D U N I Y A – page 5

BY
MissDmk ✍🏻
Page 5
Tace shege Maye,tsohon banza zaka koh ci awara tayi magana tana kwashewa da dariya, Mam Nazeef yace dariyan Me kke yi haka?
Bakomai Mam Nazeef, bara na shigar da kayan ciki sai na fito, tana fadin haka ta kwashe kayan tuyan ta shiga ciki tana kwala wa Inno kira, Inno kina Ina?na dawo fa,
Inno dake bayi ta fito rike da buta tace Shegiya da kka ce ba zaki tuyan ba? gashi koh takwas baki Kai ba ya kare, dariya Tasleem tayi tace walhy nafita yau a sa’a wannan Alhaji ya siya na dubu, ga dubu biyar yace a tuya me na tiya daya,gobe zai zo ya amsa, amsan kudin Inno tayi ta kirga tana dariya, toh ga dubu biyu kisa a asusu, ki barshi kawai Mam Nazeef yace ya biyamin kudin saukar…
Kai Talatuwa banso ya biya ba,kinsan wa’inan ustazai dason aure,Atoh tun wuri ki gayamai karatu zakiyi ba aure ba…
Toh Inno Shima yasan da haka ai na gayame aure ba Yanzu ba saina kammala jami’a, bara naje,komawa gun Mam Nazeef tayi, hira su kayi akan saukar kafin ta shige ciki…
Kwantawa tayi a wani kwakwararran katifa kamar wata barauniya ta ciro phone tayi dialing number Meems bugu daya ta amsa,
K’awa na hadu da wani Mula fa,ke saina zo gobe zaki sha labari tayi magana tana kwashewa da muguwar dariya kafin ta yanke..”Hmmmm tsoho kenan idan baka san wataba zaka sani yau,ta dauko English novel Mai suna”The Queen of the South” Anan ne take samun more ideas and how to improve her English, ba ita ta kwanta ba sai Karfe dayan dare bayan tayi nafilah ta kwanta..
Abin duniya duk ya ishe shi,ya rasa ina zaisa kansa ya samu sauki.. He just can’t believe he’s getting married in the next two months to come.. Tunani yakeyi on how to call off the wedding ba tare da anga lefinsa ba…
Tunawa yayi da friend insa Hydar wanda sukayi service tare, dauko wayar sa yayi ya duba number kafin ya kira, saida ya kira kusan sau biyu ana ukun ne ya amsa da
“Hello Ali Cuba the hottest guy of all time sai yau ka tuna dani..?
Hydar kana ina? I need to talk to you and it urgent yay maganar da ya nuna cewa yana cikin damuwa…
Hydar yace wait? You mean that you’re in town? Har fada naje kai gaisuwa amma ba wanda yacemin kazo…
Hmmmm nide ba wannan ba, kazo guests house namu dake GRA yanzu please..
Toh shikenan inama ogano amman gani nan zuwa, koh minti Ashirin beyi ba sai Gashi a guest house din, escorts in Ali suka rako sa har entrance,
Hydar irin guys innan ne wanda daka gansu kasan basa jin magana, da sauri ya mika ma Ali hannun yace Ali Cuba men, kaine ka zama wani kato haka? Gym kk zuwa halan?kace matan turawa suna kwasan kaya..
Jan tsuka Ali yayi ya daure fuska kamar baisan wani Abu dariya ba yace please..
Ali Cuba kenan you’re still that Misogynist I used to know? Nifa na dauka lokacin yarinta ke damun ka, duba da yadda kke tsoron mata,
Please Hydar I didn’t call you here for that, ni wani Abu ke damuna Hydar.. Hydar matsowa kusa dashi yayi with so much care yace meke damun min abokina?
Hydar wai aure za’ayi min.. Yanda yayi maganar Hydar ya kusa fashewa da dariya amma sai ya dake yace ban gane ba Ali Cuba..
Ali yace, wai aure zasuyi min da Khadijat Baba Hamza..
Wow! Khadijat my crush, well Ali Cuba am so happy you’re getting married to her ya fada with so much excitement.. Jan tsuka Ali yayi yace banson auren bana so na aure kowa please advice me on how to stop the wedding..
Wooo wait Ali Cuba are you gay or something? Hydar yayi magana outta curiosity..
Wani irin mugun kallo Ali ya watsa mai kafin yace Idan ba zaka nema min hanya daza afasa auren nan ba ka fice ka bani gu Hydar…
Sorry dude, ai Kai din akwai ayan tambaya akanka duba da Lokacinda muke Camp kowa ya Shana amman banda kai, kai koh magana ba kayi da mata gashi kuma kaine crush din mata a lokacin, but sai naga gaba daya ka tsane mata bt why Ali?
Thank you Hydar, thanks for your time you can go now ya fada maganar a zuciye… Hakuri Hydar ya fara basa kafin ya hakura yace gayamin yadda zanyi…
Hydar yace well Ali zuwa za kayi ka sameta, ka nuna mata kaifa dan iskane kuma mashayi nasan mata sun tsana irin set of guys..
Jan tsuka Ali yayi yace never, ni na bude bakina nace ni Dan iska ne wannan shawara ba tayi ba..
Hydar yayi shuru for few seconds can yace, tell her that you’re into Me..Hydar bai karasa magana ba Ali ya wanke shi da Mari tsabar zuciya, cikin wata Amo murya yace banso mata ba sai maza zan so? Hydar baka da hankali Sam, wannan ne shawara? Please get out before I go crazy on you…
Kasa cewa kome Hydar yayi yabar mai dakin,Ali Bari yaji jikinsa da zuciyarsa yana kuna tsabar fushi da yayi, fadawa toilet yayi ya kunna shower da kaya a jikinsa ruwa na sauka tun daga kansa, yafi minti 20 a toilet kafin yace I’d sort out things myself shafe gaban wandon sa yayi, he sighed deeply yace why? Why me? fitowa yayi daga toilet direct gun wayar sa ya nufa, dialing number Dr Kelvin yayi yace hello doctor? Any review?
Wanda aka Kira Dr Kelvin yace the only review I’ve for you Ali is to exercise,diet and sleep, trust me Ali it works… Sauke ajiyan zuciya yay kafin yay cutting call din yayi wurgi da phone din, Shima ya fada kan bed yace for how long Ali? Yayi maganar yana lumshe ido tsabar yadda Zuciyar sa ke kuna shi kadai yasan yadda yake ji
As early as possible suka fara aikin awaran da Inno, sai wajan 9am suka gama komai, Tasleem tace bara naje nayo wanka nai shirin islamiya, Inno sai Karfe shidan yamma zamu dawo idan Alhajee yazo sai ki kai masa Kinji Inno…
Sakin baki Inno tayi tana kallon ta,can tace to mai kke nufi ne Talatuwa? Ni nasan Alhajee ne ko me? Bake ya kamata ki jira zuwansa ba?
Zunburo dan bakin tayi waje tace haba Inno kullum sai na gyaramiki cewa Tasleem ba Talatuwa ba, don ALLAH wannan Talatuwa ya fita daga bakinki haba mana saikace wata tuwo koh talge wai Talatuwa..
Don ubanki baza akira ki da tasalam ba, kiyi abinda zakiyi man, ranan da aka haifo ki kenan,uwarki na haihuwar ki ta sheka nikuma naga ba wani sunan da yadace dake face ranan haihuwar ki don haka banga mahalukin da ya isa yasani nakira ki da wata Tasalam ba ehe…
“Toh shikenan Inno, kwana nawa ne ma ya rage ki dena gani na? Nide bara naje na shirya Karna makara tana fadin haka tai wucewar ta, tayi abinda zatayi ta fito sanye da zunbulelen hijabin ta, tace Inno na wuce islamiya bata jira abinda zatace ba ta fice..
Bata tsaya ko ina ba sai gidan su Meems, suna hada ido suka kwashe da dariya tace waye nawa? Meems tace yar baiwa tawa kenan ALLAH yay miki baiwa, kai K’awa anya ba gun wani kk je ya baki wannan sa’a haka ba?
Dariya Tasleem tayi kafin ta mike ta cire hijabin ta tace, kinga Babban makamai na nan, ta fada tana rike da kirjinta kafin ta juya ma Meems bayan ta tace da wannan ta shafa mazaunan ta, tace Meems kinga wa’inan sune sa’a na, Meems ta kwashe da dariya tace inayinki K’awa ta..
Tasleem tace ba wannan ba kinga wannan siyayyar da Yasir yayi min, zan barshi agunki idan Zanje school zan tafi dashi, yanzu so nake ki rakani bank nayi depositing kudin nan sannan inaso nayi magana akan gyara suna da shekaru na..
Gyara shekaru da suna kuma? Meems tayi magana tana sakin baki…
Yes. Inno tace ita tasa min sunan da kanta, sannan kinsan bankai shekarun ajiye kudi a bank ba,naje nasa shekara sha takwasa to zan mayar dashi shekaruna kuma na mayar dashi student account. Amma Yanzu ba wannan ba, bara nakira Mula ciro wayar tayi mai kiran Samsung Galaxy S5,
Bugu daya Alhajee ya dauka da sallama, jin voice din mace yasa ya gane Talatu ce, “Talatu tun dazun nake expecting call naki”
Tasleem tace ALLAH sarki Alhaji sai Yanzu na samu wayar kiranka, Alhajee daman nakira ne nagaya ma cewa waran na gidan mu, saurin katse ta yayi dacewa bai gane ba? tace Alhaji Saura sati saukar mu yanzu maganar da akeyi ina islamiya sai 6 na yamma zan dawo, nayi waran na ajiye ma da sauran kudin nace in kazo a baka..
Kyalkyacewa da dariya Alhajee yayi yace yaro yarone,yanzu babarki bata tambaya inda kke samo kudin ba koh ba ita kka baima kudin ba?
A’ah K’awata nabar ma sakon Tasleem tayi magana tana daga hannunta sama alamar yes..
Alhajee yace to shikenan, amman banda ke Talatu ina kk taba ganin an mayar da hannun kyauta baya? Wannan kudin dana baki harda ladan aikin ki, da ace kinzo da na Kara miki amma nevertheless next time..
Alhaji da gaske kke yi kudin ladan aikin wara da nayi maka ne? Talatu ta fada tana kallon Meems dake darawa,
Yace ofcuz, Talatu wanna kudin kadanne akan wanda na shiryama zuwanki amna karki damu Yanzu yaushe ne saukar naki?”
Tasleem ta Mike ta daka tsalle kafin tace Alhaji Sunday na sama, Alhaji yace dame dame kke bukata kiyimin list anjima zanzo da Karfe 7
Cikin murna tace Nagode Sosai Alhaj, ALLAH ya biya maka bukatun ka na alkhair, narasa irin godiyan da zan maka Tasleem tayi magana cikin shakiyanci tana kallon Meems..
Talatu wannan ba komai bane,Talatu kidena godemin kamar yadda zan yiwa ya’ya na hakan zan miki Talatu Alhajee yayi magana cikin duniyanci wanda suka kware a harka, but Talatu wayar waye wannan?
Tasleem tayi saurin cewa K’awata ce, yayi saurin cewa shine muka cinye mata Kati ah bara a mayar mata, yana fadin haka ya yanke Kiran koh minti biyu ba ayi ba sai ga katin 5k a wayar ta, wani tsalle ta daka ta rungume Meems tace, Kai ALLAH Nagode ma, gasashen nama daga sama, K’awa bara nayi maki transfer kema, nan take tayi mata transfer katin 2k sannan ta bata 3k acikin kudin, sauran suka dauka suka wuce Bank…
Basu wanni Sha wahalar bin layi ba sabida tasan wani agun, har office yakai su, suna zaune Anayi masu abinda ya kawo su can sai ga Alhaj…
MissDmk✍🏻
09074267236
Thanks