Hausa Novels

DOCTOR HAJAR COMPLETE

DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Related Articles
GODIYA

Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah. Mai kowa mai komai muna neman gafaransa. Ya Allah ka azurta mana tsoranka wanda zai iya hana mu sab’a maka. Ina kodiya a gareka Allah daka bani ikon fara wannan littafi lfy Allah kasa na kareshi lfy Allah ka bani daman isar da sak’on da nakeson isarwa ga Al’umma Allah kasa kuma ya amfanesu Allah ka ganar damu abunda bamu ganeba Allah karabamu da sharrin duk wani me sharri Allah ka biya mana buk’atunmu ……

*TSOKACI*

Wannan labarin ba gsky bane be faruba k’irk’iranshi nayi kawai don nisha d’antar da masu karatu ,Allah ka bani ikon isar da sak’on da nake fatan ze amfaneku insha Allah duk wani wanda ze karanta labarin don haka ina rokon yan uwana da duk yanda kukaga littafin ya kasance karku ce komai cox haka na riga na tsara…

*SADAUKARWA*

Na sadaukar da wannan Littafin gareki yar uwata HAJARA HUM’D BUBA Allah ubangiji ya cika miki burinki Allah yaji k’an mahaifinki yasa haske kabarinshi Allah ya Albarkaci ruyuwanki Allah ya rayaki muga har auren ki ,Ameen……

KUNA RAINA YAN MUTUNCI

Neeratluv my Besty
jannat (k’awar arziki)
My zee yabour
First lady
Husna Bauchi
Zara Bukar
Mss Xoxo
Yar ficika
Sajna
Aisha Abbakar
Khadija Candy
Maryam S Bello
Anty Khadee
Mummy Sultan
Maman ihsan
Beebei dee
Zara B-B
Action baby
Ayusha Ilyasu

Da sauran wanda ban lissafoba duk kuna raina ina muku fatan Alkairi Allah ya k’ara muku basira da, daukaka Allah ya rabaku da sharrin mak’iya😍

Ban manta dakuba yan group d’ina (D&W Novels) Nagode ,da irin son da kuke nuna min Allah ya barmu tare ya k’ara had’a kanmu, ya biya muku buk’atunku Ameen…

LITTAFIN MARUBUCIYAR

FANSA (RIVENG)
BURIN MINAL
NADIYA
ZURI’A D’AYA
K’IYAYYAR NAMIJI

   KANO

“Kaga Malam pls live me alon na fad’a maka wai ana soyayya dolene? Kafa takura ma rayuwa ta”.

“Baiwar Allah don girman Allah kiyi hak’uri ko sunanki ki fad’a min pls I’m begging u,” sai kuma kayi ae, khadija zomu tafi ” kije ina zuwa” khadija ta fad’a ranta ‘a b’ace …

Wucewa tayi tabar khadija wurin kallon mutumin khadija tayi tace “bawan Allah kayi hakuri da ‘akwai dalilin dayasa kaga tak’i sauraron ka ‘amma kar kayi fushi insha ‘Allah zan shawo maka ,kanta ga number na, za muyi waya dakai duk yanda mukayi da ita”..

“Ok na gode (god bless you) ” murmushi khadija tayi tace “Ameen sai anjima”, har zata wuce ya tsaidata da cewa , pls baki fad’an sunan kiba da kuma sunan k’awar taki “ohhh sorry sunana khadija ita kuma Hajo ” wow ashe sunan mamana gareta”, Allah sarki tow barin wuce kar tayi ta jirana ” ok tow thank you very much Nana Khadija am captain murad by the way” ur wlcm captain sunan babana gareka so bazan iya fad’a ba” Allah sarki ,kice zaki dinga gaisheni har k’asa kenan duk sanda muka hadu” murmush tayi tace “maizai hana barin tafi kar tayi ta jirana” ok tow ki gaida mun ita kow bye”….

Tawuce ta , tafi da Sauri don tasan ba k’aramin aikin Hajara bane tatafi ta barta..

“Dallah yar rainin wayo kin sani sai jiranki nake , kuma kinsan nace miki zan d’auki Jawahir a school” fuskar Khadija ‘a d’aure tace sorry tow muje”..

Tunda suka fara tafiya babu wanda yawa wani magana cikin su, Hajar ta fahimci khadee haushinta ,take ji , murmushi tayi tace “Khadee wai yanaga sai wani 6ata rai kike?”.

“Hmmm Hajar kenan ba dole na 6ata rai ba wlh abunda kike baya dacewa sam” rayuwan duniya tana kunshe da abubuwa da yawa, na d’aya farin ciki, bak’in ciki, haduwa, rabuwa ,samu, rashi lafiya, ciwo,mutuwa, Annabi ya horemu da muyi hakuri da duk wanda mukayi karo dashi domin ba zai dauwama ba, zai wuce.

Amma ke sam kink’i mance abun daya riga ya wuce she karu biyar da suka wuce, haba Hajar wlh kiwa kanki fad’a, shi kenan haka zak k’are rayuwanki bazakiyi aure ba ‘ina gudun ranar da Jawahir zata buk’aci ki ,kaita gurin mahaifinta, mezaki ce mata ?wacce amsar kike da ita da zaki fad’a mata? I hope kin tanadesu?”.

“Hmmm Khadee wlh bazan ta6a iya mancewa da abun daya faru ba ‘a kullum na kalli Jawahir sabo yake zamamin Khadee namiji bad’an goyo bane Bazan kuma yarda dawani d’anamiji a rayuwata ba, namiji mugune Allah ya isa min”ta k’arashe tana kuka ,

Kiyi hakuri Hajar nasan abune mai wuyar mancewa a gareki bake kad’ai ba har muma bazamu mance ba Amma idan kinyi la’akari bafa duka maza bane masu mugun hali kuma keba yarinya bace yanzu Dr Hajar”…

“Duk nayarda da abunda kika fad’a Khadee Amma mubar zance kawai, don kina tayar min da ciwan dake damun zuciyata ne kawai”. da haka suka isa school d’in su Jawahir suka d’auko ta sannan suka d’auki hanyar d’anladi nasidi

A hotoro Dr Hajar ta ajje Khadee ita kuma suka, k’arasa cikin estate d’in Ibrahim kunya wani k’aton gida suka shiga mention wanda ya gaji da haduwa daga gete din gidan, anrubuta wlcm to Doctor galadanci house da wani abu me kelli…

Cikin gidan kuwa abun kallone don komai da tsari aka yishi ginin gidan sama ne, wanda ‘akwai wurin da zaka iya ganin mutanen waje wurin da glass akayi shi, wasu furanine a zagaye a gidan masu bada wani kamshi me kwantar da hankali cen gefe guda kuwa wurin shak’atawa ne wanda yasha kujeru na alfarma sai kuma wurin parking spaces wato gurin (ajje motoce) motoci guda bakwaine a gidan ferari da BMW lemozin CRV Lombagini Land rovar sai 406 wanda ake kai yara school…

Daga ,gefe guda kuwa akwai k’aton masalaci had’ade ,sai kuma d’akin me gadi kusa da get din gidan ,get din kofee brow ne me remot da an danna ze bud’e kansa, sai kuma k’asan gidan dayasha intalock masu kyau kalan ja da ruwan toka,

Karnuka ne kwance wurin guda shida masu kama dana surawa sai harkan gabansu suke kala kala…

Fitowa tayi ta kama hannun jawahir suka nufi wata kofa me kyau ,dannan bell tayi wata yar budurwa tazo ta bud’e mata ga dukan ‘alamu yar aikin gidan ce , da murmushi ta kar6i jakar dake hannun Dr Hajar da kuma lunch boxs din dake hannun Jawahir ,

Shiga sukayi suna shiga k’amshin abinci ya daki hancin su , wuri coredor ne haka sai kitchen ta gefe sai kuma wani k’ofa transperant ana iya ganin nawaje amma nawaje bazai iya ganin na ciki ba, falow ne wurin yasha royar chairs ruwan madara da goldin masu masifar kyau da laushi cen gefe guda kuwa daining aire ne shima royal ruwan madara da goldin sai kuna wani drowar da aka ajje cups dasu madara confals da sauran su zubi da tsarin falon yayi ga wani taf keken tv tare da stand dinshi na gani a fad’a gefe guda kuma stairs ne me hannun k’arfe yasha carpet gefen wurin anjera wasu cendulls masu bada wuta different colos sai kuma wani shoglass wanda yasha humurori da turarukan wuta masu k’amshi

Hawa saman sukayi nan ma wani falow ne wanda taci uwar na k’asa a haduwa ,kujerun ciki royal ne suma amman ruwan toka hannun kuma sky blue da carpet dinma haka sai santa tabel kalan jikin hannun kujeran ,sai katon tibin bango wanda sai wane da wane ake ganin irunsu a gidan su gefe guda kuma wani standard a.c ne, had’ad’e gefe da gefen gurin t.v kuma wasu manya manyan sufiku ne tare da hufan su,falon ba k’arya yayi k’amshin turaren wutane kawai ke tashi sai sanyi ac dake bugawa gidan shiru babu hayaniyar kowa sai tv dake aiki sai kuma na’urorin gidan na more rayuwa ,cikin falon akwai daki daya sai kuma da’an fito akwai dakuna guda uku daya na kalifa daya na Dr Hajar d’ayan kuma ciki da falo ne shima na ‘alfarma shi kuma na mahaifin sune…

Zama tayi kan lalausar kujeran dake falon tana ,maida numfashi irin ta gaji dinnan, kuma kowa yaga fuskarta yasan bata, da walwala kuma tana cikin damuwa, “Alawuya ina Mami” ta fad’a tana cirewa Jawahir doguwar rigan school din ta” tana d’aki bata jima da shigaba yanzu bak’inta suka tafi” ok maybe ta shiga sallar la’asar ne ,yau me kike dafa mana?” Sakwara miyar igusi sai kuma marfesun naman kai sai gashe -shen kifi da ,dankali,” wow my best food yau zanci abinci kenan na koshi kin kusa gamawa?” Eh miyar igusi da farfesu suna wuta sakwara da kifi da dankali kuma nagama su”…

“Yawwa tow kiyi sauri ki gama kafunnan nayi wanka sai naci, yanzu tafi da Jawahir ki hada mata confax tasha” suna fita Dr Hajar ta fara sana’ar nata wato tunani , har Hajiya ta fito bata sani ba ,saida ta dafata sannan ta dawo daga duniyar tunani data shiga..

“Wato Mamana ,har yanzu baki dena tunanin nakiba kow? kina so ki sawa kanki hawan jini a banza .

Hajara!! mun fiki jin d’aci da zafin abundaya faru” a razane Dr Hajar ta dago tana kallon Hajiya tana hawaye don wannan shine karo na farko data ta6a kiranta da sunan Hajara saboda mamana take ce mata saka mak’on sunan maman baban su Hajar d’inne..

“Amman mun fawalana Allah tunda munsan k’addara ce zata iya fad’awa kan kowa , tow ke don meyasa bazaki kar6i k’addarn kiba ? Jarabawa ce Allah yake miki kuma ina miki fatan Allah ya baki ikon cinye ta.

Manzan Allah ya bamu addu’a yace Wanda ya gamu da wata masifa ko bala’i tow ya dinga karanta wannan adu’ar insha ‘Allah zai samu waraka,

inna lillahi wa-inna ilayhi raji’oon, allahuma -ajurnee fee museebatee wakhluf Lee khayran minha.

Fassara:mu daga Allah muke kuma hak’ika mu ,masu komawa ne zuwa gare shi ya Allah !ka bani ladan hakurina a kan wannan masifa kuma ka mayar mini da abin da yafi ta alheri..

Kow kuma ki dinga yin wannan addu’ar yayewar baqin ciki.

Wanda ya hadu da bakin ciki ko damuwa aharkan rayuwa ,ana so ya yawaita karanta wannan addu’ar isha Allahu Allah zai yaye masa dukkan damuwarsa ,kuma zai saukaka masa dukkan lamarin sa.

ALLAHUMMA LA SAHLA ILLA MA’A JA’ALTAHU SAHLAN WA’ANTA TA JALUL HAZNA IDHAA SHI’ITA SAHLAN..

MA’ANA:ya Allah babu wani abu sassauka sai dai abinda ka saukaka .kuma kaine idan kaso kake sanya bakin ciki ya zama abu mai sauki , Aduba SUHIHU IBNI HIBBAN hadisi mai lamba 2,427 IBNUS SUNNEE hadisi na 351 domin k’arin bayani..

“Kuma ki yawaita salatin annabi da karatun Alkur’ani, ya fiye maki wannan tunanin da babu inda zai kaiki”…

D’agowa tayi tana hawaye tace”nagode Hajiya insha ‘Allah zanyi amfani da ‘abunda kika fad’a min”.

“Yawwa mamana ‘Allah ya miki albarka”..

“Ameen Hajiya barinje na watsa ruwa nazo na ci abinci”..

“Tow sai kin dawo ina takwara ta?” Tana k’asa wurin Alawuyya”..

D’aki tashiga kai d’akinta kawai abun kallo ne pink color ne dakin da fari komai naciki pink and write ne, kaya tacire ta dauki towel ta shige toilet tayi wanka tayo alola , tana fitowa ta d’auko wani riga da wando na kanti marasa nauyi tasa wandon skin tait ne baki dogo har k’asa sai riga ja me hannun bes da hoton mage a gaban rigan wanda ‘aka zana da bakin abu doguwa amma baikai gwaiwa ba kama kanta tayi da ribbon ta d’auki hijab ta ,tada sallar la’asar…

Tana idarwa saiga Alawuyya da Jawahir sun shigo , littafin add’u’oin ta ,ta dauka ta fara karan tawa, alawuya kuwa toilet suka shiga tayiwa Jawahir wanka ta samata wani doguwar ,riga mara nauyi mai lk’aramin hannu…

Dr Hajar na idarwa tasa Jawahir a gaba saida tayi bacci sannan ta sauka k’asa doncin abinci, daining area ta wuce nan tayi karo da mahaifinta doctor galadanci da Mami da Khalifa sunacin abinci. Da fara’a sanye a fuskarshi yace “mamana dama kin dawo?” itama murmushin tayi tace yes tun d’azu na dawo ” ok amma mum d’inki bata fad’an ba don tsabar son kai ita taganki amma ni bata sanar dani kin dawo ba” a zolaye yayi maganar yana kallon Hajiya , dake murmushi kawai tace”tsakanin ku da yarka ai sai kai, nima lokacin da kake bata abu sani nake ae saidai na ganta dashi “dariya kawai yayi ita kuma ta nemi waje ta zauna ta fara cin abinci…..

WACECE DR HAJAR DA KUMA ‘ASALIN SU

Dr Hajar yar ce ga Dr Muh’d Tahir Galadanci da hj Asma’u, Dr Galadanci babbab likitane yana da babbab hospital me suna get well special hospital, Dr Galadanci ba karamin atajirin mutun bane yana da dukiya me tarin yawa, yana da matarshi ta ‘aure guda d’a Hj Asma’u auren soyayya suka Hj Asma’u yar bokoce sosai Amman bata ‘aiki saboda Dr kafun suyi aure ya nuna mata baya buk’atar tayi wani aiki inde kud’i shi ya d’auki nauyin babu abinda zata nema tarasa ‘a gidanshi Hj Asma’u saida ta shekara 3 gidan miji sannan ta samu ciki ta haifo santaleliyar yarta me kama da maman mijinta sak, Dr Galadanci yayi matuk’ar farin ciki da kyautar da Allah yayi musu don tunkan yayi aure yake kwad’ayin idan yayi aure Allah yabashi d’iya mace don yasa, sunan mahaifiyar shi Hajara ,sai kuma ‘Allah ya karb’i addu’ar shi, ranar suna yarinya taci sunanta Hajara, mahaifiyar Dr ta d’auki son duniya ta d’aura wa Hajara haka iyayen tama sunaji da ita basa k’aunar suganta cikin bak’in ciki duk abunda takeso to shi ake mata, tundaga lokacin da aka haifi Hajara Dr ya maida sunan hospital dinshi sunan ta, kuma yaci burin saitayi zurfi a karatunta ta zama babban docton mata hakan yasa ya tsaya mata ‘akan karatunta sosai,

Dukda irin sakalcin da suke nuna mata be hanasu bata tarbiyya ba, tun tana jss 3 mahaifinta ya d’auketa ya kaita chaina ‘anan ta k’arasa secondary school d’inta har jami’a, bayan ta gamane tadawo naija tayi NYC d’inta sannan ta koma london tayi masters d’inta tow daga nan kuma tafara aiki a hospital d’in mahaifinta, bawai don taso ba taso ace ya barta, tayi Phd kafun ta fara aiki. Saida ta shekara 13 da haihuwa sannan Hj Asma’u ta sake samun wani cikin ta haifo san talelen danta beby boy shi kuma yaci sunan mahaifin Hj Asma’u tow tundaga lokacin Allah be sake basu haihuwa ba..

ASalin su yan Adamawa ne amman suna zaune a garin kano mahaifin Dr ya rasu tun yana ciki shi kad’ai mamarsa ta haifa, tow tundaga lokacin bata sake aure ba tanan Dr yayi mata gidanta me kyau tare da masu kula da ita..

Dr Hajar ba fara bace sosai kuma ba bak’a bace, tana da hanci dai-dai misali tana da yalwar gashin ido dana gira tana da gashi sosai tana da ken jiki dadi Dr Hajar tayi tako ina don zan iya cewa tacika goman lol tsayawa fasaltata b’ata lokacin me karatu ne

Wannan shine tak’aitaccen labarin Dr Hajar

masu karatu
Hope zaku biyoni don jin cigaban wannan lbrn comments dinku shine k’arfin gwaiwa naπŸ˜‰

Ya kuke gani acigaba ne koya?

Sai naji daga, gareku zan cigaba……

DIJA_WAZIRI CEπŸ‘Œ
[18/12 7:31 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

DOCTOR HAJAR πŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Allah yana jaraftar bawanshi ta kowace hanya don yaga iya k’arfin imanin shi,

Dukkan tsanani yana tare da sauk’i ,duk abinda kaga ya sameka na farin ciki kona bak’in ciki tow ka da’uki hannu ka gode wa ‘Allah kuma ka ,kusan cesa ,sosai insha ‘Allah zai yaye maka dukkan damuwar ka

idan ka rasa abinka, kada ka rasa hankalinka, damuwa bata maidoda b’atacce ,bata dawoda matacce, bata hana k’addara yin Aikinta. Barwa Allah duk abinda ya sameka ,sai Allah ya isar maka duk Al’amuranka

nasiha ce Allah yasa mudace

Dedicated to Sadfa, Faty azland, zara k’awata, ummixey ,kuna raina Allah yabarmu tare πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”πŸ’”

Jannat mungode da soyyar Allah ya biyaki da gidan Aljanna, 😍

Naga sabon buk yanda kika fara lfy Allah ubangiji yasa ki gama lfy, Allah
Yasa mutane su amfana da ‘abunda kike son fad’akarwa AmeenπŸ™

Chapter 2

“Madam dan Allah ki taimaka ki shigar da files d’ina gurin likita d’ana zai mutu, ” kinga Malama na fad’a maki mutane sun rugaki ha’a nifa kin dameni ” haba!!, baiwar Allah ke kuwa ki taimaka mata mana bakiga yanda ‘d’an yake burgima kamar zai mutu ba,” kaga Baba ,babu ruwan ka nagafa mutane sun rugata”….

“Tow Allah ya kyauta ‘amman gsky inde haka wannan asibitin yake gara mutun yaje na gomnati” kiyi hakuri Baba na tabata da Dr Hajar me asibitin tana kusa da wlh kunshiga…

Bayan minti 20

Subhannala ya take amai meke damun ta ? Ina nurses d’in suke? wlh tun jiya take fama da ‘amai da gudawa shine muka kawota ‘tow munyi munyi da masu gurin su shigar damu muga likita sunk’i “…

“Ya salam jamila “Na’am Doctor ” ku tafi dasu x ray aje yai masa maza sai kuzo yaga Doctor kuma karnaji karna gani ,zanje naga patient d’ina nasan suna jirana “ok ma’am….

Dr Hajar tana wucewa mutanen dake zaune wurin suka fara k’usk’us, “wannan fa itace me Hospital din bakuga yanda take da mutunci ba tasan darajan dan adam ” gsky kam wlh saida muce Allah ya saka mata “kugafa tsabar karamci cewa tayi aje ayi masa kyauta”…

Dr Hajar tana fita bata tsaya ko inaba sai gainic word nan tad’an duba marasa lfy daga nan kuma ta wuce dakin masu rainon ciki suma ta duba su…

“Baiwar Allah ki bama bebyn naki mama bakiga sai kuka yakeyi ba ” Matar dake kwance kan gadon ke faman zubda hawaye ,tayi shiru bata iya cewa da Dr Hajar komai ba , kallon matar dake jinyar ta Dr Hajar tayi tace meke damun ta ?” wlh Doctor nima na rasa meke damun ta ,tun jiya da aka haifi yaron take ta faman kuka kuma taki shayer dashi “..

“Tow ina mijin ta ?” shiru matar tayi nadan sakanni sannan ta d’ago ta kalli Dr Hajar dake jiran mezata ce”Bashi da uba ” Dr HAJAR sai da taji tsikar jikin ta ya tashi nan danan taji duk wani walwala da farin ciki sun kushe mata ,tausayin matar duk taji ya kama ta …

” Yan fashine sukazo har gida suka kashe iyayen ta sannan kuma suka bata mata rayuwa “sosai Dr Hajar tajin jinawa matar zama tayi kan kujeran dake kusa da gadon matar fuskar ta ba walwala don ta fama mata wani ciwo dake damun ta shekaru 5 da suka wuce, hannun tasa ta d’auki yaron sannan ta fuskanci inda uwarshi ke kwance fuskarta dauke da hawaye ta fara magana…

“Nasan dole zakiji zafin abunda ya faru dake ,kuma dole duk sanda kika kalli yaron nan sai kin tuna abun daya faru, amman don Allah kiyi hakuri ki shayar dashi, ki sani cewa, wannan dan besan komai ba kuma bashi da laifi….

Daker Dr Hajar ta lala6a matar ta karbi yaron ta shayer dashi ,ita kuwa tana fita office dinta ta shiga ta kulle ta fara kuka me tsuma zuciya
Tare da tunani barkatai, nocking d’in da akayi ne yayi saurin dawo da ita daga tunanin data shiga ,cikin sanyin murya tace “yes who is that? “Daga b’angarin wacce ta buga kofar ne tace khadee ce” ok come in”….

“Morning Dr Hajar ya aiki “lfy Alhmdul ya naki aikin? lfy qlau “tow masha Allah ….

“Dr Hajar ya naganki wani iri yau kamar akwai abunda dake damunki? ” k’akalo murmushi tayi tace”wlh babu komai kawai wata matace yau ta bani tausayi “eyyah meya sameta? Hmm ni bana ma son fada kawai dai haihuwa tayi kuma yaron data haifa bashida uba kuma itama marainiya ce yan fashi ne suka kashe mata iyaye kuma suka b’ata mata rayuwa, kai dai dakinga matar zakisan tana buk’atar taimako “..

“Allah sarki ,kai Allah ka rabamu da sharrin mutun da Aljan Allah kuma ka rabamu da azaluman mutane “Ameen dai ni yanzu inaga zan taimaketa tunda tace ko gidan da zata zauna bata dashi kuma bata da kowa tow inaga zan taimaketa na kaita gidanmu har Allah ya kawo lokacin da zatayi aure…..

“Dr Hajar kinko san me kike fad’a gsky nidai ban goyi bayan ki kaita gidanku ta zauna ba inama laifin ki taimaketa ki bata wasu yan kudi da zasu isheta ta dan fara juyawa, Amman kawai daga mutun yace miki gashi gashi harkin yarda da ita tow idan kuma karya take miki fa ya zakiyi da ita? “…

“Hmmm khadee kenan ni nasan ba karya takeyi ba, kuma karki manta Allah yace idan kana da hali kaga na k’asa da kai yana cikin mawuyacin hali ka taimake shi tow don meyasa zaki hana? “..

“Nasan da haka Dr ae yanzun ma bance karki taimake taba, zaki iya taimakanta amman karkiyi kuskuren kaita gidan ku, cox mutun yanzu ba abun yarda bane barinma a zamanin yanzu da muke ciki Dr karkiyi gangancin kaita gidan ku”….. Murmushi Dr Hajar tayi tace “karki damu k’awata insha Allah babu abinda zai faru sai alkairi”….

“Tow Allah yasa ‘amman Hajor naga kamar baki daddara da abunda ya faru dake shekara 5 da suka wuce ba, shima kuma yarda ce tasa kika fad’a cikin halin da kika shiga , Dr Hajar taji zafin furucin Khadee cikin zafin nama tace “Khadee ya isa haka abunda ya faru dani kaddara ce kin gane yanzu kuma taimako zanyi kuma baki isa kisa na fasa ba” hmmm Hajar kenan nifa bawai nafad’i haka kodon na b’ata miki rai bane amman naga kind’auki abun dazafi kiyi hakuri dama nibance na isa ba na barki lfy “Khadee ta dauki jakarta, ta fice

      ****

Dr Aiman yanzu ya kake ganin za’ayi wannan abun tsakanina da kaine bana so kowa ya sani promise me bazaka fadawa kowa ba” hmmm Dr Samir kenan basai nama alkawari ba ‘amman yanda muke dakai kasan bazan taba fada ma wani sirrin kaba ,ya jikin naka hope yanzu kana samu lfy sosai kow? “Alhmdulh jiki da sauki yanzu kam saidai some times nakanji gefen kirjina namun wani irin zafi da k’una ” tow Dr Samir haryanzu baka dena tunane tunanen nakaba kenan kow? ” haba ae kasan ina son mum bana son abunda zai tab’a lafiyar ta kuma inajin maganar ta, tunda tamin magana wlh narage “, ae kaji karage fa kace Doctor ya kamata ace kadena ne yanzu kwata kwata cox yanzu abunda ka fad’an tunanin ne ya saka jin haka kuma kana shan sugar sosai kow? ” Yes ina shan suga “tow ka dena idan kana son lfyn ka sannan kuma kana shan nonon rak’umi da fitsarinshi kasha kamar na 40 days shima maganine sosai ” tab’e fuska Dr Samir yayi yace” fitsarin rakumifa kace da nonon sa? ” yes sufa har sunfi maganin da nike baka na hospital ” kai gsky bazan iya shaba ‘abokina “suna cikin magana, ne sukaji knocking da sauri ta shigo fuskarta ba walwala sosai ,

“A’a Dr Hajar mutuniyar kinanan abunki, kin manta da best friend d’inki “hmm Dr Samir kenan wai namanta dakai kaje ka duba chat d’inmu kaga nayi ma, magana ka share ni “lah sorry wlh bana chat yanzu aiki sunmin yawa Aminu kano ba sauk’i babu hutu ” ae kai kaso hakan tun yaushe nace ma kadawo nan muna buk’atar Doctor d’in brin kak’i “cewar Dr Hajar…..

“No bazan dawo ba nafi jin dad’in hospital d’inmu “tow ae kaji dad’i wai meye ma yake kawoka nane naga duk Friday sai kazo? ” murmushi yayi, yace “nothing gurin abokina nake zuwa ” tow ae yayi kyau doctor Aiman muna da meeting 4:30 “cewar Dr Hajar, “ok Allah ya kaimu d’azu kuma Dr Khadee tace wai sai gobe “Eh da munbari gobe tow dad yayi waya yace ayi kawai ” tow Allah ya kaimu “Ameen ” hartazo fita taji muryan Dr Samir yana magana “aminiya sai nazo office d’inki yanzu idan na gama zan zo ” tab’e baki tayi tace,

“Bana, neman ka “..

“Tow nidai sai nazo “…

“Tow ina jiranka “ta wuce ta, tafi

Dr Aiman ya bawa Dr Samir shawar wari sannan sukayi salama ya wuce office d’in Dr Hajar

Wurin k’arfe biyar da rabi na yamma Dr Samir ya gama abunda yake cikin Babban Asibinti Aminu kano ,fitowa yayi ya shiga motarshi yayi gida, wani k’aton gida ya shiga mention zubi da tsarin gidan yayi tsayawa fasaltashi bata lokacine ,sojojine kewaye a gidan daga get ya fita daga cikin motar yabar driver ya k’arasa fuskarshi babu wani walwala sosai ya shiga cikin wani dank’areren falo, wata jattijuwa ce zaune kan sofa fuskarta d’auke da glass tana karanta jarida gifenta kuma kayan fruit ne da drink masu sanyi daganinta bazata wuce shekara 59 ba, amman tsabar hutu ya ratsata wani ma yace yar shekara 40 ce…

Salamar Dr Samir ne ya k’aste mata karatun da takeyi da fara’a ta d’ago ta amsa…

“Doctor harka dawo how is work?”

“Fine gud afternoon ummi ya gida”

“Fine son gida lfy yanaganka haka wani iri kamar akwai abundake damunka ,kasha maganin ka?”

“Babu komai Ummi wlh kawai nagaji ne ,maganina kuma wlh yau mancewa nayi dasu agida ‘amman yanzu ,zanje nasha” Son kafa dena wasa da shan maganin ka ,kaifa yanzu ba yaro bane kuma kafi kowa sanin wace irin ciwo kedamun ka ‘amman saikayi ta wasa dashan magani ,kaje kaga Dr Aiman d’in ?”

“Eh d’azu naje ya dubani yakuma ce komai nomal” tow Alhmdul Allah ya k’ara maka lfy son Allah kuma ya baka mata ,tagari don ,nak’osa naga jikokina”…

Murmushi Dr Samir yayi ,yace”Ameen Ummi Barin shiga ciki nad’an watsa ruwa ,wai ina Salma ne ni ?” Salma na d’aki tana karatu exam zasu fara gobe ” ok Allah ya bada sa’a” nan ya tashi ya shiga d’akinshi

“Mamana bazan lamuntaba, bazai tab’a yuwuwa ki kawomin wata wanda bansan ko ita waceba, yanzu ba’a yarda ,damutane mutun ba’abin yarda bane gara idan temokon kike sonyi ki temaketa kurabu lfy , ko ,kinmata abundaya faru dake ? Kin manta cewa yardan da kikayi yasa hakan?” Dr Hajar dake zaune kanta ‘a k’asa tace mami wance lokacin k’addarace wannan kuma taimako zanyi Mami bana son kuna tunamin abundaya faru shekarun baya “

“tow nidai na fada miki ,karki yarda ki kawomin wata cikin gidana ban yarda ,da wannan ba” ranta ‘a 6ace tayi d’akinta tabar Hajar gurin, itama ,mik’ewa tayi Ranta ‘a b’ace ta fita daga falon tayi dakinta , tana tunanin mafita…..

Jawahir dake zaune kan bed tana wasa da kayan wasanta ,tayi saurin mik’ewa ta rungume ,mummyn ta tana dariya tace “welcome home mommy how is work? “

Murmushin k’arfin hali tayi “fine beby kinci abinci ?” Jawahir da dariya daga gani tana cikin farin ciki tace “yes mummy naci sosai ” gud “Dr hajar tafad’a tana shafa kan yar tata, Shiru Jawahir tayi tana kallon maman, nata tace “Mummy ina dady na ?”

Dr Hajar dake kok’arin cire rigan jikinta ,tayi saurin juyowa ta kalli Jawahir a razane ,nan danan idanunta suka juya suka ,koma jazuri jikinta yayi sanyi , azuciyarta ,tafurta ‘ranar da nake gudun faruwa yau gashi ya faru ni yanzu mezance wa Jawahir game da inda mahaifinta yake Akram! Inazan ganka? tab’ata da jawahir tayi shine ya dawo daita daga tunanin data lula….

“Mummy ,yanaga idonki yayi ja bakida lfy ne?” Murmushin k’arfin hali tayi tace”Eh bebyna kaina ke ciwo kibari’ idan ,nasamu time zan kaiki gurin dadyn ki” tsale Jawahir tayi kan gadon tana murna zataje taga dadyn ta , Dr Hajar dake ,kallon Jawahir taji wani tausayinta ya kamata a zuciyarta ,tace dakinsan waye ubanki da kinyi regrating kasancewa cikin family dinshi koda yake balefin shi bane lefinane, hawayen daya zubo ta gefen idonta tayi saurin gogewa ba tare da jawahir tagani ba

Tow fa babbar magana waye Akram kuma?

Shin kun yarda Dr takawo, wannan matar cikin family d’inta? Meyi ra’ayunku game da hakan?

BY DIJA_WAZIRI🀞
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Ana sanin dad’in haduwane idan an rabu ,godewa ni’imomin Allah wanda ka sani da wanda baka saniba

zauna da jama’a lfy domain watarana sune zasuyi rakiyarka izuwa maqabarta

kayi tunani mai kyau ka dogara ga ‘Allah duk da kuncin rayuwa da kake cikin

Ya ubangiji kayi mana tsawon rai mai amfani da, daukaka marar yankewa da lafiya mai dorewa ‘Ameen

Chapter 3

Mik’ewa Jawahir tayi tana dariya ta fita daga d’akin, ita kuwa Dr Hajar dama kamar jira take Jawahir tafice, batasan sanda ta 6arde da wani kuka me tsuma zuciya ba, wanda kowa yaga fiskanta yasan abubuwa sun mata yawa magana ta farayi a zuciya wanda batasan yafito filiba “yazanyi da rayuwata ni shikena haka zan dawama cikin bak’in ciki Akram kacuceni bazan ta6a yafe makaba ka yaudareni kaci amanata ka wargazamin duk wani farin cikina ka rabani…..

Jin Muryan Mami ne yasa ta kasa k’arasa furta abunda take da niyan furtawa” Haba Mamana kukan me kuma kikeyi? bafa nason ganinki cikin damuwa,kodon nayi miki fad’a ne?”

Girgiza kanta tayi alamar A’a “tow meya sameki?” kallon mamin tayi cikin kuka tace Jawahir ne tace tanaso tasan waye Babanta” saida jikin Mami yayi sanyi da taji furucin Dr Hajar. “Sai kika ce mata me?”cikin kuka tace “cewa nayi zan kaita”…

Kallon ta Mami tayi cikin tausayawa tace “abunda nake gude kenan tun baya danake ta binki ,kiyi aure saboda irin wannan ranar, mamana manema nawa sukazo gurinki amman kikayi k’irmisi kice ke ba’aure a ranki? ,da kinyi aure da wlh duk haka baze faru ba dama na gaya miki akwai wannan ranar kuma gashi tazo, yanzu ae , kinwa kanki fad’a kiyi aure Akram de bazaki tab’a ganin shiba don shekara biyar kenan mahaifinki na ,nemanshi amman anrasashi”….

Itadai Dr Hajar batace komaiba har Mami tagama ,mata nasiha ta fita tabar d’akin, ita kuwa wani sabon kukan ta dasa tasan cewa Mami tayi gsky…

Dole tayi aure dole tajanye kudurinta!! kodon saboda Jawahir ta samu rayuwa me kyau , tow tayaya zata kuma yarda ,da wani d’anamiji a rayuwanta ? Akram yariga daya 6ata kowani d’anamiji a gurinta gani take duk maza haka suke ,tow yanzu miye abunyi gashi bataso Jawahir tagirma tasan kow ita wace…hakadai tayi ta tunanin mafita da taga babu mafita dole ta kira Khadee don ita kad’ai ce zata iya taimakon ta kuma gashi sunyi fad’a yaya zatayi? Da wannan tunanin tashiga wanka…

       *****

Kwance yake kan lallausar royal ded dinshi wanda yasha kwaliya idonshi a rufe ,fuskarta kawai yake hangowa yana tunanin yaya za’ayi ya malaketa , wayanshi ya zaro daga k’asan fillow yayi dailing number din Khadee bugu d’aya ta daga…

“Hello my dota ya kike?”

“Lfy qlau my father ya aiki? “

“Alhmdulh yasu mama da sauran su ina mutuniya ta? “

“Duk suna lfy tana gidan su “

“Tow masha Allah yanzu ya ake ciki kin mata magane? “

“Np bamuyiba tukun mutuniyar takace yar bori sai anbita a hankali so idan ,nasamu time inaso naje gidan sune sai muyi magana “

“Ok tow thank you so much ni gata zan tafi turkey duk yanda kukayi kin fad’an”…

“Ok Allah ya kiyaye “

“Ameen”…

Nan sukayi salama ya kashe wayan yana murmushi duk wanda yaga fice dinshi yasan yana cikin farin ciki….

WANENE CAPTAIN JUNAID?

Captain Junaid haifafen dan garin kano ne su biyar Mahaifinsu ya Haifa shine Babba dagashi sai Atika sai Musa kalamula, sai shabina, sai mina autarsu.

Atiki tana aure a kano musa kuma yana cairo yana karatu (computer science) Shabina kuma tana turkishi (jss 1) Mina kuma batakai zuwa school ba .

Mahaifin Captain ya dauki son duniya ya d’aurawa yaran nashi ,kuma hakan be hanashi basu tarbiyya me kyau ba…

Captain Junaid zaikai shekara 37 Amman haryanzu beyi aure ba babu yanda mahaifinshi beyi dashi yayi aureba yace shi haryanzu be samu wanda yake so ba

Wannan kenankenan

Yana gama waya da Khadee yayi dailing number din best friend nashi Dr Samir, (Dr Samir Abokin shine tun suna wasan k’asa kuma abokaine da Mahaifin Captin Junad da Mahaifin Dr Samin kafun Allah yayiwa Mahaifin Dr Samir rasuwa)….

Bugu d’aya ya d’aga daga bangaren Samirne yayi magana.

“Hello friend ka manta dani kow”…

“Haba dai wlh tunda nazo ban zauna bane ya gida da kowa da kowa ya jikinka hope kana samun sauki sosai?”…

“Hmmm jiki da Sauk’i Friead amman akwai magana kuma secret ne kasan bana b’oye maka damuwata “….

“Tow Allah ubangiji yasa ‘Alkairine nima wani labarine dani kuma bazan iya beyema ba nasamu mata”.

“Don Allah fa kai congrt gsky nama murna yar ina ce ? Hmmm yar kano ce amman fa tak’i saurarena bare na sanar da ita batuna hasalima sau d’aya na tab’a ganinta”

“Kai freiad wlh kai banzane harna fara hongo irin bidirin dazamuyi aiko baka samu mataba ,da sauran ka”…

“Hhhhh wlh kam da saurana nidai Allah yasa ta karb’eni kana gidane nazo?”….

“Ameen Eh ina gida kasan bani da isashen lfy tow yau jikin nawa babu dadi kuma banaso mum ta ,tada hankalinta…

“Gsky kam tow ganinan zuwa”…

“Ok saikazo ina jiranka “ya kashe wayar…

Wani pic naga ya d’auko daga cikin drow ya tsirawa hoton matar dake jiki kallo , yana kwala ,Allah ya miki rahama Jamila ,I love you so much Jamila nasan bazan samu mace kamar kiba kinmin komai a rayuwa , Jamila haryau kina cikin zuciyata aduk randa na tunaki nakayi kuka yanzune lokacin daya dace ku samu kulawata yanzune lokacin daya dace na saka miki da irin karamcin da kika min yanzune lokacin da yadace kiji dadin rayuwa ‘Amman Allah beyi ba Allah yaji kanki keda prince ina matuk’ar jin zafin rabuwa daku shine abunda yake furtawa….

TUNA BAYA (RAYUWAN DR SAMIR)

“Rabi niba me nisan kwana bane nasan mutuwa zanyi wannan ciwan k’afan bakisan yanda yasani a gaba, ba gashi bamuda komai ” haba Alhaji ka dena fad’an haka insha Allah zaka samu sauk’i ,karfa ka manta dukkan tsanani yana tare da sauki “Asalamu Alaikum” wa’alakum salam A’a samir harka dawo ina matar taka?” cewar Hajiya “wlh na barota gidan mamanta ‘anjima zata dawo , sannu Abba ya jikin ?” Jiki da sauk’i samir ” Tow Allah ya k’ara sauki ga kayan marmari na siyo maka “…

“A’a Samir hidimar ae tayi yawa kayi hidima da gida kuma kayi hidima ga d’awai niyar makaranta duk kai daya ‘Amman harda hidimar siyomin wani abun kullum ka fita saika rik’omin wani abu ” Tow Baba idan ban mukuba wazanwa ni duk abunda zan samu ku nake tunani da kuma ,matata ” hakane d’ana Allah ya maka albarka “Ameen Baba Allah ya baka lfy “Ameen”….

Samir a duniya bashi da wanda yake so sama da iyayenshi duk wani abunda yaga zesasu cikin farin ciki tow yana masu daidai gwargwado kuma baya son abunda zai ta6a lfyn jikinsu gashi yanajin maganar su..

Samir be shirya ‘aure da wuriba ‘amman iyayenshi suka buk’aci had’ashi da Jamila yar k’anwar mahaifin Samir , saboda baya son yi mu ,su musu yasa ya ‘amince da auren Jamila wanda ta zame masa tamkar jinin jikinshi takuma zama ‘alkairi a rayuwan shi….mahaifin samir talakane yana ‘aiki a company din saida taburma kuma ba wani babba bane duka duka Albashinsa naira dubu ishirinne duk wata dashi yake cida gidanshi dakuma biyawa Samir kudin makaranta, kwatsam wata rana aka kulla masa sharri , yayi sata kuma ‘Alhalin besan komai ba tow tundaga lokacin suka koreshi daga wajen aiki ya zama bashi da ‘aikinyi watarana abincin da zasucima gagaransu yakeyi…..

Suyan Asalin garin kano ne haifafun yan unguwar hausawa ‘amman suna zaune a gadon k’aya shekara biyar kenan mahaifin Samir yake tare da laruran ciwan k’afa wanda yayi sanadin dena tafiyarshi kullum ana cikin magani gidan da suke zaune gidan hayane ,Shekarun Samir 19 Aka masa aure lokacin yana level 3 a B.U.K yana karantar medicine fannin kwakwalwa….

“Zaune suke cikin d’aki shida matarshiJamila da bakinta dukya bushi idanunta sukayi ciki ciki ga dukkan alamu yinwa takeji “Jami wlh rashin kud’i beyiba aduniya mutun sai yana da kud’i akeyi dashi kinga yanda nakeshan wulak’anci a school kuwa “hmmm ae sai hakuri rayuwance haka me arziki dashi akeyi” Jami wlh ina shi’awar inga kinyi karatu kin zama gainic dani me arzikine da babu abinda zai hana kiyi karatu “murmushi tayi tace” nasani mijina yanzu dai kai ,kayi din ka gama insha Allah ,Allah ya d’aukaka karatunka kayi kud’i inde muna tare ae zanyi” b’ata fuska Samir yayi yace “banason jin kalmar in muna tare bana hanaki fad’aba isha Allah muna tare har k’arshen rayuwar mu” murmushi tayi kawai tace “Ameen “…

“Kai kinga karna makara inada lecture 10 to 11 kinga kuma har 9 tayi kuma ‘a k’afa zani gara na hanzarta karna makara ” har bakin k’ofar gida Jami ta raka Samir saidaya k’ule sannan ta shigo gida tana hawaye ,don tana mugun tausayawa mijin nata beci komaiba ya kama hanyar school kuma a k’afa ” Allah ka rufa mana ‘asiri ta furta azuciyarta….

D’akin Baba ta shiga ta masa yajiki sannan ta fito ,tayi d’akin hajiya ta gaidata sannan taje ta gyara dakinsu tafito tsak’ar gida ta share tayi wanki -wanke, wani tsohon dawa ta dauko wanda kwari harsun fara lalatashi baze wuce kwano d’aya ba ta wankeshi tsaf tasa kayan kamshi ta bayar aka kaimata nik’a ,ta taceshi tayi gasaranta me kyau ta , karare tasa yara suka samo mata a waje tahad’a wuta ta d’aura ruwan zafi bata wani jimaba ta dama kunu me kyau ,

Mayafinta ta d’auka taje shagon kusa da gidan nasu tace ya bata suga na hamsin bashi kafun Samir ya dawo , Sule da yake yana ganin mutuncin Mahaifin samir yasa ya d’auka ya basu.

Dawowa tayi ta zuba sugan Tasawa su Malam nasu takai Hajiya kawai tagani d’akin “A’a Jamila Samir ya dawone?” A’a bedawoba Hajiya ae be jima da tafiya ba ” ok ae nazaci ya dawo ya kawo abun karin kumallo ne tow ina kika samo gasara?” Murmushi Jamila tayi tace” wlh randa naje gidan Mamane naga wani gida sunfito da dawa zasu zubar wai ya lalace shine nace suban inaso ” Allah sarki rayuwafa kenan abunda wasu ke ganin bashi da ‘amfani a gurinsu wasu kuma shi suke gani me amfani Allah ya miki Albarka jamila yajik’an mahaifinki” Ameen Hajiya”….

Shiko samir tunda ya shiga makaranta babu wanda yake tunani sai iyayenshi da matarsa ya barsu babu abinci , karfe 4 suka gama lecturs Amman be koma gidaba har karfe shida na yanma ya tafi neman kud’i amman be samuba sai naira d’ari da yayi dako akasuwa , haka ya koma gida a tsakar gida ya iskesu suna hira nan ya tsuguna ya gaida iyayenshi sannan ya k’arasa ciki don cire kayan jikinshi yayi wanka biyoshi Jamila tayi tana masa sanuda zuwa ,haske fitilar dake dakin ma bakoina take haskawaba tsabar batter ya mutu…

“Sannun da zuwa Dr ya karatu” dama Dr take kiranshi….

“Alhmdul Jami wlh yau narasa yanda zanyi duk aikin danasan zanyi na samu kudi babu kinga d’ari na tsira da ita ,gashi tun safe bakuci komaiba”

murmushi tayi tace “karka damu Mijina da safe na dama musu kunu sunsha da rana kuma sauran tsakin dawan daya rage na tuk’a mana tuwo sai na ranto kayan mida da manja da magi gurin sule na sabain sugan hamsin nayi mana miyar kuka yanzu da dare kuma dama na cika palas da kunu saina iba musu ga naka cenma tare da tuwan ka, wani ajiyar zuciya ya sake yana me k’ara jin son Jamila cikin zuciyar shi…..

Jamila bawata babba bace shekarunta 14 amman idan tana wani abun hartafi wani babban “Jamila Allah ya miki Albarka Allah ya baki abunda kike so ” murmushi tayi tace “Ameen Dr

Bayan kwana biyu

Yau Jamila ta tashi taji jikinta duk babu dad’i ga matsanacin ciwan ciki dake damunta da ciwan kai wanda takai sati tanayi da yawan zafin jiki fitsarinta ma ya cenza kala , Hankalin Samir a tashe ya dauketa sai asibitin murtala kafun suga likita duk Jamila tagama galabaita ,tafita hayyacinta ,sun shiga sunga likita yayi mata ,tambayoyi ta kuma amsa bayan ya gamane yace suje suyi gojin ciwan hanta (Hepatitis)..

Jikin Samir duk yayi sanyi sukaje sukayi suka kawo sult , kallon Samir Doctor yayi cikin tausayawa yace ” matarka tana dauke da ciwan hanta kuma yaci jikinta sannan tanada juna biyu na wata biyu”…

Lokacin da Samir yaji furucin doctor ji yayi kamar an sara masa guduma akai ita kuwa Jamila hawaye ta soma fitarwa ita tasan bazatayi rayuwa da Samar kamar yanda ta tsarama kanta ba ,cigaba da bayanin doctoe yayi” sannan zaka iya diba idan har baka dena kusantar taba sannan shi wannan cuta ya kasu kashi biyar Hepatitis A Hepatitis B Hepatitis C Hepatitis D Hepatitis E cikinsu akwai masu b’acewa da kansu Bayan sun kama, mutun, wasunsu kuma sai anyi maganai .haka Nan wasunsu basa tsananta wasunsu kuma suna tsananta . Saidai bincike yayi nuni da cewa, Hepatitis A ,Hepatitis B da kuma Hepatitis C Sune sukafi wanzuwa tsakanin mutane .kowacce cikinsu Alamominta ,Abunda yake Haddasata, yanda Ake maganceta,Hanyoyin kamuwa da ita yanda ake kare Afkuwanta ya ban-banta da kowacce . sannan kuma kowanne cikinsu yana da alamomin shi Alamomin Hepatitis A :- mutun zainajin ciwon ciki (Abdominal pain) ,fiver (zafin jiki) , vomiting , tashin zuciya, kasala (fatigue) ,choluria, jaundice symptoms , da sauran su kwata-kwata bata tsananta bayan mutun ya kamu da ita .

Hepatitis B kuma yawan fever, kasala, jaundice symptoms, gudawa, da kuma wasu Alamomi masu kama da cutar flu wani Lokacinma bata nuna alama, tana iya tsananta dakaso goma cikin dari na mutanen da suka kamu da ita Hepatitis C iri dayane da Hepatitis B. Sai dai wannan tana iya tsananta da kaso 75-80 cikin dari na mutanen da suka kamu da ita.
Tsahon kwanaki daga lokacin shirgar kwayar cutar cikin jikin mutun izuwa lokacin bayyanar Alamominta (incubation period) Hepatitis A sati biyu zuwa bakwai .Hepatitis B 6-23 weeks Hepatitis C 2-25 weeks , Abubuwan da suke hadasa ciwan Hepatitis A ‘abunda yake haddasata shine wani kwayar cuta da ido baya iya gani mai suna Hepatitis A virus (HAV) Hepatitis B (HVD) ma’ana Hepatitis B Virus ,Hepatitis C (HCV) sannan yawan shan giya ,guba ,(toxic substances) ,matsalar garkuwar jiki (Autoimmune diseases), yin Amfani da kwayoyin magani ba ,bisa k’ainda ba gado (genetic cause), da sauransu na iya haddasa ciwon hanta.

Hanyoyin kamuwa da cutar ,Hepatitis A gurb’atuwar abinci na ruwan sha Wanda ya gaurayu da kashin wani mai d’auke da cutar ,wanda kwaruna (flies) ke yad’awa ,da kuma had’a jiki (body contact) da sauransu , Hepatitis B idan aka sanyawa mutun jinin mai d’auke da ita (transfusion of infected blood ) , yin amfani da ‘Allura ko razor na masu d’auke a cutar (use of infected sharp objects), daga uwa zuwa d’anta ,lokacin saduwa da mai d’auke da cutar (sexual contact) ,da sauransu. Hepatitis C sanyawa mutun jinin mai d’auke da cutar ,use of infected sharp objects ,sharing of parsonal hygiene implements, e.t.c nan dai docto ya fada musu abubuwan daya kamata tadingaci wanda ze kara mata lfy tanacin kayan fruit sosai sannan kuma tanashan rake sosai tana shan zuma shan abarba yakuma rubuta musu magani….

Salim bai k’ara shiga tashin hankali ba saida ya je gurin siyan magani yaji suna kira masa wurin dubu goma wanda ko naira biyar ta kanshi bashi dashi a lokacin ,kallon Jamila yayi cikin tausayawa kamar zeyi kuka yace “Jami kinji kudin maganinki kow?” Girgiza masa kai tayi tana hawaye tace”karka tada hankalinka Doctor sauk’i na Allah ne idan Allah ya rubuta zan warke ko babu magani zan warke ” Hmm Jami amman ae Allah yace tashi in taimakeka yanzu ke kiwuce gida ni zanje neman kud’i ko wani irin aikine zanyi don naga nasamu kudin da zan siya miki magani”….

Koda Jamila ta koma gida ta sanar dasu Hajiya Abunda likita yace ba k’aramin tausaya mata sukayi ba, Samir kam daya fita aikin dakwan gawayi ya samu akace a kwashe buhu dari biyu yakai kuma gurin da zaikai danisa , idan ya gama za’a bashi dubu uku haka ya dinga jida yana kaiwa tsabar gajiya saida ya fasa buhu biyar a rashin sani mutumin ya dinga masa bala’i ya zaro dubu biyu ya watsa masa dubu dayan yace a bakacin asaran dayayi masa, salim Babu yanda ya iya haka ya kwashi dubu biyun ya tafi kamar zeyi kuka gayunwa da k’ishin ruwa dake damunshi, koda yabar gurin wani aikin yaje ya nema yayi saida ya tabatar ya had’a kudin maganin tukun ya je yasiya ya koma gida….

Rayuwa dai haka tayi ta ,tafiya musu babu dad’i babu walwala ,Jamila kuwa sai jinya takeyi gashi babu wani abu da takeci wanda ze kareta gaciki ya girma duk kayan d’akinta ,tasaida su don suci abinci yanzu bata da komai a d’akinta ko katifa babu….

Salim ko yana final year a b.u.k abubuwa duk sun tab’ar bare mai……

  BAYAN WATA TARA 

Jamila ce kwance cikin jini sai birgima takeyi tana ihu ,jin ihun tane yasa Hajiya saurin fitowa kwance ta sameta sai nishi take kan d’a ya fara fitowa nan dai hajiya ta taimaka mata har Allah ya sauketa lfy ta haifo san talelen danta fari tas me kama da ubanshi , saidai kuma wani babban matsalan shine Jamila tasuma ta dena motsi jikin hajiya a sanyaye ta gyarata ,takira Samir aka dauketa sai asibiti….

Salim ba k’aramin tashin hankali ya shigaba ,sintiri ya dingayi kofar dakin da aka kwantar da ita , bayan wasu yan mintuna wani doctor ya fito daga cikin dakin fuskarshi ba fara’a, da sauri samir yace “doctor ina fatan lfy” ,kallon shi yayi yace “ka biyoni office “

Suna shiga doctor ya kalli samir da masifa yace “matarka tana cikin matsala kunbar cuta yaci jikinta baku kula da ita yanda ya kamata , kuma gsky cutarnan taci jikinta da yawa hantarta ya dagargaje idan ba sa’a ba ma sai anyi mata tiyata ancenza hantar don zata iya Rasa santa a kowani lokaci, zamuyi admiting dinku harsai Allah yasa ta samu sauki , nan yaje aka fad’a masa kudin gado da sauran abunda zai siya da yake Aminu kano sukaje …..

Dak’er samir ya samu ya biya kudin komai Hajiyace tazo tana zaune da ita da jaririn da ta haifa , Ranar suna yazo da yake bazasuyi bikin sunaba yaro yaci sunanshi Muh’d sunan mahaifin Samir sai kace da yaron prices shima tunda aka haifeshi bashi da koshin lfy kuma bayashan nono sai madara sabida uwar bata da ruwan nono, watan Jamila d’aya a hospital dukta kwanjame ta rame kamar ba itaba tayi wani fari fayau kamar bata da jini Salim ne ya shigo d’akin ya ganta kwance ita kadai sai hawaye takeyi tunda samir yayi mata kallo d’a yayi saurin dauke kanshi shima yana hawaye don tarame sosai duk me tausayi da imani ya ganta sai yayi mata kuka….

Gefen gadon ta ya samu ya zauna ya kamo hannun ta da suka mik’e sukayi fari alamun rashin isha shen jini” Jami meya saki kuka?” Mikewa tayi tad’an jingina da fillon da take kwance hawayen be dena zubaba tace”kukan rabuwa daku nake Dr nasan daga yau bazan kuma ganin kuba nasan daga yau zanyi bankwana da duniya nasan……

Saurin rufe mata baki yayi hawayen da yake ta danne wane suka zubo “ke dena fad’in haka Jami insha Allah zaki warke Allah yana tare dake ” murmushin k’arfin hali tayi tace Dr kenan bakasan abunda nakeji ba da kasan me nakeji da bakace hakaba, Allah ya baka mata tagari wacce tafini Allah kuma ya had’amu a Aljanna Almdullh Allah nagode maka da ka bani danda zemin addu’a bayan raina , Samir prince amane agurin ka Allah ya raya mana shi samir sai wata rana sai munhadu a ‘Aljanna “….

Samir na hawaye yace haba Jami pls ki dena fad’in haka insha Allah zaki warke” bud’e baki tayi zatayi magana taji hakorinta ya tsarke dak’er ta fara kalmar shahada tana ina lilahi wa inna ilaihi raju’un ,idanunta suka fara juyawa bakinta ya fara fitar da jini , da sauri Samir ya fice da gudu ya kira doctor….

Suna shiga ya sameta kwance idanunta suna kallon sama fuskarta dauke da murmushi , nufar gurin doctor yayi da sauri ya girgizata yaji bata motsi ya duba idanunta yaga basa motsi rufe mata ido yayi yaja zanin gadon ya rufe mata kanta…..

Samir da yayi tsuru yana kallon doctor ya kasa komai ,dafashi doctor yayi yace “kullu nafsin zaikatul maut Allah yayi mata rahama Allah ya baku hakurin rashi” Samir kasa gasgata abunda doctor ya fad’a yayi sai bayan fitar doctor ya nufi gawan Jamila yana hawaye Addu’a yayi mata ya kira Hajiya don sanar da ita abunda ke faruwa ,Abunda yaji hajiya tace ba k’aramin girgizashi yayi ba innalilahi wa inna ilaihi raju’un shine abunda ya iya furtawa kafun ya fad’i k’asa ‘a sume….

Farkawan da zeyi Hajiya ya gani kusa da gadonshi tana rik’e da hannun shi fuskarta yayi luhu luhu alamun taci kuka harta gode Allah ,da sauri ya mik’e kamar zarare fuskarshi babu Alamun kuka ya fik’eta yana tmbyn d lfy meya sameshi kamar wani zarare dafashi tayi tace “Samir ka kwantar da hankalinka dama duk mairai mamacine Alhaji da Jamila abubu abinda suke buk’ata ‘a gurinmu sai Addu’a da fatan dacewa , duk Alhaji kam ya tafi ta fashe da kuka don mutuwan Jamila da Baba ,ba k’aramin girgizasu yayi ba kasa kuka samir yayi donshi abubuwan sun masa yawa ga mutuwar mata ga mutuwan mahaifi ga danshi ba lfy gashi ze fara exam din gama school shi yanzu ina zesa kanshi?….

Tatara kayansu ,sukayi aka d’auki Jamila suka taxi gida, suna zuwa aka yi musu wanka kowa ‘aka kaishi makwancin shi mu tanan unguwa babu wanda beji mutuwan Alhaji ba don mutune me iya zama da jama’a kuma mutunne me ilimin bok’o dana arabic haka zalika matarshi Hajiya itama yar bokoce kawai dai halin rayuwa ne yasa rayuwansu ta kasance haka……

Bayan rasuwan Firce tun lokacin da Allah yayiwa Jamila rasuwa Princes ya cigaba da rashin lfy Anyi magani anyi magani amman kamar ba’ayi da yake shi sikla ne haka dai har Allah ya d’auki kayan shi, tow tundaga lokacin Samir ya dena tsoran mutuwa don shi a yandu mutuwar mahaifiyar shice kawai ze kuma girgiza shi….

BAYAN SHEKARA SHIDA

Samir yayi kud’i sosai ya zama cikakken doctor na brin ya gina gidanshi me kyau a nasarawa G.R.A yana aiki a ‘asibitin Aminu Kano….

Fad’uwa samir yayi yana tari bakinshi yana fitar da wasu gudan jini idanunsa ,suka juye suka ,koma jawur kamar gauta , Captin Junai de ya banko ,k’ofar dama sun saba haka ‘a tsakanin su basa wa junansu knocking “innalilahi wa inna ilaihi raji’un meya sameke Dr? ” hannu ya fara nuna masa yana tari alamar karya k’araso, shiko sai k’arasowa yake………….

DIJA_WAZIRI CE🀞
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

   *(P. M. L)*

Duk wanda kaga ya zama wani a duniya tow yayi hakuri ne kuma yacire girman kai, lalle tabbas ni, nayarda cewa hakuri yana d’aga dara mutin, idan har kazamto mai Hakuri da dukkan abunda zai sameka ‘arayuwa kuma ka mik’awa Allah saikaga cenji me cike da ‘Alkairi

ya Allah ka bamu juriya da hakuri akan duk abinda zamu fuskanta narayu Ameen

Chapter 4

Kama hannunsa yayi ,ya taimaka masa ya koma kan gadon ya kwanta yana wani ,irin ,nufashi har a lokacin jini bedena fita tabakinshi da hancin saba tissue Carpin Junaid ya zaro ya taimaka masa ya goge masa jinin dake zuba sannan ya bud’e fridge d’in dake d’akin ya dauko faro water ya zuba ‘a cupe ya mik’a masa, girgiza kai Dr yayi ,yana tari alamar bazai ,iya shaba .

Cikin tausayawa Carpin ke ,kallon shi kamar zaiyi kuka ya ajje ruwan kan bedside drower, ya sauka k’asa, a falo ya samu Ummi tana kallo hankalinta kwance kowa ya ganta yasan tana cikin farin ciki da walwala bata da damuwa fuskarta d’auke da fara’a ta dawo da hankalinta kan carptin “lfy dai kow Junai ina Samir d’in yake? ” Captin Junai fuskarshi ba yabo ba falasa kowa ya ganshi yasan hankalinshi baya kwance”Ummi wlh shigata naga Samir cikin wani hali…gsky ciwan shine ya tashi amman dai ,dasauki….

Kafun ya k’arasa furta mezai ce Mami hartakai bakin stairs tana kalmar shahada , shima bin bayanta yayi tana shiga ta zauna bakin gado kusa da inda yake kwance tana hawaye “Dr don Allah kamir rai karka mutu ka barni bani da kowa saika ,kaine farin cikina my Son idan kamutu inazansa kaina yazanyi darayuwa ta ?” tana maganar tana sheshek’ar kuka ta damk’e hannun shi murmushin k’arfin hali Dr yayi ,yace Ummi ki kwantar da hankalinki insha Allah ina tare dake har abada bazan barkiba “maganar dayayi ne yata d’agota tana kallon shi hakanne ma yasa tad’anji sanyi azuciyar ta.

Mik’awa Captin Junai waya ,yayi yace ya kira masa Dr Aiman, da rawan jiki Captin ya karb’a yayi dailing bugu d’aya, yad’aga daga b’angaren shine yayi magana “hello Abokina ya ‘akayi? ” bashi bane Abokin shine don Allah Doctor idan kana free kayi sauri kazo wlh ciwan shine ya tashi pls, “what!! ciwanshi fakace tow ganinan zuwa” yayi sauri ya kashe wayan.

Basufi minti 10 da wayaba saiga shinan yazo shigowar sane yasa Ummi tashi tabasu guri, “Abokina meya sameka bayan nasan munrabu dakai d’azu lfy?” Murmushi yayi idonshi a lumshe yace “Abubu komai Dr yau d’inne d’azu dana tuna Jamila kawai naji zuciyata namin kuna da zafi ” OMG Dr haryau ka, kasa mance Jamila cikin zuciyar ka shekara nawa yanzu? haba Dr Samir kana so ka, kashe kanka ne? ” Allah sarki Dr Aiman ae inajin bazan ta6a iya cire son dake tsakanina da Jami ba kuma bazan ta6a iya dena tunanin taba saidai zan rage “tow Allah yabaka lfy nidai taimakon dazan iya maka yanzu shine kadaure karinga shan maganinka sannan kuma kabi shawar -warin dana fad’a maka sai kuma nonon rak’umin da fitsarinshi dana fad’a maka, koda yake zan fad’ima ,Ummi nasan idan anbi ta, taka basha zakayi ba ,yanzu ga wannan maganin kasha kullum d’aya zakana sha ze rage maka zafin da kake yawanji “ya mik’a masa wani magani cikin leda sannan sukayi salama ya tafi…

Ruwa Captin ya mik’a masa yasha maganin sannan ya zauna kusa dashi yana k’ara masa, sannu “Friend kafayi hankali wlh gara ka daure ka cire tunanin Jami a ranka wandafa ya mutu yariga ya mutu bazai tab’a dawowa ba wlh ciwannan zai iya kaika lahira akan tunane- tunane dakasa wa ranka, yanzu kodon Ummi aika dena, kana ganifa yanda take tada hankalinta idan akace ciwanka ya tashi duk tabi ta gigice, kow sow kake hawan jini ya kamata? “.

“Hmmm friend dama nifa tunce nasan bame nisan kwana bane friend inada sirrin da babu wanda yasan dashi a duk fad’in duniyar nan sai Dr Aiman sai kuma mahalillci na su kad’ai suka sani saikuma kaida zan gayawa yanzu ina son abunda zan gayama yanzu yazama sirri tsakanina dakai duk rintsi duk wuya karnaji a wani guri “mik’ewa yayi yaje dede kunen sa ,sanan yafad’a masa .Captin tsabar rikicewa saida idanunsa ,suka juya zuwa ja besan sanda ya furta innalilahi wa inna ilaihi raji’un ba “yanzu Friend kana d’auke da wannan mugun ciwan shine kake b’oyewa why?” Junaid kafi kowa sanin cewa Ummi babu wanda takeso sama dani Ummi zata iya rasa, ranta sabodani haka zalika nima babu wanda nafi so sama da ita zan iya sadaukar da komai nawa saboda ita zan iya k’ask’antar da kaina saboda ita zan iya yin duk wani abunda nasan zesata farin ciki inde be sab’a addini ba kana ganin tasan halin da ‘ake ciki bazata iya rasa ranta ba ? Koda ace bata rasa ranta ba kana ganin wani abu bazai faru da ita ba ?”….

“Lalle yau na sake tabatarwa kana balain k’aunar mahaifiyar ka Samir ,Amman dai ,ina fatan kana shan magani?” Yes akwai doctor d’in da nake gani hospital din danake aiki sow ya d’aurani akan magani” Tow Allah ubangiji ya yaye maka yasa kaffara ce ,Amman friend ga shawara mana ni aganina da kayi aure kaga ciwanka yakan tashi any tima kuma babu kowa kusa dakai kaga kuwa idan kayi aure matarka ,kullum tana tare dakai ita zatana sanin halinda kake ciki kuma zatana d’ebema kewa “…

“Nima nayi wannan tunani ,ni inaso nayi aurene ma saboda Ummi tanaso taga jikokin ta kuma kaga tajima tanamin magana ,tow haryanzu dai ban samu wacce tamin bane amman ahankali zan samu” tow Allah ya mana za6i mafi Alkairi nima dad yasani gaba ‘nakawo mata inbahaka zeban da kansa yanamin gori wai duk kunyi aure kun barni ,nazama gauro”..

Dariya Dr Samir yasa yace”aishi aure rabone inde tima dinshi beyiba tofa baza’ayi shiba ,nifa bantab’a tunanin zanyi aure a age d’ina lokacin danayi ba ” hakane kuma aure ba’ayi masa gaggawa kaga ni wlh nasamu yarinyar nidai ina ‘addu’a Allah yasa ta k’arbeni “Ameen friend wai ya sunan ta?” Dr ya tambaya yana gyara kwanciyar shi “sunanta Hajjo” ok tow Allah ya daidai taku “Ameen ni barin tafi zan dawo gobe insha Allah jibi zan wuce “tow thank you freand kafun katafi nima zan shigo inaso na gaida dad” nan sukayi salama ya tafi

   WASHE GARI

“Morning dad nd Mami? “Morning dear kin tashi lfy ? ” suka had’a baki suka fad’a ,”lfy qlau “tow masha Allah ina Jawahir ?” Cewar Mami, “tana sama ‘Alawuya na shirya ta ni na makara patient na jirana” ok amman dai saikinci abinci kafun kifice kow?” Mami ta ,tambaya tana shirin zuba mata chips da egg “no Mami karki damu idan najecen zanci ” ok tow saikin dawo ki tabata kinci kuma” tow Mami insha Allah zanci bye” hartazo k’ofar fita daga falon taji muryan Dad,” Mamana idan kin dawo inason magana dake ,Allah ya tsare take care of your self” ok Dad Allah ya kaimu by 2:30 zanbar Hospital so zanbiya gidan grany ” tow kin kyauta saikin dawo “cewar Dad ,

Tana fita gurin motarta, ta nufa idi tagani yana goge motar yana ganinta ya durk’usa har k’asa yana gaisuwa “barka da safita Doctor antashi lfy? “Fuskarta d’auke da fara’a ta ‘amsa da “lfy qlau idi ka gama ne? ” Eh nagama Doctor barin bud’e miki yau mamanmu bazata makaranta bane ,naga baku fito tare ba? ” zataje yanzu zatafito idan kakaita idan antashi gidan Hajiya zaka kaita,” tana maganar tana kutsa kayai cikin motarta, “tam Doctor insha Allah yanda kikace haka za’ayi saikin dawo Allah ya tsare “Ameen ” da gudu tafigi motarta, tabar harabar k’ofar gidan cikin mintina kad’an ta isa harabar asibitin, wurin da take parking ta nufa direct tayi parkin sannan tafito dauke da hand bag d’inta da kuma court d’inta a dayan hannun me d’auke da sunan hospital d’in tafiya take furkarta d’auke da murmushi sai d’agawa yan tsiranin mutanen dake yawo cikin haraban asibitin hannu takeyi tana musu murmushin ta me k’ara fito da kenta ,office d’inta, tashiga direct fale tagani guda 15 jirke kan table d’inta zama tayi tana maida nunfashi ta saka court d’inta , ta kira wata nurse ta zauna don tana taimaka mata da wani abun fara duba marasa lfy tayi sai da ta duba mutun 7 sannan taci Abinci tacigaba da dubawa saida ta dubasu duka wurin 3:45 tana shirin tafiya gida taji knowking da sauri tace “waye” jin munyar Attendant yasa tace “come in ” shigowa yayi yace ma’am you have a visitor, yace wai yana son ganin ki sunanshi Dr Samir “6ata fuska tayi tace kace ya shigo ” yana fita bejima ba Dr Samir ya shigo fuskarshi d’auke da murmushi sanye yake cikin black suit sun balain yi mishi kyau “afternoon K’awa ya aiki? ” Alhmdulh ya naka aikin ” ta ‘amsa masa tana maida wasu file ma’ajin su “lfy dama wata magana, nazo maki da ita idan kina da time saina fad’a miki idan kuma kinada abunyi mayi waya ” cewar Dr Samir duba agogon dake d’aure a tsintsiyar hannunta tayi taga hud’u saura minti goma, fad’ad’a murmushin ta, tayi tace ina jinka Dr Samir ae bazan iya k’in sauraran kaba har ka tako kazo “yawwa k’awa na gode da lokacin ki akwai wani da yake kawo matarshi hospital d’inmu ne so tanda problem da yawa kuma duk matsalar daya shafi matane so shikuma baya so namiji na tab’a masa mata shine yace idan nasan wata Doctor mace mana don Allah nahad’a su wlh mutumin yanada kirkine babu abinda zai iya nema ide zan iya ban masa ba yanzu na bashi number d’inki zasu dinga zuwa nan ” eyyah ae babu komai Dr godiya muke ” nan sukayi tahira suna fad’ace fad’acen su don duk randa suka had’u sai sunyi fad’a, tare suka fita kowa yayi wurin motarsa hadire ne sosai a garin keta had’uwa, tafiya take cikin k’warewa da iya tukin cikin nutsuwa take taka motar gari kuwa sai k’ara duhu yakeyi hadiri sai had’owa yake dede nasarawa G. R. A motarta ya fara yin abu kamar ze tsaya taji tafara yawo kan titi mutane sai hon suke dannan mata gashi tayi tsakiyan titi sosai hasbunalah shine abunda take ta furtawa cikin zuciyar ta…

Muje zuwa

BY DIJA_WAZIRI🀞
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJAR
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

chapter 5

Dak’er ta samu tayi parking gefen hanya tafito gashi anfara yayyafi yan tsirarin mutanen bakin hanya duk sun watse saboda ruwan ya soma k’arfi, motoci sai wucewa suke abunsu babu wanda ya tsaya tafi minti goma tsaye a bakin motar batare data shiga ba ruwan dayayi k’arfi sai dukanta yake ,kayan jikinta duk sun jik’e jak’af babu abinda take sai faman tsaki gashi tana so ta koma hospital 8 na dare , tana cikin tunanin hakan ne taji anyi mata hon wata black mota ce k’iran ferari tayi parking kusa da motarta, wani wawan tsaki ta kuma saki tare da zumar komawa cikin motar ta, don yanda take jin haushi bata, tunanin zata iya kula kowa, wani guy ne ya fito cikin motar sanye yake cikin dakaken shedda gezna ruwan toka ,k’arasawa yayi har inda take ya kwankwasa mata glass d’in mota da har bazata bud’eba wata zuciyar tace ki bud’e kika sani kozai taimaka miki motar ta tashi , saukewa tayi fuskarta ‘a d’aure ta d’ago ta kalleshi, tunani ta farayi aina tasan wannan fuskar don ta ta6a karo da mutun me irin wannan fuskar amman ta manta “Hajjo ya ‘akayi kika tsaya ruwa sai dukanki yake baki tunani ya saki mura” tsintar muryanshi yana magana ne yasa tayi saurin dawowa daga tunanin data shiga ‘a firgice ta kuma d’agowa ta kalleshi da manya manya idanunta masu haske da ‘Alamun tmby a tare da ita..

Fad’ada murmushin shi yayi yace nasan akwai ayar tambaya a kallon nan naki yanzu barin duba miki motar naga matsalar shi idan yaso zan maki bayani daga baya ” itadai Dr Hajar kasa cewa uffan tayi don ita tasan babu wanda ke kiranta da Hajjo sai yan gidan su sai kuma k’awayen ta Khadee da basmard tow shi kuma waye aina ya santa meyi halak’anta dashi? tambayoyin da tayiwa zuciyar ta kenan wanda itama bata da amsar su, duk yanda taso ta tuno inda tasan fuskar shi amman ta kasa “Hajjo gwada tada motar muga ko zai tashi” ko k’arin tadawa tayi amman motar sam tak’i tashi, kallonta yayi yace ina tunani sai me gyara ya duba ta yanzu muje na kaiki inda zaki idan yaso daga baya idan angama ruwa na kai maki motar gurin gyara, “Dr batayi gardama ba ta bishi don tasan babu yanda ta iya tarauni tace ya kaita gidan grany ,tunda suka fara tafiya babu wanda yayi magana cikinsu, ita kuwa Dr Hajar kanta ya kulle ta shiga duhu jira take ,kawai ya fad’a mata ina ya santa ko taji dad’i ,kasa jurewa tayi ta fara magana da muryanta me sanyin dad’i “bawan Allah ina kasanni kuma har kasan sunana?” Murmushi Captin Junaid yayi ,yace” kin tuna wata rana keda k’awarki ,kun fito daga jufatu na ganku na tsaidaku ,ki kak’i tsayawa sai k’awar takice ta tsaya tow itace ta fad’an sunanki “, sai alokacin Dr Hajar ta ,tunoshi nan danan kuma taji kunya ta kamata ,tun daga haka bata kuma cewa uffan ba har suka isa d’an madede cin gidan granyi me kyau da tsari hon Captin Junaid yayi megadi yazo ya bud’e musu gate , suna shiga Jawahir Dr Hajar tagani kanta babu d’ankwali gashinta ‘a sake daga ita sai pant tana wasa cikin ruwan sama ,ganin danowar motarne yasa tayi saurin k’ara sawa wurin tana “oyoyo Mummy “.

Fuskar Dr Hajar a d’aure cikin tsawa tace “wayace kiyi wasa ‘a ruwa? Bana hanakiba ? Tafi ki bani wuri mara kunya kawai bazan kuma zuwa dake ,ko inaba tunda bakijin magana”.Da gudu Jawahir ta koma cikin gida tana kuka , Sorry Hajjo Cool down naga kamar ,ranki ya b’aci sosai kinsan yara da son ruwa adunga hakuri dasu” ko kallon inda yake batayi ba don idonta ya fara zubar da kwallah fita ,tayi daga motar ko nagode batace ba tayi ciki…

Shiko Captin Junaid tambayoyine mak’il a zuciyar shi wanda bashi da amsar su ita kad’ai ce zata iya ‘amsa masa su shin dama tanada ‘aure? yake b’ata lokacinshi akanta kuma harda yarinya lalle tamasa nisa dole yasan abunyi ,tow Amman meyasa Khadee bata sanar dashi ba? Meyasa ta b’oye masa metake nufi dayin hakan? , buga kanshi yayi da jikin murfin motar ya furta ‘a fili Khadee kece zaki amsamin tambayoyina jan motar yayi zai bar gidan kawai yaga wayan Dr Hajar kan kujeran inda ta zauna da sauri ya rubuta number d’inshi yayi sauri yayi dailing sannan ya mik’awa megadi yace yabata…

Zaune taga datijuwar matar da bazata wuce shekaru 85 ba, tana sanye da doguwan rigan abaya, ta mik’e k’asan carpet tana kallon Aljazeera jawahir kwance a cinyarta, tana kuka, k’ara sawa tayi fuskarta ba walwala ta zauna kusa da datijuwan “grany barka da yamma ya gida ?” A’a Hajjo harkin shigo ne lfy qlau gida Alhmdulh ya aikin hope komai nomal kow?” Aiki lfy qlau ” gud yana ganki kamar baki da wata walwala waya ta6amin ke?” Tab’e ,baki tayi tace babu komai grany wlh Jahari ce kawai ta 6atan rai” tow me tayi kuma naga tashigo tana kuka ,kuma tak’i magana? “..

“Ruwafa taje tana shiga grany kalan idan dare yayi tahanani bacci tadameni da kuka ” tow ae yaranne yanzu basaji hak’uri zakiyi kumafa haka ‘akayi ta fama daku” tab’e baki tayi a shagwab’e tace “nidai banyi k’iri niya irin na yaran yanzu ba” dariya grany ta saki tace”sai kace lokacin kinada wayo “sun jima suna hira saibayan sallar isha’ sannan suka tafi gida….

“Mummy kince zaki ,kaini gurin dady na kuma haryau baki ,kaini ba, ni ,inaso naganshi ne ,nima inaso Babana yana kaini school kamar yanda yan class d’inmu babansu ke kaisu, kuma inaso na dinga ganinshi kusa dani” Dr Hajar ji tayi kamar ansara mata guduma ‘aka ,kasa driving d’in tayi ,tayi parking a gefen titi, taji kanta ya fara juyawa kalmar shi nak’arshe take tunawa…

~Hello my love kin yarda dani kamar yanda kika yarda ,da itayenki ,kin aminta dani ,ina sonkI Hajjo I love you so much Amman bazan iya zama dakeba domin bazan tab’a ganinki da daraja ba bazan ta6a ganinki da k’ima ba , ba kece mace tafarko dana gudu na bariba sunada yawa nariga na biya buk’atana don haka nakecewa dake nabarki lfy kije ki nemi wani mijin kiyi aure domin namiki nisa bazaku kuma jina ko ganina ba~

“Innalilahi wa inna ilaihi raji’un Allahuma ajirni fi musibatin” shine kalmar da take ta maimai tawa don aduniya bataso taji ,Jawahir ta ,tambayeta ina Babanta , danne hawayen dake k’ok’ari zubo mata ,tayi ta k’ak’alo murmushin dayafi yak’e ciwo ta kama hannun Jawahir “karki damu bebyna soon zan kaiki gurinshi banace miki saina samu hutu agurin aikina ba?” girgiza kai tayi tace”tow Mummy shi yana inane meyasa bazamu koma wurin shiba ?” Duk sanyi ac dake cikin motar be hana Dr Hajar jin zafiba ,zufane keta kwaranyo mata ,tako ina amsar da zata bawa Jawahir ta ,tsaya tana ,nazari cen kuma hikima ta fad’o mata, kama kumatun ta ,tayi tana dariyan dabekai zuciba tace” yana dubai yana ‘aiki shiyasa bama tare Amman idanya tara mana kud’e zai dawo mukoma gidanmu “…

Matsawa tayi sosai ta rungume maman “yeeh zamu koma gidanmu idan dady na yadawo ” shafa gashin kanta Dr Hajar keyi tana hawaye sunfi minti biyar ahaka sannan suka ,kama hanya saida ta ,tsaya tasiya ma Jawahir ice cream sannan suka wuce gida…..

Koda suka isa Jawahir tariga da tayi bacci ,d’aki ta kaita darect ta kwantar da ita sannan tadawo falon k’asa Dady ,da Mami ta gani zaune suna sauraron labarai a NTA “barkan ku da ,dare ” barka dai Hajjo ya hajiyar?” Dad ya tmby ..

“Tana lfy tace nagaida ku”. Muna ‘amsawa “cewar Mami “tow yayi kyau Hajjo !! “Dad yakira sunan ta “na’am Dad “ta’amsa fuskarta ‘a sake ,saida yayi shiru nayan mintuna sannan ya fara da “wai yaushe zakiyi aurene? Me kike nema yanzu da bazaki fidda mujiba ? nagaji da ganinki haka “.

Shiru tayi batace komai ba ita sam babu aure aranta hasalima batada wanda takeso don ita maza basa gabanta “kinyi shiru ko baki da kowane ,Nina kawo miki cikin yaran abokaina ?” Da sauri ta d’ago ta kalleshi tace “Dad zan kawo kad’an bani lokaci insha Allah zan kawo ” tow ina zuba ido badai naso wannan shekaran yawuce kina gidana, nagaji da gorin da yan’uwa da ,abokai kemin ” tow Dad insha ‘Allah zanyi k’ok’ari ” Tow Allah ya miki Albarka zaki iya tafiya “..

Tashi tayi tahau sama tayi d’akinta ,tana shiga ta fad’a kan gado tafashe da kuka ,tana ,nadamar haduwa da Akram a rayuwan ta, farkon had’uwanta adashi ta fara tunawa….

 NAIL UNIVERSITY 

Students ne keta zurga zurgansu a cikin haraban makaranta ,kowa harkan gabanshi yakeyi sanye take cikin English wears white T sheet da pink leggings sai ta d’aura kimona ‘a saman kayan tayi rolling pink mayafi me stone tasa weg takalmi white na company d’in Aldo hannunta rik’e da wani k’aramin white purs me d’auke da sunan tommy a k’asan face d’inta yasha kwaliya idon ta yasha eyelashes wanda ya k’ara mata kyau tana zaune jikin wani bishiya ta maida hankalinta kan wayanta k’iran iPhone 7 wanda yasha pink cover kunne ta sak’ale da earface tana bin wak’ar kal_ho_naa ho heart beat instru…..

Tafe yake cikin kayan kanti wanda suka karb’i fatarshi sosai ba fari bane kuma ba bak’i bane za’a iya kiranshi da wankan targwad’a dogone sosai yana da fafad’an fuska kanshi duk gashi fuskarshi duk saje sun kwanta sunyi luf luf ,su uku suka nufo inda take zaune biyun kamarsu d’aya ga dukkan alamu yan gida d’aya ne, zama yayi kusa da ita suma sauran zama sukayi a sauran kujerun dake gurin, ko d’agowa ta kallesu batayi ba sunfi kusan mintuna ‘ahaka sannan ,nakusa da ita yayi gyaran murya ,yace “Hy beby ” d’agowa tayi ta kalleshi ba tare da tasan abunda yace ba don ta k’ure volum d’in wayar ta stop tasa ,ta kalleshi a hasale tace” lfy malam zakazo ka zauna kusa dani duk ,kujerun wurin basu makaba sai wanda nake a zaune?” Murmushi yayi yana shafa sajen fuskar sa yace “sorry ni bazama nazoyi ba wurinki nazo don Allah ke student ce anan school d’in?”..

Kallon sama da k’asa tayi mishi sannan ta juya taci gaba da sauraron wak’arta ba tare da tace uffan ba, haka yayi ta magana kamar batasan ma da mutin a gurin ba , suna cikin hakane saiga Bersmad ta nufo inda Dr Hajar ke zaune tanai mata murmushi itama ,murmushin take maida mata “harkun gama?” Dr Hajar ta ,tambaya “yp mungama tashi mu tafi sanun ku” ta d’agawa mutanen hannun “yawwa sanunki kema wannan saurayin ya bata amsa, mik’ewa Dr Hajar tayi tana kad’e jikinta “Bersmar bani kuma rakoki school d’inan kuna jimawa a lectur wlh ” sorry Hajjo kinsha zama yau gsky wlh malamar ce ta ,tsaidamu ” tow muje kow ,wucewa sukayi suka shiga mota Bersmad ce ke driving d’in saida sukabar haraban school d’in sund’au hanya Bersmard ke tmbyn Hajar suwaye nazan da tagani tare dasu , nan ta kwashe komai ta fad’i mata “kai Hajjo wlh dakin kulashi kuma wlh daga ,ganinshi zeyi hankali gashi handsome guy dashi wlh kundace ,kuma gasky bad’an school d’inmu bane don ban ta6a ganin shiba ” tsaki Dr Hajar taja tace”kekika sani ,ni ,inaruwana kinga ni yanzu ba love a gabana study d’ina shine a gabana insha ‘Allah saina cikawa dad burinshi” in banda ‘abunki hajjo karfa ki manta ‘aski yazo gaban goshi kwana nawa yarage ki gama ?” Kajiki fa Basmed masters d’in fa? ” shi ko agidan mijin ki zaki iya yi “. Ke ni mubar wannan zancen ya isa haka “…

Akaram dai ,dashi-shige saida ya shigewa Dr Hajar suka fara shiri dashi duk randa bata raka Besmard School ba har haushi yakeji , don sun shaku sosai soyayya me k’arfi ta wanzu a tsakanin su iya wata biyun da Dr Hajar tayi a ‘Abuja ranar da zasu rabu har kuka saida tayi sanan kuma yayi mata ‘alk’awarin zezo chaina ganinta bayan ta koma….

K’ara sautin kukanta, tayi taname k’ara regreting saninshi a rayuwanta shine mutun na farko da tafara so aduniya kamar zata mutu kuma shine mutun nafarko da ta fara tsana kamar yanda ta ,tsani ranar mutuwan ta , Dr Hajar ko runtsawa batayiba ‘a wannan dare hargarin Allah ya waye sai wurin k’arfe tara ta samu bacci ya d’auketa don yau bata da niyar zuwa hospital ,har Alawuya ta shirya Jawahir ta, tafi school tana bacci har wurin 12…

Ganinta shiru yau har 12 yasa Mami tunanin ko lfy har yanzu bata ,tashiba d’akinta ,tashiga ta isketa zaune kan gado tana waya da Khadee, fuskarta ya kunbura idanta yayi luhu -luhu alamun tasha kuka , k’arasa shiga tayi tazauna gefen ta harta gama wayan takashe..

“Mami gud Afternoon ?” Afternoon dear lfy yau najiki shiru kuma bakije aiki ba?” Lfy qlau Mami kawai yau d’inne banji dad’in jikina shiyasa banje ba”.

“Allah ya sawak’e Amman ninasan meke damunki dukda bazaki sanar daniba , Mamana ko ,kad’an bana son ganinki cikin rashin walwala jibi yanda fuskarki ta kumbura idanunki sukayi jazur alamun kinci kuka ,meyasa kike son sawa kanki damuwa ne?”.

“Mami ki kwantar da hankalinki am ok fa kinsan daga bacci na tashi ,shiyasa kikaga fuskata haka” tow nidai bana son ,nadinga ,ganinki cikin kunci Khadee zatazo ne?” Eh wai k’arfe biyu zata shigo” tow Allah kawota barin koma ciki lokacin sallah yayi”….

BY DIJA_WAZIRI🀞
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

     *(P.M.L)*

Chapter 6

“Friend ya jikin naka? ” jiki da sauk’i sosai ” Allah ya k’ara sauk’i ” Ameen da gaske gobe zaka wuce? ” insha Allah gobe zan wuce karfe 1:20 na dare jirgin da zan tuk’a zai tashi,” Allah ya kaimu ya maganar girlfriend d’inka ,kun dai -dai ta kuwa? “…

“Hmmm nifa lamarin tama ya fara d’aure min kai jiya mun had’u da ita motarta ya lalace a hanya na kaita gida, kasan ashe tana da ‘aure” aure !! Kuma ban gane ba? ” yes Aure harda beby wlh “.

“Tow meyasa ta b’oye maka”.

“Ae ita sau d’aya na tab’a ganinta jiya shine ganina da ita na biyu, k’awar tace tab’oye min bansan dalilin hakan ba kuma nakira wayarta bata d’auka ba”..

“Tow babban magana kuma kiranta muji ” wayarshi ya d’auka yayi dailing number d’in Khadee bugu d’aya ta d’aga “Hello my father sorry naga call d’inki am busy ne shiyasa ban kiraka ba ya kake ya komai da komai katafi ne? ” nvr mind dota np sai gobe insha Allah zan tafi ” tow Allah ya kaimu “Ameen kunyi magana da mutuniyar? ” no wlh kwana biyu bama had’uwa da ita ‘Amman yau zani gidan su around 2 o’clock ” ok tow ina jiran ,amsa dama nakira na tambayeki wani abune ” ok inajinka Allah yasa nasani “..

“Ameen, Hajjo tana da ‘aure ne?” Jin tambayar tayi wani ban barakwai ta fara tunanin ko anfad’i masa ‘wani abu daga Dr Hajar ne “A’a amman meyasa ka tambayeni ?” ,no ba komai fa kawai dai na tmby ne sai najiki bye” bejira abunda zataceba ya kashe wayar…

Ita kuwa ‘ajje wayar tayi tare da tunanin kodai an fad’i masa wani abu game da ita ,ta k’osa 2 tayi taje suhad’u..

“Kaji bata da ‘aure amman ita wannan yar danaji tana ce mata Mummy yar wace ?” Maybe yar sister d’in tace ko brothe d’inta “cewar Samir “tow zai ‘iya yuwuwa ” sun jima suna tataunawa sannan sukayi salama kowa ya kama gabansa

“Khadee ya gida ya mama? ” lfy qlau Hajjo ya jin nyc ” wanwi nyc Ae Khadee abubuwa sun jagule min wlh narasa yanda zanyi pls kiban shawara ” tow Allah ya fidda, daki mekuma ya faru ?”..

“Jiya Dad yace na kawo masa miji kuma bayaso year d’innan ya k’are batare da nayi aure ba, gashi Jawahir tasani a gaba wai sai na kaita guran Babanta wlh duk narasa yanda zanyi Khadee” murmushi Khadee ta saki “wannan ae me sauk’i ne k’awata ,kina da wanda kike so a yanzu?” Girgiza kai Dr Hajar tayi “bani da kowa ” ban yarda ba Dr Samir meye halak’arki dashi nifa tunba yauba na fad’a miki wlh sonki yakeyi Doc.. Koki yarda ko ,karki yarda keda Doc.. Kuna son junan ku ?” Har cikin zuciyarta, tasan tana jin wani feeling game dashi amman tarasa nameyi na shakuwa ce koko na so ne ta kasa ganewa D’aure Fuska tayi tace” Khadee kinga irin abunda ke had’ani fad’a dake kow nina ce miki ,ina son sa? ” dariya Khadee ta saki tace “ni bance ke kika fad’a ba nice da kaina na hango wani abu tsakanin ku ” tow uwar sa ido ni basonshi nike ba kawai abokinane kuma duk shekarun da kikaga munyi dashi bawai na sake masa bane, don banajin zan iya k’ara yarda, dawani d’anamiji arayuwa ta, ko auren ma da kikaga ina son yi zanyi ne saboda Jawahir da kuma don nafaran tawa iyayena’ amman idan tanine nariga dana haramtawa kaina sake kusantar wani d’anamiji ” tow nayarda Hajjo amnan wlh kinji na rantse Doc.. Sonki yake tun kwanakin baya na gane abunda yake nufi kuma, munan dake wataran zai furta miki ” tow mubar wannan zance dai yanzu miye abunyi? “…

“Tow ni aganina kawai ki yarda da batun Captin Junaid tunda ya nuna yana sonki, kibashi dama ya fara zuwa ” cikin rashin fahimta Hajar tace “waye kuma captin Junaid? ” oh sorry na manta fa ‘ashe baki san shiba” nan tayi mata bayanin komai “….

“Chap wlh bason shi ke nifa wlh haushi yake ban tun randa na ganshi be kwanta min a rai ba jiya ae mun kuma had’uwa dashi shiya kaini gidan hajiya ” dama ae ba tafara d’aya so yake kama mutun ba wani ken halinshi da d’abi’un sane zaisa kiji ya kwanta miki wani kuma kyautatawan sa, wani kuma haka nan tun randa kika hadu dashi zakiji yamiki, kiyi hakuri ki, karb’i number d’inshi insha Allah zaku daidai ta wlh yajima yana kirana ‘akanki “..

“Tow nidai bana son shi Khadee bana kuma jin zan sosai zan dai karbi number dinne sabida ke ” yawwa k’awata nagode “wayan ta Khadee ta karb’a tasa mata number d’in tayi seving, k’asa suka sauka sukaci abinci suka d’anyi hira sannan Khadee ta, tafi

       ******** 

INDIAN INSTITUTE OF ARTS ND SCIENCE

   5 o'clock 

Susu shidane zaune kan wasu kujeru da ‘aka kewaye, duk kansu farare ne ga dukkan alamu yan k’asar ne d’aya daga cikin sune bak’e amman bacenba yana da saje kuma yana tara gashi bakinsa baki, kirin gadukan Alamu yana yawan shan taba….

“bak’in cikin nasune yace “kutashi mutafi gidan rawa nagaji da zaman cikin makarantar nan, dukkansu a kwale suke don k’atuwar kwalban giya ce a tsakiyan su….

Mikewa sukayi suna dariya da hauka irin na wainda suka bugu, gurin motarsu suka nufa suka shiga sukaja sukabar haraban makarantar, basu tsaya ko inaba sai babban gidan rawan dake, k’asar, parking sukayi sannan suka fita suka shiga cikin wuri, yan matane keta rawa wasu daga bra sai pant wasu kuma rigace me shara shara babu abinda ba’a gani najikin su, yan matadai kala -kala gasunan sai wanda suka zab’a ,haka kowa ya kama wacce tayi masa,suka sauka dancing flow suka fara ,rawa , harsaida sukayi me isarsu suka ,k’ara cika, cikinsu da barasa ,suka tab’a mata yanda ransu keso sannan suka tafi wurin k’arfe 2 nadare , wannan bak’in suka fara saukewa gidan su ,sannan sukayi gaba….

Gidane d’an madai -daici me d’auke da ,d’akuna uku sai kitchin da madai- daicin falo ,gidan dai yayi kyau ginin irin na indiyawa..

Wata datijuwa nagani sanye da parkistan fari ta yafa mayafin shi tana zaune kan sofa bazata wuce shekara 41 ba ,bak’ace sosai , shigowan shine yasata ,tashi da gudu tayi ,inda yake rik’oshi tayi ,tana zubda hawaye” Akram daga ina kake tun dazu ina jiran ka ? har yanzu baka dena yawo da yan iskan abokan kaba kow? Akram kasan dai muba yan k’asanan bane karka jawomin rigima fa” tana maganar tana k’okarin d’aurashi kan sofa…

Cikin muryan yan maye yace” koki fad’an inda mahaifina yake ko kuma idan ,natafi bazaki kuma jina ko ganina ba waye ubana? ” shiru tayi tana hawaye batasan tayanda zata fara yimasa bayani ba tun farko itace tayi kuskure itace sanadin gur6acewan tarbiyyar d’anta ,ita kanta ,tasan ba uwa tagari bace sai yanzu tafara dana sanin abubuwan data ‘aikata abaya ,kuka take sosai …..

“Kuma ki fad’a min dalilin dayasa kike shigo da maza cikin gidannan tun ina k’arami ” towfa ‘ana wata ga wata dama ance ranar wank’a ba’a b’uyan cibiya inji hausawa duk abunda kake b’oyewa watan wata rana dole gaskiya tayi halinta…..

Bata iya cewa da’Akram uffan ba tayi d’akinta da gudu tana kuka me tsuma zuciya , ita yanzu inama tasan inda mahaifin akram yake ita dai tasan a kano yake amman batasan inda zata sameshi ba shekara 30 rabonta da naija tasani ma ko yamutu ko yana raye da wannan tunani ta, tashi tashiga toilet tare da ‘Alwashin sai taje naija ta nemoshi duk inda ya shiga ya fita…

Naigera 

Knocking d’in da yaji anayi ne yayi saurin dawo dashi gada tunanin da yake “waye ?”ya tambaya “bro nice “Salma tabashi Amsa “ok come in” shigowa tayi, fuskarta d’auke da murmushi tace “bro Ummi is calling you ” ok hope bawani abu bane ya faru kow? ” yes bro “jekice mata ina zuwa ” tana fita bata jimaba shima ya sauko downstairs zaune ya samesu sun baje kan carpet suna cin abinci, k’ara sawa yayi ya zauna “Ummi gani yau abincin kuma ‘afalo kuke ci ” wlh bana son daining d’innan kasan tsufa yazo baya na ” bece komai ba sai murmushi da yayi ” Salmace tayi magana “Bro ga naka cen kona kawoma nan ” harta mik’e ya tsaida ta “no banajin yinwa zauna ki gama cin abincin coffee kawai zansha “..

Sun gama cin Abunci Salama ta, kwashe komai takai kitchen sannan ta had’o wa Dr Samir coffee ta kawo mai..

“Doc… Wai yaushe zakayi aure ne? ” Ummi ta, tambaya murmushi yayi, “Soon Ummi har yanzu ban samu wacce ta kwanta min arai bane ” tow Allah ya kawo tagari kamar Jamila “saida ya d’anji wani iri da Ummi takira sunan Jamila don shi ko sunanta, yaji ankira saiyaji wani iri “Ameen Ummi ” sun jima suna hira sai karfe goma da minti arba’in sannan kowa ya shiga d’akin sa, Dr yana shiga d’aki wani box ya zaro daga k’asan bed d’inshi ya bud’e ya d’auko wasu k’ananan keys drawer d’in dake jikin godon shi yasa ya bud’e da wannan key d’in wani box ya d’auko me kyau yasha kwaliya zura key yayi yabud’e ya ciro wani d’an madai-daicin diary ya hau kan bed ya fara rubutu yana murmushi saida ya shafe wurin 30 minutes yana rubutun sannan daga bisani ya rufe ya mayar ya kulle ya maida keys d’in cikin favourite box d’inshi yarufe yamayar k’asan bed duba ‘agogon dake mak’ale a bangon d’akin yayi yaga saura 10 minutes 12 tayi da sauri ya d’auki wayanshi ya shiga wurin text massage ya fara typing….

Zaune take kan sofa fuskarta sanye da glasses, ta maida hankalinta kan wasu takardu dake gabanta wanda take shigar da wasu abu cikin system d’inta wutar d’akin akashe, jin k’aran shigowan massage ne yasa tad’auki wayan ta dake bayan System azuciyarta, tana fad’in “waye kuma cikin darenan damin text, ganin number d’in Dr Samir ne yasa tayi saurin bud’ewa, fara karanta massage d’in tayi kamar haka….

There are so many things about our friendship that i love. Your birthday is going to be the perfect time to celebrate your day and all that our friendship means to me. I look forward to showing you how much i care Happy birthday day ones again Doctor wish you more years ahead Allah ya ‘albarkaci rayuwan ki ya baki nisan kwana muga har auren ki

Tayi matuk’ar farin ciki daganin massage d’in Dr Samir, don ita , tama mance yaune birthday d’inta, kuma bata tab’a tunanin zai tuna ba ,murmushi tayi, sannan tayi masa reply.

“Thank you so much Doc… Really appreciate it “daga k’arshe ta tura imojo d’in murmushi.

Tana matuk’ar jin dad’in yanda suke hurd’a da, Dr Samir Amman har yanzu tak’i yarda ta sake dashi 3 year kenan suna tare k’aran massage ne taji ya kuma shigowa dubawa tayi da sauri taga ya turo mata reply…

“Ur wlcm dear you deserve more, gud nyt I’m not feeling fine today”…

Murmushi ta saki ta kuma yi masa reply.

“Ok Sweet dreams meke damun ka? “

“ta tura, ba’ajima ba yayi mata reply “

“Gefen heat d’inane kemin zafi tun jiya”

“Eyyah wishing you a complete and restful recovery, hope you feel better soon “

Reply

“Tnx Doc…. Gud nyt”

Kashe wayanshi yayi gaba d’aya sannan yasha maganinshi ya kwanta….

Itama rufe system d’in tayi takoma kan bed ta kwanta, tajawo Jawahir kusa da ita, tana shafa gashin kanta haka nan ta, tsinci kanta cikin farin ciki duk wani kunci da, damuwan da take ciki taji sun gushe, ita, tarasa dalilin dayasa ko waya sukayi da, Doc…. Takejin farin cikin sannan kuma tarik’a jin feeling something game dashi……

BY DIJA_WAZIRI🀞
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

chapter 7

Thursday morning

“Hy wake up!! Hajjo “

“Ha’a wai waye ne “cikin muryan bacci doc.. Tayi tmby

“Ki tashi idan kin tashi zakiga kow ,waye “ahankali tafara bud’e idon ta, tana bud’ewa ta sauke su kan kyekyewar yar budurwan dake zaune gefenta, mutsuka idon ta, tayi ko karya yake nuna mata still dai itan ta gani, da sauri ta mik’e ta rugumeta “Besmerd yaushe kika zo ?” Wacce aka kira da Besmerd d’ince tayi murmushi tace “tunjiya da safe how are you Hajjo? “I’m gud nd u? ” same to you Happy birthday ” tnx wlh nayi farin cikin ganinki Bersmard ” me two sisto ina Jawahir? ” Jawahir tana school ” cewar Dr Hajar..

“Ok kin dena kawo mana ita ‘Abuja ” wlh ban dena ba school ne amman dama inada niyar kaita idan sunyi hutu ae sunkusa befi 2 week ya rage ba ” ..

“Shikenan ma saina tafi da ita dama 2 week d’in zanyi yau baki da work ne? “

“Wlh inada patient amman sai 10 zan shiga ” tow ae saura 30 minutes 10 d’in tayi ki tashi ki shirya zan rakaki barin cire wainnan kayan na cenza ” sai alokacin Dr takaleta sosai taga kayan aikine a jikinta taci fari da bak’in kayanta wanda suka karb’i jikinta sosai “Barrister Basmer kinyi kyau kayanan suna maki kyau wlh ” I know sister nima duk randa nasa nakanji ajikina suna min kyau tnx” mik’ewa Dr Hajar tayi, tashiga toilet tayi wanka tafito sannan Bersmerd ma tashiga..

Bata wani jimaba tagama shirinta cikin wani dakaken less wanda ‘ak’ala zaika dubu d’ari da hamsin farine sai flowers d’in jiki silver yasha d’inkin riga da sket kayan sun balain k’arb’an ta, sun gama duk shirin da zasuyi cikin sauri suka sauka downstairs saboda ta makara gaishe da Mami sukayi kawai suka wuce kota ‘abinci basubi ba.

Tana zuwa hospital saida taje ta duba patient d’inta taga lfyr kowa sannan tawuce office d’inta shima saida taga patient 5 sannan..

“Basmad wai ya maganar bikin ki an fasa ne? ” wlh yanan dai kurum and’aga ne sai nanda 4 month dama Mum bata gayawa Mami ba? “..

“Wlh ban saniba kota gaya mata don bamuyi zancen ba ‘Allah ya kaimu ae kamar yau ne”…

Basmad cousin d’in Hajar ce da Maman hajar da Maman Basmad yaya da, k’anwa ne maman Hajar itace gaba da Maman Basmad..

“Ameen Hajjo ke yaushe zamusha naki ne wai yanzu wa kike dashi ?” B’ata fuska Hajar tayi tace “bayanzu ba ‘amman zanyi soon ” dariya Basmad tasaki tace “kin janye kudurin naki, kenan? “.

“Tow yazanyi Basmad Jawahir ta sani gaba na kaita gurin mahaifin ta Dad yace kafun shekaranan ya k’are na kawo masa miji inba haka ba ze za6a min cikin yara ‘abokan shi, zanyi aure ne badon soyayya ba sai don na faran tawa iyayena da kuma d’iya ta ‘amman nikam nariga da na cire soyayya ‘a raina zanyi aure ne don karna gamu da fushin uban gijina amman badon ina soba ” tak’arasa zancen tana hawaye me cin rai …

“haba Hajjo daga magana kuma sai kuka, maganar kin maga so be taso ba wlh Hajjo idan har zaki auri namiji inde shi yana sonki tow, wlh zakizo ki soshi bafa duka maza bane suka taru suka zama d’aya Akram yayi maki abunda koni yayiwa zan iya cewa hakan amman ki dunga la’akari da baduka maza bene irinshi karfa ki manta Hajar A soyayya ake samun yarda, A soyayya ake jin dadin rayuwa A soyayya ake samun farin ciki A soyayya ake shiga kunci A soyayya Ake abota A soyayya….. “

“Dakata Basmad ta katseta duk abunda kika lisafa ban yarda, dasuba Basmad naso Akram, kamar me Amman daga k’arshe Akram ya nunamin halin maza nayarda, da Akram d’ari bisa d’ari ban tab’a tunanin akram zaici amanata ba ko yaci amanar soyayyar muba Basmad natsani mak’aryacin mutun na tsani mayau darin mutun na” tana fad’a tana kuka me sauti “tun randa Akram ya tafi ya barni farin ciki ya gushe daga, gareni nadena jin dadin rayuwa ta, wlh Basmad ke, kad’ai na gayawa wannan maganar shekaru biyar kenan da suka wuce kullum sai nayi kuka ‘akulu yaumin bazan iya k’irga adadin kukan da nakeyi ba ,barinma idan na kalli Jawahir ,idan aka bud’e zuciyata wlh babu abinda za’a gani ciki ilah bakin jini cox ni yanzu babu farin ciki arayawa ta najima da, dena ganin farin ciki, zaki ganni ina wasa ina dariya da jama’a amman nik’adai nasan zuciya ta”….

“Hajar Hakuri zakiyi idan kina son kiji dad’in rayuwan ki kada ki damu da ‘abinda ya wuce, laifi kowa anayi masa masu rauni su ke daukar fansa masu karfi su, suke yafewa ‘amman bance ki yafewa ‘Akram ba don yayi abunda dawuya ‘ayafe masa’ amman inaso ki manta da anyine kawai Allah zai bimaki hakkin ,ki Allah zai saka miki zaluncin dayayi maki Allah zai had’ashi da gamon shi ,Ruwan teku duk yawansa baya iya nutsar da k’aramin jirgi sai idan ya ratsa shi. Haka matsalolin rayuwa suke, idan ka bari suka ratsa ka sannan ne zasuyi maka ilah Dr Hajar ki d’auki hannun ki godewa ubangijinki wlh yana sonki tunda har ya barki da ranki da lfyn ki, wlh da wata ce a irin halin da kike da tuni tarasa ranta ko takamu da wata cutar “

Daga Dr Hajar har Basmad maida kallon su, sukayi inda memaganar ke tashi, Khadee suka gani tana kokarin k’arasowa inda suke tana magana…..

“Kiyarda, da tayin da captain yayi miki insha Allahu bazaki tab’a yin nadama ba, ae yanzu keba yarinya bace kinsan yanda zaki tafiyar da irin rayuwan soyayyar dazakuyi har kuyi aure, don yanzu duk kinfimu hankali

Dr Hajar k’ara sautin kukanta tayi, azahirin gsky duk abunda khadee tafad’a hakan yakamata ace tayi tow amman tayayi zata koyawa zuciyarta son captin? Tana tsoran k’ara jefa kanta cikin torkon soyayyar wani shima yaje yayi mata irin cin’amanar da Akram yayi mata tana sheshekar kuka tace.

“Khadee bazan iya son shiba sai dai zan iya auren shi kawai don gujewa fushin ubangiji ne ” munyarda Hajjo amman ki daure ki dinga d’aukar wayan sa “cewar Khadee..

“Waye captin Khadee ” Basmad ta, tambaya “wlh wanine yake sonta yajima yana bibiyar ta ” Khadee ta bata ‘amsa…

“Allah sarki, keko Hajjo ki jaraba kulashi man wlh zakiga banbanci sai angwada ‘akansan na kwarai ” cewar Basmad “wlh fa Basmad kin fad’i gsky sai angwada ‘akansan na kwarai yaushe kika zo? “

“Jiya nazo wlh akwai wani cases na Rep da zamuyi shara’a jibi ” eyya Allah ya bada sa’a itadai Dr Hajar bata kuma cewa dasu komai ba har suka gama hiransu….

“Dr Hajar nifa nazo maki da case d’in yarinyar nance me blood cancer zamuyi transfer d’inta zuwa Aminu kano ” sai alokacin Dr Hajar ta d’ago tayi magana “why Khadee mud’in bamu da kayan aiki ne? “

“No muna dasu amman ni gsky bazan iyaba ‘abun yafi k’arfina kuma Dr Lloyd da Dr David ,kinsan basanan gashi yarinya sai shan wuya takeyi ” tow bari zanwa Dr Samir magana inyaso idan yayi magana acen Hospital d’in sunyarda sai’a maidasu cen zan gayawa dady Yau idan ,nakoma”…..

Suna cikin hirane sukaji knocking Basmad ce tace “Yes waye shigo ” Dr Aiman ne yashigo hanunshi dauke da wani red kwali wanda yasha zanan rose…

“Happy birthday Doc… Wish you more years ahead ” murmushi tayi tace thank you Doc… “

“Ur wlcm gashi friend d’inkene ya turo yace abaki ” ya ajje kan table d’inta be jira mezatace ba yafice

“Happy birthday Hajar wlh na manta yau ne birthday d’inki ” tnx Khadee ‘ tacigaba da rubutun da take tun d’azu don bata da niyar bud’e kwalin ma, suko su Khadee cigaba da hiransu sukayi, wayanta da yayi ring ne yasa ta ‘ajje bairo dake hannunta, taga me kiran wayan….

Captin Junaid taga ‘anrubuta kamar yanda Khadee tayi mata seving, babu wani fargaba ko tashin hankali ta d’auki wayen, daga b’angaren shine yayi magana…

“Hello my angel how are you? “..

Fusk’ata ba fara’a tace”I’m gud “..

“Masha Allah ya beby? “

Maganar ce tajishi wani ban barakwai ya ‘akayi yasan tana da beby bayan koyan hospital d’insu babu wanda ya sani hasalima daga Khadee sai Basmad sai iyayen ta su kad’ai suka sani, sai cen tatuna ranar da ya kaita gida yaga Jawahir….

“Lfynta qlau ” tana maganar kamar baza tayi ba …

“Tow ashafa min kanta kafun nadawo nagan ta “..

“Tow zataji “…

“Nagode, dama nabugo naji muryan ki “….

Bata bashi amsaba tace sai anjima takashe wayar….

“Dawa kike waya Dr Hajar? ” Khadee ta, tambaya “dawa kuwa zanyi waya in banda ,d’an nacin cen ” murmushi Khadee tayi tace “kideyi hankali karki fara sonshi kizo kiji kunya” Hajar batace da ita komaiba tacigaba da ‘abunda takeyi , “wai miye cikin kwalinan ne idan bazaki bud’eba ni barin bud’e ” Basmad ta fad’a tana shirin bud’ewa..

“Wow “

Shine abunda ,Basmad ,da khadee sukace , birthday cake ne aciki red volved cake me shep d’in heart yasha kwaliya anrufeshi da red icen sai kwaliyan jiki fari anrubita Happy birthday my lovely friend a jiki abun gwanin ban shi’awa.

Ta gefen idon Dr Hajar ta ‘akilli cake d’in ita kanta ya balain burge ta, amman tashare tacigaba da rubutun ta..

“Hajjo gsky friend d’inanan naki naji dake sosai wannan irin abu haka gsky ,yayi kyau ” cewar Bersmed, ita kuwa Khadee ganin cake d’innan, ne ya k’ara tabatar mata da cewar Dr Samir yana son Dr Hajar….

Kuyi hakuri da wannan,

Nasan tamboyoyi ne mak’il cikin zuyiyan ku, kubini sanu ahankali zan amsa muku su

Shin kuna ganin Dr zata fara son captin?

Kuna ganin maganar Khadee zai ,zama gsky?

SAI NAJI AMSAR KU ZANCI GABA

BY DIJA_WAZIRI🀞
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

   this page goes to you may lovely sister Aisha Abbakar thanks for always supporting me, and encouraging me you 're a true friend and l want you to know how much l love and appreciate ur effort . You 'are the best ❀❀😍😍

Chapter 8

“Ummi shikuma wannan letter na miye shi ? Kuma pic d’in wacece wannan? Wacece ita? Meyasa kike kuka Ummi kinsan aduniya babu wanda nake so, sama dake bana son ganin hawayen ki “….

“Kafun mahaifinka ya rasu yabani yace nabaka Samir ka bud’e ka, karanta zakaga komai”, shidai Samir be gane komai ba ya bud’e pepar ya karanta sannan ya dubi Ummi cikin tashin hankali yace…

“Ummi, ki kwantar da hankalinki kiyi shiru insha Allah zanje inyi “iya bakin kok’arina zan cikawa Abba burin shi ” yawwa Doc… Don Allah duk yadda za’ayi kanemo d’an uwanka mahaifinka da bak’in cikin rashin d’an uwanka ya mutu be ta6a nuna maka bane soboda baya son ganinka cikin bak’in ciki”.

“Insha Allah idan ,nasamu tima next week zani ijift d’in don ganin ,nagano inda suke…

     ******

Gida suka dawo Basmad tun a mota ,takejan Hajar da surutu amman Hajar fir tak’i sakewa suyi hira don bata buk’atar magana tana son keb’ewa ita kad’ai don tasamu damar bawa kanta ‘amsoshin tmbyn ta. Suna shiga ciki, direct d’akin ta suka wuce kwance suka samu Jawahir daga ita sai pant tana gema cikin tab d’inta , ganin shigowan sune yasa tayi saurin ajje tab d’in tayi hugging Hajar tana oyoyo Mumy , itama Hajard’in ruguman ta ,tayi “my beby ya kike ” lfy qlau Mumy i miss you so much” shafa gashin kanta ,tayi tace me two darling ina kayanki? ” b’ata fuska Jawahir tayi tace “Mummy zafi nakeji shiyasa ban saba ” sai alokacin Dr takula da ac d’anki ba’a kunne yakeba, d’aukan remot tayi tafara kunnawa…

“Aunty Basmard gud afternoon? “.

“Nayi fushi tunda sai yanzu kika tuna dani Mummy d’inki kawai kika sani ni kodan hugging d’inma baza’a min ba” Sorry Aunty tayi saurin rugumeta, tana dariya….

Jawahir yarinyace k’an k’anuwa duka-duka shekarunta 6 amman idan tana wani abun kamar wata babba, ga shegen wayo kamar dila, aduniya babu wanda takeso masa da mahaifiyar ta bataso taganta cikin wani yanayi, wataran idan taga maman, nakuka itama saita sata gaba suyi tayi tare, tunda take bata ,tab’a ganin baban taba ko’a hoto kullum mahaifiyar ta, take gani sai kakanin ta bata zuwa ko ina daga school sai gida sai kuma gidan Kakar su Hajar shikenan inda take zuwa..

Basmad ,data huta ,tayi wanka taci abinci d’aukan Jawahir tayi suka nufi BQ d’in gidan suna yan hiransu , ita kuma Dr Hajar wanka, kawai tayi tasa kaya marasa nauyi kasa cin abinci tayi sai ruwan Lipton data d’ansha, shima kad’an, kwanciya tayi tad’an kishingid’a tana kallon tv dake manne jikin bangon d’akin mbc Bollywood take kallah ammah ga dukkan alamu ba film d’in da ‘akeyi take kallo ba ta, tafi duniyar tunani …

K’aran wayan tane yayi saurin dawo da ita ganin, number d’in Doc… Yasa tayi saurin dagawa cikin muryanta me kwantar da hankali tace…..

“Asalamu’alaikum”..

Lumshe idonshi yayi don dukranda yaji muryanta sai yaji wani abu ya tsarga mishi

“Was’alaikum salam Doc.. Ya kike ya ‘aiki? “…

“Lfy qlau aiki Alhmdulh ya jikin naka?, naga cake thank you “…

“Jiki da sauk’i gobe zanzo hospital d’in ae “…

“Tow Allah ya k’ara sauk’i wai me kake zuwa yi wurin Dr Aiman duk Friday ne? “….

“Babu komai zan gaya miki amman bayanzu ba “..

“Tow sai yaushe kenan baka yarda, daniba karfa ka manta I’m your friend yanzu akwai abunda zaka iya boyemin ?”….

“No karki dauka da wata manufa Allah i promise you zan fad’a miki, niko na yarda dake 100% amman ke haryau baki yarda, daniba don ban ta6a sanin wani abu nakiba duk shekarun da mukayi muna tare”…

Bezama wajibi kuma kasani ba kama dena saran zaka sani don think you know me you only know what i allow you to know cox ban yarda, dakuba tafad’a cikin zuciyar ta ‘azahiri kuma tace…

“Ae bani da wata damuwa shiyasa ‘amman da inadashi zan nemi shawaran ka “…

“Ban yarda ba Dr nifa ba k’aramin yaro bane wlh duk wanda ya tsaya, ya kalli cikin idonki sosai zaisan kina da damuwa sosai ae labarin zuciya ‘a tmby fuska tafad’a “…

Some time abubuwan Doc… Suna d’aure mata kai duk abunda take yana kula da ita ya ‘akayi yasan tana cikin damuwa? ‘abunda sai wanda taga dama ya sani sannan yake sani…

“Bani da, damuwa Doc… Believe me “…

“Tow nayarda yanzu ki shirya zanzo mufita yau anjima wurin 5 o’clock “…

Yace mata ya, yardane don bayaso suja zance amman azahiri yasan tanada, damuwa

Wani yawu taji ta had’iya lokaci guda zuciyarta, tafara mata zafi da taji furucinsa na k’arshe sake maimai tawa tayi cikin zuciyar ta, ki shirya zamu fita karfe 5 ,shiru tayi batace dashi komai ba kuma bata kashe watar ba saida hawaye data fara zubda wa…

“Hello Doc.. yanaji kinyi shiru ko akwai wani abune? “..

Lokaci guda muryanta ya cenza

“Babu komai amman kayi hakuri bazan iya ba “…

Cikin tashin hankali dajin muyanta kamar maikuka yasa yace…

“Meyasa Hajar? Meyasa daga magana kuma naji muryan ki ya koma na kuka ranki, kamar ya b’aci? “..

“Bubu komai Doc…. Zamuyi waya letar ” batajira mezai ceba takashe wayar…..

Shiko sai hello- hello yake wasu tunanuka ne suka fara zuwa ma,

Tow ko miye dalilinta nacewa ‘a’a? Ko batayarda, dashi bane? hakadai ya ringa tunani kala kala…

Tana kashe wayar tayi cilli da ita, ta juya fuskarta jikin fillo tana wani irin kuma me cida zuci ..

TUNA BAYA

Dr Hajar macece mai adini tasan yakamata mace me kamun kai me tarbiyya, ita sam batasa love a rayuwan taba karatunta kwai tasa gaba…

Kwatsam saiga ‘Akram yazo yashiga rayuwan ta shine ya ruguza mata duk wani burinta, tun bata ‘amince da Soyayyar Akramba tsabar naci irin nashi sai da yasa ta yarda, da soyayyar sa…

Lokacin da takamu da son Akram tana final year a matakin karatunta ‘ak’asar chaina, soyayya suke me ciki da ‘abun shi’awa da tsafta wasu lokunta Akram ya kanyi, yinkurin ta6a wani sassa najikin ta ‘amman saita nuna mishi bataso hakan badaidai bane..

Tow tunda Akram ya lura da bataso, ita ba irin matan daya saba kulawa bane watsatsu sai yake, kiyaye wa..

Akwana ‘a tashi bawuya agurin Allah Dr Hajar harta kamala karatunta tadawo gida, wata rana Babanta ya kirata cikin ladabi taje “Dad gani” yawwa Hajjo kina lfy? ” lfy qlau Dad” tow masha Allah”…

“Dama inaso na miki wata, tambaya ne ” tow Dad Allah yasa nasani” saida ya d’anyi jim kad’an sannan yace “miye tsakaninki da wannan yaron da kullum yake zuwa? “…

Shiru tayi taji kunya ta kamata, tace “Dad shine wanda nake fad’awa Ummi ” ok tow… Tow dama shine tow kiyi masa magana kice ina nemansa gobe da yamma ” tow Dad insha ‘Allah zan fad’a masa “…

Bayan da Dr Hajar tabar gurin Dad Akram takira ta sanar dashi abunda Dad ya gaya mata, shikuma ya ‘amince zaizo goben…

Washe gari da ‘Akram ya tashi zuwa gurin wani abokinsa yaje ya aro babban riga dahula yasa, yayi shigan mutunci ya b’oye gashin da yake tarawa da hula…

Dad na ganinshi yaji yaron ya kwanta masa ‘arai rusunawa yayi har k’asa ya gaida, Dad ” Barka da yamma Alhaji ina wuni? ” fuskar Dad, d’auke da murmushi yace “Barka dai lfy qlau ya gidan naku? ” Alhmdullh” tow masha Allah ” kaine kake neman Hajjo kow? ” Eh nine Alhaji ” kanshi a sunkuye yake bada “Amsa..

“Tow yayi kyau, kai d’an wani garine yaya sunan mahaifinka? ” shiru yayi, yashiga tunani don baitab’a zaton tmbyn da za’ayi masa kenan ba idan yazo ,”nidan, nan garin ne mahaifina kuma yajima da rasuwa saidan yanzu ina hanun kanin mahaifina Sunanshi Alhaji inuwa mai dala ” ok yasunan unguwar ku ” Akram jiyayi Dad ya fara bashi haushi donshi arayuwan shi baya son bin didigi kuma baya son tmby ,yacika yawa kuma yana ganin kamar wannan mutumin neman kureshi yakeyi, daurewa yayi, yace .

“gidanmu na lamid’o cresent”…

Daganan babu wanda yace komai shirune ya biyo baya sai cen Dad yace kaje zan nemeka, salama sukayi cikin ladabi da biyayya ,yatashi ya fita, yana fita ya d’aure fuska, koda Dr Hajar ta nufo inda yake, k’in d’aga ido yayi ,yakaleta “Akram, meyafaru naga lokaci guda ka cenza wani abun Dad yace maka? “.hankalinta ‘a tashe tayi maganar,

Kollon ta yayi ranshi a b’ace yace “dama kinsan zancen da Mahaifinki zemin kenan shine baki sanar dani ba” wani zance kuma ‘Akram ?wlh ni bansan komai ba ” ni arayuwa ta bancika son tmby, tayi yawa na tsani bin didigi Haba sai kace wani wanda zai cutar dake za’a wani sani agaba ‘anamin tambayoyi sai kace k’aramin yaro “…

“Haba Akram ae naga ba laifi bane don ansan asalinka miye abun tada hankali? ” au hakama zakice ” yaja tsaki yayi shigewar sa mota yana kok’arin tadawa, binshi tayi tana masa magana ‘amman ina tuni yaja kan motarsa yabar haraban gidan …..

Shiga ciki tayi tana kuku don bataso ko, kad’an taga ran Akram ya b’aci ita jitake aduniya zata iya sadaukar masa dakomai nata inde be sa6ama ‘adinin taba don taga farin cikin shi ganin kukanta ne yad’aga ma Mami hankali don bataso ko kad’an taganta cikin damuwa….

“Mamana meya faru naga kina kuka kunyi fad’a da Akram d’inne? “
Girgiza mata kai tayi Alamar a’a tak’i ta fad’a mata yanda sukayi da Akram..

“Mami pls don Allah kar arabani da ‘Akram wlh ina sonshi zan iya rasa raina inhar ban aure shiba… ” saurin rufe mata baki Mami tayi “dena kuka Mamana insha ‘Allah kamar kin aure shi kin gama Dad ,d’in ,naki meyace da shi Akram d’in?” Wlh nima bansan meyace ba” nandai maman tayi ta rarashin ta hartayi shiru..

Tow tundaga wannan ranar Akram be sake ,kiran Hajar ba kota kira baya d’auka , ita kuwa ‘abun namatuk’ar damun ta ,kwatsam rannan tana zaune taga shigowan text d’inshi kamar haka..

idan kin damu dani kizo adobayaro mall ki sameni

Agogon d’akinta, taduba taga karfe biyar harda minti biyu tunani tafarayi anyakuwa zata iya fita yanzu? Kuma tasan Mami bazata barta ba, Amman dole tasan k’aryan da zatayi kodon ganin Akram yadena fushi da ita, tashi tayi tasa rigan Abaya red tayi rolling black mayafi batayi wani kwaliya sosai ba ta d’auki hand back d’inta black da makullin motarta, tafito tayi d’akin Mami..

Zaune ta sameta, tana shan fruit da fara’a ta k’arasa inda take, ganin hannunta dajaka yasa Mamin b’ata fuska tace “ke kuma ina zuwa k’arfe biyar harda minti 9?” Murmushi ta saki tace “shoprite zani Mami yanzu, zan dawo, wlh bazan jimaba ” mezakije yi shoprite? “..

“Mami cake zan siyo kinsan gobe birthday d’in Dad so inaso inyi masa suprise da safe yana tashi ” hakane tow kin kyauta, kideyi sauri, kidawo kafun ya dawo gida kinsa dokar shice rashin fita at this time ” tsale tayi tace”thank Mami insha ‘Allah yanzu, zan dawo…

Muje zuwa fans

Shin me Akram kenufi dama antab’a aur ba’ayi bincike ba? Meyasa baya son ayi bincike? Meyake b’oye musu?

Yakuke jin buk d’in?

Sai naji comments d’inku zan cigaba

BY DIJA_WAZIRI🀞
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Sakonki ya Iso gareni baiwar Allah nagode da soyayya ‘Allah yabar zumunci ,kuma insha Allah zan k’ara yawan rubutun ,nima ina k’aunar ki😊❀❀

DAGA TAIMAKO

Sadnaf ina tayaki murnar kammala littafinki ubangiji Allah hasa mutane su amfana da’Abunda kika fad’akar, Ameen

Allah ya Kara miki basiri, muna jiran sabon, novel

Chapter 10

next day

11:30am

“Hajjo! Hajjo!! Tashi Dad ,d’inku na ,neman ki” cewar Mami cikin bacci ta mik’e tana sosa idonta ,”na’am Mami good morning?” Morning Dear kiyi sauri kije Babanku na, neman ki” tawuce tafita..

Itako Hajar mik’a tayi tareda lumshe idanunta ,tna salati don yau baccin yayi mata sweet, wayarta ,ta duba taga Akram yakira harso 5 nan danan hankalinta ,ya tashi tayi sauri danna number d’inshi takira bugu d’aya ,ya dauka.

“Hello Bee how are you” cewar hajar

“Fine sweety ,meyasa nayi takira baki dauka ba?”.

“Wlh bacci nakeyi sai yanzu natashi “..

“Ok tow ya kike i miss you kishirya zuwa anjima zamu fita “..

“Ina zamu? “.

“basai kinji ba kedai ki shirya kawai “.

“Tow zan tmby idan ,anbarni tow”.

“Tow yanzu idan ba’a barkiba shikenan bazaki ba ke baki iya irin k’aryan nan taku ta mata bane?”.

“Insha Allah ma za’a barni bye barin shiga toilet”.

Nan sukayi salama takeshe wayar tana murmushi tare da tunanin k’aryan da zatayi don abarta ,tafita ita shef tamanta ma Mami tace Dad na jiran ta sai a yanzu ta , tuna hijabi ta zura tafita ,tana fara’a

A falon sama ta gansu tarusuna har k’asa tagaida su cikin girmamawa…

Dad ne yayi gyaran murya ,yace “Hajjo !!” Dagowa tayi takalleshi tana wasa da yan yatsun hanun ta “Na’am Dad” saida yad’an yi shiru sannan yace “kina son yaron nan?” Kunya ce taji ta kama ta ,tasunkuyar da kanta ,tana rufe ,fuska..

“Kinyi shiru”Dad ya fad’a yana murmushi “tana sonshi tunda kaga har tana kulle fuska” Mami tabashi amsa tana dariya “tow kice yazo yau ina son ganinshi zuwa bayan magrib”, tow Dad zan gaya masa” sannan tamik’e tabar falon..

Koda takoma d’aki wayar ta, tad’auka takira ‘Akram ta sanar dashi abunda mahaifinta yace beyi musuba ya ‘amsa da zaizo yakuma shaida mata sunfasa fitar yau amman dai zasuyi..

Bayan salar magrib kamar yanda Dad yafad’a ‘Akram yazo amman saidai yau shigan k’ananun kaya ,yayi sunyi magana ta fahimtar juna da, Dad sanan ya shaida masa da yaturo magaba tansa ya kuma ‘amsa da tow (Tow fa wata sabuwa inji yan caca)..

Dad beyi wani bincike sosai akan Akram ba don shi dukya d’auka mutumin arziki ne daga ,ganin yanayin shigarsa da kuma ,magan ganun sa nanko besan duk siyasa bace…

“Musa kaji wata sabuwa kuma, mutaninan dagaske suke fa ” meya faru kuma ‘abokina ?” Wai naturo iyayena ‘ayi maganar aure nida bani da kowa ‘a k’asar nan ” dafa kafad’ar Akram Musa yayi ,yace”kwantar da hankalinka wannan duk me sauk’i ne kana da kud’i?”..

“Yes inada kud’i ,inada ,dubu dari biyu ,tow zan maka hanyan wasu mutane su aikinsu shine suje suyi ,iyayen k’arya abiya su kud’i” tow ni cewa nayi maka ‘auranta zanyi nifa ba sonta nakeyi ba jikinta kawai nake buk’ata”.

“Tow idan ka aureta kabiya buk’atarka basai ka saketa ba” kai No bazan iyaba ” tow zokaji inada shawara Musa yajawo shi ya rad’a masa ,tafawa sukayi Akram yace abokina ka iya plan yanzu yaushe zamuje wurin mutanen saimuyi ciniki muji nawa zamu biya su

      *****

“Wannan ae me sauk’i ne karku damu dayaushe kuke so naje? Akwai abokan sana’ata su ukku zan d’ibesu ,suraka ni “..

“Jibi nake son kuje “cewar Akram “tow Allah ya kaimu jibin ” .

“Ameen ,nawa zamu baka?” Cewar musa” kallon su mitumin yayi ,yana jijiga k’afa yace nera dubu d’ari shine kud’in aikina ,sannan kuma idan aiki yayi kyau zaku ,k’aran ,nera dubu sittin” zaro ido Akram yayi yace “dubu d’ari da sittin fa kenan zamu baka haba malam”..

“Gaskiya, yayi ,yawa inama laifin dubu d’arin ace duka” Musa yafad’a ,wani shi’umin ,murmushi mutumin ya saki yace”hakan shine sauk’i ” Akram ne yace “kayi hakuri mubaka dubu dari ” mek’ewa mutumin yayi ,yace “ba aikin ,kuke soba kuje kunemi dai-dai ,daku “harzai fita Akram ya tsaida shi.

Nan dai suka ‘amince akan zasu bashi yanda yabuk’ata inde aiki zeyi ,yanda suke so,

Akram ya kira Hajar ya sanar da ita cewa magabatanshi zasuzo tasanar da iyayenta, bayan kwana biyu sukazo akayi magana ta fahimta ,tare da saka ranan aure wata d’aya da sati d’aya ,don sunce basu ,so asaka ranar dayawa…

Akram duk yayi ‘iya buga ,bugan shi akan yasamu kud’in da zai sayi kayan lefe amman ina kud’i sunk’i shigo masa, haka daya rasa yanda zeyi gashi biki sai matsowa yakeyi sai ya ,yanke hukuncin gayawa Hajar abunda ‘ake ciki ,koda ya sanar da ita bata wani tada hankalin taba, tace zata saida gwala- gwalan ta da aka siya mata ,tabashi idan yaso saiya bata daga baya, dama k’arya ,yayi mata ‘akan yayi odaring kaya da kud’ad’anshi duk ,kuma basu isoba, ko za’a d’aga ‘auren ,itakuma ‘ayanzu bata da wani buri daya wuce taganta gidan Akram..

Koda ‘Akram yaji tace zata bashi ba k’aramin farin ciki yayi ba ,bayan sun gama da ‘Akram ne Khadee ke tmbyn ta “Amarsu mata ga Akram yau ko gobe wai me kuke tattau nawa da ‘angon ,nakine?” Hajar dake faman kwaso gold d’inta batace da Khadee komai ba saida ta gama kwasowa ta ajje su gaban Khadee sannan tace”muje ki rakani bakin asibiti” bakin asibiti kuma Hajjo kije kiyi me?” Zan saida gwala-gwalai nane” tana fad’a tana shirin zura hijabin ta da nik’af don ‘anfara mata gyaran jiki ,kuma bata son rana ya bigi fuskan ta, kamo hanunta Khadee tayi ,tace “meyasa zaki saida su Hajjo idan kud’i kike buk’ata kije gurin Mami ko Dad nasan bazasu hana kiba” hmm Khadee bazaki gane ba ‘amman bana fad’a miki dalilin dayasa zan saida kuma wannan sirine tsakanina dake “nan takwashe duk yanda sukayi da ‘Akram ta fad’ama Khadee ,ran Khadee a b’ace tace haba Hajjo ina kika bar hankalinki walahi karki ,kuskura ki fara wannan gangancin zakiyi rigreting nan gaba Hajjo namiji bad’an goyo bane kuma wannan zance kamata yayi ace Dad ,da Mami ya sanarwa bakeba wlh nifa tun sanda kuka had’u da ‘Akram jikina be yarda ,dashi ba gani ,nike ,kamar akwai abunda yake son yi mik……”

“Ya’isa haka Malama kar kuma kiwuce gona da iri kin gane kow ,Wai saunawa zan gaya miki ,Khadee bana son abunda kike min ya zaki dinga fad’an magana son ranki akan mijin da nake fatan ya zama uban yarana wlh zan iya Rabuwa dake akan Akram inde bazaki so abunda nake so ba ,idan zaki rakani tashi muje”.. Khadee sakin baki tayi ,tana kallon Hajar wai yau itace ke fad’i mata haka zata iya rabuwa da ita kan ,namiji lalle duk yanda ‘akayi Akram ya mata wani abu amman zata jenyi jikinta daga duk wani abunda ya shafi Hajar kuma bazata sake mata zancen shiba zata zuba musu ido ,azahiri kuma tace “kije bazan jeba” tana hawaye don furucin Hajar yayi mata zafi ,Hajar batace da ita ufan ba tawuce tabar d’akin itama jakarta ,ta d’auka tayiwa Mami salama sannan tabar gidan titi ,tafita tana ,neman adai-daita har Hajar tazo tawuce….

tow ,tundaga wannan rana Khadee bata kuma kiran Hajar ba kuma bata sake zuwa gidan ba itama Hajar d’in haka bata kuma kiran Khadee ba ,dayake Basmad tazo ita ke tayata shirye shiryen biki..

2 million Hajar ta rantawa ‘Akram tare da ita sukaje tazab’i duk abunda take so yabiya ‘akwati dozin yayi mata(12) kowane anzuba kaya masu d’an tsada ,da kuma kyau , ko ranar da za’a kawo lefe saida Basmar ta ,tambayi Hajar ya bataga Khadee ba ,Hajar tace itama batasan dalilin dayasa batazo ba….

Hajar dai sai hidimar biki takeyi kud’in komai Akram ne yabada ,daga gyaran jiki ,kunshi kitso , lalle dadai sauran su ,

Yau saura sati d’aya bikin Hajar mahaifinta yayi ,tafiya London amman kafun bikin zai dawo gidan ba’a fara cika ba sai a wannan satin mutane ,nanesa zasu fara zuwa yanzu ,daga k’annen Mami sai yaransu sune kad’ai agidan….

 FRIDAY 

4:50PM

Hajar da Basmad ne zaune cikin gardin d’in gidan suna ,tattau nawa ‘akan inda za’ayi bridel shawa, wayanta ya fara ,ruri da sauri taduba ganin Akram ne yasa tayi saurin d’auka ,daga b’an garan shine yafara magana…

“Hllo my wife how are you?”

Cikin shagwab’a Hajar tace “fine my husban i miss you 2 days bamu had’uba “..

Murmushi yayi tare da cije leb’en k’asan bakinsa yace “wlh aiki ne yamin yawa ‘a kasuwa kinsan kayana next week zasu iso ,so muna ta shirye shirye ,yanzu kishirya zuwa k’arfe biyar zan kaiki gidanmu ,mama tun next week tace na kaiki wlh ban samu time ba sai yau”

Saida tad’anyi jim sanan tace “tow saikazo barin sanar da ,Mami” sukayi salama takashe wayar..

Kallon Basmad tayi ,tana murmushi tace ,ke Basmad kinji wai Akram yace nashirya zamu gidan su Maman shi tana son ganina zaki rakani?” Kai gsky ban zuwa ‘anjima nima ,mijina zaizo kuje kawai” tab’e baki tayi tace karki raka d’in muje ki zab’an kayan sawa”..

Nan suka tashi suka shiga ciki ,koda Hajar tafad’a ma Mami cewan zasu gidan su Akram bata hanata ba ‘amman tace karsu jima kuma tayi mata nasiha kan takama ,mutuncin ta, Hajar tana murna takoma d’aki tayi wanka tasa wani riga da zani ,na supar kayan sunyi mata kyau sosai batayi kwaliya ba powder da lipstick ,kawai tasa tayi kyau sosai ,k’arfe biyar da rabi Akram yazo suka tafi….

Kuyi hakuri da wannan

BY DIJA_WAZIRI🀞
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 9

wurin motarta, tanufa tana fita da k’arfi taja motar cikin sauri tabashi wuta ,don bata so tajima,

Bata wani jimaba ta isa cikin shoprite ,tashiga zaune tasameshi ,shida ‘abokinsa suna hira ga dukan Alamu ita suke jira ganinta ne yasa ya tab’a ‘abokin nasa ,sannan yayi masa nuni da ya kalle ta “kagani angaya maka nid’in, nawasa ne daga kiranta hartazo ” Akram yafad’a yana shirin tashi, ita kuwa tahowa tayi tana murmushi me k’ara fito da ‘ainahin kenta..

Hannu ya ware mata ‘alumun tazo, ganin hakane yasa ta, tsaya turus tana kallon shi, takasa motsawa daga inda take, k’arasowa yayi har inda take ya rungumeta kamar wata, matarshi, kasa cemasa uffan tayi saida suka, kai kusan minti biyu a haka sannan tayi saurin kwace jikinta, tana “Beby miye haka, kuma karfa ka manta niba muhara marka bace” had’e rai yayi, yace “tow miye don kawai nad’an rungumeki yau kawai lalle ashe nikadai nayi missing d’inki ba komai ” yajuya zai tafi sauri ,ruk’o hanunshi tayi tana bashi hakuri”sorry Beby wlh nima nayi missing d’inka more than yanda bakayi tsamani ba kawai dai gani ,nayi hakan dakayi min be daceba ‘Amatsayinmu na yayan hausawa kuma ,musulmai”.

Dakatar da ita yayi “ya isa haka bance kinmin wa’azi ba ” yaja hanunta suka wuce cinima tare da yiwa ‘abokinshi sigina ‘akan ya biyosu, daman yariga ya biya komai popcorn kawai suka, karb’a suka wuce ,ciki cen k’arshe sukaje suka zauna gashi wurin Ankashe wuta hasken tangamemen Tv d’in dake cikin wurinne ke haskawa ,wani sabon film suke ,kallo amercan film ,Akram har’a lokacin be sake mata hannu ba saima k’ara matsota da yakeyi ganin hakane yasa tafara matsawa baya don duk a tsorace take ,neman fisge hannunta ,tayi daga nashi, amman dayake yarik’eshi gam saita kasa daidai setin kunne ta yaje jikinsu haryana gogan juna yace” haba Sweety sai kace wata Villag girl miye hakan kikeyi mutani fa na kallon ki “.

Itadai babu abinda take fad’i sai ,inalilahi wa inna ‘ilaihi raji’un ba’abin ta fisge jikinta ,tafiba kuma yaji haushi ,dama tasamu sunshiya ,yau tana tsoran k’ara b’ata masa rai gashi bataso taga ranshi ya b’aci saboda ita soyayya tarufe mata ido ,sam bata ganin laifinshi ko ,kad’an duk irin salon iskan da rashin mutuncin da yake mata ita ,tanaganin son dayake matane yasa haka, Khadee tasha mata ,magana ‘Akan tarabu da ‘Akram ba mijin aure bane don duk namijin da zai nemi ta’ba jikinki, kai koda hanun kine idan yana da wannan halin tow ki gujeshi domin shai’dani ne ko kuma kitsayar masa koda hakan zeyi sanadin rabuwan ku, amman sai Hajar tanunu b’acin ranta don ita tariga da tayarda ,da ‘Akram bazai tab’a cutar da itaba ..

Agogon dake hannunta ,taduba taga 6 harda minti 59 an kira sallar magrib ,kallon shi tayi a marairaice tace Beby 6 tawuce fa katashi mutafi bana so Dad yadawo ya tarar bana gida ” k’ara jawota jikinshi yayi ,yana shafa yan yatsun hanunta “kibari sai 8 akwai Film d’in da zamu kalla yanzu ma waihar kingaji da ganinane?” Girgiza kai tayi tace no Dad ,da Mami nake tsoro karsu min fad’a ” Akram ya balain tsanar Mahaifin Hajar shi tun tmbyoyin da yayi masa yasa yaji duk ya tsaneshi a hasale yace”sai kace wata Beby suyi tamiki kulle bazasu barki ,kiyi enjoyed life d’inki ba haba niwala banson takura” Hajar naji zafin yanda yake gayawa iyayenta magana son ransa Amman da yake soyayya ta rufe mata ,ido bata iya cewa dashi uffan,( kaico Allah karka samana irin wannan gurb’a taciyar soyyar cikin zuciyar mu dahar zaisa mu mance dakai muyi son zuciyar mu)..

Hakadai basu ,sukabar gurinba sai k’arfe bakwai da kusan minti 25.

Ya yan uwana mata wanda basuyi aureba muji tsoran Allah kafin ki zab’i mijin aure yakama kifara yiwa kanki tambayoyi

Shin zaki so ache wannan saurayin da kike so shine Uban yaranki ? Kuma zakiyi alfahari aduniya da lahira idan kika haifi yaro mai irin halinsa da yanayinsa?

Kuma wannan saurayin yana da halaye irin na tsoran Allah? Yawan tuna Allah ,kiyaye dokokinsa bin umarninsa ,yin abu don neman yardar sa.

Idan ya zama mijinki zaija ki zuwa ga Aljannah ne, ko kuwa zuwa ga ‘Azabar Allah?

Ya mutunta Mahaifansa da yan uwansa mata? Idan har yana mutuntasu to zai mutunta naki .idan kuma yana wulakantasu to kema sai ya wulakanta naki.

Yana miki zancen batsa awajen hirarku ? Ko kuma yana kokarin tab’a jikinku ? Idan yana da wannan halin to ki gujeshi domin dan iskane bake yake soba jikinki yake buk’ata.

Yaya tarbiyyar gidansu take ? Idan gidansu akwai tarbiyya to zakiga Alama

Nasiha ce ubangiji kasa mufi k’arfin zuciyoyin mu ka shirya mana zuri’armu , ka tsarkake mana zuciyoyin mu da aikata ‘aikin da bashi da kyau ka ,karemu da dukkan kariyan ka ,karabamu da sharrin mutun,(mutun mugun icene) kasa mugama da, duniya lfy Allah karka bamu ikon sab’awa mazajen da zamu aura Allah kasa mukai budurcin mu harcikin gidan auren mu ka karemu da duk wani me mugun nufi agaremu Allahuma ‘Ameen..

“Kai Burina yakusa cika hak’ata ,yakusa cimma ruwa, itafa dukta sakankan ce dagaske sonta nake” kai Akram wlh baka da kyau wlh arayuwata ban tab’a ganin dan iskan mutun irin kaba, kamaida mata bakomai ba kamaidasu kamar ,ruwan sha” tafawa sukayi Akram yace “kana wasa dani Baba kaga nifa bansan kowa ‘a k’asar nan ba dana cika burina zan ware bakuma zan sake dawowa ba”..

“Dan duniya zaka ,koma indai kenan ,kaje kayi tacin yaran jam’a ” kai kuma wannan ya dama barin gaya maka tarihina kad’an duk da ni banyarda ,da kainaba barena yarda ,dawani amman barin gayama waye Akram a k’asar India , tun ina d’an shekara 15 nake lalata yaran mutane ,natashi a gurin Mahaifiyata ne bansan waye mahaifina ba, don ina kyautata zaton ,ni shegene bada’aure aka sameniba saboda Mahaifiyata ,tantiriyar karuwa ce har gidan karuwai gareta ,tun inada shekara goma ‘aduniya nake ganin mahaifiyata nakowo maza cikin gidan mu , kuma ni tatacen mashayin giyane arayuwata ban ta6a yin aikin alkairi ba ,dawayona ban ta6a dungura kaina daniyar zanyi sallah ba ,natashi cikin k’azan taciyar ,rayuwa” dafa kafad’an Jabir yayi wanda tuni yayi mutuwar tsaye yace “idan ,natsaya baka lbrn rayuwata saika ce Allah wadai da wannan rayuwa don babu abun Alkairi ko d’a ‘aciki,

Daga haka be kuma cewa uffan ba sai sigari daya kunnan ya fara zuk’a tare da ‘Alwashin bazai wuce wannan watanba zai k’arbi abunda yake buri daga Dr Hajar yayi tafiyar shi don yagaji da zaman ,najeria, shiko Jabir jinjina kai yayi dajin batun Akram sai yaga duk iskancin sa kafara ce akwai wanda yafisa duk da shi be tab’a having sex da maceba sai ,saud’aya(kaico Allah karabu da uwa irin wannan don gara tamutu da nazama dan karuwa ) cewar jabir..

“Kin ,kyauta Hajjo yanzu da ‘ace mahaifinki yadawo sanda ya saba dawowa da shikenan kinjamun magana kow? Waima ,mekika tsaya, yine daga kije ki dawo?” Mami ta ,tsareta da ido itakuwa cikin rashin gaskiya ta fara sosa keya tama rasa ‘abun cewa saicen dabara tazo mata, tace ” kiyi hakuri Mami wlh trapic ne yarik’e ni”. Duk da Mami bata son ganin b’acin ran d’iyar tata haka ta dake cikin masifa tace” karki raina min hankali goslow dinne wurin 3 hours kije ae akwai gobe ” tayi wucewarta falo tabarta ,tsaye wurin stairs nata hawaye…

Koda takoma d’aki abubuwan daya faru tsakaninta da ‘Akram ,ne suka fara dawo mata sai’a lokacin tafara nadamar abunda tayi tare da ‘alwashin bazata kuma barin hakan yafaru ba yau d’inma hudubar shedan ce

BY DIJA_WAZIRI🀞
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Kowace mace bata so ace tayi aure tafito ,sannan ko wace mace takanso tayi Alfahari da uban yayan ta ‘asameshi mutumin daya had’a ‘abubuwa guda uku

Yar uwa kifara duba wad’annan abubuwa guda ukun a halayyar wanda kikeso yazama mijinki, nad’aya ,Amanarsa, Adininshi, Gaskiyarshi

Mata a mafi yawan lokuta basa ku6uta ,kullum k’ok’ari ake aliqa musu laifi

Zata zauna a gida ta nutsu da kyawawan d’abiunta ,tana jiran Allah ya kawo mata mutum na gari .sai wani yaxo yayi mata kalamai da ,dad’in baki har ta yarda ,dashi ta bashi soyayyarta ya b’ata mata lokaci kai wani ma ya b’ata mata rayuwa, sannan ya gudu ya barta, ya ,yaudareta, maza tsoran Allah

saniha ce

MEBAK’IN JINI

Congratulations for the successful completed ur fantastic novel mebak’in jini ,sis Ayusha Allah ya saka maki da ‘alkairi ya k’ara basira, da ,d’aukaka Allah yasa mutane su anfana da ‘abunda kika fad’akar

Muna jiran sabon ,novel😍

Chapter 11

Tafiya suke Hajar taga tafiya tak’i ,k’arewa , gashi kuma takasa masa magana ,saida taga sunyi hanyan TAHIR GEST HOUSE sanan tayi magana “Akram wai ,inane unguwar taku ?” Ita yau haka ,kurum hankalinta yak’i ,kwanciya dashi sai take jin kamar wani abu zai faru ammansaboda so yarufe mata ido sai tayi saurin kauda tunanin, yana murmushi yace “sorry dear namanta ban sanar dake zan d’auki wani abokina dayazo daga Uk jiya ba ,d’aukan shi kawai zanyi saimu wuce ” tow pls muyi sauri don bana son kaiwa dare bayan magrib zanjegidan friends d’in Mami zan kaimusa iv kasan bikin yazo saura 5 days”..

Murmushin da baikai zuci ba ‘Akram yayi tare da cije leben saman bakinshi yana girgiza kai alamun mugunta yace”ae ni harna k’osa akaiki gidana don hakurina ya kusa k’arewa ina so inji d’umin matana.”

Rufe ,fuskar ta, tayi alamun kunya tace “ae kamar yau ne mekake ci nabaka nazuba”, horn yayi aka bud’e masa tanga memen get d’in Tahir yashiga yayi parking ,wayan shi yaciro yayi dailing wata number, bugu d’aya ‘aka d’aga …

“Hello kagama komai gamu ,mun iso?”..

“Yes sir komai yayi dai-dai zaku iya zuwa”..

“Okey gamunan “yakashe wayan tare da kallon Hajar yana ‘aika mata da wani shi’umin murmushi yace fito muje ” A’a kaje kawai ,ina jiran ka ” haba dear sai kace wanda zai cutar dake ,kamar baki yarda ,dani ba Restaurant d’incen zamu shiga mu d’ansha wani abun kafin ya fito”.

Itadai Hajar hankalinta ba’a kwance ba tafita suka shiga ,suna zuwa ‘akram ya umarci waiter d’in daya kawo musu pizza da drink ,hakan ,ko akayi bejima ba yakawo musu moltina na gora ‘Aka ,kawo ma Hajar don ita shik’adai tafi so ,zata saka hannu tabud’e akram yayi saurin d’auka yana dariya”nizan bud’e miki bana so kisha wahala”, itadai ,dariyan yake ,kawai takeyi “..

Yabud’e yazuba mata ya ‘ajje harya kusa cenye pizzn shi Hajar bata ,tab’o komai a gurin ba “Sweety meke damunki tunda muka shigo naga dukkin cenza ,kamar akwai wani abu” dariyan yak’e tayi tace”babu komai kaina ke ciwo “eyyah sorry bari ,idan munfita saimu tsaya ‘musai magani kisha molt d’in mana ga pizzan ,ma koci bakiyi ba” nak’oshi da pizzan molt d’in kawai zan sha, d’auka tayi ,takafa ‘abaki tafara sha ,saida tayi kurb’a ukku ana hud’un ,ne taji test d’in ba’irin ,na moltina ba kantane taji yafara juyawa ,shiko Akram dake ,kallon ta yana cije leb’e yace “Hajjo” d’agowa tayi tana kallon shi ,shima taga yafara zama ,mata biyu dak’er ta iya cewa na’am “zomu tafi ” ,yamik’a mata hannu itama hannun ta mik’a masa don jitake ,kamar zata fad’i..

Suna fita mai makon suyi mota sai suka ,shige cikin tahir d’in yana shiga dama oredy ,yana da key d’in room d’in daya kama ,dakine madaidaici me shegen kyau da toilet yasha jen carpet da italiyan bed sai wani royal chair guda d’aya dogo da table sai k’aton tibin bango d’akin dai yayi kyau sosai sanyi ac ne kawai ke tashi da k’amshin turare me dad’i suna shiga Hajar ta fad’a kan gado tafara bacci dama tajima dafita hayacin ta, shiko Akram rufe k’ofar d’akin yayi da key…

“Khadee kinban mamaki yanzu har akwai abunda zai ,iya suku fad’a keda Hajjo duk irin abotar dake tsakanin ku tun kuna yara , amman ace wai yanzu kunyi fad’a ,kinga ‘ae yanzu mutanen da ,dama bason ganinku tare sukeyi ba dad’i zasuji wasu kuma suyi muku dariya”.

“Mama nifa bawai munyi fad’a bane ,abunda ya k’onan rai shine wai zata iya rabuwa dani donna fad’i mata gsky akan mijin da zata ‘aura , kuma wlh Mama yaron bason tsakani da ‘Allah yake mata ba ,tun daga yanda take bani lbrn shi nagane amman ita so yarufe mata ido “, tow basai kibita da’ addu’a ba kuma datace zata ,rabu dake ,kan mijin ta ‘aeba laifi tayiba kece kikaja ,yanzu kitashi kije gidan ,nasu ku sulhunta kanku ,kuma kicigaba da tayata hidimar auren ta” tow Mama zanje bari ,idan anyi magrib sainaje da motar ki ,idan ya kamal yadawo kuma saiya kaini” yawwa koke fa ‘Allah ya miki albarka ya k’ara kare mun ku daga sharrin mutun da ‘Aljan ya baku mazaje nagari musu ,sonku da gsky ba’abun hanun kuba ,ko ,kuma jikin ku” Ameen Mama barinje kar girkina ya k’one”.

Akram yana rufe k’ofar gyarawa Hajar kwanciya, yayi ,yafara ,rabata da kayan jikinta , saida ya gama tas ,sanan shima ya kafa ,rage najikinsa..

Niko dija tsabar bak’in ciki ban iya tsayawa kallon takaici ba na bank’o musu k’ofa nafice

Subhanallah

Maza!! Aji tsoran Allah Wlh duk wanda ya bata diyar wani sai Allah ya tambaye shi kaima zaka haifa bazaka so ayiwa naka hakan ba

Inna lillahi wa-inna ilayhi rajioon Allahumma-jurnee fee museebateen wakhluf lee khayran minha, shine abunda take ,ta maimai tawa yayin data farka taga jikinta ,ko kaya babu gashi kafafunta sunyi mata nauyi , kukata ,take me tsuma zuciya ,tare da tunanin mezata cewa iyayenta ,Khadee ce ta fara, fad’o mata ‘arai cikin sauri ta d’auki wayanta ,tana kuka takira Khadee tace tazo ,ta sameta, Khadee dake hanyar zuwa gidan Su Hajar bata san sanda ta juya kan motar, taba zuwa Tahir ,don yanda taji muryan K’awar tata kuma taji tana kuka tasan akwai matsala, tafiya take tana tunanin meyakai Hajar Tahir ?.

Hajar dak’er tamik’e, kasa tsayawa tayi ta koma kan gadon tazauna tana d’irkan kuka tare da nadamar fitowa da tayi, yau, bata kuma shiga tashin hankaliba saida taga takardan da ‘Akram ya rubuta ya ‘ajje mata, tana gama karan tawa tayanki jiki tafad’i sume …

Khadee ko sauri take zubawa, tayi ta isa aiko bata jimaba ta’isa karfe takwas da kusan min shida, dak’er suka barta, tashiga, tana shiga ta fara, raba ido tarasa wani daki zata shiga gashi takira wayan Hajar baya shiga, rufe ido dai kawai tayi tabude room 19 takoyi sa’a shine wanda Hajar ke ciki.

Yanayin yanda taga Hajar d’inne yasa ta fasa ihu “inna lillahi wa -inna ilayhi rajioon Hajjo! ” ta matsa kusa da ita, tana jijiga ta, Hajar ko motsi batayi, d’aura hannu Khadee tayi aka tana kuka tace”shikenan ya kashe ta wayyo Allah nashiga uku dama ‘abunda nake gudu kenan gashi ya ‘afku shi kenan ya kashe mana Hajjo ni Khadee ina zansa kaina ta ina zan fara yiwa su Mami bayani, Akram kacucemu Allah saiya saka mana “, Khadee bata kuma shiga tashin hankali ba saida taga jini ,jikin zanin gadon da hajar ke ,kwance , Hannu takuma d’aurawa ‘akai tace “shikenan ya rabata da budurcin ta ya ruguza mata rayuwan ta Inna lillahi wa -inna ilaihi rajioon “.

Khadee ,dataga kuka bashine mafita ba tayi saurin sakawa Hajar kayan ta, takira mutane suka taimaketa ,suka fitada ita mota ,bayan takai Hajar mota ,tadawo ta d’auki takardan data gani kan gadon ,sai taje ,jikin motar bata shigaba tafara duba ‘abunda ke rubuce ajiki ,kamar haka.

Hello my love kin yarda dani, kamar yanda kika yarda ,da iyayen ki ,kin aminta dani ,ina sonki Hajjo i love you so much Amman bazan iya zama dake ba domin bazan tab’a ganinki da , daraja ba ,bazan tab’a ganinki da k’ima ba ,ba kece mace tafarko dana gudu na bariba sunada yawa nariga na biya buk’atana ,don haka kije ki nemi wani mijin kiyi aure domin ,namiki nisa bazaku ,kuma jina ko ganina ba, dama ni bake nakeso ba jikinki nakeso kuma na samu

Dun k’ule takardan Khadee tayi da hanunta ,tana kiran sunan Allah tana hawaye, shiga motar ,tayi da mugun gudu bata tsaya ko inaba sai Aminu kano ,da tayi tunanin ta kaita Hajar hospital sai kuma tafasa, suna zuwa doctor ya karb’eta da gaggawa ‘aka shege da ita wani room aka samata drip tare da yimata wasu yan gwaje gwaje ..

   *******

“Mami Hajar fa haryanzu bata dawo ba gashi har 10 tayi ” what kina ,nufin tund’azu bata dawoba? ae ni ,nazaci tadawo shiyasa banyi magana ba ” wlh bata dawo ba kuma tun d’azu nake ,kiran wayan ta ‘akashe , ” tow anya lfy kuwa karfa yaron ,nan ya sace mana yarinya” Maman Basma tafad’a tana shirin d’aukar mayafin ta “nashiga Uku Asma’u mezan cewa mahaifinta wlh saida ya jadadda min akan indena barinta fita ,nikuma gudun b’acin ranta yasa duk sanda ta ,tambaya nake barin ta ” wannan duk bashi bane abunyi Aunty Faty Basma kiramin Kalifa” Maman Basma tafad’a . Itama ,Mami ,mayafi ta d’auka tare da wayan ta ,duba wayan da zatayi taga Khadee tayi mata 10 miss call ,cikin sauri takira ,taji wayan yak’i shiga “Usma’u kinga k’awarta ,takira harso goma gashi yanzu nakira wayan baya shiga ,wai meke faruwa ne?”Aunty Faty mutafi neman Hajjo bani da ‘amsa nima, sun sauko daga stairs kenan sukaga Maman Khadee aburkice yanayin yanda ,suka gantane ya kuma tada musu hankali “lfy Hajiya Luba ?” Balafiya ba Haj Fati Hajar na ‘hospital Nima yanzu Khadee ke sanar dani ,ita ,tace na zo nasar daku wai takira wayanki bay…..”

Kafun Haj Luba ta ida zancen ta Haj Faty ,tace “nashiga uku meya sameta ?” Wlh Khadee tak’i sanar dani don ,naji ,itama kuka takeyi muryan ta harya dashe suna ‘Malam Aminu kano ” nashiga uku meyasamu Hajar d’ina ‘Allah yasa ba hatsari sukayiba mezan cewa mahaifinta ? Idan hakanne yafaru Luba don Alkah kira min Khadee” .Haba Aunty ki dena kuka ,kuma kidena fad’in haka muje ” cewar Haj Asma’u ,duka suka d’ugun zuma suka tafi me aiki kawai aka bari

BY DIJA_WAZIRI🀞
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Nasiha zuwa ga yan uwana mata,

Da shaitanun samari da miyagun qawaye ,ki guje musu fiye da yadda zaki guje ma kura ko zaki..Domain hakikanin hallakar da suke tare dasu yafi na kura da zaki.

Wani lokacin zaka ga yarinya mai cikakkiyar tarbiyya ‘amman shaitan ya chusa mata soyayyar wani shaitanin saurayi..Ta dalilin haka har sai ya lalata tarbiyyarta ,ya jefata cikin ramun zina. Wani lokacin kuma kina tare da tarbiyyar nan mai kyau wacce iyayenki da malamanki ,suka sha wahalar d’oraki akai, sai wata qawarki ta nuna miki cewa wannan ba shine wayewa ba.. Da sannun idan baki rabu da ita ba sai taja ‘akalarki zuwa ga abinda zai kaiki har wutar jahannama

Allah ka,kiyaye mu da k’arfin ikon ka ,kasa mufi k’arfin zuciyar mu

Chapter 12

Su Mami sun isa ,wurin k’arfe 10:55 Amman basu ,samu ganin Hajar ba don ,Doctor yace abarta ,tahuta hankalinta yadawo jikinta ,tukun ,don har alokacin bata farfad’o daga ,dogon suman datayi ba , Mami duk ta k’osa taji abunda ya samu d’iyar tata ,gashi tunda suka zo suke neman Khadee basu ganta ba , zaune suke gabaki d’ayansu ,sunyi jugum -,jugum kowa da ‘abunda yake sak’awa Khadee ce ta nufo inda suke zaune da taga hankalin su baya kanta ,tayi saurin jan Basmad suka shiga wani d’aki, dake ,kusa da gurin,

Yanayin yanda Basmad taga Khadee ne ya k’ara d’aga mata hankali , idanunta sunyi jazuri kamar barkono lokaci d’aya tacenza fuskarta duk akunburu “Khadee lfy wai meka ,faruwa ne don Allah kisanar dani meya samu Hajar?” Khadee ,dake faman zubar da ruwan hawaye muryan ta ‘adashe tace Akram! Akram!! Kasa furta ‘abunda zatace tayi ,takuma fashewa da wani sabon kukan, Basma ,ma kukan tasomayi dama ita ‘akwaita da saurin kuka ,k’arasowa tayi kusa da Khadee ta rik’o hanunta “me Akram d’in yayi don Allah Khadee kidena kuka ,kisanar dani “.

Tsayawa da kukan ,Khadee tayi ,saida ta d’an tsaya nawasu mintuna sannan taja wani kujera dake ajje kusa da ita,tazauna ta fuskanci Basmad tafara magana “Abunda nake gudu yafaru Basma ninaja wlh ninaja da banyi fushi da Hajar ba da ,duk haka befaru ba ,Basma ,tayaya zan tunkari su Mami da wannan maganar ? taya zan dubesu na sanar dasu abunda yafaru da Hajar ? Wlh natabata da suji wannan labarin gara suje labarin rasuwan Hajar wlh ba laifin ta bane ,ba halin ta bane ni ,nasan Hajar d’ina bahaka takeba sharin shed’anne da kuma k’addara ,Hajar bazata ‘aikata haka ba da gangan wlh ” Khadee kinfa sani aduhu kifad’a min ,meya faru ?” Kallon ta Khadee tayi ,tace Akram ya raba Hajjo da mutuncin ta ya gud….”

Kafun Khadee ta gama ida zancen , Basma ta kwala uhu tare da fad’in “inna lillahi wa-inna ilayhi rajioon ,k’adarucali wama sha’a fa’ala fassara, ” sauren goge hawayen idon ta ,tayi “Khadee ,dana sani k’eya ce wlh danasan abunda zai faru da ban ,bar Hajar ta fita ita kad’ai ba ,saida tace na rakata nace A’a suje , Haka Allah ya k’addara ” tow yanzu miye abunyi Basma taya zamu tunkari su Mami da wannan bak’in zancen “Khadee ta,tambaya ,yayin da ta ,tsagaita da kukan ,nata “mamana zamu fad’a wa ita zata san yanda zata sanar da Mami” nan dai suka share hawayen su ,suka fita suna fita Mami ta ,tunkaro su tana hawaye ganin yanayin su yasa tayi turus tana kallon su, Aunty Asma’u ce tace “Basma ,meya sameku naganku zuru -zuru kuma ga dukkan Alamu kunsha kuka ?”.

Khadee ce ta k’ak’alo murmushin da bai kai zuciba tace”Babu komai Aunty Asma’u”tow meyasa naganku duk wani ‘iri wai meya samu Hajar?” Kallon juna sukayi Khadee ,da Basma suka had’a baki sukace”wlh muma bamu sani ba Doctor be sanar ba tukun” Aunty Asma’u ta rabu dasune kawai badon ta yarda ba ta kama Mami suka nemi wuri suka zauna, suma gurin suna ,nema suka zauna kowa da ‘abunda yake sak’awa Khadee tana son ta sanar da Mamanta ‘Amman kuma suna tare da Mami Basma ,ma tana so ta sanar da ‘Aunty Asma’u duk sun rasa yanda zasuyi,

“Mommy Doctor yace kije” cewar Basma d’agoda Aunty Asma’u tayi ,tace “meya faru ?” Wlh nima ban sani ba yace kije dai kawai ” mik’ewa tayi zata,tafi Mami tayi saurin rik’e hanunta ,tana fad’in “tsaya muje tare” A’a Aunty bari naje nik’ad’a Aunty Luba kizauna da ita”, da k’er dai Aunty Asma’u ta rarashi Mami akan tazauna suje sudawo , koda suka tafi mai ,makon Aunty Asma’u taga sun shiga offce d’in Doc..sai taga sunyi wani d’aki ,Khadee tagani a zaune tana jiransu ganin shigowan sune yasa tayi saurin mik’ewa tana hawaye…

Khalifa kuwa dayaga Mami sai kuka takeyi sai ya ,yanke hukuncin kiran Dady ,yasanar dashi halin da ‘ake ciki, mik’ewa yayi ,yabar wurin dede kofar d’akin da su Basma ke ciki yaje ya jingina don yaji dad’in kiran Dady ,ya sanar dashi ,be k’arasa lalubo number d’in Dad yaji hanunshi ya fara ,rawa lokacin da yaji furucin Khadee na k’arshe be san ,sanda wayar ta zame a hanunshi ta fad’i k’asa ba , dai -dai lokacin sukuma suka fito daga cikin d’akin Aunty Asma’u na share kwalan idon ta ,kallon Kalifa sukayi gaba d’ayansu a tsorace Aunty Asma’u tace “Kalifa me kakeyi anan wurin kuma?” Kasa boye damuwarsa yayi ,yace Dady zan kira na sanar dashi abunda ke faruwa” kama Hanunshi Aunty Asma’u tayi tace no karka ,kirashi kuma nasan kaji duk abunda su Khadee suka sanar dani hakuri zamuyi tunda ‘aikin gama ya gama “Aunty Asma’u wlh da zanga yaronan dasai na kasheshi dama nifa tuncen bana sonsa yanzu gashi ya zubar mana da mutunci da k’ima kuma waya sani ma koya kasheta ,tunda haryanzu bata,tashi ba ” kadena fad’an haka ,Khalifa insha ‘Allah zata ,tashi da izinin Allah “..

Da suka ,koma wurin da su Mami suke zaune Aunty Asma’u kasa ,sanar da Mami tayi, saidai ,idan takaleta sai taji tausayinta ya kama ta ,tafashe dakuka ,wannan wace irin bak’ar kaddara ce mara dad’in sauraro yanzu me za’a cewa mutanen da suke shirin zuwa biki me za’a cewa Dad? Yanzu haka za’a ce masa yaron ya fasa kuma ya lalatawa yarsa rayuwa koko cewa za’ayi ,ya gudu ya barta ? Yanzu idan ,nasanar da ‘Aunty halin da Hajjo ke ciki ya zatayi? Ni Asma’u taina zan fara ?meke shirin faruwa da family d’inmu ? Haka ‘Aunty Asma’u ta d’inga jerowa kanta ,tambayoyin da bata da ‘amsa ,su, tana cikin tunanin ,ne taga Doc…yafito da sauri yayi d’akin da ‘aka kwantar da Hajar ,suma ‘mara masa baya sukayi gaba d’aya suka bishi d’akin..

Ahankali take bud’e idon ta, tana bud’ewa ta sauke su kan Doc..amman ita ba fuskarshi take gani ba fuskar Akram take gani, da sauri ta mik’e ta cakumo kwalan Doc..”tana ‘Allah ya isa tsakanina dakai, shega d’an iska ,mayau dari Akram kacuceni, ka wargazamin farinciki na , ka b’ata… “Kafun ta k’arasa Khadee tayi saurin toshe mata baki ta jawota daga rik’on da tayi wa Doc….”likita don Allah kasanar dani meke faruwa da ,diyata ? Meyake shirin faruwa damu? Me Akram yayi mata” karki damu Hajiya ta tsorata ne dayawa ina mijin ,nata yake ?”..

“Miji kuma Doc…?bata da ‘aure nice mahaifiyar ta” a razane Doc…ya kalli Mami yace bata da ‘aure ?” Eh bata da ‘aure meke faruwa?” Hajiya….” karka sanar da ita Doc..idan ma za’a sanar da ita bayanzu ba mubari saita nutsu”Aunty Asma’u tayi saurin tsaida shi tana hawaye , “ban gane sai na nutsuba? kufad’a min meke faruwa da ,diyata karkuce abunda nake tunani gsky ne ?”…

“A irin wannan zancen ba’a b’oyewa Hajiya ‘sai dai kiyi hakuri Amman abunda kike tunanin shine dai” Doc…yafad’i yayi saurin barin d’aki “inna lillahi wa inna ilaihi rajooun Allah menayi maka ,kajarabceni ta wannan hanyar Allah na tu…..”kafun ta k’arasa ,sai jinta sukayi luuu a k’asa nan danan kowa ya ,yo kanta….

K’arfe hud’un dare Mami ta farfad’o ,kasa had’a ido sukayi da Hajar don haushin Hajar d’in takeji ,gani take da saninta hakan yafaru ,ita ,tunanin yanda zata ,tunkari mahaifin su tasanar dashi tafara yi nadama ce far cikin zuciyarta ,da ,dana sani barin Hajar fita ,Mami takira mahaifin Hajar ta shaida masa cewa ‘Akram ya fasa ‘auren Hajar Amman bata sanar dashi abunda ya faru da ita ba …

Dad ba k’aramin bak’in ciki yayi ba ,ya kira duk abokansa daya bawa Iv ya sanar dasu anfasa ‘auren Hajar kowa beji dad’in hakanba , Hajar saida tayi kwana biyu a hospital sanan aka salamesu ,Khadee gidan su Hajar ta,tare wai sai tadawo dai-dai tukun takoma gidan su Aunty Asma’u ma tatafi ,tabar Basma idan yaso tazo daga baya, Mami kuwa babu abinda yake had’ata da Hajar Kakar su Hajar kam batasan komai ba itadai taji cewa ‘anfasa ‘aure..

BY DIJA_WAZIRI🀞
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 14

Cikin falon ta shiga ta zauna tana wasa da k’asan hijabin ta, su Mami kuwa yi sukayi kamar basu ganta ba, “Dady Mami barkan ku da yamma ina wuni” ta furta yayin da take kwala, Dad ne yayi k’arfin halin amsawa “lafiya” sannan ya mai da kansa ga tv, “Don Allah Mami kuyafe min ,natufa wlh ba laifina bane wlh ban san haka zata faru ba ,don Allah kuyafe min kudena fushi dani wlh bani da laifi , Dad kuyafemin kozan samu sassauci a rayuwa ta ko zan d’anji sanyi azuciya ta fushinku hatsarine a gareni ,kuyi hakuri ” tana kuka me ci da zuci take rok’on iyayen ,nata ‘amman ko juyowa su kalle ta basuyi ba ,bare suce wani abu. “Mami! Dady!! Don Allah kuce wani abu ” kallon ta Dad yayi ,yace dama wayace muna fushi dake ? tashi kije “, Hajar mik’ewa tayi jiki babu laka ta fita sai k’ara wai gowa takeyi ,tana kallon su ,wannan shine kallon su nak’arshe da zatayi sai kuma idan sun had’u a lahira , duk-da tasan basu yafe mata ba idan tamutu zasu yafe mata, tana shiga d’aki peper da bairo ta d’auko ta fara ,rubutu tana kuka me cida zuci ,da wannan rayuwan da take ciki gara tamutu ,ta huta idan ta haifi wannan yar me zata ce mata ? ,tana gama rubutun ta ‘aje kan gadon ,taje tayi alola tayi sallah raka’a biyu sanan ta d’auki hannun ta fara ,neman gafaran ubangiji..

Ya ‘Allah ka sasauta min Dukkan wani kunci da ,damuwa ta, Allah ka yafemin Allah kasa iyaye na sugane gsky ba da sanina wannan abun ya faru ba, Allah natufa nasan abunda zan aikata yanzu babu kyau a ‘addinin musulunci, Amman bani da zab’ine yasa zanyi haka ,hakan shizesa na samu kwanciyar hankali a rayuwata ,tana gamawa ta shafe addu’ar tana zubar kwallah..

Kamar kullum ,Kalifa idan zai kwanta barci sai yaje gurin yayarsa ,sunyi sai da safe yauma hakan ,akayi k’arfe takwas da kusan rabi ya gama duk ,abunda zaiyi ,yayo hanyar d’akin Hajar don yayi mata saida safe , yana shiga ‘abunda ya gani ba k’aramin razanashi yayi ba ,da gudu yafita ‘a dakin yana kwalawa su Dad kira , a tsorace suka zo be sanar dasu komai ba, sai jansu da yayi d’akin Hajar , Mami na ganin Halin da Hajar ke ciki ta kurma ihu tana kiran sunan Allah. Kwance suka sameta sai shure shure ,takeyi kamar me kakarin mutuwa ba kinta na fitar da wani kumfa , Dad a firgice yace Kalifa ya d’auko mukullin mota su tafi Hospital ,Dad ,da kanshi ya sungumi Hajar wurin d’aukan tane yaga kwalbar fiya fiyan data zuk’e , cikin sauri yayi da ita mota yana salati ,dukkansu sun birkice ,

Hospital d’insa ya kaita ,yana zuwa ya kira wasu kwararun likitoci guda biyu ,dashi suka zama su ‘uku suka rufa kan Hajar ,dak’er suka samu suka ceceto rayuwan ta ‘amman tasha wahala sannan aka samata ruwa..kwananta daya suka dawo gida, a gida ta cigaba da jinyar ta iyayenta suna bata cikakiyar kulawa ,wani ‘ikon Allah cikin jikinta be zubeba, su Dad sunyi nadama sosai da suka gano gaskiya lokacin da Musa ‘abokin Akram yazo yayi musu bayanin halayen Akram da kuma kudurinshi akan Hajar, Dad yayi nadama sai yanzu yasan Hajar bata da laifi shine me laifi da bai zurfafa bincike akan Akram ba, yabawa Hajar hakurin duk abunda ya faru, Rayuwa ta koma dai-dai tsakaninta da iyayenta ,tana samun cikakiyar kulawa , sai dai kuma kunci da ,damuwa da tunani basu bartaba don kullum sai tayi kuka idan ta, tuna ‘abunda ya faru, dalilin Hakan yasa Mami da, Dad yanke hukuncin zasu kaita london ko tad’an samu kwanciyar Hankali , idan yaso idan ta haihu saita dawo, don tabuk’aci azubar da cikin Dad yak’i yarda , Tow Hakan dai sukayi sun turata london ,zata zauna gidan k’anin Mami…

Hajar ta,tafi london duk da hakan bata samun kwanciyar hankali, don adul lokacin da taga cikin jikinta, sai taji duk ta,tsani kanta duniyar ma gaba d’aya taji baya mata dad’i , tana dai zaune kullum cikin damuwa, wata rana ta je wani clinic kusa da gidan ,da take zaune tace maganin zubarda ciki take so ,subata, k’in bata sukayi saida tayi, tayi musu magiya sanan tasamu suka bata ,koda takoma gida tasha tana jiran taji ciki ya zube, amman wani ,ikon Allah ko ciwan ciki bataji ba , bare taji wani laulayi , haka babu yanda ta iya tahakura tabar cikin tare da ‘alwashin idan har tahaife cikin bazata ,zauna da koma,meta haifa ba yasar dashi zatayi ko ta kaishi gidan marayu don bazata ,zauna da jinin akram ba, (shin hakan da hajar take da niyar yi menene hukuncin sa , me d’ancikin ta yasani da zatayi masa haka meyasa laifin da banana ba zai shafeshi , ?), Haka rayuwa tacigaba da kasan ce mata babu dad’i babu walwala cikin ta kuwa sai k’ara girma yakeyi, akwana ‘a tashi ba wuya ‘a gurin Allah cikin Hajar har yakai lokacin haihuwa , harda, d’oriya..

Ranar wata litinin da misalin k’arfe shabiyu Hajar ta fara nak’uda , nan danan suka tafi asibiti, duka -duka awansu biyu da zuwa cikin hukuncin ubangiji ta haifo santaleliyar yarta, k’arfe shabiyu ga watan shabi ranar , wani abin alajabi shine anhaifi yarinyar da kunshin magani a hannun ta , koda Hajar taga maganin sai ta ,tuna ranar da tasha ganin zubar da ciki shine aka haifo yar dashi a hannun ta ‘a damk’e (kunji wani ‘ikon Allah wannan kadai ya isheta ishara ), Hajar jikinta saida yayi sanyi kuma taji aduniya bata da yarda takeso ,sama da ita ,tanajin bazata iya rabuwa da ita ba , bayan anyi suna yarinya taci sunan mahaifiyar Hajar su Mami da ,Dady ma duk sunje…

Bayan Shakara Daya

Yesmin harta girma ta yi wayo kuma tana ,tafiya ‘amman ba’a yaye taba. Hakan ya bawa Hajar daman komawa school don tayi masters d’inta ‘agida take barin Yesmeen bata ,tab’a zuwa da ita school ba ,

Bayan ta koma da wata biyu ne ,ta had’u da ,Doctor Samir lokacin ya tafi k’arin karatu kon fannun aikin shi, koda suka had’u kafun ta yarda su fara ‘abota saida ,suka, kusan shafe shekara ,sannan dataga shi ba irin mazan banza bane yasa, ta ‘amince da suyi abota ..

After two years

Yesmin ,nada shekara ukku ,lokacin ta kamala karatunta, suka dawo gida, tunda suka dawo abunda ya faru da ita ya dawo mata sabo tamkar a lokacin yake faruwa ,duk wani walwala da farin ciki suka, kuma gushe mata barin ma idan ,ta kalli Yesmeen , Hajar da tadawo ba zama tayi ba ‘aiki tafara yi a asibitin su, awajen ,ne ta, tadda Khadee ma ta soma ‘aiki dasu..

Dawowa labari

By Dija_waziri
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Amfanin ilimi da hankali shine kayi aiki dasu wajen aikata ‘abin da zai amfaneka da kuma guje ma dukkan abinda zai cuceka.

Duk yadda kike son mutum ,indai ya fara jefo miki kalaman batsa ,ko kuma yayi kokarin ta’b’a jikinki ,to ki rabu dashi yaje ya nemi wata mai irin halinsa…amma bake ba..

ki sani cewa duk wanda rashin kunyar sa takai har ya tab’a jikin wacce yake fatan ta zama uwar yaranshi, tow hak’ika shi acikin mazinatan ma shi ba k’arami bane.

Babu wacce zata ‘auri mazinaci sai ,idan ita d’inma, mazi naciyar ce ko kuma mushrika…Hakanan babu mai aurar mazinaciya sai mazinaci ko mushrika (Allah ne ya fad’a)

duk ma’auratan da suka fara zina tun kafin aure sun riga sun gurbata tarbiyyar zuriyar da zasu haifa …ya Allah ka ,kiyayemu don qarfin ikonka ka rabamu da sharrin duk wani me sharri ka rabamu da mugayen maza

Chapter 13

Bayan Dad ya dawo daga London ya kira hajar yayimata nasiha sosai akan ta kwantar da hankalinta , Hakan shine Alkairi a gareta shi yasa ‘Allah be nufa ta zama ,matar Akram ba ,yayi mata nasihohi sosai ,Hajar kallon mahaifin ,nata kawai takeyi tare da tausayin kanta,da kuma tausayin halin da zai shiga idan yasan me Akram yayi mata, tow meyasa ma ,Mami ta b’oye masa bata sanar dashi ba? Anya kuwa bazata sanar dashi ba? tow yanzu ita da wani ‘idon zata iya sanar dashi wannan mummunan labarin ,da wainan tunanin ta ,tashi ta koma d’aki…

A kwana ‘a tashi babu wuya ‘a gurin Allah yau Hajar satinta biyu a gida kuma har yau dady besan me ake ciki ba ,Mama tayi tunanin sanar dashi amman tana tsoran kar wani abu ya sameshi dalilin dayasa tayi shiru ta b’oye masa kenan..

Yau Friday kamar kullum duk ,k’arshen sati Kakar su Hajar takanzo ta gansu ,tow yauma tazo ,tana zaune a falo Khalifa da Hajar sukazo amman Hajar batada walwala duk wanda ya ganta zai gane kamar akwai abunda ke damun ta duk ta rame sai dai kuma tayi fari sosai skin d’inta yayi kyau , tunda satinan ya kama takejin bata jin dad’in jikinta ga yawan kasala da ciwan kai da takeji , kallo d’aya Kakar tayi mata kawai jikinta ya bata ‘akwai matsala yanayin yanda taga Hajar d’inne yasa hankalinta ,tashi ,cikin fargaba da tashin Hankali ta nufi ,inda Hajar d’in ke tsaye tace..

“Hajjo meke damunki ,ki fad’amin gsky karki b’oye min” dai -dai lokacin da Granny ke tmbyr Hajar dai -dai lokacin Mami ta shigo falon , kallon ta Hajar tayi suka had’a ido ,saurin Kauda kanta Mamin tayi don ko son su had’a hanya da Hajar din batason yi tun sanda ‘abun ya faru tadena kulata ,wuri tanema tazauna tana kallo ba tare da tace dasu ,uffan ba..

“Hajjo dakefa nakeyi kinyi shiru”.

“Babu abinda ke damuna Granny” Hajar ta fad’a kamar zatayi kuka.

“Karya kikeyi zo nan” hanunta ,ta kama ta zaunar da ita kan ,kujera ta fara duba hanayenta da goshinta ,su k’asan idon ta duk taduba , fuskarta Babu anuri tace “kutashi kuje daga nan kice wa Babanku yazo “…

Suna fita Mami ta tsuguna ta gaida Granny sanan tacigaba da kallon ta ,yayin da ta kawo mata kayan motsa baki , kallon Mami Granny tayi “Fatima ,meke damun Hajjo ? ta fara bin maza ne?” Gaban Mamine ya fad’i “Bin maza kuma Hajiya me kika gani?” Tow Hajjo dai kamar ciki gareta”..kofin shayin dake hanun Dad ne yayi saurin sub’u cewa daga hanunsa “ciki kuma Hajiya ? ” Mami ko dafe k’irji tayi ,tana hawaye ba k’aryata ‘abunda Granny tace ba don zai ,iya ,yuwuwa tow amman idan hakanne Hajjo ta cucesu ..

“Eh ciki gareta kuma ,kakira Doc… Yanzu ya gwadata ku gani ” jikin Dad na rawa ya danan number d’in Doc…bugu d’aya ,ya d’aga nan yasanar dashi yazo gida ‘akwai matsala ,aiko ba’a wani jimaba saiga shi ya iso,koda ya iso darect d’akin Hajar suka shiga ,da mamaki taji Dad nayiwa Doc..bayani ,ita dai tasan bata sanar da ,dad cewa bata da lfy ba tow me Doc..zeyi mata ,nan dai ,Dad suka gama ,magana da Doc…sanan yafice a tsakin yabar Granny da Mami da kuma Doc…gwaje gwaje Doc..yayi mata bayan wasu yan mintuna ya kalli Mami yana Murmushi ya fice a d’akin suma suka mara ,masa baya ,ita ko Hajar binsu tayi da kallo tare da tunane -tunane kala -kala

“Congat Dr Galadanci yarka tana da ciki ” Inna lillahi wa….” Granny bata k’arasa ba sai jinta sukayi a k’asa , Doc.. Ne yayi hanzarin taimakon ta don Mami da Dad sun daskare Agurin saida ,Doc ya tab’a Dad sanan ya dawo Hayacin sa, suka samu suka ,kwantar da Granny kan kujera sanan ya raka Doc….ya tafi shikuma ya yo gida zuciyarshi a cushe ranshi a jagule koda ya dawo Kalifa da Mami yagani kan Granny suna mata firfita har a lokacin bata farfad’o ba…

Kasa tsayuwa yayi da kafafun shi zuciyarshi na masa zafi ,yanzu wannan wace irin abun kunya Hajar ta jawo masa duk jajircewan da rokon Allah da yawaita yi musu nasiha ‘akan zamantakewa da tsoratar da su akan azabar Allah da kwanciyar kabari zai yi wuya ta faran d’aya, ya ‘aminta da ‘abunda ,Doc…ya sanar dashi, mu samman ma daya kasance Hajar yarinya mafi soyuwa gareshi wacce yakeji kuma ya ,yarda ,da irin kamun kanta ,Innalillahi wa inna ilaihirraajiun Allamuma ‘Ajurni fi musibatin , shine kawai abunda yake iya furtawa , suna cikin hakane Hajar ta sauko ba tare da tasan me yake faruwa ba ,ganinta yasa wani zuciyarshi harzuk’a be san ,sanda yayi kanta ba ya hauta da ,duka ta ko ina yana magana,”Ashe ke yar iskace bansani ba? Dole yaron ,yace bazai aurekiba Hajara ! A gidana ? Kin zubarmin da mutunci kaico wannan wace irin rayuwa ce ?koki gayamin wayamiki ciki kona kasheki yau don dana dinga, ganinki ,ina ganin bakin ciki gara na kashe ki nima ‘akasheni “duka yake yi ko ta ina batare da ya dakata ba, Mami ko Runtsa idon ta ,tayi tana hawaye ba tare da tace komai ba , Dad ko sai dukan Hajar yake ba k’ak’au tawa itakuwa ta kasa gane meke faruwa da ita yanzu Ashe Akram ciki yayi mata, kuka take kamar ,ranta ze fita Dad ko be dena jabgar taba yana fad’in “waya miki ciki don Ubanki”….

Mami dataga Abun yak’i ,karewa tayi k’arfin halin mik’ewa tsaye tana me kiran sunan Allah “

“Alhaji don Allah kayi hakuri ka rabu da ita zafa ta iya mutuwa koka manta cikine ajikin ta” Barin dukan Hajar yayi ,yadubi Mami dake tsaye gabanta cikin zafin ,nama yace ,idan tamutu sai me wlh dana ,dunga kallon wannan bak’in cikin gara babu ita ‘a doran k’asa ae duk iskanci da takeyi da saninki takeyi kece kike d’aure mata gindi yanzu ae gaki gata sai kisan yanda zakiyi da ita ,ki tattara mata kayanta ,taje tanemi wani uban don ,nikam nariga dana sal……”wlh idan ka ,k’arasa furucinki saina d’aga maka nono kuma Babu inda zataje Wannan abunda ya faru k’addara ce kuma dole mu d’auketa , Hajiya ta furta, tana daga kan kujera

“Ha..ha.. Kiran sunan Hajiya Dad keson yi sai dai kuma ya gagara kiran ,nata ,kawai gani sukayi, ya, yanke jiki ya fad’i ,da sauri suka nufeshi, ganin haka yasa hankalin Granny tashi ,Dad ! Dady!! Dad!!! Shine abunda Kalifa ke furtawa ,a gigice Mami da Granny sukayi kanshi suna girgiza shi, Hajar ko ,kuka ta sanya don jikinta babu laka ,ko tashi bazata iyayi ba jirine ke d’iban ta ,yanzu idan Dad yamutu fa itace sila ita yanzu ina zata saka ,kanta ? …

Ruwa Kalifa ya sunkuta ya fara yayyafa masa ‘amman ina Dad ko motsi bayayi ,mukullin mota ya d’auka da taimakon su Mami aka shigar dashi mota Mami da Kalifa ne suka wuce da, Dad Hospital Granny kuma taji da Hajar..

Suna zuwa Hosptal d’inshi suka ,kaishi suna zuwa Doc…d’in gaba d’ayansu ,sukabar abunda sukeyi cikin gaggawa suka, karb’eshi saida suka yi masa yan abubuwan da zasuyi sanan sukace abarshi ya huta zai farfad’o anjima kad’an

Basma tadawo dama taje gidan yan uwan Baban tane kwananta uku sai yau ta dawo ,Hajar tagani kwance kan ,kujera jikinta jina jina Granny zaune kusa da ita…

“Hajjo kinga ‘abunda kika jamana ko ? Yanzu wannan abun kunyar dame yayi kama? Ga mahaifinki cen a Hospital kuma duk ,kece sanadi ki fad’a min gsky waya miki ciki?”..

Zoro ido Basma tayi waje bata san ,sanda ta furtaba “ciki” OMG Ya salam , wannan ..

Hajar na kuka tabawa Granny labarin duk abunda ya faru A-z bata ,b’oye mata komai ba , Granny duk tayarda ,da ‘abunda Hajar tace don Hajar bata k’arya idan zata fad’i abu iya gaskiyar ta zata fad’a kuma tasan Hajar bazata ‘aikata hakan da gangan ba, ” Tow meyasa tun farko ba’a sanar damu ba ? Laifin mahaifiyar kice ” itadai Hajar batace komai ba don zafin ciwo ya dameta dak’er ma taiya bawa Granny labari don bata koson tuna ‘abunda ya faru ,koda taji tana da ciki ,kukan kin zuwa yayi ,yanda takeso kasa kuka tayi don Idanunta sun bushe tun randa tarabu da ‘Akram kullum cikin kuka takeyi tow yanzu kukan ma tadenayi saidai tayi azuciyar ta..

Granny tayi mata nasiha sosai ,sanan ta gasa mata jikinta suka taimaka, mata ita da Basma zuwa d’aki.

Dad ya farfad’o sai dai ya kasa, samun nutsuwa sai ,sambatu yakeyi ganin hakanne yasa,Doc…yi masa ‘aluran bacci ,nan danan ya fara bacci ,sanan Doc … Ya juyo garesu yace “ku kyaleshi ya huta,da ‘alama ‘an fad’amishi wata maganar da ta daki zuciyarsa, yana cikin shock ne, Amman insha ‘Allah zai tashi cikin koshin lfy ya razana, ne sosai”.

Mami dake faman kuka bata iya cewa komai ba Kalifa nema,yayi k’arfin halin iya, iyawa Doc… Magana .

Dad bai tashi ba sai wurin k’arfe hudu na rana, koda suka, koma gida be nemi Hajar ba ,kuma be sake zancen abunda ya faru da ita ba saidai duk randa ya ganta saiya tuna kuma yana jin zafin Hakan, Granny ta had’asu dagashi Har Mami tayi musu bayanin yanda sukayi da Hajar sanan kuma ta nuna musu ba laifin ta bane , duk da haka Dad be hakura ba don ko ,kula Hajar d’in basayi dagashi ,har Mami..

Koda yaji cewa ‘Akram ,ne yayi mata ciki ya d’auki alwashin saiya kamashi ya rufeshi amman babu irin ,neman da beyiba ,Babu Akram babu dalilin shi,

Rayuwa tayiwa Hajar zafi, su Mami duk sun juyamata baya basa kulata, basa ,sauraranta gaciki ga rashin lfy da take fama dashi, komai ya daina mata dad’i gidan ma ya zame ,mata kamar mak’abarta batajin dad’in komai na rayuwa, bata fitowa kullum tana d’aki ,idan kuwa taga su Dad ,da Kalifa da Mami suna hira ‘a falo suna ganinta duk zasu watse Kalifa ne kad’ai ke tausayinta ‘a gidan gashi Basma ta koma Khadee ma ta koma gida ‘Amman takan d’an zo , wajen Granny nine kawai take samun kwanciyar hankali , duk ta rame tayi wani ‘iri kamar ba Hajar sarkin gayu ba sosai take nadamar Had’uwa da ‘Akram da tayi da kuma irin saken da tayi masa harya lalata mata rayuwa ,rayuwa ta yi mata kunci ji take ,kamar ta dora hannu aka ta kurma ihu duk lokacin da tatuna ‘abunda ‘Akram yayi mata ,kullum cikin kuka takeyi….

Bayan wata d’aya da sati d’aya kwance take tana ,kallon POP d’in dake dak’in ta ,tana zubda ruwan hawaye bak’in cikine far cikin zuciyar ta don rabon da ta ,tsinci kanta cikin farin ciki harta manta, wannan wace irin rayuwa ce ina zan saka raina da ‘bak’in cikin Akram zanji ko da bak’in cikin rashin kulani da iyayena basayi ? Wai shin su basusan kaddara bane? Ya sukeso nayi da raina ,yaushe abu zai k’are gare ni. Ni kaina nagaji da ,duniyar gabad’aya ya zanyi da Rayuwata da ‘ace mutun zai iya goge abin da ya faru a baya cikin rayuwar sa ya zama tamkar bai faru ba da na saida raina don ,nayi hakan.a wannan rana Hajar ko fita daga d’aki batayi ba har wurin sallar magrib tun safe take ,kwance sallah ce kawai ke d’agata, Bayan sallar isha tafita falo taga su Mami suna hira ita da ,Dad ganinta yasa duk suka tsume kamar basu tab’a dariya ba , ganin haka yasa ,tayi niyar komawa ‘Amman da yake tana so tanemi gafaran iyayenta kafun ta koma ga ubangijin ta yasa ta dawo ,don bata da tabbacin zasu kuma had’uwa daga wannan ranar..

BY DIJA _WAZIRI🀞
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

masu biyoni privet akan ,na turo musu novel don Allah kuyi hakuri ,karkuce na shareku abubuwa ne sukamin yawa shiyasa don Allah kudinga tmby a group ,zan bude group duk meso saiya shiga idan yaso saina tura muku acen base nabiku daya bayan daya ba nagode da kulawar ku ,kuma nagode ,da k’aunar da kuke nunawa littafin nan 😍😍😍😍

DIJA_WAZIRI

Chapter 15

Dak’ar ta iya tashi ,tashiga toilet domin d’auro alola koda ta fito ,salaya ta d’auka ta ,tada salan nafila saida tayi raka’a goma ,sannan tayi salama ta d’anyi addu’ointa ,ta kama karatun kur’ani ba ita tabar kan salaya ba sai k’arfe 9 bayan ta idar da sallar isha , wayanta ,ta d’auka ta duba time ,sannan ta kashe wayar ta jona taji, tahau gado ta kanta ,kanta na fuskantar p.op d’in d’akin ,tunane tunane kawai take kala ,kala ,inama ace Allah zai d’auki ranta ‘a yanzu da taji dad’i da ‘ace akwai inda ake sayar da mutuwa da taje ta siyo ko nawa ne don tabar duniya ,haka ta dinga sak’e sak’e marasa kan gado , hannun ta d’aga sama tana rok’on Allah kan ya shige mata gaba ‘akan dukkan lamuran ta sannan ya bata sa’ar cin jarabawa ya kuma bata juriya da, dangana ‘akan duk halin rayuwan data ,tsunci kanta ciki , wasu zafafan hawaye ta fara fitarwa d’aya na bin d’aya ,haka har bacci b’arawo ya sace ta , bata san sanda Basmad, da Yesmeen suka shigo d’akin ba….Read more
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 16

       INDIAN 

“Yanda ka sanya Mahaifiyata kuka ,ka rabata da farin cikin ta, karaba da jin dad’in rayuwan ta ,kaci Amanar ta ,kaima wlh! wlh!! saina rabaka da ,duk wani farin cikin ka ,saina rabaka da ,duk wani jin dad’in ka ,kuma saina kashe ka . wlh saina maka ila kamar yanda kayiwa mahaifiyata ,abu mafi soyuwa ‘a gareni wlh kaima sai kashiga kuncin rayuwan dakasa mahaifiyata ciki “

Yar ,yarice k’an -k’anuwa ,wacce a shekaru bazata wuce shekara biyar zuwa shida ba, tana sanye da jajayen kaya doguwan rigace iya cinya ,sai bak’in gashin kanta da ya rufe mata fuskar ,k’afarta sanye da wani bakin snikas me ratsin ja, hanunta rike da wani k’aton zarto me kaifi , nufar inda yake tayi gurine me ,masifar duhu babu abunda ‘ake gani sai haske wani fitilan kwai wanda hasken be gama haske dajin ba ,babu abin dake tashi cikin dajin sai k’aran kukan jab’a da muka motsin ,namun daji ,babu komai gurin sai dogayen ciyayi koraye shar da suka tsiro , “yanzu ne lokacin daya dace na fara d’aukan FANSA ‘akan Abunda kayiwa ‘Abunda nafi so kuma nafi tausayi Hak’ika ,kai kacika cikaken mayaudari, maci amana ,be Ankara ba yaji saukan zauto a dede kwawalwar kansa…

“Ihun daya sakine yasa ,Hajja saurin banko ,kofar d’akin ba tare da salama ba, ganin shi tayi zaune kan gode ya dafe kansa yana sharara gumi duk sanyi ac dake cikin dakin be hanashi ,fitar da zufa kanar ,ruwa ba ,

“Lafiyan ka ,kuwa ‘Akram?”.

Kallon ta yayi ba tare da yace da ita komai ba yaciba da jan ,nufanshin ,sa tare da tunanin wannan yarinyan wacece ita da yake mafarkin ta, kuma metake nufi dashi?, kamoshi da yaji anyi ne yayi saurin ,k’ara ,razanar dashi don yayi tunanin ko itace ganin Hajja yasa shi jin dad’i..

“Akram, magana fa nake maka ,kamin banza ” don Allah Hajja ki rabu dani duk halin danake ciki, kece sila kece kika jefani kuma wlh ,nafada miki ,idan har baki gayamin waye niba zan gudu na barki ,kuma bazaki sake ganina ba”

“Ya ‘Allah “shine abunda ta futa cikin k’asan zuciyar ta , wasu zafafan hawaye taji ya zubo mata , nadama ce fal cikin zuciyar ta. Kud’i basuyi mata ,rana ba yanzi ‘ina zata saka ,kanta ,tajefa d’anta ,tilo guda ,d’aya da ‘Allah ya bata cikin gurb’a taciyar ,rayuwa ,wanda ita kanta ‘ayanzun bata isa futar dashi ba kuma itama ,tajefa kanta cikin halin ,nadama da kuma dana sani ,da tasan haka rayuwan ta zai kasance ayanzu da tunfarko, bata ‘aikata ‘abunda tayi ba yanzu gashi tasa kanta cikin tsaka me wuya , kuka me sauti ne ya sub’uce mata wanda shine dalilin ficewar ta daga d’akin..

Akram ,ko ajikinsa be damu da fice warta daga d’akin ba kuma be damu da kukan ,taba tashi yayi ,ya d’auki ,kwalbar giyar dake girke ,kan tabal d’in d’akin ya fara kwan -kwad’a saida yasha me isarsa, sannan ya koma ya kwanta yana rik’e da kanshi daya fara juya ma

   NIGERIA

Dr Samir a gsky ni mebaka shawara ne da ka ,fita k’asar waje tun da sauran k’arfin ka ,ka fara jinya ‘a gsky bamu da kayan aiki sosai kamar k’asar turai barin ma irin wannan cuta nake da baya bayyana da wuri sai yaci jikin mutun, sanin kanka ne kafun mu gane abunda ke damunka, munci bak’ak’ar wuya wurin ganowa, kuma koda muka gano abun yaci jikinka saboda haka gsky abunnan gaba ,gaba yake ,k’arawa gara tunda sauran k’arfinka ,kaje k’asar waje su d’auraka, kan magani tare da treatment me kyau “..

Murmushin dabekai zuciya ba Dr Samir ya saki”likita sauk’i daga ‘Allah yake yau kona fita ko karna fita, duk sanda ‘ajalina yayi dole na tafi babu wanda ya isa ya magance min abunda me kowa me komai ya d’aura min ,Addu’a itace komai da fatan cikawa da imani ,idan babu damuwa kacigaba da ,d’aurani kan magani kamar yanda kasaba ‘da taimon Ubangiji zan samu waraka”..

“Haka ne Samir Amman karka manta ,Allah yace tashi na taimake ,ka ,Amman babu komai ,insha ‘Allah zanyi ,iya k’ok’arina ,kuma zanci gaba da yi maka ‘addu’a Allah ya baka lfy”.

“Ameen likita nagode ,da taimakon da kake min”.

“Babu godiya tsakanina dakai Dr Samir dukkan mu ,muna taimakon yan uwanmu ,musulmai fatan mude Allah ya k’ara mana basira da fasaha kuma yasa mucika dakyau da imani “.

“Ameen Likita”nan sukayi salama Doc… Samir ya koma office d’inshi..


“Hajjo niko ina son magana dake ” tow Mami ‘ina jinki”..

Gyara zama ,Mami tayi ta fuskanci Hajar sosai “Hajjo meke damun ki? Idan nina haifeki kuma na isa dake, tow karki min k’arya “..

Duk yadda Hajar tayi da b’oye damuwata, takasa kallon Mami tayi idonta na zubda hawaye “Mami haryau na kasa mance rayuwan baya ,narasa ina zansa kaina Mami wlh Gabaki d’aya bana jin dad’in rayuwata’a yanzu “

“Kallon Harjar Mami kawai takeyi tare da tausayin ta , yanda taga d’iyar tata ,tarame tayi wani ‘iri yasa ta zubda kwala batare da Hajar d’in ta gani ba, “Hajjo Allah maji rokon bayinsa ne haka zalika babu wanda ya kaishi nuna kauna da soyayya ga bayinsa. Duk abunda kikaga ya samu bawa tow muk’adari ne dama yana rubuce ,kuma bawai sonkine bayayi ba wlh yafi kowa sonki don komu iyayenki baza mu tab’a had’a soyayyar da muke muki dana mahalicin kiba ,Allah yana jaraftar bawanshi tako wace hanya kuma ‘aduk sanda yaso alokacin dayaso don haka, kiyarda ,dani lokaci yana zuwa da zakiyi dariya wanda ya zalun ceki ,kuma yayi kuka ,kuka nahar abada ,don haka lokaci yayi da zaki manta da komai a yanzu ,ki maida komai ba komai ba ‘Allah ya baki miji nagari “.

“Ameen Mami ,insha Allah zanyi kokarin cire komai cikin zuciya ta zanyi, yanda kikace ” yawwa ‘Allah ya miki albarka” Ameen Mami”

Koda Hajar ta koma d’aki, tunani take kan yadda zata gina rayuwarta, ta inganta, ta kuma mori sauran kuruciyar da tayi mata saura dolenta, ta shafe babin rayuwan baya tasan abunyi arayuwa yanzu bata da wacce tafiso tafi k’auna sama da Jawahir da kuna iyayen ta kodon ganin farin cikin su dole ne yanzu ta janye kudurin ta, tare da k’arb’an soyyar Captin Junaid ,badon tana son saba sai don ginawa d’iyarta rayuwa me inganci ,wanda ko bayan ranta, tasan bazatayi kuka ba,

Ajiyar zuciya ta saki tare da wani murmushin da iya fatar baki ya tsaya , azahiri tana buk’atar kunnan wayan ta ‘amman bataso tayi karo da kiran Dr Samir, yau kwana biyu kenan rabonta da kunnan wayanta, a zahirin gsky tana son takunna kodon taji muryan shi amman tana tsoron abunda zai biyo baya ,tasan dole da tambayoyin da zaiyi mata, haka dole ta hak’ura …

Ban d’aki ta fad’a tayi wanka ta fesa kwaliya kamar ba itaba rabon da tayi ,irin kwaliyar da tayi ,yau shekara biyar kenan da suka wuce , yaune tafito a ‘asalin Hajar sarkin gayu ,wani material tasa ruwan ganye da launin ja d’inki buba ,ta yane kanta da jan mayafi tafeshe jikinta da turaruka masu k’amshi ….

“Wow Hajjo gsky kinyi kyau yau ,wlh kamar bake ba “cewar Basmad ,datashigo d’akin sanye da bak’i da farin kayan ta ga dukkan Alamu daga ,gurin aiki take.

“Thank you sister “Hajar ta fad’a tana fari da ido “nifa ban gane ba Hajjo wannan irin kwaliya haka, wanda rabon da naga kinyi tun shekarun baya da suka wuce, kode yayan ,nawane zai zo yau?”..

Nan danan Hajar ta had’e rai duk fara’an da take ta dena”haba Sister bana so yau ina cikin farin cikin shine kike son samin damuwa ina ruwana dashi meya shafeni dashi aiki zani kuma ganin damanane yasani yin kwaliyar yau ” fuuu da ja ,jakarta zata fice..

“Tow adawo lfy idan ,nab’ata miki rai sorry”..

Ko, kulata Hajar batayi ba tafice taje tayi wa Mami Salama ta ,tafi, gudu take shararawa kan titi sauri take, taisa don ta ,sameshi ,dukda tasan bazata yarda su had’a ido ,dashi ba , minti 30 ya sadata, da ‘asibitin tundaga haraban asibitin kowa sai binta yake da kallo ,shiga ciki tayi tana zuwa direct office d’in Khadee ta shiga…

“Wow Masha ‘Allah ,Hajar kece koko idona kimin gizo ?” Cewar Khadee tana nunata da yatsa “miye kuma hakan sai kace yar k’auyen datashigo birni yau ” Hmmm badole na tmby ba Hajar yaushe rabon da kiyi kwaliya irin haka gsky kinyi kyau wlh Allah nagode maka daka dai-dai tamin k’awata ka dawo da ita kan hanya ‘Allah kaine abun godiya, wlh Hajar ganinki cikin walwala yau ba k’aramin sani farin ciki yayi ba ,harcikin zuciya ta “.

Murmushi Hajar tayi “nagode K’awata ” Hajar kwana biyu meya hanaki zuwa ‘aiki ?” Wlh ,hutawa nakeyi Mami ce tahanani zuwa tace yakamata nad’an samu nahuta na kwana biyu”.

“Kaji yar gatan Mami tow meyasa kika ,kashe wayoyin ki Captin ma saida ya kirani wai baya samun ki, yauma zai dawo”..

Daure fuska Hajar tayi kamar bata, tab’a dariya ba “ni bawannane ya Kawoni ba ke duk randa muka hadu baki da magana sai nashi,tow Allah ya kawo shi lfy nikam kinga tafiya ta “..

Tana fita office din Dr Aiman ta wuce ,shikad’ai ta ,tadda shi kanshi kasa ganeta yayi saida ya kura mata ido sosai”kai Doc..wlh kinyi kyau yau Gud morning? ” morning how are you? ” I’m fine and u? “Same to you “tow masha ‘Allah kwana biyu munjiki shiru Allah yasa dai lfy?” Lfy qlau fa yau abokin ,naka bezo bane ?” Wlh yayi tafiya ne bama ya k’asar ” har cikin zuciyar ta bataji dad’in rashin samun shiba duk wata walwala da farin ciki taji sun gushi mata, dak’er ta iya cewa Dr Aiman ok ,sanan dai tadan tsaya sukayi dan hiran da ,duk rabi ,baganewa takeyi ba donta tsunduma, duniyar tunani…

Koda ta koma offce d’inta saita fara tunani ,wai meyasa ma tadamu da taganshi miye ruwanta dashi da zata sawa kanta da muwa,da haka takauda tunani tacigaba da ‘aikin dake gabanta …..

  ******

Tun sanda sukayi wayan k’arshe da ita yakasa samun nutsuwa kullumsaiya kira number dinta amman akashe shi karan kanshi ayanzun yasan soyayyar hajar tayi zurfi cikin zuciyar sa amman yana tsoran sanar da ita yayi alk’awarin bazai sanar da itaba harsai ya koya mata sonsa.

SATURDAY

“Basmad wai ina Hajjo ? Nifa idan bazata zoba zan tafi ” cewar Khadee “la sorry Khadee dama baki lek’a d’akin Mami bane ae nayi tunanin kun had’u da ita, tana cen tana gyarawa Mami kaya “eyyah wlh ban shiga ba dana shiga ban ganta falo ba kawai na shigo d’aki banaje na sameta “…

Tashi Khadee tayi taje D’akin Mami, Basmad kuma taci gaba da shafawa Jawahir mai suna wasa da, dariyan su, “Aunty ” Na’am Jawahir menene? ” tsayawa da, dariyan Jawahir tayi ta d’an had’e rai sanan tafara magana “Aunty kin tab’a ganin babana? “Eh natab’a ganinshi Jawahir menene ?” Hawaye Jawari ta fara zubdawa ,wannan shine karo nafarko da Basmad ta ,tab’a ganin Jawahir tayi kuka batare da ko ta fad’i ba ko ando keta”ki nuna min hoton shi Aunty ina so naga Babana ,Mummy tak’i ,kaini gurin shi ” tausayin tane ya kama Basmad tayi saurin rungume ta ,Hajar da Khadee na bakin ,kofa suna jin duk abunda ya faru ,gefen gado ,ta nema ta zauna jikinta ‘a mace tajuyar da kanta ,tayi tan kwala ,Khadee ce ta k’arasa inda Jawahir take ,ta janye ta daga jikin Basmad “fuskarta d’auke da murmushin yak’e tace”Jawahir my Beby Babanki ,kike son gani kow?” Jawahir na hawaye ta girgiza wa Khadee kai Alamar eh” tow karki damu yau nayi miki Alk’awari yanzu ,zakiga Baban ki ,kow” cigaba da kuka Jawahir tayi “kiyi shiru yanzu keje Aunty Basmad tacigaba da shirya ki ,amman sai naga dariyan ki ” nan danan Jawahir ta saki ranta, ta fara k’elk’ela dariya..

“Hajjo “Khadee tazo kusa da ita ,tana kiran sunan ta , Juyowa Hajar tayi tana kallon ta batare da tace komai ba, “ki tashi ki shirya kar bak’on ki yazo yayi ta jira kinsan yakusa isowa ” babu musu Hajar ta ,tashi ta fad’a toilet zuciyar ta ‘a jagule ,saida ta kusan kaiwa mintuna talatin sanan ta fito ,tana fitowa ,wayan ta yahau ruri fargaba da fad’uwar gaba taji sun riski zuciyar ta, dak’er ta iya furtawa Khadee ta d’auki wayar,

D’auka ,Khadee tayi banaji me aka ce da itaba, kawai tace tow tana zuwa sannan ta tsinke wayar, ta maida kallon ta kan Hajar da shafa mai “bok’on kine ya iso wai yana waje, bari muje nida Jawahir mu shigo dashi falon bak’i, kafun ki gama shiryawa ” kama hanun Jawahir Khadee tayi zasu fice Hajar tayi saurin dakatar dasu zuciyar ta, na mata wani irin suya

Ku biyoni yanzu Aka fara buk β›Ήβ›Ήβ›Ήβ›Ήβ›Ήβ›Ή

By Dija_WaziriπŸ’‰
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 18

Yanzu dai tsakanin Captain Junaid da Hajar ta fara d’aukan wayar shi har sud’an yi hira, cikin raha , kuma lokaci lokaci yana zuwa gurinta su gaisa ,ita dai har yanzu ba sonshi takeyi ba kawai dai babu yanda ta iya ne bata da zab’i sai wanda ‘Allah ya zab’a mata , batun Dr Samir kuwa ,kwata kwata ya dena kiran wayan ta ya hasali ma ita rabon da taganshi tun sanda suka had’u a Hospital d’inta ranar wata jumu’a da yaje gurin Dr Aiman check up, tun abun baya damun ta yanzu harya fara damun ta ‘aduk lokacin data, tuna shi ‘idan da, dare ne tow bata iya bacci sai tayi ,ta ,tunanin shi ita ,tara dalilin haka ta ,rasa meyake shirin faruwa da ita karfa ta koma gidan jiya ,tawa kanta ‘alk’awarin bazata kuma soyyah ba , tow amman meke damun ta da yawan tunanin Dr da kuma idan ta ,tunashi take jin fad’uwar gaba ko sabone yasa hakan ,karfa maganar Khadee ya zamo gsky, kai wannan ma ‘ai wasa ne daga kan Akram na gama so kuma na gama yarda don haka ‘Allah ya sawak’e naso shi nidai nasan kawai shakuwa ce, ita kad’ai take ta magana da zuciyar ta


Kwance yake kan sofa ya jingina wayan shi k’an k’irjin sa ya d’aura hanunsa bisa kansa idanunsa ‘a lum-lumshe ,ringing d’in da yaji wayarsa nayi ne yayi saurin dawo dashi daga duniyar tunanin daya lula, ganin lambar Ummi ce yasa shi saurind’agawa, daga b’angaren Ummi ta fara magana.

“Hello Dr ya kake ya kuma jikin ka hope babu matsala kow?”.

“Lfyna qlau Ummi Jikina kuma ‘Alhamdulillah sai godiyar uban giji, ya kike ya Salma?”.

“Tow masha ‘Allah ae hakan akeso akoda yaushe fatan sauk’in muke son ji, lafiyan mu qlau, ya batun abunda ya kaika?”.

Tab’e baki yayi kamar tana kusa dashi yace”wlh mami ba’a dace ba ,babu neman da banyi ba daga k’arshe ma kaini gurin da yan Naija sukafi yawa ‘akayi Amman babu kowa don ance shekarun baya da suka wuce duk mazauna gurin sun mutu saka mako wata gobara data faru ‘a yanki duk saida taci guri babu wanda ‘aka fito dashi a raye “.

“Subhanallah yanzu d’an uwanka ya tafi kenan tow Allah yasa cen d’in yafi masa nan, yanzu yaushe zaka juyo ?”.

“Tow ina tunanin gobe zan dawo Amman ina son ,naje k’asa me tsarki ,idan ban dawo gobe ,ba tow zan kira na gaya maki zan wuce “.

“Tow Allah ya kaimu ae gara kaje d’in karok’i Allah buk’atun ka, kuma kawa d’an uwanka da mahaifinka da matarka da ,d’anka ‘addu’a”.

“Tow Ummi abunda kika ced’in hakan zanyi shawaran ki zanbi “

Nandai sukayi salama ya katse wayar yana katsewa ,riganshi ya d’auk’a yasa ya shiga ,gari

Kuci gaba da hak’uri dani pls wlh abubuwa ne sukamin yawa, ga ciwan kai dake damuna kwana biyu insha ‘Allah komai na dawowa nomal zaku dinga jina ‘akai akai ,kuma zan k’ara yawan rubutun ,nawa, nagode da kulawar ku a gareniπŸ™

Dija_WaziriπŸ’‰
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 17

Da sauri Khadee ta juyo tana kallon ta,

“Hajjo lafiyan ki ,kuwa yau?”cewar Basmad “Hajar dake faman shafa mai tace “me kika gani Basmad lfy ta k’alau ” tow meyasa zaki hanasu zuwa ?” Shiru tayi batace komai ba taci gaba da ‘abunda takeyi..

Khadee dake tsaye na kallon su ,batace komai ba taja hanun Jawahir suka fice , ganin tahowar su Khadee yasa shi saurin fitowa daga cikin mota shima ya nufosu yana murmushi sanye ,yake cikin shadda d’inki tazarce tasha ‘aiki hanunsa ya wara yana Kalon Jawahir ,tsayawa Jawahir tayi ,tak’i k’arasawa kusa dashi saida Khadee ta kaleta tace taje sanan tayi saurin zuwa ta rungushe shi d’aukan ta yayi ,yana shafa gashin kanta da suka zubo, Khadee tayi masa iso daya k’arasa ciki babu musu ,suka wuce , ciki ,saida suka gaisa, sanan takawo masa ‘abun motsa baki ta, koma ciki tabar shi da Jawahir dake mafan dariya,

Khadee na shiga ciki yanda tabar Hajar haka tazo ,ta ganta zaune ko motsawa batayi ba, murmushi kawai tasaki, tasan Yanzu tace zatayi mata magana sai ,suyi fad’a ran kowa ya b’aci gara ta bita’a hankali ,saida ta k’arasa dabda ita sanan tace “tow Hajjo nikam nagama bak’on ki na jiran ki” ,Hajar batace da ita ufan ba ta mik’e ta zura wata doguwan riga me k’aramin hanu sanan ta zura wani zunbulelen hijabi har k’asa, ko powder bata shafa ba haka ta fice…

“Hajjo uwar masifa wlh tana da matsala” cewar Basmad “ae Basmad wannan cousin d’in taki akwai tsatsauran ra’ayi ,yanzun mafa kafun ta yarda yazo saida Mami tasa baki shigar da nayi nasamu ,Mami nayi mata fad’a ne” Uhmm inde Hajjo ce zata iya fitan kuma tak’i ,kula shi inda kika san me jinu haka take ,ni fad’a ma ,mukayi da ita jiya” haba ke kuwa Basmad dukda bansan meya had’a kuba ,bedace ba kuna yan uwa kinsan Hajjo da sauri k’uluwa abu kad’e ke bata haushi ,ke ,kuma ‘akwaiki da zolaya” tow Khadee gara ke ina da ‘aiki bana shirya ,yau insha ‘Allah zan gama komai jibi zan koma ‘abuja “tow Allah ya kaimu, nima Hajjo na dawowa zan tafi gida “

Da salama ta ,tura kofar falon ta shiga kanta ‘a sunkuye ta daure fuska ,jawahir kuwa sai wasa ,suke da,dariya kamar bayau ta, tab’a ganin shiba”Dady ga Mummy tazo barinje na d’auko bebyna ,na dawa, “Jawahir ta fad’a yayin da ta sauk’a daga kan cinyar sa ta fice, itako Dr Hajar guri ta nema ta zauna tana wasa da yatsun hanun ta ,tace”ina wuni ciki ciki take gaisuwar kamar baza tayi ba shiko da fara’a ya ‘amsa da lfy haka dai ya dinga janta da hira Amman tak’i sakewa jifa jifa nema take amsa masa haka dai har suka gama yaje mota, ya kwaso mata wasu ledoji guda uku manya biyu sai kuma wani d’an daidai guda ,d’aya ya bata manya biyun daya nata ne d’aya na Jawahir k’aramin kuma na Khadee batayi musu ba tasa hanu ta karb’a takumayi godiya ,sukayi salama ya tafi ita kuma tayo ciki .

Koda ta dawo d’aki kan gado ta watsa kayan ta nunawa Khadee nata sanan tahau gado tayi kwanciyar ta ba tare da k’ara kallon ledar ba ,Khadee ko tayi murna sosai takumayi godiya, bud’ewa tayi taga jaka da takalmi ne sai wani mayafi me kyau data bud’e na Jawahir kuwa wasu dogayen riguna, ne masu kyau da tsada kala biyar sai takalmi kala uku da ribbon ribbon masu kyau sai kuma sweet da bistcut, Hajar kuwa dogayen riguna ya siyo mata kala ,kala guda shida da takalmi da jaka da agogo mekyau da tsada “kai gsky cpt yayi kokari Hajjo ,juyo kiga kayan daya siyo miki ,Khadee ta ,tab’a ta “don Allah ki barni Khadee nagani Allah amfana “magana take ba tare data juyo ba “tow yau a tsinki ,kike nikam zan wuce gida “ta mik’e Hajar ma ,mik’ewar tayi ta raka ta har bakin mota sanan ta dawo ciki d’aki ta koma ta kwanta, tana kallo, Jawahir ko sai surutu , take mata ,tun tana biyewa Jawahir gar bacci b’arawo ya sace ta ,ba ita ,ta farko ba sai bayan sallar magrib , Basmad ta gani zaune kan durowan madubi tana shirya ‘akwatin ,ta “ke ,kuma ina zuwa?” Dr Hajar ta, tambaya ,da murmushi dauke a fuskar ta” gida man gobe zan koma ‘Abuja ” cewar basmad “kai harkin gama ‘abunda zakiyi Amman dai tare da Jawahir zaku tafi tunda ta samu Hutu taje tayiwa Aunty hutu” yp yanzu ma zan had’a mata kayan ta ‘ae ban Isa natafi nabar uwata ba “dariya suduka suka Sa ,sannan Dr Hajar ta shige band’aki ta dauro alola tafito, sallah tayi data idar ,tace da Basmad ta ibi dogayen riguna guda biyu daga cikin Wanda Captain ya kawo mata har a lokacin bata kalle suba bare tasan ya suke Basmad taji dad’i sosai tako dibi masu kyau, a wannan dare Dr Hajar da Basmad har kusan asuba suka ,kai suna hira ,harma sun manta da sunyi fad’a,

K’arfe shabiyu da kusan rabi su Basmad suka tafi Hajar kuma ta wuce hospital

By Dija_WaziriπŸ’‰
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Ina k’ara baku hakuri da jina shiru kwana biyu ,abubuwa ne sukamin yawa ga wayar tawa yanzu hauka take min ,tow amman yanzu angyara komai ya dawo ,dai-dai ,insha Allah zaku fara jina yanzu akai -akai kamar yanda kuka saba ,nagode da kulawar ku

Na sadaukar da shifinnan ga dukkan masoyana na kusani ‘ina k’aunar ku akoda yaushe😍😍

Ina jidaku Maman khairee Rabi’a haruwa rukky zainab matazu respectable da sauran ku ina jin dadin commentis d’inku sosai love you gus lodi lodi😍😘

Chapter 19

Hajar ce zaune cikin offce d’inta ,tana duba wasu files ,fuskarta d’auke da farin gilashi ta maida hankalinta kan files d’in dake gaban ta jin kwan-kwasa k’ofar office d’inne ya sa ta d’agowa ba tare da ta ,tambayi waye ba ta bada izinin shigowa , wata nurse ce ta shigo hanun ta d’auke da wani farin envelop cikin girmamawa tace “Doctor gashi wata ,tace a baki, “sai alokacin Hajar ta d’ago ta kalleta ,tace “wata kuma wacece ita ?” Wlh nidai ban san taba hasalima gsky bata, tab’a zuwa asibitanan bama ,kawai ganin ta nayi kuma tana mik’o min takardan ta wuce ba tare da wani k’arin bayani ba” tow ita kuma wacece ,kiramin Dr Khadija ‘a office d’inta Hajar tafad’a tana shirin bud’e takardan , rubutu ,ta gani dajan biro kamar haka…

Ke Hajara kike ,ko wa ki fita daga harkan mijina don naji ance kece wacce ya mato akai tow ,wlh tun muna cikin salin alin kifita harkan Captin Junaid ,don kuwa nawa, ni kad’ai ne ,ke in banda ma shirme irin ,nasa me zeyi dake wacce ta gama zubar da mutuncin ta’a titi wadda tayi cikin shege ,koda yake shid’in duk besan hakan bane ,tow ina jaddad maki da babbar murya da kifita harkan mijina idan ba hakaba zan falasa ‘abunda kike b’oye masa ki sani ,nasan duk wani sirrin ki ,kuma nasan duk wani sirrin gidan ku idan kina ,k’aunar iyayen ki da wannan shegiyar yar taki ,tow kifita hanyar mijina don ko ba sa’an yinki bane idan ko baki fita harkan shiba duk abunda ya faru da, d’iyar ki ,kece sila ,sak’o daga matar Captin wanda ze aura ko yak’i ,ko yaso nice matar sa ehee….

Duk wanda ya ga hajar a wannan lokacin yasan ta shiga tashin hankali mara ,misal tuwa , kallon Khadee ta farayi da fuskar ta dake alamun hawaye, karb’an takardan Khadee tayi ,ta karanta, itama idan ranta yayi dubu toya b’aci, “Hajjo ita kuma wacece dabin diddigi haka ?” Hmmm ina zan santa Khadee idan tayi hak’uri niba, bakuwar zafi bace inde akan ,namiji ne dama ni bason shi nakeyi ba ,kuma insha ‘Allah bazan sake ,kula shiba ,bana son wani abu ya samu shegiyar yar tawa kamar yanda ta fad’a haka nake son abata ,Khadee kinga babban dalilin dayasa nace bazan yi aure ba’a rayuwa ta don ko bajima koba dad’i duk mijin dazan aura koshi bemin goriba yan uwansa zasumin “tana maganar tana sheshek’ar kuka, Khadee ko dafe kanta kawai tayi don tama kasa cewa komai ..

Wannan wace irin rayuwa ce ,ya ‘Allah kaika jarabceni da wannan abun Allah ka fiddani Allah idan ,nayi maka laifi ne ka yafe min ,natuba ya Allah duk wani me ,mugun ,nufi a kaina ‘Allah ka, kareni daga sharrin sa ‘Allah wannan jarabawa daka d’aura min Allah ka bani sa’ar cinyewa Allah natufa ,duk a zuciyar ta Hajar keyi tana kuka me tsuma zuciya.

“Kiyi hak’uri Hajjo Allah yana tare dake ,ki dena kuka ” dole nayi kuka ,Khadee arayuwa ni shikenan bazanji dadi ba Khadee tun ina k’arama nake cikin bak’in ciki tun shekaruna basu kai na shiga damuwa ba, ko iyayena wlh basu kaini damuwa ba Khadee wannan wace irin rayuwa ce Khadee da wannan rayuwan dama ‘Allah ya d’auki raina ,Allah na tufa” subhanallah haba Hajjo sai kace bakiyi ‘imani da ‘Allah ba ‘ashe dama baki yarda, da k’addara ba ?kowa da tasa k’addaran aduniya ke ,kuma tak’i k’addaran ,ce haka mahakurci mawa daci ,komai nisan dare gari zai waye akwai ranar da zaki manta da wannan rayuwan da kike ciki ayanzu ,zai zamo tarihi ,saboda haka na kwab’eki da cewa Allah ya d’auki ranki akan abunda kike tunanin kobajima koba dadi dole zai wuce ” gaba d’aya Hajar ji tayi jikinta yayi sanyi don aikin ma da ‘alamun yau bazata iya k’arasa shiba dole ta koma gida”nagode Khadee kuma nagodewa Allah da ya kawoki cikin rayuwa ta samun k’awa tagari ,irin ki sai an tona ,ni zan tafi gida, don kuwa bana tunanin zan iya cigaba da ‘aikin yau dinnan ” Ahaka sukayi salama Hajar jiki babu laka ta fita


“Tali wlh baki da kirki ,baki san mutun ba kawai zaki je ki tadawa baiwar Allah wuta” hhhhh barni da shegiya gara namata warning tun kafun abu yayi nisa, don wlh Akan Junaidu zan iya b’atawa da koma waye ke har iyayena zan iya rabuwa dasu akan shi”.

“Towfa babban magana kenan ,Tali wlh kinyi nisa shekara da shekaru kina bin wannan bawan Allah ya nuna bayayi dake amman kin ,nace ,ni wlh dariya ma kike bani kinfa girme, masa nesa ba kusa ba ‘amman waike dole saishi kike so ,”hmmm Susu kenan wato dariya ma nake baki ,kow ? Tow ,wlh !wlh!! Wlh!!! Kinji na rantse ko saina ‘auri Junaidu ko yak’i ,koya so ina ruwana dana girmeshi aiba haramun bane don ,na ‘aure shi donko ya halasta , koma yak’i amincewa ,wlh shida farin ciki har abada saina ruguza masa rayuwan sa nasa ya dena jin dad’in komai na daga rayuwan shi, ke wlh idan be aureni ba sai yayi nadamar zuwa duniya sai ya fara neman ,mutuwa ido rufe kuma wlh ,harna kusa dashi bazan bari suji dad’i ba ,zan ,nuna masa wacece Talatu diyar Alk’ali matar soja ‘ada ” dariya Susu tasa tace “Allah ya baki nasara tow

BAYAN SATI D’AYA

tafe yake cikin asibitin sai kalle -kalle yakeyi ganin ya iso ciki yasa ya fiddo da wayar shi daga ‘aljihon sa ya kirawo Khadee bugu d’aya ta d’auka, ya sanar da ita ya iso ,sannan ya kashe wayar ya cigaba da kallon zubi da tsarin asibitin komai da tsayi akayishi gwanin ban shi’awa ,be kula da sunan da ,dake rubuje ,jikin asibitin ba yadai san shekaru masu yawa sunan asibitin get well rabon shi da zuwa tun sanda ‘aka ,kwantar da kakar sa ,shekaru masu yawa lokacin yana matakin ,k’arshe a karatun sa na secondary school yanzu yaga komai ya cenza masa ‘asibitin ya balain burge shi donko za’a iya sashi a sahun farko gurin kyau da tsari, “Father tunanin me kakeyi minti na uku anan fa ” Uhm wlh kawai ‘ina tuna yanda hospital d’innan yake dane shekaru baya da suka wuce maybe ma lokacin kina jaririya “azolaye ,yayi maganar “Amman ,niko Dr Galadncin yana raye kuwa? Idan ban manta sunan saba?” Suna tafiya suna hiran ,murmushi Khadee tayi tace “Halan baka tab’a kallon kofar gidan su Hajjo ba ko? ina ,nufin baka tab’a d’aga kankaba ” gsky ban kula ba meya faru ?” Murmushi tayi tace”tow shine mahaifin ta kuma yana raye be mutuba, sai da ‘alamun tsufa sun bayyana masa sosai, don yanzu baya zuwa ma Asibitin sai jifa jifa ” ikon Allah ,Allah sarki rayuwa Dr Galadanci yasan darajan mutane yayi mana halacin da bako wani likita ne ze iya mana irin shiba yasan aikin shi Allah ya k’ara masa nisan kwana “Ameen “Khadee ta fad’a da haka suka ,k’arasa cikin tangamemen office d’in wanda komai da tsari akayi shi nuni tayi masa daya zauna kan wata kujera me laushin gaske sannan tayi gurin tangamemen tagan dake cikin office d’in taja labulen dake wangale ta rufe ta kunna iyacondishan ta bud’e farji d’in dake girke gaban teburin royal ta fiddo ruwan gora da memon kwali ta ‘ajje masa ,sannan ta d’auko ,kofin tangaran ta ‘ajje masa ,sannan ta koma ,mazaunin ta, ta zauna ,”captin ina wuni ya ‘aiki? “.
“Lfy qlau Khadee ya naki aikin?”.

“Masha ‘Allah aiki gashinan muna ta fama”.

“Tow Allah ya taimaka, niko meyasa yanzu Hajjo bata d’aga wayata sai yayi ta ringin amman bazata d’aga ba?, kuma sau ‘uku ina zuwa gidan su ,sai acemin batanan hope lfy dai kow?”.

“Tow bazan ce maka ba lfy ba captin amman akwai matsala, batun zuwa gidan su da kake baka samun ta zai ,iya yuwuwa lokacin da take gurin aiki ,kake zuwa, zai kuma iya, yiwuwa sab’ani kuke samu, d’aukan wayan ka, kuma da batayi wata yar uwar kace tayo mata lettar………….tow kaji abunda ya faru ” OMG “shine abunda ya fad’a yayin daya rik’e ,kansa tashi yayi ,yabar offce d’in ba tare da yace da Khadee uffan ba ya shige cikin motarsa ya figa zuciyar shi na suya ,ita ko ,Khadee kallo ta bishi dashi…

Be tsaye ko inaba sai Rijiyar zaki dede kofar gidan su Tali yayi parking ya fito ya shiga ,gidan ya koyi sa’a babu kowa daga ita sai k’anwar ta Susu , ko salama beyiba yasa kai cikin falon idonshi jawuri, Susu ya tadda falon tana kallo, ganinshi yasata yak’e hakora”A’a yau Captin ,ne agidan ,namu lale maraba ” Tale dake cikin d’aki jin anboton sunansa da Susu tayi ,yasa ta saurin fitow tana yak’e hak’ora kamar gonar auduga “A’a lale maraba sannu da zuwa masoyina ga wuri ka zauna”.

Fuskar shi a d’aure yace “ba zama nazoyi ba “ya fara nunata da yatsa “Talatu kifita harkata ki fita daga rayuwata, wlh!! Zumuncin mu zai’ iya ,yankewa muddin baki fita daga ,gonata ba waikekam wace irin matace me kike nima dani ? Nace bana sonki banayi dake ,koko ana so dole ne? Wancen karon ,kin ruguzamin auren da nayi niya shekarun baya kuma ,kinyi nasara tow ,kuwa ,wannan karon baki ‘isa ba ,ki fita harkana tun muna cikin lalami da ‘arziki ,ki zauna ‘a matayin ki na yar uwata “yana gamawa ya juya ze tafi ,kawai ya tsinci muryan Tali “idan kuma nak’i fita sai yaya ?wlh !idan ina raye baka isa ka ‘auri ko wacce mataba face ni ,idan kuma ka musa tomuzuba nidakai muga waye,xeyi nasara ,ni dakalin majinace kowa ya hauni ya sule kuma zama dani ya zama dole , kai ,idan ma banda jaraba irin taka me zakayi da yar iska wacce ta gama zubar da mutuncin ta ‘a titi “.

“Haka nake son ta duk mugayen kalaman da zaki jefeta dashi tunda ni ,nasan ba haka takeba ‘aeshikenan ,ke Allah ne kad’ai yasan me kikeyi kina neman shekara 45 amman kin kasa zaman aure, kin gommace kiyi ta yawo a titi ,sannan yanzu ki rasa wanda zakice ,kina so saini sabodani lusari ne kuma saina ‘aure ki Allah ya sawak’e”yaja tsak’i ya fice zuciyar shi na suya…

“Lalle wannan mutumin zesan ya tab’a Talatu ,wai harni zeciwa fuska tow ,wlh be isa ba yayi bye bye da farin ciki har abada kuma itama yarinyar ya jaza ma “fuuuuu ta shige d’aki tad’au mayafin ta, ta fice..

Shikuwa yana barin layin gidan su Talatu layin Dr Samir ya kira ya tambayeshi ko yana gida gashinan zuwa ,ya koyi sa’a yana gari hakan yasa shi k’ara gudu ,don ya isa da wuri

Karku manta comments d’inku sheke k’ara min k’arfin gwaiwa

Tow fa ‘ana wata ga wataπŸ˜ƒ Talatu kuma ta faso

Shin wacece ita wannan Talatun ?

Ashedai wahalan Hajar be k’are ba?

Tow Dr Samir ya dawo sabon cause

Kucigaba da kasan cewa dani

Dija_WaziriπŸ’‰
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 21

Wasu indiyawa ne su uku ,sukayi parking dede k’ofar gidan su Akram ,samarine guda biyu sai wani datijo yana sanye da bak’ar riga na yadi ,da farin k’ale daya daura ‘a kunkumin sa kamar d’aurin zani ya had’e gashin kansa guri guda ya tufke, fuskarshi duk yazane da kala, ga duk, kan alamu daga ,gurin bautayake ,cikin harshen indiyanci yace “muje ciki” shiya fara shiga sannan suma, suka mara masa baya ,door bell ya dannan , Jin k’aran ,ne yasa Maman Akram saurin mik’ewa daga kan sofar da take kwance zuwa tayi bakin wendo ta duba ko suwaye ganin mutanin ya sata zare ido ,da ,dafe k’irji fargaba da tashin hankali suka riski zuciyar ta damuwar da take danewa ‘alokacin ya bayana hawayen da take danewa tun shekaran jiya karya zubo amman saida ya zubo a wannan lokacin, jin ank’ara tab’a kofar ne yasa ta goge kwalar idon ta sannan taje ta bud’e kofar tana murmushin dabekai zuci ba …

Cikin harshen indiyanci tace “sanunku da zuwa ina wunin ku”..

Wannan datijon daya had’e rai ne yace”lfy qlau munzo karb’an kudin haya ne yaukam babu alfarma wata shida kenan baku biya ba kullum saidai kubamu ,hakuri to yau wlh idan baku biyani kud’ina ba jami’ar tsorone zasu rabamu daku ,kuma bazaki ,kuma zamamin agida ba “.

“Ya subuhanallah don Allah kayi hakuri wlh yarona yau sati d’aya kenan ina, neman shi na rasa shi, daya dawo zan had’a maka ,kud’inka na baka” cikin zafin ,nama mutumin yace “bazai yuwu ba “ya umarci wa inannan mutanin dasu kamata sutafi da ita chargi office, yanda yace suyin kuwa haka sukayi tana ihu suka tafi da ita ,shikuma ya shiga ,gidan ya dinga musu watsida kayan su waje daga bisani kuma yasa kwad’o ya datse gidan ya tafi da mukulin…

Acen chargi office yaje ya samesu, akayi magan ganu masu yawa ,police suka umarceta data bashi kud’insa ita kuma tace bata da kud’i don akram dukya kwashe duk wani abu data malaka ya gudu yau sati d’aya kenan rabon ta dashi ita yanzu bata da komai sai kud’in jirgin da tabiya zata koma najeriya , tow jami’an tsaro dai sun jefa Mahaifiyar akram a gidan kaso harsai randa ‘akayi belin ta ,tukun

  Nigeria

Hajar yau kwanan su biyar da tafiya ‘abuja Mami kwananta biyu ta dawo kano tabar Hajar acen , zaune suke ita da Basmad Jawahir ,na kan ciyar Hajar tana game suna tatauna yanda bikin Basmad ze kasan ce don Ansa rana ,nan da wata d’aya za’ayi ,

“Hajjo maganar anko idan kin ,koma kano zaki fitar d’in?” Kai gsky ban maki ,alk’awari ba ,Basmad , ina da ‘aiki ,kuma ba lalle abunda nina zab’a shi friend d’inki suke so ba, gara kibar su kawai su zab’i wanda ransu ke so, mu idan yaso Family sai muyi namu ,muma ,mekyau “, tow ranar dennar fa?” Ae ranar dennar dama nake magana ,ranar kamu ,kuma atamfa za’a fitar me tsada me kyau wainda bazasu iyaba saisu ,sai me arhan kud’i koya kika gani?” Hakan ma is ok”…

“Hajjo wai ,ina Captin ,ne ,ni tunda kikazo banji kunyi waya dashi ba” tsaki Hajar taja tace”mun b’ata” tow meya had’a ku?” Nan Hajar ta kwashe labari ta bata, “kinji dalili ,ni bana son tashin hankali kuma itama ,matar bansan wacece itaba ,bansan wace iri bace, gara na janye jikina tunkan a kuma ,maimaita ,tarihi tunkan inkuma shiga bala’i kwatan kwacin wanda na shiga ‘a baya “..

“Gsky gara da kika janye ,don ko baki san wace iri bace Allah yayi maki zab’i mafi Alkairi ,Amman ,nikam mezai hana ki auri Dr Samir wlh haka ,kurum nake shi’awar naga kin aure shi don ko, kun dace kuma ki kali yanda yake kula dake ,kullum sai ya kiraki”, Murmushi Hajar ta saki “tow ar Doc….ba saurayi na bane Basmad Friend d’inane kuma ba soyayyah mukeyi ba mutunci kawai mukeyi dashi “..

“Tow ae daga ‘Abokantaka yake juyawa ya koma love, koma dai miye nidai nafi sonki da likita, kuma insha ‘Allah saikun fara soyayyah ko bajima ko ba dad’i zanyi ta ‘Addu’a ” murmushi Hajar ta saki har cikin zuciyar ta dad’i take ji bata san ,sanda ta furta Ameen ba sannan ta wayence da “kinga muyi abundake gaban mu kinga dai gobe zan koma ,kano”..

Sun juma suna tattaunawa ,sannan daga bisani Basmad tayiwa hajar list d’in abunda take buk’atar tasiya mata daga kano wanda zatayi amfani dashi…..

BY Dija_WaziriπŸ’‰
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 20

Jiya nayi mestake gurin numbers 18 zansa nasa19 inafatan zaku gane

Wanan shafin na sadaukar dashi gareku Hauwa (jidda) , it’s me nd Hauwa sani umar Allah ya Barmu tare ,idan kun karanta kunban lbr don shafin nakune lol😺😺😺

Talatu na fita bata ,tsaya ko inaba sai gidan Hajiya Jumai k’awar ta, ko salama babu ta fad’a mata cikin gida tana huci .

“Lafiyan ki ,kuwa Taliy zaki shigomin gida ko salama ?”. Hmm ba lfy ba Maman Hanif “. Tow meya faru kuma waya tab’amin ke?” wancen yaron wai harni zeciwa fuska don yaga ina sonshi tow ,wlh idan yasan wata besan wata ba zan shayar dashi madaran mamaki zan ,nuna masa cewa haryanzu beyikwari ba shi yaro ne ” wani yaro kuma ?Kardai Junaidu ?” Shifa “.

Dariya Haj ,Jumai ta saki “kai Taliy kina da matsala ,najima ina gaya maki, kifita harkan gayenan bafa ‘auren ki zeyi ba ‘amman kince no, karfa ki manta keba sa’ar sa bace ke idan banda ma shirme irin ,naki mezakiya da yaro kamar Jumaid wlh da ‘ace kin zauna gidan mijin ki, da yanzu kina da d’a kodai bekai shiba ze kusa kaishi”..

“Kinga Maman Hanif ba dogon zance nazo kimin ba ,kin gane kow taimako nazo nema ” tow Taliy ,yanzu me kike so ayi ?” Yawwa yanzu kikayi zance gurin bokan nan ,nakeson ki rakani wanda shekarun baya mukaje akan batun wannan buduruwan tashi ” tow fa ‘Allah yasa be mutuba don yanzu rabon mu da zuwa gurin she ana neman 7 year harda ,d’oriya ,yaushe kike son muje?” Gobe nakeso muje ” kai banda gobe Baban su Hanif yana gari ki bari jumu’a ze koma bakin aikin shi asabar sai muje ,tunda guri banan kusaba “tow Allah ya kaimu ,”cewar Talatu sannan suka shentake da wata hiran …

Wacece Talatu?

Talatu d’aya ga Alhaji muntari wanda ‘akafi sani da Judge Muntari ,Mahaifin Talatu cheef judge ne dashi da Mahaifin Captin Junaid yaya da k’ani ne Alhaji Muntari shine babba sannan Mahaifin Junaid sai kuma k’anansu mata guda uku susu biyar ne agurin mahifin su kafun ya rasu ,Talatu itace jika ta biyar a family d’in su Junaid ,Amman yanzun itace jika ta farko saboda sauran hud’un duk Allah ya karb’i abinshi , shekarun Talatu 45 auren ta d’aya tun tana yar shekara 14 mahaifinta ya d’aura mata ‘aure da wani datijon arziki Talatu badon tana soba tayi auren, don ita ‘a rayuwan ta ,tana k’aunar taga tayi zurfi a karatu, tow kuma dokar mahaifin ta shine dasun gama aji shida yake masu aure , tunda Talatu ,tayi aure take musgunawa mijin ,nata take jifarshi da mugayen kalamu da habaice habaice, gata dama gwanace gurin masifa da bala’i don kaf ,family sunsan ta, bata barin ta kwana ,Saida suka shafe shekara biyar suna ‘abu daya kullum babu dad’i mijin baya jin dad’in zama da ita ,haka har Allah yasa Talatu ,ta samu ciki ,tana tabatar wa da cewa ciki gareta ,ta inda take shiga ba tanan take fita ba , mijin ta kuwa yasha ruwan ashar ,har saida ranshi ya b’aci ,shi dama darajan mahaifinta da kuma ganin mutuncin sa yasa shi yake ragwantawa ,Talatun bega dalilin da zesa datijo dashi zata dinga zagewa haka ba don ahaife ze haifeta don dai kawai Allah be,bashi haihuwa bane duk matan da yake aura guduwa sukeyi saboda baya haihuwa, Talatu kuwa tayi alk’awarin saita zubar da cikin ,babu irin lalab’i da rok’on da beyi mata ba ‘amman tak’i fir shiko dayaji haushi yace idan har ta zubar masa da ciki tow, karta dawo masa gida ta koma gidan ubanta, itako tayi gud’a tace gaba ta kaita ,yanda ta fad’a ,d’in kuwa hakan tayi tazubar da cikin sannan kuma ta koma gida ta shera k’aryan ta kuma yan gidan su ,sukahau suka zauna , bayan auren ta ya mutu da shekara 4 wata ,rana da Junaid ya dawo hutu daga makaranta, tunda ta k’elara idonta, ta ganshi tace idan bashiba sai rijiya ,lokacin ta bashi shekara tara, shiko yak’i yarda shine take ta bibiyar shi ,ita kuwa tundaga lokacin bata sake aure ba mahaifinta babu yanda beyi da itaba ‘amman tak’i yace zeyi mata nadole tace koyayi wlh saita kashe ta fito, su ,harsun fara tunanin ko aljani gareta , har Allah ya d’aukin ran mahaifin Talatu batayi aure ba ,babu yanda mamansu batayi da itaba ‘amman tace ita ‘arabu da ita ,ita Junaid take jira, hhhhhh lol tow kunji kad’an daga cikin wacece Talatu


Zaune take kan prayer mat tana karanta Al-Ma’thuuraat, Mami ce ta shigo d’akin ta zauna gefen gado har Hajar ta salame “Mami lfy ?” Lfy qlau Hajjo ina son ki shirya gobe zamu tafi Abuja maganar bikin Basmad za’a kawo kayan ta kuma, kinga dole naje “lah ,har bikin yayi kusa haka ‘amman Basmad bata sanar dani ba wlh Allah ya kaimu dama nayi Missing Beby na” Murmushi kawai Mami tayi ,ta mik’e ta fice tare da sanar da ita idan tagama taje falon k’asa Dady na ,neman ta .

“Abokina lfy kuwa naganka haka?” Samir akwai matsala narasa me ,matarnan take nufi dani ,nace bana son ta amman duk lokacin dataji labarin inada budurwa sai tasan yanda tayi ta rabani da ita” wace matace haka”Samir ya tambaya “wace kuwa idan banda Talatu” dariya Samir yasa ,yace kacemin “masoyiyar yanzu metayi maka” tsaki Captin yaje yace “kaga bana son iskanci ya ina mata magana zaka wani fara min dariya duniya ce ba masoyiya ba ” duk yanda Samir yaso da ,danne dariya saida ya fito”sorry wlh ban san yazo ba dariyan, me tayi maka?”

Captin duk ya gama kulewa dama tuncan a kulen yake, mik’ewa yayi ze fice Dr yayi saurin tsaida shi “sorry mana kai matsalata dakai saurin fushi” tow ya bazan yi fushi ba nazo ma da matsala ta zaka fara wani mun dariya ” tow ya hakuri nadena gayamin ,meke faruwa” nan Captin ya kwashe duk yanda sukayi da Talatu ya gaya masa da kuma ‘abunda Khadee ta fad’a masa “ni yanzu taimakon da zakamin shine muje dakai ,ka tayani bata hak’uri” tow babu damuwa yaushe zamu ?” Ni gobe ma don Allah “tow Allah ya kaimu ” tsale yayi ,ya rungume abokin ,nashi sannan yace”kaga nama ,manta ban tambayeka jikin ,kaba ya jiki ,-jiki? da sauk’i ni ciwan zuciyata ma nake ganin yanzu babu don gsky ya kwana biyu be tashi ba ,tow d’ayan ciwanne dai kawai sai hamdalah amman kwana biyu kam sai a hankali ” tow shima ‘Allah ya k’ara sauk’i na zuciyar ma kardon ka samu sauk’i ka watsar da shan magani don ,nasan halinka ,gara kaci gaba” kai wlh bazan iya ba magun gunan sunmin yawa tunda wannan sauk’i ya samu wlh nikam na watsar ” tow ko ,kamar a kunnen Ummi” sanin cewa babu wanda Samir ke tsoro sama da Ummi yasa shi cewa hakan, hak’uri samir yayi ta bashi daga bisani sukad’anyi hira sannan Samir yayi wanka suka fice…

Tun dare Hajar ta gama shirin ta ,tsaf don ko idan taje sati d’aya zatayi , bayan ta gama had’a kayan tane tana kwance tana kallon kind of heart na Philippines wayan ta ya fara ,ruri ganin ,number d’in wandake ,kiran yasata ,sakin Murmushi ,d’auka tayi ba tare da tayi magana ba daga b’angaren me kiran, ne ya fara magana..

“Asalamu alaikum”.

“Wa’alaikum Salam barka da ,dare likita”.

Murmushi ya saki tare da ‘ajiyar zuciya don duk lokacin dayaji muryan ta saiya tsinci kansa cikin farin ciki mara misal tuwa “barka dai Doc…lefin me nayi kwana biyu akamin yaji?”.

Ajiyar zuciya ta saki ta had’iyi wani yawu me zafi, dama tasan dole saiya tmby murmushin da baikai zuciya ba tayi “wlh babu komai wayar ce ta samu matsala”.

Murmushi ya sak’i yasan akwai alamar ,rashin gaskiya cikin zancen ta “wayyo ina fatan yanzu angyarata ?”.

“Eh angyara yanzu kam”.

“Tow masha ‘Allah idan babu damuwa next week ina son ,nazo gurin ki akwai abunda nake son tmbyn ki”.

“Tow Allah ya kaimu” dak’er ta iya bashi amsa don tasan tambayar da zeyi mata yana da nasaba da ‘abunda ya faru kwanaki.

“Yawwa tow dama na bugo na gaishe kine kuma na shaida maki nadowa “..

“Nagode sanu da, dawowa “.

Nan sukayi salama ya kashe wayar shi…

   Indian

BY DIJA WAZIRIπŸ’‰
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 22

Aduk, k’arshen wata Hajar tana ziyartan manyan asibitocin kano kamar su Murtala da ‘Aminu kano , da asibitin k’ashi don bada gudumawar ta ga marasa lfy da kuma yi musu ‘addu’a ,kwanan ta yau ,uku da ,dawowa ita da Jawahir saka makon sun koma school yasa ta dawo da ita..

Tafe take cikin tangamemen asibitin Aminu kano , tayi shigan ja da bak’i materiyal tasa ja da ratsin baki ajiki d’inkin A shep gwon saita yane kanta da bak’in mayafi tayi kyau sosai idon ta d’auke da farin gilashi wanda ya k’ara fito da ‘asalin kenta dede emergency tayi parking motar, ta, tafito, ta shiga tayiwa marasa lfy addu’oin samun sauk’i sosai takuma basu goma ta ‘arziki daga nan ta fita tayi part d’in marasa lfy suma ta dubasu ,tare da musu fatan samun sauk’i ,daga,gurinta wuce gainic word anane ma tafi jimawa saboda yanda taga mata kejin ,jiki wata ma haihuwa zatayi ‘amman saboda basu da kud’in da zasu biya, yasa likitocin barin su gurin batare da ankula suba ,gsky ta, tau sayawa mutane da ,dama cikin guri a k’ala saida ta, taimaki wurin mutane 6 yan kud’in data shiga dashi duk anan ya k’are takuma bawa marasa lfy shawar warin yanda zasu kula da kansu dadai sauran abubuwa, a wannan rana Dr Hajar saida ta zageye ko wani b’angare na marasa lfy ta dinga musu addu’a da fatan sauk’i ,bangaren masu fama da laruwan kwakwalwa ne kawai ya rage mata bataje ba ,dama tunda take ziyartar marsa lafiyan asibitin ,nanne kawai Allah be tab’a bata ikon zuwa ba ‘amman yau kam tasha ‘Alwashin sai taje ,tafe take tana waye dade kofar da ze sadata da cikin gurin ,ne kawai taji tayi karo da mutun ,kayan dake hanunsa duk suka zube, “subhanallah “shine abunda tace ba tare da ta kali mutumin ba taduk’a ta fara kwashe takardun da suka zube ,shiko tsayawa kawai yayi ,yana binta da kallo yana murmushi ,saida ta gama kwashewa sanan ta d’ago ta kaleshi tana”don Allah kayi hakuri wlh….” ganin wanda ke tsaye a gurin,ne yasa ta kasa k’arasa furta ‘abunda take fad’a…

“Is ok ae nasan ba da gangan kika bigeni ba ,tunda kika fara tsenewa na tsaya kawai ‘ina kalon ki”…

“Doc…wlh tunda ,nadoso kaine a zuciya ta ina ta zuci zucin ,nagama wayanan, nakira ka naji ko ,kana kusa na k’araso mu gaisa ,sai ko gashi Allah ya had’ani dakai “….

“Eyyah nima yau nake da niyar zuwa ,wurin ki ,kinga kowa yanzu na huta me kikazoyi nan ?”..

Murmushi ta saki sannan ta ce”ziyara ” kai Amman kin kyauta wlh ,har kina da lokacin ziyara ‘Allah ya biya ki”..

“Ameen yanzu ina kayi ?” Office zan koma ” ok tow bari ni, nak’arasa ciki ,idan yaso inagama na k’araso ,office d’in ,naka “…

“Ok tow sai kinzo”..

Anan suka rabu shiya wuce office ita kuma ta k’arasa ciki, ba wani jimawa tayi sosai ba ta fito…


Captin ,ne zaune cikin office d’inshi yana da danna system d’inshi ,wayar sa ya jawo yayi dailing number d’in Samir bugu d’aya ,ya d’aga ..

“Hello freind ya kake ya ‘aiki?”..

“Lfy qlau ya naka?”.

“Gashi muna fama, dama nakira na tuna maka cewa yau zamuje gidan su Hajjo “…

“Tow Allah kaimu Amman gsky sai zuwa dare ,don yau inada ‘aiki sosai ,sai 5 zanbar asibiti”…

“Tow Allah ya kaimu idan ma kagaji saimu bari gobe muje tunda Satuday ne babu aiki”…

“Yawwa hakan ma zefi kam ,zan kiraka lettar ina ‘kan aiki yanzu bye”…

Dede ya kashe wayar dede lokacin harjar ta shigo cikin office d’in , tsayawa tayi tana kallon cikin office d’in komai tsaf-staf gonin ban shi’awa kamai a tsare gashi office d’in babba ne sosai don harda gado da Tv ,tsayawa tayi ,ta fara kallon komai na cikin office d’in , wani elargiment ,ta gani hoton mace da namiji ne sai kuma d’an jariri dake rik’e hanun mace, pic d’in babu kala ‘amman duk wanda yaga matar jiki yasan ba k’aramar kyakyawar mace bace ,ko ina cikin office d’in hoton tane dama ,mijin sai nawata datijuwar mata da wani tatijo shima ‘anyi masa gurin sa daban a ‘ajiye….

“Harkin gama ne bisimillah ga wuri ki zauna”yayi mata nunu da wani kujera, sai a lokacin ta ,tuna ‘a ina take wuri ta nema ta zauna ,shi kuma ya kawo mata ruwa da cake da lemo, Amman ko d’aya bata ,tab’a ba don kuwa tadena wannan gangancin,…

“Bismillah kisha lemo don ,nasan zirga-zirgan da kikayi ma kurin ta ishe ki” A’a wlh nagode kafun nazo ,nan saida na tsaya ‘a wani shago nasai ruwa nasha”…

“Tow nawa nedai ba’a so ae shikenan”…

“A’a wlh ba haka bane” tun daga haka babu wanda ya sake ce da wani uffan ,itace ma dataji shirun yayi ,yawa ta fara magana “likita wancen pic d’in Ummi ne da dadyn ka dakai lokacin kana jariri ?”…

Murmushi yayi ,yace “A’a matatace da ,d’ana ” matatace da, d’ana saida ta maimaita yakai sau ,uku a zuciyar ta ,yanzu dama Samir yana da mata harda, d’a ‘amman ban tab’a sani ba ,yanzu dama duk haukar banza nakeyi , wata zuciyar ,tace tow ke ,meya sani game dake ,kema ‘ai kina da yar amman be sani ba , “abun ya baki mamaki ne ,naji kinyi shiru” ta, tsinci muryar shi yana magana, Dariyan yak’e ta saki tace “ae abun da mamaki ace duk zamana dakai ban tab’a sanin kana da mata harda ,d’a ba kaga kow dole nayi mamaki” Hmmm labarin yana da tsaho Doc…bana son ina tuna labarin ,nan yana tayar min da ciwo na , amman zan baki labarina yau da kuma ,koni waye ,wannan matar da ,d’an da kike gani sun jima da barin duniya ,Arayuta na kasance……………..kinji cikaken labari na , Hajar tsabar hawaye har idanunta,sun cenja kala daga fari zuwa ja tausayin shi duk taji ya kama ta haka nan taji ziciyar ta ya k’ara kwanciya dashi ,”tun daga wannan lokacin ,na kamu da matsanancin ziwan zuciya dalilin da kikaga yasa ina zuwa ,wurin Dr Aiman kenan bawai wani abu ,bane ,Arayuwa ta yanzu bani da kowa sai mahaifiya ta ,” Hajar kam ,kuka ya hanata iya cewa komai, ..

“Allah sarki Doc….kaga rayuwa kaga jarabawa ko nace kana kan gani ,duk irin jarabawan da nagani arayuwa ta naka yafi nawa ,Allah ya baka mace me irin halin marigayiya Allah yayi musu rahama ita da prince”….

“Ameen ,nagode yanzu yanda na zage na baki labarin rayuwata da kuma waye ni ba tare dana b’oye miki ,komai ba nima ina so kiban ,naki don ko nasan akwai abunda ke damun ki tun randa nace ki shirya mu fita kika ce A’a nasan akwai wani abu a k’asa ina so yau kisanar dani damuwar ki ,idan har kinyarda, dani “..

Lokaci guda taji zuciyar ta ya fara bugu da sauri ,da sauri Ba ta da niyyar yi masa k’arya ‘a labarin rayuwan ta ‘amman idan yasani yaya ze d’auki abun ze cigaba da ‘abota da ita koko zai gujeta , bazatyi k’arya ba zata fad’a ma sa komai koda hakan zeyi sanadin rabuwan su.

Saida tad’anja wani gauron ,nufashi sannan ta fara magana” zan sanar dakai wacece ni da kuma tarihin rayuwata har zuwa lokacin da ‘Allah ya had’ani dakai a matsayin abokina ‘Amman ,ina so kasani labari na babu wani abun farin ciki, ciki sai tarin kuncin rayuwa da bakin ciki da tsantsar yaudara irin ,na d’a ‘namiji, nasan idan kasan labarina ba lalle bane mucigaba da ‘abota dani dakai amman ina so labarin da zan baka ya zama ‘amana ban yarda ka sanar da kowa ba idan har bada izinina ba, kadai san nauyin amana kuma labarina dogon labari ne zamu iya kaiwa gobe anan ba tare da mun gama ba , kaine mutun ,na farko aduniya da zan fara bawa labarin rayuwa ta , zan bayana maka’ abunda nakai shekaru ina danewa ciwan daya jima yana damu na”…

“Insha ‘Allah nad’auki alk’awarin bazan fad’ama kowa ba ,kuma bazan tab’a gujen kiba, duk da bansan labarin ,naki akan me ya kunsa ba”..

murmushi da iya kacinsa fatar baki tayi “tow nagode saida tad’an nisa sosai , sannan ta ‘ajje jakarta kan table ta cire gilashin idon ta ma ta ‘ajje ta zaro wani farin towel k’arami daga jakar ta ,tafara goge hawayen dake bin fuskar ta, zu ciyar ta na mata zugi…

“Sunana Hajara wacce akafi sani da Dr Hajar ,ni cikakiyar bafula tanace gaba da baya……………..”

BY DIJA_WAZIRIπŸ’‰
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 23

Wannan shine labarina, kuma har yau da nake baka wannan labarin ,ban kuma saka ‘Akram cikin idanuna ba ,hasali ma wai abokin sa yace baya ma k’asar ya gudu ,tana maganar tana kuka me tsuma zuciya,hankiy d’in dake hanunta ya jik’e sherk’af kamar ansa masa ruwa,

Dr Samir ko kura ma ta ida yayi lokacin da ta kifar da kan ta, tana wani sabon kukan mai tsima jiki. Bai san abun da ya dace yayi a lokacin ba don tausayin ta ya gama kama shi, ji yake da zega ‘Akram babu ,abinda zai hanashi harbe shi, idan ko be harbeshi ba to dole ze masa ila, don aduniya ‘idan akwai abunda ya tsana be wuce ,cin mutuncin da maza keyiwa mata ba tare da keta musu haddi, ya tsani cin amana da yaudara ..

Lokaci guda Doc… Ya ji kan sa na wani irin sarawa kamar zai rabu gida biyu ,zuciyar sa kuwa sai buga k’irjin sa takeyi, Hak’ika taga rayuwa taga tashin hankali mara misal tuwa ta tsinci kanta cikin watarayuwa mara dad’i ,ba ko wani d’a namiji bane zeji labarin ta ya, yarda hakan shine gsky kuma ba ko wani d’a namiji bane ze iya ‘auren ta har idan yaji tana da ,d’iyar da bata da uba ,Amman shikam harga ‘Allah ya ,yarda ,da ita kuma ya ,yarda ,da labarin data bashi da zata ‘amince ta ‘aure shi da zaiso hakan , amman ze jaraba hakan ya gani koba yanzu ba…

D’agowa tayi ta kalli agogon dake manne jikin bangon office d’in taga har shida saura minti biyar na yamma , d’aukar jakar ta ,tayi ta kalle shi da idon ta dayayi jawur kamar gauta “barin tafi gida ,kar magriba tamin ‘anan”.

Cikin kunci take, ya lura da hakan. Ta na buk’atar waraka, ko ba ‘alokaci d’aya ba ne.sake tuna labarin ta ya na matuk’ar rugurguza ta. Ji yayi yana son taimaka mata wajen sa mun sassaucin in har zata yarda, dashi.

Don haka ya ,yanke shawaran ze meni yardan ta ,ze aureta baze tab’a jure ganinta cikin damuwa ba ,tun ba yauba yake dakon son ta don haka labarin ta baze iya janye wannan kwauna daya dasu cikin zuciyar saba..

“Tow Dr Hajar labarin ki yana cike da ban tausayi na jinjina maki wajen danne zuciyar ki da hakurin da ,kikayi kan abunda ya sameki , kaddaran kice hakan dama tuncen me sama ya rubuta faruwan hakan, wayon ki ,ko dabaran ki basu isa hana faruwan hakan ba , abunda na fahimta cikin labarin ki ,ki dena cewa laifin kine ba laifin ki bane laifin iyayen kine ,kema kina da naki laifin (wato yanzu ankai wata gab’a da idan yaro nason yarinya ba ko wasu iyaye bane masu tsaurara bincike ,kan yaron da sun d’anyi kadan shikenan anwuce gurin basa tsayawa suyi bincike dakyau ,tow yanzu ma ‘a wannan zamanin da muke ciki an tsaurara binciken ma ba’a kubuta ba ,bare kuma ba’a maida hankali gurin yin ba , Allah kasa mudace ka, kuma karemu da, dukkan ,kariyan ka ‘Ameen) kiyi hakuri da ‘abunda na fad’a ban fad’a ,don cin fuska ba , kuma wannan labarin bazesa na guje kiba, ina tare dake zanyi kokarin ,naga kin maido ,da farin cikin ki, kin samu ingataciyar ,rayuwa kamar yadda ko wace mace take mafarki, kuma zanyi kokarin fahimtar da, duk wanda yazo neman auren ki cewar wannan abunda ya faru dake ,kaddara ce ni dake mun tashi daga ‘abota mun koma yan uwan juna, zanyi kokarin share maki hawaye kamar yanda yaya da k’anwa kewa keyi , Jawahir kuma daga yau ta dena kukan rashin hamaifi insha ‘Allah, Abunda nake so dake shine kiyi hakuri kamar yanda kika sabayi ubangiji ya baki miji nagari me sonki tsakani da ‘Allah”…

Dukda tana cikin damuwa hakan be hanata tsintar kanta cikin farin ciki ba dashin furucin Doc…Amman wani tashin hankalin shene ya zatayi tace da Jawahir ba Captin bane ,baban ta bayan tariga da tace mata shine ? Shin idan ta dawo tace bashi bane hakan baze jawo matsala ba? Haka ta d’inga tsak’e sak’e daga bisani ta kawar da zance , “Ameen Dr Samir nagode ,da kulawar ka ‘Allah ya saka barin tafi “. Tare suka fito dashi har bakin mota ya rakata, ta shiga sannan shima ya shiga nashi….

        Indian 

Yau ne Maman akram ta cika sati biyu a gidan kaso , duk ta rame tayi bak’i duk da ,dama bak’ar ce ta kuma bak’an cewa , da safiyar ,yau asabar wani ba indiye ,yazo yayi belin ta , tare da biyan wannan mutumin kud’in da yake bin su, wannan ba indiyan ,ya shaida mata cewa Akram ne ya turo shi ,Amman be sanar da ita ko ina yake ba, babu yanda batayi dashi ya kaita gun Akram d’in ba yak’i daga baya ma tafiya, yayi ,ya barta gurin taci kuka ,kamar ba gobe takumayi nadamar rayuwan ta , daga caji office bata wuce ko ina ba sai filin jirgi, a ranar ta gama komai kawai jira take ta shiga jirgi ,basu suka shiga jirgi ba saida suka, k’ara kwana da ini k’arfe bakwai na dare jirgin su ya d’aga zuwa najeriya…

A b’angaren Talatu kuwa ,koda taje gurin boka da basu a raba Captin da Hajar idan ,da hali ma ‘a kashe ta ,boka babu yanda beyi ba don yaga hoton Captin dana Hajar ya fito kan Allon tsafin sa ‘amman ina sunfi k’arfin sa ,haka ya shaida mata cewa baze iya dasu ba wannan karon Captin yayi masa nisa don ko baya iyawa dashi ,sun rik’e karatun kur’ani da ‘azkar tare da addu’on tsari ,kuma sun rik’e salan dare dana farillah don haka, babu wani bokan duniyar da ze iya dasu, hakan yasa ta hakura ta koma gida tare da ‘Alwashin baza ta b’a bari suyi aure ba.

***

“Abokina Hanzar ta pls kar magrib tayi nafiso idan ma magrib d’in zatayi tow tayi mana ‘a gidan su , Dr Samir dake ,kokarin b’ale botuns d’in rigan shi yace” kwantar da hankalinka,na gama yanzu zamu tafi, ni wlh haka, kurum jikina keban akwai abunda ze faru idan mukaje”..

“Kamar ya kana ,nufin bazamu samu nasara ba?” No bana fatan haka ,kawai bana jin dadin yau d’inne ,wlh don ,kawai nayi maka ‘alk’awari ne dase nace na fasa “, tow nidai mutafi tunda ka gama “….

Mota suka shiga sai k’amshi suke suka d’auki hanya..

Tow fa me kuke ganin ze faru?😳

Muje zuwa πŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€

Banyi editing ba yau sai kuyi hakuri da typing errors da zaku samu gajiya nayi

By Dija_waziri
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Tabbas duk wata d’aukaka bata zuwa ma bawa babu jarabawa ‘a cikin ta

duk halin daka tsinci kanka na farin ciki, kona bakin ciki, ka gode ubangijin ka.

idan ka samu ci da sha da gurin da zaka rufawa kanka ‘asiri kayi hamdala ga ‘Allah ,koda ace a rana so d’aya tak zaka samu abunda zaka sawa bakin ,ka ,kad’au hanu ka godewa ubangijin ka ,wasu ,sau d’ayan ma suke nema basu samu ba

ina jin mamakin mutanin da sunsan ,sunfi k’arfin abu amman bazasu iya d’auka suyi kyauta dashi ga wanda basu dashi ba ,sai dai su ,siyar masa ,saboda suna ganin ,idan sun bashi kyauta sunci baya ,

yan uwa ku sani cewa idan kayiwa na k’asa dakai Alkairi Allah ze baka lada kuma shima wannan mutumin baze tab’a mantawa dakai ba, barin ma ‘ace yana cikin buk’atar abun ka bashi, kullum idan ya kalli abun koya tuna da ‘abun zeji dadi kuma zeyi maka ‘addu’a da fatan Alkairi, me yafi wannan dad’i..

Amman yanzu mun shigo wata gab’a wanda idan talaka yaje neman taimako , wajen wanda yasan yana da ‘abunda ze iya taimaka ,masa dashi dede gwargwadon yanda ze iya, Amman ,mutun sai ya dinga nuna shifa bayi da ‘abunnan kuma ‘Alhalin yana dashi bayar wance kawai bazeyi ba saboda idan ya bada yayi asara.

Yanzu munkai wani zamani da mekud’i bazeyi cud’anya da talaka ba sai mai dukiya irin shi , saboda yana ganin wannan talakan bashi da ‘abunda ze bashi sai dai shi yayi ,taci a jikin sa yan uwa ku sani cewa ubangiji shike bada wannan dukiyar, ba wayon mutun ba ko dabaran sa ,baka tunani a kowani lokaci Allah yaga dama ze iya kwace wannan dukiya taka ya bawa shi wancen da kake tunanin bashi da ,Amfani a cikin rayuwan ka, idan hakan ta faru ya zakaji , shi talauci ba mutun bane yake d’auka ya k’ak’abawa kansa ubangiji ne yake bashi ,haka ‘arziki ma, kuma wani me kud’in Allah yakan bashine don ya jarabashi kuma ya ga k’arfin imanin shi ,shin ze iya tafiyar dasu yanda ,ya kamata..

Naga wani abuda ya bani mamaki ,wata baiwar Allah ce taje tallan ged’a wani gidan me rufin asiri, tunda basa rasa ci basa rasa sha kuma basa rasa, suturan da zasu ,saka bakuma sa rasa kud’in da zasu b’atar , wannan tsohuwa da taje gidan matar, gida ta ,tambayeta nawa nawa ne gyad’ar tsohuwa ta fad’a sai matar ,ta nemi arage mata ,tsohuwar tace wlh idan ta rage mata zata kwaru don yanzun ma tafito neman yanda zasuyi ne tabar yara babu abinci tun safe, Amman ta d’au ged’an kwano d’a idan yaso ,sai ta bata hatsi dede ged’an , ae ko babu kunya matar ta karb’a tako bata gero mudu d’aya geron ma irin k’asa ne wanda suka ‘ajeye bazasu iya ‘amfani dashi ba , najima ina jimamin abun ,abunda kasan kafi k’arfin shi meyasa bazaka iya badawo kyauta ba har sai kun fanshe ,wannan tsohuwa yau koda ba talle ta kawo ba ‘ae abar tausayawa ce idan kasan kafin k’arfin abu meyasa zaka ,dunka ,k’ask’antar da kanka ,kana ,nuna baka dashi wannan shi ake ,kira da rashin wadatar zuci baka tunanin Allah ze iya hanakan….

Allah ubangiji kasa mudace masu irin wannan d’abi’a ‘Allah yasa, su gane AmeenπŸ™

Chapter 24

“Wai , ya sunan uguwan tasu ne?” Samir ya tambaya, “bata ma uguwar su d’azu Khadee tace min tana gidan Kakar ta, tarauni zamuje ” Samir ne ke driving k’ara bawa motar wuta yayi ,suna isa unguwar aka ,kira sallah magrib ,saida suka tsaya ‘ sukayi sallah a wani masalaci sannan suka ,k’arasa cikin layin ,suna isa horn sukayi get man yazo ya bud’e masu kofa suka, k’arasa da motar , shidai Samir tunda suka shiga ,gaban shi ke fad’uwa , Captain , ne ya fita yace da megadi yaje ciki yace ana salama da Hajjo, me gadi be jira wata ,wata ba ya fad’a cikin gida Inna ya samu a ktichin tana yanka ,kub’ewa me aikin kakar su Hajar kenan , ganin shigowan shi yasa inna washe baki” a’a idi ya ‘akayi ko yinwa ce ?”..

“A’a Inna kinsan ido dayawa ni shikenan bazan shigo ba sai naji yinwa ,sai kace wani acici naga ban, jima dacin ,na rana ba ma “…

Dariya Inna tasa tace”tow ae naga babu abinda ze higo dakai cikin ,ne”.

“Tow yanzu dai bashine ya kawo niba ,kije ki sanar da likita wai ,wasu ,sunzo gurin ta , suna waje suna jira” yana gama fad’a ya wuce sauri sauri don yabar kofar gida’a bud’e …

Inna kuwa falo ta shiga ta iske Hajar na karansa jarida Hajiya kuma da Jawahir suna kallo suna d’an hiran su , rusu nawa tayi tace” Barka da, dare Hajiya Maman Jawahir wai kinyi bak’i suna waje “..

Hajar taji abunda inna tace sarai, sai tayi kamar bataji ba ,taci gaba da karatun jaridan ta, “Hajjo bakiji abunda ‘akace bane?” Hajiya ta ,tambaya.

Sai a lokacin Hajar ta d’ago ta ,kalleta “me akace Hajiya banji ba, ni hankali nama yana kan wannan jaridar ” zaki iya jid’in ma ki share don ,nasan hali cewa ‘akayi kinyi baki don Haka sai ki tashi” wasu bak’i kuma ni babu wanda mukayi zezo gurina don haka babu inda zani halama ba gurina suka zo ba, b’ata sukayi ,Inna kije kice musu bananna gidan bane .

Har Inna zata Mik’e Hajiya ta dakatar da ita da cewa ,”Inna kice da me gadi ‘injini ya kaisu falon bak’i, ke kuma ki had’a ruwa da lemo kikai masu”..

Yanda Hajiya tasa Inna tayi hakan tayi, “don Allah kiyi ta zama Hajjo kar kije don bakisan ,suwaye ba sai shikenan bazaki fita kiga ko suwaye ba tow kuma idan mijin auren kine fa shikenan kinwa kanki asara kow, tow karki tashi kije ” Hajar na tura baki ta zari hijabin Hajiya tasa ,ta cire gilashin dake idon ta, ta ajje shi kan Tv sand ,har tazo ,zata fita Jawahir tace”Mommy nazo na raka ,ki?” Kafun tayi magana har Hajiya ta riga ta, “A’a babu inda zaki muna hiran zaki tafi ki barni, ni kuma na zauna dawa…

Zaune suke suna d’an shawaran yanda zasu shawo kan Hajar , suna cikin Haka wayan Dr Samir yahau k’ara ganin Ummi yasa shi d’aukar wayan tare da fita.

Fuskar ta babu ko fara’a ta shigo cikin falon k’amshin turaren da taji ne yasa ta ,saurin d’agowa taga ko waye don ko mutun d’aya ne wanda take jin k’amshin turaren a jikin shi ,da mamaki taga bashi bane Captin ta gani zaune yana murmushi, k’ara hade rai tayi ta zauna ba tare da tace uffan ba ,tana wasa da yan yatsun hanun ta …

“Barka da ,dare Hajjo ya kike ya Jawahir?”.

Fuskar ta ‘a d’aure ta ‘amsa da “lfy qlau “.

“Masha ‘Allah kwana biyu laifin me nayi kika dena kulani?”.

Shiru tayi batace komai ba zuciyar ta na suya ita haka, nan jininta bezo d’aya da nashi ba..

“Duk abunda ya faru naji Khadee ta sanar dani ,kuma ita wacce ta ,turo maki wannan lettar wlh ba ,budurwa ta bace , hasali ma ba yarinya bace don ashekaru zata iya kaiwa 45 cousin d’ina ce, kuma naje nayi mata ,magana don haka ina rok’on ki da kiyi hakuri “…

Ita dai Hajar tunda ya fara zancen shi bata ce dashi uffan ba , da murmushi ya shigo falon hanunsa d’auke da wayan shi ganin wacce ke zaune a kan ,kujera ne yasa shi fad’in ,”innalilahi wa inna ilaihin raji’un” besan ,sanda wayar hanunshi ta subuce ta fad’i ba ,gefen zuciyar shi ya rik’e yana wani ‘irin numfashi nan danan fuskarshi ta juya ta koma jazur babu abinda ke tashi cikin falon sai sautin ,nufashin sa dake fita, sama sama , da gudu Captin yaje ya tareshi dede lokacin da yake shirin zubewa k’asa , “innalilahi wa inna ilaihi rajiun” Dr Samir meya kawoka ,nanna gidan ? Waya maka kwatance? “Hajar tazo da gudu tana ,tambaya…

Captin kanshi yayi mugun d’aurewa dayaga Yanda Hajar ta rud’e,kar dai ,tasan shi tow miye halak’an su ? Shi kadai yake ta ,wasu tunani cikin zuciyar shi…

“Sashi mota barin sanar da Hajiya sai nazo mu wuce hospital , nanna ta sanar da Hajiya sannan suka d’auki hanya basu jima ba suka isa Hajar Hospital suna zuwa ‘aka shigar dashi wani d’aki , Dr Aiman takira takoyi sa’a yana ‘asibitin nan suka rufu kan Dr Samir aka fara saka masa wasu na’urori wanda zasu taimaka wajen sevin life d’in shi , daga nan Dr Aiman yayi wasu yan binciken shi , kallon Hajar yayi ,yace “akwai matsala fa Dr Hajar idan ,da hali ki ,kira mana Dr Khadee pls Samir ze iya rasa ransa at any time ,Hajar da jikinta ke wani ‘irin kyarma tayi saurin d’aukar waya ta kira khadee ta kuma sanar da ita cewa tazo Hospital yanzu akwai matsala …

Shiko Captin kanshi ya gama d’aure wa yana so yasan menene dalilin fad’uwar Doc….kode an fad’a masa wani abunda ya girgiza shine a waya , shi yanzu mezece da su Ummi kuma yasan dole su ,sani don abun bana b’oyewa bane , Salma ya kira ya sanar da ita ‘abun dake faruwa Salma cikin Fargaba da tashin hankali ta sanar da Ummi koda ta gaya ma Ummi kuka sata, sukayi asibiti

Shiko Dr Samir har a lokacin be farka ba, Ummi ko idan banda kuka babu abinda takeyi dak’er Hajar ta shawo kanta, tayi shiru ,suna cikin Haka ne Hajar taga Khadee ta fito daga d’akin da ‘aka ,kwantar da Samir babu walwala, “lfy dai kow Khadee ?” Hajar ta, tambaya girgiza mata kai Khadee tayi ,tace Muje office d’in Dr Aiman…..

“Dr Aiman akwai babban problem ,Hajar gsky zan gaya maki ‘idan ,nace zan karb’i aikin Dr Samir zan wahala tun daga kan wannan yarinya na dena daukan irin wannan cuta, “nifa ban gane abunda kike nufi ba meke damun sa ,shi nike son ji?” Cewar Hajar…

“Tow binceke ya nuna cewa Dr Samir yana d’auke da ciwan daji na huhu wato kidney cancer disease kuma cutar tariga da tafara cin jikin sa ‘ a nawa shawaran kawai shine gara ‘a fitar dashi waje ,cox idan ba hakaba ze sha wuya daga k’arshe ma ya rasa rayuwan sa, kinga ita dama wannan cuta bata bayyana sai taci jikin mutun , shi kansar huhu ba’a cika yinshi ba don ,nikam ma tunda nake ,karb’an cancer patients ban tab’a haduwa da me kedney ba gsky tunda na fara ‘aiki a rayuwa ta ” innalilahi wa innailaihi raji’un jarabawa da yawa take aduniya daga wannan sai wannan ,Allah ka bamu sa’ar cinyewa ,wannan bawan Allah yana cikin matsala ga ciwan zuciya ga cancer ubangiji kayi masa, sassauci a rayuwan shi” Ameen Dr Hajar yanzu haka halin da ‘ake ciki sai munyi masa wanki zuciya ” cewar Dr Aiman. “Tow Dr Aiman idan hakan zesa muceto rayuwan shi ae sai ayi”…

“Tow Allah yasa muyi a sa’a wai miye musababin tashin ciwon ,nashi ne?” Dr Aiman ya tambaya “wlh nikam ban sani ba Ina gidan Hajiya Muna tare Da Junaid kawai naga ya shigo ban ma san waye ,yayi nasa kwatance ba ,shigowar da yayi mukaga ya fara kalmar shada yana wani ‘irin nishi”, tow Allah dai yasa lfy cewar Khadee

By Dija_waziri
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Hakika kyakkyawan amfani da lokaci wani al’amari ne mai matuk’ar muhimmanci a cikin rayuwar mu domin kasancewar lokaci wani haja ne mai tsada wadda ke saurin kubucewa ko shudewa a cikin rayuwa.

Zamu iya daukar ma’anar lokaci a matsayin duk wata gusawa da ‘aka samu tsakanin wani zango zuwa wani a cikin rayuwar dan adam kamar gusawa daga dazu ,yanzu, jiya zuwa yau, gobe zuwa jibi ko dare zuwa rana da dai sauran su.

idan muka duba fadin Allah a cikin littafin sa mai girma, suratul nisa’a ‘aya ta dari da cesain ,inda yake cewa, lalle ne a cikin halittar sammai da kasai da sabawar dare da yini akwai ayoyi ga ma’abuta hankali (nisa’i) zamu fahimci muhimmancin tunani akan juyawan lokaci wadda ke zuwa saka makon sabawar dare da rana ,a cikin rayuwar dan ‘adam.

Akwai wasu ni’imomi guda biyu wadanda mutane da yawa ,suke tozarta su wadannan ni’imomi sune lafiya da kuma lokaci wadannan abubuwan suna daga cikin ni’imomin da Allah yayi wa dan adam wadda kuma yake bukatar su gode masa ta hanyar kyakkyawar amfani da su.

yadda zamu ribanci dukkan lokutan mu sune kamar haka, mutun zai ribanci lokacin da mutane suke cikin kunci da wahalhalun rayuwa wajen maida hankali akan taimakon masu rauni da ,dukiyoyin sa’a maimakon ya takaita kansa wajen hidimar yayan sa da iyalin sa kawai ,Alhalin alummar dake kewaye da shi suna cikin matukar bukatuwa da taimakon sa. Monzon Allah (SAW)yana cewa duk wanda ya kuranye wa dan’uwan sa musulmi wata damuwar duniya Allah zai kuranye masa damuwar ranar alkiyama. Duk wanda ya kawo sauki a rayuwan dan ‘uwansa musulmi, Allah zai kawo masa sauki anan duniya da kuma lahira .kuma Allah na cikin taimakon bawan sa matukar bawa na cikin taimakon dan uwan sa

Chapter 25

4:30Am

A hankali yake bude idon shi yana motsa kafar shi alamun yana son tashi , da sauri Salma ta k’arasa kusa dashi tana “sanu Yaya” dede lokacin daya k’arasa bude idon shi dede lokacin Dr Hajar ta banko ,kofar d’akin ta shigo,

Be sauke idon shi kan kowa ba sai kan ta, ita ma shid’in take ,kallo saurin kauda idon shi yayi daga ,gareta, tare da maidashi kan Captian daya shigo shima….

“Dr Samir sanu ya jikin ,naka hope da sauk’i kow? Ya kakeji yanzu ?” Dr Hajar ta, tambaya..

Bece da ita komai ba sai girgiza mata kai da yayi ,yaja pillo da taimakon Salma yad’an jingina.

“Likita ya kamata kad’an ci wani abun tunda ‘Allah yasa ka tashi lfy” cewar Ummi ,kallon Ummi shi kawai yayi tausayin ta yakeji da tasan halin da yake ciki da ko magana bazata iyayi ba , yanzu idan ya mutu ya Ummi zataji yayi rayuwanta ze kasance ? Da’ ace mutun yana d’aukewa kansa ciwo daya cire ma kansa larurar da take damun sa kodon Ummin sa, Wasu zafafan hawaye ne suka fara fita, ta gefen idon shi ba tare da kowa ya sani ba yayi saurin gogewa, duk abunda yake idon Dr Hajar na kansa , itama hawayen taji sun fara yinkurin zubo mata ,wani sabon tausayin shi taji ya kama ta, da sauri ta mik’e tabar d’akin ba tare da kowa ya sani ba…

“Ummi banajin yinwa yanzu ki bari anjima zanci” dak’er yake iya maganar yanayi yana ,nishi Dr Aiman da ,Dr Khadee ne suka shigo d’akin hanayensu dauke da wasu na’urori…

“Sanu Doc… Ya jikin ?” Cewar Dr Khadee da ,Dr Aiman “jiki Alhmdullah na samu sauki” tow Hakan muke so dama, ka shirya dai ko ?” Dr Aiman ya tambaya..

“Shiri kuma name?” Dr Samir ya tambaya ,” kwantar da hankalin ka ba wani abu ,bene wanki zuciya za’a maka ,kuma ,muna fatan insha ‘Allah zaka tashi lfy “cewar Khadee…

Binsu da Kallo Dr Samir yayi ,yana magana d’ekar “taya kuka san zan tashi nifa nace muku nawarke saboda haka babu inda zani” , duk abunda akace Allah ae angama Dr samir da yardar ubangiji zaka tashi kayi hakuri muje hakan shine ze iya kub’utar da rayuwan ka daga had’arin dake tare dakai, kai kasan komai basai nama bayani ba ” cewar Dr Aiman…

“Look Doc.. Nifa nariga na gama ,magana ” Haba ‘abokina me kake nufi da hakan kenan kana ,nufin haka zamu zuba maka ido ciwo ya kashe ka tun ajalinka beyi ba?” Captian ya tambaya ranshi a b’ace. “Junaid ka tab’a ganin wanda ya mutu lokacin sa beyi ba? Duk wanda kaga ya mutu ,tow dama iya kwanakin da ‘aka yanke masa ne ya k’are don haka ,ko amin wanki zuciya ko ,kar’a min wlh dama idan ajalina yayi dole natafi kuma dole kuyi hakuri dama haka ‘Allah ya k’addara min saboda haka ina so kuyi ,imani da’Allah kawai”..

“Anya Samir kana son farin cikina kuwa ?”.da sauri Dr Samir ya juyo da kallon shi kan Ummi “kamar ya Ummi ban gane me kike nufi ba?”.

Jakar dake hanunta ,ta ‘ajje tana hawaye tayo inda yake ta kama hanun shi “idan har kana ,sona kuma kana son farin cikina tow kaje ” .duk yadda yaso da, danne hawayen idon shi amman ya kasa, saida suka zubo” shikenan Ummina zanje Amman ina so ki yarda, da k’addara kuma kisani cewa duk abunda ya faru dani haka ‘Allah yariga ya k’addara min ina so kisani cewa ina sonki ,ina k’aun……. Wani ‘irin tari ya farayi me had’e da jini duk yadda yaso daya k’arasa maganar da zeyi ,ya kasa …..

“Innalilahi wa inna ilaihi raji’un” shine abunda Dr Hajar ta iya furtawa yayin data shigo taga Halin da samir ke ciki..

Da sauri nurses suka shigo suka tafi dashi Ummi na rik’e da hanunsa tana kuka ,dak’er aka b’anb’are ta daga rik’on data masa ,suka wuce dashi itako Hajar office idinta ,ta shige tana kuka me tsuma zuciya Captian ko ,kama Ummi yayi suka zauna yana rarashin ta..

Dr Aiman da wasu manyan likitoci ne suka rufu kan Dr Samir don ceto rayuwan sa ..

“Hajjo “

“Na’am Khadee”.

“Hajjo kina cikin damuwa ki fad’a min meke damun ki ,miye halak’arki da Dr don akwai wata ‘a k’asa ?”..

Gilashin dake idonta ,ta cire ta fara goge hawayen fiskar ta”Khadee ni kaina ,narasa me nikeji game da Dr Samar Khadee bazan b’oye maki ba ina jin Dr Samir a raina kamar yanda nakejin Akram a wancen lokacin”.

“Ban gane ba Hajjo kina ,nufin kice min kina son Dr Samir?”.

“Kusan hakanne Khadee bazan iya auren Captian ba , kuka ne ya kufce ma ta.

“Ya ilahi tow meyasa kika b’oye man baki sanar dani ba Hajar?”.

“Alokacin banyi tunanin da gaske son shi nike ba sai yanzu na tabbatar da hakan don Allah Khadee karku bari ya mutu ,mutuwar Dr ze ,zama barazana ga rayuwa ta kuma kiyimin Alk’awarin bazaki fad’awa kowa ba ina nufin amana ,na baki ,ko bayan raina karki fad’a ma kowa kinde san girman amana ?”.

Cikin tausayin Halin da Hajar keciki ,Khadee tace “tayaya zesan kinayi Hajjo matsawar ba’a sanar dashi ba, kina ganin hakan bazai zama barazana ga rayuwan kiba?”.

“Bazan iya bayyana masa ba Khadee cox ba lalle bane shi ya soni Amman inaso ki sani cewa komai ,ma ze iya faruwa dani har idan ,narasa shi”.

Dafa ta Khadee tayi “ki dena kuka ,k’awata insha ‘Allah zanyi iya kokari na, naganin ya samu sauki, Allah ya mana jagora.”

Hajar da kanta ke, kife tana kuka ,tace “Ameen “

Bayan Awa biyu.

Ganin fitowar Dr Aiman, ne yasa su Ummi saurin ,nufo shi “lfy dai kow Doc”..cewar Captian ,murmushi Dr Aiman yayi “lfy qlau sai mugode wa ‘Allah anyi masa ‘aiki lfy ,yanzu ,za’a gyarashi a kaishi d’akin daze huta sai kud’an barshi ya samu hutu kamar na awa goma ” wani ajiyar zuciya Ummi ta sauke tare da hamdala da godewa Allah

Nasan kuna hakuri dani kudai kara komai ya kusa dawowa nomal ku sani ina k’aunar ku❀❀❀❀❀

BY DIJA_WAZIRIπŸ’‰
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 26

KAD’AN DAGA CIKIN ILOLIN CIN AMANA

TUNA TARWA

Cin Amana wata ‘abace da wanda ‘Allah ha hana yinta cin Amana yana d’aya daga cikin halayen munafurci manzon Allah ya lissafta wasu halaye guda uku ,yace duk wanda yake dasu acikin halayensa ,to hakika shi munafiki ne. koda yayi sallah yayi Azumi yayi hajji yayi umrah, koda yace shi musulmi ne (subhanallah!!)

Cin Amana yana sanya mutun yayi baqin jini acikin al’ummah, darajarsa da mutuncinsa su zube, sannan kuma al’ummah su rik’a gudunsa.

Yana daga cikin abubuwan da suke tauye imanin mutum. Matuk’ar mutum zai rik’a cin amanar mutane ,to kullum imaninsa raguwa yakeyi

Yana d’aya daga cikin halayen da suke qaskantar da darajar mutum awajen Allah.matuk’ar mutum bai rike amanar bayin Allah ba,

wannan tuna tarwa ce garemu baki daya yan uwa musulmai, ya zama wajibi mu rik’a kiyaye amanar junanmu don samun mutunci a wajen Allah da bayin Allah.

Idan kasan bazaka iya rik’e waba tow karma ka ,karb’a bare ya zame maka ,kayaπŸ‘

Allah yasa mudace ya kuma bamu ikon rik’e amanar yan uwan mu Ameen

Chapter 26

TWO WEEKS LETAR

Kwance yake kan Sofa yana kallon MBC action, Ummi na gefen shi tana had’a kan magun gunan data gama bashi “Likita “Ummi takira sunan shi tana cigaba da zuba magun gunan cikin wani basket, “Na’am Ummi” ya ‘amsa yana cigaba da kallon film d’in 4 brothes d’in da ‘akeyi .

Saida ta gama kwashe magun gunan sannan ta mik’e ta nufi wurin Tv ta kashi ,ta dawo ta zauna kusa da ,Dr Samir “munyi magana da Dr Aiman wancen satin daya wuce bayan an salame ka , ya shedamun cewa ‘akwai damuwa ‘a tattare dakai don haka na tmby ka , kasan baka da kowa ‘aduniyar nan saini baka da wanda yafini a yanzu ,da wannan damar nike rok’on ka daka sanar dani damuwar ka likita ina son ka rashin kwanciyar hankalin ka babban matsala ce a rayuwa ta rashin ganinka cikin walwala ba k’aramin dagamin hankali yake ba don Allah kasanar dani damuwar ka”, murmushin da iya karshi fatar baki yayi sannan ya mik’e daga shingid’ar da yayi ,ya kama hanunta yana shafawa”Ummina ki ,kwantar da hankalin ki ,insha Allah ina tare dake har gaban (ABADAN) Littafin safiya Bani da wata damuwa Ummi yau rabon da ciwona ya tashi ,irin haka ,kinga ‘ai anjima yan zun ma Allah ne yayi ze tashi” tow Likita naji tunda kace baka da matsala ‘Allah yasa hakanne , yanzu dai na yanke wani hukunci Amatsayina ,na mahaifiyar ka ,nasan bazaka ,k’i abunda zan sanar dakai yanzun ba ,ni bazan tursasa maka dole ba idan kaga bema ba hukuncin ,dana yanke ,karka b’oye man ina so ka sanar dani ,na zauna ,nayi nazari da tunani ,kuma naga yadace na sanar daikai buk’atata mezai hana ka ‘auri Salma….”

Kayan abincin da Salma tashigo dasu ne sukayi saurin sub’ucewa daga hanunta, yayin da taji furucin Mami, “subhanallah lfy Salma tunanin me kike haka ?” Cewar Ummi , Salma jiki babu laka fuskar ta,babu walwala tsugunawa tayi tana tsince kofin tangaran d’in daya fashe ,idon ta na son zubda hawaye Amman ta danne alamun damuwa suka bayyana ‘a fuskar ta ,kanta na k’asa ta maida hankalin ta kan kofin da take tsincewa tace”Afuwan Ummi tuntub’e naci ban sani ba ” tayi saurin daukan farantin ta koma kitchen .

Shiko Samir sanda rewa yayi ,yana k’ara maimaita furucin Ummi cikin k’asan zuciyar shi ka auri Salma! Ka auri Salma!! Da wani ,idon ze kalli Salma taya ze iya ‘auren k’anwar matar shi ? Wata zuciyar shice tace tow ae ba haramun bane ,yaya zeyi da soyayyar Hajar ? Wannan shine rana zafi ‘inuwa kuna dole ya janye kudurinshi akan Hajar saboda tamai nisa baze tab’a furta mata cewa yana son taba koda hakan zeyi barazana ga rayuwan shi ,tunda Captian yariga shi dole ya cire duk wani soyayyar da ya jima yana ginawa cikin zuciyar sa koda hakan zesa ya rasa, rayuwan shi da wannan tunanin ya ,yanke hukuncin karb’an umarnin Mahaifiyar sa ,don bashi da zab’i sai wanda ‘Allah yayi masa dole ze koyawa Salma son shi ze koyawa zuciyar shi son ta, tow Amman tayaya? Bayan shi ya d’auketa ,tamkar kanwar da suka sha mama tare. Anya baze cutar da ita ba kuwa baya so ta d’and’ana kwatan kwacin abunda ya d’an d’ana lokacin da ‘akace ya rasa Jamila ,shi yanzu bame nisan kwana bane ya riga yasan iya adanin watanin daze k’ara nan gaba likita ya shaida masa cewa kodar sa ta kagar ,gaje matsawar beje ancire taba ,nan dayan watanin ze iya rasa, rayuwan sa yaki sanar da Ummi ne saboda besan irin halin dazata shiga ba, bayan ta sani

“Ya naji kayi shiru Likita bafa umarni ,nike baka ba shawara ce , idan kaga bema ba babu dole kaji d’ana ban tab’a ma dole ba kuma bazan tab’a ba insha Allah abunda kake so kake muradi shine ,nawa “.

Salma dake jikin k’ofar kitchen tana jin duk abunda ke faruwa ‘addu’a kawai takeyi Allah yasa karya ce ya ‘amince don ko bazata ,tab’a iya ‘auren saba zata cikawa yayar ta burin ta , kuka take wanda babu hawaye , tunanin rayuwanta na baya ta farayi tare da irin wahal halun data sha.

“Ummi nasan bazaki tab’a min zabi mummuna ba ,kuma bazaki tab’a bani abunda kika san ze cutar dani ba , Nasan Salma bata da matsala mace me hakuri da sanin ya kamata, na ‘amince zan aureta kamar yanda kika buk’ata “.

Ajiyar, zuciya Ummi ta saki tare da hamdala ga ubangiji, rungume shi tayi “na gode d’ana kai ,kadai zaka iya rike marainiyar Allah Salma yar uwar kace nasan bazaka cutar da ita ba, shiyasa na zab’i ka zauna da ita badon komai ba, Allah ya maka ‘Albarka ya k’ara maka lfy”. Ameen Ummi na fahimce ki ” tashi yayi ya kunna tv ya cigaba da kallon shi ,Ummi kuma ta d’auki jaridan Daly trust wanda tun wancen satin Habu drive ya siyo mata bata karan taba kasan cewar ita ma’a bociyar karance karancen labarai ce dalilin dayasa kullum safiya da maraici Habu saiya siyo mata

Salma ko, kasa b’oye damur da tashiga a wannan yammacin tayi, sama tahau zuwa d’akin ta ,ta kulle tafara, rusa kuka,

“Innalilahi wa inna ilaihi rajiun Samir ” Na’am Ummi lfy?” Yayi saurin matsowa kusa da ita ” inafa lfy kaga Mahaifiyar d’an uwanka ‘ankama ta da coken cikin kaya ” subhanallah ” karban jaridan yayi ,ya kalleta sosai yaga tabbas itace ,tacikin hoton da mahaifiyar shi ta bashi yaje ya nemo su, karan tawa yayi anan yaga sunan gidan yarin da ‘aka rufeta ‘anan birnin tarayya ‘abuja…

Ga wannan bubu yawa sai anamin uzuri buk din ma yazo karshe πŸ‘

By Dija_WaziriπŸ’‰
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

WANNAN SHAFIN NAKUNE TEAM CAPTAIN JUNAID INAJIN DADIN COMMENTS DINKU LOVE YOU GUYS 😍😍

Allah ya halicci dan adam akan halaye daban daban .don haka ake samun masu sauk’i da masu tsanani cikin mu’amalar mu ta yau da gobe.

Yana daga cikin shiriyar Annabi an nusar damu neman tsarin Allah daga sharrin kawunan mu da miyagun aiyukan mu, don haka duk wanda zakayi mu’amala dashi to yana iya yi maka dai-dai kuma yana iya yi maka kuskure.

Mu sani duk wata tawaya ko jinya ko laruri data same ka maganinta shine ayi hakuri a mayar da abin ga Allah .yana da wuya ace kullum sai anyi maka yadda kakeso ,ko sai kaji abinda zaiyi maka dad’i, ko sai idon ka yaga abinda zai faranta maka rai. Don haka rayuwa sai ka had’a da hakuri akan komi.

Hakika ba wanda kuskure ko matsala ba zata riskeshi ba cikin harkokin rayuwar sa a tsakanin sa da iyalan sa, makusantan sa ko al’ummar da yake raye a cikin ta.maganin kowacce irin damuwa shine hakuri ,addu’oi da mayar da al’amarin ga Allah, gamuwa da kunci ,wahala tsanani da ,damuwa duk mai yiwuwa ne ga kowa gwargwadon yadda aka qaddara masa ,kuma ba wanda zai iya kaucewa abinda ‘aka qaddara masa na sauki ko tsanani a rayuwar sa don haka anan ma hakuri da duk halin da ake ciki shine mafita ga kowa

Ya ubangiji ka bamu juriya da hakuri akan abunda kana iya ramawa ko daukar fansa Allah ka sawa zuciyoyin mu kasa mana hakuri alokacin da muke cikin damuwa

Chapter 27

   ABUJA

Cike gidan su Basmad yake da ,d’unbin jama’a yan uwa da ‘abokan arziki,

Zaune suke cikin daki su wurin biyar suna , ta yiwa ‘amarya tsiya Hajar ko ta koma gefe tayi shiru hanunta bisa kumatun ta zabga uban tagumi, “Hajjo wai meke damun kine tunda kuka zo kin ,kasa ,sakewa kow kina kewar Jawahir ne?” Cewar Basmad Hajar bata masan Basmad nayi ba don ko ta lula duniyar tunani, saida Khadee ta ,tab’ata ,tukun ta zabura hankalinta ya dawo gareta”lfy Khadee ?” Cewar Hajar “nice nace ta ,tab’a min ke nace meke damun kine wai” Basmad ta ,tambaya..

“Babu komai me kika gani wlh kurum ina tuna rayuwan dane ” Eyyah ki dena wannan tunanin ke ,kinsan babu abinda ze haifar maki na farin ciki ,yanzu kitashi muje ku anso d’inki ,ku daga nan su Khadee su dawo gida ke ,kuma sai kirakani gidan su lusey” Basmad ,da kunje kawai keda su khadee in yaso idan kun karb’o d’inkin Farida ta rakaki gidan su luseyn ,ni kaina ke ciwo” kedai kawai kice bazaki rakani ba karki wani fake da ciwan kai Khadee muje kurakani”.

“Hmm Basmad kinsan de bazan maki ,k’arya ba kow? Amman tunda kikace haka muje” taja mayafin ta suka fice, koke fa ‘Amman da ,duk ,kinbi kin takure kanki cewar Khadee


“Samir wai mekazo yi abuja ne ma?” Captian ya tambaya “wlh wani Babban abune ya kawoni, ina sadiq k’anina dana ce maka zanje neman shi kwanakin baya ? Tow shine mukaga mahaifiyar shi wai ankama ta da coken cikin kayan ta ,kai meya kawo ka?” Eyyah nagane Allah dai yayi da rabon zaku gana da k’anin ka da har ance sun mutu ,wlh Dady ne ya turo ni wai na yi masa wani aiki “.

“Masha Allah yanzu tunda ‘Allah yasa mun hadu dakai zaka rakani gidan yarin bayan sallar azahar” ok Allah ya nuna mana cewar Junaid.

“Tow na manta ban sanar da kai ba zanyi aure nan bada jimawa ba ” what kana ,nufin kace min kasamu wacce kake so?” A’a ‘ae ni bazan kuma samun wacce nike so ba sama da Jamila , kawai zanyi auren ,ne bisa bani da yanda na iya sai abunda ‘Allah ya tsara mi. ” tow ,Wacece madam d ‘in tamu ?” Murmushin da bekai zuciya ba Dr Samar yayi ba kowa bace kuma kama santa Salma ce”.

Zaro ido Captian yayi ,yace “Salma fa kace ?”, Eh itafa kaji mamaki ,kow umarnin Ummita zanbi ” ba dole nayi mamaki ba ‘Allah ya tabbatar da ‘Alkairi, nima dai na kosa wlh naga nayi aure Amman wannan k’awar taka tak’i bani dama na tura magabata na”.

“Ni ba k’awata bace Hajjo k’anwa tace don ko najima da cireta sahun k’awaye na , kad’an k’ara hakuri nasan zata baka daman , duk da ban saniba ina tunanin dakwai dalilin daya hanata baka daman Amman ka ,k’ara hakuri ” tow ae gashi munayi ni yanzu ita kawai nake jira “, sun jima suna hira sai gurin k’arfe shabiyu suka rabu..

“Kinga tsabar iskanci Hayati yabar mu sai jiran sa mukeyi Hajjo”. Wai ma ,mezai kawo maki ne Basma nifa kaina ciwo yake idan bazai zoba muwuce gidan su lusiy idan yaso ,yaje cen ya sameki , tun shabiyu ,ya shanya mutane gefen titi gashi har d’aya tayi”.

“Yi Hakuri barin kuma ,kiran shi shaddar dazan sa jibi zeban , angon ,nawa ne ya shanya ki?” Basmad ta fad’a ‘a zolaye , Hajar bata kula taba taci gaba da, danne dannen wayar ta ,suna cikin zaune ,ne wani yazo ya kwan-kwasa gefen glass d’in Basmad kansa d’auke da farantin kifi ga dukkan alamu na siyar wa ne , bud’ewa Basmad tayi ,tana “Malam lfy?” Lfy qlau Hajiya zaku sai kifi gasheshe?” A’a Allah bada sa’a ” Hajar ce ta d’ago da sauri “sai….” Ganin mutumin yasa ta kasa k’arasa furta ‘abunda take da niyya bakinta ne ya fara, rawa tana, nunashi da yatsa “wannan ba Musa bene?” Innalilahi wlh saida kika fad’a na gane shine mana ‘abokin Akram kow?”.

“Tabbas nine Musa ‘Abokin akram wlh najima ina ,neman ki Hajjo na rok’i gafaran ki ,Akan abunda ‘aka had’a baki dani akayi maki ,kinga yanda ‘Allah yayi dani kow , hakika bayan tafiyar Akram naga rayuwa nahadu ,da balai masu yawa ‘a wannan lokacin , nayi nadamar abota da ‘Akram ina cikin zamana yazo ya d’aurani a hanyar banza .

Yanzu kunga yanda rayuwata, ta kasance don Allah ina rok’on ki da kiyafe man wlh nayi nadama ,nine babban mutumin dayafi bawa ‘Akram gurb’a taciyar shawara Akan yaga ya ci nasara ‘a kanki”.

Hajar da kuka yaci k’arfin ta bata iya cewa komai ba , basmad cema ta samu kwarin gwaiwar yin magana “yunzu Musa miye riban ka na ‘abunda kayi jibeka fa yanzu kabi son zuciyar ka ,yanzu ji yanda ‘Allah yayi da rayuwan ka ,kai kenan ma shi kuma ‘Akram d’in Allah shine masanin irin halin da yake ciki , wannan kad’ai ya isheku darasi a rayuwa dama ance duk wanda ya zalunci d’an uwansa tow Allah saiya saka masa fad’ar manzon Allah ne, ku cin amanar ma kurasa wanda zakuyiwa sai mace me hakuri sanin ya kamata mace me karamci kasani cewa yanzu ka fara ganin rayuwa inde ku junanku cin Amana ce , cin Amana yana daga cikin abubuwan da suke tauye imanin mutum .mutukar mutum zai rika cin amanar mutane, tow kullum imaninsa raguwa yakeyi, haka zalika yana zama sanadiyyar dulmiyar mutum acikin wutar jahannama. Kamar yadda yazo acikin hadisi , Allah zai sanya amanar acikin chan qasan wutar jahannama , sannan a umurci maciyin amanar cewa ya shiga ya dauko -ta sai ya dauko ya hauro wani babban tudu, sannan sai ita kuma Amanar ta subuce ta koma chan qasan ramin jahannama .sai mala’iku su daka masa tsawa suce ya koma ya daukota. Haka zai yi ta yi har illa masha’Allah .

Tow kaga kuwa kuncin rayuwa da bala’in rayuwa da masifa yanzu kuka ,fara fuskanta tunda junanku b’ata yaran jam’a”.

Kuka Musa yakeyi sosai “Nasan ,na ‘aikata ba daidai ba Hajiya don Allah ku gafarce ni”.

Sai Alakacin Hajar ta d’ago daga ,durk’ufar da kanta da tayi tana kuka ,cikin kakkausar murya tace ” bani da buri a duniya daya wuce naga Akram da ma duk wani wanda ‘aka had’a baki dashi akaci mutunci na sun wulak’anta sun tozarta sun zama ‘abun kwatance a duniya ‘Allah ya isa tsakanina da ‘Akram Allah ya isa tsakanina daku Basmad ja motar nan mutafi ” Babu ,b’ata lokaci Basmad taja sukabar gurin ,suka barshi yana kuka .

Doc… Kaga wancen motar kamar Hajjo ce aciki ” kallon gun Doc…yayi ,yace itace ma ” tow me tazoyi abuja kar dai har bikin cousin d’in ,nata yayi ?” Tow ,wata k’ila ” don Allah bari mu bisu Doc…sorry ” murmushi kawai Dr Samir yayi ,yace muje

Kuyi hakuri da wannan babu yawa

By Dija_WaziriπŸ’‰
[18/12 7:32 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Dedicated this page to my mom who has love and taken care, of me for all of my life she has taught me to love others and to always tell…i love you so very much my mother Allah ya k’ara maki lfy da nisan kwana 😘😘😘

Chapter 28

Dede kofar gidan su Lusy sukayi parking , Dr Hajar ce ta fara fitowa , sai Basmad ma ta fito dede zasu shiga cikin gidan sukaji an kwala musu kira.

“Hajjo”

tsayawa hajar tayi cak ba tare da ta juya ba ,Basmad ne tayi saurin juyawa tana “suwaye kuma haka” ganin Captin yasa tayi shiru..

Har inda su Hajar ke tsaye sukazo , “Barka ‘Amarya, ya garin munyi fushi tunda mu ba’a gaya cemu bikin ba ” Cewar Captian

Murmushi Basmad tasa “sanun ku gari lfy qlau ae nazaci Hajjo ta gaya maku ” kallon Hajar tayi da kanta ke ,k’asa “Hajjo damun baki sanar dashi ba ?” Ko d’agowa Hajar batayi ba ,bare ta basu amsa. Shiko Dr Samir tunda suka tsaya ‘agun hankalin shi ke ,kanta shi a yanzu ya hakura da ita duk ,da har cikin zuciyar shi yana jin zafin rashin samun ta, Amman kuma yana jin dadi had’uwarta da Captian don kuwa dashi ta ,dace yana da masaniya’ akan idan ta ‘auri Captian zataji dad’in rayuwar ta zata manta da komai, Amman shi ‘idan ta ‘aureshi babu abinda ze haifar mata sai tarin wani k’unci da ,damuwar zeyi ‘iya kokarin shi na ganin ya taimaki abokinshi wajen shawo kanta, har soyayyar sa tayi tasiri a cikin zuciyar ta, wannan shine halacin daze iya, yiwa ‘abokin nashi kamar yanda suma suka masa halaci shida mahaifiyar sa ‘alokacin da suke tsananin buk’atar taimako da ,d’auki..

“Yau kuma ko yar gaisuwar bazamuyi ba Hajjo naga kin b’ata rai kamar kina cikin damuwa hope lfy dai kow?” Captian ,ne yayi maganar

D’agowa tayi ,tana wasa da k’asan gelen ta , murmushin da bekai zuciba tayi “wlh babu ‘abinda ‘akamin kaina ke ciwo ,ina wunin ku?”.

“Allah sarki Allah ya sawak’e hope kinsha nagani dai kow ? “.

“Eh nasha kafun ,na fito me kuka zoyi abuja?”.

Dr Samir haka ,kurum yaji baze iya tsayawa yana kallon suba, don komai ma ze iya faruwa dashi matsawar ya ciba da kallon su “Hajar Allah ya sawak’e , idan kinajin ciwon sosai ,idan kin koma kisha panadol nyt insha ‘Allah zaki samu ,sauki” Abokina ,ni bari naje mota na jiraka , kasan ban cika tson tsayuwa ba “..

“Tow nima yanzu ,zanzo bazan jima ba sorry nashiga lokacin ka ‘Amman insha Allah yanzu ,zanzo mutafi “

“Karka damu ku gama hiran ku a tsanake ko 4 ne zamuje”.

“Tow nagode abokina”.

Har ze wuce ya tsinto muryan Hajar tana ” sai anjima Doc…”.

Batare da ya kalle taba yace sai kin dawo kusha biki lfy ni gobe zan koma”

Basmad ce tace ae ko Doc… Sai kajira anyi daurin aure tukun kakoma, gama card ,d’inku “..

Captian ,ne ya k’elk’ele da ,dariya “dama nace kajira mu koma tare kaki, yanzu ae ka jira”…

Murmushi Dr Samir yayi ,yace “sorry Basmad wlh ina da ‘aiki cikin kwanakinnan kwata ,kwata bana zama ‘aiki sunmin yawa yanzun ma Ummi ta ,tursasani ,nazo “..

“Eyyah tow babu damuwa Doc… Nama uziri , Amman idan munzo shan bikin Hajjo baka zo ba karkayi tunanin zamu ,ma ‘uzuri”..

“Ae dolen shima yazo yana babban abokin ,nawa ‘ai idan bezoba ,bani bashi”…

Murmushi Hajar tasa tace “Haba Captian kai, kobaka uzuri ,kasani lokacin bikin ,naka ya kasan ce kuma yana muhimmin wani abun ?”..

“Tow tayani tmby Kanwata , ae wannan saurayin naki besan uzuri ba”..

Hajar najin Dr Samir yace saurayin ta, ta wani hadarai ta sunkuyar da kanta…

“Ae abokin ,nawa ne bashi da kirki Hajjo” cewar Captian..

“Tow nikam barin shiga ciki, Dr kai yaushe zamu sha naka bikin ,ne ?”..

“Nima ,mota zanje na jira shi” murmushi yayi, yace Soon insha ‘Allah”…

“Allah ya kaimu “cewar,Basmad..

Hajar kam bata, sake cewa komai ba ,

Mota Dr ,ya koma basmad kuma ta shige ciki ,suka bar Hajjo da Captian..

Gyaran murya Captian yayi ,yad’an jingina da jikin motar,Basmad “Hajjo haryau baki ,bani amsa ba kince kuma zaki sanar da ,Dady duk abunda yace zaki sanar dani, Hajjo ina so ki sani ,ina son ki tsakani kuma da ‘Allah komai naki yamin , soyayyar da na keyi miki tamkar tafiyace mai nisa da na fara yinta wadda bata da lokacin yankewa har abada.na san burina zai cika matsawar ina tare da ke domin kuwa dukkanin burina yanzu bai wuce na samun ki a matsayin matata uwar ya’yana ba. Ina son ki fiye da gwal ko kud’i”..

Tsaki hajar taja cikin zuciyar ta, tace sai kuma kaje kayiwa ,wasu dad’in baki amman bani ba ,don ko nariga da nagama sanin halin maza ,na gama sanin dad’in bakin su, duk wannan kalaman banzan da kakeyi jinka ,kawai nake don ko Akram ya rigaka fad’an su, kuma ‘Akram ya gama b’ata duk wani d’a namiji a gurina, da mutun d’aya na yarda ‘a yanzu shin ma bawai nayarda, dashi duka bane, azahiri kuma tace..

“Ina sane da zance kad’an bani lokaci zakaji amsa ta ,na kuma gode , da wainan kalaman duk ni kadai”.

“Tow ina nan ina jira ,ai kad’an ma kikaji matsawar ina tare dake zakiji ,kalamai masu kwantar da hankali don , ko ina son ki ked’in kamar hasken wata kike mai hasken da ke haske idaniya ,haka kuma kalaman ki tamkar sugar suke ma’abocin zaki, tabbas kinyi kama da kan ki hakan ya sanya naji ina son ki, don haka bazan tab’a gajiya dake ba gurin ganin ,nasaki cikin farin ciki ,koda bazan samu hakan daga, gurin kiba”..

“Tow nagode Allah ya mana me kyau ni barin shiga ciki, gara kaje ka samu Doc…kar yayi ta jiran ka babu d’ad’i”..

“Tow habibty na ki kularmin da kanki, ki shafa min kan beby na “…

“Tow zataji sai anjima” nan sukayi salama..


Yau jumu’a yau ne aka d’aura ‘auren Basmad k’arfe biyun narana bayan sallar jumu’a…

Mutane sai shirin tafiya Kano kai amarya suke, motar da za’a kai amarya har tayi gaba tare da k’awayen amarya da su Hajar , iyaye ne kawai basu fito ba ,suma suna shirin fitowar ne…


Kano

“Ummi kinji yanda mukayi da ita ,ban samu lokaci bane shiyasa ban miki zancen ba, sai yau kuma ta shaida min cewa ita kanta bata san inda yake ba ‘a halin yanzu don tabaro shi a india ,gadai pic d’inshi ta bani “..

Karb’an pic d’in tayi ,ta fara kallo kamar shi d’aya da mahaifin su, Samir kamar anyi kaki “Allah Sarki Malan har ka mutu Allah besa ka cika burin kaba, wannan d’a bashi da maraba da Malan, insha ‘Allah mun kusan cika maka burin ka , Samir duk yanda za’ayi ka samu lokaci kaje indian pls “.

“Tow Ummi duk abunda kika ce shi zanyi ,farin cikinki nake so, amman Ummi ina so ki bani lbrn su meyasa tunda nake arayuwa ban san ,suba se yanzu ?”..

Dafa ‘Doc…Ummi tayi ,tana hawaye wannan ,wani sirri ne wanda mukayi alk’awarin bazamu tab’a bud’e shiba, bazan iya fad’a maka ,komai ba Samir kuma ina me umartan ka da, karka sake tambaya ta matsawar ,kana son farin ciki na , da kaje ka nuna mata cewa kai d’an Malam ne?”..

“A’a ban ,nuna mata ba ,naji ance gobe za ‘ayi shara’an k’arshe anan kotun dake jahar kano daga, nan kuma zata, zauna ,anan gidan yarin kano”…

Ummi ,na kuka tace “meyasa baka sanar da ita kokai waye ba Samir , idan sunzo ina so zanje na ganta , yanzu baka ganin akwai hanyar da zata iya fita?”..

“Duk yanda naso da ta gane waye ni ta kasa ganewa dalilin dayasa kawai na rabu da ita kenan, na nuna zan taimaka mata idan ta sanar dani ‘inda ,d’anta yake, gsky babu wata hanya da zata iya fita ‘Allah nekawai ya isa fitar da ita sai kuma wanda ya had’a mata wannan mugunta …

“Ni ‘idan ,naje zata ganeni zata san wacece ni duk da munyi shekaru da, dama bamu had’u ba, Allah yasa had’uwarmu yayi kyau Allah yasa ta cenza hali “.

“Ameen Ummi don kince karna sake miki zancenne amman da zanso jin labarin ta koda ,d’an kad’anne “…

“Hmmm Samir lokacin Sallah yayi barin tashi, idan ,nace zan baka labari babu ‘abinda zai haifar min sai tuna Malam aduniya kaf rayuwa ta babu ,labarin dana tsani tunawa irin lokacin da mukayi zama da Lubabatu , “tana gama fad’ar haka ta mik’e tayi dakin ta …..

K’arfe bakwai na magrib yan abuja suka isa kano , gidan su mijin Basmad aka ,kaita nan zata kwana da k’awayen ta washe gari a mik’a ta gidan mijin ta,.

Su Hajar na zuwa basu jima ba suka tashi ‘ita da Khadee zasu tafi subar sauran k’awayen tare da Basmad ,babu yanda Basmad batayi dasu akan subari sai gobe ,ba ‘amman suk’i suka tafi Khadee tayi gidan su Hajar ma tayi gida tare da wasu yan uwan su da zasu kwana cen gidan….

Suna isa tun daga bakin ,kofa Jawahir tayi kan Hajar ,tana murna ta rungume ,maman ,nata, tsam tsam kamar zata koma ciki , itama Hajar rungume tan tayi ,ta d’auketa suka shiga ciki.

“Beby na bani lbrn abubuwan da yaya Kalifa yayi maki bayan tafiya ta”..

Jawahir dake ,kan ciyar mamanta ,tana shan ice cream d’in data siyo mata ,tace” kullum ya dawo daga office yana fita dani ya kaini park ya dinga siyamin abun dadi , kuma idan dare yayi , shida Grandfather kafin su kwanta bacci sai sun tabbata nayi bacci ,da grand f ze tafi London ,nayi ta kuka, kuma ‘Ancle Kalifa ma yazo ya tafi abuja ya barni dagani sai me aiki shima nayi kuka, Mummy na dan Allah karki sake tafiya ki barni”.

Murmushi Hajar tasa ta kuma matseta ‘a jikin ta, tana shafa gashin kanta “naji Beby na bazan sake ba kow , sauka ,ki zauna kijirani ,nayi wanka saina baki tsaraban ki”….

Washe gari

“Doc…nannane gidan yarin ?gsky duk da banshigaba tukun ,nasan mutanen ciki suna cikin ukuba ” Eh Ummi nanne saima kin shiga ciki zakiga mutane abun tausayi muje”…

Suna shiga suka fad’i sunan wacce suke son gani aka musu ‘umarni da suje gurin da idan bak’i suka zo, suke zama, bayan minti k’adan saiga wani ya fito da wata mata, matar na ganin Ummi sai tayi k’okarin komawa ciki tana, “wlh bansan taba wlh muguwa ce kufitar da ita nashiga uku wlh muguwa ce nashiga uku idan baku fitar da itaba ,harku zata kashe”..

Muje zuwa

BY Dija_WaziriπŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 29

Wanda ya taho da ita ne ya daka mata tsawa “ke bama son haya niya da rashin hankali, kin gane kow idan zaki ‘iya ganunsu ga wuri ki zauna idan kuma bazaki ‘iya ba wuce muje ,don kina b’ata man lokaci “. Tana daga k’ofa ta rik’e kofa kamar wata mara hankali “ni bazan jeba ,ban san suba wlh mugaye ne kasheni zasuyi”. Nata maganar tana shirin komawa, jin muryan Ummi ne ya dakatar da ita.

“Lubabatu ina son kid’an bani lokacin ki, ni ba nazo nayi miki wani abu ,bane ,nazo ne don in sanar dake abu”. Jiki a sukwane ta dawo ta zauna tana kuka duk ta rame ta fita hayya cinta ‘Amman hakan besa ‘Ummi kasa gane taba don ko a mafarki taga fuskar ta zata gane.

“Hajiya kinga yanda ‘Allah ya dawo dani kow? Nayi nadaman rayuwan dana,jefa kaina ,abunda na shuka yau gasu ina ta girbewa, Malam yayi gsky da yace nabi duniya a hankali hak’ika na cuceku na cuci rayuwa ta kuma na cuci d’ana tilo na jefashi wata gurb’a taciyar rayuwa, najima ina ,neman ku ,keda malam na rasa inda zan samo ku sai yau gani gaku shekaru da ,dama don Allah kuyafe man “.

Wani d’aci da k’una zuciyar,Ummi keyi ,”ba wannane ya kawo niba Luba, cuta kam da zalunci kin man shi sai dai nace miki Allah ya saka man kuma, mu had’u a lahira ba komai bane ake yafewa, Malam kuma ,ki bari ‘idan kinje cen kunyi shari’a don ko ya rigamu gidan gaskiyi kuma bak’in cikin da kika cusa masa yana d’aya daga cikin abunda ya mutu dashi cikin zuciyar sa “..

“Inna lilahi wa inna ilaihi raji’un Hajiya karki cemin Malam ya rasu ? Na shiga uku ni Luba ya zanyi da hakkin bawan Allah ya zanyi da Hakkin shi, Hajiya ki taimaka, ki yafe man ko na samu sassauci a rayuwa ta, “.

“Hmmm yau kuma Luba ko kin manta kece Lubabatu ko ,kin manta irin cin zarafin da kika man ko kin manta cutar da kika man arayuwa ,yanzu kinyi wa kanki adalci bakiji kunyar cewa na yafe maki ba? Yanzu duk irin duniyar da kika nema ina riban shi? Jibi yanda ‘Allah yayi dake yanzu dama ‘Ai Allah baya barin wani don wani kuma duk wanda ya hau motar kwad’ayi tow ,wlh sai ya sauka ‘a tashar wulak’anci ,kinga yau naga riban hakuri na daman ,Malam yana ,nusar dani akan duk abunda ze saman ,na zama ,me hakuri da juriya ,yau gashi hakurina ya kaini matsayin da banyi tunanin zanje ba tun randa kika zalunceni, Abunda ya kawoni daman shine wannan yaron kin san shi? Ta mata nuni da, Dr Samir ,kanta dake ,k’asa ta d’ago takai ,idon ta kan Dr Samir”Eh na san shi, shine wanda yace ze taimaka man ,naga d’ana “. Yawwa tow ,wannan yaron ba kowa bane sai Samir wanda kike ikirarin baze tab’a arziki ba ko bayan ya girma kuma ze wulak’anta ‘a duniya idan kina raye sai kinga bayan shi, yau gashi dai shine wanda ze taimakeki ,kuma wanda ,duniyana tasan da zaman shi ina fatan kin tuna shi ?”..

Girgiza kai tayi tana, nunashi tana kuka” nayi kuskure arayuwa ta ki dena tunamin rayuwan da yariga ya wuce ,na zalunci wannan yaron yana k’arami na zalunce shi, hak’ika ni butulu ce ni ,nasan hakan Amman don Allah kuyi hakuri ku yafe man “. Murmushi Ummi tayi tace “a halin yanzu babu wannan zancen kin makara ‘dama ni bani da burin daya wuce naga kin wulak’anta ‘a duniya kuma nagode Allah daya nunan wannan rana ina raye Samir tashi muje” tad’au jakar ta zasu fice .

K’afar Samir Luba ta kama tana kuka tana cewa “don Allah ka rok’i mahaifiyar ka da ta yafe man ko zan samu sassauci ,cikin ziciyata ,Hakika na kasance yar adam ‘Amman butulu wacce ba’a mata ‘Alkairi ta kyautata, na kasance mace me son duniya fiye da komai a rayuwa na kasance mace mara juriya da hakuri mace wadda bata, tab’a yarda ,da k’addara ba mara zuciya , Hak’ika na citar da iyayen ka fiye da kowa ‘a duniya na jefasu cikin halin k’unci da, damuwa musamman mahaifiyar ka nafi cutar da ita , nasan bata ‘tab’a sanar dakai wacece ita ba, tow yau zan baka labarin zamana da ita tun daga farko har k’arshe ,Amman ina neman Almarman ka da karka gujeni ko bayan ka sani ka tayani rok’on ta da tayi hakuri ta yafe man”..

Ummi da takai bakin ,kofar fita ,taji muryan Samir “Ummi karki manta kece kike yimin nasiha ‘a kullum akan na zama mejin k’an yan uwana musulmai na zama ,me yawan yafiya na zama ,me hakuri akan duk wata damuwa ko bak’in ciki da hakurin abinda ina iya ramawa ko d’aukar fansa. “

Juyowa tayi ,tana kuka tace “Samir wannan matar ta cutar dani arayuwa bazan iya ,yafe mata ba” tabbas ,Samir na zalunce ta na cutar da ita batayi k’arya ba zauna ,na baka lbrn koma ” karki yarda na fad’a maki karki yarda wannan maganar sirrice danagi sai ke sai Malam sai Allah , sai kuma wainda mukayi rayuwa dasu a lokacin su kad’ai suka sani don haka, ki barshi ‘iya nandin”. Bazan iya ba Hajiya gara duniya tasan wacece ni gara na gaya masa irin zaluncin da nayi wanda yanzu nake nadama ” komawa da kallon ta kan Samir tayi , Samir ni kishiyar mahaifiyar kace ni Malam ya fara’aure kafun ita”..

    LABARI

shekaruna biyar da Malam ban tab’a haihuwa dashi ba, kuma bawai haihuwar ce banayi ba ‘a’a duk sanda na samu cikin zubarwa nakeyi saboda bani da niyan haihuwa dashi kuma badon komai ba sai don shi talaka ne, kuma ni a rayuwata babu wanda na tsana, sama da talaka na tsani talauci saboda nima ‘a cikinta na tashi,

Babu yanda Malam beyi dani akan ,nadena shan maganin zubar da ciki ba sai ,na nuna masa be isaba idan har nabari na haihu dashi me yake dashi da zai rik’e yaran , haka yaci gaba da hakuri yana zama dani ,yaki sakata ne saboda yana jin ,nauyin mahaifina don shine yayi sanadin samun aikin shi, tow ana tafe ana tafe ya bijiro man da zeyi aure babu yanda banyi ba ‘akan kar auren ya, yiwu Amman da ‘Allah ya tsarawa Hajiya shan wahala saida ta shigo gashi yar babban gidace ita, tafito daga family d’in manyan mutane masu karamci da mutunci ,

Mahaifin Hajiya babban malami ne a k’asar nan kowa yasan da zaman shi kuma babban atajirin me kud’i ne ,ita kad’a ya haifa , bayan ta girma Allah yayi masa rasuwa ya barmata dukiya masu ,yawa ..

Shigowanta, gidan Malam yasa komai ya cenza nadaga rayuwan mu , muka koma katon gida ci da sha babu wanda yake gagaran mu ,kuma duk ba dukiyar kowa bace muke wadak’a dashi face nata duk iya kyautatawa da girmamawa Hajiya naban ko ,kaya ta siya sai ta sayoman irinshi idan ta dawo daga ‘aiki duk motar data cenza nima irinta zata cenza man , idan ta d’auki albashi takan samman ,nasamu na kashewa tunda ni banyi karatu ba , ta d’aukeni da zuciya d’aya amman ,ni ba haka na dauke taba don ko duk abunda take man ban tab’a son taba, burina ‘a kanta shine ,nasan yadda zanyi na mallaki dukiyar ta, kud’in gadon ta kuwa Malam ta baiwa tace ya dinga juya mata su..

A kwana ‘atashi Allah yasa ta ,samu ciki, alokacin hankalina yayi dubun tashi don kuwa nayi alk’awarin yanda ban haihu ba itama bazata haihu ba , saboda tunda rayuwan mu ta cenza nake neman haihuwa ido rufe ,Allah be ,ban ba Hajiya ta fuskanci bana k’aunar ta ‘Amman hakan besa ta dena mun duk wani abu da take man ba ,tsakanina da ita habaice habaice maganar banza zagi kai ,k’arshe ma ciki dake jikinta cewa nayi bana Malam bane awaje ta samo shi, amman ahaka take hakuri dani, hajiya ta kasance me zurfin ciki da hakuri duk abunda nake mata be tab’a damun taba ko ,tanunan taji haushi, ni kaina ,nakan zauna, nace wace irin matace ita wacce bata fushi.

Ko ,kad’an Malam be tab’a nuna mana banbanci nida ita ba ,Amman ,ni kullum a korafi nake , yafi sonta a kaina don ita mekudi ce kuma suna cutar dani shida ita basa ,sona, cikin ta yana wata biyu nasan yanda nayi da wayo nabata wani ruwa tana sha bayan awa 3 cikin ya zube..

Ba k’aramin bakin ciki sukayi ba ita da malam haka suka d’auki ,kaddara sukaci gaba da addu’a , niko nayi farin ciki da gud’a.

Tow haka na dinga yi mata saida na zubar mata da ciki uku ana ukun nne suka gane , ranar da suka gane Malam ji yayi kamar ya kasheni ,don bak’in ciki har yayi niyar sakina ‘Amman Hajiya tace karya sakeni ya barni da ‘Allah ze saka masu , tow tundaga wannan lokacin muka fara samun ,matsala da malam ta b’angare Hajiya kuwa babu abinda ya cenda komai tanamun kamar da..

Bayan shekara uku Allah ya kuma bata wani ciki, shima babu hanyar da banyi ba ,Akan naga ya zube amman da rabon sai kazo duniya ,cikin yak’i barewa , haka tayi ta rainon abunta har Allah yasa kakai wata ,tara ta haifo ka , Malam ya soka kamar babu gobe soyyar danaga yana yimaka ,kaida mahaifiyar ka yasa nace saina rabaku dashi.

Dalilin dayasa naje wajen boka yamin aiki akanku , ku ,kenan yazama duk ,dukiyar mahaifiyar ka ya dawo hanuna ,nike juya kujeran kud’in gidan, Malam kuma ya zama yana tafin hanuna sai abunda nace yayi zeyi ,kuma nasa ya tsaneku , ko ganinku baya son yi , nakuma sa ‘aka, kori Hajiya daga, gurin aiki nasa boka yamin aiki akan duk inda taje neman aiki ,karta samu

Muje zuwa

BY DIJA_WAZIRI

TEAM AKRAM😜
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 31

Ya zama Hajiya ta shiga matsananincin kuncin rayuwa ,ta rana ‘abinda zataci ma gagaran ta yakeyi, Malam kuwa ko damuwa dasu bayayi don ko na hanashi zuwa inda ma suke.

Haka rayuwa taci gaba min cikin daula da walwala ,cikin jin dad’i duk wannan abunda ‘akeyi mahaifina besan komai ba, bayan shekara hud’u , lokacin kana da shekaru hudu da wasu yan watanni Allah yasa na samu ciki dad’i kamar ya kasheni , mahaifiyar ka , kuwa na dawo da ita kamar baiwa ‘a cikin gidan itace girki gidan wanke wanke ,wankina dana Malam duk ita keyi , duk irin cin zarafi da wulk’ancin da nike yi mata babu wanda ta, tab’a gayawa cikin dangin ta haka tayi ta hakuri dani a kullum dai takan ce Allah ze saka mata ba kuma zata ,tab’a yafe man ba nakan ce da ita gaba ta kaini karta yafe d’in dama ‘ae ban tab’a neman tayafe man ba…

Kaiko tsakanina dakai duka zagi hantara cin fuska , haka Hajiya tayi ta hak’uri da, dukkan wani hali nawa har Allah ya saukeni lfy na haifo san talelen d’ana ,namiji ,yasha gatan da bako wani d’a bane ze samu irin shi a lokacin gashi Malam yanaji dashi..

Bayan yarona ya cika wata ,takwas a duniya ,kwatsam sai ga k’anin mahaifin Hajiya ,yazo gidan ,namu ranar wata ‘asabar da yamma ,zuwan bazata yayi mata ,a farfajiyar gidan ya sameta, tana tik’an wanki ,kai kuma kana gefen ta kana wasa , ganin halin da take ciki ba k’aramin d’agawa kawunta hankali yayi ba , ita kanta saida ta ,tsorata da ganinshi bata so yazo ya ganta haka ba, don kuwa batayi niyar,kowa yasan halin da take ciki ba ,tayi niyar barina da ‘Allah ne idan munje cen yayi mana hisabi,

Kawun Hajiya ,dak’er ya shawo kanta, ta fad’a masa halin da take ciki tare da cin Amanar da mukayi mata, ni da Malam, da ita ‘alokacin batasan shima ba’a hayacin sa yake ba, kawunta bece komai ba, ya tashi ya tafi ,tare da sanar da ita zed’au mataki.

Ni kuwa duk maganar da sukeyi inajin su, jin kawun ta yace zed’au mataki yasa na tsorata dashi ,don ko naji mutane,na cewa bashi da mutunci ko ,kad’an kuma ‘asiri bata kamashi cikin sauk’i, Hakan yasa na yanke hukuncin guduwa da ,dukiyar gabaki d’aya tun kafun me afkuwa ta ‘afku…

Bayan ,nabar najeriya ban tsaya ko ina ba sai ijif anan ,na baza koli na, wata gobara ce da ‘akayi wanda yayi sanadin mutuwar mutane da yawa na wannan yankin da muke yasa na tattara na koma, indian anan na yada zango na,na nemi had’aden gidan haya na kama nida ,d’ana..

Ina wada k’a, da dukiya son raina da naga kud’in sun fara k’asa kawai na zuba rabin dukiyar a wani gidan karuwai da’ake ginawa ya zama gidan nawa ne da na wani babban mutun d’an kasar ,bayan angama ginin ya zamana mice babba ‘acikin gidan karuwan , gidana kuwa daga wannan ,namijin ya shiga yau sai wani sabo gobe, yaro na kam yana kallo ,tun yana d’an karami yake ganin maza na shigowa gidan mu, har ya fara wayo ,tunda yake ban tab’a sa shi yayi sallah ba, na maidashi arnen dole ,don ,nima tunda na koma cen ,na shiga wata sabuwan rayuwa na manta, menene musulunci (wa’iya zubillah).

Sunan da malam yasa masa na cenza ,masa, suna ya koma ‘akram ,.

Bayan mahaifina yaji labarin ,abunda na ‘aikata ma su hajiya, ciwan shi ya tashi dalilin hakan yayi sanadin rasuwan shi Amman kafun ya rasu saida ya tsine man,” ta k’arashe maganar tana kuka, gatan da, nasan ,nayiwa ‘Akram shine besa na manta da koyar dashi yaren shiba, kuma dukiyar da nake tak’ama dashi wannan mutumin ya zalun ceni ya gudu, da, duk wani abu dana tara ya zamana duk wani abunda nasa gaba sai ya lalace” Samir wannan shine labarin da mahaifiyar ka bata son ka sani, don Allah kuyafe man”.

Mutumin daya kawo tane yace “ke lokacin ki ya k’are ki tashi mu tafi ” tow malam d’an jirani pls ” kallon wulk’anci yayi mata ,yace “kinga nayi kama dame jira, ae wlh ke baki cencenci a yafe miki ba ,don ko ,ke acikin butulun ma za’a iya saki a sahun farko, dama tsiyar tala kawa kenan, ka d’aukesu da zuciya d’aya su kuwa su d’aukeka da zuciya biyu, dallah ni tashi muje” yaja hanun ta..

Shi dai Samir be iya cewa komai ba ya mik’e ya fice, koda ya fita be samu Ummi ba don ta, tafi..

BAYAN SATI BIYU

Hajar ce zaune a kan wata farar kujerar, k’arfe cikin lambun gidan su mai d’auke da korayen ciyayi da ni’ima mai dad’i ,wajen da ya zamo tama wajen hutawar ta kenan duk lokacin da ta dawo daga ‘aiki bayan tayi aiki ta gaji nanne inda ta saba zuwa ta zauna don tasamu nutuwa cikin zuciyar ta, jin muryan Jawahir na dariya harda shewa ne yayi saurin dawo ,da hankalin ta jikin ta, kara, sowar sune yasa ta saurin mik’ewa tana gera gelen jikin ta daya koma gefe daban, sanye take cikin riga da siket na kanti, rigan shara shara me k’aramin hanu ,har ana iya hango rigan ciki.

Fuskar ta ‘a d’aure ta dakawa Jawahir tsawa”bana hanaki kawo man kowa nan gurin ba Jawahir koba ,nace maki ,idan anzo nema na kizo, ki fara sanar dani ba?” Sorry Hajjo ba laifin ta bane laifi nane, saida tace zata, zo takira man ita nace a’a barin biyota muzo tare mun yi kuskuri kiyi hakuri” Caotian ya kama, kunnen sa yana bata hakuri..

Murmushi kawai tayi, tace “ba komai ya wuce, wuce kije ki d’auko hulanki, kisa bana hanaki fitowa ba d’an kwali ba?” Mami ne tace nazo na gaya maki Dady ,yazo ” tayi saurin barin gurin da niyar zuwa saka hula, kamar yanda Hajar ta umarce,ta shiko Captian guri ya nema ya zauna “Maman Beby sannu da hutawa ya ‘aiki ?”.

“Lfy qlau Alhamdullih ya office?”.

“Office lfy qlau “.

“Masha ‘Allah ina ‘abokin ka, kwana biyu ,ya dena zuwa hospital karb’an magani, kuma yasan sarai ba’a tsalakewa idan ,anfara Khadee sai fad’a takeyi kow miye dalili?”.

“Hmm kinji ba wlh ban san meyake damun gayenan ba, kwata kwata nakasa gane masa cikin kwanakinan tunda ‘aka saka ranar auren shi ,shi besan ba’a wasa da cutar daji ba”.

Ji tayi gabanta ya fad’i jin cewar ansa ,ranar Dr Samir, duk yanda taso ta b’oye damuwar da tashiga ‘a lokacin amman ta kasa , innalilahi wa inna ilaihi raji’un ,shine abunda kawai take iya furtawa cikin zuciyar ta, yanzu Dr Aure zeyi ,ya barta duk irin dakon sonshi da tayi, yanzu ya tashi a banza , anya tayiwa kanta ‘adalci da tak’i sanar dashi abundake ranta ,yanzu ga wata, tariga ta, dole ta jenye duk wata ,soyayya da take yi mishi koda hakan ze ,zame mata, matsala kuma dole ta nisan ceshi don kuwa had’uwa dashi wani babban tashin hankali ne a rayuwan ta dole ta gujewa duk wata hanya da ze had’asu dashi zatayi blockin .

“Hajjo tun d’azu fa nake magana kinyi banza dani lfy dai kow” da sauri ta dawo hankalin ta, wani yak’en da yafi kuka ciwo tayi , “lfy qlau Captian wlh na tuna wani abune , kace abokin ,naka ‘aure zeyi ashe kuna da babban biki Allah ya sanya ‘Alkairi”.

B’ata fuska yayi”ae harda ke ,kune ma kan gaba wajen d’aukar amarya kuda kuke ,k’anne”. Yak’en da yafi kuka ciwo ta kuma saki ‘a karo na biyu “Allah ya kaimu dai tukun darai da lafiya”.

“Ameen” tun daga Ameen d’in da yace be sake cewa komai ba ,sunfi minti goma ‘a haka batare da wani yace da wani uffan ba, “Hajjo ya batun ,maganar mu?” Cewar Captian.

“Munyi magana da, Dady jiya ,yace wai ranar jumu’a kazo, ka sameshi bayan sallar jumu’a …

Muje zuwaπŸƒβ€β™€πŸƒβ€β™€

By Dija_WaziriπŸ’‰

Team CJ😊
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DOCTOR HAJARπŸ‘©πŸ»β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 34

Hajiya ce tayi saurin dakatar da Captian “anya Junaid bakayi hauka ba kuwa, yau har lalacewa takai haka ,Samir fa ko ,ka manta waye Samir ne ? Tow ka shiga taitayin ka na gaya maka, ko ance maka, kai kad’ai ne kake shiga irin wannan yanayin arayuwa idan kaji na wani zaka maida naka ba komai bane, kul, kakiyayeni duk wani abunda zakayi ban yarda kayiwa Samir ba ,don ko ya wuce haka’a gurin ka”, ta juya da kallon ta kan Samir “kayi hak’uri Samir kaji ina jinka ” murmushi Samir ya saki “babu komai Hajiya nasan abunda yakeji sai munyi masa uzuri baya cikin hayacin sa “. Guri Captian ya nema ya zauna zuciyar shi na suya ,don dai Hajiya Mahaifiyar sace babu yanda ya iya da ita da babu abinda zesashi gaya mata magana ‘ahalin da yake yanzu don idonshi ya rufe baya ganin kowa sai Hajar.

“Hajiya Hajar macece me kamun kai da mutunci , batun yar kam wannan ba’ayi k’arya ba yar bata da uba Amman hakan ya farune a matsayin k’addara don zan iya cewa reping d’inta ‘akayi ” inalilahi wa inna ilaihi raji’un amman Samir meyasa, suka b’oye mana basu, sanar damu ba ?”.

“Tow a gsky ban san miye dalilin su na b’oye war ba Hajiya ,Hakan da sukayi kuma gsky ba daidai bane”. Wlh naga wautan su kaga yanzu Alhaji yace idan yana raye Captian be isa ya ‘aure taba ranshi yayi masifar b’aci don ahalin yanzu ma yace Talatu ze aura masa, kuma kasan tsaf ze aikata don shi ‘idan yayi magana guda ,d’aya baya kuma maimai tawa , kuma har idan yayi Alk’awari tofa saiya cika yake jin dad’i”.

“Subhanallah gsky abu beyi dad’i ba ‘amman da yafara zuwa yaji dalilin su kafun ya, yanke hukunci” tow kasan Alhaji da zafi an bashi, shawaran hakan yace bazeje ba ,Amman ,nikam gobe da safe idan yafita office zanyi kok’ari naje ,naji komai”.

“Yawwa hakan ma yayi Hajiya ‘Allah ya mana jagora ” ameen ,ni bazan shiga daga ciki zanyi sallah”.

Tashi ,tayi ta shiga ta basu guri, Captian da idon sa, suka cenza kasa zuwa jajazur kamar gauta, ya dubi Samir cikin kunan rai yace ” Samir yanzu ashe duk ,kasan wannan zancen kak’i sanar dani ? Miye anfanin abotar mu ,yanzu dama ‘akwai abunda zaka iya b’oye min aduniya? “

Samir ,rik’e gefen k’irjinsa dake masa wani ‘irin suka ,yayi ,yau sati biyu kenan yana jin ,naman jikinsa nayi masa wani ‘irin zafin daya rasa namiye gashi Doc…d’in dake duba shi na ciwan Cancer d’inshi ya fati abrod k’aro karatu, gurin Khadeen daya koma, ma tun ranar da ‘aka saka ranar shi da Salma be sake zuwa hospital d’in ba ya dena zuwa k’arb’an magani , idan yaji zuciyar sa nayi masa zafi yakan ,kira Dr aiman gida yazo ya dubashi tow, duk yanzu ya watsar da komai maganin ma ba kasafai yake shaba , ciwo nata cin jikinsa be sani ba gashi yanzu ko abinci baya iya ci kullum sai ruwan shayi .

Karfin halin magana yayi, ya kalli Captian “haba Junaid wannan shine adalcin da zaka man, karfa ka manta yariyar nan buduruwar kace , ya dace ace lokacin da kuka fara deting ka tambayeta wasu yan labarin ta da kuma yanda ‘akayi tarabu da mijin ta, tunda ‘ae kaganta da yarinya , kuma sau nawa ina ce maka, ka tambayeta kana cemin tow ka tab’a tambaya? Wlh wannan d’in ma ‘amana ta bani kade san girman amana babu yanda na iyane kawai yasa na furta kuma sena, nemi gafaran ta dalilin dayasa ban sanar dakai ba kenan “.

Dafashi Captian yayi da yaga ‘alamun ranshi ya baci kuma, kamar shima yana da ,wata damuwar da yake b’oyewa “na gamsu abokina kayi hakuri abun da ya faru d’azu wlh bana cikin hayacinane shiyasa, wai meke damun ka nifa tun randa ‘aka saka ranar ka ,naga kamar kana cikin damuwa kuma ‘akwai abunda kake boyewa ,wanda baka san kowa ya sani gashi duk, ka rame ” murmushi Samir yayi yace ” ka gama ji da, damuwar ka tukun zan gaya maka, koma miye ni yanzu burina be wuce naga komai ya daidai taba, Hajjo naban tausayi kuma, nasan kai kad’ai ne zaka rik’eta da’amana ba tare da wata, rana ka goran ta mata ba, ni zan wuce gida bani da isashen lfy “.

Tare suka fita saida ya rakashi, har bakin mota sannan ya dawo gida…

      Washe gari

Da misalin k’arfe shabiyu na ,rana Hajiya da Fadila sukayi shirin zuwa gidan su Hajar bayan fitan Abba.

Basu wani jima ba suka isa kofar gidan su Hajar , me gadi ne yazo ya bud’e musu k’ofa ,suna fita sukaci karo da kakar su Hajar itama shigowar ta gidan kenan, tana sanye da wata sufa ruwan ganye da ratsin blue tasa wani farin shijabi me hanu, ganin ta yasa hajiya Saurin fita daga motar har k’asa ta duk’a ta gaida ta sannan tayi mata bayanin kosu ,suwaye Kakar su Hajar da fara’a suka gaisa ,sosai sannan ta umarce su da sushiga ‘a falon k’asa ,suka zauna duka harda Kakar Hajar d’in ta umarci me aiki data kawo musu lemo da ruwa, sannan tahau sama ta kira su Ummi,.

Jawahir ce ta sauko daga sama da gudu tayo falon ta rungume Kakar , Maman Junaid kuwa tsayawa kawai tayi ,tana ta kallon yarinyar me kyau da ita ‘amman wai shegiya ce, ita ,tausayin yar cema taji ya kama ta, suna cikin Haka saiga Dad, da Mami sun sauko har k’asa suka duk’a suka gaida Kakar sannan suka nemi guri suka zauna bayan sun gaisa da Mahaifiyar Junad.

Falon tsi yayi Jawahir na cinyar Kaka tasa Alawuya ta ,kaita gurin Hajar “sanunku sunana Hafsat nice mahaifiyar Junad wanda yake, neman yar wurin ku, nasan zakuyi mamakin dalilin daya sa jiya ba’a zo ba ,nan ta kwashe lbr ta basu, shiru Dady yayi kawai ya tsaya ,yana ,nazari sai daga bisani kuma ya bud’e baki yayi magana ” duk naji batun ki Amman da yayi hakuri yazo da kanshi, wa inda ‘suka zo neman auren yarinyar nan duk saida nayi bayanin komai sannan daga bisani ,naja d’aya daga cikin su na sanar masa dakomai ,kuma nace ya sanar muku ,don wannan abu ba ‘abin boye wa bane tunda harka ce ta ‘aure”.

“Tow nima dai abun ya d’aure min kai , gsky nasan babu yanda za’ayi ace baku fad’a ba shi Alhaji Samani ne be sanar damu ba,” gsky tow sai dai shid’in ae nayi tunanin yaron ya sani ze iya sanar muku ” wlh be sani ba duk muma jiya mukeji “

Dady ,yayi wa Hajiya bayanai sosai gome da rayuwan Hajar na baya kuma ta gamsu da ,duk abunda ya fad’a mata, takumayi Alk’awarin sanar da ‘Alhaji komai duk abunda suka yanke zata sanar musu ,takuma ,matuk’ar tausayawa Hajar , sunyi magana sosai sannan daga bisani suka, tashi suka ,tafi….

“Tow Alhaji kaji abunda ya faru yanzu miye abunyi , duk mahaifin ta yamin bayani kuma na gamsu, kasan k’addara tana iya fad’awa kan ,kowa kowa da tashi k’addaran tow ita natane yazo da hakan, don Allah kayi hakuri a ‘aura wa yaronan yarinyar nan ,shine kawai kwanciyar hankalin mu ,tunda abunnan ya faru wlh duk ya susuce yana ,neman lalacewa ko abinci ma ya dena ci gashi baya samun bacci kullum cikin tunani , tunda kayi tafiya, yau satin ka biyu kenan ,naka sa, samun, nu tsuwa” Hmmm Hafsat kenan tow ni ‘ina ruwana ya mutu ma, mana idan shi besan ciwan kansa ba tow ni sanani ,don haka ,ki sanar dashi na bashi nan da sati 1 idan be kawo min wata, matar ba tow ni zan aura masa, wacce naga dama na gama ,magana” fuuu ya tashi ya bar falon..

Sakin baki Hajiya tayi kawai tana kallon shi harya fice, cikin zuciyar ta, tace Allah ya kyauta

Kwance yake ,kan gadon shi duk ya rame yayi wani ‘iri kamar bashi ba, wayan shine a hanunsa tun safe yake ,kiran Hajar amman tak’i d’auka yau sati guda kenan bata d’aga wayan shi tun randa yakira tace masa, surabu kawai tunda iyayen shi basa, son auren , har yanzu be hak’ura ba dad’a kira yakeyi dayaga bata da niyar d’agawa saiya tura mata test.

_ Hi Hajjo don Allah ki d’auki waya ta ,wlhi na son ki bazan iya rabuwa dake ba , so tamkar rayuwane, ba ko yaushe yake zamowa abu mai sauk’i ba haka kuma ba’a koda yaushe yake wanzar da farin ciki ba, to amma mene ne zai sa matsawar muna raye da, rai da lfy za mu yanke alak’ar soyayya a tsakanin mu? Har zuwa yau babu kamar ki a cikin zuciyata domin kuwa jin muryar ki a kullum na rubanya adadin soyayyar da na keyi miki a cikin ko wane dare ko safiya .karda ki rabu dani don Allah, domin hakan zai iya sanyawa na zamo mutum ,mai rauni a rayuwata. Ki sani ‘ina sonki_

Ya tura, mata sannan ya mik’e ya shiga toilet don watsa ma kanshi ruwa kozai ji dadi cikin zuciyar shi..

Salma ce zaune Falo tana kallon zee word ,jin salamar Dr Samir ne yasata kashe Tv yayin data ‘amsa salamar , shigowa cikin falon yayi, ya zauna bashi da wani walwala yana sanye da Jalabiya ga dukkan alamu daga bacci ya tashi wurin k’arfe Biyar “ina Hajiya?” Ya tambaya ” tun wurin 4 ta, tafi gidan k’awar ta taje zatayi maka, magana ma tasamu kana bacci, tow bata d’agaka bane saboda tasan kayi aiki ,kagaji kana buk’atar hutu ” ok ,kawo min Coffe ” mik’ewa tayi, ta kawo masa, tana bashi ya mik’e zebar falon saurin tsaidashi tayi “yaya pls ina son magana dakai ” fuskar shi babu walwala ya dawo ya zauna “ina jinki”.

Saida ta d’anyi jim kad’an sanan ta kaleshi tace “yaya dama ‘akan batun auren mune kaga ‘abu sai matsowa yakeyi shiyasa naga ya dace nasanar dakai, wasiyar Aunty Jamila ” tana fad’ar haka sai tayi shiru , sai alokacin ya ‘ajje coffe d’in hanunshi ya dubeta sosai “ina jinki “.

“Dama Aunty Jami tunkan kuyi aure idan muna zaune agida, muna hira idan mun sako hiran aure sai tace min ita ko mutuwa tayi bata yarda ,wani k’aninta ya ‘auri mijin taba , kuma ita har cikin ranta , take fad’i ni kuma tun alokacin ,na d’aukar mata ‘alk’awarin hakan bazai tab’a faruwa ba insha ‘Allah kuma ,kafin ta rasuma saida ta jadadamin cewar narik’e Alk’awari karnaci amanar ta, kaji dalilina yaya don Allah kasan yanda za’ayi ka fahimtar da Ummi , kaima nasan ba sona kake ba kawai biyayya zakayi pls Yaya don Allah katayani cika wannan alk’awarin dana d’auka “.

“Tow Salma tun farko meyasa baki sanar dani ba ? Ni yanzu bazan iya tunkaran Ummi da wannan maganar ba, gsky garama ke ,kisanar mata da kanki”.

“Yaya kana ganin haka babu matsala kana ganin wani abu ,bazai iya faruwa ba gsky bazan iya fad’a mata ba “.

“Tow zan duba nagani zan san abunyi ” ya mik’e ya fice , shi kad’ai yasan halin da yake ciki, don jikinsa na bashi ma zeyi wuya Salma ta zama ,matar sa

By Dija_waziri
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJAR πŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 35

Hajar ce zaune cikin lanbun gidan su tana hutawa ,tana sanye da riga da wando na kanti, sai ta d’aura wani boyfriend jacket akai ,kanta sanye da wani hula me kamar toban ,ta kishin gid’a kan wani kujera tana karanta wani ,inglish novel me suna happiness at last gefen ta wani d’an madai-daicin table ne ta ‘ajje Apple da kilishi, tana karatu ,tana d’an ci a zahiri kowa ya ganta baze tab’a tsamanin tana da wani damuwa ba , amman cikin zuciyar ta,ita kad’a tasan me take ji.duk da ‘acikin kaso100% na damuwar ta ,ta cire kaso 70 a ciki don Doc…yace ta rage sama kanta damuwa idan ba haka ba zai ,iya haifar mata da wani damuwa ,a kullum takan godewa ‘ubangiji daya bata ,tawakali da yarda, da k’addara ‘akan duk irin yanayin da zata, tsinci kanta , hakan yasa duk irin abunda ze sameta ‘a rayuwa takan yi k’okarin ganin ta danne shi.

“Sister ” Kalifa ya kira sunan ta ,da sauri ta d’ago ta kalle shi “na’am bro ya work d’in har ka dawo ne ?” Aiki gashi ‘inata fama yanzu nakama o shigowata kenan ma, Naga wannan friend d’in, naki yazo shine nace bazan kira mishi ke don ,nasan kinanan gurin ke, dai lanbu ya ‘aure ki, kullum idan baki zoba ,baki jin dad’i, ya naki aikin likita bokan turai, ae wannan aikin saike da Dady mukan muna office “ya fad’a ‘a zolaye ,murmushi ta saki tace “Aiki Alhmdulh ae kai ragon, namiji ne shiyasa bazaka iya’aikin likita ba “Habawa ,wlh kinsan duk ,da ke yayatace idan ‘an had’amu fad’a kin san kezan cuta ni kawai ‘aikin likitanne banajin yi barin shiga daga ciki ,kije bak’on ki na jira ” tow sai nashigo wai waye bak’on ,nawa ne?” Wannan likitan Dr Samir yake, kowa tow shine yazo” ok pls idan kafita kace yazo inanan ya sameni ?” Ok tam” ya wuce ita kuma, taci gaba da karatun littafin ta,

“Hajar ” saurin firgita ,tayi ta juyo da sauri ,tana “wlh ka razanani ” tow ba dole ba nafi mintuna ina maki magana kin maida hankalinki ,kan novel ke har kina ma da lokacin karatun ,novel?” Wlh ban tab’a karan tawa ba wannan shine firts tima d’ina da na fara karanta Novel shima wlh gurin Basmad na gani ,itace ma’a bociyar karatun novel ,shine fa ta ban dak’er na karb’a wlh ” lokacinne dake ae ni fushi nakeyi dake yau wajen 1 month kenan rabona da naganki, kod’an gaisuwar da mukeyi awaya ma yanzu kin dena ko laifi nayi?”

“Hmm Dr Samir kenan ,ni bance nayi fushi daikai ba sai kai zakace kayi fushi dani, ko ka manta ranar ka’ aka sa ‘amman ko kabugo ka gaya min ,ni meyasa bance ina fushi dakai ba?” Murmushi yayi, yace “ae gani ,nayi na sanar da mijin ki kuma dama shiya dace ace ya sanar miki” nan da nan ta had’e rai tace “mijin wa ‘an shafa mana fatiha dashi ne ko yaya da zakace mijina karka sake fad’an haka don kuwa ni ba mijina bane , kuma naga kafun ,na sanshi kai na fara sani don me sai shi ya fad’a min?” Tow Ran mata ya b’aci fa daga magana har kin wani cenza fuska ,ae idan be zama ba ze ,zaman, nan bada jimawa ba, “bata sake ce dashi komai ba tayi shiru taci gaba da karatun , ta da yaga bata da niyar magana shima sai yayi shirun , ya mik’e Ya nufi gurin wata bishiyar mangoro daf da inda suke a zaune, hannu yasa ya tsinko ganyen mangoron sannan , ya juyo ya fuskan ceta sosai yace “Hajar pls ina son ,magana dake ,kuma nasan bazakiyi min ,musu ba ina kuma fatan ki fahim ci abunda zan gaya mi….” Kafun ya k’arasa tace “idan akan abokin kane bana son jin komai , don munriga mun gama, magana dashi nace yayi hak’uri ya bi umarnin iyayen shi, tunda nid’in ce ba aso ya had’a zuri’a dani ,tow na fasa yaje su bashi wacce tafi dacewa dashi, mutuncina dana iyayena ,nike nema ‘aduniya bani da tamkar yasu ,sune kad’ai zasu iya zama dani aduk irin halin da zan shiga’a rayuwa don haka bazan so naga ‘anci mutuncin suba Doc… Ada na fara son abokin ka tow amman ayanzu gsky bana son shi kuma bazan iya ‘auren shiba sai dai kuma ban san k’addara ba , don Allah idan har zancen sa zakayi ,kayi hakuri bana son ji” shiru Dr Samir yayi, ya kasa cewa komai don kuwa zancen zeyi mata komawa yayi, ya zauna ya fuskanci kujeran da take zaune “kiyi Hakuri Hajar kiyi masu ‘uzuri wlh ba laifin iyayen shi bane duk wannan matar da take son shine take had’a komai, amman wlh ,harga ‘Allah mahaifiyar Junaid na son ki don kuwa ita ‘abunda ,d’anta keso shi ‘itama take so , kiyi hakuri ” kaga Dr Samir naface maka bana son maganar sa don Allah karabu dani, ae bakaga ‘abunda sukayi ma iyayena ba ,dole kazo bani hakuri ” kafun ya bud’e baki yayi magana yaji muryan Jawahir ta nufo gurin da gudu tana dariya, dalilin daya sa ya kasa magana kenan, jikin Hajar ta haye tana dariya “Mummy kinga Ancle Kalifa ko, ya tsorata ni ” tunda ta shigo ,gurin Dr Samir yasa mata ido wannan shine karo na farko daya fara ganin ta, ya rasa dawa take masa kama don tunda yaga fuskar ta ya fara tunanin akwai wanda ya tab’a gani suna kama da ita ‘amman ya rasa ‘a ina ya tab’a gani, dukyanda yaso ya tuna ya kasa , kalon ta yayi ,ya kalli Hajar yaga itama suna mugun kama da ita hakan yasa ya gane cewa itace Jawahir lokaci guda yaji son yarinyar har cikin ransa har yana Jin inama shine mahaifin ta, yaji ta shiga ransa ,sosai wani b’an gare na zuciyar sa kuma ya fara jin tausayin yarinyar, idan tagirma tasan matsayin ta ya zataji? Gsky mahaifin ta ya gama cutar, ta’arayuwa ‘ayau daze ganshi da saiya kwatar ma Hajar hakkin ta nacin zarafin da yayi mata, yanda yaga Hajar da yar tata suna wasa da, dariya sai yaji sun bashi shi’awa yaji ,inama ‘ace Captian be ruga shiba da ya ‘aureta ya kuma gina musu wata rayuwan wanda yafi wanda suke ciki jin dad’i amman hakan baze tab’a yuwa ba don kuwa ,ko mutuwa zeyi baze tab’a furta mata yana son taba, tunda har abokin shi kuma ‘aminin shi ya riga shi, duk da yana da tabacin cewa koda basu samu, matsala da Captian ba yau ,yace ita yake so zata iya fasa ‘auren Captian ta aure shi amman baze tab’a bari hakan ya faru ba, satar kallon su yakeyi suna d’an hiran su irin ,na Uwa da ya, “Hajar wannan itace Jawahir d’inki ?” Ya tambaya, sai alokacin ma ta ,tuna da ashe fa yananna da murmushi ta bashi amsa “Eh itace bama kama Kama kow” ita kuwa jawahir tsireshi da ido tayi tana ta kallon shi “A’a kuna mugun kama da ita sai dai tafiki ,kyau sosai yar tunda naganta naji tashi raina wlh ki barmin ita “dariya Hajar tasa, sosai rabon ta da ‘ariya irin haka har ta manta “tow kar ka damu idan ka shirya kazo ka d’auke ta, amman fa bata ji” Jawahir fuska ‘a daure tace “Mummy ni bazan bishi ba ni gurin Dady na zaki, kaini kince min ,munkusa komawa ‘kuma haryau bamu koma wajen shiba ” kallon ta Dr Samir ya tsaya ,yana yi ,yarinya k’arama ‘amman sai wayo “zo Jawahir” ya kira sunan ta, tun da yashigo ta, tsireshi da ido taki saukewa “ni bazan zoba ” Hajar ta ,tsani Halin Jawahir na tsayawa tana kurawa mutane ido ,dama ga idon manya manya tayi maganar tayi maganar har ta gaji Amman Jawahir bata denawa ita kuma ‘abun yana k’ona mata rai wasu ma sai ,suyi tunanin bata mata fad’a ,daka mata, tsawa tayi “ke Jawahir dan gidan ku ban hanaki kallon mutane cikin ido ba ? Kuma sa’an kine shi da zai kira ki ,kice bazaki ba, zaki Wuce ko sai nai ball dake mara kunya kawai” Babu musu Jawahir ta ,wuce, taje gurin Dr Samir” Haba Hajar ki dinga mata uzuri mana yarinya ce fa sai da lallab’i” barni kawai Doc…sau nawa ina hanata irin haka she karunta nawa yanzu 10 fa take nema gara na dinga yi mata fad’an idan ta kama,ma harda, duka zata shiga hankalin ta ,sam yarinyar nan bata gudun b’acin raina duk abunda na hana ta nad’an kwana biyu ne zakaga taci gaba da ‘abunta saboda ta rainani” haka zaki ci gaba da hak’uri komai ,mai wucewa ne ,wata rana baza tayi ba” Hajar batace komai ba tad’au ruwan faron dake gefen ta, tahau sha ,shiko ,kama hanun Jawahir yayi ,yace “sorry Beby kinji , ki d’inga jin maganar Mum d’inki kinji kow beby ne nima daga yau Dadyn kine ina kina sona?” D’aga masa kai tayi alamun eh , yayi murmushi yace “gud girl me jin magana , wane school kike zuwa ?” Lokaci guda taji ta sake dashi zama tayi kusa dashi tace “Turkish nike zuwa ‘amman ,Mummy tace ,cireni zatayi “a shagwab’e tayi maganar “A’a meyasa Mummy zata cire ki?” Saboda banyi kokari ba nazo ta 3 don Allah Dad kace tayi hakuri Allah next ,tima zanyi kok’ari” tow karki damu zan gaya mata ‘amman ki tabata zaki dena wasa, idan kika zo ta 1 nima ‘zan baki wani abu amman bazan gaya miki, ko miye ba” tsale tayi ,ta rungume shi ,insha Allah na dena wasa kayan wasan ma ,Mummy ta b’oye su ” tow yayi kyau ajinki nawa ?” Primary 5″ gud ashe bebyn tamu babba ce idan kin gama karatu me kike son ki zama?” Da sauri tace “Barrister nake so irin ,na Aunty Basma” meyasa kike son zama Barrister?” Shiru tayi batace komai ba sai da ya sake tmby sannan fuskar ta babu walwala tace”saboda na kama ,mutumin da kullum nakeji mummy nayi masa ‘Allah ya isa tana cewa ya cuceta kullum ,kuma idan dare yayi sai tayi kuka , shiyasa zan kama shi na kulle shi saboda ya dena zuwa cikin dare yana sa ,Mummy na kuka shiya sa nakeso na zama Barrister” Hajar dake ,karatun littafi kasa karatun tayi ,ta tsaya tana jin yarinya karama kamar Jawahir sai d’an banzan wayo Ashe tana kula da, duk abunda takeyi kenan ,abun na damun ta , kallon Dr Samir tayi suka Had’a ido ya girgiza mata kai, sannan ya koma, da kallon shi kan Jawahir ” tow Beby zan tafi gida ‘Amman gobe zan dawo na d’auke ki muje musha ice cream ina zaki bini” da saurin ta ,tace “eh zan biki ” shafa kanta yayi ,yace “haka nake so Allah yayi miki Albarka ” ya mik’e sukayi salama da Hajar ya tafi bai zarce ko ina ba sai gidan su Junaid d’akin shi ya shiga ya sameshi kwance kan gado shi ba ,bacci yakeyi ba ga dukkan alamu ya fad’a kogin tunani ,ne don Har Dr Samir ya k’araso cikin d’akin besan yazo ba, gefen daya zauna kayan abincin da ‘aka kawo ma Junaid ne ,na rana be tab’a ko, kad’an ciki ba,”kai ” Dr Samir ya tab’o shi, sai a lokacin yayi saurin dawo da hankalin shi ” Junaid ka dena sawa kanka damuwa haka fa, ka tashi kaci abinci ” Samir ya ‘ake ciki bazan iya cin komai a yanzu ba matsawar banji me ake ciki ba ,bazan tab’a samun ,nutsuwa ba Samir ina son Hajjo ina k’aunar ta ,zan iya Mutuwa idan har na rasa ta ka taimakeni ” zan taimake, ka Junaid Amman sai kaci abinci tukun ” kayi Alk’awarin idan ,naci zaka taimaka min “yes nayi ak’awari” d’aukan abincin yayi ,yaci kad’an yasha ruwa sannan ya dawo ya zauna kusa da Samir “tow ya kukayi da Hajjon ” duk yanda sukayi Samir ya kwashe ya fad’a masa , “ya ilahi duk Abba ne ya jamin yanzu ya za’ayi? ” tow gsky mafita d’aya ce Junaid shine kawai hanyar da nake tunanin komai zai koma daidai, kuma shine hanyar da nake tunanin Hajjo taza iya komowa gareka “, tow ,wace hanya ce Haka Samir wlh zanbi matsawar bazan cutu ba” tow hanyar dai ‘itace Zamu had’a plan ,ne da wani doctor a hospital d’in da nake aiki, ace ma su Abba kana cikin wani hali zaka iya rasa ,rayuwan ka cikin awani ishirin da hudu matsawar ba’a maka ‘abunda kake so ba ita kuma hajar mukira ta muce gaka zaka mutu ,ta, taimaka mana ka gane?” Yes na gane amman kana ganin babu wata matsala ?” Insha Allah babu matsala ” tow tashi muje bana so ma Hajiya ta lek’o ta..

By Dija~WaziriπŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Na sadaukar da wannan shafin gareki, k’awar arziki action beby tnx for ur love care and support Allah ya barmu tare 😘😘

Chapter 36

Bayan awa biyar

Hajiya ce ta fito daga cikin d’aki da sauri , a burkice, Abba ta samu zaune a falo yana karan ta wasu takardu ganin ta yasa ,shi saurin ajje takardun ya cire tabaron idon shi, “lfy Hajiya kika fito da wannan uban saurin haka?” Ba lfy ba ‘Alhaji Junaid yana ‘asibiti ba lfy ,yanzu samir ya kira ya sanar dani” dariya Abba yasa, yace “kai wlh kunban dariya wai ko ,kun manta nariga ku zuwa duniya, nifa ba yaro bane ,ni zaku had’a ma plan ba rashin lfy ,yakeyi ba k’arewa ‘asibiti ya d’aura wa kanshi, ya mutu ni be shefeni ba ” ya maida gilashin sa ya cigaba da, duba takardun sa, sakin baki Hajiya tayi tana kallon shi “yanzu dai Alhaji kana so kace min had’a baki, mukayi kow? Saboda gani mara hankali sai na bari a had’a baki dani ace d’ana bashi da lfy kow? Tow kar ,kaje asibitin ,ni zanje naga halin da, d’ana yake ciki, kuma ka sani wlh d’ana ya mutu ,ta dalilin ka bani bakai na fad’i maka , ta zari mayafin ta, ta fice .

Tana fita ya ‘ajje takardan hanun shi ya fara, tunani tunda yaga Hajiya ta, tayar da hankalin ta yasan dole akwai matsala, kuma yasan babu yanda za’ayi a had’a baki da ita ‘ayi masa k’arya dole ya tashi ya bita ,tun kafun ta pfice, ba shiri ya d’auki hulan shi ya fice yana fita , ya iske motar zata bar haraban gidan megadi har ya bud’e musu kofa, da sauri yasa ‘aka tsaida Drive yaje ya shiga suka tafi.

Mintina kad’an ya kaisu Aminu Kano, basuyi wata ,wata ba suka nufi b’an garen da Samir yace musu an kwantar da ,Captian , suna isa Dr Samir ya nufo inda suke, hankalin shi a mugun tashi “Sannu Hajiya har kun iso?” Hajiya na kuka tace “Eh Samir ya jikin junaid ,d’in ?” Tow gashi nan dai likitoci na kanshi tun d’azu ” subhanallah Allah ya bashi lfy zamu iya ganin shi?” Abba ya tambaya ” gsky a halin yanzu bazaku iya ganin shiba ‘Alhaji sai dai zuwa ‘anjima ” tow ,wai meyake damun shine ” bari yanzu likita ze fito zeyi muku bayani” kafun Samir ya k’arasa maganar ma likitocin suka fito daga cikin d’akin da Junaid yake “yawwa ‘Alhaji gama likitan ya fito, Dr Jalo kazo kayi musu bayani ” Dr Jalo yana murmushi ya k’araso inda su Hajiya suke tsaye , yace “Dr Samir wainannan sune iyayen yaron ?” Eh suna Dr Jalo kayi musu bayanin komai ni banaje office na dawo” yana kaiwa nan ya wuce yabar su Hajiya da ,Dr Jalo “likita meke damun d’ana don Allah ka sanar dani ?” Abba ya tmby hankalin shi a tashe , hanunu Dr Jalo ya bashi suka gaisa ,sanan yace “kwantar da hankalin ka ‘Alhaji muje office zan sanar daku ,komai ” babu musu ,sukabi ,bayan shi har cikin office d’in shi ,suna shiga ya basu gurin zama shima ya nemi guri ya zauna yana fuskantar su ,sannan ya fara musu bayani”Alhaji d’an ku yana cikin wani hatsari zuciyar shi ta kunbura kuma zata iya fashewa cikin a wanin tara idan har baku bashi abunda yake so ba, don alamu sun ,nuna yana cikin damuwa ,wanda yayi sanadin kunburin zuciyar sa ,a lokacin da ,Dr Samir ya kawo mana shi ya kawo shine a sume ko nufashi baya iyawa , dak’er muka samu ,muka ceto rayuwan shi saboda haka zeyi wuya, ya rayu cikin a wanini tara nan gaba matsawar baku bashi abunda yake nema ba, ina ganin yakamata ,koda baku san me yake nema ba ya kamata ku bincika, kafun awa tara, idan kuna son rayuwan d’an ku” Abba yana sharara wani uban gumi ya cire hulan kanshi yana share zufar daya kwaranyo masa, Hajiya na kuka tace “ae kaga ‘abunda nake gudu yanzu sai kasan yanda zakayi ” kallon Doc..Alhaji yayi ,yace “mungode Doc…kuma insha ‘Allah zamuyi abunda kace kafin lokaci ya cika ” ya mik’e yaja Hajiya zasu fice Dr Jalo yace “Allah ya bada sa’a ya kuma bashi lfy “Abba yace Ameen suka fice ….

Hajiya wuri ta nema ta zauna tana sharan kwala ‘Abba ko sai kaiwa da kawowa yakeyi mafita kawai yake nema, da wani ‘idon zaije ya tunkari ‘iyayen Hajar mezai ce musu, taya zasu yarda haka ya dinga sa k’awa da kwancewa yana ciki haka yaji an dafa shi da sauri ya juyo ,yaga Samir ” Sannu Alhaji ” Samir ya fad’a , Abba idanun shi sun kad’a sunyi jawur yace “yawwa Samir Doc.. Yamin bayanin komai yanzu ya kake ganin za’ayi , miya dace muyi?” Gyara tsayuwa Dr Samir yayi, ya saki murmushi, tare da farin cikin sun kusa, samun ,nasara .

“Alhaji ni a ganina ‘abunyi shine kuje ku samu iyayen Hajar ku fahimci juna, ku basu hakuri, kuma ku fahim tar dasu halin da Junaid ya shiga, ina ganin shine kawai mafita” shiru Alhaji yayi, yana kallon Dr Samir be ce komai ba. Sai daya d’an jima sannan yace.

“Kana ganin iyayen yarinyar zasu amince kuwa ?” Kafun Dr Samir ya bashi Amsa Hajiya ta mik’e tana kuka tace ” Alhaji Idan zakazo muje gidan su yariyar nan kazo muje ina Samir zesan da matsala ko babu shine iyayen, yarinyar ? Naga tun farko, kaine ka b’ata lamarinan , kabi abunda Talatu tazo ta d’aura ka’akai yanda ka b’ata sai kaje ka gyara nan gaba dai yanzu saura mana awanni bakwai , cikin sa kuma zamu iya rasa d’anmu idan bamu san abunyi ba”.

Abba kallon agogon hanun shi yayi ,yaga saura ‘awa bakwai ,kacal ya rage musu, kallon Dr Samir yayi, yace “bari muje mu dawo”.

Gudu suke ,kamar zasu tashi sama cikin mintuna kad’an ya kaisu gidan su Hajar , Abba ko bari megadi ya bud’e musu get beyi ba, ya bud’e mota ya fice , ya shiga ,gidan shida Hajiya sunko yi sa’a ‘Dady ,yana Haraban farfajiyan gidan yana zaune yana had’a wasu cemicals, ganin su yasa ,shi cire Safar hanun shi, ya umarce su da sushiga cikin falon bak’i, “Ina wuni Alhaji Galadan ci” Abba ya gaida shi ,da fara’a Dr Galadanci yace “barka da rana ya gida, da yaran ka?” Lfy qlau ya naka iyalan ?” Duk lfyn su qalau ince dai lfy na ganku da tsakar ,rana haka?” Kallon Hajiya Abba yayi sannan ya koma da kallon shi kan Dr Galadanci da, dariyan yak’e yace “lfy qlau ” tow masha ‘Allah barin sa’a kawo maka ruwa Hajiya ke, kuma ,muje ciki sai ku gaisa da Matar gidan” A’a Doc.. Karka damu nasha ruwa zauna kawai ,wata magana, nazo da ita ” tow ae babu damuwa ina jinka ” Doc.. Nasan banyi dai-dai ba ,ban kuma kyauta muku ba lokacin da yadace nazo ban zoba sai yanzu , ina ,neman alfarma da kuyi hak’uri lokacin abubuwa ne suka min yawa ” murmushi Dr Galadanci ya saki yace” mu baka mana laifin komai ba ‘Alhaji dena bamu hakuri ae ya wuce wannan zancen yau wata nawa Haka dama ‘Allah ya k’addara ba laifin ku bane” , nidai ‘ina k’ara baku hakuri Doc.. Duk da k’addara ce atemaka , ayi hakuri na gane komai kuma nafahimta, tunda Hajiya tamin bayanin abunda kace mata, kuma nagane cewa ,wannan abun daya faru da yarinyar ka ba son ranta bane kuma yana iya fad’awa kan kowa , yanzu ayi hakuri a dai-daita sai ‘asa ranar “. Dariya Doc..yayi ,yace “ae kun makara ,kayi hak’uri kawai Malam gsky na jima da fasa baku d’iya ta, kuma itama tazo ta shaida min cewa ko ,kundawo ta fasa kuma bata son yaron kaga kenan maganar baiko be taso ba kuyi hak’uri kawai ku bashi ‘ita wacce kace ka zab’a masa ” innalilahi wa inna ilaihi raji’un Doc… Don girman Allah kuyi hak’uri ka taimakeni , na tabbata idan har ka ‘amince itama zata janye pls Doc…” Alhaji Kayi hak’uri don Allah bazan iya baku d’iyata ba ,na fasa, bazan mata, tilas ba, bakuma zan musguna mata ba”, Abba ,be sake cewa komai ba sai faman duba ‘agogo da yakeyi awani biyar , ya rage musu.

Hajiya ce ta durk’usa gaban Doc.. Tana kuka tace “don Allah don Anabi Doc.. Ka taimaka, min duk wanda ya taimaki wani Allah ze taimake shi d’ana ze mutu awani biyar suka rage masa kacal idan bega yariyar nan ba ze iya rasa ransa don Allah ni ko bazata ‘amince ta ‘aure shiba don Allah ka, kirata muje asibitin da ita, doc ka dubi darajan haihuwa”. Lokaci guda, gaba d’aya jikin Doc.. Yayi sanyi darajan Hajiya ,yasa ze ,janye batun sa don kuwa yana ganin mutuncin ta ” tashi Hajiya ki ,koma ki zauna , na janye idan Alkairi ne zaman ta dashi Allah ya nuna mana, barin kira ta , sai dai gsky bazan mata ,tilas ba idan taga zata iya auren sa tow la ba’asa idan kuma tace A”a tow fa bazan tilasta mata ba” ya mik’e yashiga ciki, be jima ba ya dawo shida Mami da Hajar d’in duka, zama tayi gefen kujera, kanta sanye da himar ,cikin ladabi ta gaida su , da fara’a duk suka ‘amsa.

Dady ne ya dubeta sannan yace “Hajjo ina fatan dai ko, kin gane suwaye ” kanta ‘a k’asa tace “Eh Dady na gane su Allah yasa dai lfy ” ,yawwa lfy qlau ki ,kwantar da hankalin ki” nan yayi mata bayanin duk yadda sukayi “tow shine ,nike so naji daga ,gareki miye ra’ayin ki don,ni bazan tursasa miki ba, zaki yarda ki aureshi kow yaya ?” Shiru falon yayi ,kowa ya maida hankalin sa kanta, ita kuwa jikinta na b’ari bakin ta na rawa tace ” Dady na hakura dashi gsky bazan iya ‘auren shiba kuma bazan iya zuwa ko ina, na same shiba saboda” kafun ta k’arasa har Hajiya ta sauko daga inda take zaune ta durk’usa gaban Hajar idanun ta sun rune sun sauya sun koma ,kalan ja “Y’ata don Allah kiyi hak’uri ta dalilin ki d’anan ze rasa, rayuwan shi don Allah kiri hak’uri ki janye batun ki awa uku ,kacel ya rage idan har be samu abunda yake so ba zuciyar sa zata iya bagawa , a matsayina, na mahaifiyar shi ‘ina me neman gafaran ki da kiyi hak’uri ‘idan ma yayi mak’i wani laifine” gaba d’aya wani ,nauyi da kunyar Hajiya Hajar taji ya kamata, k’atuwar mace kamar ta, ace ta d’urk’usa tana, neman alfarma harda kuka, Haba Hajiya ki tashi wannan abu ,ko tsari babu ya zaki d’urkusa ma yar cikin ki haba ki tashi mana” Mami ta fad’i , tow me nema ,miye bazeyi ba Dole na k’ask’antar da kaina tunda nike ,nema kuma dama don kyautawa gsky ba’a kyauta ma yariyar nan ba ” suna cikin maganar ne suka tsinci muryan Hajar tana magana “Hajiya ko baki , durk’usa min ba wlh zanyi hak’uri abunda kika min yanzu banji dad’in shiba naji wani ‘iri kamar yanda bazan so uwata, ta durk’usa ma yar, yarinya kamar ni wai da niyar tana, neman alfarma ba haka, kema bazanso hakan ba mutuncin ki da ,darajan ki da k’imar ki da kuma ,karamcin kima sun isa na janye komai Hajiya ke suruka ce me ,mutunci me sanin yakamata, kuma ,me son duk abunda yayan ki ,keso na ‘amince zan auri d’anki da zuciya d’aya ” da gudu Hajiya ta mik’e ta rungume ta, tana shi mata ‘albarka ,Abba ma ‘albarkan yake zuba mata Dady da Mami duk sunyi murna kuma suna ‘Alfahari da yar su , sun san tarbiyyar da suka bata ,ba’a banza ba..

Hajiya ce ta duba’a gogon hanun ta, taga saura minti d’aya , da sauri suka tashi suka wuce asibiti harda Hajar amman banda Dady da Mami

Muje zuwa

By Dija_WaziriπŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

*INA KIKE MY JANNAT WANNAN PAGE D’IN ,NAKINE KEKE ,KAD’AI , KI SANI ‘INAJI DAKE πŸ˜ƒ KED’IN TADABAN CE😘😘

Chapter 37

BAYAN WATA D'AYA 

su Hajar sai shirye shiryen biki akeyi don tun sati uku daya wuce aka saka ranar ta da Captian ansa shine dede ,dana Dr Samir rana d’aya za’a d’aura ‘auren Samir dana Salma da kuma Captian da Hajar yau saura kwana 60 bikin su wata biyu kenan..

Ta b’an garen Salma babu ‘abinda take shiryawa don ita dama bason auren takeyi ba, haka shima Dr Samir Babu abinda yake shiryawa hatta ‘akwati Ummi ce me had’awa don shi besan komai game da ‘hidimar da ‘akeyi ba, shi cikin kwanakin ma sam baya jin dadin jikin shi gashi sam yak’i zuwa ‘asibiti , idan Ummi ta, tambaye shi sai yace yana zuwa , yanzu ko ,kaki yayi sai yaga jiki ,kuma kullum sai yayi aman jini guda guda ‘amman yak’i sanar da kowa har Captian be gaya mishi ba gashi sai ya dinga jin cikin shi kamar an hura masa wuta, duk ya rame yayi bak’i , Ummi ta kula da ramar tasa, amman sai ta bari akan, kodon zeyi aure ne yasa haka.


Zaune suke d’akin Junaid , junaid na k’irga wasu kud’i da zebawa Hajar yayi fari yayi frish ya k’ara kyau da k’iba , sai jan Samir yake da hira ‘amman Samir yak’i sakewa dashi suyi hiran kamar yanda suka saba” Samir wai meke damun kane kwana biyu kwata -kwata na kasa gane maka ? Kai ,naga kod’an murnan zakayi auren ma bakayi, ko aurene baka son yi ko, kuma Salman ce baka so?”.

Murmushi Dr Samir yayi wanda iyakanshi fatar baki ne ,yace “duk abunda ka fad’a basu ,suke damuna ba Junaid , ni dama kaji na tab’a maganar aure na?” Gsky ban tab’aji ba ” tow kagani ‘ina ganin ma zance wa Ummi a d’aga bikin ,nawa ” da sauri Junaid yace Akan me?” Saboda bana son barin yarinya k’arama cikin k’unci Salma bata sona ‘a yanzu saboda wasu dalilai amman ,nasan da zaran, na ‘aureta zata soni, tow bana so ,sai ta fad’a kogin sona kuma na barta kaga najefa rayuwan ta cikin hatsari , nafiso ta ‘auri wanda zasu jima suna rayuwa kuma su hayyafa subar masuyi musu add’u”.

Junaid cikin rashin Fahimta yace “Samir ban gane me kake nufi ba , kana ,nufin kace min zaka saketa kenan idan ka ‘aure ta, koya ‘abun yake” ba haka nake ,nufi ba Junaid abunda nake nufi shine mutuwa zanyi Junaid inaji a jikina bazan kuma wani dad’ewa ‘a duniya ba ‘Kuma ina rok’on Allah ya nuna min ranar auren ka da Hajar shine babban, burina , na k’arshe arayuwa naga kun zama, miji da mata ina da ,damuwa Junaid amman ,na barwa zuciya ta kuma ,koze kasheni wlh bazan furtashi ba dagani sai mahalicina mu kad’ai muka san miye shi” Haba Samir idan kana irin wainan magan ganun kana ,karya min zuciya, ka sani fa cuta bata kisa sai ‘idan ajalin mutun yayi don Allah kadena irin wainan magan ganun “.

“Tow Junaid na dena ‘Amman inaji ajikina kamar wani abu ze faru dani cikin, kwanakinan haka nakeji don ,nayi wani mugun mafarki jiya, wanda ina tsoron ya zama gsky ” ina fatan kayi sadaka?” Eh nayi sadaka” tow insha ‘Allah babu ,abinda ze faru sai alkairi ” tow Allah yasa Junaid ni zan koma gida, gobe zanyi shirin tafiya Turkey sai nan da 1 month zan dawo” tow abokina ‘Allah ya kiyaye ,ya kuma dawo dakai lfy “.

Su khadee itace babbar k’awar Amarya tunda ‘aka saka rana dayake badayawa ‘aka saka ba Khadee ta, tare gidan Su Hajar tare suke zurga zurgan su, Basmad ma kullum tana hanyar gidan,da tsohon cikin ta , Hajar ta saki jikin ta da Captian sosai soyayya suke zabgawa ita dashi, a yanzu har tana jin bazata iya rayuwa babu shi ba ‘a kullum idan basuyi waya dashi da yawa ba tow shine sau goma , tsantsar soyayya suke nunawa junan su na gaskiya kuma, me tsafta, Hajar a yanzu ita har tamanta da rayuwan ta na baya, wanda takeyi ,yanzu shine kawai a gaban ta ,bama ta ,tuna wance.


“Mrs Jumaid Khadee ta Kira Hajar don da sunan take ,kiran ta , da murmushi Hajar ta ‘amsa da “na’am Khadee na lfy nasan baki ,kirana da wannan sunan sai da, dalili “. Murmushi Khadee tayi ,tace dama tmbyn ki zanyi wai ‘ina masoyin ki Dr Samir ne ko ,kin dena son shi yanzu?” Azolaye tayi maganar ” ki ce min ango Samir dai ban dena son shiba gani, nayi ,yamin, nisa , kuma ‘abokin shi naso na shiyasa na hak’ura dashi Amman wlh ,har yanzu ina son shi, ae Salma ta more don kuwa ta samu , miji me hak’uri da sanin ya kamata ,gashi da kawaici wlh ina tayata, murna , inama ace Junaid ne me irin halin shi wlh da bani da matsala” tow shi kuma Junaid me yayi ?” Beyi komai bafa ni matsala ta dashi abu guda biyu ne , wannan rashin yardar tashi da kuma d’an banzar kishin sa, kifa duba ranan ze taran jama’a ‘a hospital don yaga Dr Aiman a motata ” ki dinga masa uziri duk cikin sone, yanzu dai kina ,nufin kice kin fi son Samir akanshi kenan ,?saina fad’a masa”.

“Ki rufa min asiri Khadee ni bance ba kibar ma zancen , kar uwar surutu Basmad tajimu , taje tayi sub’utar baki ” dariya sosai Khadee tayi ,tace ba ruwana idan tajiyo ki..

Karfa ku shagala ‘Akram yana hanyaπŸ€—

By Dija_WaziriπŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Na sadaukar da wannan shafin gare ku dukkan masoyana ,na.

Kusani ‘ina ji daku ,kuma ina k’aunar ku sosai, naji dad’i da irin k’aunar da kuka nuna min lokacin da kuka jini shiru da kulawar ku agare ni.

Dama baka gane masoyan ka sai ran da ‘akajika shiru, bani da ‘abunda zan ce muku sai godiya da fatan Alkairi😘

Masoyi duk inda yake baya b’uya so gamon jini , Action bazan gaji da mik’a godiya ta gareki ba, nagode nagode Allah ya barmu tare yabar zumunci, Ana tare sosai sosai🀝❀❀

Chapter 38

Yau biki ya rage saura ,sati d’aya, Dr Samir ya kira Ummi ya sanar da ita cewa ,yau ze dawo gida najeriya , yanzu haka ma yana filin jirgi…

 Istanbul

Tunda ya fito daga otal d’in shi yakejin fad’uwar gaba har ya isa filin jirgi , awan shi d’aya jirgin su ya d’aga daga istanbul zuwa najeri, yaso yabi k’asa me tsarki amman hakan be yuwu ba..


“Beby kwana biyu kin min horo da ganin fuskar ki ,meyasa? Ko wayar kima ya dena shiga, gaskiya idan haka wannan gyaran jikin yake a barshi kawai”, dariya Hajar tayi da muryan ta me zak’i tace “sorry dear wlh Mami ce ta hanani fita ko ina yanzun ma bata, san ,nafito ba wayata, kuma Jawahir ta ,jefa min shi cikin ruwa yana gurin gyara Fadil ya kaimin , kayi hakuri kwana, nawa ya rage zakayi ta ganina harsai ka gaji dani” haba ‘ae bazan tab’a gajiya dake ba ,kin tab’a jin masoyi ,ya gaji da masoyiyar shi?” Sunkuyar da kanta, tayi alamun kunya tace”dear barin shiga ciki ,kad Mami ta , nemeni “tam zan rabu dake ne ba’a son raina ba, don kar Mami tayi fad’a bana son b’acin ranki, hope babu abinda kike buk’ata ?” Eh ayanzu kam babu amman idan ma ‘akwai zan gaya maka ta wayar Khadee, wai ni ‘ina Dr Samir ne ?”.

“Samir yau ,watanshi d’aya da sati uku a Turkey ,yau ,yana hanya halama ya kusa, isowa don yace idan ya iso ze kirani,naje na d’aukeshi a filin jirgi” lalle a gaida Yayana ,yana ‘Angon ze kama hanya, ya wani tafi wata k’asa me nakon ya bari ayi auren tunda yakusa, sai su tafi ,tare” kema dai kin fad’a kibar Samir kawai na rasa meke damun shi, hatta kayan dazesa ,saini nakai masa d’inki na had’a da nawa baya komai akan bikin duk ni keyi masa” tow miye dalili, ko yana tuna matar shine don gsky ,yanda naji lbrn ta ba k’aramin so yake mata ba, ” gsky ,yaso Jamila ko nace har yanzu yana son ta, yak’i cireta cikin zuciyar shi sam , don ma k’anwar ta ze aura ” au kar ,kace min Salma k’anwar matar sace ?” Dama baki da lbr uwa d’aya ‘uba d’aya ma kuwa ” Allah Sarki wlh bani da lbr Ashe Sister d’in tane ,ae.yarinyar akwai kirki sau ,uku muna had’uwa da ita ” ae Salma kam tana da kirki ,ga son jam’a kowa nata ne”gsky kam tow Dear Bye sai munyi waya ” ok i love u ” love u too” ta shige ciki shima yayi motar sa…

BAYAN AWA GOMA SHA UKU

UMMI ce kwance kan sofa tana kallon ,NTA ganin wani jirgin sama na hayak’i ne yasa, ta saurin mik’ewa ta k’ara volum d’in talabiJin d’in ta fara jin labaran kamar haka..

~innalilahi wa inna ilaihi raji’un ayaune da misalin k’arfe bakyau na dare, wannan babban jirgin me suna * ya samu hatsari a daidai ,inda ze sadashi da filin jinrgin saman, nan garin kano, wanda mutane kimanin guda d’ari biyu ne cikin wannan jirgi, duk sun rasa, rayukan su ,sai mutane biyu da suke da sauran, nufashi a duniya tow suma dai rai na hanun Allah Jami’an kula da lfy sun tafi dasu, Hajar Hospital ,tow jima’a sai a garzaya idan kayi sa’a da ,d’an uwan ka ciki tow ,wainan mamata kuma ubangiji yaji k’ansu da rahama labaran kenan~…

hannu Salma tasa ‘akai tana kiran sunan Allah, Ummi kuwa mik’ewa tayi ,tana kiran ,number d’in Dr Samir akashe, han kalinta idan yayi dubu ya tashi , kiran wayan Captian tayi bugu d’aya ya d’aga da ‘alamun tashin hankali a tare dashi, shima .

“Hello Junaid kana inane pls?”.

Muryan shi ciki ciki yace “ina hanyar komawa gida Ummi lfy dai kow?”.

Muryan ta da ‘alamun kuka tace “Junaid ba lfy ba Junaid Jirgin su, Samir yayi hatsari yanzu muka gani a labarai, kuma duk yan cikin jirgin sun rasu mutane biyu ne kawai sukayi saura “.

“Innalilahi anya kuwa jirgin su , Samir ne Ummi ? Shifa sai 8 zasu ,sauka “.

A wannan karon Ummi kasa jurewa tayi ,kuka takeyi sosai tace “Junaid Jirgin su ,Samir ne don Allah kazo ka, kaini asibiti naga ko hardashi cikin wainda ‘aka ,suke cen”.

“Tow Ummi ki jira ni yanzu ,zan iso” ya kashe wayar ya juya kan motar sa zuwa gidan su ,Samir yana cikin far gaba da tashin hankali ,sai kiran wayar Samir yakeyi akashe..


Su Basmad ne zaune cikin d’akin Hajar tare da. Sauran yan uwan su Hajar yan mata suna kallo Khadee ,dataga hankalin su duk baya kan tibin yasa, ta d’auki remot ta cenja zuwa NTA dayake ita ma’a bociyar son labarai ce, tana kaiwai taga ‘ana ,nuna yanda hatsarin ya faru..

Hajar kuwa shigowa d’akin tayi dede lokacin da labaran ya k’are ,amman taga dai jirgi naci da wuta, kallon Khadee tayi ,tace “Khadee lfy kuwa naga jirgi naci da wuta kuma ,kamar a kano ,nema nan d’in?” Sai a lokacin yan d’akin suma suka maida kallon su kan Tv.

“Hmmm kedai bari Hajjo wlh abun babu dad’in ji abun ma be jima da faruwa ba ,minti ,talatin kenan da faruwan Hakan , wai jirgin ya samu hatsari duk yan ciki sun rasu, mutane biyu suka tsira, Hospital d’inmu ,ma ‘aka ,kaisu ,suma kuma rai na hanun Allah daya…”

Kafun Khadee ta k’arasa zancen ta har Hajar ta zube a wurin a sume, han kalin su Khadee yayi masifar tashi ,sukayi kanta ,suna ihu wasu kuma suka fita kiran Dady da Mami..

BY DIJA_WAZIRIπŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

YAN UWA MASU DAD’I , WANNAN SHAFIN GABAKI D’AYAN SHI SADAUKARWA CE , GAREKU YAN UWANA ‘ABUN ALFAHARI NA😍

ADDA SADIYA WAZIRI, NANA WAZIRI, MIEMIE WAZIRI, WALIDA WAZIRI, UMMI SALMA, BEBY ,HAUWA ,NAJMA(BABBAR YAYA)😎 AND AUTARAS HUSNA

SOYAYYAR KU DABAN TAKE BASAI NA TSAYA DOGON TURANCI BAπŸ’˜πŸ’˜

Chapter 39

Kwantar da ita ‘akayi akan kujera Dady yasa, Mami ta kawo ruwan d’umi da farin k’ele ya fara ,saka mata’a goshin ta, cikin min tuna kad’an ta farka ,tana farkawa sunan Dr Samir ta fara kira, ganin mutanen dake kanta yasa ta mik’e ta fara kallon su d’aya bayan d’aya har ta sauke, idon ta kan Mami da gudu ta mik’e tayi kanta, tana kuka tana “Mami shi kenan Dr Samir ya rasu shi kenan mun rasa ,shi “rik’eta Mami tayi, tana rarashin ta Dady kuwa kallon Mami yayi ,yace “wai meke faruwa ne waye kuma Samir kode tayi gamo ne?” Ba gamo tayi ba ‘Alhaji har ka manta Samir d’in wannan abokin ,nata doc..” Ok natuna shi meya sameshi ?” Dady ,ya tambaya” Wlh ina zan sani Alhaji gashi dai munji tana ya mutu Khadee ko ,kunsan meke faruwa?” Mami ta ,tambayi Khadee “wlh bamu sani ba Mami kawai muna kallon had’arin jirgin saman da ya faru d’azu ne mukaga ta yanki jiki ta fad’i”.

“Tow Allah dai yasa lfy “cewar Dady duban Hajar Mami tayi ,tace “Hajjo lfy meya samu Samir d’in” hajar na kuka tace “Mami mun rasa, Samir har dashi cikin jirgin d’azu Junaid yake cemin yana hanya daga turkey ze dawo kano”..

Gaba d’aya falon suka ,fara salati, Khadee ma bata, san lokacin da kwala yazo mata ba , ki dena kuka Mamana ba lalle harda shi ba tunda ‘ance da ‘akwai ragowan biyu suna hospital d’inmu ,kuje ku duba cikin su ko Allah zesa yana ciki”.

Babu musu Hajar ta zari hijabi da takalmi suka, kama hanya ita da Khadee da wata yar uwar su ,sukaje kasan cewar Basmad tayi nauyi bazata iya zuwa ba ..

Suna isa kafun ma su shiga sukayi karo da Captian da Ummi da Salma sun fito, ganin su yasa Hajar tayi saurin nufar inda suke ko gaishe da Ummi batayi ba tace “Captian Allah yasa dai be mutu ba kun ganshi?” A firgice take maganar ,murmushi ya saki mata yace “kwantar da hankalin ki bashi bane yanzu ,nakira wayan shi ya shiga kuma wai yana legos ,sai gobe da safe zasu iso an dakatar dasu tun 7:30 na dare suka sauka, rashin charge yasa be kira ba” lokaci guda Hajar tayi wani ajiyar zuciya tace Alhmdlh wlh yau ,mun tsorata mun girgiza ni wlh har hantar cikina saida ya k’ad’a ubangiji mun gode maka, Salma ina tayaki murna ” murmushin yak’e Salma tayi ,tace nagode Hajjo harkin d’an fad’a , wlh kowa yaganki zesan da ‘alamun tashin hankali a tare dake “ba dole ba Salma rashin Dr Samir a garemu babban rashi ne a rayuwan aluma baki d’aya ‘ae rabon da nashiga tashin hankalin dana shiga yau har na manta” ae abun babu da d’i “cewar Salma “ae Hajjo har suma saida tayi na gaya miki Salma tsabar tashin hankali” Khadee ta fad’a fuskar ta d’auke da fara’a “suma lalle Hajjo kina son wannan yayan ,naki “Captian ya fad’a yana dariya murmushi kawai Hajar tayi suka durk’usa har k’asa ita da su Khadee suka gaida Ummi , sannan su Captian suka wuce ,suma su Hajar d’in ko ,k’arasawa cikin asibitin basuyi ba suka juya suka, koma gida….

“Junaid wai wacece ,wannan yarinyar “Ummi ta ,tambaya “au dama baki san taba Ummi ?ae itace me wannan hospital d’in diyar Dr Galadanci ,ce itace first bon d’in shi ,kuma k’awar Samir ce sunfi 5 years tare kuma itace dai Hajar d’in matar da zan aura” Allah sarki ni ‘ina zan sani kasan Samir miskilin mutune shi ko hira baya wani tsayawa muyi sosai bare nasan da ita, kanaga har Salma ta santa da yake ita matar sace ae har ya nuna mata ita, kuma kaima tun yaushe nakece ka nuna min hoton matar taka, kak’i yau dai gashi na ganta ,gsky kayi sa’a duk da ban san halin taba ‘amman daga ,ganin alamu tana da tarbiyayya da kunya Allah ya baku zaman lfy” sunkuyar dakai Salma tayi batace komai ba ” a kunyace Captian yace “Ameen “.

“Junaid kaga yaron da muka gani cikin wainda sukayi hatsarinan d’ayan med’an gashi akai d’innan me bak’in riga ,wlh kamar d’an uwan Samir ne, don ,naga kamar yana kama da wanda mahaifiyar shi ta. Nuna mana hoton shi” Allah Sarki ze kuma iya kasan cewa shid’inne amman gsky ,yana jin jika Ummi har fa yafi d’ayan don gsky ina tunanin k’afar sa ,sai dai a yanke don duk ta dadage ko ,k’ashi fa ba’a iya gani tun daga cinyar shi har zuwa d’an yasan hanun shi, gashi kanshi yayi mugun fashewa sai jini yakeyi hanun daman shima gsky zeyi wuya ,ya kuma ‘aiki don shima ya dadage kuma daga k’asan cibiyar shi yayi k’asan shi duk ya k’one zafin wuta ,wlh abun ,babu ken gani bari gobe idan Samir ya iso ,sai mukuma zuwa mu duba ko shine”.

“Innalilah Allah ya bashi lfy ,shiyasa na fito ina ganin k’afar sa naga bazan iya tsayawa ba, fuskar shice kawai batayi komai ba ,wlh duk me imani tow zai tausaya masa, gsky ,yana jin jiki” Ameen Ummi wlh ya wahala kam” Captian sai da yakai su Ummi har gida sannan shima ya koma gida..

   WASHE GARI

Da misalin k’arfe sha biyu na rana Captian yaje filin jirgi ya d’auko Dr Samir , koda ya d’auko shi cewa yayi ,su wuce asibitin Hajar don yaje yaga ko d’an uwan shine ,don tun jiya Ummi ta fad’a masa cewa taga me kama da ,d’an uwan shi cikin masu hatsari..

“Abokina jiya ka firgita mutane da ,dama Hajjo harda suma duk mun zata ka rasu” Uhm Allah Sarki tow ranar da ‘akace nayi mutuwan gsky ,kuma ya zakuyi?”zaka fara kow tow mubar zancen ya isa haka”cewar Captian .

“Tow dama ae kai kafara kawowa kuma, mutuwa dai ta zame ,mana dole ko munaso ko bama so ” Captian bece komai ba ya cenza ,zancen .

“Wai ,kai awani gida zaku zauna kaida Salma naga bakayi tanadi ba?” Ni bazan rabu da Ummi ba ‘a sashina zata zauna babu wani gida ,dazan siya”.

“A’a kaji d’an gidan Umma hakan ma yayi, nikam a zoo road zamu zauna ‘anan ,nasai gida ‘amman gsky zaman mu zefi yawa ‘a Faris ” Allah dai ya nuna mana “Ameen ae saura 4 days “cewan Captian.

Parking yayi , cikin Haraban asibitin, lokaci guda Dr Samir yaji wata fad’uwar gaba da fargaba sun ruski zuciyar shi.

Gabaki d’aya ,yaji ,jikinshi yayi sanyi har suka ,k’arasa cikin d’akin , shi kad’ai ne kwance a ciki babu kowa kusa dashi an saka mishi ruwa d’ayan hanun kuma roban jini ce ,sai kuma roban abinci da ‘aka sa masa , k’afar shi ta dama ‘an rufeshi da wani farin k’elle kan shi kuma ‘an d’aure shi da bandeji.

Hanun shi na haguma da wani farin k’ellen aka rufe, yanda mutun bazai ‘iya sanin me ‘akayi ma gurin ba.

“Innalilahi wa inna ilaihi raji’un “

Shine abunda ,Dr Samir ya iya furtawa.

“Lfy Dr Samir”.

Cikin fargaba da tashin hankali Captian ya tambaye shi.

Dak’er Dr Samir ya iya ‘amsa masa bakin shi na rawa.

“Shine Jinaid Shine D’an uwana da nake ,nema wlh shine”.

Ganin yanda Dr Samir ya rikice yasa Captian dafashi yana ,bashi hakuri, kasa jurewa Dr Samir yayi ya nufi kofar fita daga ,d’akin don bazai ‘iya jure ganin d’an uwan ,nashi cikin irin halin da yake ciki ba.

Don tunda ya ganshi yanzu yaji wani k’aunar shi da soyayyar shi, sun mamaye shi, dama ya jima yana son yaga yana da yaya ko ,k’ani a duniya ‘amman hakan be yuwu ba, yau gashi rana tsaka ya ga d’an uwan ,nashi amman yana shirin rasashi.

Dede ze fita likita ya banko ,k’ofar d’akin da sauri ganin likitan yasa Dr Samir daka tawa .

Har inda ‘Akram ke ,kwance yaje ya duduba shi yaga be tashi daga bacci ba kuma yaga komai yana tafiya daidai.

Sanun ku pls ko ,kune yan uwan, wannan bawan Allah don yanzu wata nurs tace min wasu, sun zo?”.

Junaid ne ya iya amsa Doc.. D’in.

“Eh mune Doc ya jikin ,nashi wlh bamu samu labari da wuri bane sai d’azu muke ji”.

D’an jim kad’an Doc… Yayi sannan yace.

“Tow jiki gadai shinan zance, Amman ina son ku sameni a office yanzu idan ba damuwa”.

Ya wuce ya barsu gurin.

Kallon Captian Dr Samir yayi ,Fuskar shi da’alamun tsoro da fargaba ya girgiza ma Captian kai alamun suje.

Γ—Γ—Γ—Γ—Γ—Γ—

“Yawwa ‘a jiya da ‘aka ,kawo mana wainnan mutane guda biyu d’aya ,yan uwan shi sun sameshi kuma sun tattara shi sun tafi da ‘abun su ba tare da munsan ina suka ,kai shiba,

Shi kuma wannan d’an uwan ,naku ,mun zauna mu jira ko, Allah zesa wani ,nashi yazo mukaji shiru ,har wurin k’arfe uku na dare babu wanda yazo.

Ga ciwo ajikin mutun Hakan yasa ,muka ,kira Dr Galadanci muka sanar dashi ,halin da ‘ake ciki yace muyi mishi duk abunda ya kamata.

Kafun a samu yan uwan shi suji . hakan yasa muka yanke hukunci yi masa ‘aikin daya dace .

Tow sai dai kuyi hak’uri da ‘abun da zan fad’a kun san ita kadaddara takan fad’a kan ,kowa ne aduk sanda tazo ma bawa , jarabawa ce ,wacce sai mai rabo ke iya cenye ta.

Ina so kuyi tawakali da Ubangijin mu, kuma ku gode masa ku d’auka cewa komai ba komai bane face tsarin ubangiji ,kusani duk abunda ze faru da bawa dama cen rubutatce ne ku…….”

“Doc….ka fad’a mana meke faruwa pls shi muke buk’atar sani ayanzu”.

Dr Samir ya tsaida shi.

Sai daya d’anyi jim kad’an sannan yace.

“D’an uwan ku ,kanshi ya bugu sosai ,muna ‘addu a da fatan kar Allah yasa wani abu ya faru da kwakwalwar shi.

Sannan ya rasa k’afar shi na dama da hanun shi na hagu ina ,nufin an yanke su don koda an barsu bazasu kuma ‘aiki ba.

Daga cinyar shi yayi kasan shima ya samu konuwa sosai wanda nake tunani abubu ,abinda ze kuma ‘aiki a gurin.

Ya kuma samu karaya a k’ashin bayan shi bazai kuma tashi ba, ze k’are ,rayuwan shi a hakane har Allah ya kawo ranar daya, kayade mishi a duniya “

“Ya ‘Allah “

Dr Samir ya fad’a yayin daya dafe kanshi yana ,jin yana masa wani ‘irin nauyi zuciyar shi na masa wani ‘irin zafi da zugi

Magan ganun Dr ne kawai suke tayi masa yawo a konyar kanshi .

Lalle rayuwa ba komai bace babu komai a duniyar nan face tarin daud’a da takaici ,

Abu mafi sauk’i a rayuwa da zakayi wa kanka shine kusanci da ubangijin ka , yau ga ‘Akram yazo da lfyan shi yana murnan ze sadu ,da mahaifiyar shi .

Yana tunanin ze nemi gafaran ta ,tare da, duk wanda ya b’atawa ,sai dai kash ya makara don kuwa ‘Allah ya fara nuna masa jarabawan shi”.

Dr Samir be iya cewa Da Doc… Komai ba ya mik’e ya fita, yana rik’e gefen zuciyar shi ,Captian ,nema ya iya ,yiwa Dr godiya, ya fice yabi ,bayan Dr Samir.

Dak’er yake iya takawa don k’afar shi tayi masa wani ‘irin ,nauyi sai nishi yake ,k’asa kasa.

Ko gabanshi baya iya gani ko ina ya koma, masa duhu tafiya kawai yake ba tare da yasan inda yake nufa ba.

Saida yazo dede kofar da zata sadashi da waje ya rik’e kofar yana fitar da wani ,irin ,nishi me zafi .

“Lfy kuwa Samir? Barin kira Dr Aiman karka fad’i “

“Kar kaje ,Junaid “

Dr Samir ya tsaida shi.

Zan iya tafiya

” kamani pls jiri nakeji “.

Cikin rashin fahimta Junaid yace .

“Meyasa Samir? Meyasa bakaso a sanar ma Doctor d’inka halin da kake ciki , kafi kowa sanin damuwar ka”.

“Zan gaya maka Captain idan har zakayi mun alfarma guda ,d’aya”

Da sauri Captian yace

“Wata irin Alfarma ce?”

Sai da ,Dr Samir ya k’ara jingina da jikin ,kofar don ji yake, kamar ze fad’i shi kad’ai yasan abunda yakeji cikin cikin shi don komai ,ma ciwo take masa.

“Mu tafi gida pls shine Alfarman da nake so daga ,gareka”.

Kallon shi kawai Captian yake, yana tunanin anya kuwa samir be fara zaucewa ba.

Kamar Dr Samir yasan tunanin da yake cikin zuciyar shi,

Langofar da kanshi yayi a shagwab’e yace

“Ka yarda ,dani pls”.

Tau sayin shi Captian yaji ,ya taimaka ya kama shi suka fice.

Saida ya ,saisai ta kanshi tukun ya shiga ,gida ,don kar Ummi ta gane Halin da yake ciki.

Captian kuma gida ya koma tare dayi masa ‘Alk’awarin ze dawo da yamma.

Ummi na ganin shi taji wani fad’uwar gaba don ko ba’a fad’a mata ba tasan d’an ,nata yana cikin damu kuma yau kam ta yanke hukunci sai ,ta ,tambayeshi abunda ke damun shi.

Duk da ramar da yayi be hana kenshi fitowa ba, gani tayi ,ya k’ara mata kyau da fari kamar bashi ba.

“Ummi ,ina wuni ya gida”.

Sai a lokacin ta dawo hankalin ta don har ya k’araso cikin falon bata kula ba.

“Lfy qlau Doc… Ya naganka ha ,kamar….”

“Babu komai Ummi “.

Yayi saurin katseta.

“Ka tabbata Samir? Bana so ina ganin ka cikin damuwa fa jibi yanda ka rame

Ka fad’a min damuwar ka, wlh inde ina da halin da zan iya , yaye maka shi zanyi , idan kuma na ‘addu’a ne sai na tayaka”.

Da Murmushi d’auke a fuskar shi yace.

“Babu komai Ummi kedai ki tayamu da ‘addu kawai Allah yasa mucika dakyau da imani yakuma yafe mana zunuban mu.

Shiru tayi kamar me karantar wani abu daga ,gare shi ,me yake nufi da hakan?.

Itafa bata so taji yana irin wainnan zantukan ,Amman kuma gsky ,ya fad’a.

Kamar yasan me take fad’a cikin zuciyar ta yayi saurin cewa.

“Karki d’auka wani abune fa Ummi kawai ,naji kwad’ayin ,nace miki hakanne don shine babban Addu’ar da mukafine a gareku ,ku iyayen mu”.

Murmishin k’arfin hali tayi ,tace.

“Hakane Dana ‘Allah ya maka ‘Albarka ya k’ara maka lfy .

Ya jikin ,naka ina fatan dai kana shan magun gunan ka, akan lokaci ?”.

Ina sha Ummi jiki ,kuma da sauk’i mun gode Allah”.

Shi kad’ai yasan abunda yakeji cikin jikin shi, Ummi tana karya masa zuciya ‘aduk lokutan da zata kalle shi sai yaji abubu dadi

Don kuwa barin ta ‘abune me wuya ‘a gareshi amman ta zame ,masa dole duk da yasan mutuwa ba’a hunun shi take ba ,baya tunanin kuma ,kwanaki da watani da shekarun da yayi a baya.

Ba mutuwan yake tsoro ba yanda rayuwan Ummi ze kasance bayan ta rasashi ,shi yafi d’aga masa hankali .

Yana son ya sanar da ita wani abu amman yana tsoron abunda ze haifar bashi da kowa ‘a duniya sai Ummi bashi da wanda ze iya sadaukar da rayuwan shi sai Ummi.

Amman baze iya fad’a mata komai ba, bakuma ze tab’a bari ta rasa life d’inta saboda shiba.

Wasu zafafan hawaye ne suka zubo mishi ba tare da ya bari ta gani ba yayi saurin goge su.

Sai daya d’an sai saita kanshi sannan yace.

“Ummi naje asibitin kafun ,na shogo gida shine Ummi” babu wani b’ata lokaci ya sanar wa da Ummi duk yanda sukayi da Doc…a hospilat.

“Ya ilahi ya Allah ,mun san komai dayake samun bawa ‘a duniya jarabawa ce kuma rubutacce ne a gurin ka.

Dama kariga da ka rubuta ‘acikin Allon k’adaddara ‘Allah kai maji rok’on bayin kane Allah ka sausauta mana wannan irin jarabobi da kake ta jaraftar mu dashi”.

Cikin tausayawa tace .

Barin shiya sai ka ,kaini gurin shi na zauna karmu barshi ,shi kad’ai.

Dija_waziriπŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 40

Yana sauke Hajiya asibiti ya wuce gidan su Junaid ,don yana son ya keb’e shi kad’ai bazai ,iya zuwa ‘asibiti a yanzun ba.

Koda yaje be samu Junaid a gida ba d’akin shi ya shiga ya kwanta , kanshi na mishi wani ,irin ,nauyi

Yinwa yakeji amman bazai ,iya cikin komai ba duk da halin da yake ciki be hana bacci d’aukar shiba.

Γ—Γ—Γ—Γ—Γ—Γ—

“Samir”.

Captian ya biga pillon da Dr Samir ke kwance a kai

“Haba ,Junaid meyasa zaka tasheni kasan daya nayi baccin ya d’auke ni?”.

“Sorry ban san bacci kakeyi ba”.

Ya nemi guri ya zauna gefen shi.

Tsaki Dr Samir yaja ya mik’e yad’an jingina da gadon dake ,kwance kai.

Ruwa Captian ya d’auko ya dawo ya zauna yana sha.

“Samir miye abunda kace zaka fad’a min”.

Ajiyar zuciya Dr Samir ya saki lokaci goda Captian ya tayar masa da ciwan dake damun shi wanda ya samu yad’an kwanta.

“Junaid Allah ya sani ,ina son Ummi na.

Bani da kowa ‘arayuwa ta sai ,ita itace komai na Junaid,

Ina tsoron Halin da zata shiga idan ta rasani Junaid, ba mutuwa nake tsoro ba tunda tana kan kowa jiran ta yakeyi.

Abunda nake tsoro shine abunda ze faru bayan ta rasani. “

Kallon shine Captian yakeyi kawai cikin rashin fahimta yace.

“Ban gane ba Samir wai me kake fad’a haka ne ?”

Darin takaici Dr Samir ya saki.

“Dama bazaka gane ba Junaid har sai na ganar dakai .

Dakai ,kad’ai na yarda Junaid shiyasa zan fad’a maka damuwa ta”.

Jiki a sanyaye Dr Samir ya cire ,rigan jikin shi ya zama dagashi sai bes d’aga rigan cikin yayi ,ya nunawa Captian cikin shi.

Da murmushi yace

“Me kagani Junaid?”.

Zaro ido junaid yayi ,lokaci guda yaji ,yawun bakin shi duk sun k’afe dak’er ya iya tattaro wani yawu me d’aci ya had’iya.

Cikin fargaba da tashin hankali yace.

“Miye a jikin ,ka haka Samir?”.

Saida ,Dr Samir ya d’anyi jim kad’an sannan yace .

“Ciwo ne Junaid bayan tafiya na Turkey da kwana hud’u na kwanta rashin lfy da naje asibiti .

Doc…ya dubani sosai ya kuma gano cutar Cancer d’in da nake mafa dashi ,wanda ni ban sanar dashi ba.

Yace ina da wata d’aya ‘anan gaba idan har ba’a cire kidney d’ina ba tow zan iya rasa raina.

Yace duk kidney d’ina sun lalace saka makon ciwan dayake jikina ,

Bani da kowa da ze iya magan cemin wannan damuwar sai Ummi na , kuma itama kedney d’aya gareta .

Har idan Ummi tasan meke faruwa dani zata iya sadaukar da rayuwan ta sabo dani, kuma ni bazan so hakan ba Junaid shiyasa kawai kaga na bar komai ku….”

Cikin b’acin rai Captian ya tsaida shi ,idanuwanshi sunyi jazur alamun b’acin rai .

“Me matsayin abotar mu Samir ,da zaka dinga tunanin baka da kowa mud’in kenan baka d’aukemu yan uwan kaba kenan?

Samir ina jinka ,kamar d’an uwana kuma jinini!!

Babu abinda bazan iyayi makaba ‘a rayuwa matsawar wanda nasan zan iyayi ne.

Idan har ka d’aukeni d’an uwanka ba ‘abokin kaba, ka yarda zan baka ,kidney d’ina guda ,d’aya matsawar zesa ka rayu”.

Daro ido Dr Samir yayi ,yanajin wani dad’i cikin zuciyar shi ,da irin karamcin da ,Junaid yayi mishi.

Yasan babu ,abinda Captian bazai yi masa shiba ‘arayu don yaga ya samu lfy , Amman idan har ya bari aka cire kodar Junaid tow ya tabbata, yaso kanshi da yawa.

Hawan da tun d’azu suka ciko idon shi ya barsu ,suka fara fita.

Murmushi yayi wanda iya kanshi fatar baki ne yace.

“Junaid nagode ,da karamci nagode bani da ‘abunda zance maka dayafi haka,

Amman kayi hak’uri bazan iya bari a cire k’odar kaba idan ,nayi haka naso kaina da yawa.

Mutuwa bata salama koda anyi mun bashe ze hana ,na mutuba idan har kwanana ya k’are ,

Junaid yanda ,nakeji yanzu ya wuce kwatance ina ganin mutuwa ita kad’ai ce hutu a gareni.

Shine k’arshen k’addara ta , Allah ya nuna min jarabobi da, dama ‘a rayuwa ta, Hakan yana ,nuna shine k’adaddara ta,

Rubutu ne wanda ‘akayi kamar akan dutse wanda baze tab’a gogewa ba sai dai , ya wuce Amman tarihin sa baze wuce ba har abada”

A wannan lokacin Captian kasa jurewa yayi ,wasu Zafafan hawaye ,yaji sun zubo mishi.

Dafa kafad’ar Dr Samir yayi zuciyar shi na k’una yace.

“Idan har baka yarda ba Samir nasan matsayina ‘a gurin ka kuma……..”

Saurin katsashi Samir yayi , ya mik’e ya tako har inda Junaid yake ya tsuguna gaban shi.

“Na yarda ‘Abokina ,nagode da wannan karamcin dakayi mun Allah ya saka maka da mafificin Alkairi.

Samun aboki ‘irinka sai an tona Junaid ba kowa ze iya, yimun abunda kamun ba?”

Murmushi Captian yayi ,yace.

“Is ok babu god’iya tsakanina daikai Ana tare ,tashi mu koma ‘asibiti”.

Babu musu ,Samir ya tashi suka tafi


Tun jiya takejin bugun zuciya ta rasa dalilin hakan , kawai tana tunanin akwai abubuwan da zasu faru da ita cikin kwanakin .

Tun safe data, tashi bataji komai ba, babu yanda Khadee batayi da ita, taci abinci ba ‘Amman tace ta k’oshi bata jin cin komai a ranar.

Haka ,Khadee ta hak’ura ta rabu da ita.

K’arfe tak’as da kusan rabi Hajar ta shirya cikin wani daguwan riga na material ruwan madara, da zanen fulawa ruwan ganye ,

Ba tayi kwaliya ba mai kawai ta shafa , tad’an goga hoda ,ta yane kanta da wani mayafi ruwan ganye ,

Duk ,da rashin kwaliyan dake fuskar ta be hana kenta fitowa ba.

“Khadee kiyi sauri mutafi pls kinga ina so na biya hospital ,akwai abunda zan d’auka ‘a office d’ina “.

Kadee ,dake jikin mirro tana kwaliya tace.

“Sorry na gama barin saka, kaya ‘Amarsu “.

Hajar batace da ita komai ba sai murmushi data saki ,har yanzu tanajin bugun zuciyar ta me ,makon ya ragu k’aruwa ma yayi..

DIJA_WAZIRI
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 41

Suna cikin mota Hajar tace wa Khadee.

“Nifa yau tunda natashi ,nakejin ,jikina babu dad’i Khadee.

Sai bugun zuciya da fad’uwar gaba nakeji ,sai ,ina tunanin akwai abunda ke shirin faruwa dani”.

Khadee dake tuk’i tace.

“Kiyi ta innalilahi insha ‘Allah babu ,abinda ze faru dake”.

Yanda Khadee ta fad’a hakan tayi tayi har suka k’arasa hospital.

Sai dai suna shiga taji bugun zuciyar nata ,na k’aruwa da fad’uwar gaba, Addu’a take tayi har ta k’arasa ciki.

“Hajjo barin shiga office dina zan ,zo na sameki”.

Cewar Khadee

Dak’er Hajar ta iya ce mata .

“Don Allah kar ki jima Khadee kinga bamu da isashen lokaci”

D’aga mata gira kawai Khadee tayi ,ta wuce ,

Itama Office d’inta ,ta nufa da mamaki taga Captian ,na tahowa hanun shi d’auke da ledan magani da ruwa ,shi ko kula da ita beyi ba har zai wuce tayi saurin tsaida shi da fad’in.

“Captian lfy na ganka ‘a nan waye ba lfy baka fad’a mun ba?”.

Sai lokacin ya juyo ,ya kalleta da fara’a.

Gani tayi ,ya k’ara kyau da haske hancin sa ya k’ara tsayi .

“Hajjo sanun ki ,kinyi kyau “.

Ya fad’a yana murmushi.

“Tnx me kake anan ?”.

Ta tambaya fuskar ta babu fara’a.

“Wlh k’anin Dr Samir ne yayi hatsari har dashi cin wainda sukayi hatsrin jirgin samman”

Magan ganun Captian ,ne suka fara yawo a kwanyar kanta dama Dr samir yana da k’ani ?.

Tambayar da takeyi wa kanta kenan a fili kuma tace.

“Allah sarki ae daka ,kira kagaya mun, damur Doc…ae tamuce duka, kodon mutuncin sa.

Bari idan ,nafito daga office zan shigo na duba shi “.

“Ok babu damuwa muna room 15”.

Yana gama fad’ar haka ya wuce ,

Itama office d’in ta shiga tare da tunanuka bar katai.

Abunda ta zo daniyar d’auka shi kawai ta d’auka ta fice daga office din don sauri takeyi,

Dakin da su Dr Samir ke ciki ta nufa dede kofar dakin taji fad’uwar da gabanta yake, ya sake tsanta ,taji wani ‘irin ciwan kai da bata, tab’aji ba , subhanallah kawai take ta furtawa har ta shiga d’akin.

A zaune ta samu ,Ummi kan darduma tana jan cerbi ga dukkan alamu idar ,da sallah tayi gefen ta Dr Samir ne ya kifar da kanshi ,cen gefe guda kuma Captian ,ne zaune , bata kalli gadon da ‘akram ke ,kwance akaiba ba.

“Asalamu alaikum “

Shine abunda ta furta, gabaki d’aya hankalinsu ya koma, kan ta su duka saku ‘amsa da

“wa’alaikum salam”.

K’ara sawa tayi ,inda Ummi ke zaune ta durk’usa.

“Ina wuni Ummi yame jiki?”.

Hajar ta, tambaya

Ummi da fara’a tace.

“Lfy qlau jiki da sauk’i ya shirye shiryen biki ?”.

Akunyace ta amsa da.lfy qlau ,sai alokacin ta kali Dr Samir suka gaisa ta, tambayeshi me jiki sannan ta maida ,duban ta kan Akram.

Wani fargaba da tashin hankali taji na ruskar ta, lokaci guda taji komai ya tsaya ,mata wani ,irin dokawa taji zuciyar ta, tayi.

Ko a mafarki bazata ,tab’a mancewa da wannan fuskar ba, ta kasa gasgata shid’inne kuwa gaban ta yau rana tsaka.

K’afafun ta, taji sun fara rawa lokaci guda taji zuciyar ta na wani ,irin dokawa.

Kallon Dr Samir tayi ,tana son yi mishi magana, yayin da take nuna ‘Akram da ,d’an yatsan ta sai dai kalma ko d’aya ta kasa fita daga bakin ta.

Lokaci guda taji wani jiri na d’ibar ta, lu ta ,tafi zata fad’i Junaid yayi saurin rik’ota yana .

“Lfy Hajjo” .

Sai lokacin Dr Samir yayi saurin tashi daga inda yake zaune ,han kalin shi a mugun tashe ,

Ummi ,ma ,mik’ewa tayi, tayi kan Hajar tana jijiga ta.

Da Sauri Captian ya fita kiran Doc… Yana fita kuwa yaci kara da Khadee, hankali a tashe yace.

“Khadee pls muje ki taimake mu Hajjo ta fad’i “.

Wani yawu me d’aci Khadee ta had’iya cikin tashin Hankali tace

“Ta fad’i kuma, meya sameta”.

Ita dai tasan tabar ta lfy qlau tow meya sameta kuma, kar tarihi ya ,maimaita kansa fa ‘Allah sa ba wani abu Captian yayi mata ba ,shine addu’ar da take tayi.

“Wlh nima ban sani ba Khadee”.

Ta ,tsinci muryar shi da fad’in haka

Bata iya k’ara kula Captian ba tayi saurin k’arasawa cikin d’akin.

Abunda ta gani ba k’aramin d’aga mata hankali yayi ba.

Wani abu taji yana mata yawo tun daga d’an yatsan k’afar ta har zuwa tsakiyan kanta. Lokaci d’aya jikin ta ya d’auki ,k’erma .

“Ya ‘Allah ,huma ‘ajirni fi musibati “.

Shi kad’ai ta iya furtawa ita ,tasan shikenan duk wani farin cikin da k’awar ta ke ciki ya tarwatse , basu tab’a tunanin zasu ,kuma ganin akram ba

“Lfy Khadee”.

Cikin fargaba Dr Samir ya tmby.

Fuskar Khadee ,d’auke da hawaye tace , Dr waye ,wannan ?”

Ta masa nunu da ‘akram.

Babu wata fargaba Dr Samir yace

“k’anina ne “.

Sai alokacin Khadee ta fashe da kuka me sauti .

“Pls Khadee kibar kukanan ,ki sanar damu ,meke faruwa”.

Dr Samir ya kuma tambaya.

Cikin ,kuka ,Khadee tace .

“Sh……shi….ne….wlh shine Akram ,mahaifin Jawahir”.

“innalilahi wa inna ilaihi raji’un”.

Dr Samir yake ambato ,lokacin dayaji wani ,irin bugun zuciya.

Nufashin sa yake ,kokawa dashi wurin fita saboda tsabar tashin hankali da yake ciki.

Yana jin yanda zuciyar shi ke zafi,kanshi na wani ‘irin juyawa.

Wani ‘irin ,nishi yake fitar wa me zafi kansa nayi masa wani ‘irin ,nauyi , lokaci guda fuskar shi ta sauya ta koma jawuri jiri ne kawai ke d’ibar shi.

Jikin shi sai b’ari yakeyi, Khadee ,da Captian ,na shirin fitar da Hajar basu ankara ba kawai suka jishi a k’asa.

Wani ‘irin k’ara Ummi ta saki tana wani ‘irin kuka me sauti.

K’aran da tayi ne yasa ‘akram farkawa .

DIJA_WAZIRIπŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

ina jin dad’in yanda kuke biye dani cikin wannan novel d’in ba tare da wani k’orafi ko gajiya ba, comments d’inku shi ke sani son naji kullum naturo muku ,kuma shike sa nasan kuna biye dani

Rashin comments d’inku shike sa naji k’in son yin typing da wuri Allah ya barmun ku

Chapter 42

Bayan su Khadee sun kai Hajar wani d’akin sun saka mata Drip .

Da sauri Khadee ta dawo takira wasu nurses maza ,suka ,kama Dr Samir suka shigar dashi wani d’aki, har alokacin ,wani ‘irin nishi yakeyi.

Wasu manyan likitoci ta kira guda biyu kasan cewar Dr Aiman baya, nan suka had’u da ita su uku suka rufu a kanshi.

Oxgyen suka ,sanya masa tare da wasu na’urori da suka jajona masa ,sanan suka saka masa roban ruwa.

Captian yana d’akin Hajar ,addu’a yake ,kawai Allah yasa ta, tashi.

Ji yake zuciyar shi kamar zata fito daga k’irjin shi tsabar b’acin rai, lokaci guda yaji wani tsanar Akram na ,ratsa ko ina ,najikin shi.

Yaji baze iya sake ganin shiba ,wani kishin shi ya lulub’e shi , ko d’akin da ‘aka kwantar da, Dr Samir ma kasa shiga yayi.

Khadee tayi tunanin ta kira su Mami ta sanar dasu Halin da ‘ake ciki amman ta fasa ,tana ganin hakan ze iya haifar musu da matsala.

Basmad takira ,ta sanar wa halin da’ake ciki,

Babu yanda Basmad batayi da mijin ta ya barta, taje asibitin ba’amman yace tayi nauyi baya son wani abu ya faru da ita, hakan yasa ta hak’ura ta rabu dashi.

Hajar bata jima da sumaba ‘Wani daga cikin yan asibitin har ya kira Dady ,ya sanar masa babu wani b’ata lokaci Dady ,ya sanar da Mima ,suka d’ugun zuma ita da ‘Aunty Asma’u suka tafi tare da ,addu’ar Allah yasa ba wani abu, bane ya same ta.


A hankali take bud’e idon ta , d’akin taga yana juya mata ,tana gama bud’esu bata sauke su kan kowa ba sai kan Mami hanun ta, taduba taga d’aure yake da roban ruwa hakan yasa tayi sauri mik’ewa ‘a firgice .

Mami ne ta k’arasa inda take da sauri ,ta rik’e ta, tana share mata hawayen dake zuba daga idanun ta.

Don tunda sukazo Khadee tariga da tasanar dasu duk abunda ke faruwa.

Mik’ewa ‘Aunty Asma’u tayi ,taje dab da Hajar ta k’ura mata idanuwa tana rik’e da hanun ta jin hanun Aunty Asma’u cikin ,nata yasa ta sakin nufashi.

Muryan ta na wani irin Sama sama ta k’ara damk’e hanun ta cikin na ‘Aunty Asma’au tana wani ‘irin kuka tace.

“Aunty ban san randa wainan jarabawan zasu….”

Saurin dafe mata baki Mami tayi ,

Juyawa tayi ta kalli Mamin Sosai ,itama ta jawo hanuta ta damtse ,zuciyar ta na k’ara dokawa kamar ze fasa k’irjin ta ya fad’o tace.

“Mami yazanyi na gaji da wanan rayuwan mutuwa nake so”.

Wani jiri ke d’ibar ta ,take fad’in.

“Ganin Akram ya sosa min ciwuka da, damana dana samu suka dena min zafi”.

Shiru tayi tana jin yanda duniyar ke juyawa mata.

“Ki dena fad’in haka Hajjo komai yazo k’arshe yanzu haka yan sanda mahaifin ki yasa’aje a d’auko , yau ze biya duk cin zarafin dayayi miki, yau zai fara girban abunda ya shuka.

Yau zamu rama ,miki abunda yayi miki shekaru masu yawa, yau zeyi nadamar ,zuwanshi duniya ,yau zesan cewa ko wace mace tana da gata .”

“Mami bazaki gane halin da nake ciki ba ,Mami bakisan yanda nakeji cikin zuciyata bane”.

Hajar tayi saurin k’atse Mami.

“Akram k’anin Dr Samir ne Mami ,”.

Cikin bacin rai Mami tace.

“Tow ina ruwam mu Hajjo ko Baban shine wlh sai an hukun tashi ,kamar yanda yayi miki, ke ,kinfi kowa sanin waye mahaifin ki.

Shekara nawa yana ,neman shi ,ko kin manta”.

Jin yanda ‘aka banko ,k’ofar d’akin da k’arfi yasa duk hankalin su ya koma, kan guri.

Ummi suka gani fuskar ta chab’a chab’a da hawaye ,idanun ta sunyi jawuri har sun kun bura.

Takowa tayi ,ta k’araso cikin gurin ba tare da tabari tashin hankalin da take ciki ya bayayyana ba.

Tsintar muryan ta Hajar tayi tana cewa.

“Sanu y’ata yajikin ,naki ?”.

D’ago ido Hajar tayi ta sauke su kan Ummi ,murya ‘a dashe tace.

“Da sauk’i ya jikin Samir ?”.

Ummi bata iya bata ‘amsa ba kawai ta ce da ita.

“Allah ya k’ara sauk’i “.

Sannan tadubi Khadee tace.

“Doc….pls kizo ki salame ,mu Samir yace baze iya zama anan ba pls kizo ki cere masa roban ruwan da kika sa masa tare da na’urorin da kuka saka “.

Tana gama fad’ar haka ta fice.

Kallon Hajar Khadee tayi ta gyed’a mata kai alamun taje amman kar tayi salamar .

Khadee na fita bata ,tsaya ko inaba sai d’akin da ,Dr Samir ya ke.

Tana shiga abunda ta gani ba k’aramin d’aga mata hankali yayi ba.

Shi kad’ai ta samu cikin d’akin yana aman jini guda -guda lokaci guda idanuwan shi suka sauya daga fari zuwa jawuri .

Ko ina najikin shi b’ari yakeyi shi kad’ai yasan abunda yakeji.

Ayanzu sunan Allah kawai yake kira da fatan cikawa da kalmar shada .

Tana ganin haka tayi saurin toshe bakin ta ,tafice.

Duk wanda yaganshi acikin halinan idan yana da imani tow dole yaji tausayin shi , tana fita suka had’u da Ummi na shirin shiga hanun ta d’auke da ruwa.

Yanayin yanda taga Khadee yasata saurin tmby.

“Lfy Doc….”.

Khadee bata iya ce mata komai ba sai girgiza mata kai da tayi ,ta wuce da sauri.

Office d’in Dr devid tashiga ta sanar dashi halin da ‘ Dr Samir yake ciki.

Cikin sauri suka had’a kayan aiki suka ,koma d’akin dak’er Captian ya iya b’an b’are Ummi daga jikin gadon da Dr Samir yake, ya fita da ita waje.

Su Khadee sunyi wa Dr Samir gwaje gwaje sosai, sannan suka k’ara saka masa ruwa sunfi awa d’aya ‘akan shi.

Ko da suka fito su dukan su babu wanda yake walwala , da sauri Captian ya tsaida Khadee da fad’in .

“Khadee ya jikin ,nasa lfy dai kow?”.

Girgiza masa kai Khadee tayi ,kawai tana kallon Ummi tausayin ta, takeji bata iya cewa dashi komai ba sai.

“Kubiyo ni office “

Tana kaiwa nan ta wuce.

Captian babu yanda beyi ba da Ummi akan tabari yaje shi kad’ai ba’ amman tak’i yarda .

  *********

D’akin, ne yaji yana juya masa duk yanda yaso da ya tashi ‘Amman ya kasa don wani ‘irin zafi da zugi yakeji.

Hanun damar sa me karaya ,ya d’aga dak’er ya shafa k’afar shi ta dama jin babu komai yasashi ,zaro ido.

Hawaye kawai yake fitarwa masu zafi, be tab’a tsamanin zai shiga halin da yake Ciki a yanzun ba, yanzu ne ya gane ainahin abubuwan da yake shukawa ya fara girbewa,

Yanzu ne ya fara ‘ainahin ,nadamar abubuwan daya ‘aikata ,a rayuwan shi.

Babu ‘abunda ke motsi a jikin shi daga kanshi sai hanun shi tsaya, wa duba d’akin yayi ,yaga babu wanda yake tare dashi.

Wasu zafafan hawayen ,ne suka ,kuma wanke idon shi.

“Allah ya isa Mama kin cucene kin b’ata min rayuwa ta kece silar duk wani hali dana shi ,bazan tab’a yafe miki ba”.

Afili yake furtawa yayin da yake wani ‘irin ihu yana, neman agaji ,duk yanda yayi, da yatashi ya zauna ‘amman ya kasa.

DIJA_WAZIRIπŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 43

A hankali Ummi ke tafiya ba tare da tasan inda zata ba komai yayi mata zafi, duk yanda taso da hawaye ,ya zubo mata ‘amman ta kasa.

Captian daya fito daga office d’in Dr Khadee yana binta ,da sauri don yasan komai ma ze iya faruwa da ita ‘a halin da take ciki yanzu .

“Ummi pls kitsaya”.

Kiran ta yake amman bata jin komai sai furucin Khadee dake mata yawo cikin kwanyar kanta.

Samir yana d’auke da kedney cancer kuma yana daf da rasa rayuwan shi matsawar ba’a cire kednye d’inshi an cenza masa ba.

Tunani daya fad’o mata shine meyasa ,Samir ze b’oye mata ?.

K’afafuwan ta ,taji sun kasa d’aukar ta .durk’ushewa tayi a dade kofar da ze sadata ,da dakin Dr Samir tasa fuskar ta cikin tafin hanun ta, tana sakin wani ‘irin kuka mara sauti.

Matsawa kusa da Ita Captian yayi ,ya dafa kafad’an ta yana rarashin ta, a haka Salma tazo ta same su.

Ummi ko d’aga ido ta kalli Captian batayi ba , ta mik’e tashige d’akin .

Gefen inda yake ,kwance ta nema ta zauna idon shi a rufe hanun shi ta kama jin yanda zuciyar ta ke bugawa da sauri da sauri.

“Na d’an dana zafin mutuwar iyaye ,na kuma d’an d’ani zafin mutuwan miji.

Tunda natashi nayi wayo nayi aure a wahala nake ban san miye dad’i ba , kaine silan farin cikina kaine gatana ‘ayanzu kai kad’ai nakeda.

Bazan iya jure ganin ka haka ba, Samir ban tab’a sanin ya akejin zafin mutuwar d’a ba , idan har nabari ka mutu bayan inada ,da ‘abunda ‘ake buk’ata wanda ,ze iya ceto rayuwan ka ban kyauta ma kaina ba.

Gara ni ,nasha miya ‘aduniya koyau na mutu nasan ,nabar memin addu’a.

Zan sadaukar da rayuwata saboda kai, farin cikin ka shine ,nawa babu abinda bazan iya bakaba nawa matsawar hakan be sab’a ‘adini ba ,da ‘ana iya cire zuciya ‘a bayar dana cire nawa na baka.

Bana so kowa yayi maka wannan abun saboda ni kad’ai ya cen -canci nayi maka haka shine kad’ai gatan dazan mata kuma shine kad’ai ze iya gane irin soyayyar da nake maka “.

K’asan mayafin ta, tasa tagoge kwalan dake shirin zubo mata ,kafun ta k’ara da cewa.

Zan baka kodana sabo……”

Kafun ta k’arasa taga Samir ya mik’e dak’er yake tashi ya jinguni da jikin gadon hanun sa nakan bakin ta daya toshe saboda karma ta k’arasa zancen ta.

“Ummi ,taya kikayi tunanin ko ,kin bani zan rayu?.

Idan ,narayu mezanyi kuma ‘aduniyar babu ke?

Kokin manta kidney ,d’aya gareki? Ummi soyayyar da zaki min kawai shine kimin addu’a da fatan cikawa shinafi buk’ata ‘ayanzu”.

Duk ,k’arfin halin da Captian yakeyi na danne hawayen da baya so ,suzubo saida suka zubo masa.

“Samir ya mukayi dakai?”.

Captian ya tmby.

Lumshe ido ,Dr Samir yayi ,ya sauke su kan Captian tare da fad’in.

“Junaid na ‘amince maka ‘alokacine sobada, bana son magana .

Kayi hak’uri junaid nasan kamun komai arayuwa kuma duk irin halacin dakamin bani da ‘abunda zan ce maka sai fatan ‘Alkairi , wannan shine karo na farko dakayi min kyauta ban k’arb’a ba”.

Captian bece dashi komai ba ya fice.

Kallon shi Ummi tayi tare da wani tausayin shi tace.

“Idan baka ,karb’a ba Samir wlh sai dai aci…..”

Kafun ta k’arasa yayi saurin tareta da fad’in.

“Bana son rantsuwan ki Ummi na ‘amince “.

Ajiyan zuciya ta saki ta kalli Salma tace taje d’akin da ‘Akram yake ,kow ya farka.


Roban ruwan dake hanun ta, ta cire ta kalli su ,Ummi tace

“Mami ku, koma gida naji sauk’i zamu taho da Khadee idan ta gama”.

Kallon ta Mami tayi lokaci guda ta kuma burkicewa kamar ba Hajar d’in taba.

“Kin tabbata ?”.

Ummi ta, tambaya.

Murmushi tayi wanda iya kacin sa fatar baki ,ne amman zuciyar ta bak’i ,kirin ,ne komai ya dawo mata sabo kamar ayanzun yake faruwa .

Da ,da hali ma gidan zata bisu don jitayi shi kanshi asibitin ma ta, tsane shi.

“Kune Mami babu komai”.

Mami ta barta ne kawai badon ta yarda ba suka ,tafi.

Tashi tayi ,tasa mayafin ta da takalmin ta ,tafice office d’in Khadee ta shiga ,yanayin yanda taga khadee yasa ta k’arasawa ta zauna tana .

“Lfy Khadee?”.

Sai lokacin Khadee ta ,d’ago ta kalli Hajar d’in , mamakin k’arfi Hali ‘irin na Hajar taji, bata ,tab’a tunani ‘idan ta ,tashi zata dawo dai-dai ba.

Bata san sanda ta furta.

“Hajar kece kuwa?”.

Murmushi Hajar tayi, tace .

“Nice mana Khadee lfy”.

Girgiza kai Khadee tayi tace.

“Gsky na jinjina ma k’arfin halin ki, ban tab’a kawowa zaki iya walwala haka ba”.

Girgiza kai ,Hajar tayi ,tace.

“Tow ya zanyi Khadee kashe ,kaina zanyi ko me, shekara nawa najima ina jin ciwan shi.

Bawai yanzun ma bana ji bane wlh ganin Akram ya miyar min da komai sabo kamar ayanzu suka faruwa.

Amman yanda naji rayuwan shi ta kasance a yanzun ma kawai yasa na sare ,ko a yanzu wlh Al lah ya bimun hak’ina Khadee ko haka ‘Allah ya barshi ,shi kad’ai darasi ne “.

“Haka ne”.

Khadee ta fad’a yayin da take sauke numfashi.

Tablet d’inta ,ta mik’a, ma Hajar tana mata nunu da ‘abun dake jiki.

“Miye wanan d’in kuma Khadee?”.

Hajar ta ,tambaya , sai da Khadee ta sauke wani ajiyar zuciya sannan tace .

“Hajar Dr Samir yana buk’atar taimakon mu , yana cikin wani hali ” .

Nan ta kwashe duk halin da ,Dr Samir yake ciki ta fad’a ma Hajar.

“Kuma gsky mu bazamu iya, yi masa wannan aikin ba ,bamu da yakan su ,shine nadubo wani hospital a new delhi aikin su kenan “.

Murmushi Hajar ta saki ta kalli Khadee tace.

“Meyasa kika ce mu bazamu.iya, yi masa ‘aikin ba Khadee?

Wai meyasa ne mu yan najeriya bazamu had’a k’arfi muma ,muga munayin aiki kamar yanda su cen k’asashe waje keyi ba?

Meyasa da zarar munga cuta, tayi tsanani ajikin mutum sai muce zamu turashi k’asar waje?

Me suka fimu ne wai da…..”

Kafun ta k’arasa Khadeee ta katse ta da fad’in

“Hajjo kema dai kin san akwai ban ,banci sosai .

Na d’aya sun fimu kayan aiki ,mu shine babban abunda yake tauye mu kuma sun fimu abubuwa da,da ‘ama”.

“Khadee tayaya ‘ake samun kayan aiki? Ina ce dai abun kud’ine ? Tow mu zamusai komai inaso mu kafa tarihin da ba’a tab’a kafawa ba ‘a wannan asibitin insha ‘Allahu muma zamuyi amfani da ilimin mu kuma zamuyi ‘iya k’ok’arin mu na ganin komai ya tafi daidai.

Koda ‘ace Dr Samir be rayuba gurin wannan aikin da zamuyi masa, dama ‘Allah ya rubuta iya lokacin daya d’iba masa ne ya ciki, bawayon muba kuma ba dabaran mu ba “.

Kalon Hajar kawai Khadee keyi tasan duk wani abu da takeyi a yanzun k’arfin haline kawai.

Kamo hanun Hajar tayi tace

“Kinyi gsky Hajjo insha ‘Allah zamuyi ‘iya bakin k’okarin mu na ganin anyi masa komai cikin lfy Amman gsky ina tsoro Hajjo”.

Murmushi Hajar tayi ta kuma damtse hanun Khadee cikin ,nata ,tace .

“Karki damu insha ‘Allah babu wata matsala, tashi muje d’akin ,nashi”.

Babu musu Khadee ta mik’e suka fita.

*

kwance ta sameshi ‘idanun shi alumshe ga dukkan alamu ba ,bacci yakeyi ba, Ummi kuwa na gefen gadon shi kan carfet ,tana zaune.

Har gefen shi ta, taka ta ,ta nemi kujera ta zauna, tana zama sai ga Captian ma ya shigo d’aki .

“Sanu Dr Samir ya jikin ,naka “.

Muryan ta da’alamun tana sonyin kuka tayi maganar, don tausayin shi taji ya kama ta, barin ma Ummi dataga ta d’un kule guri d’aya tana kuka mara sauti.

Sai a lokacin ya sauk’e jajayen idon shi kan ta, itama shid’in take, kallo ,kallo d’aya, yayi mata ya sauke idon shi daga nata

A raunane yace

“Jiki da sauk’i Hajjo, inajin zuciyata kamar zata fasa k’irjina ta fito Hajjo, inajin gabaki d’aya duniyar ta isheni bana jin dad’in komai Hajjo.

Ina jin takaicin ,cewa ‘Akram k’anina shine sanadin wargajewan duk wani farin cikin, ki, kuma ina jin d’acin cewa shine Mahaifin Jawahir.

Inaji dama’ace ba uba d’aya muka fito dashi ba , wlh da ‘ace kisa ‘abune mekyau dana k’arasa ‘akram yabar duniya ,kaico ,wannan wace irin rayuwa ce”.

Tari ya farayi jini ,na fita, ta hancin sa da sauri Ummi ta mik’e ta rik’oshi tana goge masa jinin da Hanki.

Hajar kuwa ,wani kuka takeyi me sosa zuciya, gabaki d’aya taji komai ya tsaya mata, fari ya koma, mata bak’i haske ya koma, mata duhu , ko d’an yatsan ta ,ta kasa d’agashi don ta daskare akan kujeran da take zaune sautin kukan tane kawai ke fita .

Khadee ce tanufo inda yake don ta, taimaka masa yayi saurin tsaida ita, sannan ya maida kallon shi ga Hajar.

“Na jima ina,neman wanda ya miki wannan d’an yan aikin don ,na hukun tashi Allah bebani dama ba,

Yau danaji d’an uwana ,ne yayi miki wannan aika ‘aikan wlh nayi girgizan da ko sanda mahaifina da matata, suka rasu banyi ‘irin shiba.

Mahaifin mu, mutumin kirki ne har bayan ransa mutane suna yaban halayan sa, Mahaifiyar Akram itace silar tab’ar b’arewan tarbiyyan Akram.

Wlh duk ,da ‘akram d’an uwanane badon ya nakasa ba, wlh da ‘ashirye nake da hukun tashi dede ,da ‘abun dayayi miki Hajjo”

Dak’er ya mik’e daga kwanciyar da yayi, ya had’e hanun shi.

“Hajjo don Allah kiyi hak’uri nasan baki son ko ganin mu ayanzu, nasan muma ya shafa mana bamu k’ad’ai ba duk dangin mu ya shafa mana.

Ya tozar tamu ya tona mana’asiri, ya zubar mana da mutunci .

Da wannan ,nake rok’on ki da kiyi hak’uri , k’adaddara ce kowa da irin tasa, ke taki d’adaddaran ce haka”.

Joyawa yayi da kallon shi kan Ummi yace.

“Ummi ki yafe min ba lalle nakai gobe, ba ,bakuma lalle nakai anjima ba,

Captian Hajar kuyafe min kuma, haka , kawai yau nake kwad’ayin naga yayi muku wasiyya.

Ka rik’e Hajjo da hanu biyu don Allah kad ka watsa mata k’asa’a ido , nasan baka da mak’iyi ayanzu daya wuce Akram ,don Allah ka dubi girman Allah albar kacin annabi muhamad kad ka wulak’anta Jawahir.

Ka rik’eta ‘amana yarinya ce batasan komai ba,”

Ummi na hawaye ,ya dafa kafad’an ta yace.

“Ga mahaifiyata Captian amana bata da kowa saini ,nima bani da kowa sai ‘ita don Allah kad ka bari ta wula k’anta ‘aduniya kad ,kabari tayi kukan rashina.

Hajar ga ‘amanar Ummi na, nasan zaki ,kula min da’ita ,

Shine Kad’ai Alfarman da nake nema ‘agare ku bayan raina, ku, kulamin da mahaifiyata, da kuma Jawahir ,”.

Gabaki d’aya, yan d’akin ,kuka sukeyi ,kamar ba gobe, Captian duk yanda yaso da k’arfin halin shi, saida yayi hawaye.

Ummi kasa jurewa tayi tabar d’akin tana wani ‘irin kuka , babu wanda ya iya tsaida ta harta fice.

“Captian pls zoka d’agani ,ina son akaini d’akin akram zan….”.

Kafun ya gama rufe bakin shi Salma ta shigo ‘a guje.

“Lfy Salma?”

Captian ya tmby

A firgice Salma tace yan sanda, ne sukazo tare da wata mata, wai kuma zasu tafi da’akram, “.

Sai a lokacin Hajar ta d’ago ta kalli Salma, bata ce dasu komai ba ta mik’e tayi d’akin da Akram ,ke ciki, zuciyar ta na wani ‘irin bugawa da sauri da sauri .

Dad tagani tsaya tare da wasu yan sanda, da kuma wata datijuwan mata bak’a.

Muryan da bazata, tab’a mancewa dashi ‘arayuwan ta bane taji yana magana.

“Ku tafi dani, wlh bani da baki magana na cencenci fiye da hakan ma, yanzu na fara girban abunda na shu-shuka.

Wlh da zakuyi min gata’ayanzu shine kawai ,kukashe ni bani da sauran amfani aduniya , kaico na, kaico da irin wannan rayuwan tawa.

Nagode Allah daban haihu ba, don wlh bazanso ayiwa,y’ata ‘abubuwan da nayi ba, kuma bazan so d’ana ya d’auki halaya irin tawa b…..”.

Kafun ya k’arasa ida zancen sa Dad yayi saurin katseshi da cewa rai ‘a b’ace.

“Dama zakayi tunanin baka da, y’a mana saboda lokacin daka b’ata min y’ata bakayi tunanin komai ba.

Tow kasani Hajjo katafi ka barta da ciki, kuma ta haife maka, don haka baka fara girban ‘abunda ka shuka ba sai nan gaba.

Zan ,nuna maka cewa ka tab’o ni kuma zakasan yar wa ka tab’a”

Rai a b’ace Dady yace wa yan sanda ku ,kamashi ku tafi dashi, daga nan har birnin sin sai munyi shar’a dashi”.

D’aya daga cikin yan sandar ne yace .

“Alhaji bazamu iya tafiya dashi yanzu ba har sai ya warke zade mu cigaba da tsare shi”.

Cikin zafin ,nama Dad yace .

“Bade a hospital d’ina ba ,kufita min dashi bana son ganin shi”.

Saurin tsaida shi Hajar tayi da idanun ta da suka, koma jawur.

“Dady kayi hak’uri ka barshi ,ko ayanzu ya koyi darasi, kafa kaleshi amfanin me ze sakeyi nan gaba? Duk abubuwan da yayi abaya wlh be isa ya sake yin suba “.

D’ogo kai Akram yayi, ya sauke su kan hajjo, be tab’a tsamanin ze sake had’uwa da ita ba..

BY DIJA_WAZIRIπŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Duk naji k’orafe k’orafen ku, dakuma ra’ayoyin ku ,kuma naji dad’i sosai da kulawan da kuke nunawa ,wannan litattafi.

Amman ‘abunda nikeso ku gane ,shine karku damu da ,komai dayake faru cikin littafin ,nayi muku alk’awarin akwai happy ending ,abunda nafiso ku fahimta, shine darusan dake ciki

Ina fatan zaku bini sanu a hankali, har Allah ya bani ‘ikon kawo k’arshen sa

Chapter 44

Wannan karon kwala yaji sun kwaranyo daga cikin idanun sa , yanaji wani abu tun daga tsakiyar kanshi har cikin ,naman jikin sa.

Babu abinda ya razanashi, sai furucin da yaji Dad yayi na cewa yana da y’a, har cikin ransa beso hakan ba’ amman ta wani fanin yaji dad’i .

Zuciyar shi ce ke wani ‘irin bugawa da sauri da sauri, farkon had’uwan su kawai ya tuna, da kuma k’arshen rabuwan su.

Wata ,nadama ce ta daban ta ziyar ceshi, da za’a iya maida hanun agogo baya da yamayar ,ya gyara duk wani kuskure daya ‘aikata ‘a rayuwan shi,

Kasa kod’a motsa bakin shi yayi, sai kallon ta yake tana magana da, Dad

“Dad yaki hak’uri ka barshi acigaba da jinyar sa’anan din rama ‘Alkairi ga azalumi ‘ibada ce, badon shi zamuyi ba, kuma badon halinshi zamuyi ba, zamuyi ne don Allah da kuma girman Annabin mu, ae Allah yana sane da, duk irin cin zalin da yayi mun”.

Dad be iya cewa da Hajar komai ba don ranshi a matuk’ar b’ace yake, fita kawai yayi daga d’akin shida yan sandar, da suka zo.

Su Dr Samir duk suna d’akin sunyi cirko cirko Salma ce ta, turo shi a keken marasa lafiya, Ummi ,ma tashigo d’akin.

Juyawa Hajar tayi zata fice tana hawaye, kawai taji muryan Akram yana kiran ta.

“Hajjo pls ki bani minti d’a ya don Allah”.

Tsayawa tayi chak ba tare da ta juyaba kuma ba tare da tace komai ba, zuciyar ta na suya, don ko muryan shi bata son ji.

“Hajjo nayi kuskure arayuwata, sosai nayi wasa da, damata ‘alokacin daya kamata ‘ace na more ta.

Nayi shuke shuke da, dama wanda ban samu damar girbe suba sai yanzu, Kinga yanda ‘Allah ya dawo dani kow , nasan ina da lefi sosai Amman laifin Mahaifiyata yafi yawa, itace sulan shigana cikin matsala, itace silar komai nawa.

Nuna ta yayi da yatsa yace kin cuceni Mama “

Mahaifiyar Akram bata iya cewa komai ba sai kuka da take tayi tun shigowan su da yan sanda.

“Na tashi a wulak’ance ,na tashi cikin k’azan taciyan rayuwa, na tashi bani da uba don kuwa Mahaifiyata, ta samoni a yawon ban….”

Kafun ya ida zancen sa Dr Samir ya d’aga masa hanu da jajayen idanun sa , zuciyar shi nayi masa wani irin rad’ad’i da k’una , kanshi na wani ‘irin juyawa .

“Kana da Uba kuma kai d’an halak ne, ni dakai ubanmu d’aya ,

Mahaifiyar ka ita ce taja maka, komai , kayi gsky bakayi k’arya ba”

Akram da mamaki lulub’e a fuskar shi yace kana, nufin kace min kai d’an uwanane. Kuma kaima wannan mazinaciyar ce….”

Daka ma ‘akram tsawa Dr Samir yayi,

“Kai ,kana da hankali kuwa ‘kasan me kake fad’i duk lalacewa dai ‘ita ce mahaifiyar ka , karna sake jin haka”.

Akram na hawaye yace.

“Mahaifiyar k’adaddara ba, wannan matar tacuceni arayuwa, wlh bazata, shiga ‘Aljana ba, Allah ya isa tsakanina dake “.

Tari Dr Samir ya soma yi don furucin akram sun fara tab’a masa zuciya baze iya jure jin suba.

Duk yanda ‘akayi bugun da yayi akan shi sun tab’a masa brin d’in shi , tari yake sosai har yana shid’ewa duk tarin daze fitar sai jini ya zuba ta hancin sa, Salma da Khadee ne sukayi saurin taimaka masa ,sukabar d’akin dashi, Ummi ma bayan su tabi.

ITako Hajar ta kasa koda motsa d’an yatsan k’afar tane bare ta, tafi tana daskare agurin.

“Hajjo na zalun ceki Allah ma ya sani pls ki yafe min ko zan samu ,sassauci arayuwa ta, nayi nadaman rayuwa ta , don Allah ki ,kawo min yata na ganta ko sau d’ayane arayuwa ta kafun ,nabar duniya.”

Sai alokacin wani k’arfi ya zowo Hajar ta juyo ta kaleshi daga shi ,har mahaifiyar sa,

Wata dariyan takaici ta saki tace

“Yanzu kai bakaji kunyar cewa kana son ganin yar kaba, waya baka ita? Ita ina ka samo ta? Ta hanyar zina ? Kasan duk zakaje ka ‘amsa wainan tambayoyin kow?.

Tow kasani wlh !wlh!!wlh!!! Har abada,bazaka tab’a sanin taba kuma bayar ka bace,

Maganar hakuri kuma, baka cencenci nayafe maka ba kuma baka isa na yafe maka ba, kuma baka ,kai matsayin da zan yafe maka ba, zan yafe makane kawai saboda nayi koyi da fiyayyan halitta ‘Anabi muhamadu, dayace damu ,muzama ,masu hak’uri a inda mukasan muna da k’arfin ramawa , mu zama. Masu tawakali ,kaji dalilin dayasa zan yafe maka.

Ko yanzu Alhamdulilah Allah ya bimun hakina, ko yanzu addu’a ta ,ta k’arbu , ko yanzu Burina ya ciki.

Dama bani da Burin daya wuce naga ka wulak’anta ‘aduniya ka tozarta ‘aduniya bama kai ,kad’ai ba da ,duk wanda ‘aka had’a baki dasu, ko a haka ‘Allah ya barka wlh ya rama, min kuma kad’au darasi bama kai d’aya ba harma da masu Hali ‘irin ,naka.

Sai kuma kajira hukunci da Ubangiji zaiyi maka tsakanin ka da y’ar ka”.

(Rayuwa ba komai bace face makaranta , kuma litattafi ce wace idan ka bud’e wannan babin ka ,karance shi tow gobe bashi zaka bud’e ba wani daban zaka ,gani, yan uwa musani cewa duniya ba wajen zama bane aro aka bamu kuma yanda mukazo haka zamu koma.

Ku sani cewa mutuwa bata salama, zuwa takeyi aduk sanda lokacin zuwan ta yayi, mezai hana mu watsar da, duk wani rayuwan duniya mu rungumi abunda ‘allah ya turo muyi.

Da yawan mutane sukan manta, cewa ‘akwai mutuwa ,akwai ciwo akwai k’adaddara, suyi ta shuka tsiyar su a duniya, suna tunanin ,nan gaba zasu gyara.

Basu ,san cewa lokaci k’urewa yakeyi ba rayuwa k’arewa takeyi ba, sai sunga ‘abu ya jagule musu kuma sai ,su fara neman Ubangijin su, bayan lokaci ya riga daya k’ure musu, damar su tariga data kufce musu

Da wannan ,nake tunatar da yan uwana musulmai da mufarka daga baccin da mukeyi , duniya ba wajen zaman ,mu bane

Ubangiji kasa mudace, kasa mufi k’arfin zuciyar mu)

Tana kaiwa nan ta kama hanyar fita jin anrik’ota yasa, ta ,tsayawa.

Maida hankalin ta, tayi kan wanda ya rik’e mata k’afa ganin Maman Akram yasa ta jin wani bugun zuciya.

“Hajjo kad’in daban ce, cikin mutane, ba kowani mutun bane ze iya ,abunda kikayi a yanzun , mun gode Allah ya ,yimiki Albarka.

Tababbas Akram beyi k’arya ba, nice sular gurb’acewar tarbiyayyar sa, nice silar shigarshi duk wata ,matsala, nid’in karan kaina ,nasan ba ‘uwa ta gari bace, na kasance mace meson abun duniya, na zalunci abokiyar zamana tare da mujin mu , na kasance mace meson kanta da yawa, arayuwa zan iya komai akan ,kud’i.

Yau jibi yanda ‘Allah yayi dani, abubuwan dana shuka ,su nake girba, kaico na kaico da masu hali ‘irin ,nawa , bansan makomata ba ,wlh ban san matsayina ‘agurin ubangiji naba.

Saboda ni, nasan ,nayi abubuwa dadama na zunubi arayuwa ta, Hajjo nima dole na ,nemi yafiyar ki saboda nice anadin komai nice sula , don Allah kiyafe min”.

Hajar nason tayi kuka ‘amman ta danne zuciyar ta, wani dariyan takaici ta kuma sakewa tace.

“Karki damu ,Mama nikam ,nayafe miki duniya da lahira, fatan da nike miki dai shi Ubangiji ya, sau-sauta miki, ya kuma yaye miki zunuban ki ,na barku lafiya”.

Tana kaiwa nan ta fice daga ,d’akin ,komawa Maman Akram tayi gareshi, ta dinga bashi ,hak’uri da neman yafiya ‘akan irin tarbiyayyar data bashi dak’er ya ‘amence ya ,yafe mata, yan sanda ,suna jiranta bakin k’ofa ,sun barta , zuwa gobe zasu tafi da ita.

**

“Talatu kamar akwai abunda kike shiryawa , kwana biyu sai naga kina ta murmushi ke d’aya”.

Wani shu’umin ,murmushi Talatu, ta saki tace.

“Susu , akwai dalilin wannan murmushin ,nawa ‘Amman ki bari zuwa jibi zaki gane manufar ,murmushina, zan shayar daku madaran mamaki, ke bama ku ,kad’ai ba har dangin mu gaba d’a ,wlh sai na yi abunda zasuji kunya muje zuwa”

Murmushi Susu tayi tace.

“Kidai bi ahankali Talatu nasan halin ki, kuma kinsan baki shike ,karya wuya, ki dena fad’in haka ,kad wani abu ya faru ‘a dangi ace kace”.

“Tow sai me Susu afad’a idan anfad’a tsiro zemin ? Koka mutuwa zanyi? Koka shize hanani cigaba da walwala ?”.

Girgiza kai Susu tayi tace.

“A’a ko d’aya ‘amman ,nidai nace miki ,kibi duniya ‘asani ,kinfa girma Talatu kefa ba yarinya bace ,yakama ‘ace kinwa kanki ,karatun tanutsu, Alhaji Hadi ya jima yana k’aunar ki ,kin tsaya shirmen banza da hofi, Umma tayi maganar har tagaji, ta zura miki na mujiya ‘Abba ma kafun ya rasu ,yayi yayi ,ya gaji, muma ,munyi munyi mun gaji haba Tali kiyawa kanki fad’a tunkan lokaci ya k’ure miki”.

Talatu idon ta cike da bala’i da masifa tace.

“Eyee lalle Susu wuyanki, yayi kwari ya isa yanka, yanzu ni kike fad’i ma haka?, tow dan gidan ku bazanyin ba ko ,ina da ,damar da zaki min, ne? ,shasha kawai”.

Tana kaiwa nan tabar d’akin tana jan tsaki.

*
“Sanu Dr Allah ya baka lfy ni zan wuce gida, dare yayi ,insha ‘Allah jibi zamuyi masa’Aiki Captian idan akwai wata matsala zaka iya kirana “.

Khadee na gama fad’ar haka ta kwashe komo tsanta, tayi gaba.

Shiko Dr Samir a halin da’ake ciki ma baya iya magana, sai da kawai ya d’agawa mutane hanu ,

Wurin k’arfe tara na dare lokacin Dr Samir yana bacci Maman Akram tazo ,ta dubashi sanan ,suka zauna sukayi doguwar magana da Ummi , sosai Maman akram ta nuna mata, nadamarta ‘afili sananna ta nemi gafaran ta, daga nan kuma ta, tambayi abunda ke damun Dr Samir babu abinda Ummi ta b’oye mata ,ta gaya mata koma.

Jin, jina kai ,kawai tayi ,tana me ganin k’okari da juriya irin ,na Dr Samir.

Koda ta koma d’akin Akram bata b’oye masa komai game da’abunda ke damun Akram ba
.

Jin ,jina kai yayi lokaci guda ya fara hawaye ,yana duban Maman tashi da ido yace.

“Mama daga safiya zuwa yanzu ,nayi kuka babu adadi, nayi nadama babu adadi, Mama jibi yanda rayuwata, ta koma.

Ina son tashi na kasa ina son juyi na kasa, ina son inji ‘ina motsa kafafuna da hanayena ‘Amman babu dama.

Yau mun wayi gari bani da k’afa ,d’aya bani da hanu d’aya , bazan kuma tashi ba, wannan yana ,nufin haka zan dawama har k’arshen rayuwa ta,

Wannan yana, nufin bazan kuma ,moruwa ba, ina son ,naje naga d’an uwana ‘amman babu dama ina son ,naga d’iyata koda sau d’ayane a rayuwa ta, Amman hakan bame yuwa bane.

Duniya kenan ,duniya makaranta , rayuwa ‘abin tsoro, wato shi rayuw kamar pencil yake ahankali yake cinyewa har yazo k’arshe, Mama da ina da hali dana gyara kuskure na, pls mama kimin ,magana da ‘wannan abokin d’an uwan ,nawa da kuma ,mahaifiyar shi ‘ina son magana dasu kafun ,na cika.”

Yanda ‘ Akram d’in ya buk’ata hakan tayi Amman Captian dak’er ya, yarda yaje Saida Ummi tasa baki tukun.

*

Idon shi na rufe ya kama hanun Captian yace.

“Naji irin sadaukarwan da kayiwa d’an uwana , kuma hakan yasa naji dad’i, mungode mungode Allah yabar zumunci.

Amman ina, neman wata ‘alfarma guda ,d’aya ‘agurin ka “.

Yana kaiwa nan yayi shiru.

“Ina jinka “.

Captian dayaji shirun yayi, yawa ,yace haka.

Saida ‘Akram ya busar da iska daga bakin shi, ya sauke wani ajiyar zuciya, sannan ya sauke idanun shi kan Captian yace.

“Ka barni ,na bawa Samir k’odata, pls ina son , nima naga nayi masa wani abu ‘arayuwa ta koda sau d’aya ne kafun ,nabar duniya”……

By Dija_WaziriπŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 45

“Ina son ,naga nima na faran ta masa pls Junaid kayi hak’uri ka barni”.

Hawayen da ya zubo cikin idon Captian ya goge, yana jin tsanar Akram har cikin naman jikin sa, yayi k’arfin halin cewa.

“Babu damuwa ‘Akram d’an uwan kane, kuma kana da, damar da zaka iya bashi koma ,miye, Ubangiji ya baku lfy”.

Yana kaiwa nan ya tashi ya mik’e ya fice daga cikin d’akin.

Ummi na kuka ta kama hanun Akram tace.

“Allah ya baka lfy Akram Allah ya saka maka da mafificin Alkairi akan wannan, irin sadaukarwa da kayi ma d’an uwan ka, Ubangiji ya baka ladan ,niya.

Allah ya ,yafe maka ,kura kuren ka, wannan jarabobi da kake gani k’addara ce Allah ya sasauta maka”.

Akram idanun shi arufe yana wani’irin ,nishi yace .

“Ameen Ummi bana son cigaba da rayuwa ‘anan duniya bana so , a yanzu nafi buk’atar mutuwa ‘akan kome na rayuwan duniya, kuyi min addu’an cikawa da imani kawai shi nafi buk’ata ‘ayanzun”.

Ummi na kuka, tare da tausayin Akram ,jinshi take tamkar itace ,ta haife shi,

Hak’ika be samu ‘uwa tagariba ‘a rayuwan shi, da Mahaifiyar shi batabi son zuciya ba, da, duk hakan be faru ba.

Kama hanun shi tayi, tace.

“Tabbas Akram ,mutuwa itace zata ,zame maka hutu, a irin wannan halin da kashiga ‘ayanzun,

Amman ,mud’in munfi son ganinka, a hakan da rashin ka, ba mutuwar ake tsoro ba’abunda mutuwar ze haifar ake tsoro bayan babu kai”.

Murmushi Akram ya saki ,kawai ba tare da yace komai ba, hakan yasa Ummi ta, tashi ta fita, takoma d’akin Dr Samir.

Tana shiga ta samu Salma harta dawo daga, gida ta gyara musu inda zasu kwanta. Ta kuma taho musu da’abinci.

Dak’er Ummi ta iya shan, shayi shima saida Salma ta matsa mata sannan tasha badon tana jin dad’in shiba.

**

“Khadee ya jikin Dr Samir d’in hope da sauk’i ,kow?”

“Tow zan iya cewa da sauk’i Amman gsky yana jin ,jiki sosai, saidai fatan sauk’i kawai, nace Captian idan akwai matsala ya sanar dani koma yaushe ne”.

“Tow Allah ya bashi sauk’i.

Wlh Khadee nifa har yanzu fad’uwar gaba ,nakeji sai nake tunanin kodai , akwai abunda ze kuma faruwa dani”.

Dafa kafad’ar ta khadee tayi tace.

“Babu komai fa insha ‘Allah kawai ganin Akram ,ne ya girgiza ki ,ki, kwantar da hankalin ki dan Allah,

Karfa ki manta jibi ne d’aurin auren ki”.

Sai alokacin Hajar ta, tuna da ,d’aurin auren wani fargaba da tashin hankali ne taji sun kuma ziyartan zuciyar ta, lokaci guda taji k’irjin ta na dukan tara tara.

Jawahir dake ,kwance kusa da ita, ta kuma ,matsewa ‘ajikin ta kamar wacce ake shirin kwace ta, lokaci guda ta fara tunani yanda ‘Captian ze k’arb’i Jawahir da kuma, matsain daze sata.

Haka ta dinga sak’e sak’e har bacci b’arawo ya sace ta.

*
KARFE UKU DA MINTI D’AYA NA DARE

“Hajjo tashi “.

Kamar a mafarki taji k’iran Khadee , ba tare data bud’e idanun taba ta juya taci gaba da baccin ta, tana.

“Pls ki barni Khadee wlh dak’er na samu bacci ya kwashe ni”.

Khadee na kanta, ta kuma cewa .

“Hajjo ki tashi muje Hospital Dr Samir ciwan shi ya tashi sosai, yanzu Captian ya kira ya sanar dani wai sumar sa ‘uku, kuma sai wani’irin ,nishi yakeyi kamar ,me neman, mutuwa”.

Babu shiri Hajar ta wangale idon ta, kamar ba ita bace wanan me gigin baccin,

Ko ,kallon Khadee batayi ba, tadiro daga kan bed tazari hijabi da key d’in mota, tace.

“Mutafi”…..

Sauka ,k’asa ,sukayi suka ,wuce ko su ,Ummi basu ,sanar wa ba, suna zuwa me gadi ya wangale musu geta, suka fice.

Taka motar, take da mugun k’arfi cikin ,mintuna kad’an suka, k’arasa ‘cikin asibitin.

Suna zuwa ,sukayi sa’a Dr Dived yana ,kusa be tafi ba, suka ,kira shi , suka had’a kayan aiki suka shigar da, Dr Samir wani d’aki , wasu na’urori suka fara jona masa, wanda saida ya d’auke su awa biyu suna yinshi, kafun suka gama , sannan suka saka masa ruwa da roban abinci , suka fito.

Ummi na ganin fitowan su ta nufo su ,tana kuka tace.

“Lfy likita ya ‘ake ciki ya jikin ,nasa kozan iya ganin shi?”.

Murmushin k’arfin Hali Hajar tayi tace.

“Kwantar da hankalin ki Ummi , jikin da sauk’i , insha ‘Allah ze warke.

Yanzu bazaki ‘iya ganin shiba harsai munyi masa’aiki zuwa gobe da ‘azahar insha ‘Allah zaki ganshi.

Yanzu mune kawai zamu iya shiga don, duba lfyn shi”.

Ummi na kuka tace

“Tow mungode Allah ya biya ku, ubangiji ya bashi lfy “

“Ameen Ameen”.

Cewar Khadee.

“Hajjo “.

Hajar taji Captian, na kiran ta yayin da zata wuce office d’inta , tsayawa tayi tare da fad’in .

“Na’am”.

Saida ya matso daf, da ita sanan yace.

“Ya jikin Samir d’in?”.

Kanta ‘ak’asa tace .

“Jiki da sauk’i”.

“Tow Allah ya k’ara masa lfy barin je masalaci na dawo zanzo ,office dinki muyi magana”.

Ji tayi gaban ta na wani ,irin fad’uwa ,bakin ta na rawa tace.

“Tow sai ka dawo”.

Ta wuce shima ya wuce

By Dija_WaziriπŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 46

Bayan ,ya idar da Sallar Asuba ya shigo ya samu Hajar ta kifa, kanta ,kan tabel.

Takawa yayi, ya k’arasa ya zauna sanan yace.

“Hajjo”.

Sai alokacin ta d’ago, ta sauke manya manyan idanun ta kanshi ,tace.

“Na’am harka dawo ne?”.

Da fara’a ,d’auke a fuskar shi yace .

“Eh har mun idar”.

Kanta, ta sunkuyar tace.

“Yayi kyau”.

Shirune ya biyo baya, saida ya gama nazari da tunane, tunanen sa ,sanan ya tsuke baki yace

“Hajjo dama, nazo da wata magana ce akan Aikin da za’ayi wa Dr Samir na dashin k’oda.

Tow da ,dai gsky kamar yanda nayi alk’awari nine zan bashi , k’oda ta, so yanzu kuma bani,bane”.

Be k’arasa ba yayi shiru.

Shirun da taji yayi, ne yasa ta d’ago ta kalle shi tace.

“Ina jinka Captian ya kuma kayi shiru?”.

Saida ya d’anyi jim kad’an sanan yace.

“Akram…”

Jin sunan Akram daya fad’a yasa taji wani fad’uwar gaba, lokaci guda taji yawun bakin ta ya k’afe , kafafun ta sun sage, k’irjin ta ,na wani ,irin bugawa da sauri da sauri, zuciyar ta na yi mata wani, irin k’una.

“Akram yace ze bashi, ya nemi Alfarman hakan daga wajena, ni kuma bazan iya ce masa ‘A’a ba saboda ,d’an uwan shine”.

Hajar b’oye damuwar ta, tayi tace.

“Hakan ma yayi kyau, Allah ya nuna mana ranar, ni zan koma gida, kuma daga yau balale, na sake fitowa ba, har sai bayan d’aurin aure.

So Khadee zasu cigaba da kula da, Dr Samir Allah ya bashi lfy”.

Murmushi yayi ,yace.

“Ameen ,my wife Allah ya nuna mana, darai da lfy, anjima zan, zo”.

“Tow Allah ya kaimu, tow shi auren Dr Samir d’in fa ya ‘ake ciki za’ayi gobe,ne koko sai ya warke?”.

“Da munce a d’aga kawai, Ummi kuma tace kawai a d’aura”.

“Gara ‘a d’aura d’in Ummi tayi gsky matar shi, ta cigaba da jinyar shi, har Allah ya bashi lfy “.

**

“Captian ya shirye shirye, da zirga ,zirgan asibiti”.

Hajar ta, tambaya.

“Gashi muna ta fama dai, yanzu daga nabar nan gidan ku asibitin zan koma, idan ,naga ko mai na tafiya dai-dai sai na je na karb’o d’inki da zan saka gobe”.

“Ae dama ka wuce gurin d’inkin, ka ,kawai don Khadee tace, min komai na tafiya dai-dai, kuma kasan bama samun ganin shi zakayi ba”.

“Haka, ne sai na wuce d’in kawai,kinji wai zariya za’a tafi d’aurin auren ko?”.

“Eh ,Haka Dady ,yace kasan wani kawun mune ze d’aura so baze iya zuwa nan kano ba, shiyasa Dad yace aje cen d’in kawai”.

“Eh duk Abba ya fad’a min,ni wlh ,haka nan yau tun safe bana jin dad’in jikina, kuma sam duk abunda naci sai naji babu test, narasa dalili”.

Murmushi Hajar tayi tace

“Nima dai haka, ni duk satinan ,ma haka nike jina wata iri wlh, sai nake jin akwai abun daze faru”.

“Tow miye dalili hakan? Ubangiji kasa’alkairi ne “.

“Ameen dai “.

Captian saida yad’anyi shiru sanan yace.

“Tow kinga yanzu aure zamuyi Hajjo zamu shiga wata sabuwan rayuwa nidake, duk zunuban mu Allah ze wanke mana shi, hakan yasa nake rok’on ki da kiyafe min duk wani abu danayi miki arayuwa ,saboda ina so gobe ,na fara wata, rayuwan daban”.

Murmushi Hajar tayi tace.

“Nikam bakamin komai ba, nayefe maka nima ka yafe min pls”.

“Baki tab’amin komai ba Hajjo na yafe miki, ina Jawahir kwana biyu ban ganta ba?”.

“Tana ciki”.

Hajar ta bashi amsa.

“Pls d’auko min ita ,ina son ganinta kuma, mu gaisa.”

Yanda yace tayi hakan tayi.

 WASHE GARI

yaune Jumu’a za’a d’aura, auren Hajar da Captian da kuma Dr Samir da Salma bayan Salar jumu’a ‘a Babban masalacin dake yankin zariya.

K’arfe goma da kusan rabi Salma ta koma gida, don d’auko wa Dr Samir kaya, don yau ne za’ayi masa ,dashin koda, k’arfe biyu dai-dai zasu shiga dashi dak’in tiyata, kamar yanda suka fad’a.

Tana shiga ,gidan sashen ,shi ta shiga Darec d’akin shi ta danna kai.

D’akin kaca kaca ,duk ya baza kaya’akan gado, zama tayi gefen gadon ta fara duba masa kaya cikin wanda suke zube agurin.

Tana d’aga wani ,wando ta hango diyari d’in shi ta d’auka.

Ju-juyashi ta farayi a hanun ta, wata zuciyar tana ,kibud’e ki ,karan ta wata zuciyar kuma tana kad, ki bud’e , cikin jakar hanun ta, tajefa shi ciki, tayi sauri ta zab’a masa kaya ta fice.

**

Sanye ,yake cikin wata dakakiyar shedda ruwan toka, yashi aikin hanu, Babban riga ce, sai ya sanya wata Zana buk’ar wacce zata shiga da kayan sosai, ya d’auki takalman shi mekyau da tsada sau ciki ya saka, ya fashe jikin shi da turaruka masu tsada ,da k’amshi.

Kanshi ya kalla jikin madubi.kayan sun balain masa kyau sajen fuskar shi sun kwanta luf, luf saman fuskar shi, ya wani k’ara kyau da haske ,sai dai kuma ya d’an fad’a , wayan shi daya fara, ruri ya d’aga yaga d’aya daga cikin abokan shine, d’auka yayi da Salama yace.

“Abdul ya ‘akayi”.

“Kaji ango tun ba’aje ko ina ba har ka fara cenza min ,murya”.

Dariya Captian yayi yace.

“Kaga malam bana son wanan zolayar taka ya’akayi ne?”.

“Babu komai dama,nakira nace maka, mund’au hanya ne tunda kace kai ,d’aya zaka taho, mukam, munyi gaba”.

“Yawwa ‘Allah yasa kuriga su Abba isa don suma sun d’auki hanya, mu kawai ake jira don ,iyayen Hajjo sun jima da isa, nima yanzu, zan fito insha ‘Allah”.

“Tow kade hanzarta ‘ango sai mun had’u”.

Ya tsinke wayar.

Fita, yayi daga ,d’akin shi yaje sashen Hajiya cike yake, da yan uwa da’abokan arziki, sai tsiya suke masa, beda kula suba har ya samu ya shige d’akin Hajiyar sa.

Zaune ya sameta, ana mata k’itso tsugunawa yayi har k’asa cikin girmamawa yace.

“Sanu Hajiya zan tafi”.

Hajiya na zaune gaban me kitso ta juyo tace.

“Harka fito Junaidu, Allah ya kiyaye, kayi sauri kasan tun d’azu su Alhaji suka fita, kuma kasan baya son jira, ina ce ,cen d’in zakayi, yanzu”.

Cikin girmamawa Captian yace.

“A’a zan biya gurin Dr Samir”.

“A’a menakon ,ko bari sai kun dawo Junaidu?”.

Girgiza mata kai Captian yayi ,yace.

“A’a hajiya kibarni kawai naje, k’arfe biyu za’a masa dashen k’oda ,kuma gsky bazan iya tafiya ban yi masa, salama ba ,nidai addu’ar ki nake buk’ata”.

“Tow D’an lelena, Ubangiji ya tsare min kai yasa kuje a sa’a ku dawo a sa’a yayi maka ‘Albarka, sai ka dawo kuma ‘akula da tuk’i banda tuk’in gan,nanci”.

Mik’ewa yayi, yace.

“Ameen Hajiya nagode kuma insha ‘Allah ahankali zan tafi”.

*

Captian yaje ya samu su Khadee sai had’a kayan aiki suke, kafun lokaci yayi, gurin ta yaje ya nemi Alfarman yana son yaga Dr Samir dak’er ta ‘amince masa don, dokar asibiti ce babu me shiga wanan d’akin sai ,iya likitoci.

*

Kwance ya sameshi ‘idanun shi biyu , yana kallon sama.

Kallo d’aya Captian yayi masa ya kauda kai, don baze iya kuma kallon shiba.

Duk ya rame yayi bak’i ya fita hayacin sa, kamar wani me ciwan H.I.V haka ya koma.

Jin k’amshin turaren Captian ya sashi kallon k’ofa , tsaye ,ya ganshi yana hawaye.

Cikin k’arfin Hali a hankali yace.

“Junaid lfy kake, kuka yau ranar farin cikin ,ka?”.

Maganar tashi ma dak’er take fita.

Saida Captian ya matsa kusa da, Dr samir ya tsuguna jikin gadon shi yace.

“Samir bana jin farin ciki, kamar yanda zakayi tsamanin zanji, naci Burin wannan auren kamar ba gobe.

Amman rashin ka gurin d’aurin auren yasa naji komai baya min yanda ,nakeso .

Tun jiya nake jin fad’uwar gaba Samir bana son katafi ka barni, inaji ajikina kamar akwai abunda ze faru Samir, inajin ajiki ,kamar akwai wani babban abuda ze faru da kai ko dani.

Da ina da hali Da nace bazanje gun d’aurin auren ba, kodon naga lokacin da za’a shiga dakai da kuma lokacin da za’a fito dakai, Amman hakan baze yuwu ba”.

Samir ayanzu kwata kwata baya iya Kuka baya iya hawaye saidai, ya d’inga jin zugi cikin zuciyar shi.

Wani abu yaji ya tsaya masa’a mak’oshin sa, lokaci guda yaji komai ya tsaya masa cak.

Dafa Captian yayi ,yace.

“Ka, kwantar da hankalin ka ‘Abokina ka d’auka cewa komai dake faruwa muk’adaddari ne, da kuma wanda ze faru.

Ina so kayi ‘imani da Allah kuma ya, yarda, da k’adaddara, ka d’auka cewa komai ba komai bane face jarabawa, idan Allah yayi zan fito dole ka dawo ka gani, idan Allah yayi zan tafi dole ka dawo ka samu babu ni.

Ko ,kana kusa dani ko baka, kusa dani dole indan lokacinane dole natafi.

Kuma ina so ka sani cewa cuta bata kisa, sai ‘idan kwana ya k’are, zakaga me lfy ya tafi yabar mara lfy kaga wanan yana, nuni da cewa bafa sai baka da lfy zaka tafi ba.

Da wanan ,nake rok’on ka da katashi, ka tafi gurin d’aurin Auren ka, kad lokaci ya k’ure, Allah ya baku zaman lfy”.

Jiki a sukwane Captian ya tashi ya fice batare da yace wa Samir komai ba.

A k’ofar d’akin ya iske Salma fuskar ta ya kunbura tsabar kuka, so take ta ,tsayar dashi tayi masa ,magana ‘Amman ta kasa tsaida shi ,harya b’ace ma.

Zama tayi ta cigaba da rera kuka, abunda ta gani yau ,ya balain d’aga mata hankali, ji tayi dama tun cen tasan da hakan da, duk Dr Samir be shiga halin dayake ciki ya’yanzun ba.

“Ya ‘Allah “.

Shine abunda ta iya furtawa, yayin data lalubo wayan ta don kiran Captian, ta sanar dashi komai tun kan lokaci ya kure musu…….

By Dija_Waziri
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 47

Hajar tun jiya da, dare take ,kuka ita kanta ,takasa gane ainahin meke damun ta.

Su Mami sunyi rarashin harsun gaji sun barta,

Tunda ta kulle kanta cikin d’aki bata fitoba har safiya kuma duk takashe wayoyin ta.

Haka, kurum taji shi’awar ta keb’e ita kad’ai don bata son hayaniya.

*

Zariya

K’arfe biyu daidai aka gama d’aurin aure ,yan uwa da ‘abokan Captian sai sanya Alkairi sukeyi masa tare da fatan Allah ya basu zaman lfy.

Shiko Captian binsu kawai yake da murmushin yak’e shikad’ai yasan abunda yakeji cikin zuciyar shi, ji yayi gabaki d’aya komai ya cenza masa lokaci guda.

Salama yayi da ‘abokan shi akan shi ze fara gaba, soboda baya jin dad’i kanshi na ciwo , Abdul babu yanda beyi dashi ba’akan ya bari sutafi tare Amman yace suje kawai shi ze tuk’a ,kansa haka babu yanda ya, iya dole suka barshi ya tafi.

*

Mami na gama waya da ,Dady ta nufi d’akin Hajar babu walwala ‘atare da ita .

Tana shiga ta sameta zaune kan gado tana danna wayar ta, tayi wanka fes da ita, tasa wani shedda ruwan ganye yasha duwatsu da fulawu, Amman batayi kwaliya ba sai k’amshi takeyi.

Kusa da ita Mami ta nema ta zauna , fuskar ta da ‘alamun tausayawa tace.

“Hajjo And’aura , Auren ki yanzu Dad ya kira ya sanar dani.

Sanan yace gashi a hanyar dawowa gida yanzu, yana son ya ganki, yana son kuyi wata muhimiyar magana.

Abunda ,nake so dake shine ki ,kwantar da hankalin ki, insha ‘Allah komai yayi ,yanda zuciyar ki, da gangar jikin, ki, keso”.

Tunda Ummi tace And’aura ,Auren ta, taji gabaki d’aya jikinta ya mutu, wani kasalalan ,nufahi ta saki tace.

“Alhmdulh Allah na gode mana daka nunamin wanan rana, wanda ban tab’a tsamanin shi da wuri haka ba”.

Rik’o hanun Mami tayi tace.

“Mami ,ina tunanin rabuwa dake, babban abundake d’agamin hankali, kenan shine zan rabu dake bazamu sake ,kwana gida, d’aya nidake ba , Mami bazan iya barin kiba”.

Goge mata hawaye Mami tayi tace.

“Karki damu Hajjo ai ba mutuwa zanyi ba, kuma gari d’aya zamu zauna dake, mutuncin ki shine d’akin mijin ki, yau ne mahaifin ki yaji sakat cikin zuciyar shi tunda kika malaki hankalin kanki, bashi da wani burin daya wuce yaga, ya ‘aurar dake Amman hakan be yuwu ba sai yanzu Allah ya bashi ,dama .

Dama tunda ‘Allah ya haliceki mace dole zaki ,tafi kibar ni ko, kinaso ko baki so, nidai fatana ‘shine Allah ya baku zaman lfy”.

Ummi na kaiwa ,nan ta mik’e tafita don d’aukar wayan Dady ,daya hau ruri.

“Hello Alhaji lfy dai kow ya hanya kun, kusa ,isowa ne?”.

Banji me yace mata ba sai Salati data fara yi,

“Unnalilahi wa inna ilaihi raji’um

*

Ummi na bak’in kofar da’aka shigar da, Dr samir tiyata, sai kaiwa da kowowa takeyi.

Ganin Dr Aiman ya fito yana cire safar hanun shi yasa, tayi saurin k’arasawa gurin shi tace

“Lfy Doc..na ganka, haka, kamar akwai abunda ya faru, ya jikin Samir d’in?”.

Dr Aiman kallon ta kawai yakeyi batare da yace mata, komai ba idanun shi sunyi jazur kamar me shirin yin kuka.

Hankalin ta idan yayi dubu ya tashi ta kuma kallon shi tace.

“Don Allah Doc..kafad’a min meke faruwa, kow ya mutu ne?”.

Girgiza mata kai, kawai Dr Aiman yayi, ya wuce.

Durkushewa tayi agurin tana wani ‘irin kuka me tsuma zuciya.

Dr Khadee ma haka ta fito daga cikin dakin tana cire, rigar ta jiki babu laka da’alamun tashin hankali k’arara ‘a fuskar ta,

Kallon Ummi tayi bata iya ce mata komai ba ta wuce , don a halin da take, ciki bazata iya magana ba…

BY DIJA_WAZIRI
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

KULLU NAFSIN ZA’IKATIL MAUT😭😭

Shafinan gabiki d’ayan shi sadaukarwa ce gareki, Inna “Allah ya k’ara girma da ‘arziki AmeenπŸ‘

Raruwa takan cenza ma bawa cikin ,mintina kad’an ,Abunda ka saba dashi ze iya cenzawa , zuwa ga wanda baka tab’a tsamani ba.

kowa, da irin tashi k’adaddarn Arayuwa , ba lalle abunda kake so bane kake iya samu Arayuwa.

da yawan mutane sukan saka burin samun wani abu da suke so , idan Allah ya nufa wannan abun ba ‘Alkairi bane agareka, sai kaga ya kawo maka wani sanadin da zaka rabu da ‘abun

Komai yana tafiya da tsarin kaddarar ka

Nasan zakuyi mamakin wanan page d’in sosai, ze tab’a suciyoyin wasun ku ,Amman kuyi hakuri ‘insha ‘Allah nayi muku Alk’awarin komai ze koma daidai

Kuma naji Comments d’in wasu daga cikin fans d’in buk d’inan jiya, Abunda nake so ku gane shine book d’inan ,nariga da natsara shi tun farko , labarin zuwa k’arshen sa, so duk abunda ,dama ze faru tuncen a tsare yake, Fatan akwai shine ku fahimci sak’on da nike son isarwa

Allah kasa mudace kasa muyi kyakyawan k’arshe AmeenπŸ‘

Chapter 48

Dady , ya shigo ,gida jiki a mace idanun shi jazuri kuma duk ya birkice .

Zaune yake, kan kujera’a falon k’asa ya had’a yanayen shi cikin tafukan hanun shi, zuciyar shi na wani ‘irin bugu da Sauri da sauri.

Hajar na gefen shi a Zaune a kan Carpet, Mami na kusa, dashi tana zaune itama tayi jigum, tausayin yar, tata kawai takeji, Aunty Asma’u kuma na d’aya daga cikin kujerun falon itama tana Zaune tayi tagumi.

Hajar tunda ta shigo falon gaban ta, te wani ‘irin dokawa , zuciyar ta na wani ‘irin matsewa kamar kayan da ‘aka matse kafun a shanya.

Jin Furyan Dad yasa ta maida hankalin ta kanshi.

“Hajara”.

Dad ya kira sunan ta,

Ras taji k’irjin ta yayi, tasan duk yanda’akayi ba k’aramin ,magana ‘ Dad zeyiba tunda ya kira sunan ta da Hajara, don be saba kiran ta da hakan ba.

D’aga idanun ta, tayi tace .

“Na’am Dad”.

Tana shafa lalausan gashin carpet d’in dake shinfid’e a falon.

Saida, Dad ya d’an dakata, na dak’ika guda sanan yayi k’arfin halin cewa.

“Hajara, Kinga jarabobi da, dama ‘arayuwan ki, kinga tashin hankali, iri da kala, Hajjo ina so ki d’auka cewa hakan baze nuna cewa ‘Allah bayan son ki bane da yake ta jaraftar ki, kuma karki d’auka cewa baya sane dakene.

Duk wani abu da kikaga ya faru dake, da sanin shi kuma shida yasa hakan ta faru dake shi ze yaye miki, ina so abunda zan fad’a miki ayanzu , kad ya k’arya miki zuciya.

Ina son ki d’auka cewa ‘Babu wanda ze iya ja da ikon Allah, bazan iya hanaki, kuka ba don ,nasan dole zakiyi, Amman daken samune Addu’ar ki shi yafi buk’ata’ ayanzu”.

Surutan Dady taji suna mata yawo a kwanyar kanta, alokacin taji komai ya d’auke mata d’if kamar d’aukewan wutan lefa, abunda take iya furtawa cikin zuciyar ta shine k’ardai, Dr Samir ya Rasu ,shine abunda ta iya furtawa.

Komawa da hankalin ta kan Dady tayi don taji Mumunan maganar da zata fito daga bakin sa..

“Ayau da misalin k’arfe biyu an d’aura miki aure da, Dr Samir !!! Abisa, sadaki naira dubu hamsin.

Sannan Abu na biyu shine Munyi rashin ,mutum ,mafi muhimaci a gareki, bake ,kad’ai ba mu gabaki d’a , mutun me karamci me hakuri da sanin ya kamata,

Hajjo saidai kiyi hakuri, dama ‘ance dukkan merai mamaci ne Allah yayi wa Captian Junaid rasuwa, a hanyar shi ta dawowa kano bayan and’aura ‘aure”.

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” ta fad’a a fili tana dafe da k’rji, idanunta ya cicciko da ruwan hawaye ,yayin da jikinta ya d’auki rawa.

Furucin shi na jiya ne ya fad’o mata.

“Kiyafe min Hajjo ina so nashiga sabuwan rayuwa gobe”.

Bata ,tab’a sanin zaka iya jin tarwatsewan zuciyarka ba sai a wannan lokaci.

Tashiga tashi hankali da, dama ‘arayuwa ‘Amman wannan yasha banban da sauran, bata tab’a gane rayuwa ba ‘abakin komai takeba sai ayau d’inan.

Wani irin ,numfashi taja ,tanajin yanda zuciyarta ke tafasa kamar hot water,hawayen da take jine. Suka zubo mata a hankali.

KAFUN D’AURIN AURE

Kud’an ,k’ara min uzuri nasan page d’in yana muku kad’an karku d’auka hakan jan rai ne wlh ina busy ne Amman insha ‘Allah na samu dama gobe zamu gaba, bakid’aya novel d’in.

By Dija_WaziriπŸ’‰
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Chapter 46

Bayan ,ya idar da Sallar Asuba ya shigo ya samu Hajar ta kifa, kanta ,kan tabel.

Takawa yayi, ya k’arasa ya zauna sanan yace.

“Hajjo”.

Sai alokacin ta d’ago, ta sauke manya manyan idanun ta kanshi ,tace.

“Na’am harka dawo ne?”.

Da fara’a ,d’auke a fuskar shi yace .

“Eh har mun idar”.

Kanta, ta sunkuyar tace.

“Yayi kyau”.

Shirune ya biyo baya, saida ya gama nazari da tunane, tunanen sa ,sanan ya tsuke baki yace

“Hajjo dama, nazo da wata magana ce akan Aikin da za’ayi wa Dr Samir na dashin k’oda.

Tow da ,dai gsky kamar yanda nayi alk’awari nine zan bashi , k’oda ta, so yanzu kuma bani,bane”.

Be k’arasa ba yayi shiru.

Shirun da taji yayi, ne yasa ta d’ago ta kalle shi tace.

“Ina jinka Captian ya kuma kayi shiru?”.

Saida ya d’anyi jim kad’an sanan yace.

“Akram…”

Jin sunan Akram daya fad’a yasa taji wani fad’uwar gaba, lokaci guda taji yawun bakin ta ya k’afe , kafafun ta sun sage, k’irjin ta ,na wani ,irin bugawa da sauri da sauri, zuciyar ta na yi mata wani, irin k’una.

“Akram yace ze bashi, ya nemi Alfarman hakan daga wajena, ni kuma bazan iya ce masa ‘A’a ba saboda ,d’an uwan shine”.

Hajar b’oye damuwar ta, tayi tace.

“Hakan ma yayi kyau, Allah ya nuna mana ranar, ni zan koma gida, kuma daga yau balale, na sake fitowa ba, har sai bayan d’aurin aure.

So Khadee zasu cigaba da kula da, Dr Samir Allah ya bashi lfy”.

Murmushi yayi ,yace.

“Ameen ,my wife Allah ya nuna mana, darai da lfy, anjima zan, zo”.

“Tow Allah ya kaimu, tow shi auren Dr Samir d’in fa ya ‘ake ciki za’ayi gobe,ne koko sai ya warke?”.

“Da munce a d’aga kawai, Ummi kuma tace kawai a d’aura”.

“Gara ‘a d’aura d’in Ummi tayi gsky matar shi, ta cigaba da jinyar shi, har Allah ya bashi lfy “.

**

“Captian ya shirye shirye, da zirga ,zirgan asibiti”.

Hajar ta, tambaya.

“Gashi muna ta fama dai, yanzu daga nabar nan gidan ku asibitin zan koma, idan ,naga ko mai na tafiya dai-dai sai na je na karb’o d’inki da zan saka gobe”.

“Ae dama ka wuce gurin d’inkin, ka ,kawai don Khadee tace, min komai na tafiya dai-dai, kuma kasan bama samun ganin shi zakayi ba”.

“Haka, ne sai na wuce d’in kawai,kinji wai zariya za’a tafi d’aurin auren ko?”.

“Eh ,Haka Dady ,yace kasan wani kawun mune ze d’aura so baze iya zuwa nan kano ba, shiyasa Dad yace aje cen d’in kawai”.

“Eh duk Abba ya fad’a min,ni wlh ,haka nan yau tun safe bana jin dad’in jikina, kuma sam duk abunda naci sai naji babu test, narasa dalili”.

Murmushi Hajar tayi tace

“Nima dai haka, ni duk satinan ,ma haka nike jina wata iri wlh, sai nake jin akwai abun daze faru”.

“Tow miye dalili hakan? Ubangiji kasa’alkairi ne “.

“Ameen dai “.

Captian saida yad’anyi shiru sanan yace.

“Tow kinga yanzu aure zamuyi Hajjo zamu shiga wata sabuwan rayuwa nidake, duk zunuban mu Allah ze wanke mana shi, hakan yasa nake rok’on ki da kiyafe min duk wani abu danayi miki arayuwa ,saboda ina so gobe ,na fara wata, rayuwan daban”.

Murmushi Hajar tayi tace.

“Nikam bakamin komai ba, nayefe maka nima ka yafe min pls”.

“Baki tab’amin komai ba Hajjo na yafe miki, ina Jawahir kwana biyu ban ganta ba?”.

“Tana ciki”.

Hajar ta bashi amsa.

“Pls d’auko min ita ,ina son ganinta kuma, mu gaisa.”

Yanda yace tayi hakan tayi.

 WASHE GARI

yaune Jumu’a za’a d’aura, auren Hajar da Captian da kuma Dr Samir da Salma bayan Salar jumu’a ‘a Babban masalacin dake yankin zariya.

K’arfe goma da kusan rabi Salma ta koma gida, don d’auko wa Dr Samir kaya, don yau ne za’ayi masa ,dashin koda, k’arfe biyu dai-dai zasu shiga dashi dak’in tiyata, kamar yanda suka fad’a.

Tana shiga ,gidan sashen ,shi ta shiga Darec d’akin shi ta danna kai.

D’akin kaca kaca ,duk ya baza kaya’akan gado, zama tayi gefen gadon ta fara duba masa kaya cikin wanda suke zube agurin.

Tana d’aga wani ,wando ta hango diyari d’in shi ta d’auka.

Ju-juyashi ta farayi a hanun ta, wata zuciyar tana ,kibud’e ki ,karan ta wata zuciyar kuma tana kad, ki bud’e , cikin jakar hanun ta, tajefa shi ciki, tayi sauri ta zab’a masa kaya ta fice.

**

Sanye ,yake cikin wata dakakiyar shedda ruwan toka, yashi aikin hanu, Babban riga ce, sai ya sanya wata Zana buk’ar wacce zata shiga da kayan sosai, ya d’auki takalman shi mekyau da tsada sau ciki ya saka, ya fashe jikin shi da turaruka masu tsada ,da k’amshi.

Kanshi ya kalla jikin madubi.kayan sun balain masa kyau sajen fuskar shi sun kwanta luf, luf saman fuskar shi, ya wani k’ara kyau da haske ,sai dai kuma ya d’an fad’a , wayan shi daya fara, ruri ya d’aga yaga d’aya daga cikin abokan shine, d’auka yayi da Salama yace.

“Abdul ya ‘akayi”.

“Kaji ango tun ba’aje ko ina ba har ka fara cenza min ,murya”.

Dariya Captian yayi yace.

“Kaga malam bana son wanan zolayar taka ya’akayi ne?”.

“Babu komai dama,nakira nace maka, mund’au hanya ne tunda kace kai ,d’aya zaka taho, mukam, munyi gaba”.

“Yawwa ‘Allah yasa kuriga su Abba isa don suma sun d’auki hanya, mu kawai ake jira don ,iyayen Hajjo sun jima da isa, nima yanzu, zan fito insha ‘Allah”.

“Tow kade hanzarta ‘ango sai mun had’u”.

Ya tsinke wayar.

Fita, yayi daga ,d’akin shi yaje sashen Hajiya cike yake, da yan uwa da’abokan arziki, sai tsiya suke masa, beda kula suba har ya samu ya shige d’akin Hajiyar sa.

Zaune ya sameta, ana mata k’itso tsugunawa yayi har k’asa cikin girmamawa yace.

“Sanu Hajiya zan tafi”.

Hajiya na zaune gaban me kitso ta juyo tace.

“Harka fito Junaidu, Allah ya kiyaye, kayi sauri kasan tun d’azu su Alhaji suka fita, kuma kasan baya son jira, ina ce ,cen d’in zakayi, yanzu”.

Cikin girmamawa Captian yace.

“A’a zan biya gurin Dr Samir”.

“A’a menakon ,ko bari sai kun dawo Junaidu?”.

Girgiza mata kai Captian yayi ,yace.

“A’a hajiya kibarni kawai naje, k’arfe biyu za’a masa dashen k’oda ,kuma gsky bazan iya tafiya ban yi masa, salama ba ,nidai addu’ar ki nake buk’ata”.

“Tow D’an lelena, Ubangiji ya tsare min kai yasa kuje a sa’a ku dawo a sa’a yayi maka ‘Albarka, sai ka dawo kuma ‘akula da tuk’i banda tuk’in gan,nanci”.

Mik’ewa yayi, yace.

“Ameen Hajiya nagode kuma insha ‘Allah ahankali zan tafi”.

*

Captian yaje ya samu su Khadee sai had’a kayan aiki suke, kafun lokaci yayi, gurin ta yaje ya nemi Alfarman yana son yaga Dr Samir dak’er ta ‘amince masa don, dokar asibiti ce babu me shiga wanan d’akin sai ,iya likitoci.

*

Kwance ya sameshi ‘idanun shi biyu , yana kallon sama.

Kallo d’aya Captian yayi masa ya kauda kai, don baze iya kuma kallon shiba.

Duk ya rame yayi bak’i ya fita hayacin sa, kamar wani me ciwan H.I.V haka ya koma.

Jin k’amshin turaren Captian ya sashi kallon k’ofa , tsaye ,ya ganshi yana hawaye.

Cikin k’arfin Hali a hankali yace.

“Junaid lfy kake, kuka yau ranar farin cikin ,ka?”.

Maganar tashi ma dak’er take fita.

Saida Captian ya matsa kusa da, Dr samir ya tsuguna jikin gadon shi yace.

“Samir bana jin farin ciki, kamar yanda zakayi tsamanin zanji, naci Burin wannan auren kamar ba gobe.

Amman rashin ka gurin d’aurin auren yasa naji komai baya min yanda ,nakeso .

Tun jiya nake jin fad’uwar gaba Samir bana son katafi ka barni, inaji ajikina kamar akwai abunda ze faru Samir, inajin ajiki ,kamar akwai wani babban abuda ze faru da kai ko dani.

Da ina da hali Da nace bazanje gun d’aurin auren ba, kodon naga lokacin da za’a shiga dakai da kuma lokacin da za’a fito dakai, Amman hakan baze yuwu ba”.

Samir ayanzu kwata kwata baya iya Kuka baya iya hawaye saidai, ya d’inga jin zugi cikin zuciyar shi.

Wani abu yaji ya tsaya masa’a mak’oshin sa, lokaci guda yaji komai ya tsaya masa cak.

Dafa Captian yayi ,yace.

“Ka, kwantar da hankalin ka ‘Abokina ka d’auka cewa komai dake faruwa muk’adaddari ne, da kuma wanda ze faru.

Ina so kayi ‘imani da Allah kuma ya, yarda, da k’adaddara, ka d’auka cewa komai ba komai bane face jarabawa, idan Allah yayi zan fito dole ka dawo ka gani, idan Allah yayi zan tafi dole ka dawo ka samu babu ni.

Ko ,kana kusa dani ko baka, kusa dani dole indan lokacinane dole natafi.

Kuma ina so ka sani cewa cuta bata kisa, sai ‘idan kwana ya k’are, zakaga me lfy ya tafi yabar mara lfy kaga wanan yana, nuni da cewa bafa sai baka da lfy zaka tafi ba.

Da wanan ,nake rok’on ka da katashi, ka tafi gurin d’aurin Auren ka, kad lokaci ya k’ure, Allah ya baku zaman lfy”.

Jiki a sukwane Captian ya tashi ya fice batare da yace wa Samir komai ba.

A k’ofar d’akin ya iske Salma fuskar ta ya kunbura tsabar kuka, so take ta ,tsayar dashi tayi masa ,magana ‘Amman ta kasa tsaida shi ,harya b’ace ma.

Zama tayi ta cigaba da rera kuka, abunda ta gani yau ,ya balain d’aga mata hankali, ji tayi dama tun cen tasan da hakan da, duk Dr Samir be shiga halin dayake ciki ya’yanzun ba.

“Ya ‘Allah “.

Shine abunda ta iya furtawa, yayin data lalubo wayan ta don kiran Captian, ta sanar dashi komai tun kan lokaci ya kure musu…….

By Dija_Waziri
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

Second to the last

shafinan gabi d’ayan shi sadaukar wa ce gareki Miss XoXo ,Allah ya barmu tare πŸ™Œ

Mata mu tashi tsaye mu kula da tarbiyyar yaran mu. Aure yana shiga cikin wani hali, zarge-zarge na yawaita a daina don yafi yawa wajen mata nasiha wurin miji yafi zargi da habaici, makaranatar farko a wajen mata uwa ce.

Nashiha yana da matuk’ar muhimmanci iyaye su ,sani cewa nasiha babbar hanya ce na tarbiyyar yara.

me ake nufi da Tarbiyya a musulunci? Tarbiyya tana ,nufin gina cikakken mutum sannu a hankali ,don bin umarnin Allah da na manzonsa ,da neman yardar Allah, da samar masa da nagarciyar rayuwa duniya da hahira bisa tsari irin ,na musulunci.

hukuncin gina yaro Akan tarbiyyar Musulunci wajibi ne. Kuma hakki ne daga cikin hakkokin yaro akan mahaifansa, ko walliyansa ,dalilai akan haka.

daga kuri’ani fad’in Allah ta’ala yace.

Yaku wad’anda kuka yi imani .ku d’auki matakin kare, kanku da iyalinku daga wuta masu tsaronta, wasu irin mala’iku masu karfin bala’i da tsananin gaske ,basa sabawa Allah abin daya umarce su, kuma duk abin da ya Umarce su shi suke aikatawa.

Daga hadisi fadin Annabi yace

Kowa ya saurara yaji dukkaninku masu kiwo ne, kuma kowanneku sai an tambaye shi kiwon da ‘aka ba… Namiji makiyayi ne game da mutanen gidansa ,kuma sai an tambaye shi akan abin da ‘aka ba shi kiwi, mace ma makiyayi yace a gidan mijinta da ya’yansa ,kuma sai an tambayeta akansu….

Allah ya bamu ikon tarbiyyan tar da yayan mu bisa tafarkin tsira AmeenπŸ‘

Chapter 49

KAFUN D’AURIN AURE

bayan Captian yabar asibiti , hanyar Zariya ,ya d’auka , gudu yake sosai kamar ze tashi sama don Lokaci ya kusa cika ,kuma yana son ya samu salar jumu’a, awan shi d’aya ya sadashi da garin zariya.

Ko daya isa ya samu an fara sahun sallah cikin Sauri ya d’aura ‘Alola shima yahau sahu.

Raka’a biyu sukayi, suna idar wa yaji wayan shi ya fara, ruri yana dubawa yaga Salma ce , beyi tunanin komai ba ya d’auka.

Bakin ta na rawa tace.

“Hello Captian, an d’aura, auren ,ne?”.

“A’a Salma ba’a d’aura ba yanzu ne dai ake shirin d’aura wa lfy kuwa?”.

Saida ta saki wani gauran, nufashi sanan tace.

“Akwai matsala Junaid “.

Cikin rashin Fahimta Captian yace.

“SubhanAllah wace irin matsala ce kuma Haka Salma?”.

D’an jim tayi kad’an sanan ta goge hawayen dake zuba cikin idanun ta, da kamar bazata fad’a masa ba , taga koda ta bari duk randa yazo yaji bazataji dadi ba, cikin rawar murya tace.

“D’azu da naje gida, d’auko wa Samir kaya , naga scret book d’inshi, ban so d’auka ba, alokacin.

Amman zuciya tayi ta ,tunzurani saida na d’auka, bayan ,nazo asibiti ne kuma sai na d’auko na fara karan tawa Captian abunda nagani yayi masifar d’aga min hankali.

Ban tab’a sanin Samir nada zurfin ciki ba sai ayau”.

Shiru tayi tana, goge hawayen da suka ,kuma wanke mata fuska.

“Ina jinki Salma kiyi sauri , ina son zan kashe wayata”.

Captian ya fad’a cikin tashin hankali dason, yasan meke faruwa.

“Captian kayi hakuri bazan iya barin abun cikin zuciyata bane shiyasa zan amayar dashi.

Dr Samir ya jima yana son Hajar tun kafun kasan zaku had’u da ita , yau wajen shekaru 8 ake nema yana dakon son ta.

Kuma bawai ya dena son ,nata bene har yanzu, dalilin dayasa ya hak’ura ,kuma yak’i furta mata shine, don yaga kariga shi furta mata shine babban dalilin dayasa, ya fasa ,yabar abun azuciyar shi.

Kuma , musababin yawan tashin ciwan zuciyar shi akai akai harda , rashin samun ta dabeyi ba, abun yana damun shi. Kuma yayi alk’awarin babu wanda ze fad’a ma koda hakan ze iya barazana da rayuwan shi”.

Captian jinshi yayi wani ‘iri kamar bashi ba, taka, k’afarshi ma kasayi ,yayi be jira ‘Salma ta k’arasa masa lbrn ba kawai ya kashe wayan ya cilata cikin mota , yanajin ranshi na balain b’aci zuciyar shi na suya.

Buga kofar motan yayi ‘idanun shi zajur yace.

“No Samir why Samir meyasa zaka b’oye min damuwar ka Samir “.

Ganin Abdul ya nufo inda yake ne yasa, shi yayi shiru ,bede motsa daga inda yakeba har Abdul ya k’araso .

Ganin yanayin shi yasa ‘Abdul d’in fad’in .

“Lfy Captian ,naga lokaci guda ka cenza?”.

Captian da idanun shi sukayi jazur yace.

“Babu komai Abdul”.

Abdul be yarda ,da hakan ba ya barshi ne kawai don baya son suja zancen yace .

“Kazo inji Abba kaifa ‘ake jira”.

Captian bece da ‘abdul komai ba , ya rufe motar shi ,ya wuce zuwa masalacin.

Zaune ya samesu gaba d’aya.sunyi shirin d’aura ‘aure , saida yad’an tsaya na wasi yan dak’ika sanan, ya dannan kai cikin Masalacin.

Abba ya kira yace ,yana son magana dashi, koda ‘Abba yazo fita sukayi suka samu wuri gefen inda babu mutane.

Sannan Captian ya sanar da ‘Abba duk yanda sukayi da Salma be ,boye mishi komai ba.

D’an jim kad’an Abba yayi sanan ya kalli Captian yace.

“Duk naji abunda kace Junaid yanzu me kake son ayi?”

“Abunda nake so ayi shine A d’aura ma Hajjo Samir Abba shine kad’ai alfarman da nake, nema ina son ,nabawa Samir mamaki ne,ni ,nahak’ura “.

Cikin mamaki Abba ke ,kallon Captian yace.

“Junaid anya kaid’inne kuwa? Kaine kuwa, wanda nasan ya kusa haukacewa ‘akan yarinyar nan?”.

Murmushin yak’e Captian ya saki yace.

“Nine Abba nine karka damu Samir yafini buk’atar Hajjo, kuma nasan yanda yake itace zab’in shi, nasan itama har azuciyar ta shine zab’in ta,

Saboda sai yanzun wasu abubuwa da, dama ke dawo min game dasu dukan wanda ban iya gane suba sai yau”.

Dafa k’afad’an shi Abba yayi ,yace.

“Lalle ka cika jarumin ,maza kuma kacika ‘Aboki nagari ,irin ku ake nema ‘Amman samun ku da wuya,

Yanzu barin kira mahaifin ta sai na ,sanar dashi, daga nan kuma sai mukira mahaifiyar shi ‘itama ,mu sanar mata”.

Murmushin da iyakan shi fatar bakine, yayi ,yayin da ya kamo hanun Mahaifin ,nashi.

“Abba nagode Allah ya k’ara girma ‘Amman Abba ,bana son Samir da Hajjo su, sani yanzu ,ni da kaina ,nake son fad’a musu”

*

Abba yayi magana da Dady ta fahimtar juna ,kuma ya gamsu da. Duk abunda yace masa, ya ‘amince, ya kuma kira Mami ,ma ya sanar da ita, takuma ‘amince , Abba ma ya kira Hajiya ,ya labarta ,mata komai ,takuma gamsu don ita ‘abunda ,d’anta keso to itama shi take so.

Bayanan sun kira Ummi sunyi dogon magana da ita, takuma gamsu ta’amince .

Suna gamawa ‘aka d’aura ‘auren Samir da Hajar Abba ne waliyin Samir .

Back to story

Su Abdul ne sukaje suka d’auko shi, koda suka isa ma yariga daya cika ,

Gidan su ,suka wuce dashi daret. Sun samu su Abba da ,Dady awaje suna zaune gurin zaman makoki,

Ganin su yasa ‘Abba tashi ya nufi motar da ‘aka sanya Captian ciki.

Abba ko, kuka ,kasayi yayi idanun shi sun bushe ,amman kowa ya ganshi yasan yana cikin tashin hankali, bafanin Captian ,ne suka ,kamashi suka shiga dashi cikin gidan.

Hajiya dake faman kuka ,kan taburma, tana ganin su ta ,mik’e da gudu ta nufi gawar Captian ,tana wani ‘irin ihu, Abba ne ya rik’e ta gam su kuma suka ,k’arasa dashi ciki don aje ayi masa. Sutura.

Bayan minti talatin an gama shirya shi tsaf ansa shi cikin makara, sanan aka fito dashi akayi masa ,salla.

Babban tashin hankalin shine lokacin da za’a fita dashi daga cikin gidan ,hajiya ta rik’e makaran gam taki saki sai ,kuka takeyi tana cewa.

“Don Allah kuce min be mutu ba, kuce min ze dawo gareni, wayyo Allah ashe ban kwanan k’arshe mukayi dashi d’azu kuce min ze dawo, karku tafi dashi “.

Yayar tace ,tazo ta jata dak’er tana cijewa tana fusgewa .

Haka tana kallo su Abba suka fita da gawan Captian ,suka sanya ‘amota, suka wuce mak’abarta,

Koda suka isa,sun samu har’an tona ramin da’za’a sanya shi ,kamar yanda ‘Abba ya Umarta ‘ayi, fito dashi zukayi suna shirin sakashi kawai sukaji. ,jiniyar motar asibiti ,ta ,tsaya ‘a dede kofar shiga mak’abartan.

Kowa hankalin shi komawa yayi kan wurin, nas ne suka fito daga cikin, motar daga bisani kuma wani daga cikin ,nas d’in ya d’auko ,kujeran narasa lfy ,ya bud’e.

A hankali Dr Samir ke saukowa, wani daga cikin ,nas d’in ya rik’e shi, idanun shi sunyi jazur fuskar shi ta kumbura ,sumtun alamun yasha kuka.

Dak’er ya sauko ya zauna kan ,kujeran suka turashi har cikin mak’abartan inda su Abba ke tsaye.

Ganin gawan Captian a gefe yasa shi kuma rushewa da wata irin kuka mecin zuciya, duk jarumta irin ta samir wannan karon be iya jurewa ba,

Har inda gawan Captian yake, yasa ,suka turashi yaji yayi masa ‘addu’a tare da fatan Allah ya rahamamasa ,ya sa cen yafi masa nan, saida ya jima yana masa ‘addu’a sanan yayi k’arfin halin kallon su Abba yace asashi, shine maganar da ya iyayi tunda yazo gurin shima dak’er ya iya furtawa.

Bayan ‘an saka Captian cikin k’asa ,Samir da kanshi ya zuba masa k’asa, yana zubawa yana jin zuciyar shi kamar zata fasa k’irjin shi ta fad’o.

Yana jin duniyar ta zame ,masa tamkar mak’abarta, rashin Captian arayuwan shi babban matsala ce, Captian yayi masa ‘abun da ba kowa bane ze iya, yi masa shi arayuwa, abubu abinda Captian yake nema ‘agarashi yanzu daya wuce Addu’a.

Rayuwan su na baya ,ya fara tunawa ,wani tari yaji ya sarke masa ‘awuya dak’er ya iya cewa .

“Ku tafi dani matsawar ina kallon kabarin Captian zan iya binshi nima”.

Hakan yasa nas d’in suka ,juya dashi zuwa motar asibiti.


**

Hajar na kwance jikin Mami tana wani ‘irin kuka mara Hawaye Khadee da Basmad da ‘Aunty Asma’u ma sunyi jigum suna me tausayawa halin da Hajar d’in ta shice.

Dak’er Hajar ta iya furta.

“Mami wai yanzu Captian ya tafi kenan har abada ,bazan sake ganin shiba?”.

Mami cikin tausayawa tace.

“Hajjo kin tab’ajin wanda ya mutu ya dawo? Hak’uri zakiyi dayi masa ‘Addu’a shine abunda yafi buk’ata ‘ayanzun”.

Fashewa da kuka me Sauti Hajar tayi ,tace .

“Wannan yana, nufin yabar duniya kenan har Abada, wanan yana ,nufin bazan kuma ganin shiba ? Ya ilahi ,mutuwa me yank’ar k’auna”.

Gaba d’aya d’akin ,kowa sai kuka ,yakeyi

BAYAN KWANA GOMA

Yaune Captian ya cika, kwana goma cif da rasuwa,

Bayan ya rasu da kwana uku aka ,kira su Hajar ake sanar dasu cewa ‘Akram ,ma ‘Allah yayi masa cikawa dalilin wani ciwan ,ciki daya kama shi.

BY Dija_Waziri
[18/12 7:33 pm] Dija Waziri: πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰
DR HAJARπŸ‘©β€πŸ”¬
πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰πŸ’‰

K’ARSHEπŸ™Œ

        πŸ”š

Gabaki d’aya book d’innan sadaukar wace gareki, yar Uwata Hajara Muhamad Buba, Allah Ubangiji ya cika miki burin ki, ya kaimu har Auren ki , duk abunda kika sa ‘agaba Ubangiji ya baki sa’a

Naga sak’oninku, mosoyana. Kuma nagode, da soyayya Allah yabar zumunci ,kusani nima dija ina k’aunar ku, fiye da yadda kuke so littafin Dr Hajar, ina muku fatan Alkairi arayuwa😍

wannan shafin sadaukarwa ce ga duk groups groups da nake ciki

Chapter 50

FIVE YEARS LETAR

wata yar madai-dai ciyar bud’uruwa ce tsaye a kitchen tana firan doya.

Gefen ta ,kuma wata mata ce tana gyaran kifi ita ba siririya sosai ba kuma ba. Me jiki ba doguwa fara ,tana sanye cikin wani doguwan riga na materiyal, ta baza gashin kanta, yayi baya sai ta d’aura wani ban akai, fuskar ta sanye da medicated glass, fari.

Tsayawa nayi ‘ina kallon matar saida na matsa kusa da ita sosai naga ‘ashe ma Dr Hajar ceπŸ˜ƒ

Juyawa tayi da sauri ta kili wannan yar buduruwan dake firan doyan tace.

“Jawahir duba min, kazanan kad ya kama “.

Da sauri jawahir ta ‘ajje firan doyan taje aikin da hajar ta sanya ta.

Suna cikin aikin, ne sukaji alamun kamar ana kwankwasa ,kofa .

Hajar na b’aran tafar nuwa zata ,zuba cikin ,kifi tace.

“Jiki duba waye Jawahir Allah sa ba, baban ku bane ya dawo, gashi bamu gama ‘abinci ba”.

Jawahir na dariya tace.

“Ae mun kusa gamawa Momy basai ,susha drinks da snaks ba, kafun mu k’arasa “.

Mumushi Hajar d’in ta miyar mata, tace.

“Jiki dai, kiduba kar suyi ta jira”.

Fita daga kitchin d’in ,tayi ta nufi kofar tana bud’ewa tako ga sud’inne da Mumushi Jawahir tace.

“Sanun ku da, dawowa Dady ,ya jikin Kakus?”.

Dr Samir na shirin dannan kai cikin gidan shida, Amir.

“Jiki da sauk’i Jawahir, tace fushu take dake ,k’inki zuwa “

Amir ne yaga Hajar ta fito rik’e da ludayin miya , yana ganin ta, yaje ya rungume ta, yana “I miss u Momy tun d’azu muke ta jira dady yaje ya d’auko mu gidan kakus beje ba sai yanzu har munyi fushi”.

Dariya Hajar tayi ta rungumo shi tana.

“Sorry beby na Dad ,d’inka tun d’azu yana office shiyasa be samu zuwa dawuri ba , ya jikin Kakus d’in?”.

A shagob’e Amir yace , taji sauk’i harma tana yawon ta, kuma,muyi ta wasa da hira da ita, nida bebyn Aunty Salma”.

“Wow yayi kyau tow jeka falo kajira ni yanzu,zan k’arasa mana girki, kow”.

Da gudu ya shige ciki yana dariya, da murnan ya dawo gida,

Kallon Jawahir Hajar tayi ,tace .

“Beby na jiki,kitchen kijira ni kar girkin mu ya kama “.

Jawahir ,turo baki tayi tace .

“Mummy nifa ,yanzu na girma ki dena cemin beby, k’awayena duk sun rainani wai agida ma wanka, kike min”.

Dariya Samir ya saki yace.

“Sorry big woman daga yau andena, shekaru 19 ae ba wasa bane”.

Hajar kam sakin baki tayi, kawai tana kallon ta harta shige kitchen ,murmushi ta saki a ranta, tace Allah ya shiya min ke Jawahir.

K’ara sawa tayi har inda Samir ke Tsaye ,ta rungume shi, dede kunan sa taje tace .

“Wlcm home, my dear”.

K’ara matse ta yayi a jikin shi ,shima yaje dede kunen ta yace.

“Thank u my love I miss u “.

Murmushi tayi, tad’an ja daga rik’on da yayi mata, ta mannan ,masa wani hot kiss, sanan tace.

“Kaje falo ka huta bari yanzu, zan gama ‘abinci .

Saida ya manna mata wani kiss d’in sanan yace .

“Ina jiran ki”.

Ya wuce itama, ta. Koma kitchen.

*

Bayan sun gama girki wanka ta sakeyi, tasa wani gajeran wando iya gwaiwa, da riga me hanun bes, sai ta kama gashin ta da ribbom, d’an tinbin cikin ta yana d’an ,nunawa ‘alamun ya fara girma.

Tare suka zauna gaba d’aya sukaci abunci sanan ,suka, koma falo suka zauna.

A sace Samir ke ,kallon Hajar dake ,kujeran kusa da wanda yake zaune shida Amir.

Kallon Jawahir yayi da tamaida hankalin ta ,kan Mbc 2 tana kallon wani series film πŸ‡»yace

“Jawahir yau ba school ne ?”.

Jiyowa Jawahir tayi ,ta kalleshi tace.

“Yau bamu da lecturs Dady “.

“Ok , ba exam kukeyi ba?”.

“Eh dady Saura 4 mugama, ma”.

Saida yad’anyi shiru sanan yace.

“Shine zaki tsaya kallo kow ki, kashe Tv d’inan ki tashi kije kiyi karatu, ko ance miki rayuwan Unvst dana scndy iri d’aya ne”.

“Girgiza masa kai tayi ,tace ‘sorry Dady barin tashi, dama so nake ,na gama kallon film d’inan sai na mik’e”.

“Saboda shid’in ibada ne kow? Idan baki ganiba zaki mutu?”.

Hajar ta fad’a tana cirewa Amir kaya.

“Ga ‘Amir kisa masa kayan isilamiya kafun ki fara karatun lokaci yayi, kuma nasan ado drive na jiran shi”.

Tow kawai tace ,taja ‘Amir suka haye sama.

Samir dama kamar jira yake su tafi ya koma gefen da Hajar take ya fara shafa lalausan gashin kanta.

Kallon shi tayi ,tana matsawa tace.

“Haba dear sai Jawahir tazo, ta gamu kabari pls “.

Tsura mata idanun yayi ,yace.

“Tow miye idan ta gani d’in ba yarmu bace ?”.

Dariya hajar tayi tace.

“Todon yar muce kuma sai me ae be dace ba ,kodon tarbiyyar su”.

“Ok tow naji ,bazan sake ba, ki sameni a d’aki”

, ya mik’e ya haye masa,ita kuwa ,kallo tabishi dashi ,harya kule sanan ta, tashi ‘itama tayi saman saida ta, tabatar Amir ya tafi school Jawahir ta fara karatu, sanan tayi d’akin Samir.

*

K’arfe biyar da rabi Hajar ta shirya ‘Amir Jawahir ma ta shirya, Samir ne da kanshi ya kaisu gidan Khadee Hajar nason tayi mata barka.

Sunsha ,hira sosai da Hajar kafun Samir yazo ya d’auke su, sai k’arfe 8 suka, koma gida.

Suna zuwa Hajar ta yiwa ‘Amir shirin bacci ta shinfid’e shi ,har sai da yayi bacci sanan tayi musu, saida safe ta fice zuwa d’akin mijinta.

Koda taje ta samu Samir haryayi shirin bacci yana kwance yana dana ,System.

Toilet ta fad’a tayi wanka, ta fito, tashafe jikinta da mayuwa masu k’amshi ,sanan ta kuma bi ta shafe da wasu turaruka na mai, masu k’anshin dad’i kuma ba masu k’arfi ba.

Ta d’auko wani rigan baci mara nauyi tasa. Sanan ta haye gado.

Sund’an tab’a hira da Samir kad’an sanan daga bisani ya kulle system d’inshi, ya fara cen salo, bargo yaja ya rufe su.

Niko dija na kashe musu wutan d’akin ,nayo waje.

ALHAMDULILLAH

Anan nake muku sallama. Da fatan alkairi a rayuwa gabaki d’aya.

Godiya ta ,tabata ga ‘Allah me kowa me komai daya bani ‘ikon kamala wannan littafin lfy .

Ina neman gafarar duk wanda na batama. Na yafe ma kowa laifin dayaimun a sani ko rashin sani .Allah ya yafe mana gabaki d’ayanmu Ameen

TAMBAYOYI

MIYE DARASIN DA KUKA D’AUKA CIKIN WANNAN ,NOVEL D’IN?

MEY KUSKUREN DAKE CIKI? Pls tatausan lafazi

WAYE BEST CHARACTER DIN KU

WANI WURI YAFI BURGE KU?

WANI WURI YAFI B’ATA MUKU RAI?

MEYAFI BAKU TAUSAYI?

SAI NAJI DAGA, GAREKU

BISALAM

BY DIJA_WAZIRIπŸ’‰

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button