta amsa sannan shi kuma ya shige falo ya zauna zaman jiranta.

Falmata tunda ta shiga Bedroom ɗinta hawaye ya ɗauke daga idanunta, sai zafi kawai da zuciyarta ke mata ita kanta tana mamakin irin matsanancin Soyayyar da take yiwa DOCTOR Zuciyarta ta kasa hakura dashi, Soyayyar sa ji take tamkar ranta hakan yasa take jin rabuwa dashi tamkar rabuwa da rayuwarta ne, meyasa DOCTOR yake wulaƙanta ta haka, bayan shima bashi da tabbacin iyayenta suna da hanu cikin ɓatar iyayen sa, zama tayi bakin bed ɗin ta zuba tagumi, cike da damuwa, ta daɗe zaune tana cikin tunani kafin ta tashi cikin natsuwa da kuma damuwa ta nufo falo a zaune ta hangesa dama kuwa Bedroom ɗin nasa ta nufa, wajen sa ta taho, ta faɗa jikinsa tare da saka hununta ta ƙanƙamesa, sai kuma tasa kuka.

Kusan suman tsaye DOCTOR yayi jinta a jikinsa, da yayi, ajiyar zuciya ya sauƙe ya kuma kasa yakice ta daga jikinsa domin kuwa rabon dasu haɗa jiki da ita tun randa wannan mummunan lamari na iyayensa ya faru, shuru yayi kawai yana jin sautin kukan ta, cikin muryar kukan tace.

” Bansan wani irin soyayya nake maka ba, ni dai nasan bazan iya jure rasa ka ba, dan Allah kayi hkr, karka rabu dani saboda kuskuren iyayena, Wallahi ban kai ƙararka wajen Hajja ba, ban kuma ce mata komai ba, bansan dalilin da yasa ta maka haka ba, ka yafe min dan Allah karkayi fushi dani mijina.”

Ta ƙarasa maganar tana kwantar da kanta a ƙirjinsa, still shuru, bai ce komai ba, itama shurun tayi tana laɓe a jikinsa, DOCTOR jin wani abu ya fara yawo tun daga tafin ƙafarsa zuwa kansa ya sashi saurin ɓareta daga jikinsa ya tashi da sauri ya bar falon duka, kallo Falmata ta bisa dashi cike da tausayin kanta harya fice, ta daɗe zaune cikin falon kafin ta koma Bedroom ɗinta.

Maji kuwa a ƙofar gidan su HABEEB ya sauƙe ta, murmushi tayi tare da cewa.

” To HABEEB na gode.”

Shima HABEEB murmushi yayi tare da cewa.

” Okay ki gaishe da Mama, sai munyi waya.”

“Zataji” Maji tace tare da shigewa cikin gidan.

Aunty YANA kuwa tun ɗazu zaman jiran ganin Falmata take da takaddar sakinta, amma ina shuru take ji wai Malam yaci shirwa, Yagana da ta shigo ne ta zauna Aunty YANA tace.

” Oh ni YAHANASU wai tun ɗazu fa nake zaune nake jiran naga yarinyar nan Falmata ta shigo min da takaddar sakinta amma shuru babu wani motsi.”

Murmushi Yagana tayi tare da cewa.

” Wai ke tunani kike dama Hassan zai saki Falmata dan kawai wannan rashin mutunci da Hajja ta masa hmmm!!! Kin manta waye Hassan kenan, to wannan dalili yayi kaɗan yasa ya saketa, wai ma Aunty Yana meye ribarki idan Hassan ya saki Falmata meyasa kike son ya saketa.”

Tsuka Aunty YANA taja tare da cewa.

” Ke Yagana baki ga dalilin ba kenan, bakya ganin yanda yake wahalar da rayuwarta kullum cikin baƙin ciki take a gidan ta, wace uwace ranta zaiyi daɗi taga ƴarta wacce ya kamata ace tana taimakon ta cikin wahala babu wannan Uwar komai lalacewar uwa tana son taga ɗanta cikin jin daɗi, duk abinda zanyi domin dawo da hankalin Hassan kan Falmata taƙi ta bani haɗin kai, naje wajen Malamai sun min aiki akansa amma abun yaƙi cinsa na karɓo wanda za’a sa masa yarinyar nan taƙi bani haɗin kai, to ya zanyi idan ba na nemi auren ya mutu, tazo ta sami wani mijin ta aura wanda zata sami kwanciyar hankali.”

Jinjina kanta Yagana tayi tace.

” Tabbas kuwa Falmata bata da farin ciki a gidan Auren ta, kuma itama tana da laifi na shige taurin kai da tausayin wanda baya tausayin ta, ni dai abinda zan faɗa miki, tunda layar nan tana nan, ki ɗauka kije gidan da kanki ki saka ki kuma ja mata Allah ya isa idan ta cire, kinga kuwa idan tana neman albarka ai dole ta barsa.”

” Hmmm!!! Kin kawo shawara mai kyau, zanje da kaina amma ba yanzu ba sai an kwana biyu saboda tsaro.”

” Hakan yafi ya kamata kije kam, bari naje wa Hajja aika gidan Su Maji.”

” Sai kin dawo” Aunty YANA tace.

” FANNA FANNA!!! Hajjo ce mai kwala mata kira amsawa Fanna tayi tare da shigowa ta zauna kusa da Hajjo tace.

” Gani Aunty.”

” Ruwan wankan Umman yayi zafi ne.?”

” Eh yayi zafi daidai wanka.”

” To maza tashi kije ki ɗiba ki sirka ki kai bayin sai kizo ki taimaka min mu kaita.”

To Fanna tace tare da tashi taje ta ɗibi ruwan ta kai sannan ta dawo Hajjo Itace ta tayar da Umma sannan Fanna ta tallafe ta, suka Kaita bayi, fitowa Fanna tayi ta bar Hajjo, itace ta mata wanka tas sannan ta kira Fanna tace ta kawo mata kayan Umma a sip ɗin Umma Fanna ta ɗauko kayan ta kawo Hajjo ta sa mata sannan suka fito da ita suka kwantar, wannan karon idanun Umma a buɗe suke tana bin kowa da kallo sai dai bata Magana, Hajjo hayaƙin magani ta ɗauko ta turare Umma dashi, Fanna kwantar da kanta tayi jikin Umma hawaye ya zubo mata,tace.

” Zaki sami lafiya Umma da yardar Allah, zaki warke ki dawo Kamar da ummana.”

Hajjo ma tausayi Umma ke bata, mata mai kazar-kazar da son ƴan UWA, mata mai kirki tana kwance cikin jinyar da ba’a gane kanta ba, suna nan zaune Hajja ta shigo, Hajjo ce ta gaishe ta, ta amsa fuskar ta a sake duban Umma tayi tace.

” Sannu Yamuram Allah ya baki lafiya, ki tashi ki tsaya akan ya’yan ki, nasan dukkan wannan abinda ke faruwa tsakanin Hassan da fatuma da kina da lafiyarki bazaki bari hakan ta faru, Allah ya yaye miki”

Da ameen hajjo suka amsa, Hajja ta juma zauna kafin ta fita tana cewa Fanna tazo zata aiketa.

Can kuwa gidan DOCTOR cikin dare kowa yayi nisa da bacci amma ita Falmata nata idanun biyu ne ta kasa bacci gashi gobe tana son zuwa school daga nan zata biya gida ta duba Umma, bata san kuma ta yaya zata sanar da DOCTOR ba, ta juma tana Nazari har bacci ya ɗauke ta.

Yayin da shima DOCTOR yake nasa Bedroom ɗin bacci ya gagaresa maganganun Hajja da HABEEB ne kawai suke masa yawo Cikin kunne, bai taɓa jin haushin Hajja irin wannan karon ba, wai shi Hajja take kira banza a banza, hmmm duk abinda aka masa bata gani ba, tafi son ya’yan kawu bukkar akansu, a cikin zuciyarsa ya furta babu komai rayuwa ce, tashi yayi ya shige tollet ya ɗauro alwala fitowa yayi ya tayar da Sallah, duk sujjadar da zaiyi sai ya roƙi Ubangiji daya bayyana masa mahaifinsa da ƴar uwarsa cikin ƙoshin lafiya, bayan ya idar da sallar ma ya juma yana musu addu’a sannan yaji zuciyarsa ta masa sanyi, bed ɗinsa ya hau ya kwanta yana bin gefen da Falmata ta saba kwanciya da kallo, lumshe idanunsa yayi tuno rayuwarsu ta baya mai cike da kwanciyar hankali da Soyayya, yau ɗaya kawai sai da yaji kewarta cikin Bedroom ɗinsa, filo ya jawo ya ƙanƙame tare da rufe idanunsa.

Naso read More ɗin yafi haka yawa amma dai ku shaƙata da wannan ɗin.

Masoya naji daɗin yanda kuka nuna min ƙauna ta hanyar siyan wannan littafin na gode sosai🤝🏻

Ki biya ki karanta cikin kunciyar hankali labari ne mai cike da Soyayya tare da ban tausayi faɗakarwa harma da nishaɗantarwa ki biya kuɗin ki ta wannan hanyar 👇🏻

Kuna iya nuna min soyayya ta hanyar siyen littafinan na DOCTOR HASSAN akan Naira 300 kacal,zaku iya biya ta wannan account ɗin 0006064512 RASHIDA USMAN JAIZ BANK ko kuma ku tura katin MTN ta wannan number 08147537180,sannan ku tura shaidar biya a ita ko a 08147537180 Nagode masoya,ina maraba da masu sayan ɗaya ko sari

Vote
Share
And Comment

ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻

(UMMU NASMAH CE)
[9/3, 7:12 PM] Ummu Nasmah❤️❤️❤️❤️: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

            💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

❤️ Love and romantic and funny story ❤️

Na

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*

Marubuciyar nan taku ta INDO A BIRNI

Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a duk inda kuke so da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.

RIGIJI GABJI TSARƘWAI MAZAƘWAI INA KUKE MASOYA WANNAN SHAHARARREN BOOK ƊIN WATO CONEL UBAIDULLAH TO ALBISHIR YANZU MA DAI GA MOMYN AHLAN ZARAH ABDUL TA SAKE DAWO MUKU DA SABON SALO MAI SABON TAKU GAWURTACCEN SOJA CONEL UBAIDULLAH RETURN MAZA KU GARZAYA KU SAMI UWAR AHLAN DOMIN KUMA A DAMA DAKU KUMA WAƊANDA BAKU KARANTA NA FARKO BA, KU NEMA KU KARANTA KAR A BARKU A BAYA, AKAN FARASHI ƘALILAN MOMYN AHLAN TANA JIRAN MASOYANTA

Waɗanda suka ce Document ɗin Ruɗanin Zuciya biyu suke so, to ga dama ta samu na gama na kuma haɗa Complete document idan kina so zaki samesa a 200 Naira only 08147537180.

بسم الله الرحمن الرحيم

________________________

🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼
🇦SSOCIATION🤝🏻
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

     *Book One*

Page 19 to 20

________________________

_✍🏻Washe gari da safe cikin ikon Allah Falmata ta tashi cikin fara’a domin kuwa haka kawai take jin Damuwar tata ta mata sauƙi, Yau da kanta ta haɗa breakfast, Ladiyo gyaran part ɗin kawai tayi, breakfast ɗin Musa mai gadi ta bawa Ladiyo ta kai masa ita kuma ta shige Bedroom ɗinta, tollet ta shige tayi wanka ta shirya cikin wani koren atamfa wanda aka mata single style sosai atamfar tabi jikinta, ba wani makeup tayi ba sai powder kawai da lipstick da ta shafa, Bedroom ɗin DOCTOR ta shige jin shuru bai fito ba, yana kwance rungume da photo ko tashi baiyi ba da alamu yau baza shi aiki ba, ƙarasawa bakin bed ɗin Falmata tayi ta zauna tana ƙare masa kallo cikin so da ƙauna, ji take tamkar ta kwanta jikin mijinta, sai babu halin hakan saboda gujewa masifar sa, a hankali tasa hanu ta zare photon daga ƙirjinsa ta maida kallon ta zuwa ga photon “JALILA” ta furta a hankali, ajiyesa tayi a gefe tare da tashi ta shige Tollet ɗinsa, wankewa tayi tas tasa air freshener a ciki sannan ta fito daining ta ƙarasa, indomie kawai taci tare da tea ta tashi, Bedroom ɗin ta ta koma ta ɗauki Mayafinta ta saka tare da bag ɗinta, hand out ɗin ta shima ta ɗauka tare da wayarta ta fito, a falo ta tsaya ta rubuta masa a takadda, “NA TAFI SCHOOL SABODA ZAMU FARA TEXT SANNAN ZANBI GIDA NA DUBA JIKIN UMMA.” sanda tazo bakin ged ɗin gidan musa ya taho da sauri yana cewa.

” Ranki ya daɗe Hajiya unguwa zaki fita ne haka da safe.”

Murmushi Falmata tayi tare da cewa.

” Wallahi school zani Musa, ga wannan takaddar idan DOCTOR ya fito dan Allah ka basa bai tashi a bacci ba, ni kuma zanyi let na tsaya.”

Karɓa Musa yayi yana cewa.

” Insha Allah Hajiya zan isar masa a dawo lafiya Allah ya tsare.”

Da ameen Falmata ta amsa tana ficewa, sanda ta kusa nufo titi sannan ta tuna da babu kuɗin adaidaita a hanunta, “Ya Salam” ta furta hanunta tasa a jaka ta ɗauko wayarta numbern Maji ta kira, tana ɗagawa tace.

” Kina makarantar ne ko gida.”?

Daga can Maji tace.

” Ina school yanzun nan na shigo, wani abune.?”

” Ehh na fito ne kuma babu kuɗin adaidaita a hanuna, akwai kuɗi a hanunki ne, idan na ƙaraso sai na karɓa na basa, nayi let ne babu halin na tsaya ko pos na cire kuɗi.”

Murmushi Maji tayi dake zaune gindin wata bishiya ita da Uwani tace.

” Ki hau ki taho akwai kuɗi Amma fa kuyi sauri domin an kusa shiga lecture.”

” Insha Allah yanzu zan ƙaraso.”

Ta ƙarasa maganar tana katse kiran, bata juma tsaye bama kuwa sai ga adaidaita, tare sa tayi ta hau tare da cewa University Of MAIDUGURI zaka sauƙe ni, amma zamu shiga ciki.

Ɗari biyu mai adaidaitan yace mata babu musu ta hau, har cikin jami’ar ya kaita, Maji ta kira a waya tare da faɗa mata inda suke, ba’a juma ba Maji ta ƙaraso tana cewa.

” Nawa ne kuɗin nasa.”

” 200 Naira” Falmata tace, Maji 500 ta basa ya basu sanji sannan suka jera Maji ne ta dubi Falmata tare da cewa.

” Makarantar nan harta fara mantawa dake, nayi zaton ma bazaki zoba.”

” Me zai hanani zuwa Maji, ai tunda nace miki zanzo to zanzo, yanzu inda matsalar take, karatun da aka wuce ni.”

Numfashi Maji ta sauƙe tace.

” Gaskiya akwai matsala, amma ba damuwa akwai Allah, ke dai kawai ki dage ki fahimci darasin gaba.”

” Insha Allah, ina Uwani ne ban ganku tare ba.”

” Wajen ta muka nufa ai yanzu.”

” Ok” tace har suka ƙarasa gindin bishiyar da Maji tabar Uwani, zama sukayi uwani tace.

” Wata sabon gani ke kuma baiwar shikenan sai kika mana hijira kika daina zuwa school.”

Hararar Uwani Falmata tayi tace.

” Shine kuma baki nemeni ba, kiji ko lafiyata kekam Uwani kikayi wasa igiyar zumunci sai ta zargeki.”

Uwani dariya tayi tace.

” Bani da zumunci ko bamu da zumunci ke zumuncin ne dake, ko neman mutane ke kike.”?

Dariya sosai Maji tayi tana cewa.

” To kaji har kun fara faɗan naku kenan daga haɗuwar ku gaisuwar da zaku fara kenan.”

Falmata cewa tayi.

” Oh mune ma kajin kenan, amma dai kin faɗa mana ba suga, KUMA bashi kikaci sai mun rama ko Uwansis”

” Ƙwarai kuwa kowa ai yaci tuwo damu miya yasha, daram zamu rama.”

Dariya Maji tayi tana cewa.

” Oho haɗe min baki kuma zakuyi, shikenan sai dai ku rame ba dai ku rama ba, kinga Falmata tashi mu shiga class time ya cika gara Uwani sai 12 zata shiga lectures ɗin ta.”

Tashi sukayi suka bar Uwani a wajen suka shige department ɗinsu, suna shiga class ɗin Kuma SIR AHMAD ya shigo wanda yake ɗaukar su lecture ɗin Chemistry gaishesa sukayi ya amsa yana kai dubansa ga Falmata, sosai yake kallon ta tamkar zai cinyeta, lura da hakan da Falmata tayi ya sata kawar da kanta gefe tana haɗa fuskar ta tamau, Murmushi Maji tayi yanda taga Falmata ta haɗa fuska daidai kunnen Falmata Maji ta mata raɗa.

” Maza da yawa suna bukatar shi kuma wannan shashashan mijin naki yana wulaƙanta ki.”

Hararar Maji Falmata tayi tare da ce mata.

” Bana son wulaƙanci mijin nawa kike kira shasha, su dai masu bibiyar matan Auren sune shashashu.”

Dariya kawai Maji tayi ta maida hankalin ta ga lectures da ya fara, duk rabin lecture ɗin da Sir Ahmad yake yi hankalinsa yana kan Falmata harya gama ya fita.

Ƙarfe 12 daidai suka fito daga lectures ɗin, a gajiye Falmata ta fito kasancewar ta kwana biyu batayi zama irin na yau ba, waje suka samu suka zauna, Falmata ranta a dagule tace.

” Maji meya kawo HABEEB gidana jiya.?”

Taɓe bakin ta Maji tayi tace.

” Nine na turo sa?”

” Ke kika turosa akan me zaki turo min shi gidana, kinsan yanzu haka kin haddasa matsala.”

Maji cike da mamaki tace.

” Matsala kuma wacce irin matsala, har akwai wata matsala wacce tafi wanda kike ciki a gidan Auren ki.?”

Falmata cikin faɗa tace.

” Hmmm Maji kenan, akwai domin kuwa Allah kaɗai yasan abinda zai faru tsakanin HABEEB da DOCTOR, Tunda yace bazai ƙyale HABEEB ya keta masa haddi, kuma DOCTOR yana da gaskiya HABEEB mahaukaci ne shi da zai shigo gidan matar Aure meye haɗina dashi, nifa nama manta sa a rayuwata, sannan ai kema bai dace ace ki turo sa cikin gida na ba.”

Tunda Falmata ta fara Magana Maji take dubanta sanda ta dasa aya sannan tace.

” To uwata tashi ki dakeni akan sakaran mijinki tunda na saka ransa ya ɓaci, sai wani tayar min jijiyar wuya kike kamar wanda zaki dakeni, akan mutumin da baisan darajar ki ba, shi DOCTOR HASSAN ɗin dokar yake bi, ko shima ba sunnar Annabi yake takawa ba, kinga Malama na turo HABEEB ne domin kuwa shine kawai damar da nake dashi na hana mutuwar Auren ki, tunda nasan gabar dake tsakanin HABEEB da DOCTOR har yanzu tana nan sannan muddun DOCTOR yasan cewa har yanzu HABEEB yana sonki zai kuma iya Auren ki idan DOCTOR ya rabu dake, nasan bazai yarda ya rabu dake ba, ko dan kar HABEEB ya Aure ki, sannan DOCTOR babu abinda ya isa ya yiwa HABEEB, Tunda ranki ya ɓaci na ɓatawa ubanki rai kiyi hkr.”

Maji ta karasa maganar tana tashi cikin ɓacin rai zata bar wajen, Falmata ta kamo hanunta tana cewa.

” Kiyi hkr ƙawata ki zauna.”

” Me zan zauna na miki na zauna kina ɗaga min jijiyar wuya ne saboda mutumin da baisan darajar ki ba.”

” Ki daiyi hkr ƙawata ki zauna ki fahimce ni.”

Zama Maji tayi sannan Falmata tace.

” Kin kasa fahimta ta, Maji, kinsan yanda nake son Doctor ina gudun abinda zai jamin matsala dashi bana son rabuwa dashi, yanzu kamar wanda yake jirana ina kuskura kaɗan zai samu ƙofar da zai ce zai sakeni shiyasa nake razane da zuwan da HABEEB yayi gidana.”

Maji cikin takaici da haushin Falmata tace.

” Zaki rabu dashi sanda ya kashe ki da baƙin ciki, idan aka binne ki, sai naga taya zaki dawo garesa, Falmata wai wani irin makahon so kike yiwa HASSAN meyasa bakya hango aibunsa ne, Falmata anya kuwa akwai zuciya a ƙirjinki, shi namiji girman kai garesa daga sanda ya fahimci Soyayyar da mace take masa yafi wanda yake mata, to daga wannan ranar zai fara takaki saboda yana ganin bazaki iya rabuwa dashi ba, har yanzu Falmata ke ɗalibace a soyayya naga alama ya kamata ki dinga ɓoyewa DOCTOR zalamar Soyayyar ki, ki dinga nuna masa ɓacin ranki domin nemawa kanki yanci, bawai ki tsaya namiji yana cin mutuncin iyayenki da naki ba, wannan ba daidai bane.”

Numfashi Falmata ta sauƙe tare da cewa.

” Maji meyasa bakya son Doctor, tun can baya baki sona dashi, baki taɓa faɗar alkairin sa ba sai dai aibunsa, amma ai kema kinsan DOCTOR yana sona wannan al’amari ne kawai ya kawo matsala a tsakanin mu amma ke kullum kina kama hanuna akan hanyar barin rayuwar DOCTOR.”

Murmushi Maji tayi tace.

” Ba son Doctor bane bana yi, dama tun baya bai dace da rayuwarki ba, makahuwar Soyayyar sane kawai yasa kika kasa fahimtar hakan, sannan ba aibunsa nake faɗa ba, halinsa nake faɗa, nifa Falmata ina kama hanunki akan hanyar gaskiya, domin inganta rayuwar ki, amma ke ƙoƙarin fisgewa kike zuwa baƙar hanya wacce bata da wajen ɓullewa.”

” DOCTOR shine Wanda yafi ko wani namiji dacewa da rayuwata, wannan makahuwar Soyayyar da nake masa ita ake kira Soyayyar gaskiya tunda wahalar da nake sha bata sa na gujesa ba, Maji Hanyar da nake kai itace mai ɓulle min ba hanyar da kike kaini ba.”

Murmushi kawai Maji tayi tana kaɗa kanta cike da tausayin Falmata tace.

” Ai bazaki fahimce ni ba Falmata, amma lokaci zaizo sanda zaki ce na faɗa miki amm…………..”

Ƙarasowar Wata budurwa wajen da Sallama yasa Maji bata ƙarasa maganar da tayi niyya ba amsawa sukayi budurwar tace.

” Sir Ahmad ne yace wai FATUMA ABUBAKAR BUKAR tazo ta samesa a office ɗinsa.”

Kallon Maji Falmata tayi tace ..

” Kije kice bazanzo ba”

Maji cewa tayi.

” Kije kice tana zuwa.”

Juyawa budurwar tayi ta tafi, Falmata zatayi magana Maji ta ɗaga mata hanu.

” Ni ba jahila bace nasan ke matar Aure ce, amma ki sani shi malamin kine bai kuma furta miki yana sonki ba, kuma kin kwana biyu bakya zuwa makaranta dan haka baki san kiran da yake miki ba, kije kiji, ina jiran ki sai kizo mu wuce gida tunda kince gidan ku zaki wuce.”

Falmata bata ce komai ba ta tashi ta nufi office ɗin da Sallama ta shiga amsawa yayi yana gyara zaman glass ɗin idanunsa ya mata nuni da ta zauna.

” Sir gani ance kana kira na.”

Murmushi ya saki tare da cewa.

” Eh ni nayi kiran ki, me yake hanaki zuwa makaranta kwana biyu.”

” Sir bani da lafiya shiyasa.”

” Subabanallah sannu, ai ban sani ba da naje na duba ki.”

Da sauri ta ɗago kanta ta kallesa tare da cewa.

” Sir zan iya tafiya ana jira nane.”

” A’a bamuyi Maganar da yasa na kiraki ba “..

” To sir ina sauraronka sauri nake.”

Murmushi ya saki tare da zare glass ɗin idanunsa yace.

” I love You fatuma, na juma ina sonki, tun sanda na fara ganinki a cikin school ɗin nan Allah ya jarabceni da sonki, kuma Auren ki nake son nayi dan Allah ki yadda ki aureni.”

A razane ta ɗago kai ta kallesa zuciyarta na bugawa dam!!! Dam!!! Dam!!!!

Tirƙashi wai dama AHMAD baisan Falmata tana da Aure bane?

Ku biyoni domin jin amsar ku.

Ku biya ku karanta cikin kwanciyar hankali.

Kuna iya nuna min soyayya ta hanyar siyen littafinan na DOCTOR HASSAN akan Naira 300 kacal,zaku iya biya ta wannan account ɗin 0006064512 RASHIDA USMAN JAIZ BANK ko kuma ku tura katin MTN ta wannan number 08147537180,sannan ku tura shaidar biya a ita ko a 08147537180 Nagode masoya,ina maraba da masu sayan ɗaya ko sari

Dan Allah masu turo min VTU su daina numbobin katin kawai nake buƙata ko transfer to bank account ɗina🤲🏻

Vote
Share
And Comment

ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻

(UMMU NASMAH CE)
[9/4, 2:43 PM] Ummu Nasmah❤️❤️❤️❤️: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

            💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

❤️ Love and romantic and funny story ❤️

Na

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*

Marubuciyar nan taku ta INDO A BIRNI

Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a duk inda kuke so da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.

Waɗanda suka ce Document ɗin Ruɗanin Zuciya biyu suke so, to ga dama ta samu na gama na kuma haɗa Complete document idan kina so zaki samesa a 200 Naira only 08147537180.

بسم الله الرحمن الرحيم

________________________

🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼
🇦SSOCIATION🤝🏻
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

     *Book One*

Page 21 to 22

________________________

_✍🏻 Falmata kamar sauƙar ruwan zafi taji Maganar sa a ranta ” Wai i love You” duban sa tayi tare da cewa.

” Sorry Sir nifa matar Aure ce.”

Murmushi AHMAD yayi yace

” Nima mijin Aure ne ai, serious da gaske sonki nake fatuma domin kuwa ban taɓa ganin macen da tamin domin na Aura ta ba, sai ke tun sanda na ganki nasan cewa na samu matar Aure.”

Zuwa yanzu Falmata ranta ya fara barazanar ɓaci, miƙewa tayi tsaye cikin ɓacin rai tace.

” Sorry Sir kayi hkr ni ba matar Auren ka bane domin kuwa ina da nawa mijin nima ba wasa nake maka ba, dan Allah karka ƙara kira min soyayya, ina da miji kuna ina sonsa kuma kasan darajar Aure kayi hkr Allah ya baka wata matar Auren wacce ma ta fini.”

Tana gama faɗin haka ta juya ta tafi har tazo bakin ƙofa taji muryar sa yana cewa.

” Idan har da gaske kina da Aure, to mijinki bai iya riƙe mace da daraja ba domin kuwa babu annurin Aure a jikinki, ki faɗa masa ya riƙeki da kyau idan bazai iya ba, ya sakar mana mu zamu iya, karki manta da ina sonki ki riƙe wannan a ranki.”

Sosai Falmata taji zafin maganganun AHMAD tsuka kawai taja tare da ficewa, shi kuwa murmushi ya saki har yanzu zuciyarsa bata yadda matar Aure bace ita, ” amma zanyi bincike a kanki” ya furta yana mai da hankalin sa kan takaddar dake gabansa.

Ranta a ɓace Falmata ta nufo Maji tace ” mu tafi.” Tafiyar sukayi sanda sukayi nisa Maji tace

” Wai ya naga kin fito ranki a ɓace meya faru.”?

Numfashi Falmata ta sauƙe suna tare a daidaita sanda suka hau sannan Falmata tace.

” Mutumin nan bashi da hankali wai cewa yayi yana sona Mtsss.”

” May be bai san kina da Aure bane shiyasa yace yana sonki.”

Murmushi Falmata tayi tare da cewa.

” Da farko na masa wannan uzurin na sanar dashi ina da Aure, amma tsabar mutumin nan tantirin ɗan duniya ne sai bai yarda ba, cemin yayi shima mijin Aure ne kiji ɗan iska fa.”

Dariya maganar ta bawa Maji kafin tace.

” Ikon kuma ya kuka ƙare dashi.”?

” Ya kuwa zamu ƙare banda sanda na MAIMAITA masa da gaske ina da Aure ke kinji baƙar maganar da ya faɗa min, wai harda cewa idan har da gaske ina da Aure to mijina bai iya riƙe mace ba, domin babu annurin Aure a jikina, na sanar da mijina idan bazai iya ba, to ya sakeni su zasu iya, kiji fa wata magana marar daɗi jin sai kace a goshi ake rubuta tambarin Auren.”

Dariya sosai Maji take sanda tayi dariyar ta isheta sannan tace.

” Ikon Allah Shidai Hassan ya shiga Uku da bakin al’umma wallahi baki ya masa yawa da zai gane daya gyara kafin lokaci ya ƙure masa, kinga wanda baisan zamantakewar ki da mijinki bama abinda yace, Allah dai ya kyauta.”

Tsuka Falmata taja cike da jin haushin Maji tace.

” Ya Isa malama mubar zancen nan, naga kina neman shige min hanci da ƙudunduno zaki fara zage min miji dake kin tsanesa.”

Dariya Maji tayi tace.

” Allah ya baki haƙuri Mrs Romio, Ke kuma baki son a zagi habibin ki ba, to Allah ya kawo miki sauƙi cikin lamuran ki ƙawata ya dawo muku da soyayyar ku shikenan abinda kike so kiji nace ko.”

Murmushi Falmata tayi tare da cewa.

” Yauwa abinda ya kamata ki dinga min kenan, ba aibata min miji ba.”

Dariya Maji tayi suka kama wani taɗin duniya har suka iso ƙafar gidan su Maji tare suka sauƙa Maji ta biya kuɗin, Falmata shiga gidan su Maji tayi da niyar gaishe da mamanta kafin ta fito ta wuce gidan su.

Shi kuwa DOCTOR bayan ya tashi daga bacci wanka yayi, kafin ya fito falo da jallabiya a jikin sa, kai tsaye daining ya nufa, tea da ƙwai kawai yasha sannan ya tashi ya dawo tsakiyar falon tv ya kunna ya fara kallon BBC News yafi 1hrs yana falon baiji motsin Falmata ba, kuma bai damu ya duba ta ba, sanda ya ga 12 daidai sannan ya tashi Bedroom ɗinsa ya wuce ya ɗauki kay ɗinsa da wayoyin sa ya fito, Motar sa ya buɗe ya shiga ya tayar Musa mai gadi get ya wangale da sauri, sanda DOCTOR yazo daidai get ɗin ya tsaya tare da cewa.

” Malam Musa, kana lafiya ya mai jikin dai.”

Dariya musa yayi yace.

” Lafiya lau ranka ya daɗe mai jiki da sauƙi, yauwa ga wannan takardar Madam tace a baka ɗazu da safe kafin ta fita.”

Cikin mamaki DOCTOR ya karɓi takaddar sai dai bai nunawa Musa wani abu a fuska ba ya buɗe takaddar karantawa yayi ya ajiye sannan yaja motar sa ya fice, Musa get ɗin ya rufe ya koma ya cigaba da jin rediyo ɗinsa, DOCTOR gidan su ya nufa wajen umman sa, bayan yayi parking ne ya shiga cikin gidan domin kuwa yau babu kowa ƙofar gidan su, Fanna da gudu ta faɗa jikin DOCTOR tace.

” Oyoyo Yayana”

Murmushi DOCTOR yayi tare da shafa kan Fanna yace.

” My dear sister har yanzu baki san kin girma ba ko, ina Hajjo naji gidan shuru.”

Dariya Fanna tayi tace.

” Suna cikin ɗakin Umma malam sani ne yazo yake mata ruƙƙiya harda Kawu Dauda ma.”

” Okay” ya furta tare da cire Fanna daga jikinsa ya shige cikin ɗakin baice komai ba ya zauna a gefe yana kallon yanda Umman sa take wani irin motsi sanda ake mata addu’ar sanda aka gama sannan malam Sani ya miƙawa DOCTOR hanu sukayi musabaha cewa yayi.

” Hassan jiya BELLO ya sanar dani gobe zaku kai mahaifiyar ku wajen MALAM GANA a can BINISHED, gaskiya naji daɗi sosai domin kuwa sahihin malami ne yana aikin sa da gaskiya, kuma ana dace sosai idan anje wajen sa Allah yasa aje a dace, sannan munanan muna yiwa mahaifinku addu’a insha Allah zai bayyana, idan kunje ku sanar da malam Gana maganar ɓacewar mahaifin naku ko Allah zaisa a samu wani taimako daga garesa.

DOCTOR cike da girmamawa yace.

” Insha Allah Malam zamu sanar dashi, kuma a cigaba da mana addu’a kamar yadda kuke mana kullum, na gode sosai mlm”

Kawu Dauda ne yace.

” BINISHED kuma, wajen wani malamin zakuje baku sanar dani ba, maganin da muke anan bai isa ba har sai anje BINISHED, to bazai yuwu ba, babu inda za’aje ai duk inda ya kamata aje anje ba’a samu sauƙi ba dan haka, muyi hkr mu zauna mu cigaba da neman magani a gida ba sai munje wani BINISHED ba.”

Cike da mamaki DOCTOR yake bin Kawu Dauda da kallo, kafin yace.

” Kawu magani fa zamuje nema, meyasa to zaka ce karmu je, ai ba’a gajiya da neman magani, haka zamu zauna muta kallon Umma cikin ciwo, gaskiya Kawu kayi hkr zamuje BINISHED gobe bazan iya jurewa kallon Umma a halin da take ciki ba.”

Mlm Sani ne yace.

” Tabbas wannan yaron yana da gaskiya Dauda ba’a gajiya da neman magani, komai nisan waje indai za’a samu magani to za’a je bare kuma shi wannan malamin mawuyacin abune aje wajen sa ba’a dace ba, sai dai kuma idan cutar mutuwa ce.”

Kawu Dauda cewa yayi.

” Mlm Sani wannan ciwon na YAMURAM wani irin magani ne ba’a nema masa ba, ina ne ba’a jeba, dan haka babu inda za’a je da ita”, ya faɗi maganar kamar wanda hankalin sa yake tashe ga Kuma goshin sa daya tsatstsafo da zufa.

DOCTOR cike da damuwa yace.

” But amma Kawu……….”

Ɗaga masa hanu Kawu Dauda yayi tare da cewa.

” Ni ƙanin mahaifiyar ku ce baku fini sonta ba, kuma dole kubi umarni na, babu inda za’a kaimin ƴar uwa.”

Malam Sani zubawa DOCTOR Ido yayi cike da mamakin yanda ya gigice lokaci guda jin an ambaci za’aje wajen Malam Gana ko meyasa oho, Allah ya kyauta Malam sani yace tare da tashi ya fice.

DOCTOR shuru yayi kasancewar yana yiwa Kawu Dauda biyayya Kamar yadda yake yiwa Umman sa, sai dai hankalin sa yayi matuƙar tashi jin abinda Kawu Dauda yace, sai dai yana ji a cikin zuciyarsa bazai iya haƙura da zuwa BINISHED gobe, Falmata ce tayi sallama ta shigo cikin ɗakin Fanna kauda kanta gefe tayi ganin Falmata, Hajjo dake zaune gefe itace ta amsa mata sallamar, Hajjo ta gaishar cikin sakin fuska ta amsa mata.

” Aunty Hajjo ya jikin……..”

Bata ƙarasa ba DOCTOR ya daka mata tsawa.

” Keeee!!!! Tashi ki fita ki bar gidan nan tunda ba ɓangaren ubanki bane, an baki wani munafurcin ne ki kawo, fita karki kuma shigowa sashin nan ficeee manaaaa!!!!”

Ya ƙarasa maganar cikin tsawa, Falmata kallo tabi DOCTOR dashi cikin zafin zuciya, tashi tayi ranta na ƙuna yayin da idanunta suke zubar da hawaye ta fita daga ɗakin, Hajjo ma sosai ranta ya ɓaci da abinda DOCTOR ya yiwa Falmata cikin ɓacin rai tace.

” Meye kayi haka Hassan, dama ashe da gaske ne abinda yake yawo a cikin unguwa cewa kana wulaƙanta matar ka, matar kace fa ta SUNNAH kake yiwa wannan cin zarafin akan gabarku ta banza wacce zargi kawai kuke baku da tabbas akai, wallahi gaji tsoron Allah ka daina wulaƙanta Aure, ko akwai laifin iyayenta ita meye laifinta, ko laifin iyayenta shine nata laifin, ka dawo hankalin ka, ka ɗauki abinda ya samu iyayenku a matsayin ƙaddarar da Allah ya ɗaura musu, kana Cutar da yarinyar da bataji ba bata gani ba, wallahi idan ka kuskura ka rabu Fatuma bazaka kuma samun mace ta kirki irinta ba, yau naga haukar banza, yanzu kai idan an hukunta ka da laifin iyayenka zakaji daɗi, to karna kuma ji karna gani ka ƙara wulaƙanta wannan yarinyar albarkar.”

Shuru DOCTOR yayi kansa a sunkuye zaiyi Magana cikin zafin rai Hajjo tace.

” Karka cemin, bana son ji domin kuwa duk abinda zai fito daga bakinka akan Falmata shirme ne, ka tashi kaje ka sami Bello ku shirya tafiyar da zamuyi BINISHED gobe, ka barni da Kawu Dauda ni zanji dashi dole gobe zamu tafi.”

Kaɗa KANSA kawai DOCTOR yayi tare da tashi ya ficewa, yau ko kallon part ɗin su Hajja bai ƙalla ba saboda yana jin haushin ta ya bar gidan.

Hajjo rankwashin Fanna tayi tana cewa.

” Wato kema kinbi sahun ɗan uwanki ko, kina biye masa akan zuciyarsa ta banza.”

Tura bakin ta Fanna tayi bata ce komai ba ta yi shuru.

Ita kuwa Falmata sanda ta tsaya ta goge hawayen ta sannan ta shige cikin sashin su, babu Kowa tsakar gidan duk suna cikin ɗaki, ɗakin Mahaifiyarta ta shiga da Sallama Aunty YANA dake zaune ta amsa mata zama Falmata tayi tana duban Aunty YANA tace.

” Ina kwana Mama.”

Aunty YANA amsawa tayi da lafiya tana hararar Falmata juyowa tayi ta fuskancesa tare da cewa.

” Wato Falmata kin raina ni, kin zaɓi sakaran mijinki a kaina ko.”?

” Na raina ki kuma Mama, mena miki.”

Aunty YANA cike da hasala tace.

” Ubanki kika min!!! Nace ubanki kika min dan ubanki har ni zan aiki Yagana da saƙo har gidan ki, ki saka a dawo min dashi kice wai bazaki iya Cutar da mijinki ba kega wacce kika fi kowa tsoron Allah, to aishi zai iya cutar dake, shashashar banza kin zauna namiji sai taka ki yake kamar kare.”

Shuru Falmata tayi bata cewa Aunty YANA komai ba, harta gama faɗanta sanda ta gama sannan Falmata tace.

” Kiyi hkr mama Allah ya huci Zuciyaki.”

Aunty YANA cewa tayi

” Yanzu me kika zoyi.?”

” UMMA na biyo na duba da jikinta.”

” Okay kin shiga ne.?”

” Ehh na shiga, bari ma na shiga wajen Hajja na fito zan tafi .”

” Hajja bata nan ta fita gaisuwar mutuwa ɗazun nan, daga zuwan naki zaki tafi yanzu fa kika shigo.”

” Mama ai dama ba jumawa zanyi ba, ba wuni na tambaya ba, duba jikin Umma kawai na tambaya.”

Taɓe bakin ta Aunty YANA tayi tare da tashi ta buɗe drowern ta, layar nan ta ɗauko tare da miƙawa Falmata, shuru Falmata tayi tana bin layar da kallo, tsawa Aunty YANA ta mata tana cewa.

” Karɓiii!!!! Mana kina kallo na, ki saka a ƙasan katifar mijinki, wannan wulaƙanci da yake miki yazo ƙarshe, Falmata ki fahimce ni, ƙaunar ki tasa na karɓo wannan layar, zuciyata bata jin daɗin abinda mijinki yake miki, bazan cutar da rayuwarki ba, dan Allah Falmata kiyi amfani da wannan layar domin samawa kanki kwanciyar hankali cikin gidan Auren ki.”

Shuru Falmata tayi tare da saka hanu ta karɓi layar cikin mutuwar jiki, tabbas tasan kalaman mahaifiyar ta gaskiya ne, babu uwar da zataji daɗi taga ana wulaƙanta mata ɗan ta a gidan Auren sa, jakarta ta buɗe ta saka layar sannan ta tashi tana cewa………….

FREE PAGE YA KUSA ZUWA ƘARSHE SAURA 2 PAGE IDAN KINA SON CIGABA DA KARANTA LITTAFIN NAN BIYA KUƊIN KI TA 👇🏻

Kuna iya nuna min soyayya ta hanyar siyen littafinan na DOCTOR HASSAN akan Naira 300 kacal,zaku iya biya ta wannan account ɗin 0006064512 RASHIDA USMAN JAIZ BANK ko kuma ku tura katin MTN ta wannan number 08147537180,sannan ku tura shaidar biya a ita ko a 08147537180 Nagode masoya,ina maraba da masu sayan ɗaya ko sari

Vote
Share
And comment

ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻

(UMMU NASMAH CE)
[9/5, 9:29 PM] Ummu Nasmah❤️❤️❤️❤️: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

            💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

Love and romance and funny story

Writing by

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*

Marubuciyar nan taku ta INDO A BIRNI

Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a ko yaushe, da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.

Special Gift to

Masoyan Asali waɗanda suka kasance dani a cikin book ɗina na kuɗi wanda ya gabata wato Ruɗanin Zuciya biyu kun sayi wannan book ɗin fiye da zato na Tabbas kun nuna min ƙauna domin kuwa hakan ya gwada min kuna tare dani ako yaushe koda kuɗi ko babu nima dai Ummu Nasmah ina ƙaunar ku🥰

بسم الله الرحمن الرحيم

________________________

🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼
🇦SSOCIATION🤝🏻
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

     *BOOK ONE*

PAGE 23 to 24

_________________________

__✍🏻 ” Shikenan zanyi yanda kikace Mama na gode ni zan wuce.”

Murmushi Aunty YANA tayi tare da cewa.

” Yauwa ƴar albarka ko ke fa, raina ɓaci yake idan ina jin labarin abinda yake miki, wallahi muddun kinyi amfani da layar nan dai dai to Tabbas, Hassan zai dawo hanun mu ke ko cewa kikayi ya miki shara wallahi sai yayi, kije ki jarraba Allah yasa mu dace.”

Da to Falmata ta amsa tana cewa.

” Mama ɗari biyar nake so zanyi adaidaita idan akwai kuɗin a hanunki “

Aunty YANA cewa tayi.

” Oh Allah ya wadaran naka ya lalace, yanzu kuɗin adaidaita ma baki dashi kuma wai a haka mijinki yana da kuɗi, kai Falmata wannan Auren naki sam babu daɗi”

tsuka taja tare da ɗauko 500 ɗin ta bata, ita dai Falmata bata ce komai ba ta karɓa ta fito, da har zata shiga tayiwa Aunty Hajjo Sallama sai kuma ta fasa tuno walaƙanta ta da DOCTOR yayi, fita tayi ba tare da ta koma ba, a daidaita ta tara tace masa Gra zai kaita bayan ta haune sunyi nisa da tafiya, ta buɗe jakarta hanu tasa ta ciro layar da Aunty YANA ta bata, ƙarewa layar kallo take cikin zuciyarta take cewa ( Allah ka tsareni da saɓa maka Allah karka jarabci zuciyata da faɗawa ga hallaka saboda Soyayyar da nake yiwa DOCTOR, ko wannan layar dana karɓa wajen Mama na karɓa ne kawai saboda gujewa ɓacin ranta amma ba dan nayi amfani dashi ba) wurgar da layar tayi tana lumshe idanunta hawaye na gangaro mata, hanu tasa ta goge hawayen tare da nemawa mahaifiyar tata shiriyar Ubangiji, da wannan nazarin mai adaidaita ya sauƙeta a ƙofar gidan ta, kuɗin sa ta basa tare da buga get ɗin Musa ne ya leƙo tare da buɗewa da sauri yana cewa.

” Barka da dawowa ranki shi daɗe, na bawa Oga sakonki ai tun ɗazu ban manta ba.”

Murmushi Falmata tayi tare da cewa.

” To na gode musa, Ladiyo ta kawo maka abincin rana kuwa.?”

Musa yana dariya yace.

” Eh ta kawo min jalop ɗin shinkafa kuma taji kifi ranki shi daɗe ai Ladiyo ba dai iya girki ba alƙur’an rangaɗaɗau take girki kamar kunnen mutum zai cire, idan ba karnayi ƙarya ba sai nace ma ta fiki iya girki.” Sai kuma yayi saurin toshe bakin sa yace ” Oh yi hkr Uwar gidan Oga aradu baki nane ya zarme.”

Dariya Falmata tayi tana tafiya tare da cewa.

” Lallai kace Ladiyo ta karɓi numbern yabo na girki a gidan nan to nima Allah ya sani a danshin ta”

” Sosai ma kuwa dan har Oga yana yabon girkin ta.”

Dariya kawai Falmata tayi ta shige part ɗinta a zatonta doctor gida ya dawo tana shigowa kuma sai taga baya nan Bedroom ɗinta ta shige tayi wanka, three cuttern wando tasa da best sai wata ƙaramar hula faɗawa tayi saman bed yunwa takeji haɗe da bacci, sai dai baccin yafi ci mata jiki, lumshe idanunta tayi bata kuma juma da kwanciyar ba bacci ya sace ta.

Shi kuwa DOCTOR daga, gidan su, Companyn HABEEB ya nufa, kai tsaye, sakatariyar sa ya yiwa Magana kan cewa taje tace wa ubanginta DOCTOR HASSAN ya iso, tashi kuwa tayi taje ta sanar dashi ba’a juma ba, ta fito tare da sanar dashi cewa ya shiga, DOCTOR cike da izza da kuma zafin rai ya shiga, zama yayi ba tare da HABEEB ya basa izini ba, ƙafarsa ya ɗaura ɗaya kan ɗaya fuskar sa na ɗaure tamau, murmushi HABEEB ya saki dake riƙe da biro yana ƙarewa DOCTOR kallo, hanu ya miƙa masa tare da cewa.

” Barka da zuwa masana’antar HABEEB, Likita bokan Turai DOCTOR HASSAN A MALA.”

Taɓe bakin sa DOCTOR yayi yana cije leɓensa yace.

” Bana haɗa hanu da kare wanda bai san darajar Aure ba.”

HABEEB yaji zafin kalmar kare da DOCTOR ya kirasa dashi sai dai a maimakon ya nuna masa ɓacin ransa sai murmushi mai sauti da ya saki tare da cewa.

” Ehh ai a wani lokacin gara kare akan jaki wanda shi kullum bai san abu mai mahimmanci daya kamata ya riƙe ba komai wulaƙantawa yake ciki harda abu mai mahimmanci tsabar rashin sanin darajar kai irin na jaki, shi kuwa kare ai yasan alkairi domin kuwa yana riƙe amanar uban gidansa da kuma mutanen da yake tare dasu, harda wanda ya masa alkairi, shi kuwa jaki ko kaɗan baya gane daidai yafi gane yaji duka kafin ya gyara dalilin kenan da yasa karen shigowa gidan wannan jakin domin ya masa bulala ɗaya ko zai dawo cikin hankalin sa.”

Runtse idanunsa DOCTOR yayi yana jin maganar HABEEB tamkar ana caka masa mashi a cikin ƙahon zuciyarsa wato shine ma jakin, cije leɓensa yayi a fusace ya daki teburin dake gaban HABEEB yace.

” Ya Isa!!!!! Haka maci amanar Allah, kai har kana da bakin da zaka gaya min Magana, gargaɗi nazo na maka ka fita a harkar matata idan ba haka ba, wallahi sai na wulaƙanta rayuwarka, kasan halina sarai tamkar yunwar cikin ka.”

Dariya HABEEB yasa har dumple ɗinsa yana lotsawa fararen wushiryarsa suka bayyana, cikin dariyar ya miƙe tsaye tare da cewa.

” Kaga banbancin mai hankali da mahaukaci shi mai hankali duk sanda aka ɓata masa rai ko aka tsokanesa baya nuna fushin sa bare kuma fusatar sa, saɓanin mahaukaci da baya iya jure tsokana, kaga kenan ko a nan ka nuna min halin ka na jakuna, malam Hassan baka iya riƙe Aure ba kaje ka koyi yanda ake kula da mace daga nan sai ka dawo ka min gargaɗin ” kofa HABEEB ya nunawa DOCTOR yace ” fice min daga office kafin nasa security suyi waje dakai a wulaƙance domin kuwa daga ni har kai munsan halin juna, sannan kasa a ranka ko yau nayi niyyar ƙwace Falmata a hanunka, 10 hours sunyi yawa Auren ku ya ƙare, ko ranar da naje gidan ka, naje ne kawai na ganta raina yayi sanyi saboda na juma ban ganta ba kasan dai irin son da nake mata, zaifi maka alkairi kaje ka rungumi matar ka, tunda tana sonka kafin lokaci ya ƙure maka, domin kuwa duk randa kayi sake lokaci ya ƙure maka ni kuma daga ranar nawa lokacin zai fara, tik!!! Tak!! Tik!! Tak!! Ka rabu da ita kenan, dan haka fice min a office.”

Wayyo Allah kuzo kuga ɓacin rai wajen DOCTOR dama Hausawa sunce idan baki yasan mai zai faɗa baisan me za’a mayar masa ba, ga dai DOCTOR shiya fara kiran HABEEB da kare, yazo kuma yafi HABEEB jin haushi, hanu DOCTOR ya ɗaga cike da ɓacin rai zai zabgawa HABEEB mari, kafin hanunsa ya isa fuskar HABEEB tuni HABEEB yasa hanu ya riƙe hanun DOCTOR yana cewa.

” Karka kuskura ka fara wannan babban kuskuren domin kuwa fuskata tafi ƙarfin mari, ko ubanda ya haifeni bai taɓa ba bare kuma kai, ina raga makane fa HASSAN saboda bana son mutunci na ya zube a gaban ma’aikata na, fice min daga office, idan ba haka ba wallahi zan wulaƙanta ka a cikin 1hrs kasan kuma zan iya.”

Wani irin huci DOCTOR yake idanunsa sunyi jawur, nuna HABEEB da yatsa yake yana ja da baya yana huci har yabar office ɗin, tsuka HABEEB yaja yana komawa ya zauna tare da dafe kansa yana jin wata sabuwar Soyayyar Falmata na bijiro masa, innalillahi ya fara furtawa yana koran sheɗan harya samu nutsuwa, aikin sa ya cigaba dayi cike da kwanciyar hankali.

Shi kuwa DOCTOR wani irin dreving yake idanunsa rufe tsabar ɓacin rai ikon Allah shine kawai ya dawo dashi gida parking yayi ya fito cike da ɓacin rai da gudu ya karasa part ɗin nasu, Ladiyo dake zaune tana kallo a falon sai da ta tsorata da ganin yanayin uban gidan nata, Bedroom ɗin Falmata ya shige yana ƙwala mata kira cike da ɓacin rai.

FALMATA!! FALMATA!! FALMATA!! FALMATA!!

Ita kuwa tayi nisa da baccin ta sam bataji kiransa ba, tsayawa yayi a kanta yana ƙare mata kallo, runtse idanunsa yayi yana jiyo kalaman HABEEB, a fusace ya saka hanunsa ya fisgo ta, da ƙarfi, ai kuwa a firgice ta farka zata danna ihu yasa hanunsa ya toshe mata baki yana saka hanu a bakin sa tare cewa.

” Shiiiiiii!!”

Shuru Falmata tayi tana zaro idanunta cike da tsoro, hanunsa yasa ya ja gashinta cike da mungunta ƙara Falmata tasa tana jin kanta na wani raɗaɗin azaba sake mata bakin yayi still yana riƙe da gashin nata yace.

” Ban taɓa ganin munafukar mace ba irin ki ballagaza wacce bata san mutuncin kanta ba, faɗa min a ina kuke haɗuwa da HABEEB, a ina kuke haɗuwa, wato ke ga jarababbiya ko saboda yanzu na daina haɗa shimfiɗa dake shine bari ki nemi HABEEB kuje ku lalace, kinyi asara wallahi, koda meye ma abun mamaki tunda kinsha nonon tsiya a wajen uwarki ai…………”

Wani irin hankaɗa Falmata ta yiwa DOCTOR HASSAN idanunta sun kaɗa sunyi jajur hawaye ne kawai yake gudu a saman fuskarta tunda DOCTOR yake walaƙanta ta bata taɓa jin zafinsa irin na yau, miƙewa tayi tsaye cike da ɓacin rai cikin tsawa tace.

” Ni ba munafuka bace saboda babu wanda na taɓa munafurta, Zagin iyayena ya isheka haka DOCTOR!!!!! Zan iya jure dukkan wani wulaƙancin ka amma bazan lamunci cin mutuncin iyaye ba, domin kuwa duk tsiya sune suka kawo ni duniya harka ganni ka aura, wato ma zargina kake ina Zina wa’iyazubillah ban taɓa kuma yanzu ma bazanyi ba, da ni jarababbiyar ce da kake faɗi da nayi zina tun sanda ka koya min mu’amala da ɗa namiji ka tafi India ka barni tsawon shekara bakwai da zanyi zina a wannan lokacin ya kamata nayi HABEEB ba mazinaci bane ko a gaban Ubangiji zan masa wannan shaidar, wa mai da baka san da nonon tsiyar nasha ba ka auro Ni, ya isheka DOCTOR cin mutuncin iyaye ya tsaya iya dole ka mutunta iyayena tunda har ka auri yarsu.”

Ta ƙarasa maganar tana kuka mai cin rai tare da jingunuwa jikin bango, DOCTOR Tunda ta fara Maganar ya saki baki yana kallon ta, yarinyar da duk sanda ya ƙuntata mata sai dai ta basa hkr yau itace take mayar masa da magana girgiza kansa yayi yana huci ya tunkaro gabanta hannayensa yasa ya dafe bangon da take jingine ya sunkuyo da kansa har suna jin numfashin juna yace.

” Kece kika fara mayar min Magana ina faɗa kina faɗa, Oh na fuskanta, kinje gida ɗazu ba, wannan uwar taki marar mutunci ta zugoki nace wannan Uwar taki marar mutunci ta zugoki ko.”

Cike da ɓacin rai Falmata ta ɗauke DOCTOR da mari ta tankaɗe sa gefe, riƙe fuskarsa DOCTOR yayi yana jin zuciya na taso masa jajayen idanunsa ya ɗago cikin mungun yanayi ya nuna ta da yatsa yace.

” Ni kika sa hanu kika mara saboda shegiyar Uwar ki, da kyau da kyau Falmata tabbas kin gwada min kin kai bazan saka hanu a jikin ki ba amma zan miki abinda yafi duka zafi dan haka kije na SAKE KI SAKI ƊAYA

Wani dum Falmata taji tare da wani jiri ” SAKI ta furta tana kallon DOCTOR cike da tashin hankali sai kuma tasa kuka, lokaci ɗaya kuma tayi shuru tana sauƙe ajiyar zuciya gabansa tazo ta tsaya tare da cewa.

” Ka sake ni kace, ni ka saka DOCTOR Saboda son zuciyarka, saboda kasan ina sonka bazan iya rayuwa babu kai, gaskiyar Maji ne tana faɗa mini bana yarda sai ga zancen ya fito yanzu, dama ku maza haka kuke da zarar kunga ta tana tsananin sonku ku kuma a wannan lokacin baku da abun wulaƙantawa sai ita, meye laifi na DOCTOR dan kawai na soka shine kuskure na, na gode amma ka sani Allah ya isa tsakani na da kai ka cuceni.”

Tana faɗin haka ta juya da sauri ta jawo akwatin ta, tsuka DOCTOR yaja tare da ficewa daga Bedroom ɗin, ita kuwa kayanta ta dinga zubawa a cikin akwatin, sannan ta saka kayanta, da mayafin ta, akwatin ta jawo ta fito hawaye na gudu saman fuskarta, Ladiyo dake zaune ne ta tashi da sauri tana cewa.

” Aunty Lafiya, kika fito kina kuka, ina zaki da akwatin Aunty.”

Cikin muryar kuka Falmata tace.

” Gidan mu zan tafi, Aure ne ya ajiye ni a gidan nan kuma yau Auren ya ƙare, idan akwai wani abu na kuskure daya shiga tsakanin mu a zaman da mukayi ki yafe min.”

Girgiza kanta Ladiyo tayi hawaye na gudu mata itama tace.

” A’a Aunty baki taɓa min laifi ba, sai ma kyauta ta min da kike, Aunty nima tafiya zanyi bazan zauna a gidan nan babu ke ba.

Ta ƙarasa maganar ta na shigewa da gudu Bedroom ɗinta, Falmata share hawayen ta tayi taja akwatin ta ta fice……………

Dan dan dan dan dan dan dan

Akwai ƙura fa cikin wannan labarin ku biyoni mu ninƙaya cikin sa domin jin yacce zata kasance amma ta hanyar 👇🏻

Kuna iya nuna min soyayya ta hanyar siyen littafinan na DOCTOR HASSAN akan Naira 300 kacal,zaku iya biya ta wannan account ɗin 0006064512 RASHIDA USMAN JAIZ BANK ko kuma ku tura katin MTN ta wannan number 08147537180,sannan ku tura shaidar biya a ita ko a 08147537180 Nagode masoya,ina maraba da masu sayan ɗaya ko sari

Vote
Share
And comment

ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻

(UMMU NASMAH CE)
[9/6, 3:39 PM] Ummu Nasmah❤️❤️❤️❤️: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

            💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

Love and romance and funny story

Writing by

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*

Marubuciyar nan taku ta INDO A BIRNI

Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a ko yaushe, da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.

Special Gift to

Masoyan Asali waɗanda suka kasance dani a cikin book ɗina na kuɗi wanda ya gabata wato Ruɗanin Zuciya biyu kun sayi wannan book ɗin fiye da zato na Tabbas kun nuna min ƙauna domin kuwa hakan ya gwada min kuna tare dani ako yaushe koda kuɗi ko babu nima dai Ummu Nasmah ina ƙaunar ku🥰

بسم الله الرحمن الرحيم

________________________

🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼
🇦SSOCIATION🤝🏻
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

     *BOOK ONE*

PAGE 25 to 26

_________________________

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻 DOLE NA MUKU GODIYA FANS DOMIN KUWA INA GANIN RUWAN MASOYA A WANNAN BOOK ƊIN I LOVE YOU UMMU NASMAH FAN’S😘

__✍🏻 Musa mai gadi cike da mamaki yake kallon Falmata da ta fito da akwati idanunta hawaye yana gudu, da sauri musa ya ƙaraso tare da karɓar akwatin hanun nata yace.

” Ranki shi daɗe meyake faruwa, naganki kin fito haka kina hawaye, kuma yanzu kika shiga kina dariya kuma ki fito da akwati ina zaki.”

Falmata hanu tasa ta goge hawayen ta, sannan tayi murmushin dole tace.

” Babu komai Musa zanje gida ne, zan dawo zuwa anjuma, Mama zan kaiwa akwatin.”

Falmata ta faɗa masa hakane kawai dan bata son yawan Magana.

Kaɗa kansa Musa mai gadi yayi cikin rashin yadda yace.

” A’a ranki ya daɗe ba lafiya ba, kuka fa kike.”

” Kaga Musa nace maka babu komai, bani jakata na tafi dan Allah bana son yawan tambaya.”

Ajiyar zuciya Musa ya sauƙe tare da cewa.

” Shikenan kiyi hkr muje na rakaki ki hau adaidaitan”

Akwatin Musa yaja suka fice a ƙofar gidan suka tsaya jiran mai adaidaitan sun ɗan juma kaɗan kafin adaidaitan ya zo, Musa ne ya tare mai adaidaitan, Falmata ce masa tayi ” UNGUWAR BULUNKUTU TSALLAKE zaka kaini amma zaka ɗan jirani na shiga na karɓo maka kuɗinka, Musa cewa yayi.

” Malam nawa ne kuɗin ta da zata biya.”

” Ɗari Uku ne” mai adaidaitan ya faɗa, Musa cike da tausayin Uwar ɗakin nasa ya saka hanu a aljihun sa ya ciro Yan canjin sa, ɗari huɗu ne, ya zare ɗari Uku ya bawa mai adaidaita, sosai Falmata taji daɗin karan da Musa ya mata godiya ta masa sannan ya saka mata akwatin ta cikin adaidaitan hawa tayi Musa yana ɗaga mata hanu mai adaidaita yaja suka tafi, Musa cike da sanyin jiki ya shiga cikin gidan, zama yayi shuru yana tunanin meya fitar da Falmata cikin gidan a wannan yanayin, yana tsaka da wannan tunanin yaga Ladiyo ta fito da gana masgo ɗin ta a kanta, ware idanunsa yayi kansa ya ƙara ɗaurewa ” to ita kuma Ladiyo meya fito da ita da wannan dangwalin.” Sanda ta ƙaraso kusa dashi yace.

” Ke kuma ina zaki da wannan gana masgo ɗin.?”

Ajiye gana masgo ɗin tayi ta zauna a kai sai kuma ta fashe da kuka, cikin kukan tace.

” Ƙauyen mu zan koma, tunda Aunty tabar gidan nan, DOCTOR ya sake ta, ya mata walaƙanci, dan haka nima bazan zauna babu Aunty ba, tafiyata zanyi, na tsani doctor bashi da tausayi da imani, Aunty tana sonsa sosai tana masa biyayya amma baya gani tana haƙuri sosai dashi shine ya sake ta.”

” Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un allahumma ajirni fil musibati!!!! Lallai Oga ya yiwa kansa babbar asarar dan bazai taɓa samun mace tagari irin Hajiya ba, Mtsss!!! Wannan ƙaddara data faɗawa waɗannan mutanen tayi muni domin kuwa rayuwar su ta baya ba haka take ba, Rayuwa suke mai tsafta da kuma burgewa a wajen ko wani mutum, Allah ya kyauta, kina da gaskiya Ladiyo bai kamata ki zauna a gidan nan ba tunda babu mace a cikin sa, ke zaki iya tafiya, amma ni zan iya zama, Allah dai ya daidaita tsakanin su, yanzu kin sanar da Oga zaki tafi ne.”?

” A’a ban sanar dashi kuma bana son sanar dashi bare kuma na ƙara kallon fuskarsa.”

Musa ce mata yayi.

” Karkiyi haka Ladiyo baki san me Allah ya ƙaddara tsakanin su ba, sai kiga idan Allah ya gyara tsakanin su, ko gobe ma sai ki iya ganin Hajiya ta dawo cikin gidan nan, abinda zakiyi yanzu kije ki sanar dashi cewa zaki tafi ƙauyen ku, sai sanda Hajiya ko wata mace ta dawo cikin gidan nan zaki dawo, kije ki sanar dashi kinji.”

Kaɗa kanta Ladiyo tayi alamun ta gamsu, gana masgon ta ɗauka ta koma ciki.

A kofar gidan nasu mai adaidaitan ya sauƙe ta, akwatin ta ta ja ta shige cikin gidan nasu matan gidan yawancin su suna zaune a tsakar gidan, bunta da akwatin hanunta sukayi da kallo, sallama ta musu tare da gaishe su zata wuce taji muryar Lami uwar gulma tana cewa.

” Mai kantu ya naga ƴar taku da akwati ko dai Hassan ya koreta ne.”

Taɓe bakin ta mai kantu tayi tare da cewa.

” Gata nan dai kam da alamar korar, dan zai aikata tunda ba mutunci garesa ba.”

Lami cike da tsurku tace.

” Hmmm idan anbi ta ɓarawo abi ta mabi sawu, suma fa idan da gaske ne zargin da Hassan yake musu to duk abinda ya yiwa Falmata yayi daidai.”

Tsuka Mai kantu taja tare da cewa.

” Ke kuma lami gulma gareki, to ina ruwan ki, da wannan maganar, ke komai kika gani sai kinyi Magana Mtsss!!”

Ta ƙarasa maganar tare da tashi tabar wajen, lami taɓe bakin ta tayi, tana bin mai kantu da harara.

Falmata shigewar ta Part ɗin nasu Darect ɗakin Hajja ta shige, sallama tayi jikinta a sanyaye, Hajja dake zaune tana lazimi ne tabi Falmata da kallo, ajiye tsarbin Hajja tayi tare da tasowa tazo kusa da Falmata ta dafa ta tare da cewa.

” Fatuma lafiya na ganki da akwati, kuma ga alamun kinyi kuka a idanunki meya faru.?”

Falmata kuka tasa tare da zama ta dafe kanta cikin muryar kuka tace.

” Hajja DOCTOR ya sake ni, yaci amanata Hajja, na shiga Uku na rasa farin ciki na Hajja, bana jin zan iya rayuwa babu DOCTOR Hajja ina sonshi Hajja ina sonshi.”

Kamar sauƙar aradu Hajja taji Maganar saki daga bakin Falmata, zama tayi itama Hajja cike da sanyin jiki ta dafa kafaɗar Falmata tace.

” Dama nasan dole wannan Auren naki zai mutu, alamun haka sun nuna tun sanda Hassan ya juya miki baya, bazaki mutu dan kin rasa Hassan ba, ko mutuwa yayi dole zakiyi haƙuri, Fatuma ki cire Hassan cikin ranki ki manta dashi a rayuwarki ki gina Sabuwar rayuwa karki dinga tuno Soyayyar da, ki dinga tuno walaƙantaki da yayi, ki barsa da Allah na Tabbata zai miki sakayya, Yagana dake kwance ta riƙe haɓa cike da mamaki tace yanzu naji naji muryar bukkar ya shigo jeki kira min shi harma da Yana.”

Tashi Aunty Yagana Tayi tare da amsawa da to ta fice Falmata cikin kukan ta cigaba da cewa.

” Bazan iya manta DOCTOR a cikin rayuwata ba, ina sonshi sosai Hajja koda rayuwata zata cigaba da wanzuwa zata wanzu ne cikin Soyayyar DOCTOR, bazan taɓa iya daina sonshi ba hajja.”

Cike da tausayin ta Hajja ta jawo ta jikinta tare da bubbuga mata bayanta alamun rarrashi, BUKKAR ne yayi sallama shida Aunty YANA suka shigo kusa da Falmatan shima ya zauna yana cewa.

” Lafiya kuwa Hajja yaushe Falmata ta shigo gidan nan kukan me kuma take haka.?”

Hajja amsa ta basa da cewa.

” Hassan ne ya saketa.”

Aunty YANA wani irin farin ciki taji a cikin ranta domin kuwa ta daɗe tana neman DOCTOR ya sakar mata ƴarta, kodan ta huta da baƙin cikin da yake shaƙa mata Baba Bukkar ne yace.

” Shikenan Allah yasa haka shi yafi alkairi, yaron nan Hassan yana min munanan abubuwa akan zargin sa na banza wanda bani da hanu a ciki, ya saketa Hajja domin ya ƙona min rai, amma insha Allah gaskiya zatayi halinta, kiyi hkr Falmata ki cigaba da addu’a Allah ya kawo miki wani mijin wanda ma yafi hassan.”

Da ameen Aunty YANA tace fuskar ta cike fam da farin ciki, Hajja cewa tayi.

” Bukkar daga kai har Yana kar wanda ya yiwa Hassan Magana akan meya sa ya saki Fatuma, kar Kuma ku nuna masa ɓacin ranku nima bazan sanja masa fuska saboda haka ba, Zuru ma ya ishi mai hankali, sannan ke kuma fatuma ki dinga control ɗin kanki duk sanda kika gansa dan Allah ko kallon sa karkiyi.”

Falmata ƙyaɗa kanta tayi alamun taji, Aunty YANA tashi tayi ta fice tana jin zuciyarta wasai, shima Baba Bukkar fita yayi ya rage daga Falmata sai Hajja, kwanciya Falmata tayi a gadon Hajja tayi shuru tana tunani, Hajja kuwa cigaba tayi da lazimin ta tana jin wani irin haushin DOCTOR a cikin ranta.

A cikin mintuna kaɗan Maganar mutuwar Auren Falmata ya karaɗe cikin gidan, koda labari ya iske su Hajjo da AJIRAM da tazo, sosai hankalin su ya tashi barin ma Hajjo har wani jiri take ji, FANNA kuwa farin ciki ma taji, Hajjo tashi tayi ita da AJIRAM suka nufi sashin su Falmata, ɗakin Hajja suka shige da sallama, Hajja ce ta amsa tare da nuna musu wajen zama, zama Hajjo sukayi cikin mutuwar jiki tace.

” Maganar da mukaji a cikin gida gaskiya ne, wai Hassan ya saki Falmata.”

Murmushi Hajja tayi cike da nuna rashin damuwa ta musu nuni da akwatin Falmata tace.

” Ganan Tabbas, amma yaje duniya ce ta isheshi riga da wando, ki duba yarinyar yanda take ajiyar zuciya duk son da take yiwa Hassan, ya cutar da ita sosai sai dai Allah baya barci zai mata sakayya.”

Runtse idanunta Hajjo tayi cikin ɓacin rai tace.

” Abinda Hassan zai aikata kenan wacce irin zuciya ne haka dashi, Tabbas ya cutar da ita Hajja, kuyi hkr dan Allah, zan kirasa yanzu dole sai ya maida Auren nan.”

Murmushi Hajja tayi tare da cewa.

” Allah ya sauwaƙa ai Falmata tabar Auren Hassan kenan har gaban abada, dan haka ku bar wannan maganar mutuwar Auren nan kwatakwata Allah yasa haka shi yafi alkairi, ni kaina idan naso dole sai ya maida Ita amma bazanyi haka saboda zaman Auren su baida wani amfani koda an mayar da Auren Cutar da ita kawai zai dinga yi, dan haka haƙura da wannan Auren shi yafi alkairi.”

Jinjina kanta Hajjo tayi har yanzu ranta a ɓace yake, duban Falmata tayi da tayi shuru ta kasa Magana domin kuwa ita kaɗai tasan abinda take ji a cikin zuciyarta, ƙarasawa Hajjo tayi ta dafa ta tare da cewa.

” Kiyi hkr Falmata, insha Allah Hassan sai yayi kukan rashin ki a rayuwarsa bazai gane kurensa yanzu sai sanda komai ya kufce daga hannun sa hankalinsa ya dawo jikin sa a ranar ne zai gane kuskukuren sa lokacin da baida damar gyarawa Allah ya baki haƙurin rashin sa.”

Hajjo ta faɗi tare da tashi suna ficewa cikin sanyin jiki AJIRAM kasa Magana tayi tsabar kunyar abinda ɗan uwanta ya aikata.

Wunin ranar Falmata tayi shine cikin baƙin ciki da damuwa, ko abincin dare gagara ci tayi, baccin ma kansa rabi da rabi tayi sa, haka ta kwana cikin ƙunar rai da Soyayyar mijinta.

Washe gari da sassafe DOCTOR ya tashi, ya shirya kasancewar yaune zasu je ƙauyen BINISHED, Bello ya kira ya sanar dashi cewa karya ɓata lokaci 11 zasu wuce, falo ya fito yana ɗaura agogon hanunsa, sharaf ya manta da babu mata a cikin gidan ya nufi daining, wayam ya gani babu komai, dafe kansa yayi ya manta da cewa Ladiyo ta tafi gashi ya tashi da yunwa tsuka yaja tare da ciro wayarsa ya dace kawu Dauda kira, ringin ɗaya ya ɗauka, cikin girmamawa DOCTOR ya gaishe sa tare da cewa.

” Kawu mun gama komai, anjuma zamu wuce da UMMA BINISHED.”

Da ƙarfi Kawu Dauda cikin tashin hankali ya furta.

” Whatttt!!!!! Wato ban isa da kai ba kenan, dana hana zuwa BINISHED ɗin wato zaka ce sai kunje to baza’a je ba, idan kuma kuka tafi to kuwa ranku zaiyi mungun ɓaci.”

Cike da ɗaurewar kai DOCTOR yace

” Kawu wai meyasa baka son muje ƙauyen nan ne kam, ka ɗagawa kanka tunda nace maka zamuje BINISHED, wai meye yake faruwa ne, ko akwai wani abune.”

Kawu Dauda saurin dawowa yayi cikin hankalin sa tare da cewa.

” Babu wani abu ni gani nayi munje wajaje da yawa neman maganin nan bamu sami wani nasara ba, shiyasa kawai bana son muje BINISHED ɗin saboda karmu sha wahalar banza.”

DOCTOR cewa yayi.

” Insha Allah Kawu ina ji a jikina zamu sami nasara dan haka zamu tafi anjuma ka mana fatan Nasara.”

” To shikenan Allah ya bada Sa’a.”

Ya faɗa a taƙaice yana kashe kiran, jikinsa kuwa ya jiƙe da gumi sharƙaf duban Jummai matar sa yayi dake gefen sa cikin tashin hankali yace.

” Mun shiga Uku asirin mu yana gaf da tonuwa, idan har muka bar yaron nan yaje BINISHED domin kuwa wannan malamin hatsabibin mutum ne, muddun YAMURAM ta dawo hankalin ta, to fa asirin mu ya tonu, domin kuwa tasan komai taji komai tasan mune muka ɓatar da mijinta da ƴarta, dole musan abinyi kafin su isa ƙauyen nan.”

Jummai a matuƙar har zuƙe ta tashi tace.

” Ƙarya ne asirin mu bazai taɓa tonuwa ba, wannan ƙauyen bazasu isa lafiya, domin dole sai mun dakatar dasu, YAMURAM BAZATA TAƁA SAMUN LAFIYA BA A HAKA ZATA ZAUNA HAR MUTUWAR TA TA RISKETA ka kwantar da hankalinka ni nasan abinda zamuyi.

Tir ƙashi wannan shi ake ana zaton wuta a maƙera, to fa ya zata kasance ku biyo ni domin sani👇🏻

WACCE TAKE DA INTEREST TAKE ƘAUNAR KARATUN WANNAN LITTAFIN TAYI ƘOƘARIN BIYAN KUƊIN TA DOMIN KUWA FREE FAGE YA ƘARE WANDA YA BIYA SHI ZAI SHA KARATU AKWAI WAƊANDA SUKE CEWA 300 YA MUSU YAWA TO DUK MAI SO TAMIN MAGANA RAGI BAZAI GAGARA BA

TABBAS NAGA RUWAN MASOYA A WANNAN BOOK ƊIN UMMU NASMAH TANA ƘAUNAR FAN’S ƊINTA SOSAI😘😘🥰🥰👇🏻

Kuna iya nuna min soyayya ta hanyar siyen littafinan na DOCTOR HASSAN akan Naira 300 kacal,zaku iya biya ta wannan account ɗin 0006064512 RASHIDA USMAN JAIZ BANK ko kuma ku tura katin MTN ta wannan number 08147537180,sannan ku tura shaidar biya a ita ko a 08147537180 Nagode masoya,ina maraba da masu sayan ɗaya ko sari

Vote
Share
And comment

ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻

(UMMU NASMAH CE)
[9/7, 5:40 PM] Ummu Nasmah❤️❤️❤️❤️: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

            💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

Love and romance and funny story

Writing by

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*

Marubuciyar nan taku ta INDO A BIRNI

Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a ko yaushe, da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.

Special Gift to

Masoyan Asali waɗanda suka kasance dani a cikin book ɗina na kuɗi wanda ya gabata wato Ruɗanin Zuciya biyu kun sayi wannan book ɗin fiye da zato na Tabbas kun nuna min ƙauna domin kuwa hakan ya gwada min kuna tare dani ako yaushe koda kuɗi ko babu nima dai Ummu Nasmah ina ƙaunar ku🥰

بسم الله الرحمن الرحيم

________________________

🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼
🇦SSOCIATION🤝🏻
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

     *BOOK ONE*

PAGE 27 to 28

_________________________

_✍🏻Me zakiyi Jammai wannan yaron yanda kika san shaiɗan haka yake taurin kai garesa, mawuyacin abune mu iya dakatar dashi daga wannan tafiyar domin kuwa idan yasa abu a gabansa sai ya kai ga cin Nasara ina mungun jin tsoron yaron”

murmushi Jummai tasa tare da cewa.

” Ka manta da cewa nima shaiɗance mai zaman kanta wallahi na fisa shaiɗanci, kasan dai zan iya aikata duk abinda nake so, ka barsu su tafi, ni kuma zan kira waya abi ta kansu da babbar mota.”

Zaro idonsa Kawu Dauda yayi yace.

” Me kike nufi, kina nufin a kashe su, to ma wai waye zaki saka yayi wannan aikin, ki dai sanja wani tunanin amma banda zancen kisa dan gaskiya akwai rai da yawa a cikin tafiyar Hajjo AJIRAM Bello ga kuma Hassan ga YAMURAM bazai yiwu ba gaskiya a sanja wata mafitar ba dai wannan ta kisa ba.”

Tsuka Jummai taja cikin tsawa tace.

” Ina ruwan ka da rayukan da za’a rasa, badai mutuncin mu muke nema ba, da kuma kuɗaɗen nan su tsira, to ka sani a wajen neman mutunci rai ba a bakin komai yake ba, wallahi sai naga bayan su kafin suga namu, JAMO zan saka ya min wannan aikin, dole mu dakatar dasu.”

Ajiyar zuciya Kawu Dauda ya sauƙe tare da cewa.

” Shikenan ayi hakan Allah ya huci Zuciyarki, ni ma bari na shirya naje muyi sallamar ƙarshe da su, idan sun mutum ma zamu fi samun sukuni wallahi, sai yanzu na hango zancen ki.”

Dariya Jummai tasa tare da cewa.

” Uhumm ko kai fa, shirya kawai kaje kuyi sallama saboda gudun zargi, karka nuna musu tsoro ko damuwa a tattare da kai na zuwan su ƙauyen kuyi komai cikin farin ciki da sakin fuska ka nuna musu kafi kowa son ganin ƴar uwarka ta samu lafiya, yanda bazasu fahimci komai a tattare da kai ba kace nima ina musu Allah ya kiyaye hanya.”

Shewa suka saka, kafin Kawu Dauda ya shige tollet, taɓe bakin ta Jummai tayi tare da furta ” haka kawai muna tsaka da jin daɗin mu, muna cin duniyar mu da tsinke ace za’a dakatar damu, wallahi bazai yiwu ba, duk mutumin da yace zai yanke mana jin daɗin mu wallahi sai naga bayan sa.”

Ita kuwa Falmata da damuwar ta tashi daga bacci, komai cikin sanyin jiki take yinsa, Hajja duk tana kula da yanayin ta, gaishe da Hajjan tayi ta amsa tare da cewa.

” Ga nan abincin karyawar ki, ki ɗauka kici maza, ina zaki naga kin shirya kina ɗauko jaka.”?

Cikin sanyin Murya tace.

” Makaranta zan tafi ina da lectures 11:30 abincin nan kuma DOCTOR ya isheni!!!”

Bakinta Falmata ta riƙe jin ta ambaci sunan DOCTOR a maimakon ta ambaci na Hajja, tana kallon Hajja cike da tsoron masifar ta, Hajja haɗa fuska tayi tamau tare da cewa.

” Wato har yanzu wannan uban yan iskan ne a cikin ranki ko, wai ke Fatuma baki da zuciya ne kam, duk wulaƙancin da Yaron nan ya miki amma yana maƙale a cikin ranki, to Allah ya yaye miki wannan jarrabawar da kike ciki, amma da zaki taimaki kanki ki cire wannan Soyayyar a cikin ranki da yafi miki sauƙi domin kuwa babu ke babu komawa gidan Hassan har abada, tashi kije kici abinci kafin na ɓata miki rai, me kikaci da zakice kin ƙoshi jiya ma haka kika kwana baki ci komai ba, shine yanzu ma zakice bazaki ci abincin ba to baki isa ba Wallahi ko zakici ki amarsa sai kin ci, kuji min ja’irar yarinya dai to Soyayyar taci uwarta Soyayyar banza Soyayyar da ba’a damu da dake ba, Soyayyar shan kwana maza ci abinci kafin raina ya ɓaci.”

Tura bakin ta Falmata tayi tana ƙunƙuni ta tashi ta ɗauko kwanon abinci tasa a gaban ta, Hajja hararar ta tayi tace.

” Ba dole kimin ƙunƙuni ba, tunda ni kin raina ni, aida shi uban naki Hassan ne yace kici da kin ɗauka jikinki yana ɓari kinci, to wallahi bazai yiwu ba, bazaki zauna kamar icce babu cin abinci ba saboda wani katon banza yana can yana ci yana sha yana walwalar sa, ke kuma kin zauna cikin damuwa da rashin kwanciyar hankali, bazai yiwu ba, bazan lamunta ba, ki cinye abincin nan tas ki bani kwanon.”

Falmata dai bata cewa Hajja komai ba sai famar cin dole take yiwa abincin, da ƙyar ta iya cin rabinsa ta ajiye tana duban Hajja dake zaune ta tsareta da idanu, bata ce mata komai ba hakanne yasa ta ɗaukar ruwan tea ɗin tasha kaɗan, wayar ta ta jawo ta dannawa Maji kira, bayan Maji ta ɗaga ne Falmata tace.

” Ƙawata idan kin tashi tafiya school ki biyo min ina gidan mu na nan BULUNKUTU TSALLAKE.”

Cike da mamaki Maji ta duba agogon bangon dake manne cikin Bedroom ɗinta, 10:39 cewa Falmata tayi.

” Falmata lafiya kuwa kike gidan ku wannan lokacin sassafe haka.?”

Numfashi Falmata ta sauƙe tare da cewa.

” Ke dai ƙawata sai kinzo kawai Maganar bata waya bace sai mun haɗu.”

Da shikenan Maji ta amsa tare da kashe kiran.

10:45 daidai DOCTOR ya shigo cikin gidan nasu part ɗin mahaifiyar tasa ya shige Darect, ya samu Hajjo da AJIRAM har sun shirya ta suma sun shirya, murmushi ya saki tare da cewa.

” Hajjo ina kwana har kun shirya kenan bari mu jira Bello to.”

Hararar sa Hajjo tayi cikin ɓacin rai tace.

” Ka kyauta Hassan ka kyauta da kaci amanar ƴar uwarka yarinyar da take maka Soyayyar gaskiya, kuma matar ka mai ƙaunar farin cikin ka, saboda kaga babu idon UMMA shiyasa kake abinda kaga dama, to wallahi ka sani kayi asarar mace ta gari, bazaka taɓa samun Mace mai biyayya da haƙuri irinta ba, kanka ka cuta ba mu ba kai ka sani.”

Ta ƙarasa maganar tana hucin Haushi, tunda ta fara Maganar DOCTOR ya sunkuyar da kansa ƙasa bai ce mata komai ba, tana gama ya juya tare da cewa.

” Bari naje na sanarwa Hajja tafiyar mu.”

Hajjo bata ce masa komai ba harya fice da sallamar sa ya shiga Part ɗin Yagana ce kawai a tsakar gidan, da har zai shige bai kulata ba, sai kuma ya tuno Maganar mahaifinsa da yake cewa ( Hassan duk abinda zai shiga tsakanina da Yan uwana babu ruwan ku a ciki karku raina su koda yankan naman junan mu muke munfi kusa tare kuka ganmu idan kun raina su tamkar kun rainani ne) runtse idanunsa yayi yana sauƙe ajiyar zuciya a dakile yace wa Yagana.

” Ina kwana Aunty Yagana.”

” Lafiya” itama ta amsa masa a taƙaice, DOCTOR shigewa yayi ɗakin Hajja da sallama, amsawa Hajja tayi cikin sakin fuska ba tare da ta sanja masa fuska ba, Falmata jin sallamar DOCTOR sai da taji zuciyarta ta tsinke, gefe kaɗan da Falmata ya zauna yana ƙare mata kallo ta kasan Ido gaishe da Hajja yayi ta amsa fuskarta a sake yace mata.

” Hajja yau zamu tafi da Umma BINISHED wajen mai magani shine nace bari na sanar dake.”

Hajja cewa tayi.

” Masha Allah yayi kyau yanzu zaku tafi kenan.”?

” Eh yanzu zamu tafi Bello kawai muke jira.”

Ya ƙarasa maganar yana duban Falmata da ta tashi zata bar ɗakin, Hajja cewa tayi.

” To Allah yasa aje cikin Nasara, nima ina shigowa yanzu na duba YAMURAM ɗin kafin ku wuce.”

Da to DOCTOR ya amsa tare da yin shiru yaji ko Hajja zata masa zancen sakin Falmata da yayi, amma shuru Hajja bata ce masa komai ba, ya juma zaune kafin ya tashi cikin sanyin jiki domin kuwa Hajja ta dafasa da ruwan sanyi, ita bata ɗaure masa fuska ba kuma bata sake masa fuska ba, babu wasan da suka saba da ita yau, cikin sanyin jiki ya bar ɗakin, koda ya fito Falmata da yana da kuma Yagana suna zaune babu wanda ya kallesa har Aunty YANA dama ita saboda ya sakar mata ƴarta take faɗa dashi, yanzu kuma ya saki yarta bata da wani contract dashi , daf da DOCTOR zai fice daga part ɗin shi kuma Baba bukkar yana shigowa, amma DOCTOR bai basa hanya ba, ya saka kansa, Baba Bukkar ganin yana da niyyar bigesa ya sashi matsawa gefe DOCTOR ya shige, Falmata da take kallon rashin mutunci da DOCTOR ya yiwa mahaifinta ne ya sata runtse idanunta hawaye ya gangaro mata saurin gogewa tayi gudun karsu Aunty YANA su gani, Ranar farko da ta fara jin haushin DOCTOR kenan a cikin RAYUWARTA tashi tayi da sauri tabar wajen jin kuka na neman ƙwace mata, Sarai Baba Bukkar ya ganta amma ya kauda kansa kamar bai gani ba, ya shige ɗakin sa shi kansa yana jin ɓacin rai akan abubuwan da ɗan yayan nasa yake masa, Falmata faɗawa tayi saman gadon Hajja ta saki kuka mai cin rai, Hajja haɓa ta riƙe tana cewa.

” Ikon Allah yanzu kuma me aka miki daga ganin sa shikenan sai ki hau kuka, Oh ikon Allah ni Maryam ina ganin wata shegiyar soyayya shifa yanzu baima nuna ya san Allah yayi ruwan tsoron ki a wajen nan ba, amma ke kin dagawa kanki hankali to wallahi ki cire yaron nan a ranki kafin hawan jini ko ciwon zuciya ya kamaki dan idan mutuwa ma kikayi shi baida asara.”

Shuru Falmata tayi sai kuma sauƙe ajiyar zuciya da takeyi bata kuma tanka Hajja ba, Itama Hajja bata kuma cewa komai ba, ta ɗauki hijabin ta ta shige duba YAMURAM.

Shigarta ta samu har sun fito suna shirin fita waje rike da Umma a hanu gefe guda kuma ga kawu Dauda tsaye kana ganin fuskar sa bazaka ce mungu bane, Hajja cewa tayi.

” Kaddai har kun fito, to Allah ya kaiku lafiya yasa a samu sauƙi, Allah ya baki lafiya YAMURAM”

, da ameeen Hajjo ta amsa har ƙofar gidan Hajja ta rakasu, suka shiga motar DOCTOR harda Fanna, Bello da DOCTOR sune a gaba, Kawu Dauda a dawo lafiya ya musu tare da fatan Nasara, Hajja tana ɗaga musu hanu har suka tafi, ta juya zata koma Cikin gida, sai taga Maji ma zata shiga murmushi Hajja tayi tare da cewa.

” Umhum yanzu kam zamu dinga ganinki ai tunda ƙawarki na gida, ina DANDA kwana biyu bana ganinta bata shigo mana.”

” Tana nan kuma Yan yawon nata ne basu biyo da ita ta nan ba.”

Tare suka shiga suna zance, har ɗakin Hajja, Maji Falmata dake kwance tana sauƙe ajiyar Zuciya tabi da kallo zama tayi saman gadon ta dafa ta tare da cewa.

” Ƙawata wannan yanayin da na ganki a ciki ba lafiya ba, nasan matsalarki bata wuce DOCTOR, meya faru.?”

Tashi Falmata tayi idanunta sunyi jajur ta kama hanun Maji tace.

” Kinsha cemin DOCTOR ba Soyayyar gaskiya yake min ba, ban taɓa yarda da kalamanki ba, a zato na kawai bakya son Doctor ne, ashe abun ba haka yake ba, ke kin hango min abinda ni na kasa hangowa, Maji DOCTOR ya sake ni, bayan ya gama ciwa iyayena mutunci ya zagesu a gabana, ya zargeni da zina da HABEEB, a karshe ya bini da takaddar saki, hakan bai masa ba, yau a gabana DOCTOR yayi niyyar bige mahaifina, sai hanya Baba ya basa, Tabbas yau na tabbar da cewa DOCTOR ba sona yake ba, sai dai kash zuciyata ta kasa wurgar da Soyayyar sa, kullum sonsa ƙaruwa yake a cikin zuciyata, ina son na cire Soyayyar DOCTOR a raina ki faɗa min taya zan cire ta yaya.”

Ajiyar zuciya Maji ta sauƙe cike da tausayin kawar tata tace.

” Hmmm!!! Dama nasan haka zai faru domin babu imani a zuciyar DOCTOR, iya da mungun son kansa da zafin zuciya ta tsiya, ƙawata ki dage da addu’a baki cuci DOCTOR insha Allah Allah zai cire miki Soyayyar sa a ranki, shi kuma yaje kansa ya yiwa asara, akwai maza da yawa wanda suka fishi komai kuma suna sonki dan haka zaki samu wanda ya fisa sonki wanda zai adana miki rayuwarki, ki barsa da Allah insha Allah sai ya miki sakayya, dan tashi ki wanke fuskar ki ki shafa powder mu tafi school time ya kusa.”

Ajiyar zuciya Falmata ta sauƙe tare da tashi ta shige tollet ɗin Hajja dake cikin ɗakin ta wanke fuskar ta, powder da lipstick ta shafa sannan ta dauki bag ɗin ta suka fito, Aunty YANA taje ta yiwa sallama Baba Bukkar ne ya ɗauki 1k ya bata yace tayi transport, karɓa Tayi ta masa godiya sannan suka fice.

Su kuwa su DOCTOR hanya suke ta famar ƙwasa domin kuwa tafiyar 50 minute ne zata kaisu BINISHED, sunyi nisa da tafiya kamar wanda akace DOCTOR ya ɗago kansa yaga doguwar Mota tana nufo kansu gadan-gadan, innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un DOCTOR ya furta a kiɗime tare da duba gefen da zai kaucewa Motar nan ma dai wata motar ya hango, zuciyarsa ne ta tsinke Bello shima cike da tsoro yake bin motar da kallo yace.

” DOCTOR Motar nan fa kanmu take biyowa ka kauce mata mana.”

Su Hajjo kuwa babu abinda suke sai salati Fanna kuka tasa DOCTOR cewa Bello yayi

” Ta ina kake ganin zan kauce masa, ka duba ka gani ko ina na juya ƙarshen karo zamuyi da wata Motar.”

Dafe kansa yayi ba kansa yake ji ba, matan dake cikin motar yake ji, yanzu meye abun yi ta ina zai iya tseratar da rayuwarsu…..?????

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

Amsar ku tana page ɗin gaba ta hanyar 👇🏻

Kuna iya nuna min soyayya ta hanyar siyen littafinan na DOCTOR HASSAN akan Naira 300 kacal,zaku iya biya ta wannan account ɗin 0006064512 RASHIDA USMAN JAIZ BANK ko kuma ku tura katin MTN ta wannan number 08147537180,sannan ku tura shaidar biya a ita ko a 08147537180 Nagode masoya,ina maraba da masu sayan ɗaya ko sari

WAƊANDA SUKA CE 300 TA MUSU YAWA SUMIN MAGANA TA PRIVAT RAGI BAZAI GAGARA BA INDAI KINA DA INTEREST AKAN BOOK ƊIN

Kumin afuwa yau ban samu nayi Editing ba.

vote
Share
And comment

ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻

(UMMU NASMAH CE)
[9/8, 6:04 PM] Ummu Nasmah❤️❤️❤️❤️: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*🩺DOCTOR HASSAN🩺*

            💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

Love and romance and funny story

Writing by

*Rasheedat Usman*

*(Ummu Nasmah*

Marubuciyar nan taku ta INDO A BIRNI

Na sadaukar ga wannan littafin gareku MASOYANA a duk inda kuke ina Alfahari daku a ko yaushe, da wanda na sani da wanda ban sani ba, domin kuwa naji daɗin yanda kuka karɓi wannan book ɗin nawa na Indo a Birni.

Special Gift to

Masoyan Asali waɗanda suka kasance dani a cikin book ɗina na kuɗi wanda ya gabata wato Ruɗanin Zuciya biyu kun sayi wannan book ɗin fiye da zato na Tabbas kun nuna min ƙauna domin kuwa hakan ya gwada min kuna tare dani ako yaushe koda kuɗi ko babu nima dai Ummu Nasmah ina ƙaunar ku🥰

بسم الله الرحمن الرحيم

________________________

🌈🇰AINUWA 🇼RITER’S✍🏼
🇦SSOCIATION🤝🏻
{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
________________________

     *BOOK ONE*

PAGE 29 to 30

_________________________

_✍🏻Doctor gabaki ɗaya ya kiɗime ya shiga cikin tashin hankali ya rasa ya zaiyi ga Umma da numfashin ta yake neman ɗauke wa, mirrorn motar ya kalla yana ƙarewa bayan sa kallo, babu wata mota a bayan sa hakanne ya sashi ya fara ribas yana ja da baya da sauri, har ya samu ɗan tazara tsakanin sa da waɗannan motocin, layin dake gefen sa DOCTOR yasha kwana ya fasa jejin, wani wawan ribas yaja kafin yayi parking yana sauƙe ajiyar Zuciya, kansa ya kwantar jijin sitiyarin motar yana sauƙe numfashi shi kansa Bello ajiyar zuciya yake sauƙewa, Fanna sai yanzu ta daina kuka, su Hajjo kuwa ko magana sun kasa tsabar sun tsorata, ai kuwa kamar wanda akace DOCTOR ya ɗaga kansa, wannan Motar ya hango ta faso jejin da gudun tsiya ta nufo matar su, idanunsa DOCTOR ya zaro, Motar ya taka da karfi ya figi motar da mungun gudu, cikin jejin suka nufa Allah sarki UMMA numfashin ta sama sama ya fara yana neman ɗauke mata saboda jijjigar motar, Hajjo da AJIRAM kuka suka saka tare da kanƙame Umma suna kiran sunan ta, zuwa yanzu ran DOCTOR ya fara ɓaci, ya fahimci wannan drevern turo sa akayi ya kashesu, kaɗan ya hana motar ta daki tasu DOCTOR, sai Allah ya bawa DOCTOR Sa’a yayi saurin kauce masa, wata babbar bishiya Motar ta buga da ƙarfi, ta tsaya cak, DOCTOR daya kauce ne ya faka motar ya fito da sauri a matuƙar harzuƙe a fusace, sai dai ina wannan drevern doguwar Motar yana hango DOCTOR ya daka tsalle daga cikin motar ya shige cikin dajin da gudu, DOCTOR binsa zaiyi Bello ya riƙesa yana cewa.

” Binsa zakayi kasan meya shirya, idan kuma bashi kaɗai bane fa, kaga da Allah ya kare mu ma mu gode masa kazo mu tafi, Umma tana cikin wani hali, shi kuma ko waye shi yaje shida Ubangiji.”

DOCTOR yana huci ya juya suka shiga cikin Motar ba kowa yake zargi da turowa a ɗauki rayuwarsu ba, sai Baba Bukkar da matarsa, juyawa yayi ya kalli Umma da take famar sauƙe wani wahalallen numfashi wanda yake fita da ƙyar tausayin ta ne ya kamasa, motar yaja da gudu suka fito daga jejin, titi suka hau yayin da DOCTOR yake wani wawan gudu ya samu ya isa da Umma BINISHED da wuri, a cikin lokaci kaɗan kuwa suka dumfaro ƙauyen

BINISHED

” AYYARE iye ala gidigo ala gidigo ala gidigo baban goggo ala gidigo ke yarinya zaɓi dogo zaɓi dogo na ɗan wuro dokin iyali alagidigo ita mai wada turmi ta tuno turmi ta tuno zuwa ƙasa ta hau kujera alagidigo budurwar guntu ɗan wadas.!!!!! Ahayye nanaye, cap aradu wata taji kunya, ƙwal uba, yau saurayi haka kamar ɗan tsako abu ɗan yol babu kyan gani sai uban ƙaton kai MERAMA yasin saurayin kin nan bashi da kyan gani sai kace irin aljanu Yan gwaigwai ɗin nan masu rusheshen kayi kamar Rasha, ga wata shegiyar yar sharar sa ta shan iska da baya sanja ta kullum itace a jikin sa kamar ɗan matsiyata, cap wai sunan wata unguwa a Gombe BAGADAZA UNGUWAR SHAN ISKA “

Ta ƙarasa maganar tana sheƙewa da dariya tana nuna mairama da yatsa, yaran dake wajen suma dariya suka saka har suna riƙe ciki, wani irin haushi ne ya kama mairama idanunta suka ciko da hawaye Muryar ta raurau tace.

” Haba AI’SA wannan wani irin wulaƙanci ne, naga ai Allah shine ya hallici dogo ya hallaci guntu, kuma duk wanda ya raina tsayuwar wata ya hau sama ya gyara, da kike zaginsa ai gara shi akan Kacalla yayanki mai ido ɗaya, cap wannan shine wurƙilina Kacalla baƙi mai ido ɗaya ɗan FEREBUWAYE jikan KAKA gurguwa masifaffiya.”

Ta ƙarasa maganar tana murguɗawa AI’SA baki, ai kuwa take Ai’sa ta cika tam kaɗan ya hana ta fashe, ɗan kwalinta ta cire tasha ɗamara dashi ta sunkuya ta daki ƙasa, tare da cewa.

” Na rantse da wanda ya hallici wannan ƙasar yau babu mai hanani cin Durun uwar ki sai Allah, wani irin wawan duka ta kaiwa Mairama sai kuwa aka tirke da kokuwa, AI’SA cike da kwarewa a faɗa ta jidi ƙafar Mairama ji kuke tim Mairama ta faɗi ƙasa, kanta Ai’sa ta hau ta dinga dukanta danneta tayi ta dubi KARIMA, Tace.

” Karima cika min wannan ɗan iskan bakin nata da ƙasa, karima cike da tsoron Ai’sa ta ɗebi ƙasa ta dinga ɗurawa Mairama sanda suka cika mata bakin ta da ƙasa Ai’sa ta wawwanka mata mari sannan ta tashi a kanta tana riƙe ƙugu tare da.

” Dan ubanki gobe ma ki ƙara zagin halittar ƴan gidan mu kiga yadda zan sanja miki kama, ta ƙarasa maganar tana juyawa ta bar wajen karima bayanta tabi, yaran dake wajen suka dinga yiwa Mairama dariya, haushi ne yasa Mairama saka kuka ta bar wajen da gudu.

Sunyi nisa da tafiya karima ta saka dariya tana duban Ai’sa tare da cewa.

” Gaskiya AI’SA yau kin yiwa Mairama rashin mutunci, Allah ta bani tausayi yanzu bakya tsoron ta faɗawa wannan mahaukacin yayan nata BABA KAWU ya ritsaki a hanya ki shiga Uku”

Tsuka AI’SA taja tare da cewa.

” Mtsss!!!! Ke rabu da shegiya, daga na zagi saurayin ta shikenan sai ta zagi Yan gidan mu, ni Yan gidan su na zaga, ta faɗa masa mana wallahi ina dai dai dashi.”

Hommmmm da sukaji ne yasa su ɗaga kansu wata farar mota ce ƙal mai kyan gani da sheƙi ta ɗauke musu Ido, Karima cike da ƙauyanci take kallon Motar, ita kuwa AI’SA bakin ta ta taɓe sam bata wani yi ƙauyanci ba, kasancewar ta saba ganin irin Motar suna shiga birni sa’i da lokaci, ko gezau Ai’sa batayi ba daga wajen da take tsaye Karima ce ta matsa gefe tare da cewa.

” AI’SA kinga wata moto mai kyan gani, ki matsa mana shigewa zatayi fa.”

” Ke dallah gafara can, na matsa naje ina, waya zo ya sami wani a nan, ko itace kaɗai hanya anan ga nan nan yabi ya wuce mana.”

Ta ƙarasa maganar tana nuni da gefen dake cike da ciyawa, Karima shuru tayi bata kuma cewa komai ba saboda tasan yanzu Ai’sa zata iya zaginta.

DOCTOR Haushi ne ya kamasa ya ƙara danna hommmmm!!! Da ƙarfi amma ina yanda kuka san da kurma yake, cije leɓensa yayi cike da ɓacin rai dama kuwa ran nasa a ɓace yake, Motar ya tayar tare da cewa.

” Zanbi kan yarinyar na taka ta da ubanta, kai duk wanda aka kirasa da ɗan ƙauye Wallahi an cucesa, yanzu idan Banda jakanci da dabbanci irin na baƙauyen mutum kina ganin mota na danna miki homm kiyi kunnen uwar shegu.”

Hajjo ce cikin tsawa tace.

” Kai dakata uban Yan zafin ran tsiya, kai sam baka da haƙuri a rayuwarka, Bello fita kaje ka mata Magana ta kauce ko.?”

Da to Bello ya amsa tare da fita ya nufi wajen Ai’sa, a bayan ta ya tsaya tare da cewa.

” Baiwar Allah, dan Allah ki ɗan matsa gefe kaɗan zamu wuce da mota.”

Tsabar tsiya da Rashin mutunci dake gaban goshin Ai’sa bata juyo ta kalli Bello bama bare kuma ya samu arzikin amsa, ya mata Magana yafi baki biyar bata kulasa ba duban Karima dake gefe yayi yace.

” BAIWAR ita wannan ɗin kurma ce.?”

A fusace Ai’sa ta juyo cikin faɗa tace.

” Ba kurma ba Allah yasa bebiya ce Ni, bazan matsa ba idan duka hanyar dake gefen nan bai isheku wucewa ba, kuta tsayuwa a wajen daga nan har zuwa sanda zan gama tsayuwata.”

Cike da mamaki Bello yake kallon ta, yau yaga ikon Allah, babu ƙira kuma mai zaici gawayi, lallai wannan DOCTOR shine daidai ita, juyawa yayi ba tare da yace komai ba, motar ya buɗe ya shiga tare da cewa.

” Wannan yarinyar bata da mutunci, domin kuwa bazata kauce daga wajen nan ba.”

DOCTOR da yake cike fam da haushinta ne ya buɗe motar ya fice a fusace, yana zuwa wajen yace.

” Ke jakar ƙauye, mahaukaciya ce ke, ko kuma tsabar ƙauyan ci da daƙiƙanci ne yake damunki, ku Yan ƙauye haka kuke sam babu hankali a jikin ku, ki kauce mana a hanya idan ba haka ba, zan takaki da mota kuma na taka banza, wawiya kawai “

AI’SA runtse idanunta tayi cike da haushin Maganar sa, tunda take babu wanda ya taɓa mata zagin da wannan mutumin ya mata, a fusace ta juyo, zata fara zaginsa kawai sukayi Ido huɗu dashi shima cike da mamaki ya nunata da yatsa yace.

” Dama kece, no wonder zakiyi abinda yafi haka, dama can da haukarki a kanki, kauce ki bamu waje.”

Ƙanƙance idanunta AI’SA tayi na rashin mutunci tace.

” Baran matsa ba jakin Birni, kazo ka takani idan ka fasa takani ka raina Allah daya hallice ka, ni da kai waye daƙiƙin yanzu, da nayi niyyar matsawa amma yanzu bazan matsa ba, kayi uban da zakayi, banza marar lissafi.”

Ta ƙarasa maganar tana riƙe kunkumi, tunda yake a rayuwarsa babu wanda ya taɓa masa zagin da wannan yarinyar ta masa, ransa take ya ƙara ɓaci ya hasala, hanu ya ɗaga da niyyar wanka mata mari, tayi saurin kaucewa tana cewa.

” Dakata jakin Birni karka sauƙe fushin ka a kaina da alamu dai yau, mahaukatan aljanun ka suna kanka wata ƙil ma harda daƙiƙanci ke damunka, bari na baka hanya kafin ka sauƙe haukar a kaina.”

Ta ƙarasa maganar tana kaucewa tare da jan hanun Karima suka bar wajen, DOCTOR Zuciyarsa sai tafasa take yi ta gaya masa maganar da ba’a taɓa faɗa masa ba, dama ashe suma ƙauyawa sun iya baƙar Magana wani irin tsanarta yaji tsanar da bai taɓa yiwa wani ɗan adam shi ba, hmmm ya jima tsaye yana jinjinawa Maganar ta…………………..

Last Free page ne shiyasa na muku typing kaɗan yau ƴar uwa idan kina buƙatar wannan rikitaccen labarin mai ƙunshe da Zazzafar soyayya tausayi rikici ban dariya faɗakarwa tare da gurmi, maza ki garzayo kizo ki biya kuɗinki domin kuwa daga yau Free page ya kare bazaku sake ganinsa ba, sai wanda ya biya kuɗin sa ki biya ta👇🏻

0006064512 Rashida Usman Jaiz Bank ko kuma mtn card ta wannan number 08147537180 sai ki turo da shaidar biyan ki ta ita number, 300 Naira kacal zaku biya wacce bata da ƙarfin biyan haka tamin Magana ni kuma zan mata sauƙi yadda zata iya biya Ummu Nasmah tana ƙaunar masoyanta domin kuwa taga ruwan masoya a wannan BOOK ƊIN kun saya sosai.

Kuna iya nuna min Soyayya ta hanyar siyan littafin nan

Vote
Share
And comment

ALƘALAMIN RASHEEDAT USMAN✍🏻

(UMMU NASMAH CE)
[9/10, 11:03 AM] Ummu Nasmah❤️❤️❤️❤️: Cike da ɓacin rai ya koma cikin motar baice musu komai ba yaja motar tare da kallon Bello da idanunsa da sukayi jajur yace.

” Sai wata hanya zamu bi kuma ya kaimu zuwa gidan.”

Bello kwanar dake gefen daman su ya nuna musa, DOCTOR kan motar ya karya zuwa kwanar, suna tafiya Bello yana nuna masa hanya har suka iso ƙofar gida, mai cike da yara suna karatu harda almajirai, bayan DOCTOR yayi parkin ne suka fito da Bello daga cikin Motar tare da nufar wani kyakkyawan dattijo fari sol fuskar sa cike da haiba yana zaune kan taburma ta kaba, sallama sukayi ya amsa musu yana matsa musu ya nuna musu wajen zama, zama sukayi DOCTOR ya miƙa masa hanu sukayi musabaha shima Bello hanu ya miƙa masa sukayi musabaha Malam Gana yana dariya ya cewa Bello.

” Muhammad Bello ko.?”

Murmushi Bello yayi tare da cewa

” Ehh malam ashe baka manta dani ba.”?

Murmushi malam yayi yace.

” Ina zan manta da kai duk sintirin zuwan da kayi wannan ƙauye.”

Dariya Bello yayi yace.

” Hakane, Malam wannan Ɗan uwana ne sunan sa Hassan likita ne shi, Malam mahaifiyarsa ne bata da lafiya yau kusan shekara ɗaya tana kwance anyi maganin asibiti anyi na gida amma babu wani sanji shiyasa nace muzo wajen ka ko Allah zaisa a dace.”

Murmushi Malam yayi tare da cewa.

” Ayya ayya!!! Sannu yaro kaji, yanzu ina take marar lafiyar kunzo da ita dai ko?”

DOCTOR ne yace.

” Eh Malam munzo da ita tana cikin mota ma yanzu haka.”

Tashi malam yayi tare da cewa.

” Ayya ai sai ku sanar dani da wuri suna cikin motar, ku fito da ita maza a shiga da ita cikin gida.”

Da to suka amsa tare da tashi suka nufi motar leƙawa DOCTOR yayi yace.

” Aunty Hajjo ku fito da UMMA.”

Ya faɗa yana buɗe musu ƙofar Motar, fitowa sukayi riƙe da Umma, malam cike da tausayi ya musu jagora zuwa cikin gidan da sallama suka shiga Mama Ferebuwaye tana zaune a shinfiɗar taburma ta karamno ta amsa tana tashi da sauri ta basu taburmar suka kwantar da Umma a taburmar sannan Ferebuwaye ta shimfida musu wata taburmar tana musu sannu da hanya Fanta dake zaune gefe ne ta gaishe su tana musu sannu da zuwa, malam Gana zama yayi a gefe yana ƙarewa UMMA kallo tare da nazarin ciwon nata, sosai ya ƙare mata kallo kafin ya dubi DOCTOR yace.

” Wannan ciwon nata Asiri ne aka mata, ba ciwon Allah da Annabi bane sannan kuma asiri ne mai wuyar karyawa saboda an mata ture harda aljanu shiyasa take wani kamar na marassa hankali.”

Da sauri DOCTOR ya dubi Malam cike da kiɗima yace.

” Malam duk inda mukaje karɓar magani abinda ake faɗa mana kenan, malam anya kuwa Umma zata sami lafiya.”

Ya ƙarasa maganar cike da raunin murya, murmushi malam ya saki tare da cewa.

” Zata warke bi’izinillah, hanune yayi asirin ai, Kuma hanune zai karya sa, na ɗauka maka alwashi da izinin Allah sai na karya wannan sihirin, karka samu damuwa mahaifiyar ku zata warke kamar bata taɓa wani ciwo ba.”

Jinjina kansa yayi tare da cewa.

” Shikenan Allah ya sa mun gode sosai, to yanzu malam nawa zamu bada kuɗin maganin.”

Murmushi Malam yayi tare da cewa.

” Karka damu da kuɗin magani, bana buƙatar su, bana karbar kuɗin magani ina yine fisabilillah, zan mata magani kyauta fatan dai Allah ya mana jagora ya kuma bata lafiya.”

Da ameen dukkan su suka Amsa DOCTOR yana jinjinawa karamci irin na wannan malami da abun duniya sam bai ruɗe sa ba DOCTOR duban Bello yayi tare da cewa.

” To Bello kai da AJIRAM da Fanna zaku koma gida anjuma, ni da Hajjo zamu zauna, ni ɗin ma ba zama zanyi, gobe zan dawo Hajjo ma kaɗai zatayi jinyarta idan yaso sai adinga zuwa ana dubata.”

Da to suka Amsa, Fanta ne ta taho da ƙwarya a hanunta mai cike da nono wacce tasha fura damammiya ta ajiye musu a gaban su, komawa tayi ta ƙara dawowa da wata ƙwaryar tuwon BURABUSKO NE MIYAR GANYEN YAKUWA ta ajiye sannan ta samu waje ta zauna (Yasin nasan idan akwai kanuri mai karatun book ɗin nan yawunsa ya tsinke 🤣) Malam yace musu Bismillah kuci abinci.

Abincin suka ci shidai DOCTOR furar kawai yasha, saboda ransa a ɓace yake baya jin zai iya cin abinci har yanzu Maganar da yarinyar nan ta faɗa masa ne take masa yawo a kunnen sa, hanu yasa ya toshe kunnen sa tare runtse idanunsa yana jin zafin Maganar.

Da gudu Kuwa ta shigo cikin gidan tana tuntsire dariya har da sunkuyawar ta, ADDABO LUTIYA ne ta biyo ta cikin gidan da gudu itama, ƙara AI’SA ta saka sanda su Hajjo suka tsorata DOCTOR da sauri ya buɗe idanunsa yana duba wajen da ƙarar ta fito, fes ya ɗaura idanunsa akanta cike da tsana yake kallon ta, Malam ma cikin ɓacin rai ya dubeta ita kuwa ɗakin Kaka ta shige tana cewa.

” Na shiga Uku kaka, wannan ɗimemiyar mai ƙirar samudawa zata kashe ni, dan wallahi tana zama a kaina sai dai wata amma ba niba.”

KAKA dake zaune tana ɓarar gyaɗa ne ta rarumo sandar ta, ta miƙe da ƙyar ta fito bakin ƙofa ta tsaya, turus ADDABO ta tsaya tana ajiyar Zuciya kallon ta kaka tayi tace.

” To Uwar marassa kunya, yanzu biyota kikayi har gidan ubanta ki daketa Saboda baki da mutunci, to ai ko mutuwa ma tana Kunyar idon uwar ɗa bare kuma ke, maza fice min daga cikin gidan nan kafin na raɗeki da sandar nan, marar Kunyar wofi “

ADDABO cike da haushi tana haki tace.

” Wallahi kaka bazan bar nan ba, sai nayiwa Ai’sa shegen duka, uban waye yace ta ce min ADDABO ƳAR LUKUTA MAI SIFFAR KWAƊI Allah bazan yadda ba sai na rama.”

Ta ƙarasa maganar tamkar zata saka kuka, ai kuwa tun kafin kaka tayi magana, AI’SA ta rigata cewa.

“Ubanki ne, tunda sune suka haifeki ƴar lukuta, Kuma na faɗa ADDABO ƳAR LUKUTA MAI SIFFAR KWAƊI, ƙarya nayi ke ba mai siffar kwaɗin bane, kiga fa yanda kike dunƙule kamar kwadon.”

Kaka dariya tasa tare da cewa.

” Shakka babu jikata Ai’sa batayi ƙarya ba, kamarki sak da kwaɗin, dubeki fa tsabar dunƙulewa da kikayi ko wuya baki dashi, zaki kauce min a ƙofar sauro ne ko sai naci uwarki SA’A mai koko.”

DOCTOR Kaka kawai yake bi da kallo mai cike da ɗunbin mamaki, yau yaga ɗaurewa ƙarya gindi, yarinya ta nemo faɗa, ta gudo gida maimakon a hukuntata sai kuma a ɗaure mata gindi Tabbas dole wannan yarinyar tayi rashin kunya.”

Girgiza kansa kawai yayi yana ƙara jin wata irin sabuwar tsanar yarinyar, idanunsa ya ɗan rufe tare da buɗesu yana cigaba da ƙarewa kaka kallo na marar adalci, Malam Gana tashi yayi ya nufesu, sanda yaje ya tsaya a gaban ADDABO cike da kulawa yace.

” ADDABO kiyi hkr kinji duk naji abinda kikace ta miki, kiyi hkr bata kyauta ba, Kuma insha Allah zan hukunta ta, bazata ƙara miki ba kinji.”

ADDABO cike da jin haushi ta jinjinawa Malam kai kafin ta juya ta fita tana ƙananan magana, kaka ce tace.

” Zata sake !!! Nace sai ta sake tsokanar tata, kazo kayi abinda zakayi, har wani zaka hukunta ta, to hukunta ta mu gani, tunda kana gadarar kai ubanta ne, to bari kaji wallahi babu ruwan ka da yarinyar nan, ka fita idanunta ka barta tayi abinda take so haka kawai kunsa yarinya a gaba.”

Malam Gana cike da girmamawa ya cewa mahaifiyar tasa.

” Allah ya huci Zuciyarki AMMA (dake haka yake kiranta dashi), amma AMMA baki ganin abinda A’ISHA take a cikin garin nan yayi yawa, ina guje mata bakin duniya ne AMMA kar bakin mutane yayi yawa a kanta bakin mutane guba ne wani bakinsa bashi da kyau, abinda nake so ki fahimta kenan, saboda ita macece wa zai yadda ya aureta da wannan rashin ɗa’ar da take dashi ni kaina uban da na haifeta zan bada shaidar rashin kunyarta dan Allah Amma ki daina biye mata na roƙeki.”

Cike da faɗa kaka tace.

” Ni na auru ai ko tunda har na haifeka, tunda na auru to Itama zata auru domin kuwa na fita faɗa sanda nake kamar ta, Kuma a haka ubanka yake sona Ko ɓacin raina baya so, haka zamuyi faɗan mu, cikin dare ya rarrashe ni, mu shirya, dan haka karka kuskura ka mata mungun baki, juyawa tayi ta kalli Ai’sa tace mata, Ai’sa duk wanda ta miki a cikin garin nan kema ki masa karki raga masa ko ubansa waye ne.”

Wani ɓacin rai Malam Gana yaji a cikin ransa harga Allah baya jin daɗin abinda AI’SA keyi, sannan baya son irin tarbiyyar da kaka take bata, ɗan yaune kawai ka haifesa baka haifi halinsa ba da Ai’sa ta ɗauko sa ko yatsa aka sa mata a baki bazata ciza ba, juyawa yayi ya koma ba tare da yacewa kaka komai ba, amma sam ranshi babu daɗi, kaka komawa tayi cikin ɗakin itama tana zungurin Ai’sa da sandar hanun nata tare da cewa.

” Munafukar Allah, da kika tsokanota da ta riƙeki, ta zaune a ruwan cikin ki da wannan ɗimaɗiman ɗuwaiwan nata, da sai kinyi kashin hanjin ki, gobe na sake jin kin tsokanota kiga yadda zan barki da ita ta jibgeki kamar Allah ne ya aikota”

Bakin ta Ai’sa ta tura cike da rashin mutunci tace.

” Malama daina zunguri na mana, niɗin shegiya ce zan tsaya harta dukeni, kuma wallahi ko gobe na ganta sai na tsokanota.”

Ta ƙarasa maganar cike da tsiwa tana fita, wajen Mama ta wuce tana ganin su Hajjo ko kallon su batayi ba zata wuce, Malam ya kirata.

” Ke AI’SA zonan.”

Tahowa tayi tana tura baki ta tsaya a kansa ba tare data risina ba tace.

” Gani Malam.”

Malam ɗaga kansa yayi ya kalleta cikin ɓacin rai yace.

” Bani maganin nasha, kinji uwata tunda kin tsaya a kaina.”

Bakin ta tura tare da zama tayi shuru Malam Gana faɗa ya hau mata.

” Wai yaushe zakiyi hankali ne kam, sam ke a Duniyar ki baki daraja mutane, Ai’sa ina son ki dawo hankalin ki ki nutsu kisan me kike yi bana son duniyar ta nuna miki kurenki domin kuwa baza kiji daɗi ba, jiyan nan Malam Umaru ya kawo min togaciyar ki kin zagesa, sa’anki ne shi, to wallahi ki kiyayi duniya, ki daina biyewa AMMA tana ɗauraki a turbar da ba itace gaskiya ba, ina miki faɗa ne a matsayina na mahaifinki, sannan kina kallon Mutane bazaki gaishe su ba, sai ki saka kanki ki wuce, to maza ki gaishe su.”

Ƙara turo bakin tayi gaba, kafin ta kalli su Hajjo tace.

” Inda dabtu.”

Ta gaishe su cikin harshen kanuri, amsawa sukayi cike da mamakin yarinyar, juyowa tayi zata ɗagawa su DOCTOR gaisuwa, karaf kuwa suka haɗa Ido dashi, zaro ido tayi tana mamakin meya kawosa gidan su, shi kuwa harara ya wurga mata, tsuka taja tare da cewa.

” Malam ya isheka harara ta, sai wani kallon banza kake min da wasu ƙananun idanunka kamar wanda ka roƙa aka sammaka, an faɗa maka gaishe ka zanyi da kake shirin nuna min IZZA, Mtsss!!!! Marar lissafi kawai.”

🤣 Kuzo kuga baƙin ciki a ZUCIYAR DOCTOR ji yake kamar ya shaƙo wuyanta sai ya kaita lahira kafin ya saketa, yunƙura yayi zai tashi, Bello yayi saurin riƙesa yana girgiza masa kai, alamun ya bari baƙunta sukazo, komawa yayi ya zauna iya jin wani takaici yana hauro masa, Malam Gana cike da haushi ya yunƙura zai jawota ya mata shegen duka, ganin haka da AI’SA tayi ya sata tashi ta fice da gudu, cike da jin haushin abinda ta musu Malam yace.

” Kayi haƙuri Yaro kaji ɗan yaune ka haifesa baka haifi halinsa ba, haka nake fama da Ita, kayi hkr, ka mata addu’ar shiriya.”

Tsabar takaici DOCTOR kasa amsawa Malam yayi, shi dai bai taɓa tsanar mutum ba, irin yanda ya tsani wannan yarinyar.

Awansu biyu Malam ya fara yiwa UMMA magani bayan ya bada ɗaki guda wanda za’a ajiyeta a ciki da la’asar lis DOCTOR ya bawa Bello kay ɗin mota yace su koma gida, gobe da azahar yazo ya ɗauke sa, haka kuwa akayi suka kama hanyar cikin Maiduguri har suka tafi Ai’sa bata dawo cikin gidan ba.

✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨

 *MAIDUGURI*

“What!!!! Kasan kuwa mai kake faɗa min kana nufin sun tsira karka cemin sun isa cikin ƙauyen nan.!!”

Daga can Jamo yace.

” Ehh sun tsira gaskiya, nayi duk yanda zanyi dan ganin basu kwana a duniya ba, amma abun yafi ƙarfi na, saboda Yaron yana da mungun wayo.”

Tsuka Jummai taja tare da kashe wayar kanta ta dafe zuciyarta sai famar tsinkewa take, a fili ta furta.

” Ina bazai yiwu ba, bazan bari YAMURAM ta dawo cikin hankalinta ba, dole sai ta bar numfashi a duniya dole ne ma, zanje wajen Malam gobe, idan har ya tabbatar min zata sami lafiya ni kuwa sai nasa an bita har cikin ƙauyen an Kaita lahira.”

Ta ƙarasa maganar tana huci, sai kuma taja tsaki tare da kwanciya cikin tashin hankali.

       *UNIMAID*

A matuƙar gajiye suka fito daga lectures ɗin Maji ne ta dubi Falmata tare da cewa.

” Muje Capteria yunwa nake ji sosai wallahi, tun abinci safe kinga yanzu har 3:40.”

Juyawa sukayi suka nufi Capteria suna taɗi, waje suka samu suka zauna Maji ta dubi Falmata tace.

” Me za’a kawo miki, ni jalop nake bukata.”?

Numfashi Falmata ta sauƙe tare da cewa.

” Babu abinda zanci ruwa kawai nake buƙata nasha magani.”

Kallon ta Maji tayi tare da cewa.

” Me kikaci da zakice kin ƙoshi, Wai Falmata na lura tun ɗazu lectures ɗin da ake babu rabin hankalin ki a kansa, duk rabi ya tafi ne a tunanin mutumin da baisan darajar ki ba, a rayuwarsa ki dawo hankalin ki, ki manta da wani Hassan a cikin rayuwarki, domin kuwa shi ya juma da mantaki tunda harya sakeki dan haka ki daina ɓata lokacin wajen tunanin mutumin daya manta ki a duniyar sa, yanzu dan baki da hankali ke sai kisha magani ba tare da kinci abinci ba.”

Murmushi mai ciwo Falmata tayi tare da cewa.

” Bazaki taɓa fahimtar irin Soyayyar da nake yiwa DOCTOR bane, da ana iya cire Soyayya da ƙarfi a cikin zuciya dana cire Soyayyar DOCTOR daga cikin raina, sai dai hakan bazai yiwu ba, saboda bani nake da iko da zuciyata ba, ni kaina nasan bana cikin zuciyar DOCTOR, sai dai ina mamakin yanda ni kuma yake maƙale a cikin zuciyata, kullum Soyayyar sa ƙaruwa take a zuciyata maimakon ta ragu, lissafi na yakan ƙauce min a duk sanda na gansa ina son mijina Maji bazan iya doguwar rayuwa babu shiba, taya zanyi DOCTOR ya dawo gareni, ki taya ni neman hanyar da zan koma gidan mijina ƙawata pls.”

Tunda ta fara Maganar maji take kallon ta cike da haushin ta, tsuka taja tare da cewa.

” Wai ke Falmata meyasa shashasha ce ke a cikin Soyayya, meyasa kike ƙaunar mutumin da baya ƙaunar ki, meyasa kike son mutumin daya Raina iyayenki, shin kishin iyayen kine bakya yi, ko kuma kinfi sonsa ne sama da iyayen ki, wallahi Falmata ina jin haushin zuciyarki, da ana bada aron zuciya dana baki aron tawa ko Allah zaisa ki cire Soyayyar wannan ɗan iskan azzalumi wanda bashi da imani bare kuma tausayi, Falmata idan har nine kike tunanin zan share miki hanyar da zaki koma gidan Hassan to ki saka a ranki kin rasa sa kenan har abada, domin kuwa na gwammace na ɗebo ƙayoyi na watsa a hanyar domin ki rasa wajen takawa bare kuma ki shiga.”

A fusace Falmata ta miƙe tsaye cikin ɓacin rai tace.

” Maji ya isa haka ki daina zagin DOCTOR, kina ƙona min zuciyata ne idan kina aibata sa, Maji, wallahi komai tsinin ƙayar dake Hanyar gidan DOCTOR zan juri takata domin ta isar dani har cikin gidan sa, na faɗa miki zuciyata bazata taɓa iya doguwar Rayuwa babu DOCTOR a tare dani ba.”

Kaɗa kanta maji tayi tare da cewa.

” Lallai kina cikin masifa da jarabawa…………………”

Ki biya ki karanta yar uwa, 0006064512 Rashida Usman Jaiz Bank ko kuma mtn card na 300 sannan ki turo shaidar biyan ki, yafi miki sauƙi akan a baki wanda ba gumin kiba

Alƙalamin UMMU NASMAH CE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button