Hausa Novels

Darajar Ya yana part 4

Darajar Yayana4-01
Posted by ANaM Dorayi on 05:26 AM, 08-Apr-16
Under: DARAJAR ‘YA’YANA
________________NA ___________HALIMA K/MASHI Na kalle shi cikin tsananin tsoro, na dafa kirjina. Ni Yaya? In jiwa??? Saukar mari naii dau! Sannan yace, Ba zan iya zama dakeba kina cin amanata.Nadafe gurin tare da gigicewa, jina ya gushe na wasu ‘yan dakiku, jin abin nake tamkar a mafarki,ahe kuka samun dama ne. Nasa ke dago kai na kalle shi. Yaya mece ce hujjar ka da zakayimin wannan zargin? Ya fita, na zauna a bakin gado ina maida numfashi, cikina yanayi min wani irin juyi. Ya sake shigowa, a fili nake furta ‘Allahumma ajirni fimusibati….. Ya hada laptop din shi ya dube ni cikin tsawa. Zo ki ga hujjar tawa, na san kin san komai nema ki ke ki raina min wayo. Kai tsaye ya shiga inbox din shi, Ki karanta, duk da na san alaye kikeyi. Duk da dishi dishin da nake gani na zaku in karanata,da farko an rubuta.Sunana Sulaiman kuma bana bukatar sai na fada maka in da nake, amma zan nuna maka abinda matarka ke ciki da wani malami a makarantar da take koyarwa. Kila kace ya akayi nasani? To shi ne yake ba ni labari tare da yi min forward din duk abin da suka tattauna, kuma shine ya bani labarin cewa kana aiki ne a Abuja dansanda ne kai. Ga amsar da Yaya ya ba shi. “Me yasa ka ke son fada min?” Sulaiman. “Sabida tausayinka,sannan ina fatan yanda na taimake ka nima Allah ya kawo mai taimakona wata rana ko ba a kan irin wannan matsalar ba.” Aliyu: “Ina jin ka.” Sulaiman: “To bari in maka forward.”Sai ga sunana ya fito: Sadiya Abubakar. “Ina jin ka malam, ba nisa na yi ba,na dan tashi ne savida banason a fahimci ina tare da kai” Malam: O.k, to me labari? Ina fata dai za ki shigo gobe don na matsu inga fuskar ki tana burge ni. Sadiya ina son ki fiye da matata dan kin fi ta komai,wai ba za ki iya hada mana wata dabara ba da za mu je wani guri mu kwana ba? Sadiya Abubakar. Ba zai yiwu ba malam saboda ciki,amma ka jira in haihu,ni kaina da a ce tuni na same ka ba zan aure wannan mijin nawaba,wanda da shi gara babu,kullum ba ya gida,ga shi ya kara aure. Malam. Hahhaha! Ki yi min irin wannan kunshin da ki ke yi, kwanan nan zan sa a kara miki matsayi a makarantar nan. Sadiya Abubakar, turo min hoton sharabarki don tana burge ni. Ya kara yin sama kadan sai ga hoton sharaba an turo. Gashi masoyina. Sulaiman. Kai! Ina jin dadin kallonta,ina son yadda ki ke min shagwaba,in muna tare,ina son hannuwanki masu laushi. Sadiya Abubakar. Da gaske masoyina? Nagode, zamu hadu anjima ina fata yau za ka yi min hira cikin dare,zan sauka yanzun don yarana sun dawo daga makaranta. ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Jikina ya jike sharkaf da gumi,haka
fuskata,hawaye da majina sun gauraya, na dago
na kalle shi. ‘Yaya ka yarda,wallahi ban san
komai kan wannan abin ba, hasali ma ni nawa
account din ba da sunana na bude shi ba.Ya
daka min tsawa, ‘Ke rufe min baki! Wannan ba
sunan ki ba ne? Na ce, sunana ne. Ya ce, To,
inbox din ki ne fa,ko kina zaton wani yana shiga
inbox din wani? Na ce ni ban sani ba abin da na
sani kawai ba ni da wata masaniya kan wannan.
Ya ce, ‘O.k, za ki ci gaba da raina min wayo
kenan? Ga shi nan kun yi labari a kaina kun
tattauna sirrin gidana, Allah Ya Isa Sadiya, ina so
ki sani zaman mu ya kare da ke. Na ce, ‘Haba
Aliyu ka yi bincike mana? Jikina ya soma bari.
Yace, Abin daba zahiri ake yiwa bincike. Ya nufo
durowa ya yage takarda ya dauko biro daga
aljihun gaban rigarsa. Da karfi na furta. Yaya
Aliyu kada ka sake ni ba’a son sakin mace mai
ciki!!! Ban san cewa na rike hannunsa ba,sai da
na ji ya fincike ya miko min takardar,ban karba
ba sai dai idanuna sun haskomin in da ya ce
‘SAKI DAYA. Na daga idanuna na kalle shi,sai na
ga yana dusashe min,ina kallon bakinshi yana
motsi,amma bana jin ,me yake fada,sai kuma na
ga ya soma juya min da shi da dakin a hankali
duhu ya mamaye idanuna sunfara dushi-
dishi,haka nan dana farka da dishi dishin na
farka,ban fahimci komaiba ban tuna komai ba
har tsawan dakiki.sannan naga Iya tsaye bakinta
na motsi,amma banajin me take fada.A sannu na
fahmci ina asibiti ne,sabida shigowar likita da
kuma ma’aikaciyar jinya(nurse)mai fararen
kaya,likitan ya dafa iya yana min magana da karfi
kinsan wannan?na kalli Iya,sannan na daga kaina
nace eh yace wacece? Dakyar na daga lebunana
nace mamana,ta kallon bkina ya gane abinda na
fada,naji yce Alhmdullh ta farfado yanda ya
kamata zata warware a hankali,kwatsam na tuna
cewar inada ciki nan take na soma tuna
komai,gaske ne yaya ya sakeni?na kai hannuna
na shafa cikina sainaji wayam,na yunkura zan
tashi sai naji Iya takamani ta maida ni nace iya
nayi 6ari ne?tace a’a kin haihu ne sai dai dan bai
cika taraba.
Nace y mutu? Tace a’a,yana can garinsu sun sa
shi a kwalba.
Na lumshe ido a fili na furta cewa,shikenan nayi
IDDA.
Wasu zafafan hawaye suka soma zubomin.
Iya tace Sadiya me kikace?
Na bude idanuna nima ina kallonta,take kuma
naji dan karfi na ciji le6e nace,iya ai in mace mai
ciki ta haihu tayi IDDA ko?Ta sake tattaro
hankalinta gareni,in an sake ta ba?me ya kawo
wannan tunani cikin kwakwalwarki?ta yunkura.
Bari in kira likinta nan ina zaton har yanxu b ki
dawo cikin hayyacinki ba Gam!nariketa iya! Ina
cikin hayyacina,na soma kuka,yanxu ni ba matar
shi b ce salati naji Iyar ta saka,sannan ta sake
tambayata,saki kuma sadiya?na kama
hannunta,kiyimin addu’a in cinye wannan
jarabawar.shiru tayi ta kasa magana sallamar shi
ce tasani lumshe ido,sam bana son ganinsa kojin
muryarsa.Iya ta subule hannunta daga nawa ta
fita,kuma cikin fushi,sanan taki ansa sannu da
yayan keyi mata.yabita da kallo har ta fita,y iso
kaina,na bude ido na kalleshi,kallon tsana,fuskar
shi babu alamar nadama yace.
Daga ganin yanda Iya ta fita rai a bace,nasan kin
fada matane,banso kikayi saurin fada ba,sabida
in rufa miki asiri,kamar yanda kikayimin.
Duk da halin da nake ciki ban san lokacin dana
tashi zaune ba,cikin kuka nace Aliyu bana bukatar
rufin asirinka,domin in kaji mutm yana neman
rufin asiri bashida gaskia,sai dai bansan mekazoyi
nan ba,tunda yanzu ba matarka bace,nayi
iddarka ka tafi banason sake ganinka,yace nasan
haka zuwa nayi in duba jikin ki matsayina na
yayanki kadai kuma uwar yarana,Nace,to
nagide,tafi yace yanxu kuwa,sai dai zan miki irin
halaccin da kikayimin,har abada iya bazata ta6a
jin dalilin sakin ba.nagirgiza kai,dole tasani,don ni
zan fada mata,ka tafi bana son ganinka,ka tafi,na
jefeshi da filo,Iya ta shigo,Gadanga fita daga nan!
ya juya ya fita.tazo ta kamani ina kuka ta
rungumeni a jikinta tana lallashina tana bni baki
har na hakura nayi shuru.
ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Kwana na 2 na dan murmure mutane suna ta
zuwa dubani,sunayimin barka,amma kishiyata da
yarana shuru bare yaya.tsakanin da da mahaifi
sai Allah,zuciyita tana can gurin yan yarana dana
tuno su sai inji hawaye yana bin kumatuna,Iya
tayi ta lallashjna.
Sati na 1 aka sallameni,Usman ne ke tsaye gurin
kula dani da biyan kudin Asibitina,sam baiyi
mana zanchenba,muma ba muyi masa ba,Anty
Abida kecemin wai yayi bakin cikin abunda Aliyu
yayine yasa shi jin kunyata.nace rayuwace kice
masa ba komai,shida yayi bai ji kunya ba sai shi?
Kai tsaye gidan Iya muka wuce,sun bani dana sun
mana gargadi banda jagwalgwalonshi.
Daran ranar Usman yazo kan batun sunan
yaro.Iya ta bamu wuri na mika masa
yaron,sannan na zauna muka gaisa,Ya dubeni
Sadiya,wallahi nauyi da kunya sun hanani in miki
jajen abinda ya faru,lokacin da Aliyu yazomin da
batun nan wallahi karkiga tashn hankalin dana
shiga,na tabbata an hado sharri ne don kawai a
tarwatsaku,hawaye suka soma kwaranya daga
idanuwana,na soma magana cikin kuka,
Yaya Usman wallahi bansan komai akan abinda
Abban Kausar yazo min dashi ba,sannan yaki
tsayawa ya fahmci hakan.A tunanina yafi kowa
sanin wacece ni,kuskurena 1 daya ce in rufe
account dina sai ban rufe ba,wannan kuma
mantawa nayi don ina ta kaina bana hawa.
Yace,kiyi hakuri ki dauki abin amatsayin
jarabta,Allah ya baki lafia,sannan ya raya miki
yaronki.wane suna za’ayimasa huduba dashi?
nace,ni bani da za6i a sa masa duk wanda
yakansance rabonsa.
Usman yayiwa yaro huduba da Abubakar,nace
sunan babana?yace rabon shine,Iya ta fito daga
uwar daki dama tanajinmu tace Allah yaraya
Abubakar Saddiku mukace amen. Ta
zauna,sannan tace,Usman abinda Gadanga yayi
sam bai kyauta ba,ba’a ta6a 6atamin rai b kamar
wannan tunda nazo dunia,Sadiyar ce bai sani ba?
in ya gaji da zama da ita sai yayi mata sharri?
abin da batayi da kuriciyartaba shine zatayi
yanxu wai tana bin wani Malami? Murya iya ta
soma rawa.Allah zai saka mata insha
Allahu.Usmn yace kiyi hakuri Iya,rashn bincike ne
kar kiyi masa baki.da sannun gaskia zatayi
halinta,nikaina baram baram muka rabu
dashi.ina kalln kiranshi dazu ban daukaba,
saboda ina son ya san cewa yayi laifi.nafada
masa in an bincika za’a gano duk wanda ya
shirya wannan sharrin sannu a hankali,mudake
aiki da internent muka san computer mun san
ana yin irin wannan sharri sai wani can ya bude
account din mutm ya kwace yayita aikata sharri
ko batsa ko kuma hotunan banza yayita turawa
da sunan mai wannan account mutane kuma su
zata shne.Inatasan inyimasa bayani lokacin
amma yaki’saida y iso gida ya aikata abinda da
yasha masa kai,amma insha Allahu komai zai
wuce a koma tamkar da.nayi yar daryar takaici
tare da cewa ta6di! Insha Allahu hakana bar
auren yaya.Iya tace insha Allahu kuwa,nidai
dama na guji hakan,amma ganin sun zauna lafiya
harda yan yaransu sai na saki jikina,ashe yace
tsiyar tana gaba,Usmn yace insha Allahu komai
ya wuce,yaba Iya yaron yamike tare da cewa
yana zuwa.jim kadan y dawo da manyan ledoji
dauke da kayan shayi zuwa su pampers.nace
yaya Usman dan Allah kabar dawainiyarnan dani
haka,yace haba dai ina abinyake?mukayi gidiya
tare da cewa ya gaida Anty Abida da yara,yace
zasuji.
Washegari da safe wayar Iya na kar6a na kira
Anty Abida nace mata kayan sawa na dana Baby
za’a kwaso min a gidan Yay Aly.iya tace ai ba
kayan sawa ba anjima zan nemi mota komai naki
za’a kwasomin tas.
Haka kuwa ranar a ka kwaso gadona da kujeru
dake falo tare da kayan kicin dina,iya da kanta
taje gidan.Mujidat sunata shewa da wadannan
yaren nasu,ta shigo da yaran makota da Anty
Abida suka kwashe.
ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Nace iya kingasu kausar tace a’a suna
makaranta.
Nasoma kuka,gaskia Iya zan kar6o yarana,wallahi
Mujidat bazata iya rikeminsu ba,Iya tce Sadiya!
nasan cewa da ciwo inaso ki danne ki kau da
kai,musawa Gadanga ido nace shikenan.
Cikin ‘yan kwanaki duk na rame na kade ba na
iya cin abinci sai Iya ta matsa min da fada,sabida
tunanin yarana ina son in gansu. Wata rana Aisha
ta zo min yini, na ce don Allah ta je ta dubo min
yarana,amma tana zuwa gidan an datse shi da
kwado,cikin kuka na kira Yaya Usman ina
tambayar shi ina yaya ya kai min yara? Ya ce
Sadiya ki yi hakuri ya kwashe iyalan shi sun koma
Abuja. Na lura baniba hatta Iya ranta ya baci,
tace wato ban isa ma yace min zai bar garin
ba,shi kenan yayi in dai duniya ce ga shi ga ta
nan.
Nafi sati ina kukan yarana,sai da Iya ta saka aka
yomin rubutu wai na dangana,ni dai duk da haka
ban dangana ba.
Aliyu zaune a kan kujerar shi ta office,duk da
ayyukan da ke gabansa da kuma matukar son
aikin shi, ya kasa yin aikin. Baya ya tura kujerar
shi ya jingina da bango yana tuna tun daga
shigar sa dakin Sadiya zuwa yanda ta zube a
sume ya kwashe ta zuwa asibiti,ko da uban shi
ya mutu bai yi kukan da yayi saboda cin amanar
da Sadiya ta yi masa ba.A fili yake fadin,Sadiya
dame na rageki?meye bana miki,me yasa zakibi
wanina ina mijinki?Ya kalli saman silin,inasonki
Sadiya,saidai bazan iya zama dake ba,ya mike
tamkar an tsikare shi y nufi kofar fita,kai tsaye
gida ya nufa,kmar yanda ya zata yaran suna
zaune guri 1,Mama ta kwantar da kai a cinyar
Kausar shima Al’amin ta kafadarta yasa kanshi,ya
tsugunna gabansu.Kausar yaku ka zauna anan?
ina kayan wasanku?
Ta dubeshi da wayayyun idonta,Abba ka taimake
mu ka kaimu gurin Momy,kaga Mama kuka ta
gama yi yanzu,karya nayimata nace kaje
kawotane.
Ya rungumesu,nace kuyi hakuri zan kaiku ina
Auntynku?
Khausar ta ta6e baki,tana ciki.ya dafo fuskar
Al’amen ga mamakin shi sai yaga idon yaron biyu
yace kunci abinci?
Khausar tace a’a bama jin yunwa.yasa hannu ya
dauki Mama jikin yarinyar zafi rau ga dukkan
alamu bata da lafia. hankalinshi ya sake tashi,ya
kira Mujidat wadde ke can kwance kan gado da
yaranta tana faman yin sana’ar tata chatting da
abokanta,ta tura wayarta a kasan fiilo,sannan ta
tashi,yace yaya za’a bar yarannan?tace to ya
zanyi musu,suci abinci sunqi,na kunna musu TV
sunki,tome zanyi musu?
ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Yace ki dauko hijabinki mukai yarinyar nan
asibiti,bada son ranta ba suka tafi,,anbata
magunguna har da allura,sannan suka
dawo.ranar dakinshi yayiwa yaran
masauki,Mujidat anyo kwallia anzo dakin miji sai
ta tarar da yaran kwance kan gadonsa,ya tasa su
ya zabga tagumi,turus ta tsaya,Anan zasu kwana?
ba tare da yadubetaba yace eh.tsaki taja sannan
ta juya zuwa dakinta,Wannan ta zamar mata
baka,kuma tsanar yaran ta ninku a ranta,tana
murna ta kashe maciji ashe bata sare kanba,dole
ne tayi wani abu akan yaran nan,shikuma sam
bai runtsaba yatasa yaran yana kallonsu hawaye
na bin kumatunsa,bai san ko na mene neba
hawayen,na tausayin yaran ne ko na bakin cikin
da uwarsu ta kunsa masa?ckin haka Mama ta
farka,Momy kawai take kira,hankalin shi ya sake
tashi,zafin jikinta na nan,ya bata magani yasata a
kafada,Kausar ma tatashi ta zauna tsakiyar gado
tana kallonsu,itama kukan take amma na
zuci,dakyar Mama tayi barci,sannan yaje kusa da
Kausar ya dafata,’Yata kiyi hakuri kar karkiga
laifina,mamanku ce ta jawo hakan,Khausar tace
metayimaka Abba?intayi maka laifi ne Abba ka
yafe mata,kaji?yaushe zaka kaimu,Anty bata
sonmu Abba,yarungumeta,kiyi shuru zan kai ku
kinji,amma sai kunyi hakuri kun dan kara kwana
2 kinji?Haka yayita lallashinta har tayi bacci.
Hudu daidai aka bukaceshi wurin aikinshi,
sakamakon yan fashi da suka shiga wani
gida,dole y fice zuciyar shi cike da tunanin
yaran.Mujidat kuwa yana fita ta koma gurin dan
ta tare da cewa babu wanda zai hanani
bacci,tanajin lokacin da Mama ta tashi,tana ta
kuka amma matar nan taki fitowa,Khausar ta
farka taje ta dora kan Mama a kan cinyarta dan
bazata iya daukar taba tana ta jijjiga ta tana cewa
yi shiru Mama zan kira miki Momy,in kira miki
ita?tayi shuru.
Al’amin ma ya tashi ya zauna,kashi da fitsari
mama tayi,Khausar ta rasa yanda zata yi gashi
jikin Mama y saki,ba zata iya daukarta ba,haka
suka tasata suna kuka,har gari ya waye.Khausar
ta je dakin Mujidat ta same ta tayiwa danta
wanka tana bashi madara,ta ce, ‘Anty Mama ta yi
kashi. Mujidat ta dalla mata harara, sannan ta
ce, ‘To ina ruwana? Kije ki wanke mata. Khausar
ta dawo da kuka, suka ci gaba da zurawa Mama
ido.
Fitar Aliyu zuwwa takwas na safe ya kira Mujidat
sama da sau biyar yana tambayar yaran, tana
fada masa cewa suna bacci har yanzun basu
tashi ba. Badon ya kira ta cewa gashinan ba to
da zai samu yaran a yanda ya bar su, ko kuma
yanda suke. Jin cewa ga shi nan sai ta nufi dakin
da gudu ta dauki Maman zuwa bandaki inda ta
shiga wanke mata tana yi tana zagi,da ta fito sai
da ta rankwashi kan Khausar wai me yasa da ta
ji kashin ba ta kai ta bandaki ba?
Kausar din da Sadiya ke yi wa wanka yau ita ce
da yin wanka da kanta,sannan ta yi wa kannanta.
Maama tana ta rawar sanyi, Mujidat dama tun
da ta nade zanin gadon ta aje tare da cewa. In
ubanku yazo dole ya wanke ko inyardashi.
ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Tana hada musu tea ya shigo,duk suna zaune
rakube lungun kujera, Mama tana manne jikin
Khausar, ya isa gurin ya dauke ta.Mama ya jikin?
Khausar ta soma kuka, ‘Abba don Allah ka kaimu
gurin Momy, kaga Mama bata da lafiya, tayi kashi
na fadawa Anty sai ta koreni, kuma har ta
dokeni. Ya kalli Mujidat rai a bace, da sauri ta ce,
‘Ta shigone ba sallama, da yake ta san tun a
gaban uwarsu in sun shigo ba sallama yana
korarsu yace suyi. Khausar tace Allah Abba nayi
sallama. Nan yashiga ruwan bala’i, ya ce itamafa
zai iya rabuwa da ita kan yaranshi, ta soma kuka
duk abin da take yi baya gani, ta aje hada Tea
din ta nufi dakinta,nan ya hada musu kawai suka
sha da kyar, sannan ya shiga gurinta. Ya ce shi
dai ya roketa ta duba masa yaranshi amma in
har son datace tanaymaasa na gaskene, tsakanin
mata da miji nan da nan ya lallabata suka shirya,
kuma tayimasa alkawarin lura da yaran.Tun daga
ranar sai ta dauki salon da mata da yawa
sukeyi,in yana nan ta nuna kulawa in baya nan
sai zagi, hantara gami da kyara. Hakan ya sa shi
sakin jikin cewa zata rikesu, har ma ya daina
yarda da korafin Khausar na cewa ta musu kaza,
ta yi musu kaza.
Cikin wannan halin ya nemi makarantar boko
yasasu, sannan ya samo musu malamin
Islamiyya,sai dai sam yaran tamkar kurame ko
sun je makarantar basa magana bare karatu,in
an tashi break sukan hada kansu guri guda, kallo
daya zaka yimusu kasan suna da matsala.
Ni kam zuwa yanzun an samu wata biyu rabona
da yarana har na dangana da kukan fili sai na
zuciya. Haka nan kullum cikin tunanin su da
ambaton su tare da yi musu addu’a Allah ya kare
minsu. Wani dare nayi mafarki wai Mama ta rasu,
tun Asubahi nake kuka, Iya ta yi ta lallashina wai
taci ta koshine, duk da haka shida daidai na kira
Anty Abida nace tataimakeni tabani Yaya Usman,
tabani shi nace, ‘Yaya ka taimake ni ka je ka
dubo min yarana, ina zaton akwai wadda ta rasu
a cikinsu,dan na yi mafarki. Ya ce, Sadiya nutsu ki
kwantar da hankalinki. Nace, Yaya don Allah
zakaje? To shi kenan zanje jibi ranar Lahadi. Na
ce, To yaya na gode.
ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ina ajiye wayar ya kalli Abida ‘Wallahi ina
tausayin yainyar nan kinsan Allah banda ita,
wallahi bazani inda aboki yake ba,domin ranar da
zai bar garin nan sai da naje na sameshi, ba
yanda ban yi ba a kan cewa ya bar yaran gurin
uwarsu,sai ya ce shifa sam bazai bar mata yaran
shiba,tunda ita iskanci ta zaba,nace masa baka
da tabbas, kana yin abu sai ka ce bakaje
makaranta ba, wai kuma kana jami’in tsaro, ka
gaggauta maido da auranku ta hanyar sake daura
wani,domin idan ba matata ba ce nasan cewa ba
za ta iyaba. Kin san me ya ce? Abida ta ce, ‘A’a.
Usman ya ce, Budar bakinsa sai cewa yayi ba zan
maida taba,kaima kana da dama bai haramtaba
inka shiga layin zawarawa,sai ka aure ta kasata
gidanka. Abida ta zaro ido tare da rike haba
‘Lallai Aliyu ya dauki abin da zafi. Usman ya ce,
Shi duk ya manta abin da ya yi na zaci yarinyar
nan za ta tona masa asiri,saboda abin da yayi
mata, amma da yake ‘yar halak ce. Abida ta ce,
In nice Allah saina tona. Usman ya ce mata, Da
yawama bazasu shanyeba, ita wannan yarinyar
daban ce, amma bazai ganeba sai nan gaba
(Nasan dayawanku kuma bazaku iya abin da
Sadiya tayiba ko idan kuma da wacce zata iya ta
fada muji! Duk da banayiwa kowace mace daga
cikin fatan makamacin wannan rayuwar…ANaM)
Abida ta ce, Inzaka je muje tare ina son ganin
yaran. Yace bari mugani. Har gida Yaya Usman
yazo yayi ta lallashina tare da daukar min
alkawarin zaije ranar Asabar ko Lahadi, sannan
ya ce ya yi alkawarin binciken duk wanda yayi
wannan kulli. Cikin kuka nake masa godiya. Haka
kuwa ranar Lahadi Anty Abida ta kirani ta sanar
da ni cewa gasu a hanyar Abuja,cikin raunanniyar
murya nace. ‘Anty ki taimakeni in kunje ki kirani
mugaisa. Ta ce to. Na san ba kowa zai fahimce ni
ba, wasu za su ce na cika kawa zucin ‘ya’ya,
amma duk wadda ta taba shiga irin wannan halin
ina nufin ta rabu da ‘ya’yanta, ba wai ta yi
tafiyane tabarsu taje ta dawoba, ba wai sunje
hutubane, sakinta akayi,sannan aka kwashe mata
yaranta dole zata dandana irin abin da naji, ko
nake ciki yanzun.
Ina ta zaman jiran kiransu. Sha biyu da ‘yan
mintuna Usman ya kira wayar Alliyu,a ringing na
biyu ya daga suka yi sallama a tare, Usman ya
amsa,sannan yace, Aboki ina zan same ka,ina
Abuja yanzun haka. Aliyu ya ce, Ina office ko
zaka karaso? Aliyu ya ce, Shi kenan.Sun sameshi
bakin hanya sannan suka karasa gidan.Abida sai
kallinshi take duk ya rame suka gaisa, sannan
suka isa gidan.kamar kullum yaran suna takure a
gurinda suka maida tamkar gurin zamansu,wato
gefen kujeru,Mama da Al’amin duk sun jingina
jikin Kausar wadda suke ganinta tamkar uwa a
garesu,domin itace take yi musu duk abinda
uwarsu take musu,in har kaga Mujidat tayi musu
wani abu to tabbas mahaifinsu yana gidan.
Ko da sukaji sallamar mahaifinsu basuyi wani
yunkuri tashi ba don taryarsa.sam Abida har ta
zauna bataga yaran ba,Aliyu ya kalli gurin.
ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Khausar ku taso mana,yaushe zaku daina zaman
gurin nan?
Abida ta zaro ido tare da mikewa”Khausar!yaran
suka mike da sauri dukkansu suka rugo da gudu
tare da rungume Abida sannan sukayi gurin
Usman,Aliyu ya cika da mamaki,ya manta rabon
dayaga yaran haka suna murna ya nufi ciki kiran
matar, Abida duk da cijewar da takeyi sai da
hawaye suka soma yimata sintiri,Usman ya kalle
ta ya girgiza kai alamun tadaina, amma ta kasa
saboda yanda yaran sukayi baki suka rame,gashi
ba wata cikakkiyar tsafta,kitson kan su Khausar
duk ya tsufa,ba’a ko ganin layin kitson.ta tuna
yanda yaran suke kansancewa tsaf cikin tsafta da
tsantseni kowa sha’awarsu yake,ta dauki mama
ta rungume.Khausar tace,aunty maman mu fa?
cikin rawar murya tace,lafiyarta kalau,tace a
gaidaku,Al’amin yace yaushe zatazo? Khausar
tace,kai sunzo tafia damu ne.ta kalli Usman
Uncle ai dai zaku kaimu gurin Momy ne ko?kafin
Usman yayi magana,Aliyu suka fito da Mujidat
tana sanye da riga da siket na shadda mai ruwan
kwai,shikuma yana sa6e da Abdul,wanda aka
tsafta ce shi ckin jeans blue da riga ja,sai wani
dacin rai takeyi.ta zauna tana gaida su cikin
yatsina, Usman ne ya amsa Abida kam ta kasa
magana don bakin ciki.
Usman yayi mata sako cewa don Allah ta
nutsu,sabida yaran sun soma kuka suma.Aliyu ya
kalli Mujidat,a kawo musu abinci da abin sha
mana,ta tashi can ta kwalawa Khausar kira da
sauri ta tapi,sai ga ta da pure water leda biyu da
dan kwalin juice,sai kofi 2,ita kuma ta fito da kula
yar madaidaiciya. Abida ko ruwa batayi burin
shaba,bare abinci,Usman dai ya dan kurbi Juice
din da Aliyu ya tsiyaya ta mika masa,daidai
lokacin ni kuwa na kasa hakuri nakira layin
Abida,ta dauka yanda naji muryarta sanyi
kalau,sai na soma kuka,nace Aunty ta mutu ko?
Abida tace a’a lafiyarsu lau,bari kijisu.
Ta kamo Kausar zoki gaida Mamanki,cikin doki ta
amsa tace Momy,nace na’am…’kukan yaki tsaya
min,cikin rishn nace kausar.ita ma yarinyar ta
saka kuka tana cewa Momy don Allah kizo ki tafi
damu,hankalina yakara tashi nace,Khausar kuyi
hakuri kinji?ki lura da yan uwanki kinji? Cikin
kuka mai tsanani tace,wayyo Momyna! don Allah
zamu zo Momy.
Abida cikin hawaye sharkaf ta amshi wayar ta
rungume Khausar,Sadia yaya zakiyi haka?kinsan
zaki kara tadamin hankali ne,kika kirani,nace yi
hakuri Aunty,Aunty kibani Al’amin da Mama.tace
a’a bazan baki suba dan ganin Khausar tana kuka
suma gasu nan sunayi.Khausar ta sake janyo
hannun Aunty Abida tana cewa,Momy don Allah
kinji Momy!!! Tilas na kashe wayar na dasa sabon
kuka,iya dake kallona itama hawayen take
sharewa tana cewa “Sadiya kidangana da ‘ya’yan
nan. Na kalleta Iya kitayani addu’a Allah yaba ni
hakurin jure rashin su kinji Iya? Tace to Sadiya ta
taso ta kamani ta rungume tana lallashi tamkar
yarinya karama. Su kuma a can Aliyu ya kalli
Khausar meye abin kuka? Mujidat dake gefe ta
tabe baki tare dace ” a to” Ta gatsina hanci gami
da hararar Abida tana magana kasa kasa Abida
tace Kuka ya zamar musu dole wadannan yaran
kanana a ce an rabasu da uwarsu? Aliyu na
rokeka arziki kayi hakuri ka bamu yaran nan
mutafi dasu Uwarsu tana cikin damuwa Yatabe
baki Kadan tagani ma kin san Allah bazan bada
yarannanba ko zasu mutu daga ita har su,Usman
yadagawa Abida hannu alamun tayi shiru sannan
yakalli Aliyu Aboki zamu tafi daman munzo ganin
yarane,ya dauko ledar gefenshi Khausar yi shiru
ga tsarabarku tana sheshshekar kuka ta amsa
tana ji da dan nauyi har ya mike ya cewa Abida
tashi muje sai kuma ya tuna da binciken shi
yadawo yazauna yace Aboki ina son wani taimako
daya Aliyu ya kalle shi inajin ka. Yace zaka bani
sunan wannan account din zanyi searching zan
gudanar da wani bincike Aliyu yaruntse ido
wallahi bana son a tunamin komai game da ita
ban san tuna account din nan. Usman yace bazan
samu ba kenan? Aliyu yakalli Mujidat dauko min
laptop dina sun kunna inda suka fito da komai.
Aliyu yadauke kai inda Usaman yashiga bincike
cikin sa’a akwai lambar kuma ta MTN sannan
shima Malam din ya dauki lambarsa haka nan
yadauki ta wanda yakawo gulmar wanda yace
sunan shi Sulaiman yakulle komai sannan yamike.
Mujidat tazaro ido tana kallon Usman cikin
zuciyarta tana tsine masa, suka mike suka tafi
Abida tana kuka su Khausar na kuka haka aka
rabu yaran suka ruga daki suka dora sabon kuka.
Mujidat da gudu tashige daki lokacin da Aliyu
yatafi rakasu Usman takira layin Jamilu daya
dauka yace lafiya? Ina ta kiran layinki kin ki
dauka don kada ki bani cikon dubu 2 na koh?
Tace zan baka mun tashi daga kaduna ba shirine
zan aikowa Anty Ramata zata baka amma kana
ganin asiri bazai tonuba? Yayi Tsaki Sungama su
hkr Mujidat ta sauke ajiyar xuciya sannan takashe
wayar.
ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Aliyu yakalli Usaman Aboki na godefa tunda
abinnan yafaru banga wani nawaba sai yau ga
tunanin Iya a xuciyata bansan ya zan tunkaretaba
dan nasan Sadiya ta fadamata abinda nabinne.
Usman yayi murmushi, ay Sadiya mutumce
wallahi har yazu Iya batasan wancen zancenba
kayi mamaki koh? Aliyu yayi ta kallon Usman
tunanin cewa zata fada shiyasa ya tattara ya bar
kaduna ya maimata bata fadaba? Usman yace ko
daya Aliyu yace Uhm duk na zata ta fada. Usman
yace shiyasa nace kayi bincike kan wannan laifin
dakake zarginta. Aliyu yace tafa aikata laifinnan
bazanyi mamakiba sabida shaidan ba rago bane,
nima nazaci zan tsinci kaina acikin haka?Usman
yace inma gaske ne bazakayimata adalci ba? Aliyu
yace adalcin kenan nayi mata na saketa kalau ba
tare danayi mata dukan hauka ba sannan banda
ta fada na so in ramawa kura aniyarta wato in
bar zancen tsakaninmu inkuma dauki nauyin
zunubin zagin da za’ayi min na sakinta batare da
tayi min laifi b kawai sai ta tona. Usman yace
Aliyu kenan bari muwuce Allah yabayyana gaskiya
inga yanda zakayi Aliyu yace wahala kawai zaka
sha amma gaskiyar ce tabayyana in kalura da
hirar data gudana atsakanin ta da malamin.
Koda suka tafi ya jima bai shiga gidanba yana
mamakin yanda Sadiya taci gaba da rufa asirin
shi yayi ta ganin kiran kiran yayunsa. Yaya
Sulaiman, Yaya Sani, Yaya Zakari, kai har kawu ya
kirashi amma ya ki dagawa nashi ganin asirin
shine yatonu zasu kira suyi Allah wadai dashi to
shi in ya dauka dabatun sakinnan ze kare kanshi
Aliyu Kenan.
Koda Anty Abida ta dawo sam bata nunamin
cewa yarana suna cikin matsalaba, illa fadan da
tayimin na kukan danayi tace shine yasa su kuka.
Jin hakan sai na kwantar da hankalina kadan, don
har Usman ma yace min kada in damu suna
samun kulawa. Haka na dangana sai dai duk na
rame yarona kawai ke tafka kibarshi har mukayi
kwana 70 nace baxan koma aykiba,Iya tazare min
ido dole nakoma yanzun mota nake hawa zuwa
gurin aiki dan ban waiwayi motarshiba.
Ranar asabar ina zaune a tsakar guda yarona
yana cinyata na kifa shi ina karanta dan karamin
alkur’ani mai girma suratul Bakara kamshin
turaren yaya naji kafin sallamar shi tabiyo baya
badon na san mahimmancin amsa sallama ba da
baxan amsaba, sannan banko dago kainaba bare
nadube shi yayi sallama dakin Iya tana ciki can
kan gado don haka bata jishiba shima din be
tankaba yashiga dakin. Natashi nagoya dana naja
Hijabina a igiya na dauki pose dita da yan canjina
napita sai gidan Aysha, taganni hankali tashe tace
lafiya har yanzu baki kwantar da hankalinkiba?
Haba Sadiya. Naxauna hawaye suka soma zuba
daga idona nace ni na hakura Aysha yayane yazo
gidan yanxun, wallahi shine yafama min bakin
cikin daya cusamin,ta dapani yi hakuri meyace?
Nace bamu ko kalli junaba fitowa nayi dan ko
ganinshin shi banasan yi. Aysha tayi ta lallashina
tana bani hakuri tace kin fadawa Iya shima
abinda yayi? Nace har abada baza aji daga
bakinaba wannan ya wuce saidai taji gurin wani.
Ina gisan har dare sannan suka rakoni ita da
Bellonta, itama dai tana tayi min korafin cewa
Bello yanzun sai bakin halaye yake shigo mata
dasu, ya soma doguwar hira sai yakai sha daya
bai dawo gida ba yayi ta ‘yan daure daure da
fadace fadace. Nace lallabashi zaki Aysha kiji ko
kin masa wani laifi ne kar ki dauki fushi da
mijinki karamar matsala tazama babba, kar kiyi
sanadin dazaki nesanta kanki da yaranki ni na
isheki misali Aysha ‘ya’ya sune rayuwar uwa
kamar yanda uwa take rayuwar ‘ya’ya yanxun
duk macen da bata tare da ‘ya’yanta ina tausaya
mata dan na dandani ciwon dataji. Cikin bacin rai
nasamu Iya nace, Iya ya ne? Tace Sadiya ina
kikaje? Nace gidan Aysha natafi kiyi hakuri
banfada miki ba wallahi ganin yaya ne naji bazan
iya zaman gidanba shiyasa natafi. Tace baki
batamin raiba Sadiya bacin ran Ali ne yaron nan
na zata yayi nadama ne ashe zuwa yayi yabani
hakuri, nace me kayimin? Ni awa zakazo bani
hakuri? Ali banzaci zan sake sakaka a idona ba.
Yace sabida me zaki ce haka Iya? Na tafine don
ki huce sannan inzo in baki hakuri dan na san
cewa babu wanda zai fahimceni ko yabani
gaskiya akan sakin danai wa Sadiya duk kuwa da
cewa yin hakan ba laifi bane. Iya tace sai na tari
numfashinsa cikin gatse nace to dama Ali waya ce
kayi laifi? Ko guda banga laifin kaba don ka auri
mace kana sonta lokaci guda kuma kaga ka daina
sonta ko ta maka tsufa ka sake ta sai ace kayi
laifi? Laifin da kayimin daya ne bata min ita da
sharri wai tana bin maza wannan kazafi yayi min
ciwo sosai domin yarinyar nan har ta gama
kuriciyarta a cikin gidan nan kaganta kace kana so
ka aura bata taba dauko min maganaba. Iya tace
Sadiya yau har nauyin na aje gefe na tsakanin da
da mahaifi na tambayi gadanga cewa ko ba
budurwa kasame taba? Sai ya sunkuyar da kai
nace in ba budurwa kasameta ba sanar dani.
Yace Iya duk ba wannan zancen bane ai mutum
yakan canza kuma ni fara koyarwar ta dinnan ne
ta hadu da abokan banza. Iya tace na ce dakata
bata tare dakowa nabanza kai dai ka gaji da ita
ka saketa ka kuma hada mada da sharrinka na
‘yansanda to kaje Allah ze sakamata ina raye sai
naga sakayya sannan ‘ya’yanta in kun lura dasu
kuda Allah inma kun wulakantasu kuda Allah. Ya
kasa magana sannan wai ina jaririn? Nace yana
gurin uwarsa ai danaga baka waiwayeshi ba na
zata zakace ba danka bane? Yace ni bance ba
Iya, yaciro kudi ya aje wai gashi kibata sabida
siyan wasu abubuwan na yaro Iya tace dauki
kudinka babu abinda muka rasa yayi shiru can ya
sake cewa. Ina kara baki hakuri iya nace kai ne
da hakuri amma dauki kudinka in ba so kake
kaga bacin raina ba,ya dauka yafita.Na sauke
ajiyar zuciya nace, Iya na gode dabaki karba ba
na sani sosai Iya cewa bashine yayi min sharriba
wasu ne daban amma takaicina yanda yakiyin
bincike kuma yayarda cewa nice, kobe sakeni ba
aure baya yiwuwa da zargi.Iya tace ay na gaya
masa nace lokacin daka fito da abunka kana
ganin ya maka tsufa sabo kake so, lokacin wani
kuma zai ga cewa na kannan shine sabo agurinsa
Allah yayi miki zabin Alkairi, nace amin.
Daren ranar su Yaya Sulaiman suka zo da shi su
hudu wai iya tayi hakuri tayafe masa sannan
suka matsa masa cewa ya maido da matarsa
kuma ya yarda amma da sharadin zata daina
koyarwa. Ina kwance kan gado a uwar daka ina
jin su tamkar in taso in fito in ce bazan koma ba
amma sai na tsaya inji me iya zatace? Ay kuwa
sai naji Iya tace da farko dai kamar yanda na
shaida masa dazun ni bai min laifi ba bare ya
bani hakuri in da ace ni wata ce lokacin da
rigimar tafaru yaneme ni mana sai kurum yatafi
ya aikata son ransa yanzun yazo yana ban
hakuri,ni a wa? Batun kome kuwa ga matarsa
nan adaki tazo in zata koma bazan sata ba kuma
bazan hanata ba, Tadaga murya Sadiya na’amsa
tace zo nafito da dana akafada na zauna
gefe.tace nasan kinji komai dan haka in zaki
koma sai ki fada musu, shidai sun bashi baki ya
yarda,Budar bakin da nayi sai kuka nace yaya
kuyi Hakuri da abinda zance in Yaya Aliyu ne ya
rage namiji a doron duniya wallahi tallahi bazan
aure shiba bana kosan ganin shi ya fita a raina
sam.Iya tace tashi ki koma ciki sannan tace kunji
koh? To kuma na roke ku da kar ku sake
zuwamin da wannan zance ko gaba an rufe
wannan babi in dansa ya isa yaye yazo ya
dauka,bansan lokacin da nace Iya harda wannan
ma za’a rabani tace Allah ya baki wani mijin na
gari ki haifi wasu yayan Sadiya,sai lokacin Aliyu ya
dago ya dubi Iya sabida yaji zafin kalmarta
sannan ya sake sunkuyar da kai Aliyu yaba yaya
Sulaiman kudin yadan matsa yace iya ayita hakuri
shin ina Sadiyarne? Na fito ya miko mini nace a, a
yaya muna da komai na koma ciki yace ke Sadiya
zoki karba hakkinkine da danki Iya tace tunda
tace bata so saiku barta ko ku tashi kuje zamu
kwanta…zamudakata anan,fatan zamuyi sallar
juma’a lafiya
ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu
nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347

Related Articles

Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100

Darajar Yayana4-02
Posted by ANaM Dorayi on 12:11 AM, 12-Apr-16
Under: DARAJAR ‘YA’YANA
________________NA ___________HALIMA K/MASHI Haka suka fita jiki babu karfikowa ya nufi gidan shi suka nufi nasu da safe na gama yiwa yarona wanka kenan sai gashi ya shigo sanye da kananan kaya sai yaune ma na kalleshi yadan rame yayi duhu natabe baki sannan na bata rai Iya ta fita siyo mana biredi na gama na kwantar dashi kan kujera zan fita da ruwan sai naga yakai hannu zai dauke shi da sauri na dauki yarona na sashi a bayana na kwance zanin jikina wanda dama na dora ne a saman dogon wando na goyeshi sannan na dauki ruwan, yako ji haushi cikin zafin rai yace me kike nufi? Nace duk abinda kake nufi ,na kalleshi sama da kasa yace nufinki bazan dauki yarona ba? Nace au shima danka ne? Na zata inda nake zuwa na yoshi yace karfa kiga Iya na daure miki gindi ki zata har kin kai matsayin da zakiyi min rashin kunya dan kinga na kyaleki ban dauki mataki a kankiba, nace don Allah kaini kotun musulunci yace bani yarona in ganshi? bazan bayarba,Sallamar Iya tasa yazauna kan kujera nima nazauna, na kwantoshi nasoma shafa masa mai Iya tashigo dakin ganinshi sai ta daure fuska tace lafiya me kuma yakawoka? Yace Iya gurinki in gaisheki tsaki taja sannan tafita zuwa kicin Yakalleni Nan gidan ubanane ba mai hana ni zuwa. Nima na harareshi ina ruwana Allah yasa nima ina da gidan uban. Kafin yayi magana sai ga Iya ta shigo da ruwan zafi takalle ni zo ki karya cikin jego, kawo shi in sa masa kayan. Nace to, bayan na karasa sa masa pampers din na mika mata shi. Ina zama yayi caraf ya mika hannu ya dauke shi a hannun Iya na kalleshi cikin tsana nazauna shima yaharareni sannan yazauna yana kallon yaron, banzaci ya san sunan shiba sai naji ya ce Iya Sadiq ma dani yake kama sosai yanda ban tankaba itama bata tankaba. Yarungumeshi tsam a kirjinshi, sai kurum nafita tsakar gida ina karyawa. Ashe Iya ma ta shige uwar daka dan haka yadauki kayan yana sa masa yagama yamike yafito da shi ganin zai yi waje nabishi da gudu a ganina zai tafi da shine, ina fadin Iya zaitafi dashi nasha gabanshi,bani yarona dasauri Iya tace kyaleshi yatafi dashi din seme? Nasoma kuka shikuma sai hararata yake yi yaja tsaki yawuce nace Yaya inka tafi dashi saina tona asirinka tsam yatsaya sannan yawaiwayo yakalli Iya itama shi take kallo sannan takalleni na isa gabanshi namika hannu Bani yarona.Sai yamiko minshi sannan yafita da sauri naje kan kujera nazauna ina cika,Iya ta iso gabana wane irin asirene zaki tona masa?yaken dariya na kakaro birgace kawai nayi masa babu komai Iya. Tayi yar dariya haba Sadiya shi mahaukacikane bayan ba wani sirri jikinsa yayi sanyi haka? In dai da wani abu kifadamin,Nace ba komai iya tace oho miki in ma dashi, shiyasa wani lokacin banasan shiga shirginku.Ni dai sim sim nayi daki. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Hudu da ashirin ina kwashe tuwo naji sallamar
shi ciki ciki na amsa, banyi tsammanin ma zaijiba
na dago nadubeshi cikin tsana, sai naga
hankalinshi yana kan yarona wanda nashimfida a
tabarma akan katifar shi nakwantar dashi akofar
daki Iya tana zaune kusa dashi. Dagudu na aje
tuwon dake hannuna nafito har ina tsallaka iya
nasuri dana nasa a baya naja zanina a igiyar
shanya nagoye shi sannan nakoma kicin ina jin
tsakinshi a raina nace kadai karata can.Daga inda
nake ina jiyo shi yana gaida Iya, dakyar ta amsa.
Yace zantafi zaria dama wani ayki nazoyi Kaduna
akwai wani malami ne da ake zaton kasurgumin
dan fashine to kan shi nake aiki,rahotanni sun
same mu cewa ya koma Zaria acikin satin nan
kafin inzo dan wata na biyu kenan ina nemanshi
tun daga Maiduguri nake biye dashi har zuwa
nan ina son Iya kitaya ni da addu’a Allah
yataimake ni. Iya tace Allah yabada sa’a. Yace
amin. Tace malami kuma dan fashi in banda son
duniya? Ay irinsu suna da yawa Iya kuma yana
siffatuwa ne da malai manyan malamai yana da
ilimin, sai dai shi dan fashine ga tsafi ,sama da
shekaru goma ankasa kamashi,kingako kamashi
nasarace. Iya tace Allah yataimaka yace amin
yaciro kudi gashi Iya. Tace a’a ai na fada maka
bamu da bukatar komai,yasake tausasa murya
Iya wannan fa tsakanin mune ni dake in baki
amsaba sai inga tamkar kin cire ni a tsatsonki,
Ya’ajiye gefenta. Iya kiyafemin natafi.,Bata ce
komaiba kuma bata dauki kudinba yazo bakin
kicin yajeho min wasu mukullai ga mukullin
gidanki nan kije ki dauki motarki aciki. Nadubeshi
fuska daure cikin harara nace bani da gida bare
mota in kana nufin motarka to bana so,tsaki yaja
sannan ya wuce batare daya dauki mukullanba.
Nafito gurin Iya rai a bace nace Iya naga har
kulashifa kikayi kuna hira har yana wani baki kudi
kina karba? Iya tace kin san shi naci zai tayimin
shiyasa narabu da shi ya aje kudin dan yatafi
yabamu guri sannan ina zulumin yanayin aykin
nan nashi wannan malamin kuwa dan fashi
tunkararsa hadarine ina tsoron karya halakashi.
Gadanga shiba mutumbane mai son neman tsarin
kai, da kaikayi koma kan mashekiya,da kai
magana zaice yana addu’a an san dai ita ce
dama kan gaba. Don haka itama Iya ban tanka
mataba wato ma tausayin shi takeji.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Aliyu yayi masauki unguwar Mazan Gudu gidsn
limamin unguwar da sunan cewa shi bakone
matafiyi ne. Hannu 2 aka karbeshi kwanansa 2
yace a nema masa daki na haya yana son yadan
kama sana’a yafada musu cewa rani yake Zuwa
garin Kaduna daga Hadeja yake,Liman har yayi
masa tambaya game da wasu unguwanni a can
Hajejan Allah yasa garuruwan da Aliyu yasani ne
ya kuma fada masa cewa ya sani. Liman yace sun
zauna sun danyi karatu a garin shekarun baya
lokacin suna yawon neman ilimi. Liman yace Aliyu
yazauna ga daki nan a zaure a gidansa na
dansane dake karatun boko a jihar sokoto a
jami’ar shehu dan fodio. Cikin sati daya yasaba
da makota. Akwai wani dan dandali da mazan
unguwar ke zama ko in ce majalisa. Tuni Aliyu ya
saba da yan majalisar in da ake zama ayi ta
labarin wane da wane ko duk wanda yagifta.
Anan yasamu labarin wannan malami daya sauka
gidan sarkin malaman kusfa ance yanda ilimi
sosai kuma yana bada fatawa. Aliyu yace dan
Allah wanda yasan gurin yayimasa rakiya don
yana son daukan karatu. Kullum ‘yan majalisar
nan suna mamakin Aliyu duk irin shigar dayakeyi
ta kaya marasa kyau amma fatar jikinsa bata
nuna cewa daga kyauyen hadeja yakeba kamar
yanda yafadamusu. Akwaima wanda yakecewa
shifa yana wa fuskar Ali kallon sani.
Cikin sati 2 sukayi sabo da Malamin wanda yasaki
jiki da Aliyun amma sai dai Malamin ya fadawa
Aliyu shifa malamine mai yawon yada da’awa
don haka daga nan zai wuce Katsina ne tafi tafi
har Nijar. Aliyu yace in ba damuwa zaibi shi,Aliyu
ya lura da yanda malamin ke daga waya akai-
akai sannan ya lura da irin kudin da malamin ke
rabawa jama’a sadaka. Duk binciken dayayi ya
gano cewa malanin ne wanda yake nema sai dai
dama yana da labarin matsawar malamin yana
cikin daki bazai kamuba. Ana gobe zasu bar garin
kamar yanda suka shirya har da shi Aliyu
shikuma ya daura aniyar kama shine aranar
jajiberen tafiyar. Karfe 2 sun taso daga sallar
Azahar Aliyu hankalinshi tashe burin shi yanzun
idan sun iso kafin su isa gidsn malamin ya sauke
yashige daki. Aliyu yakalli malamin. Allah
yagafarta malam naga jama’ar wannan garin
suna alhinin rabuwa dakai shin bazamu dan kara
kwanakiba? Malam yakalli Aliyu ina da dalilin
barin garinnan asubahin gobe.Aliyu yace Allah
yasa haka shine mafi Alkairi. Malam yace ameen.
Sai dai kai ina mamakin yanda kake son bina ban
cika sakewa da mutaneba amma kai raina ya
kwanta dakai amma daganinka ka taba zaman
cikin birni? Aliy yace e duk cikin gari nayi
rayuwata ban zauna gidaba, Malam yayi
murmushi toh Aliyu sai dai kayi hakuri ina zaton
bazanje dakaiba. Aliyu yace saboda me malam?
Malam ya gyara tsayuwar wato malam Ali an
sanar dani cewa duk inda zan shiga kada in shiga
da mutumin cikin gari domin shine zai zamemin
hadari cikin rayuwata. Aliyu yace Allah gafarta
malam an fada maka kamannin shine munyi
kama? Yace ko kusa an dai ce min zai shiga jikina
sosai kuma zai cutar dani a rana irin ta gobe
shiyasa duk lokacin dazan bar gari nakan barshi
tun asubahi. Aliyu wanda ya kosa yaga isowar
jami’an tsaro yace toh Alagafarta yaya zaka yarda
da irin wannan kila ba gaskiya bane. Malam
yadafa kafadar Aliyu inayimaka fata nagari Allah
yasa zamu hadu wata rana amma wanda yafada
min zancen nan yasha fadamin zantuka suna
tabbata ina ji ajikina zamu sake haduwa da…..
Jiniyar motar ‘Yansanda ce tasa malam bai karasa
zancenba sai Aliyu yaga malam ya daga kafada
yasa gudu cikin azama da kwarewa Aliyu yaciro
bindiga daga bayan wandasa ya harbi malam a
kafa take malam yafadi amma burinshi yakai daki
dan haka ya yunkura Aliyu yayi azama yacafkeshi.
Mutanan gurin sun cika da mamaki harma suka
taso da nufin jin ba’asi sai dai kafin suji dalili tuni
yan sanda sunyi zobe a gurin sun kuma cafke
wasu daga cikin makarraban malamin sannan an
samu muggan makamai cikin kayan malamin da
kudin kasar Amuruka(Dollar) da irin namu na
gida. Mutanan unguwar suna ta al’ajabin lamarin
yayinda wasu ke mamakin Aliyun wanda suka
zata shima yana cikin mukarraban malam. Ta
gidan lima suka bi mai masaukinsa,Aliyu yayi
musu sallama yadauki yan kayan shi tare dayi
masa alheri haka ma yen majalirarsu yatafi yabar
su da labarinshi tare da jinjinawa aykin shi.
Cikin wata hudu da aka damka aykin hannun
Aliyu ya samu nasara ya fara bibiyar malamin
tundaga maiduguri har kawo Kaduna sannan
Zaria inda yayi nasara sakamakon haka ya samu
lambar yabo tare da karin girma zuwa
mataimakin kwamishina na can Abuja haka nan
nasarar taja masa farin jini inda akayi ta haskashi
gidajen talabijin. Ina kallon Iya tunda Aliyu yazo
da batun aykin nan kullum cikin yimasa addu’a
take tare dayawaita sadaka. Araina nace da da
mahaifi sai Allah. Dubi duk haushinsa datakeji be
hanata yimasa addu’ab. Inzanje aiki yanzu gida
nake barin Sadiq sabida yana shan kamu. Iya
tasani gaba tana min fada wata ranar Litinin na
shirya zantapi aiki. Sadiya! Dan Allah shekarunki
nawa? Nace me yafaru Iya? Tace fadamin. Nace
26 Tace dubi duk yanda kika koma ba wani ado
ba kwalliyar da kikeyi ada, ki dage ko dan ki ba
Gadanga haushi,amma kullum sai kina yawo
kamar me takaba,Nace ni banima da kayan
kwalliyar,tace inzaki dawo ki tsaya kasuwa ki saya
in ma baki da kudi in baki,nace ina dashi a cikin
account dina,tace to.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ina zaune bayan na sallami daliban ajina sun fita
break nazabga tagumu ina tunanin zancen Iya
gaskiya ta fadamin bazan tsaya in tsufar da
kainaba tilas in nafita in shiga banki sannan in
shiga kasuwa. Shigowar alert ne ya tsaida
tunanina na dauka na duba kudi ne naira dubu
saba’in sannan yaya ne ya turo min. Haushi da
bakin ciki kamar inyi kuka don haushi. Dakyar
nabari aka tashi na nufi banki na ciri kudin daya
turomin naira dubu 70 na maida masa cikin
account dinsa sannan naciri dubu 20 dan yin
siyayyata acikin account dina. Nashiga cikin
kasuwa nasiyo mai na perpect nasiya duk kayan
shafawa, sannan nasai turaruka na har da kayan
humra dan dakaina nake hada humrata nasai
mayafai da takalma har atamfa na kara. Iya na
gani tace ko kefa. Nanfa nashiga gayuna kafin
wata daya na komo da farina da gayuna, sai dai
ban maida kibata sosaiba, ba wanda zai ganni
yazata ina da yara har 4. Wani abin dariya sai ga
mutane sun soma yin sallama dani.
Ranar wata juma’a ne sunan wata malamar da
muke koyarwa tare nayi kyau cikin leshi mai
ruwan madara ni kaina nasan nayi kyau taku dai
dai nake yi na tsallaka titi zan hau abin hawa sai
mota ta tsaya a gabana na waiwaya zanyi masifa
sainaga yaya Usman ne cikin dariya na isa gurin
shi. Yaya ashe kaine? Yace to na tsaya kafin inyi
magana sai naga za’syi min masifa nayi dariya ka
san mutane wai dasunga mutum ya tsaya sai
suce zasu dauki mutum. Yace hakane sai ina?
Nace nan Askulaye zani suna watace da muke
koyarwa tare ta haihu. Yace muje. Nace a’a
dakaje kada in batamaka lokaci yace hanya tace
ni gaba naci don kurmin mashi zanje. Nace ok.
Nashiga muka hau titi nace ina su Auntyna da su
Ummul? Yace duk suna lfy shine bakya son fita
da Sadiq koh? Nace shima ya saba da Iya baya
son bina. Yace ya huta da shan rana. Nace
wallahi. Naji cewa abokina yasamu karin girma
kwanaki? Nabata rai ina ruwana. Yayi dariya da
ruwanki mana koba dangantaka akwai su Kausar
nace harsu duk na barmasa na yafesu. Yace
bacin raine. Nace wai ya batun binciken? Yace
ina kan binciken kiris yarage in kammala. Murna
ta cikani cikin zakuwa nace kun gano kowane ne?
Yace eh toh na dai yi nasarar gano cewa mutum
dayane a abu uku Sulaiman din daya kawowa
aboki gulma shine malamin makarantarku kuma
shine Sadiya Abubakar mun gano hakan ne ta
hanyar lambar MTN Din dayayi amfani da ita
gurin cike form na account din da ya bude. Nace
a’a duk lamba daya yayi amfani? Yace a’a daban
daban ne sa’ar da muka ci duka na MTN ne
kuma duk yayi musu rijista taimakon dayayi
mana kenan. Nace Alhamdulillah. Muka danyi
shiru nawasu yan dakiku sai Usman yayi gyaran
murya yace, Sadiya! Nadube shi irin kallon
dayayimin yasa gabana faduwa nayi ta maza
nadauke kaina. In tambayeki mana? Nace
eh…ina…jinka. Nafada cikin in ina yace in
abokina yaji gaskiyar batun nasan zaku sasanta
koh? Nakalleshi da sauri nan take raina yabaci na
sunkuyar da kaina yaya Usman dan Allah na roke
ka kadaina yimin zancen yaya nayi rantsuwa
bazanyi kaffara ba,Muka danyi shiru na wani
lokaci,sannna yasake yin ‘yar gyaran murya
“Sadiya nasan kisoma tsayawa da masu sonki
ko?”
Nadubeshi “banajin zan bata lilacina gurin kula
su,domin al’amarinsu sai su.”
Yayi dan murmushi “karkiyi kudin goro”
Nan nanunamasa layin muka shiga,gabana yana
ta faduwa sabida irin kallon da yaya Usaman
yake yimin. Nace ga gidannan.ya tsaya ya
dubeni.
“Zan dawo in daukeki”
Nace a’a kayi hakuri daga nan zanwuce wata
unguwar,nagode.
Yace “ina zaki!”
Nadubeshi “Gidan kawata”
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Yace “Ok! Shikenan, kila zan dawo nanda anjima
inna zaton zamu tattauna wata magama mai
muhummanci
Nace to sai kazo.
Jiki babu karfi nashiga gidan sunan,duk da irin
shewa da wasa da dariya da abokan aikina keyi
ni nakasa ko murmushi.
Malama Bilkisu ta dubeni tace wai Malaman
sadiya kodai baki da lafiyane?nai dan yake kaina
ciwo yake Sukayimin sannu mai jegon har dacewa
ke kam tunda kika haihu shi kenan kika zama
sarkin ciwo. Nace aykam gashi nan na kasa maida
jikina. Adaddape nayi minti 40 agidan nafito na
nufi gidan Ayshata sai taganni kamar an jeho ni
ta tashi tare dapadan lfy? Nace Uhm wata
sabuwace tasamu. Tace kuma, to zauna kisha
ruwa kin taki sa’a yau alalar gwangwani nayi.
Naja tsaki ni wallahi yau ko nama kikayi zalla
bana zaton zan iya ci. Tace meyafaru? Nan na
bata lbrn duk yanda mukayi da yaya Usman
itama dai ta damu amma tace balallai yace yana
sonaba wai kila zuciya tace kawai ta zargi hakan
nace toh shikenan. Sai bayan magariba na yimata
sallama ta rako ni na hau mashin ina hanya naji
wayata na ruri, ina dagawa iya ta rufe ni da fada
ina natsaya ga Sadiq yana ta ihu? Nace gidan
Aysha nawuce gani nan tafe. Ina shiga yaya naci
karo dashi zai fito dashi a kafada yana ta kuka,
duk da darene na raya cewa fuskar shi a daure
take ranshi kuma a bace yake, nashige nazauna a
falo ina ninke mayafina sai gashi. Kin tafi yawon
banzanki kin bar yaro yana ta kuka ko? Ina
kikaje? Naki ko dubanshi nagama ninke mayafina
na mike zan shiga uwar daki yace baki amshe
shiba yana kuka? Iya ta sallame sallah tace ki
daukeshi mana ya jima yana kuka, nace to. Saida
nakai mayafina na ajiye sannan nafito fuska
daure na isa gurinshi namika hannu cikin harara
yabani shi sannan yayi kwafa. Kisani in zaki tafi
yawon banzanki ki daina ajiye min yaro a gisa
yana kuka banda shashanci me zai sa mace tafita
har magriba. Na zaci acikin zuciya nake magana
ashe tafito fili ina ruwana da kukan shi zan kiyin
harkar gabana ne saboda shi? Sai muryar Yaya
naji yace Iyee haka kikace? Nayi shiru. Tozan
dauki yarona in hada shi da yan uwansa in yaso
ke kije kiyi ta gantalinki. Nazauna nasoma bashi
nono ina jijjiga nace Tabdi Ay wallahu bazan bada
dana ba koh gaban Alkali Za’a,Iya dai tana jin mu
bata tankaba yace basai Alkaliba ahannunki zan
amshe shi kicika baki kigani. Nakalli iya don na
soma fargabar zantukanshi tsaf zai iya,Nace iya
kifada masa yafitga harkata yadaina cemin ina
gantali. Iya tace ki kyaleshi yazo yadauki dan
nasa gantali kuwa ai kin isa yine. Yatausasa
murya Iya kidena dauremata gindi tanamin
rashin kunya. Yakalleni. Zan targadaki in kika yi
wasa. Namike nashige daki shi kuma yawuce.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Haka suka fita jiki babu karfikowa ya nufi gidan
shi suka nufi nasu da safe na gama yiwa yarona
wanka kenan sai gashi ya shigo sanye da
kananan kaya sai yaune ma na kalleshi yadan
rame yayi duhu natabe baki sannan na bata rai
Iya ta fita siyo mana biredi na gama na kwantar
dashi kan kujera zan fita da ruwan sai naga yakai
hannu zai dauke shi da sauri na dauki yarona na
sashi a bayana na kwance zanin jikina wanda
dama na dora ne a saman dogon wando na
goyeshi sannan na dauki ruwan, yako ji haushi
cikin zafin rai yace me kike nufi? Nace duk
abinda kake nufi ,na kalleshi sama da kasa yace
nufinki bazan dauki yarona ba? Nace au shima
danka ne? Na zata inda nake zuwa na yoshi yace
karfa kiga Iya na daure miki gindi ki zata har kin
kai matsayin da zakiyi min rashin kunya dan
kinga na kyaleki ban dauki mataki a kankiba, nace
don Allah kaini kotun musulunci yace bani yarona
in ganshi? bazan bayarba,Sallamar Iya tasa
yazauna kan kujera nima nazauna, na kwantoshi
nasoma shafa masa mai Iya tashigo dakin
ganinshi sai ta daure fuska tace lafiya me kuma
yakawoka? Yace Iya gurinki in gaisheki tsaki taja
sannan tafita zuwa kicin Yakalleni Nan gidan
ubanane ba mai hana ni zuwa. Nima na
harareshi ina ruwana Allah yasa nima ina da
gidan uban. Kafin yayi magana sai ga Iya ta shigo
da ruwan zafi takalle ni zo ki karya cikin jego,
kawo shi in sa masa kayan. Nace to, bayan na
karasa sa masa pampers din na mika mata shi.
Ina zama yayi caraf ya mika hannu ya dauke shi
a hannun Iya na kalleshi cikin tsana nazauna
shima yaharareni sannan yazauna yana kallon
yaron, banzaci ya san sunan shiba sai naji ya ce
Iya Sadiq ma dani yake kama sosai yanda ban
tankaba itama bata tankaba. Yarungumeshi tsam
a kirjinshi, sai kurum nafita tsakar gida ina
karyawa. Ashe Iya ma ta shige uwar daka dan
haka yadauki kayan yana sa masa yagama
yamike yafito da shi ganin zai yi waje nabishi da
gudu a ganina zai tafi da shine, ina fadin Iya
zaitafi dashi nasha gabanshi,bani yarona dasauri
Iya tace kyaleshi yatafi dashi din seme? Nasoma
kuka shikuma sai hararata yake yi yaja tsaki
yawuce nace Yaya inka tafi dashi saina tona
asirinka tsam yatsaya sannan yawaiwayo yakalli
Iya itama shi take kallo sannan takalleni na isa
gabanshi namika hannu Bani yarona.Sai yamiko
minshi sannan yafita da sauri naje kan kujera
nazauna ina cika,Iya ta iso gabana wane irin
asirene zaki tona masa?yaken dariya na kakaro
birgace kawai nayi masa babu komai Iya. Tayi yar
dariya haba Sadiya shi mahaukacikane bayan ba
wani sirri jikinsa yayi sanyi haka? In dai da wani
abu kifadamin,Nace ba komai iya tace oho miki in
ma dashi, shiyasa wani lokacin banasan shiga
shirginku.Ni dai sim sim nayi daki.
Hudu da ashirin ina kwashe tuwo naji sallamar
shi ciki ciki na amsa, banyi tsammanin ma zaijiba
na dago nadubeshi cikin tsana, sai naga
hankalinshi yana kan yarona wanda nashimfida a
tabarma akan katifar shi nakwantar dashi akofar
daki Iya tana zaune kusa dashi. Dagudu na aje
tuwon dake hannuna nafito har ina tsallaka iya
nasuri dana nasa a baya naja zanina a igiyar
shanya nagoye shi sannan nakoma kicin ina jin
tsakinshi a raina nace kadai karata can.Daga inda
nake ina jiyo shi yana gaida Iya, dakyar ta amsa.
Yace zantafi zaria dama wani ayki nazoyi Kaduna
akwai wani malami ne da ake zaton kasurgumin
dan fashine to kan shi nake aiki,rahotanni sun
same mu cewa ya koma Zaria acikin satin nan
kafin inzo dan wata na biyu kenan ina nemanshi
tun daga Maiduguri nake biye dashi har zuwa
nan ina son Iya kitaya ni da addu’a Allah
yataimake ni. Iya tace Allah yabada sa’a. Yace
amin. Tace malami kuma dan fashi in banda son
duniya? Ay irinsu suna da yawa Iya kuma yana
siffatuwa ne da malai manyan malamai yana da
ilimin, sai dai shi dan fashine ga tsafi ,sama da
shekaru goma ankasa kamashi,kingako kamashi
nasarace. Iya tace Allah yataimaka yace amin
yaciro kudi gashi Iya. Tace a’a ai na fada maka
bamu da bukatar komai,yasake tausasa murya
Iya wannan fa tsakanin mune ni dake in baki
amsaba sai inga tamkar kin cire ni a tsatsonki,
Ya’ajiye gefenta. Iya kiyafemin natafi.,Bata ce
komaiba kuma bata dauki kudinba yazo bakin
kicin yajeho min wasu mukullai ga mukullin
gidanki nan kije ki dauki motarki aciki. Nadubeshi
fuska daure cikin harara nace bani da gida bare
mota in kana nufin motarka to bana so,tsaki yaja
sannan ya wuce batare daya dauki mukullanba.
Nafito gurin Iya rai a bace nace Iya naga har
kulashifa kikayi kuna hira har yana wani baki kudi
kina karba? Iya tace kin san shi naci zai tayimin
shiyasa narabu da shi ya aje kudin dan yatafi
yabamu guri sannan ina zulumin yanayin aykin
nan nashi wannan malamin kuwa dan fashi
tunkararsa hadarine ina tsoron karya halakashi.
Gadanga shiba mutumbane mai son neman tsarin
kai, da kaikayi koma kan mashekiya,da kai
magana zaice yana addu’a an san dai ita ce
dama kan gaba. Don haka itama Iya ban tanka
mataba wato ma tausayin shi takeji.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Aliyu yayi masauki unguwar Mazan Gudu gidsn
limamin unguwar da sunan cewa shi bakone
matafiyi ne. Hannu 2 aka karbeshi kwanansa 2
yace a nema masa daki na haya yana son yadan
kama sana’a yafada musu cewa rani yake Zuwa
garin Kaduna daga Hadeja yake,Liman har yayi
masa tambaya game da wasu unguwanni a can
Hajejan Allah yasa garuruwan da Aliyu yasani ne
ya kuma fada masa cewa ya sani. Liman yace sun
zauna sun danyi karatu a garin shekarun baya
lokacin suna yawon neman ilimi. Liman yace Aliyu
yazauna ga daki nan a zaure a gidansa na
dansane dake karatun boko a jihar sokoto a
jami’ar shehu dan fodio. Cikin sati daya yasaba
da makota. Akwai wani dan dandali da mazan
unguwar ke zama ko in ce majalisa. Tuni Aliyu ya
saba da yan majalisar in da ake zama ayi ta
labarin wane da wane ko duk wanda yagifta.
Anan yasamu labarin wannan malami daya sauka
gidan sarkin malaman kusfa ance yanda ilimi
sosai kuma yana bada fatawa. Aliyu yace dan
Allah wanda yasan gurin yayimasa rakiya don
yana son daukan karatu. Kullum ‘yan majalisar
nan suna mamakin Aliyu duk irin shigar dayakeyi
ta kaya marasa kyau amma fatar jikinsa bata
nuna cewa daga kyauyen hadeja yakeba kamar
yanda yafadamusu. Akwaima wanda yakecewa
shifa yana wa fuskar Ali kallon sani.
Cikin sati 2 sukayi sabo da Malamin wanda yasaki
jiki da Aliyun amma sai dai Malamin ya fadawa
Aliyu shifa malamine mai yawon yada da’awa
don haka daga nan zai wuce Katsina ne tafi tafi
har Nijar. Aliyu yace in ba damuwa zaibi shi,Aliyu
ya lura da yanda malamin ke daga waya akai-
akai sannan ya lura da irin kudin da malamin ke
rabawa jama’a sadaka. Duk binciken dayayi ya
gano cewa malanin ne wanda yake nema sai dai
dama yana da labarin matsawar malamin yana
cikin daki bazai kamuba. Ana gobe zasu bar garin
kamar yanda suka shirya har da shi Aliyu
shikuma ya daura aniyar kama shine aranar
jajiberen tafiyar. Karfe 2 sun taso daga sallar
Azahar Aliyu hankalinshi tashe burin shi yanzun
idan sun iso kafin su isa gidsn malamin ya sauke
yashige daki. Aliyu yakalli malamin. Allah
yagafarta malam naga jama’ar wannan garin
suna alhinin rabuwa dakai shin bazamu dan kara
kwanakiba? Malam yakalli Aliyu ina da dalilin
barin garinnan asubahin gobe.Aliyu yace Allah
yasa haka shine mafi Alkairi. Malam yace ameen.
Sai dai kai ina mamakin yanda kake son bina ban
cika sakewa da mutaneba amma kai raina ya
kwanta dakai amma daganinka ka taba zaman
cikin birni? Aliy yace e duk cikin gari nayi
rayuwata ban zauna gidaba, Malam yayi
murmushi toh Aliyu sai dai kayi hakuri ina zaton
bazanje dakaiba. Aliyu yace saboda me malam?
Malam ya gyara tsayuwar wato malam Ali an
sanar dani cewa duk inda zan shiga kada in shiga
da mutumin cikin gari domin shine zai zamemin
hadari cikin rayuwata. Aliyu yace Allah gafarta
malam an fada maka kamannin shine munyi
kama? Yace ko kusa an dai ce min zai shiga jikina
sosai kuma zai cutar dani a rana irin ta gobe
shiyasa duk lokacin dazan bar gari nakan barshi
tun asubahi. Aliyu wanda ya kosa yaga isowar
jami’an tsaro yace toh Alagafarta yaya zaka yarda
da irin wannan kila ba gaskiya bane. Malam
yadafa kafadar Aliyu inayimaka fata nagari Allah
yasa zamu hadu wata rana amma wanda yafada
min zancen nan yasha fadamin zantuka suna
tabbata ina ji ajikina zamu sake haduwa da…..
Jiniyar motar ‘Yansanda ce tasa malam bai karasa
zancenba sai Aliyu yaga malam ya daga kafada
yasa gudu cikin azama da kwarewa Aliyu yaciro
bindiga daga bayan wandasa ya harbi malam a
kafa take malam yafadi amma burinshi yakai daki
dan haka ya yunkura Aliyu yayi azama yacafkeshi.
Mutanan gurin sun cika da mamaki harma suka
taso da nufin jin ba’asi sai dai kafin suji dalili tuni
yan sanda sunyi zobe a gurin sun kuma cafke
wasu daga cikin makarraban malamin sannan an
samu muggan makamai cikin kayan malamin da
kudin kasar Amuruka(Dollar) da irin namu na
gida. Mutanan unguwar suna ta al’ajabin lamarin
yayinda wasu ke mamakin Aliyun wanda suka
zata shima yana cikin mukarraban malam. Ta
gidan lima suka bi mai masaukinsa,Aliyu yayi
musu sallama yadauki yan kayan shi tare dayi
masa alheri haka ma yen majalirarsu yatafi yabar
su da labarinshi tare da jinjinawa aykin shi.
Cikin wata hudu da aka damka aykin hannun
Aliyu ya samu nasara ya fara bibiyar malamin
tundaga maiduguri har kawo Kaduna sannan
Zaria inda yayi nasara sakamakon haka ya samu
lambar yabo tare da karin girma zuwa
mataimakin kwamishina na can Abuja haka nan
nasarar taja masa farin jini inda akayi ta haskashi
gidajen talabijin. Ina kallon Iya tunda Aliyu yazo
da batun aykin nan kullum cikin yimasa addu’a
take tare dayawaita sadaka. Araina nace da da
mahaifi sai Allah. Dubi duk haushinsa datakeji be
hanata yimasa addu’ab. Inzanje aiki yanzu gida
nake barin Sadiq sabida yana shan kamu. Iya
tasani gaba tana min fada wata ranar Litinin na
shirya zantapi aiki. Sadiya! Dan Allah shekarunki
nawa? Nace me yafaru Iya? Tace fadamin. Nace
26 Tace dubi duk yanda kika koma ba wani ado
ba kwalliyar da kikeyi ada, ki dage ko dan ki ba
Gadanga haushi,amma kullum sai kina yawo
kamar me takaba,Nace ni banima da kayan
kwalliyar,tace inzaki dawo ki tsaya kasuwa ki saya
in ma baki da kudi in baki,nace ina dashi a cikin
account dina,tace to.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ina zaune bayan na sallami daliban ajina sun fita
break nazabga tagumu ina tunanin zancen Iya
gaskiya ta fadamin bazan tsaya in tsufar da
kainaba tilas in nafita in shiga banki sannan in
shiga kasuwa. Shigowar alert ne ya tsaida
tunanina na dauka na duba kudi ne naira dubu
saba’in sannan yaya ne ya turo min. Haushi da
bakin ciki kamar inyi kuka don haushi. Dakyar
nabari aka tashi na nufi banki na ciri kudin daya
turomin naira dubu 70 na maida masa cikin
account dinsa sannan naciri dubu 20 dan yin
siyayyata acikin account dina. Nashiga cikin
kasuwa nasiyo mai na perpect nasiya duk kayan
shafawa, sannan nasai turaruka na har da kayan
humra dan dakaina nake hada humrata nasai
mayafai da takalma har atamfa na kara. Iya na
gani tace ko kefa. Nanfa nashiga gayuna kafin
wata daya na komo da farina da gayuna, sai dai
ban maida kibata sosaiba, ba wanda zai ganni
yazata ina da yara har 4. Wani abin dariya sai ga
mutane sun soma yin sallama dani.
Ranar wata juma’a ne sunan wata malamar da
muke koyarwa tare nayi kyau cikin leshi mai
ruwan madara ni kaina nasan nayi kyau taku dai
dai nake yi na tsallaka titi zan hau abin hawa sai
mota ta tsaya a gabana na waiwaya zanyi masifa
sainaga yaya Usman ne cikin dariya na isa gurin
shi. Yaya ashe kaine? Yace to na tsaya kafin inyi
magana sai naga za’syi min masifa nayi dariya ka
san mutane wai dasunga mutum ya tsaya sai
suce zasu dauki mutum. Yace hakane sai ina?
Nace nan Askulaye zani suna watace da muke
koyarwa tare ta haihu. Yace muje. Nace a’a
dakaje kada in batamaka lokaci yace hanya tace
ni gaba naci don kurmin mashi zanje. Nace ok.
Nashiga muka hau titi nace ina su Auntyna da su
Ummul? Yace duk suna lfy shine bakya son fita
da Sadiq koh? Nace shima ya saba da Iya baya
son bina. Yace ya huta da shan rana. Nace
wallahi. Naji cewa abokina yasamu karin girma
kwanaki? Nabata rai ina ruwana. Yayi dariya da
ruwanki mana koba dangantaka akwai su Kausar
nace harsu duk na barmasa na yafesu. Yace
bacin raine. Nace wai ya batun binciken? Yace
ina kan binciken kiris yarage in kammala. Murna
ta cikani cikin zakuwa nace kun gano kowane ne?
Yace eh toh na dai yi nasarar gano cewa mutum
dayane a abu uku Sulaiman din daya kawowa
aboki gulma shine malamin makarantarku kuma
shine Sadiya Abubakar mun gano hakan ne ta
hanyar lambar MTN Din dayayi amfani da ita
gurin cike form na account din da ya bude. Nace
a’a duk lamba daya yayi amfani? Yace a’a daban
daban ne sa’ar da muka ci duka na MTN ne
kuma duk yayi musu rijista taimakon dayayi
mana kenan. Nace Alhamdulillah. Muka danyi
shiru nawasu yan dakiku sai Usman yayi gyaran
murya yace, Sadiya! Nadube shi irin kallon
dayayimin yasa gabana faduwa nayi ta maza
nadauke kaina. In tambayeki mana? Nace
eh…ina…jinka. Nafada cikin in ina yace in
abokina yaji gaskiyar batun nasan zaku sasanta
koh? Nakalleshi da sauri nan take raina yabaci na
sunkuyar da kaina yaya Usman dan Allah na roke
ka kadaina yimin zancen yaya nayi rantsuwa
bazanyi kaffara ba,Muka danyi shiru na wani
lokaci,sannna yasake yin ‘yar gyaran murya
“Sadiya nasan kisoma tsayawa da masu sonki
ko?”
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Nadubeshi “banajin zan bata lilacina gurin kula
su,domin al’amarinsu sai su.”
Yayi dan murmushi “karkiyi kudin goro”
Nan nanunamasa layin muka shiga,gabana yana
ta faduwa sabida irin kallon da yaya Usaman
yake yimin. Nace ga gidannan.ya tsaya ya
dubeni.
“Zan dawo in daukeki”
Nace a’a kayi hakuri daga nan zanwuce wata
unguwar,nagode.
Yace “ina zaki!”
Nadubeshi “Gidan kawata”
Yace “Ok! Shikenan, kila zan dawo nanda anjima
inna zaton zamu tattauna wata magama mai
muhummanci
Nace to sai kazo.
Jiki babu karfi nashiga gidan sunan,duk da irin
shewa da wasa da dariya da abokan aikina keyi
ni nakasa ko murmushi.
Malama Bilkisu ta dubeni tace wai Malaman
sadiya kodai baki da lafiyane?nai dan yake kaina
ciwo yake Sukayimin sannu mai jegon har
dacewa ke kam tunda kika haihu shi kenan kika
zama sarkin ciwo. Nace aykam gashi nan na
kasa maida jikina. Adaddape nayi minti 40
agidan nafito na nufi gidan Ayshata sai taganni
kamar an jeho ni ta tashi tare dapadan lfy?
Nace Uhm wata sabuwace tasamu. Tace kuma,
to zauna kisha ruwa kin taki sa’a yau alalar
gwangwani nayi. Naja tsaki ni wallahi yau ko
nama kikayi zalla bana zaton zan iya ci. Tace
meyafaru? Nan na bata lbrn duk yanda mukayi
da yaya Usman itama dai ta damu amma tace
balallai yace yana sonaba wai kila zuciya tace
kawai ta zargi hakan nace toh shikenan. Sai
bayan magariba na yimata sallama ta rako ni na
hau mashin ina hanya naji wayata na ruri, ina
dagawa iya ta rufe ni da fada ina natsaya ga
Sadiq yana ta ihu? Nace gidan Aysha nawuce
gani nan tafe. Ina shiga yaya naci karo dashi zai
fito dashi a kafada yana ta kuka, duk da darene
na raya cewa fuskar shi a daure take ranshi
kuma a bace yake, nashige nazauna a falo ina
ninke mayafina sai gashi. Kin tafi yawon
banzanki kin bar yaro yana ta kuka ko? Ina
kikaje? Naki ko dubanshi nagama ninke
mayafina na mike zan shiga uwar daki yace baki
amshe shiba yana kuka? Iya ta sallame sallah
tace ki daukeshi mana ya jima yana kuka, nace
to. Saida nakai mayafina na ajiye sannan nafito
fuska daure na isa gurinshi namika hannu cikin
harara yabani shi sannan yayi kwafa. Kisani in
zaki tafi yawon banzanki ki daina ajiye min yaro
a gisa yana kuka banda shashanci me zai sa
mace tafita har magriba. Na zaci acikin zuciya
nake magana ashe tafito fili ina ruwana da
kukan shi zan kiyin harkar gabana ne saboda
shi? Sai muryar Yaya naji yace Iyee haka kikace?
Nayi shiru. Tozan dauki yarona in hada shi da
yan uwansa in yaso ke kije kiyi ta gantalinki.
Nazauna nasoma bashi nono ina jijjiga nace
Tabdi Ay wallahu bazan bada dana ba koh
gaban Alkali Za’a,Iya dai tana jin mu bata
tankaba yace basai Alkaliba ahannunki zan
amshe shi kicika baki kigani. Nakalli iya don na
soma fargabar zantukanshi tsaf zai iya,Nace iya
kifada masa yafitga harkata yadaina cemin ina
gantali. Iya tace ki kyaleshi yazo yadauki dan
nasa gantali kuwa ai kin isa yine. Yatausasa
murya Iya kidena dauremata gindi tanamin
rashin kunya. Yakalleni. Zan targadaki in kika yi
wasa. Namike nashige daki shi kuma
yawuce…….Zandakata a nan, acigaba da hakuri
dani.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347

Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100

Darajar Yayana4-03
Posted by ANaM Dorayi on 10:47 PM, 13-Apr-16
Under: DARAJAR ‘YA’YANA
________________NA ___________HALIMA K/MASHI Mama natawasan ruwa a karamin fanfon cikin bandakin,Khausar ta kalleshi cikin fargaba amma bata tashi daga inda takeba,jiratake yafara yimata fada kamar yanda in Mujidat taci Zalinta sanna tayimata karya gurin Abbanta cewa Tayi kaza-tayi kaza, yayi mata fada amma sai taga yamaida kofar ya rufe kuma yamaida mukullin,dan tajiyo kara,sabon kuka tasoma Mama ta juyo tan kallonta. Cikin zafin rai Aliyu Yayi dakin Mujidat,turo kofar dayayi da karfi shiyasa ta tura wayar a karkashin pillow sanna ta mike zubur, ya kalli pillon sannan ya kalleta,rashin gaskiya ya bayyana fuskarta. Sanna tace, “My Dear sannu da zuwa.” Ya dauke kansa daga kallonta sannnan yace, “ina yarana?” Gabanta yabadi sakamakon tinowa datayi ta kullesu a bandaki,cikin inina tace sun..suna falo kokuma dakinsu bari inkirasu,yadan kauce ta wuce shikuma yabi bayanta. Cikin takun isa tashiga cikin dakin sannna tafito tace, “ina yarannan suka shiga?” Nahanasu Khausar yawonnan amma sunki,bari induba gidan maman Markus, Aliyu yace,”kinsan inda suke dan haka nunamin” Tace, “ni bansab inda suka shigabafa a falo na barsu” Yace, “yaya basu tafi da yaronkiba sai sukadai” Tace, “Amma dai kasan Abdul bashi yarda dakowa” Yace, “bansaniba, kin rufemin yara a toilet?” Ta zaro ido “suna Toilet?” Ta nufi bandakin da sassarfa,Aliyu yabi bayanta,ta bude mukullin hannunta na rawa,zunmbur Khausar ta mike hannunta na rawa tana cewa yi hakuri Aunty nadena kar ki dokeni. Tace zonan Khausar me kukeyi a nan? Tadaga Al’amin tana cigaba da cewa, “haba Khausar”…. Aliyu yana tsaye cikin takaici da bakin ciki, domin ko karamin yaro zai fahimci cewA kawo yarantayi ta rufe amma tana nema ta raina masa hankli. Sai da tayiwa yaran wanka tana cewa haba yarana karku kara ba’a wasa a toilet. Saida tagama musu wankan suna fitowa zata fito ya hankada ciki ta koma da baya tafadi,ya maida kofar ya kulle sannan ya zare mukullin yabi yaran zuwa dakinsu, yazauna bakin gado yana kallonsu.kausar ta dakko musu kaya,hawaye ke zuba daga idanunshi, yaranshi duk sun lalace ba wata cikakkiyar tsafta,yaran da mutane ungwa suke labarinsu a makaranta suke amsar kyautuna sabida tsafta dubesu duk sunyi baki, gashin su khausar ya lalace, kayansu duka bakula. A fiili yace, “Sadiya kin tarwatsamu,” yasake kallon yaran yaga suna kallonshi yamike yaje ya hadasu ya rungume yana cewa, “Kuyi hakuri yarana, ba laifina bane laifin mamankune” sunfi minti daya haka sannan ya sakesu yace, “inkaiku gurin wasan yar ko? Skace, “e” Yace, “to,kokuma kuna jin yunwane.” Nanma sukace, “e” Yace, “to bari inyi wank” Yace, “ina sababbin kayan dana siyo muku.” Khausar tace, “suna dakin anty” Yatafi dakin ya hau bincike har ya binciko kayan yazo yasamusu,sannan shima yaje yayi wanka yafito cikin wani yadi mara nauyi me ruwab siminti, sannan takalmin da hular wadanda suka dace, har zai wuce sai yaleka dakinta, har yanzun danta na bacci, yadaga fillon sai ga waya BB ya dakko ya zura a aljihu yafice ya kwashi yaran,yanajinta tana buga kofa tanacewa, “My Dear dan Allah ka budeni.” Yace, “kiji abinda sukaji” Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
yafice yazuba yaranshi a mota suka wuce.
Ranar dai yaran sunji dadi duk da Khausar ta
kasa walwala amma fuskarta a sake alamar taji
dadi, yaymusu siyayya sosai
Basu dawo gidanba sai da yayi sallar isha.
Yasamu Abdul yatashi yayi kashi da fitsari a gado
da kasa, yaje ya budeta tayi kuka ta gaji dan tana
jiyo kukan danta badamar ta je gunsa,
tasakarmasa harara sannan taja tsaki ta wuce,
dariya yayi don turamata haushi.yana ta re da
yaransa har sukai bacci sanna yaciri wayar
yasoma binciki amma hakan ya faskara saboda
security datsa, yamike yatafi dakinta yatara da ita
tana waya da karamar wayar da kullum yake
tsammanin ita kadai ke gareta ya tatsuramata ido
dan son fahimtar da wa take wayar amma sai
tayi sallma tare sa cewa, “momyi sai anjima.”
Ya dago ya nuna mata wayarta dake hannunsa
yace, “wannan wayar waye?”
Tace, “tawace” cikin gadara yace, “ina kika samu
kudin siyan wannan wayar dubu sittin?”
Gabanta ya fadi amma sai ta dake tace, “ni ba
haka na siyaba second hand na siya.”
Yace, “gurin wa kika siya?”
Tace, “gurin kawata.”
“Wacece kawar taki?”
Tace, “Azima”
Nawa kika siya?
Tace, “dubu ashirin”
Yace, “a ina kika samu kudin?”
Cikin kosawa tare da daga murya tace, “Auncle
yabani,
Wai sata nayi da kasani a gaba da wadannan
tanbayoyin?”
Ya mika mata, “ciremin scurity”
Ta amsa ta cire tana kokarin shiga wasu guraren
ta goge wasu abubuwan ya fisge wayar yafita, ta
biyoshi tana cewa ni kabani wayata ba kai
kaseminba,
Afalo yazauna sanna ya kalleta kallon zargi, “karki
karso min nan, inbadan kinsan baki da gaskiyaba
menen dan mijinki yadauki wayarki?”
Tace, “nadamune dan zaka duba wayata meye a
ciki?
Kayi ta dubawa nidai nace kabani a buna tinda
bakaine kaseminba”
Baisake tankamataba, yayi iya bincikensa baiga
wani abu ba amma cikin inbox dinta na message
yaga wani sako da yadauki hankalinsa cewa
akayi,
“Malama ki aikomin da cikon kudin aikina inba
hakaba zanyi miki rashin mutunc daga Jamilu.”
Yaduba ranar da aka turo sakon ya lissafa kwana
tara kenan,ya tura sakon zuwa wayarshi sannan
ya aje wayar a hannun kujera tazo ta dauka ta
wuce. sam bata tinanin wannan sakon
damuwarta karyashiga group dinsu yaga abinda
sukeyi,dan in hirar da sukeyi da mazane tasan
bazai ganiba tinda tana gogewa shikuma bai
tsaya wani shiga group ba.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Sunfi kwana uku suna gaba,tafita lamarinshi da
yayanshi,shinma yafita shirginta,sai hidimarsa
yake da yaransa.Nazari tayi taga suke
cutuwa,don haka ta sauke girmankai tare da
samunshi a dakinshi tsakar dare inda tabashi
hakuri,tare da yimasa alkawarin bazata karaba.
Cikin kwanakin da suka biyo baya tana kokarin
dannar zuciyarta dan ta kyutatawa yaran,sabida
ubansu ya yarda ta canja,saidai yaran sunki sakin
jiki da ita, data lura yasaki jikin sai takoma
halinta,yanzu bata rufesu a bandaki saidai duka
kamar jakuna, dan kuskure kadan na yaro sai
takama tayita duka.
Cikin haka wata ranara litinin su Khausar sun
dawo daga makaranta dauke da yunwa,sunfi
minti talatin sannan ta tashi daga chatting din
tabasu abinci,wanda ko Al’amin sai yacinye.
Kausar tace, “Anti Wannan fa bazai ishemuba,”
Ta watso mata wata harara ta nufi dakinta tana
cewa, “Dama ni nace ku koshine?”
Khausar ta Mika musu tace, “kuci,” sun cinye
Amma basu koshiba, Don haka khausar tace
kibari in ta dan dade zanje in debo muku nima in
debo nawa,Don ka dayushe dama idan basu
koshiba takan dan lababa ta debomusu.
Kamar kullum ta taka kujera tana cikin zubawa
sai taji kamar motsin Auntynsu ashe
Mamace,tana kokarin sakkowa kujerara ta gurde,
Kausar ta fado, shi kuma plate din yayi sama sai
yafada kan wasu plates din ‘yan uwanshi na
tangaran,nanfa kakejin tartsatsi yana tashi,da
gudu Mujidat ta fito.
Khausar ta mike jiki na bari tsoma cewa , “Anty yi
hakuri tana kka.”
Mujidat tace, “ok! Allah yakamaki dama kece me
satar abinci kullum inna tanbaya kice bakebace
ko?”
Cikin rawar muraya khausar tace, “zasu karane,ni
ko cima banyiba.”
Tace, “Ina ruwana,dole inzaneku yau, kizo ki
gyaramin kitchen bari innemo wayar wuta.”
Ai tana juyawa khausar tafita da gudu inda tadau
takalmansu suka gudu,Mujidat tafito bata
gansuba,tace “oh! Kunguduko?zaku dawone.”
Duk da cewa barikin ‘yan sanda da tsaro amma
sai Allah yakauda idon kowa basu gansuba har
suka fice.
Al’amen yace, “yaya Khausar ina zamuje? Ko
mutafi Office grin Baba?”
Khausar tace, “inmunje zai dawo damune ko Yayi
mata fada,in Yayi tafiyrs Sai ta dakemu,”
Al’amin yace, “emana , kawai mu tafi gurin
Momy.”
Khausar tace, “zamu iyane? Kadunafa?”
Mama tace, “nima zanje Momy kinji Yaya
Khausar”
Khausar tace, “to mama zaki iya Zuwa a kasa?”
Mama tace e
Almen yace, “in tagaji sai ki goyata”
Khausar tace, “muje to kila mugane.’
Sunyi ta zagaye cikin garin Abuja har duhun
Magriba yasoma shigowa,inda suka Isa kusa da
wani Store na saida kayan shaye shaye na
zamani, suna son su sha ruwa, ga yunwa,in
mama tayi kuka sai Khausar tace, “yi shiru mun
kusa”
Khausar ta Isa gurin wani mutumi dake tsaye
yana shan kankanar gwangwani, tace, “Baba dan
Allah kasammana ruwa.”
Yakalleta ya kalli su Mama yace, “kai inazaku?”
Khausar tace, “Kaduna”
Yace, “Inna zuwa”
Yaje yafito da ruwan gora yabasu suka sha
sannan yakirasu gefe yanayimusu tanbayoyi har
mutane suka taru,nanfa akayi ta shawarwari
wasu suna Cewa akaisu makaranarsu inyaso su
can sai su kira iyayensu,tunda ansan
makarantar,jin haka yasa Khausar tashiga kuka
tana cewa, “Kutaimakamana wallahi antynmu
zata kashemu,kukaimu kadna gurin Momynmu.”
Suma su Al’amin kuka sukeyi dan haka sai
sukace, “tinda shi wanna daya saimusu ruwa
direban motane sai yatafi dasu Kadunan indai
sunsan unguwarsu.” Dayake daga gurin babu nisa
zuwa tasha dan haka sai suka tafi..
Mujidat bata tina da cewa yarannan basa gidanba
saida Aliyu yakirata a waya yace ta shirya
yarannan zaizo yakaisu Islamiyyar dayayi musu
register,firgigit ta mike tana cewa ai saita dokesu
babu fashi.saidai me?tayi Neman duniya cikin
gidan da makota basanan,nanfa hankalinta ya
tashi,makota suka firfito,kafin wani lokaci
ankarade rukuninsu da neman yaran,amma babu
wanda yagansu, saidai masu cewa tabbas
sungansu da takalman makaranta a
hannusu,wasu kuma suce da kayan makaranta.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Mujidat taci kuka ta koshi,gashi ta kasa kiran
babansu dan tsoro.makotansu kuwa da suka San
abin da takeyi wa yaran cewa suke Allah yakara,
saidai munafukn dake bin bayanta ne ke tayata
damuwa.
Yana shirin zuwa don kaisu sabuwar islamiyyar
da yasasu saiga wayar makocins wai bafa aga
‘ya’yansaba, cikin tashin hankali yanufo gidan.Sai
yasamu gida dankam da mutne,ya kalli Mujidat
“Ina Yayana?”
Tace, “bangasuba sunyi barnane a kitchen suka
gudu.”
Baice kalaba ya nufi gidan,sannan yafito yakira
“yansanda suzo gidan shi,sanna yace kowa yatafi
yagode.
Kafin wani lokaci “Yansanda sun karaso nan yasa
sukama Mujidat sai ta fadi inda takaimasa yara.
Cikin dare ‘yansanda sai faman neman yara suke,
duk inda yakamat asanar an sanar, hanklin Aliyu
yatashi Karshe.karshe yakira Usman yafada
masa,amma yace yabar zancen a tsakaninsu dan
bayason su Iya suji,Usman yace Allah ya
bayyanasu.
Abu kamar wasa har cikindare babu labarin
yaran. Daidai wanna lokacin suna can akan
hanya,inda direban yasasu a bayan Mota yakashe
kujer daya kusa da wata mata inda yace “Don
Allah ta lurar masa dasu,” duk da tsare motocin
da ‘yansanda sukeyi suna haskawa sam babu
wanda yagano yaran,shiko direban bemasan
yaran ake nemaba balle yayi wani bayani.
Sunyi isowar dare,don haka yagama da fasinger
yanufi gidansa da yaran,wadanda harsunyi bacci,
matarsa tanada fahimta,baisha wahalaba wajen
fahimtar da itaba, nan yaran suka kwana.
Washgri akayi Tayi musu tanbayar Sunan unguwar
ta momynsu Amma suka kasa tunawa,gidan me
unguwarsu ba nisa,don haka sai yaje dasu
gurinsa,suma dai sunyi iya tanbayoyinsu
ba’aganeba,Sai matar me ungwar tabasu
shawara suje gidan TV da yaran,aikuwa basuyi
kasa agwiwaba suka nufi gidan DITV inda ake
gabatar da wani shiri na gari ya waye.
Daidai wanna lokcin inna zaune agaban TV inna
kallon shirin domin dama baya wuceni,innayi
innashan Tea. Iyama na son shirin sosai,don haka
tana ta kokari tafito daga kitchen ta iso.Kamar
daga sama sai akace ga wasu bayinAllah suna
bada Cigiyar iyayen wadannan Yara, mai
sanarwar yafada, ganin an hasko fuskar Khausar
cikin daga Murya nace Iya Iya zo kigani,da
tuntube tafita tana fadin lafiya? Itama nan
tazauna dabar.daidai lokacin ana tanbayrsu
sunayensu suka fada,dan Jaridar ya haska
Khausar
“Yarina yakikace Sunan ki?”
Tace, “Khausar Aliyu Tukur Hadeja”
“Daga ina?”
“Abuja”
“Ina Zaku?”
“Kaduna gurin momynmu”
“To can Abujan gurin wa kuke?”
“Gurin antynmu”
“Ina bbanku?”
“Yana gurin aiki.”
“Me akayi muku zaku dawo gurin momynku?”
“Dukanmu Auntynmu keyi,kuma bata bamu
abinci muna kosh,jiyama naje zankaro aboye
batasaniba,zan krawa su Momy dama ni banciba
duka nabarmusu,shine nafadi,dataji karar
fashewar abu tafito,shine taje dakko wayar wuta
sai muka fito Muka kwashi takalmanmu Muka
gudu.”
Yace, “to kinsa unguwar da momynku take?”
“Da nasani yanzu namanta.”
“To yasunan mamanku?”
“Sadiya”
“Babankufa?”
“Aliyu Tukur Hadeja”
“Meye sana’arsa?”
Tace, “dansadane”
Nantake dan jaridar yace badai Aliyu Tukur din
danasaniba,in shine kuwa ai sanannene,yataba
rike kakakin rindinar yansanda alokacin yana ASP.
Mai unguwa yace shekarun baya ko.
Ai tini na jike shrkaf da gumi da hawaye har da
majina, yaranane wadannna ? Sai ga Habu
yashigo da sauri yace Aunty Ku kunna TV,Sai
yasamemu cikin kuka,yace iya kutaso muje gidan
me unguwa,na dauki lanbar wayar dayabayar,
gidan sa kuma hayine layin yandinki,dakyar
namike wayata tana ta ringi amma nakasa
dagata,nasan kawyenane dasukaga yaran,tin
kafin mutafi mkota dai shigowa suke suna mana
jaje gami da barka da arziki.
Munshiga gidan,sashin matar me unguwar, Mama
tana wasa,khausar da Al’amin suna ta zantuka
kasakasa,mukayi sallama yaran suka dubemu, da
karfi kausar tace Momy! Se rige rigen tahowa
gurina,na hadasu su ukun na rungumesu
jikina,inna kuka suma suna kka, duk mtanen
gurin suma kuka suke.nadauki Mama inna
kallonta,nadubi Iya cikin kunci
Nace, “dubi yarana yanda suka llce,”
Iya tace, “su da Allah sun cuci Kansu,menene
riba don ka cuci karamin yaro?” Nandai akayi abin
dayakamata muka dauki yara muka nufi gida.
Gidan cike da makota Sai barka da arziki
akeyimana,Allah yasa sunfada hannu nagari.har
lanbar direban na karba dan yimasa godiya ta
musamman sabida taimakon dayayimana.
Tini Habu yafesawa Yaya cewa abga su Khausar
anan Kaduna.Habu yabashi labarin komai,shi
kansa yasan tinda yarannna sukazo gurin iya dole
ya hakura dasu,amma yaji dadin ganinsu.yanufi
office dinsu yasa asaki Mujidat,ta fito tayi wujiga
wijiga, yace to bafa gidanshiba sai ta nemi gurin
zuwa,tace ina Abdul? Yace ai ba yaronkibane
yaronane na amshi dana.
Tace, “kana zaton dan ka boyemin Yaro zanki inje
infadawa iyayenka? ai dole su Sani.”
Yace, “kekisani,saidai kisani zakikoma Kadunane
bayan kinkoma gidan Ubanki Lagos.”
Aikuwa yasa aka kaita har garin da ‘yan
kayanta,ko gani Abdul din ya hana tayi,yakaishi
gidan wani abokinsa a Asokoro.Mujidat ta
jinjinawa wulakancin da Aliyu Yayi mata,Amma
tace indai itace yaci Bashi,sannna tinda be
saketaba da sauki.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ya nufo kaduna cikin fargaba. Nikam na tsefe kan
yarana na wanne,akaje akayi musu kitso nayi
musu lalle. Munsha labarin irin wuyar da suka
sha a baki Khausar ni da iya, aikuwa munsha
kuka sabida tausayinsu.
Karfe uku ina zaune da ‘Ya’yana cikin farinciki
inna yanke musu farce,Mama nakeyiwa magama
yiwa sauran.Khausar na dauke da Sadiq
tanayimasa wasa tace “Momy Sadiq dinki wallahi
dariya Yake yimin damun hada ido ya sannine?”
Nace, “kullum sainabashi labarinku, yasanku
dukkanku….”Sallamar yayace ya katsemu,sainaga
Khausar ta mike da gudu ta nufi daki Al’amin ma
yabita,Mamace kawai naga ta nufi Yaya tanamai
Oyoyo oyoyo,na hade raina tamkar zan saki
kuka,sanna na kauda kai nadauki wayata inna
latsawa. Yanufi cikin daki gurin iya, su Khausar
duk sun makale a bayanta tana Cewa, “lafiya
kuke boyewa?” Sai kuwa Yaya Yayi sallama,tsaki
Iya taja takasa amsa sallamar, yazauna tare da
sunkuyar dakai yace, “ina yini”
Ta kauda kai tace, “lafiya,”
Yace, “nazone inbada hakuri kan laifin danasan
za’a gani nawa,duk dacewa bansan fitarsuna
tinda ni bama na gida,laifin Mujidat ne kuma
nayi mata hukunci.”
Iya tace, “can da matsalarku, sai dai abinda
zanfadamaka yarannan sunzo kenan,kuma abin
da kukayi musu Ku da Allahnku,”
Aliyu yace, “Dama ni bawai zan Koma dasubane.”
Iya tace, “ai nazaci takardara sammaci kazo
kawomana.” Ya mike yasake fadin aymin afuwa.
Ya dubi Khausar, “bazaku gaisheniba?”
Tace, “ina wuni Abba,”
Almin kuwa cewa Yayi, “mudai bazamu bikaba,”
Yace dama badaku zan tafiba.
Ya iso gurin su Khausar ya dauki Sadiq yafita.
Bai zaci zai samu sauki a guri Iyaba,yasandai
damuwar dama kar yakuma daukan yaran, kuma
dama ya yanke hukuncin barinsu fishintama na
yaune.
Yakira Usaman a waya suka gaisa samasama yace
,”Aboki kana gidane in iso ? Yunwa nake ji,gidan
su Iya kuma babu fuska.”
Usaman yayi ‘yar Dariya sannnan yace, “ka isa
gidan zan sameka a can.”
Aliyu yace, “kayi nisane?”
“Inna Office din ‘yansanda na nan unguwar.”
Aliyu yace, “lafiya me kake a gurin?”
Usam yace, “wani dan case ne.”
Aliyu yace, “shine bazaka sanar daniba, bari
inzo.”
Ciki yakoma yamaida Sadiq, a cinyata ya ajiyeshi
ya fita,yana Isa office yansanda suka soma
kamewa suna sara masa, Oga yana ciki.
Agaban DPO yasmu yaron tare da Usama, DPO
ya mike ya kame sannan suka gaisa. Aliyu ya kalli
Usman, “Yaya, me yafaru aboki,”
Usaman yace, “irin yarannanne masu bude
account da Sunan mutane su kullamusu sharri.”
Aliyu yace, “to shi wa yayi?”
Usma yace, “shine yayiwa Sadiya,”
Aliyu yace cikin sauri, “wace Sadiya,”
Usman yace,”wadda nake neman aurenta.”
Kan Aliyu ya kulle yace, “dama zakayi aure?”
Yace, “Eh,bamuyi zancen dakaiba ko?”
Ya kalli yaron, “kasan Wannan?”Yanuna masa
Aliyu, yaron yace, “a’a,”
Daga nan Usman ya kalli DPO; “yanzu ni zan tafi “
Aliyu ya zauna, “bangane zaka tafiba, wai yaya
case din yafaru?”Nan aka umarci Jamilu yayi
bayani kamar yanda Yayi dazu.
Jamilu yace, “nidai wani yarone kanin Aunty
Ramatu ya kirani inzo zanyiwa wata Auntynsu
wani aiki,dama yana zuwa Cafe dinmu yana
Browsing, danazo sai tace inbudemata wasu
account guda biyu,zata yiwa kishiyarta sharri,
kawai Sai na yarda sabida ta yarda zata bani
Dubu5,nikuma dama inna neman dubu 5 din
sabida zanse JAMB Form dan shiga Jami’a.shine
nayi mata har yau kuma bata cikamin dubu
biyunba,sunma tashi daga garin.”
Aliyu ya dinga kallon Jamilu tamkar yanason Yayi
tajin labarin kokuma labarin ya burgeshi. Usman
yace Jamilu sakamakon wanna hada Chat din
danayi nafada maka kasan aure yarabu? karaba
uwa da ‘Ya’yanta? yanuna Aliyu Kaga mijinsu
nan,wadda kayiwa sharrin da wadda tasaka kayi
aikin.”
Mamaki Yakama DOP yace, “Dama abin yafaru ne
a gidan Oga?”
Aliyu dai hannu a cikin aljihunsa yarasa me zaice,
Jamilu kuwa zubewa Yayi gban Aliyu yana
rokonshi cewa a yafemasa, shi dama wannanne
karo na farko da yasoma kuma bazai karba.Aliyu
yamike yakalli Jamilu, “Ayimaka hukunci daidai da
lefinka sabida masu hali irin naka.” Har waje DPO
ya rako Aliyu, sam Yakasa magana sai zufa
yakeyi, zuciyarshi nata fadin kayi wauta.
Suna tafe shi da Usman shiru babu mai magana
saidai shi Usman ranshi Fes yaji dadi komai
yafaru a agaban Aliyu.
Koda sukaje gidan Usman din Aliyu Yakasa yin
tinanin komai,yamaji cewa yakoshi,duk da irin
yunwar dayakeji, idanunshi sunyi jazir.
Usman yace,”Aboki bisimillah”
Aliyu yace,”haba aboki, yakake tinanin zan iya cin
wani Abu a halin danake ciki? Don Allah kaima ka
ajiye muyi magana.”
Usman Yayi murmushi, sannan yasake cika
cokalinshi ya tura baki yace, “wace magana
zamuyi.”
“Ta Sadiya mana , gaskiya nayi wauta danaki
natsaya nayi bincike,kuma saida tace inbincika.”
Abida dake jiyosu batasan sanda dariya ta
subucemataba, saidai taji Aliyu yana cewa “au!
dariyama nabaki Madam?”
Abida tace, “yanda kake maganar ne yabani
dariya.”
Usman yace, “ai abin dariyarne,ni yanzu bazan
saka bakinaba cikin wannan lamarin, Sadiya
Alkawari nayimata zanyi bincike ingano masu
hannu cikin wannan lamarin kuma Allah ya
taimaka nasara tasamu,daga nanma sai can gidan
sabida insanar da ita,saikuma mudora daga inda
muka tsaya kan maganar auranmu.”
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Aliyu yakalli Usman cikin tsananin bacin rai
yace,”kai nalurafa ba kasan kawaiciba ko?”
Usman yace, “kamar yaya?”
Aliyu yace, “wallahi dan kaine kunnuwana suka
jure jin kanacewa zaka auri Sadiya.”
Yamike tsaye,”Wato damacan kanason matata tin
muna aure ko?”
Usman yace, “sam karkayi wannan tinanin,
hasalima ka manta kaine kabani shawara in
aureta lokacin danake lallabaka kamaida ita? Kace
ai bai haramtaba inna aureta, katuna? Shine
kawai mukayi shawara da Abinda,kuma
Alhamdulillah zance yasoma bisa….”
Aliyu ya harari Usman, sannan yaja tsaki yanufi
waje yanacewa, “Kadakatar da Neman aurenka.”
Usman yace, “Sabida me?”
Aliyu wanda yakai bakin kofa, “najanye shawarar
dakace nabaka,inkuma kaki ji kada ka zargeni
akan abin dazaibiyo baya.”
Usman yace ,” aboki kazo muyi magana a zaune”
Tsaki Aliyu yayi tare da bugamusu kofa yayi
waje,ranshifa yayi zafi.,dama Habu yagayamishi
Usman ke zuwa gurinta duk kwana uku,saidai
sam bai tsammaci yanazuwa don sontabane.
Yashigo gidanmu inna shirin fita zuwa Isalamiyyar
‘ya’yana tada domin inmaidasu, yanda naganshi
yashigo a sukwane nadan tsorata.yace, “ina iya?”
Nayi masa banza,yashiga daki tare da cewa, “zo
Sadiya!” Yayi maganarne cikin taushin murya.
Nashiga.
Yace, “Sadiya don Allah kinyafemin nayi
kuskure,ashe Mujidat ce duk ta kullamiki Wannan
Sharrin?”
Iya dake cikin daka tace, ” Usman yakira waya
yayimana bayani yanzunnan,binciken da kakasayi
shi yayi kuma Allah yatoni asirinsu.”
Aliyu yace,”Usman ai ba don Allah yayiba,yayine
don manufar kanshi,kuma wallahi Usman inbai
kiyayeniba za’ayi danyen aiki”.”
Iya tace, “kai Gadanga da girmanaka kakeyin
wannan zancen,duk taimakon dayayi baka
ganiba?”
Aliyu yace, ” Bansaniba”. Yanunani.
“Kekuma zanfadamiki wallahi bake bashi.”
Namike, “baruwanka da rayuwa ta don ni yafimin
kai.”
Iya tace, “sau dubuma,kuma wallahi innaji wani
abu tsakaninka dashi Sai ranka yabaci,tsakaninka
dashi sai godiya.”
Yace , “Iya matata fa yakeso,banda cin amana
yazaice yanason Sadiya?”
Nace, “Ok! Sabida bakasona shikenan kar kowa
yasoni ko?inkaga ban auri Usaman ba saidai
inbansoba kokuma shi yafasa…..”
Ban ankaraba sainaga yatasomin zai
dokeni,nagudu nayi bayan iya innacewa, “Wayyo
Iya zai dokeni”
Yatsaya yana huci, “ni kike gayawa zaki auri
Usman?”
Iya tace , ” tafada , hauka kake kadoketa?”
Yace, ” inna tacigaba da yimin irin wanna zancen
bashakka zan jimata ciwo,kuma Usman zaisha
mamakin abin da zanyi masa.”
Nace, “karkaga wani kana dansanda,inkatabashi
baza’a barka ba.”
Yace, “kimin shiru,karkibari inzonan wallahi zan
ballaki.” Yajuya fuuu! Yafice rai a bace.
Nasauke ajiyar zuciya,nace, “wallahi natsorata
ban manta da irin fishinnan ba,irinshi yayi lokacin
da akayimin wannan sharrin,jikinshi har rawa
yakeyi, Allah yatemakeni badan keba da yau naci
duka.”
Iya tace, “tinanina yanzu Usman,ko kiranshi zakiyi
yanzu kicemasa inna nemansa?”
Nace , “to , bari inkirashi.”
Tace “kishin banza ne ke cinsa a rai.
Nace , ” Dama yabar Usman,danni ba auranshi
zanyi ba, na fadamasa hakane don kawai yaji
haushi.shima Usman din ina zaton dan yaturawa
Yaya Haushine yace yana sona.”
Iya tace, “banda matar shi dake tsakanin ai
Usman mijine.”
Daidai lokacin kiran yashiga, yadaga ,nace,”Yaya
Usman wai kazo inji Iya”
“Lafiya?” Cikin daga murya.
Nace “lafiya,kodai ba kalau ba.”
“Ko Abokinane?”
Nace, “eh, ai yacene wai kace kana sona,a ina
yaji?”
Nina fadamasa,Kice iya karta damu, ni dashi
babu a binda zaifaru,nasan dama dole yayi
haka,ni dama hakan nakeso.”
Nace, “to shikenan,sai anjima” nakalli iya bayan
nakashe wayar nace, “yace babu abinda za’a
faru.” Nandai mukayi ta tattauna zancen.
Shikam yaya police yakoma yasake bincika Jamilu
ya tabbatar da gaskiyar lamari,sannana yawuce
Zuwa Abuja cikin damuwa. A daki ya kulle kan shi
yana tinanin tsantsar rashin kyautawar da yayiwa
Sadiya,baimasan ya zaiyiba.ya daga waya yakira
layin Usman har takatse yana kallo bai dagaba,a
karo na biyu ma saida takusa katsewa sannna ya
daga.
Aliyu yace, “Usama nakirakane ince kafita harkar
matata,zan dawo da Ita dakinta.”
Usman yace, ” innaki fa?kawai Mallam ka shiga
layi zawarawa nima inna ciki mai rabo
Yasamu,kuma banda abunka wannan baikamata
yashafi zumuncinmuba.”
Aliyu yazo iya wuya,ranshi yakai matuka gurin
baci,yace, “ok! Haka kace? To shikenan kajira a
abin dazai faru.” Yakashe wayar yanata kai kawo
a dakin,zuciyarshi tagama sakamasa abinda
zaiyi,kawai zuwa zaiyi yasa akama Usman, baza’a
fito dashiba har Sai anmaida auranshi da
Sadiya,inyaso saiyaga da wanda zaija.
Mujidat tasauka a garin kaduna kai tsaye
unguwar Mu’azu ta dosa,muna tsaka da cin
abinci kwanonmu daya da Yayana,tire ne dan
babba nazubamana,Danwake mukayi munaci
muna hira,Iya kuma tana gefe tanacin sauran
Tuwon Masara da Miyar Kuka.
Kwatsam sai mukaji sallama,zunbur namike ganin
Mujidat nace, “me kikazo yi gidanmu?”
Tace, “Ba gurinki nazoba,gurin sirikata nazo.”
Iya tamike itama,”karki shigomin gida,juya.”
Su Khausar kuwa tini sun ruga daki sun rufo
kofa,nace ,” azzaluma kinje kin cutarmin da yara
duk da irin taimakon Dana yimiki.”
Mujidat ta sheke da dariya sannan tace, “kikadai
taimaki mijinki,yanzu kuwa nazo na kwance kullin
da kukayi ke da mijinki.”
Nace, “Ina ruwana,yanzu mijinkine ba
nawaba,inkinso ki tona,inkinso ki rufa.”
Iya kawai ta tsaya tana kallonmu tare da sonjin
asirin da ake cewa za’a tona.”
Mujidat ta kalli Iya tace, ” Tsohuwar ba zama
nazo ba, nazone in fadamiki gaskiya tsakanina da
danki.”
Gabana yashiga faduwa,tamkar in tashi in toshe
bakinta kar ta sanar da Iya taji bacin rai,banason
‘ya’yana suji abin da ubansu yayi.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Mujidat tace, “Danki Aliyu ciki yayimin tin a
Ilori,yace inna yarda dashi zai aureni.Yayi min ciki
ya taho, nikuma na biyoshi,shine sukace inyi
shiru kar ince haka zasuce mijinane ya mutu
yabanni da ciki,kisani Abdul jikankine.”
Na kalli Iya wadda takasa magana, na iso gurin ta
na kamata nace, “Iya zauna karki damu.”
Iya ta fincike hannuwanta tace,”Sakar min
hannu.”
Ta nuna mujidat “fita tinda kinfadi sakonki.”
Mujidat tace,”Yanzu kuwa zan tafi burina yacika
tinda kinsani.”
Nace , “To me yadame mu? Saiki fita ai ko?”
Ta saka dariya, kidena min korar kare,domin ko
bana auren yayanki uban ‘Ya’yanki inna da yaro
daku.”
Nace, “naji jeki.”
Kafin insake magana Iya ta isa bango ta dafa,na
isa gurin ta,sannan nadauki wayarta na kira Yaya
Usman , nacemasa, “dan Allah kazo in kana
kusa,Mujidat tazo ta dagawa iya hankali.”
A zaton ta Yaya Aliyu nakira,don haka saitafice da
sauri.Allah yasa Yaya Usman yana kusa ya iso
mukayi ta bata baki. Tace, ” Ashe dake za’a hada
baki a rufeni?”
Nace, ” Iya kiyi hakuri, alokacin ko anfadamiki
babu abinda hakan zai kareki dashi sai bacin rai.”
Usman yace, ” Iya lokacin abin da zaifaru yariga
yafaru.”
Sai ga hawaye yasoma zuba daga idanunta, tace,
“Wato shi Aliyu ko yaushe shi zaidinga sani zubar
da hawaye “
Usman yace , “sai hakuri iya”
“Nagaji da hakuri da laifukan da Yake
aikatamin,ya batawa zuri’a ta suna,ya
gurbatamin zuru’a yabani mamaki.”
Kukana ya tsananta,nace, “Iya kiyafemasa.”
Tace,”kema ai a gurina me laifice balleshi,kike
cemin inyafemasa.”
Usman yaciro wayarsa yakira laying Aliyu, lokacin
yagama shirya yanda zaisa a kama masa Usman
din domin bazai yuwu a kamoshi batare da wani
laifiba,dolene a nemi laifin da za’a
joganamasa,kamar kada yadaga layin, saikuma
yadaga cikin isa yace.
“Malam Lafiya?”
Usam yace, “kana inane yanzun?”
Cikin jin haushi yace, “menene kake son jin inda
nake? Innaso fa ka manta kasan ni.”
Yace, “kafin in manta nasanka din kazo ga
matarka nan tazo ta kunce kullun da Kuke ta
boyonsa yanzu haka Asibiti zamu kai Iya.”
Tace, “daina kiransa Usman, na yafeshi cikin
Yayana,ya nemi wata uwar shi ba zuri’a ta
bane…” Ta fashe da wani kuka mai ban tausayi.
Aliyu duk yaji wadannan kalaman dama wasu,don
Usman sam ya manta bai kashe wayar ba,sabida
wata irin sheshsheka da Iya tasoma.
Yace, “Sadiya dakko mayafinki da nata muje
Asibiti.”
Ta dakko,suka kama iya zuwa Mota.
Sai da Sadiya tace zamu bar yaranne ? Sai yaciro
wayar tare dacewa, “bari inkira Abida tazo ta
kwashesu,” a lokacinne yaga bai kasheba don
haka sai yakashe,sannna yasake kiran Abida.
Aliyu yanata kai kawo cikin ofishinsa gumi yajika
rigarsa sharkaf,ya balle duk botiran gaban
rigarsa, ana kallon singiletinsa,Sam bazakace da
Akwai AC a cikiba.
Kiran wayane yasashi isa gurin
wayar,kawimishinane ke nemansa wai zasuyi
wani dan meeting, a isa ofishin yana balle botiran
gaban rigarsa,sai kwamishinan yabukaci daya
zauna.
Bayan ya zauna be suka gaisa da sauran
mutanen daya gani ciki,fuskarsu ba boyayyabace
‘yan siyasane na gwamnati me ci a wannna
lokacin,wasu masu neman tazarce wasu kuma
masu son sababbin mukamai.Aliyu fa ya hade rai
sabida ya lura ‘yan siyasan nanfa sun raina
jami’an tsaro.
Wanda suka wakilta yayi magana shine ya
gabatar da kudirinsu na Neman goyon baya daga
jami’an tsaro,su zama suna bangarensu.
Kwamishina ya kalli Aliyu tare da bashi izinin
magana.
Aliyu cikin isa yace, “Ranka ya dade mu ba ‘yan
siyasa bane,bazaiyuwu mu cusa kanmu cikin
harkar siyasaba,mu jami’an tsarone dole yazama
muna tare da kowa ku da ‘yan adawarku,bai
kamata gwamnati maici dan kawai tana ganin
tanada madafan ikon a hannunta tayi anfani da
hakan gurin tursasamuba,mun San aikinmu,kuma
inshaAllahu in zabe yazo zamu tsay kai da fata
ayi zabe a gama lafiya…….zandakata anan
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347

Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100

Darajar Yayana4-04
Posted by ANaM Dorayi on 07:27 PM, 16-Apr-16
Under: DARAJAR ‘YA’YANA
________________NA ___________HALIMA K/MASHI Wakilin siyasa yace, ” amma mu muke daku tinda muke da gwamnati.” Ya kalli kwamishina. “Ranka ya dade kai yakamata kace wani abu,sabida wannan mataimakin naka ya nuna karara baya tare damu.” Yace,”zantukanshi suna kan hanaya,sai dai zamuga taimakon da zamuyi muku.” Sai suka mike tsaye suna zantuka,wani harda Cewa, ” kujerarku tana rawa,domin kunsan akwai nasama daku,kuma su namune inkunce Ku ba namu bane.” Aliyu ya lumshe Ido,baiyi wani mamakiba domin yasan su basu da wani buri sai son kansu,amma indai yana nan da yardar Allah sai ya hana ruwansu gudu,zai dawo da martabar ‘yan sanda. Bayan tafiyarsu kwamishina ya kalli Aliyu yace, “kamin dai-dai,shiyasa nakiraka.” Gida Aliyu yanufa,sintiri yakeyi tare da kai kawo daga falo zuwa dakinshi,yarasa ta ina zaibi kuma wa zaikira yabashi shawara? Yazauna yaciro wayarshi yanabin lanbobin daya bayan daya yanason yaga wa yakamata ya canja abokin shawara madadin Usman. Yaduba har karshe baisamuba,wata zuciyar tace dole dai Usman ne zaibaka shawarar data dace. Tsaki yaja,sannan yabi shawarar zuciyarsa yasoma kiran layin Usman,duk dacewa shi yafi tsana a halin yanzu.Ringing biyu Usamna ya dauka,yace,”Aboki ya akayi?” Cikin tsana yace,”bawani zancen Aboki,nakirakane inji ya jikin mahaifiyata?” Yace,”da sauki,amma zaifi kyau kazo kadubata.” Yaja tsaki ,”bayan kaje ka shishshige a gurinta don tabaka matata.” Usaman yasa dariya,”Aboki ka aje kishi a gefe guda,muyi magana me muhimmanci, Sadiya allurace cikin ruwa,kaga kenan me rabo kadauka.” Aliyu ya runtse ido,jiyake maganganun Usman na sukarsa cikin rai,amma dayake shawara yake bukata sai ya danne yace, “InshaAllahu matatace ni Daya.” Yacigaba da Cewa. “Kana ganin inzo gurin ta ko Yaya?” Yace,”zaufi kyau kazo din don kabata hakuri.” Yace, “kana ganin inzo yau ko gobe?” “Kabari sai jibima,domin lokacin ta dan huce,” inji Usaman. Aliyu yace, “to shikenan zamudinga yin waya.” Iya ta tara sauran ‘ya’yanata tafadamusu abinda Aliyu yayi,kuma tace musu ba’ita babu shi,tacireshi daga sahun ‘ya’yanta,nima da kyar na wanke kaina daga zargin datakemin wai na rufeta. Yaya Sulaiman yakira Aliyu yamasa Nasiha kan abin da yayi,Aliyu yabashi labarin yanda abubuwan suka faru,yakuma yimasa rantsuwar cewa yanzuma yadena.Yaya Sulaiman Yayi masa fadan girma sannan yace yaje yanemi iya gafara,don tadau zafi dayawa.Kwananmu Daya a asibita aka sallamemu,Yaya Usman da sauran ‘ya’yanta sunbata kulawar data kamata. Na idar da Sallar La’asar na nufi kitchen domin dafawa Iya wake da Alayyahu sai naji sallamar Yaya, na amsa amma ba lallai yajiba,bankuma kalleshiba nacigaba da harkar gabana.Bakin kitchen din yazo ya tsaya,kamshin turarensa yacika kitchen din,nakalleshi cikin tsana. “Lafiya?” Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Yace, “in ina cikin damuwa da nakalleki sai inji ta
yaye.”
Naja tsaki, “dan Allah kabani guri kaje kaji da
kalubalen da yake gabanka.”
Yace, “Don Allah kitayani bawa iya hakuri nasan
zaki iya shawo kanta.”
Nace, “eh, dama bakasan daniba sai matsala ta
sameka wadda kake ganin nice zan iya yima
maganinta.” Najuya baya.
“Malam kaje da matsalarka,Yanzu ni babu wata
alaka tsakaninmu dazan iya yimaka wannana
arzikin.jeka da kanka,innace mahaifiyarkace?”
Ya tausasa murya, “Don Allah kizo muje innason
muyi zancen gabadayane harda batun auranmu.”
Naji tamkar ya watsamin wuta,Nace,”Allah ya
kyautamin,.” Naja tsaki tankashima bata
lokacine,don haka yagaji da surutunsa da
banbakinsa ya kyaleni.
Inna jiyoshi yanatayiwa iya magana tayi banza
dashi,nasaka kujera bakin kofa na zauna,yayi ta
bata hakuri,amma kala bataceba,sai datagaji
sannan tace, “Don Allah kafitar min daga gida,
Innaso insanar dakai tini nacireka daga sahun
‘ya’yana, bana koson ganknka.”
Yace, Don Allah iya kiyi haku….”
Ta katseshi, ” inkanaso inyimaka baki to kacigaba
da zama a cikin dakinnan “
Tsam yamike yafito yanufi waje cikin damuwa,
baifi minti 5 da fitaba yayomin text wai in yara
sun dawo daga Islamiyya inshiryasu zasuje shan
Ice cream,tsaki naja na aje wayar gefe.
Shida da mintina,suna shigowa yana shigowa,
saikace dama yana wajen yana jiransu,jin
muryarshi duk yaran sukaje suka makalkaleshi
harda Sadeq dake koyon rarrafe,sai daga hannu
yake wai dole yagane babansa.Ina Mamakin
yaron.
Yace, “kuje kucire kayan makaranta kuxo muje
shan Ice cream.” Yarannan sai suka hau murna
da tsalle.
Khausar ta nufi iya tana murna tana cewa, “Iya
zamu fita da babanmu.”
Wata tsawa da iya tayiwa Khausar ni kaina saida
na tsorata,tace,”Ku tashi sama mana da Baban
naku me yadameni?”
Karshe dai da kayan makaranta ya tattarasu suka
tafi harda Sadeeq.
SaKu ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347i Tara saura suka
dawo,lokacin sadiq yayi bacci,ni da iya wai har
tsaraba yayimana don neman gindin zama.
Yanda iya bata kalli ledarba, haka nima nayi
saida Iya tafita sannan nace dasu Khausar Su
dauka su hada datasu.
A daren ne Alhajin nan yasake zuwa karo na
uku,biyun ban fitaba,nace ace bana nan,Amma
yau sainafita sabida nasan Yaya yana
nan,tayiwu yazo zanso ya ganmu. Kwalliya nayi
sosai, sannan nafita.
Cikin wata dankareriyar Mota yazo sai kamshi
Yake,na kwankwasa motar sai gashi yafito daga
gidan baya yace, “ranki ya dade yau dai naci
sa’ar samunki,amma naji Dadi.”
Nayi murmushi sannna na rage tsawo nace, ‘ina
yini?”
Yace, “Lafiya kalau,” Bayan mungaisa yace,
“Mama tana ciki?”
Nace, “Eh”
“Inna son mugaisa.”
Tofa!,bani da zabi,dole saidai inkaishi din.
Na shiga nagayawa Iya za’a shigo gaidata,tace,
“toh”
A gaban iya yazube ya gaisheta,itako Iya harda
fadamasa cewa; ni marainiyace,dan Allah in
aure ya hadamu yarikemata ni amana, saboda
na wahala a gurin mijina na farko,shi kam sai
yace ,yaji komai game dani, tinda ya ganni
yasan innada tarbiyya sabida naki yarda inhau
motarshi, mata yanzu da zakaga suna tare mota
da kansu wai dan a ragemusu hanya! Yacigaba
da cewa, “Sai danasa akaimin bincike akanta,
kuma naji sakamako me kyau don haka nashigo
da karfina zan aureta.”
Iya tace, “InshaAllahu, yanzu kaima yakamata
insanka.”
Yace, “Sunana Alhaji Badamasi Yunusa,ni dan
asalin jihar katsinane karamar hukumara
Bakori,inna nan gwamna road da iyalina,matana
biyu,yarana goma,ni ma’aikacine a matatar man
fetir dake nan Kaduna.”
Iya tace, “to shikenan,Allah ya tabbatarmana da
alherin dake ciki.”
Yace, “Ameen.”
Kan ya wuce saida ya ajiyewa iya daurin yan
dari biyar guda daya. Nafito daga uwar daki dan
innajinsu,iya tace, “da alama yanada
mutunci,nace, “nalura tin farkon haduwarmu.”
nakoma gurinsa inda yacigaba da yimin zancen
aure,shi bayason adauki lokaci,sannan yanason
muma muyi bincike a kansa,bayan nan zai turo
tinda yanzun mu ba yara bane da zamuyi ta
doguwar hira,nace , to! Yabani lokaci nayi nazari
da tinanin kafin ya turo din,Yace to yabani,nima
haka yacikani da kudi,nayi nayi yabarshi yace
Sam; dole nakarba. Yataka zai shiga Mota kenan
Aliyu yayimana sallama,shine ya amsa nikam
gabana sai faduwa yake. Yace, “Alhaji nazone
inyimaka gargadi.”
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Alhaji Badamasi yace, “name fa?”tare da
dawowa da kafarsa.
Aliyu yace,” wannan matatace, dan Allah
karkasake zuwa.”
Alhaji Badamasi yadubi gurin danake Yace,
“Wannan ne?”
Koda bansan meyake nufiba Sai nace, “Eh! Shine
Alhajina,shiga motarka kayi tafiyarka sai munyi
waya.”
Tamkar me jiran umarnina sai kurum yashiga
mota tare da cewa, “sai kunjini ginbiya.”
A hankali motar ta silala ta dauki hanyar barin
layin. Cikin zafin rai yasha gabana, “wato harma
labarina kike bayarwa ko? gani dan iska!”
Nace, “Eh!” Nacigaba da tafiyata.”
Yace kinsan Allah zakijamasa bala’i,zan tono
laifukansa inmasa tarko yafada hannunmu,ai
nasan shi.”
Tsaki naja nacigaba da tafiya inna cewa dadinta
baka isa kayimasa abinda Allah baiyimasaba.
Innashiga zaure shima yashigo, “Sadiya dan
Allah tsaya kiji.” ya tsare hanyar shiga gidan ya
tausasa murya, “Sadiya dan Allah ki rabu da
mutuminnan, yawancinsu suna ta’ammali da
matan banza.”
Nasaki dariya cikin izgili Nace, “wannanfa shine
shege! Yi da me zina,” nanunashi da yatsa,
“ashe har kai zaka dinga zargin wani cewa yana
bin mata? Kamanta da naka laifin ko? har
sakamako ka ajiye.” Nayi murmushi, “bani hanya
in wuce.”
Yace, “Naji dai,duk abin da zaki cemin
Kice,amma zan nunamiki cewa nidai nine
mijinki.”
Na ratsa ta gefensa na wuce,bansan yabiyoniba
sai da namikawa iya kudin inna cewa “nayi-nayi
yabarsu yaki.”
Ta ciro nata tace, “kingansu dami guda, Allah
yashi albarka,tinda yafadi inda yake zansa
yayanku babban a bincikomana,in bashi da wani
aibu shikenana.”
Kurum sai Yaya yafado dakin, “Dama sabida
kudi kike sonshi ko Sadiya? Sannan kuma kisani
bazakiyi aureba har sai kin yayemin yarona.”
Nace, “ina ruwanka dani? Yaro kuma dashi zanyi
aure a can zan yayeshi.”
Yasake daga murya, ” kinyi kadan.”
Da hannu iya tayimin alama wai inyi banza
dashi, don haka na shareshi Yakara masifarsa
ya nufi waje.
Ranar Aliyu yaga tashin hankali,yanzun yanda
zai shawo kan Sadiya da Iya yake nema.nikam
dan So banson Alhaji,amma zan iya auransa da
in auri Aliyu ko Yaya Usman, in anyi bincike zan
amince muyi aure kawai in huta.
Aliyu fa yadage kullum yana kan hanyar gida
daga Abuja,yana gida yana bawa iya baki,ya
turo wannna ya turo wancan,rokon gafara har
dasu mahaifina. Andau tsawon wata biyu a
haka,lokacin zancen aurenmu da Alhaji yasoma
nisa,dan batun har yakai Zaria. Yaya Aliyu kam
yadan rame duk da juriyarsa. Saifa yadauki wani
sabon salon kamun kafa da yaransa,kawai sai
mukaga yara sun canja ba kamar Khausar, in
Alhaji yazo ta dinga kunci kenan harda
Kuka,dana tanbayeta dalili wai inkoma gidan
Babanta,ranar har marinta nayi, iya tayimin
fada wai indena dukanta,ammafa baza’a
komaba. Ko Yaushe zaizo yakwashesu zuwa
yawo yanatayimusu hidima. In Iya kuma tayi
maganarsa sun dinga kunci kenan,har Mama.
Wata ranar Juma’a muna zaune iya taje
Masallacin Juma’a Yaya yayomin waya inshirya
yabiyamin kujerar maka ni da Iya zamuje,duk
da farincikin daya girgizani amma sainace nikam
nagode bazaniba zamuje da Alhajina,
( Lallai Sadiya kin burgeni,ANaM Dorayi
hhhhhhh)
Bantabaji Aliyu yayi babban zagiba sai yau,ya
kudundumawa Alhaji zagi, da sauri na kashe
waya
Yaya Sulaiman yazo da daddare cikin murna
yana gayawa Iya wai Aliyu yabiyamusu Hajji shi
da Iya da Mahaifina,ga mamakina sainaga tahau
murna harma tasoma kiran ‘yan uwa a waya,
saidai banji ana kiran sunana a ‘yan tafiyaba
Alhalin ya cemin yabiya ni da iya.washegari
makota sukai ta shigowa taya murna iya tana
yaye baki, amma da yamma da yazo sainaga
tayi kicin kicin,musamman nazo nazauna inji ko
zaiyi batun tawa kujerar, sai naga iya ta tubure,
“Naji sakon, nagode, amfa kasani karkazata zan
hakura da laifin dakayi,hajji kiran Allah ne koba
ta hannunkaba indai an kirani Sai naje.”
Yace, “hakane Iya,innadai neman afuwa,kuma
dama kujeru hudune yanzu saura daya shine
nace kowakikaga yadace abaiwa? Har na bawa
wani sai yace bayaso.”
Iya tace, “kai wannan wane mara rabone? To kai
kajene?”
Yace, “a’a zanje wata shekarar,sabida Siyasa
datake bullowa a daidai lokacin aikin
hajjin,kasarnan tana bukatar Irina.”
Iya tace, “Allah yataimaka “
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Nashiga daki cikin takaici, bakina ya
cuceni,da’ace nasan Iya zatayi saurin yadda da
batun da bance banasoba,gashi tace yabawa
kawunmu kaninta na Hadeja.
Aliyu yasamu sassauci gurin iya da yan’uwanshi
sanadin wadannan kujeru da yabiyamusu yanzu
burinsa kawai ya shawo kan Sadiya, amma ta
yaya bayan tabawa wani dama har ankawo
sadakinta.
Daya Isa Abuja kai tsaye Office yawuce sai wajen
shabiyu yaje gida, abinda yabashi shi mamaki
yanda yaga ankulle kofar falon ta ciki maimakon
ta waje, yasaka Key yaki shiga sabida akwai
wani ta ciki,don haka sai ya kwankwasa don
yaga ikon Allah,jim kadan aka bude. Mujidat
yagani, tayi kyau iya kyau,kamar farkon
haduwarsu, ta rungumeshi; Oyoyo Mijina,ya
yakiceta ya tureta yadaga murya, “Wayace
kidawo gidana?”
Tace, ” to inna can zaune bakazoba”
Ta nufi ciki ya shiga, ta nunamasa tebur da
hannu; ” ga Abinci.”
Yace, “bana ci.”
Ya nufi dakinshi ta bishi, bandaki ya fada ya
watsa ruwa, yafito yayi shirin kwanciya yana
hawa gado itama ta fada,Yace, “kifita,kuma
nabaki zuwa da safe kibar gida na.”
Tace, “Gidanmu dai, dan Allah Honey kayi
hakuri bazan sakeba.”
Yace, “kina takama da aurene ko? To ni zan
ball…..” Ta katseshi ta hanyar manna bakinta a
a cikin nasa,hmm Mujidat yar duniya, sai datasa
ya manta komai,yashiga shawagi cikin duniyar
Ma’aurata. Haka ya hakura ya barta sannan ya
dakko mata danta daga inda yakaishi Ajiya
bayan taimasa alkawarin bazatasake
sabamasaba,kuma zata mutunta kowa nashi.
An ajiye lokacin bikinmu nan da wata
biyar,lokacin na yaye Sadiq,Alhaji Badamasi
nason yin dawainiya damu danma iya tana
hanashi,su Khausar sun tsaneshi,har shidakansa
ya fahimci hakan,har yataba cemin, meyasa
yarananan ko yakirasu basason Zuwa? Nace
haka suke basu da sabo.
Cikin yan kwanakin da suka biyo baya Yaya
banda kyautatawa dangi baya komai,ya
kammala gidanshi dankarere yace Iya takoma
donshi ba shiga zaiyi ba,namu nada kuma Yaya
Sani yakoma.
Nadauka Iya zatace a’a,sainaji tace zatayi
shawara, Nace, “to iya komawa zamuyi?”
Tace, “Eh,ai abinda baifaruba shi ake gudu
Sadiya, wanda ya faru saidai a kiyayi gaba.Aliyu
yariga yanemi afuwa ta yaya zanyi? Sai addu’a
inna nunamasa fushi nane don ya kori gaba
yakuma gane yayi ba daidaiba.”
Nace, “yanzu dai za’akoma gidan kenan?”
Tace, “to waye bayason cigaba yarnan?”
Natabe baki cikin takaici nace, ” to saidai
kukoma kubarni a nan, ko kujira in nayi aure ku
kuntare.” Iya dai banza dani tayi. A raina nace
wato da da Mahaifi sai Allah,yanzu iya har
tamanta da fishin datakeyidashi.
Wata ranar asabar yazo har da Abdul su
Khausar suna ta murna ganin dan’uwansu nidai
beganeniba yaron,lokacin iya na makota.
Yaya Yace, “gabar harda danki?” Nidai ban
tankashiba, Allah-Allah neke iya tashigo naga
irin warwarar dazataimasa amma tana shigowa
sai naga ta hau washe baki.
“Ai harda Abdul din kazo.”
Al-amin yakamomasa hannu, “gashi Iya.”
Ta daukeshi tanacewa Khausar ta debomasa
ruwa a firij,Yaya ya kalleni harda yin wani
murmushi,wato inganidai bashi da wata
matsala, nima dan inkular dashi nadauki wayata
nakira Alhaji Badamasi mukagaisa,nace, “Alhaji
zanje unguwa kozaka aiko akaini.”
Cikin murna Yace, “dole inbar komai inzo inkaiki

Nakalli fuskarshi kamar zai fashe da
kuka,murmushi nayi na tashi na hau yin
kwalliya, minti shabiyar saiga kiranshi,
“Na’iso ranki ya Dade “
Nace, “dama kana kusa kenan,to ganinan
fitowa.”
Nadinga yiwa jikina aman tirare har saida ya
time,yace,”wai ke ina kike shirin zuwa haka?”
Nace, “Sai kaji? Ba matsalarkabace.”
Ya kalli iya, “haka take yawo kamar mara
mafadi?”
Iya tace, “shi zata aurafa.”..
Nazo fita ina wucewa ina cewa, Iya zanje gidan
Aisha,tace, “ki dibarmata kwai.”
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ya kara kulewa,sai yatare bakin kofar, “To Koma
ki dauki Sadeeq bazakibarshi ya tashi yadinga
kukaba.”
Dariya ke nema ta kufcemin,Nace, “Kasan Allah
yayi kukan jini inyatashi nikam bazani dashiba.”
Yayo kaina, nayi bayan Iya inna fadin, “Dukana
to zakayi?”
Yace, “bakin rashin kunyar zan buge.”
Nace, “Aiko daka amsa tanbayoyin Alhaji,domin
matsayin matarshi nake.” cike da rashin kunya
nayi maganar.
“Inma matsayin uwarsa kike be
dameniba,amma daukarmin yaro aje duk inda
za’a dashi.”
Na kalli iya wadda tinda tayi magana dazu bata
kuma yin maganaba, sai nagama dariya take
kunshewa dan abin dariya itama yabata.
Nace, “kifada masa yadena zargin mijina.” Sai
naji jifa a kafadata da wayar shi, nashiga uwar
daki inna sosa gurin domin naji zafi,bakina bai
mutuba innacewa, “Ba inda zanje dashi kome
zakayimin.”
Iya tace, ” ina ruwanka da sune? Yaza’ace
saitafita da yaro dole?”
“Iya amma inyatashifa yanason nono?”
Nace, “nawa kake biyana kudin shayarwa?”
Yace, “kifadi kudin nonon gabadaya a biyaki.”
Iya tadaure ta hade rai tace, ” to tinda ban
isaba kacigaba.”
Yazauna tare da fadin, “shiyasa tagama
rainani,domin kankomai sai a nunamata tafini.”
“Au, hakama zakace?”
Sai kuma cikin sauri Yace,”iya kiyi hakuri.” Nidai
nafi to na debi kwai kawai nayi gaba.
Tin bayan fitata kai yadafe, baisan ta ina zai
bullowa lamarinaba,abinda dai yayiwa kansa
alkawari shine , bazai taba bari Sadiya ta auri
waninsaba,yadogara ga Allah ta hanyar
tsayuwar dare tsananta addu’a,Allah baya bacci.
Nikam a gidan Aisha inna fadamata yanda
mukayi munata kwasar dariya,Aisha tace Sadiya
nidai bazangaji da fadamiki da Aliyu kadai kika
daceba,shima dake yadace, nace tabdi, ni yanzu
nacire batun wani so ko dacewa a cikin raina,
nafiso inyi aure inda za’a ga mutuncina,insamu
tsabtataccen miji mara aibu,tace ai bari
infadamiki Sadiya a wannna zamani da wuya
kisamu mara aibu,sai dai wani yafi wani,ni
innagudun kar kiyi gudun gara ki afkawa zago,
amma shi din kinbincika halinsa?
Nace, “iya ta bincika ba matsala”
Tace, “shikenan Allah yazaba mafi alkhairi.”
Aliyu yacewa iya yagama zubamusu kaya a
wancan gidan sati me zuwa zasu tare.
Iya tace, “Ai nazata sai mundawo aikin hajji anyi
bikin Sadiya don batason tarewa a gidan.”
Yace , “a’a, tafiyarku saura wata Daya da
kuntare kawai,”
Tace, “ko a barshi mutafi daga nan inmundawo
lafiya sai musauka a can.”
Ranar tafiyarsu iya har kuka nayi, nace yanzu ni
kadai zan zauna a gidannan sai yara, gashi
zandinga tafiya makaranta, iya tace, “bana
fadamiki matar kawu Hauwa tana nan tahowaba
daga Hadeja tare zaku zauna,in Allah yadawo
damu lafiya sai sutafi tare da kawun naku ko?”
Nace, “shikenan,”
Amota Daya Yaya yadaukesu wata kuma aka
debi ‘yan rakiya, nidai dama nafadawa Alhaji
kuma yaturo direbansa yakaini, Aliyu ya hana
yaransa shiga motar, nace ohodai.
Bayan tafiyarsu Iya da sati daya sai ga yaya
sunshigo da Habu, na daure fuska muka gaisa
da Habu,dama alokacin zantafi gurin aiki, sai
kawai nafita.
Aliyu yasa Habu yayi ta jidar kayan yana kaiwa
gidansu, irinsu kujeru,TV harma da fringi,Baba
Hauwa tace lafiya? Aliyu yace dama zaku
tashine,kayan nabaiwa uwar yaron nanne
mokatanmu.”
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Tace, “harda firingin? Amma danasani na
tanbayi firing din innasonshi,Aliyu yace, “inzaki
tafi sai insemiki wani”
Tasoma godiya yace ai ba komai,nidai addu’ar
dazakiyimin Allah yasa Sadiya ta yarda tadawo
gurina.
Baba Hauwa tace, “Ai dama kanasonta baka
yunkuraba?”
Aliyu yace, ” Ai babu irin yunkurin da banyiba
amma yarinyar nan taki yarda dani,yanda
kikasan inyi hauka.”
Baba Hauwa tace, “shikenan zan tayaka
addu’a,sannan zan dinga dan cusamata ra’ayi.”
Yace, “nagode, nikuma zanmiki alkhairin da
bazaki mantaba indai kika shawomin kanta.”
Nadawo naga gidan wayam, yarana da
murmushinsu suka tareni da batun wai Abbansu
yace yau zamu tashi,tsaki naja tare da cewa dan
Allah kukauce kubani guri,raina yabaci daganin
hukuncin da Yaya ya yanke, na dinga zaga dakin
inna kallon jakunkunan kayanmu a kasa anfito
da komai sai gashi yashigo, “kufito Habu yayi
gaba damu nikuma zantaho da jakunkunan, ko
bata dawoba?”
Baba Hauwa tace, “tadawo tana ciki.”
Yashigo cikin dakin, “Sadiya” nakalleshi cikin
bacin rai,har saida yayi in’ina kafinyacemin,
“kizo Habu yakaiku” Nace ina? Yace sabon
gidanku, na girgiza kai gami da tabe baki,
gidanka dai bazaniba.yashigo tare da tausasa
murya yace , Sadiya wai bazaki yafeminbane?
najuyamasa baya, “wai me zanmikine kiga
haskena Sadiya?” na waiwayo na dubeshi,
“rabuwa dani kawai za’ayi kadena shiga harkata
sai inyafemaka.” Ga mamakina sainaga yazube
gabana gwaiwa biyu biyu yanacewa, “Sadiya dan
Allah na rokeki ki yafemin kidawo aurena wallahi
ke kadai nakeso,kanki nasoma sanin wacece
mace, dake kadai nake samun nutsuwa, Sadiya
ki amince kiyimin takaba.”
“Takaba kuma?”
“Inna nufin kikoma gidan har inmutu kiyimin
takaba.”
Na tabe baki,”ga Mujidat can zatayimaka takaba
ni bazan iya zama dakaiba,” nasake juya baya,
sainaji muryar Khausar, “Dan Allah Mama dan
girman Allah mamanmu,” nace nifa bazan koma
wani sabon gidankaba bare aurenka inkamanta
abindakayimin to ni banmantaba, yamike, “ke
wace irin zuciya gareki bayan na kaskantar da
kaina na rusuna a gareki akan kiyafe kidawo
kince a’a to bari kiji dole nema ki Koma gidan,”
nace, “bazan komaba” Yace, “to ai nanma gidan
ubanane,meye banbancinsa da nawa?” Na
kalleshi cikin bacin rai, “dadin abin nima ubana
yanda gidan, kuma zankoma yanzunnan.”
Nasoma hada kayana, da sauri yafito yana
fadawa baba Hauwa wainace zantafi gidan
banana, sai gata tashigo, “haba Sadiya, me yayi
zafi haka,”
“Gorin gida yayimin, dan haka zan tafi gidan
ubana,”
“inkinyi haka kuwa iya bazataji dadiba,” nasoma
kuka to Baba Hauwa duk yatakuramin, ina
ruwansa dani? gara intafi abuna.” Tace, “ba inda
zakije, kuma yanzunnan zamu tare a sabon
gidan idan na isa dake, inkuma taurin kan zaki
nunamin ina yabinki to bisimilla.”
Shiru nayi dan babu abinda natsana a duniya
irin babban yaga na raina shi, banson ayimin
shaidar rashin kunya, inna kuka riris Muka shiga
Mota zuwa gidan da yaya ya ginamana.
Sam barka,gaskiya gidan ya tsaru. Abin mamaki
can Muka samu makotanmu sunje kallon gidan,
inna zaton Yayane yasa Habu yasanar musu
zamu tashi. Anzuba komai sabo, tafkeken falo
da dakuna hudu, nawa dana Iya dana yara,sai
na baki. Can gefe ga wani gini, dana tanbayi
Habu sai yacemin na megidanne in yazo hutu,
“muje kigani.” Nace bazaniba. yara kuwa sai
murna suke suna tsalle ga kayan wasansu nan
kala-kala. Bayan kowa ya watse na daga waya
nakiraki Aunty Abida inna gayamata yanda
mukayi, tace zatazo, A’isha ma haka.
Inna kitchen dinmu mai dauke da kayan girkin
zamani, inna yiwa yara abincin tafiya
makaranta, dayake da safene, zani na daura
akan rigar baccina,Sai hula akaina, sai naji
maganar Yaya a bayana.
“My choice, me kikeyine.? Nadafe kaina cikin
takaici,na kalli jikina, yaci ace da hijabi a jikina,
sabida kirjina yafito, dayake rigar tana da katon
wuya, nace, ” Lafiya?”
Yace, “lafiyalau, nazo ingaishekine “
Nace, “nagode, jeka.”
Ya iso daf dani, “kintashi lafiya?”
“Don girman zati kafita, mufa musulmine, bai
dace kazo inda nake cikin kowane yanayiba.”
Yace, “Ok! Hakane, sai anjima,amma
ataimakamin da abin kari.” Sabida yafita nace, “
toh.”
Banyimasa abin karinba,ina sallamar yara
nakoma na kwanta. Baba Hauwa tashigo gurin
sha daya ta tasheni.
“Kin karyane Halimatussa’adiyya?”
Nace, “a’a”
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Alhajima yana ta shigowa, wai kin hadamai abin
kari. Nace, “bazan hadaba Baba Hauwa, ni
matarsace?”
Tace, “amma Kanwarsace ko?”
“Eh, amma banason wata alaka ta hadamu.”
“Aiko da alaka ta hada, ‘Yaya hudufa, don haka
kibar batunnan,abin karidai nayimasa, shine ma
ya kunna kayan girkin.”
Nace, “ni bamanajin yunwa, sai anjima zanci na
rana gaba daya.”
Tace, “to shikenan, Allah yakaimu.”
Can saiga Aunty Abida wajen karfe daya muna
kitchen muna girki. Gaskiya tayi santin gidan,
muna cikin hira sai mukaji sallamar A’isha, nan
muka yini muna hira, dan ko dakko yara a
makaranta Baba Hauwa ce ta dakkosu.
Aisha tace, “Kyan gidannan kunmaida aurenku.”
Na daka mata duka a baya, “aniyarki tabiki.”
Abida tace nidai ba ankimuba, mene aibun
mijina? Kin gwammace mai mata biyu da yara.”
Nace, “Haka nake sonshi.”
A’isha tace, “kikoma gidan mijinki Hajiyar Allah
Ku rungumi yaranku.”
Nace, “Zanje in haifi wasu a can.” Tace,
“shikenan.”
Sun yini har dare sannan suka tafi,nakira Alhaji
a waya nace mai muntashi har yakemin korafin
Cewa bandaukeshi da muhimmancibane sai
bayan muntashi sannan nafadamai? Nace masa,
“tashinne yazomana cikin bazata, Yayane ya
uzzura.”
Yadanyi dif, sannan yace, “nifa duk lokacin da
kikace Yaya dinnan sai gabana ya fadi gani
nakeyi kamar har yanzu kinasonsa .”
Nace, “dan Allah adaina maida hannun agogo
baya, ni bazan Koma gidansaba.”
Yace, “to zaibari inshigomasa gida?”
Nace, “tinda yakawoni dole inshigo dakai.”
Yace, “a’a, bazan shiga gidansaba, in nazo kya
fito. Ina kikacema gidan Yake?”
“Nan unguwar mu’azune,Amma sabon gurine.”
Yace, “to zamuyi waya, anjima zanzo.”
Nace, “Allah yakawoka.”
Washegari yashirya zaitafi Abuja inna kwance
kan gadona na saki A.C inna Karanta wani littafi
maisuna Yayana safara na Asma’u Lamido
sainaji sallama,kafin na amsa har yashigo, naja
hijabi na rufe jikina, fuskata a hade na dubeshi.
Dan murmushi naga yanayi, sannan yace,
“menene Bako ake rufe-rufe?” Cikin zolaya yayi
maganar.
Nace, “aidai haramunne ka kalleni cikin wannan
yanayin.”
Yace, “to nidai zantafi.” Nacigaba da
karatuna,kudi ya ajiye a gefena, bankalleshiba
ballantana kudin, har yakai bakin kofa sai yajuyo
yace.
Karkijawa wani kato duka dan nacewa ‘yansanda
dake gadi su daki duk wanda yashigo gidan.
Tsaki naja tare da cewa, “Dadin abin nasa gidan
yafi Wannan.” Bai tankaba yafita yabani ina ta
fada.
Kamar ance ya wai waya, Aliyu yaga Mujidat
cikin mota tare da wani Mutum,kasancewar bata
ganshiba, sai kurum yabi bayansu,dayake mota
ukuce tsakaninsu, amma yaga Hotel din da suka
shiga, shima yabisu, ga alama ba lokacin zasu
kama dakinba,sun kama tuni, don baigansu nan
gurin karbar bakina.(Reception)
Yashiga kai tsaye yanuna katin shaidarsa ta
zama Dansanda, sannan yayi tanbaya game da
dakin da suka kama, yayimusu kwatance da
motar da yagansu, har dakin aka kaishi, ya
kwankwasa shiru, sai ya murda kofar, baizaci
zata budeba,amma sai ta bude.Irin kamun
dayayimusu ya kazanta,domin haihuwar uwarsu
suke, sannan maimakon saduwa irin ta mace da
namiji, sai yakamasu yana saduwa da ita ta
dubura,wato luwadi.
Wa’iyazubillah! Allah yayimana tsari da mugunji
da mugun gani, Ameen.
Salati Aliyu yasaka,Mujidat tayi wuki-wuki,Alhajin
yasoma yiwa Aliyu fadan meyasa yashigo?
Mujidat tace mijinane, juyawa yayi batare
dayace kalaba.
Ni naga yasake dawowa washegari da Abdul da
kaya niki-niki,ko kallonshi banyiba,Baba Hauwa
itace ta tare shi,itacema ta bawa Abdul
abinci,nabar falon nakoma dakina, sai gashi
cikin raunanniyar murya yace,”Sadiya inna
maikara nemana afuwarki, jiya naga abin
dayaban tsoro bayan komawata daganan, wai
ashe har yanzu Mujidat tana bin maza, dumu-
dumu na kamata da aurena akanta wani kato
yana luwadi da ita.”
Na kalleshi cikin zaro ido,ban tankaba yacigaba.
“Don Allah ga Abdul nan na rikeki kisakashi cikin
‘ya’yanki, kodadai yazone ba tahanyar data
daceba jinine, nasani bashi da gadona amma
baidace inbarshi ya wulakantaba,donshi ba
ruwanshi.” Ya aje kudi a gefena.
“Kisashi makarntar Isalamiyya da Boko wadda
‘yan uwanshi keyi, nasan zaki iya.”
Duk bantakamasaba, har sai dayace “zakuyi
kwanaki baku ganniba akwai aikine a hannu na
kila ya daukeni lokaci, kiyimin addu’a.”
Na tabe baki, “Allah ya tare .”
Yace, “nagode.”
Haka kuwa cikin kwnaki uku Abdul yasoma bin
‘yan uwanshi makaranta.
Aliyu wani course yaje na wata biyu
India,Yasamu Wannan damarne daga gwamnati
me ci a yanzu,yasan sunyi hakane Don ayi zabe
baya nan,tinda yanuna baya goyon bayansu suyi
yanda suke so, shikuwa ya karbi wannan dama
da zuciya daya, dankuwa ba kowane
dansandane ke samun wannan damar ba.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Su Iya sun dawo, muna ta murna,kullum
gidanmu sai yacika da Iyalai da abokan arziki,
anata rabon tsaraba, abakinta nakejin inda Yaya
Yake.
Baba Hauwa daki daya muke kullum sai tayimin
zancen Yaya tayi ta kwarzantashi tana bani
shawara har abin ya isheni nagudu dakin yara,
suma suka isheni da tanbayar ina Abbansu,
nace bansaniba kuma kada wanda yasake
tanbayata. Iyace kurum ke goyon bayan aurena
da Alhaji, ni dama tsarabar zannuwan gado
yayomin sai Jallabiyya.
Kwanci tashi saiga Yayay kamar daga sama,duk
dacewa natsaneshi bankasa ganin kyawun
dayakaraba, har da dan haske, a raina nace
anje course ko anje Hutu?……zandakata anan,
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347

Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100

Darajar Yayana4-05
Posted by ANaM Dorayi on 02:28 PM, 20-Apr-16
Under: DARAJAR ‘YA’YANA
_________________NA ___________HALIMA K/MASHI Assalamu’alaikum, kuyimin afuwar shiru da kukajini, hakan yafarune sakamakon tsaiko dana samu sabida wasu dalilai,saidai yanzu nayi yunkurin kawomuku Babi na karshe fatan kuna tare dani, inna kuma fatan kuna sane da inda muka kwana… Tsarabar daya kawo dan gulma harda ni,banki karbaba, Pakistan yakawomin kala shida masu kyau sosai, zanyi gayuna a gidan Alhajina, ga turaruka masu tsada. Yara kam ba’a magana harda yaran Usman. Ba’ayi wataba sai karin girma zuwa matakin kwamishina ‘yansanda na jihar Kaduna, anyi biki tare da duk wani abu dayakamata,. Tuni yatare a gidan kwamishinan yansanda dake kaduna. Sai naga antilomana wasu yansanda wai masu tsaron lafiyarmu. Tinda Yasamu wannan matsayin saikuma ganinshi yayi wuya,baya zuwa gida ya kwana kamar da, sai da daddare jefi-jefi yazo yagaida iya yatafi. Hidima kuwa baifasaba, saima karawa da yayi. ‘Ya’yansa yana aikowa a daukesu ranar da babu makaranta su yini can, ko zama yakeyi dasu, komenene bantaba tanbayarsuba. Daidai wannan lokacin na yaye Sadiq, kuma muka tsaida lokacin aurenmu. A lissafi yau saura kwana ashirin da takwas,inna ta shiryeshiryen gyara jikina da duk wani abu nasha wanda zan rike mijina,dan kuwa Aunty Abida zugani kawai takeyi indage innada kishiyoyi,cikin dan lokacin ni dakaina nasan nayi zam-zam. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Direban dake zuwa daukan yara yakaisu gun
Babansu nagani tsaye nadawo daga makaranta
yace, “Madam ance in kaiki Gida.”
Nace, “Inji wa?”
Yace, “inji mai gida,”
Tsaki naja nace, “bazanjeba.”
Kasancewar layin shiru sai tsoro yakamani, yace,
“Kishiga kawai da arziki Madam, sabida kalli
can.” Yanunamin Karshen titin, motar
‘yansandace. Yacigaba dacewa.
“Zasu daukeki da tsiya.”
Nace, “ai da kukuke kaini gidan?”
Yace, “Umarni akabamu daga yau, shiga muje
kawai.”
Nace, “Innakifa?”
“Hakuri zakiyi ranki ya dade,sabida kare
lafiyarkine.” Nace, “Allah ke Kare lafiya ta.”
Yace, “To kitemakeni kar inrasa aikina.” Cikin
muryar tausayi yayi maganar.
Nace, “zanshigane don aikin naka,amma badan
isar wanda yaturokaba. Yace, ” Nagode ranki ya
dade.”
Tinda muka hau titi ‘yansandannan suka
dafemana baya, haushi duk ya isheni. Munyi
tafiya me tsayi kafin na fahimci cewa ba a
hanyar gidanmu muke tafiyaba, Nace, “ina zaka
kaini?”
“Gida mana.”
Daidai lokacin naga munsha wani round about,
kafin nasake magana muka shiga wani layi muka
hari wani babban gate, Nace, “Mallam ina zaka
kainine?” Yansanda dake kofar gidan suka bude
muka shiga.
Gidan yanada dogayen bishiyoyi, dankuwa
girman gidan bazan iya musaltashiba,inna cikin
motar naki fitowa, wayata tasoma ringing,
Bansan lambarba, na daga, muryar Yaya naji
yanacewa.
“Karki zubar da kimata kishigo magana zamuyi
kitafi abinki.”
Ban musaba nabi bayan direban kamar yanda
ya bukata. Cikin wani kayataccen falo nasameshi
Zaune kan kujera daya daga kujerun falon na
Alfarma, Laptop ce a kan wani tebur a gabanshi
yana latse latse.jikinshi sanye da wata shadda
ruwan kasa wadda haske da kyanta suka tona
asirin tsadarta,kamshinsa na yau da kullum
yacika gurin.
Batare da yadubeniba yanunamin kujera da
hannunsa Yace min cikin harshen turanci,
“Zauna.” Ba musu na zauna, saidai raina a bace
Yake, Jira nake yayi magana insoma zubar da
bala’i.
Yanata danne dannenshi, na dubi agogon dake
falon nace, ” Gaskiya innada abinyi, innason
intafi.”
Ya dago ya dubeni kibani minti uku kacal in
kammala muhimmin aikina.”
Naja tsaki tare da kauda kai. Wayata tayi
ringing, nadauka A’isha ce,nace, “ya akayi?”
Tace, “ga Humra ankawo me kyau,” nace, “cikon
nawa zanbada?” Tace, “dubu ukune, namabada,
dama gudun mowar dazanbakine.”
Nace, “a’a A’isha zanbaki kudinki, nasanfa
yanayin garin.”
Tace, “Kin raina kenan?”
Nayi ‘yar dariya, “wallahi ni banrainaba Nagode
Allah yabar zumunci, zanfadawa Alhaji
kokarinki.” Mukasa dariya.
Tace, “kina inane?”
“Oho! Ni banmasan inda nakeba, kibari
innakoma gidazamuyi zancen.”
Na kalli agogo, minti ukun tacika, yature na’ura
me kwakwalwar dake gabansa yamike a hankali
yazago gefen danake, kafafunsa babu takalmi.
Yazauna a kujerar dake daf dani ya karkato.
“Sadiya!” Yakira sunana cikin lallausar muryarsa,
nasake tsuke fuska, yacigaba.
“Sadiya meyasa kika zabi ki auri wanina? Bayan
nasan cewa ni kikeso”
Da sauri nace , “a daba, lokacin da bansan inda
kemin ciwoba,amma yanzu gaskiya bana wani
sonka.”
Yayi dariyar yake, “nasan kinfadane amma in
gaskene ki kalli cikin Idona kice bakyasona.”
Cike da rashin kunya na kalli idonshi, “Aliyu
bana sonka, bana kaunar……”
Yadagamin hannu tare da rintse ido , ” naji
nayarda bakyasona,amma kiduba wasu
abubuwa. Nafarko, ‘ya’yan dake tsakaninmu,
kinfiso kije ki kula da nawasu kibar naki? Bansan
wace mata zan auroba, ke nifa tinda Mujudat ta
wahakar da yarana na janye batun aure indai
bakebace.”
Nace, “wannna ra’aynka kenan, ni nawa ra’ayin
na auri wanda yasan kimata da darajata, wanda
zaimin adalci akan komai.”
Yace, “Sadiya dan Allah kitaimakamini, wallahi
inna sonki, haka zaki tafi gurin wani kibarni?
Kinsandai yanayina kullum cikin Azumi nake,
sabida tsoron fadawa barna.”
Nace, Aliyu kayi hakuri, kanemi wata, gaskiya
bana sonka,tini kagama fita daga raina.”
Namike.
Sai kawai naga yazube gwiwoyinshi a kasa,
“Sadiya kitaimakeni bandamu cewa kowa
yaganni a gaban ki a hakaba, indai zaki amince.
Sadiya inkincire soyayyar Allah da manzonsa, sai
mahaifiyata kece kike bayanta, don Allah
kitaimakeni kisake bani dama, zanrikeki da kyau,
namiki alkawarin zanzama tamkar bawanki.”
Nace, ” kai bame cika alkawaribane, akwai
alkawurra dakayimin tun a baya wadanda baka
cikaba, nifa gaskiya banajin zan kara rayuwa irin
ta aure da kai, muyi zumunci kawai na ‘yan
uwantaka.”
Sainaga kwalla tasoma sakkowa daga idanunshi,
ya mike tare da juyamin baya, “
Matsayina,mukamina da Shekaruna duk na
karyardasu na durkusa miki, amma kin kunyatar
dasu.”
Nace, “Kaine kaja.”
Ya isa kan tebur yaciro tissue ya goge
hawayenshi, yadaga waya yakira direban, ya
dubeshi, “kaita gida.” Na mike na fuce, sam
banji tausayinsaba ko kadan a cikin raina.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Shi kuwa sintiri ya dinga yi cikin falon cikin
tsananin damuwa, duk yanda yazaci zaisha kan
Sadiya abin yaci tira, saidai bayajin zai iya
hakura da ita. Zumbur ya mike yayi hanyar fita
yakira direbansa, yasa takalmi da Hula ya debi
kudi ya zuba s cikin aljihu yafita.
Zari’a yanufa, yaci sa’ar samun Baba a gida.
Suka gaisa, Baba yayi ta murna da zuwan Aliyu,
‘yan uwansa sukazo suna kara yimasa godiya
game da aikin hajjin da sukayo, Aliyu yace
bakomai. Yakalli Baba yace “Baba dama nazone
in nemi wata alfarma a gurinka.”
Yace, “Kamar mefa?”
Yace, “Innson in maida Sadiya mu rike yaranmu,
nabi ta iya, yarinyar kuwa har durkusawa nayi a
gabanta amma taki.”
Ya karonto masa irin azabar da yaran sukasha a
hannun Mujidat, da matsalolin da suka shiga
sakamakon rashin kasancewarsu tsakanin uwa
da Uba, har yanda Mujidat ta shiga harkar
banza da irin kamun da yayi mata, yakara da
cewa, ” nayi mata saki biyu, don na tanbayi
malamai sunce yin uku babu kyau.”
Baba yace, “dama kanason maidata kayi shiru
aka karbi batun wani? Amma kabari InshaAllahu
dakai za’ayi domin dama ni mutuminnan bai
kwantamin a raiba, saboda bai taba zuwa
yagaisheniba, tinda yaturo wakilabsa, bawai inna
neman wani abun hannunsa bane, amma mai
son auren yarka yakamata yakawo kansa
gurinka ku gaisa, kodon haduwa a hanya.
Karkadamu kakoma zanzo gidan gobe.”
Aliyu yacikasu da kudi yatafi zuciya fal murna.
Nikam inna ta shirina, iyace kurum me tayani,
amma Khausar ko zancen bataso.
Washegari Lahadice, inna kwance daki yara suna
hadda, najiyo muryar Baba cikin Falo, sama
sama yake magana, nafito da sauri nashigo
falon, daidai lokacin dayake cewa.
“Don ni indai ni na haifi Sadiya to takoma gidan
mijinta shine albarkata, ta rike yaranta, ai
banzaci yana ta bintaba da yaushe zan amshi
batun wani, wanda ma ban isa yazo
yagaidaniba, matsayin mahaifinta.”
Cikin sauri na zube gabanshi, “Baba wallahi
dama gobe zamuje yagaidaka.”
Iya tace, “nima zanfiso suna tare da ‘yan
yaransu, amma Aliyu yasaki damarsa tin farko,
don haka ni duk abinda Sadiya takeso nima
innasonshi,”
Na mike nakara kusanto Baba, “don Allah Baba
ka taimaka.”
Yace, “inni na haifeki to kikoma kirike yaranki.”
Ya mike.
“Ranar da akasa ta auranki babu fashi, amma
da Aliyu za’a daura.”
Na kalli Iya, “kinfayi rantsuwa akan bazan
komaba.”
Iya tace, “Mahaifinki ya nuna ikonshi natsaya
inyi ta jayayya? In takasance yanda yakeso zanyi
azumin kaffara guda uku.”
Fuuu! Nayi daki,wato iya madai danta takeso
baniba. Nakira Aunty Abida a waya inna kuka na
fadamata, nace yanzu anyimin adalci kenan?
Tace, “Eh!, wannan shine adalcin, ki zauna ki
rike yaranki shine daidai, kiyi hakuri da rayuwa
duk inda kikaje shine jagoran zama ballanatana
tsakanin kishiyoyi .” itama na kashe waya kafin
takarasa abindatake cewa. Bankira Ayshaba dan
nasan ita yar partyn Aliyu ce.
Na kira Alhaji inna fadamasa cewa Aliyu yaje ya
zuga Babana bansan me yafada masaba. Sai
kawai mukaga yazo wai inkoma gidana.yayi shiru
yanaji har nagama,bayan kusan minti biyu
sannan yace, “Shikenan Allah yasa haka shine
mafi alkahairi.” Nasaka sabon kuka , “Haka
zakace kaima? Dama ba sona kakeba?”
Yace, “Inna sonki mana, ammafa ni ba yaro
bane da zan tsaya inna jayayya, sannana tini
jikina ke bani gidanki zaki koma, Allah yasa haka
shine mafi alkhairi.”
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ranar yini nayi kuka har yara suka dawo,
Khausar da Al’amin suka tsareni da tanbaya ,
haushinshi yasani jin haushinsu suma, nace, “Ku
fita ko inyu muku dukan tsiya,” suka fita sukaje
suna tanbayar Iya.
Iya tace, “wai dan kakanku na Zariya yazo yace
takoma gidan Babanku.” Sai iya taga yara sun
soma murna, Khausar me wayon tsiya sai ta
saci wayar iya ta nufi dakinsu ta kira layin
Babansu, Cikin murna tace, “Abba innayimaka
murna, ashe Momy zata dawo gidan ka?”
Yace, “Eh, Babyna. Ina Maman naku yanzu?”
Tace, “gatacan daki tana kuka,dan Allah kada ka
karayimata abinda zaisa kuyi rigima.”
Yace, ” To Khausar zan kiyaye, kije ki lallasheta,”
Tace, “To.” Tana aje wayar yayi murmushi,
yarinya yar shekara tara da rabi wayonta kamar
na manya.
Yashigo, “Momy inji Abba wai yana gaisheki,yace
kiyi hakuri kidena kuka.”Tsawa na dakamata ta
tashi, ga mamakina sai naga tana dariya.
Cikin dare naga sakonsa, wai: Saura sati uku ko?
Nakosa inrike lallausan hannunki, My choice ya
kike ganin darenmu na farko zai kasance? Inna
jiran amsa.
Tsaki naja na goge sakon.
Shida na safe naki tashi infita,sabida inna fishi
da kowa na gidan, wayata tasoma ruru na duba,
koda banyi saving number shiba nasan yayane,
don haka naki dagawa. Kiranshi goma inna
lissafawa, sannana sako yashigo.
My choice kiyimin addu’a zantafi wani daji
dakaina zan jagoranci yarana don cafke wasu
barayin dana gano suna tare da tsohon
kwamishinan da aka canza daga Kaduna.
Nafadamikine ba dan wani abuba sai dan kila
bazan dawo ba, nafitane a bakin raina.
Shiru nayi, dan kalaman sun tsirka zuciyata
kadan, amma duk da haka sai na tabe baki na
ture wayar.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Tamkar almara karfe goman dare na jiyo muryar
Usman a dakin iya, can sai naji tana salati na
fito ina tambayarta lafiya? Tace, “Aliyu ne wai
yan fashi sukai masa harbi uku, amma dai anyi
nasarar kama wasu, sannan aka harbe wasu.”
Take zan tukan da ya turo min dazu da safe
suka fado min, na zauna kan kujera nace, “Iya
yanzu yana ina?” Usman yace, “an tafi dashi
Abuja babban asibiti.”
Kai gaskiya hankalina yayi mutukar tashi, cikin
daren nayi ta kuka amma bazance ga dalilin
kukanaba.
Washe gari su Usman da sauran yayyanmu su
yaya Sulaiman suka kwana acan sannan suka
dawo, sunce an cire masa harsashin amma ba’a
bari ma anganshiba saboda tsaro. bance
zanjeba amma zuciyata tana can. Satin shi daya
iya ta matsa zataje ta dubo shi, ya samu sauki
sosai sannan hankalin iya ya kwanta.
Data dawo nace, “ya jikin?”
Tace “da sauki,ana dai bashi kulawa ne.”
Nace, “masha Allah.”
Ban ko kirashi ta waya ince ya jiki ba harya
dawo gida, satinshi biyu da kwana biyu wanda
ya rage saura kwana biyar aurenmu, nan gidan
aka kawo shi can shashinshi. Su Baba Hauwa
sunzo duba shi shine yake bata labarin ban taba
ce masa ya jiki ba, tazo tana yi min fada. Su
Abinda da Aisha kuwa gaba suka dauka dani. Iya
dai bata taba ce min inje ba niko zuciyata ta
kekashene ina saran zaice ya fasa tunda na
nuna masa kiyayya karara.
Washe garine ya tako zuwa ban garen mu ina
zaune a falo ina kallon T.V ya shigo, yadan rame
kuma yayi haske, yace, “ina kwana?” Na kalle
shi cikin jin kunya nace, “lafiya, ya jiki?” Yace,
“au ashe kinji, koda yake nasan kinso ace na
mutu ko?”
Nace, “duk wanda lokacinsa ya yi babu kari,
harni din.” Bai sake magana ba ya shige wajen
iya, ina jiyo muryar ta tana cewa na zaci za’a
daga bikinne,shi kuma ya ce a’a jiya su Yaya
Sulaiman sunje Zaria sunyi magana da Baba,
sunkai sadaki ya ce yau zaizo gurinki
Tace, “to Allah yasa albarka,” wani abin haushi
wai ashe ya ba Usman sun hado min setin
akwatuna cike da kaya masu tsada harda yara
duka, nidai ina ta kallon ikon Allah za’a yimin
auren dole.
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Ranar daurin aure kuwa kwanciya nayi abina,
gida cike da dangi, su A’isha suna tamin tsiya
wai inaso ina kaiwa kasuwa, jin haka naki
wanka, sai dare nayi wanka dan naji iska. Ina
sallar isha’i sai gasu Baba Hauwa tace, wai na
fito a kaini gidan mijina, sai da nai kuka mai
isata sannan na fita, wai inje gurin iya taimin
fada, “nace ba zuwan da zanyi, ni yanzu meye
ban sani ba sai kace wata yarinya? bayan itama
Iyan ta daina sona.” Ashe Iya tana jina sai
kurum tace, “ni dai da kike fishi dani Allah ya
bada sa’a, fadan ku da Aliyu ba’a shiga kwanan
nan za’a jiku shuru.” Haushi ya sake kama ni na
saka sabon kuka, dan wulakancin sai aka samin
dariya.
Gidan shi aka kaini, dakina yayi kyau mutuka,
sai dai ba kayan gadon dana zaba bane
wadannan sunfi su kyau da tsada. Sha biyu ya
shigo dakin, cikin fushi nace, “indai kana wa
girman Allah ka fita in kuma nizan fita to in
fita.” Sai yace, “Asuba ta gari.”
Tin daga ranar bai sake shigowa daki naba,
kullum shine yake min magana amma bana
kulashi. Ya siyo wannan ya siyo wan can inya fita
zai kirani yafi sau biyar naki dagawa.
Satina biyu ya debo yara, niko yaranma Sadiq
kurum nake kulawa kuma yaki zama shi sai
gurin Iya, nace a sauka lafiya, itama Iyan ta
sami dan tayin hira tunda ita daya ce, danma
da masu aik.
Ranar wata Alhamis ina xaune bayan isha kusan
tara saura Khausar ta shigo, “momy kizo inji
Abbammu yana dakinsa,” nadanyi shuru nasan
ya hada da Khausar ne dan yasha kirana kullum
dare ta waya inki zuwa, ta zauna bakin gado,
“Momy yace kije fa,” ta katse min tunani, nace,
“ke karki dame ni, kije zanje,” data fita taga
shuru ban fito ba sai ta shigo da takardunta
tahau tsakiyar gado na wai zatayi home work,
nace in gani in tai maka miki tace, “a’a kije Abba
na kiranki ko kinje?” Dole tasa na mike, acikin
dakunan bansan wannene dakinsa ba sai da
Abdul ya fito nace inane dakin Abba? ya nuna
min nace meya fito dakai yace ina neman yaya
Khausar ne bata yimin Home Work ba, nace ka
shiga dakina. Na murda kofar dakin ta bude na
shiga yana sanye da jallabiya mai gajeran hannu
kamshi da sanyin A.C suka buge ni na ji sanyi
yana ratsani sabida yanayin sanyinne ake ciki
nace “lafiya?” Yace, “Shigo mana ciki,” Na shiga
tare da maida kofa na rufe, ya tako ya kama
hannuna ya zaunar dani a bakin gado shima ya
zauna ya lalubo hannuna ya matse cikin nasa ya
sauke wata irin ajiyar zuciya, na kalli fuskarshi
idon shi a lumshe, Yaya mutum ne da yayi dai
dai da kowanne zamani yana da kyau abin son
kowacce mace amma ni sam bana jin sonsa a
zuciyata, ya bude ya kalli cikin ida nuna, “nasan
kin tsaneni koh?” Nima na cigaba da kallon cikin
idanunshi, wata siririyar kwalla ce naga ta taru a
cikin idanunsa yace, “duk da haka ina neman
alfarma ki bani hakkina,wallahi ina cikin wani
hali sai dai bazan matsa mikiba, babu matsala
in kinga cewar da takura kije abinki karki damu
kiyi baccinki,” nayi shiru ban motsaba, ya cire
hijabin jikina, rigar baccina ta bayyana, Sky blue
ce mai santsi, ya soma shafa min gashin kaina
hawaye suka soma zubo min, bansan ko na
menene ba,sai na tsinci labbansa saman nawa,
jikinsa kuwa bari yake sai kace tsohon daya
dauki budurwa, ni kaina ban san ina muradi ba
saida abubuwa sukai nisa. ranar dai mun kwana
muna aikin lada cikin wata duniya da masu
auren sunna ne kurum suka santa.
Wannan karon yaya bai dauki al’amarina da
wasaba, ji yake dani kamar yar yaye Ko laifi
nayi baya yi min fada, inna ce ina son abu baya
ja ko aiki da nake nace zan daina yace a’a in
kina son dai nawa na daina jayayya dake, nace
to zan daina dan dan nasan bakaso, yace
nagode.
Haka nan tun ina dari dari da shi na saki jikina
da shi nima ina nuna masa kulawa, zamammu
yafi na farkon aurenmu, ‘ya’yanmu sun
warware, damuwarsu ta yaye, sun ganmu a tare
cikin aminci sun zama cikin farin ciki da walwala
karkashin kulawarmu.
Wurin shi na sami labarin Mujidat ba lafiya tana
asibiti wai bata rike kashi da fitsari, yace, “kinga
illar zina da Luwadi ko?” Nace, “Allah ya bata
lafiya,” yace, “yanda nake samin labari gwara
mutuwarta da rayuwarta, Allah yasa mufi karfin
zuciyarmu.” Nace, “ameen ya rabbi……..”
Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai
masu nishadantarwa
Anamdorayi.mywapblog.com
Kokuma ku kasance taredamu a facebook
https://mbasic.facebook.com/HAUSA-
Novels-389304544597988/?e_pi=7%2CPAGE_
ID10%2C737012347
Tammat bi hamdullahi taku Halima Abdullahi k/
mashi kecewa kusaurari littafinta na gaba,
SAUYIN RAYUWA……..
Alhamdulillah yaudai cikin ikon Allah gamu
mumkawo karshen wannan labarin da muka dau
tsahon lokaci muna yi, fatan zamu anfani da
dukkanin anfanin da yake ciki sannna mu kiyayi
kusakuran cikinsa. Inna neman afuwarku idan
na sabawa daidaikunku kokuma jamhuri.
Nagode sai kunji daga gareni.

Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button