D U N I Y A – page 3

BY
MissDmk ✍🏻
Page 3
Ganin baida niyya compromising with her yasa ta fito tana kurma Uban ihu,gani ga securities agun amma basu ce kala ba,yasa ta tadinga kurma Uban ihu tana birgima a kasa, a fusace ya duka da niyyan daukan ta sai yaji murya daga saman kansa yana cewa, let go off her.A fusace ya dago da niyyan wanke Wanda yayi mai magana da mari sai kawai ya sauke hanunsa kasa, don ganin uniform Men dake bayansa, daya daga cikin uniform men yace Meyafaru ne Baiwar ALLAH ? Tasleem dake kwance a kasa tayi saurin dagowa tana kallon wannan young, handsome and sexy guy da ya kure ta da kallo,tayi saurin mikewa ta koma bayansa cike da tsoro tace Don ALLAH ka taimake ni zai kashe ni,
Guy din yace hey! Calm down gayamin abinda yafaru..? A hankali tafara bashi labarin tundaga kasuwa harzuwa iya yanzu tanayi tana kuka…maida dubansa izuwa Yasir yayi, yace meyasa kk son zubar da mutunci ka? Ace ma eh da gaske itace MEEMsALY so sai kayi mata ta karfi koh mai? kafin ya sake mayar da dubansa gareta yace daga ina ya dauko ki?
Daga Samaru,ya kwace min kome nawa tayi magana cikin shagwabe… Alama yayi wa security guard insa da ya amso mata kayan ta,
A zuciye Yasir Ya nufa motar yana tunanin ya zaiyi da yarinya don baze taba barin ta tafi scot free ba,dauko jakanta ya mika mata, ta amsa da sauri tana sauke nauniyar ajiyan zuciya..
Mayar da dubansa yay izuwa gunta yace ga driver na,zai mayar dake.
Thank you sir, ALLAH ya saka da alkhairi ta juya ta watsa ma Yasir harara ta bi bayan Dss da akace zai kaita gida…Shima ya shige nasa car din tare da escorts insa suka bar haraban guests house din..
Hankali kwance ta zauna a mazauni owners seat tana murmushi, tace I can’t wait to see their faces inda suka ga na fito a motar, shegu kawai sa’idawa banza, da wannan tunani suka issa gidan su Meems tace ma driver nan zaka sauke ni, samari layi sakin baki sukai suna kallon ta,tace driver ka sauko don Allah kafini tsawo ka dubamin wanca mota tayi pointing inda masu zaman banza suke, suna ganin Dss ya sauko suka tsare a guje, kyalkyacewa tayi da dariya tayi masa godiya kafin ta shige ciki, da sallama ta issa cikin gidan su Meems durkusawa tayi ta gaida Ummah, kafin tace ummah Maimuna fa?
Ummah tace tana daki tana shirin zuwa islamiya, kefa? yau ba zaki bane?
Tasleem tace zani Ummah ai hijabin na gun Maimuna dazun nazo nayi guga kuna gun Aiki…ummah bara na shiga ciki na same ta, da sauri ta nufa dakin Meems, suna hada ido suka kwashe da dariya, tace Talatu baki da dama..
“A’ah Maimuna karki kuma in ba so kk ajimu dake ba.. “
Ya hakuri K’awa, yanzu dai karasa min naji, nan take Tasleem ta bata labarin suka ci dariya harda kaiwa kasa,Meems tace dazun Inno ta aiko wai ya batun wara?
Kinji manta da batun wara bara muyi sallah mu wuce islamiya, kafin wannan Maye ya isheni da kira… “
Tasleem yanzu Mal Nazeefi shine Maye? Banza Tasleem tayi mata ta nufa toilet tayo alwala ta fito tayi sallah suna idarwa, taci abinci kafin suka dauki hanya zuwa islamiya, tunda ga nesa ta hango Mal Nazeefi dake ta fama murmushi a dalilin hango su da yayi…
Suna zuwa kusa dashi suka gaishe shi kafin suka wuce cikin makaranta… Zama sukayi gu daya har lokacin koyarwa yayi Malam Nazeefi ya shigo, Wanda ya kasance malamin Fiqh,gaba daya hankalin kowa ya karkata izuwa gun malam amma banda Tasleem dake fama tauna chew gum…
Jin an tabo ta yasa ta jiyo tana kallon Hauwa tace lafiya zaki kaimin Uban duka? Hauwa tace malam ne ke miki magana, toh sai akace ki dake ni?zako kici nakashi yarinya bara atashi, ganin gaba daya suna niman tayar da hayaniya ya kira dukkansu da suzo, Hauwa ne tafara mikewa kafin Tasleem ta mike taja hijabin yadda nonuwata suka tsaya cak dasu, tana wani karkade karkade tuni ya sunkuyar da kansa,yan aji suka kwashe da dariya,
Tsawa ya dakka masu kafin ya umurce su dasu zube a kasa, maida dubansa yay gun Tasleem dake fama bangare bangare yace baki ji abinda nace ba kenan?
Kunkune ta fara yi kafin ta zube a kasa, cigaba da koyarwa yay, saida ya gama ya kalla Hauwa yace ta koma ita kuma Tasleem ta bisa office, yana gaba tana biye dashi amma wanni irin tafiya takeyi na shakiyanci, yan aji suka kwashe da dariya..har suka isa office ta durkushe a gabansa..
Yanzu Talatu abinda kk yi ya dace?
Cikin shagwaba da girgiza girgize tace Mam Nazeef wai menayi ma? Kulum Saika bani punishment a islamiya, can kuma ka lalabo kazo tadi..
Kasa kallonta yayi, sabida ALLAH kadai yasan wana irin hali yake shiga Inda tana wannan shagwaban..shikin sarkewar murya yace ki koma anjima zan zo gidan.komawa aji tayi, bayan antashi islamiya ta jira fitowar Hauwa bata ganta ba, daga karshe hakura tayi,ta wuce gida..
Da sallama ta shigo wanni kwakwararan gida, Wanda ba plaster bale cement, tun daga nesa ta hango Inno a bakin Murhu tana fama da hayaki,d’aga murya tayi tace Inawuni Inno..
Wata mata ce ta juyo wacce baza ta wuce shekarun 65 a duniya ba,tace sai Yanzu Talatuwa? Lafiya kk kuwa?
Turo baki Tasleem tayi tace, Talatuwa kuma saikace wata talge ba dadin ji…?
Yo kajimin Yar banza yarinya, Wato abinda ake fadi a layi gaskiya ne, to Dan dan ubanki inda nakiraki karki amsa, gayamin daga inda kk?
kunkune tayi kafin tace, cikin makaranta na shiga, da ganan na biya gidan su Maimuna muka wuce islamiya..
Ayo ai nadauka baki je islamiyar bane, to maza kije kici abinci ki shiryo ki fita tuyan..
Kai Inno, nide nagaji wallah ki bari sai gobe man, tafada tana zunguro baki..
Anqi a bari din,kajimin yar banza Kai?bayn kinsa tara kudi mukeyi sabida walimar saukar ki, Inda baki je ba Ina zamu samu dubu goma da zamu bada?
ALLAH zai… Bata bari ta karasa ba ta bita da muchiya, da gudu Tasleem ta shige daki tana fasa ihu, kamar Wacce ake ma duka…
Muhammad Ali
Some days later
Yau ake kwana uku,Mai Martaba inda aka nema Kowa da kowa ya kasance a Fadar yau za raba gado da kuma sanni magajin Sarki..
Shi Abban Ali Wanda ya kasance shine É—a nafari a yara maza,Abban Ali, shine na goma a yaran Mai Martaba amma Nafarko kuma nakarshe agun Amaryasa Rukayya Wacce tana hyhuwar sa ALLAH ya dauki ranta, shiyasa Mai Martaba Eng Muhammad Ali Hammajo,ya daurawa Abubakar son Duniya, koh kuka yaji Abubakar nayi,sai yaji ransa ya sosu,wanda haka ya jawo ma Abubakar bakin jini agun sauran matar Mai Martaba,Da har suka fara kokarin ganin sun raba Abubakar da mahyfinsa,wannan dalilin yasa Mai Martaba ya dauke Abubakar daga masauratan izuwa Jihar jalingo a sirrince gun dagin mahyfiyar Abubakar, tunda Abubakar yabar masauratan bai sake dawowa ba sai bayan da yayi aure,har Matarsa Amina ta Kai watan hyhuwa, Wanda Al’ada ne in jikan fari ne ya kasance an birne cibiyar sa a cikin Masauratan…”
Cikin Ikohn ALLAH, ALLAH ya sauke ta lafiya ta samu Danta kyakyawa mai kama da ita, Wanda itama ta kasance yar Fulani Gembu, dake jihar Jalingo, sai ka rantse kace sudin ba yan Nigeria bane tsabar kyawun halitta su.. “
Mai Martaba da kansa yace a sa ma dan sunan sa, Wanda hakan yakara sa bakin jini Abubakar ya karu a zukatar matan Mai Martaban,especially Killishi Wacce Abin yafiwa ciwo takasa dane Zuciyar ta, Wanda yasa taje ta same Mai Martaba da maganar, tace yanzu fisblh abinda kayi ya dace? Saikace Abubakar ne kadai danka? Ka dauki son duniya ka daura mai? koh akansa aka fara hyfa ma jika namiji da zaka sa me Sunanka?
Hajara karki manta dacewa Abubakar ya kasance shine Da’na nafari a wannan masauratan wanda nake sa ran bayan bani shi zai gajeni…”
Ya gaje fa kace? ka ko San abinda kk fadi kuwa? nice fa uwargida dole wanda zai gaje ka ya kasance daga guna, sannan da kk fadin haka shidin me ya sani game da sarauta? Hamza tun yana karami ake koya me mulki da sarauta…
Mai Martaba yace Hamza bashine da’na nafari ba don haka bashine magajina ba, sannan magana sa suna danayi, Eh nayi ne sabida haka nake so, zaki iya tafiya kuma banso nasake jin kin kara kawomin irin wannan maganar…
Har Amina tayi jego ta gama bamai zuwa gunta sai kuyangu ta, daga karshe dai barin kasar sukayi a dalilin aikin da Abubakar ya samu acan kasar UK..
**
Dawowa cikin labarin, kowa ya hallara a fadar banda Ali dake guess house, sabida shi irin mutum ne Wanda in hayaniya yay mai yawa sai yakama zazzabi… Batare da bata lokaci ba akayi abinda za ayi inda akace A. M Abubakar ne Magajin Sarki, ana fadin haka Hajara da yaranta sukayo kansa suna nuna farinciki su, sukam sauran zama sukayi suna kallon Ikohn ALLAH.. Cikin kanne Mai Martaba wani yace bazan mu tashi daganan ba, batare da cikishe wasiyar da wanmu yabar mana ba, wai ina Ali yake?
Abby yace he’s down shiyasa baizo ba..
Toh shikenan ina Khadijat ? Nasan kuna da labarin kome tunda a ranan da Mai Martaba ya kirani a ranan na isar da sakon, Toh Mai Martaba yace a hada Auren Ali da Khadeejat yar gidan Hamza nan bada jimawa ba,
Sunkuyar dakai Khadijat tayi, Tana murmushi tabbas ba wanda zai ki namiji kamar Ali, she can’t wait to get married to him..
Not edited
09074267236
Thanks