Hausa Novels

D.S.P ANNUR HAUSA NOVEL

*FEBRUARY (2)  2023*

 _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA (18) SAURAYINA (19 D.S.P ANNUR PAID BOOK..==..... And Other's BUT NOW (19) D.S.P ANNUR PAID BOOK..... loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱

Related Articles
      _Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken *D.S.P ANNUR.* Ina fatan yabada darussuka ga kowacce macce Kai hardama mazan baki d'aya Allah ka k'ara shiryamu dukanmu_

   *INAYIN LITTAFAINA BADAN NEMAN SUNA KO D'AUKABA KAWAI INAYINE DOMUN BADA DARASI DA FAD'AKAR DA AL'UMMA BAKI D'AYA....... AKODA YAUSHE ALK'ALAMIN MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 BAYA RUBUTA SHIRME KO BATSA KO LALATA RAYUWAR AL'UMMA SAIDAI INA K'OKARIN WAYAR DA KAN AL'UMMA DAMA DAWO DAMU KAN HANYA MADAIDAICIYA ALLAH KA TSAREMU DA AIKATA AIKIN DANA SANI.. INASONKU MASOYANA ADIK INDA KUKE NID'IN CE DAI TAKU HAR KULLUM MAISON GANIN FARIN CIKINKU MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱*

 *Kwanaki sai gudu suke shekaru sai shud'ewa suke inda mutuwa take riskar kowanne bawa, Rayuwa sai ficewa take inda mutuwa tana maye gurbinta, ya Allah 🙏 kajik'anmu tinkan mukoma gareka, ya Allah kasomu kasa Asomu, ya Allah kaimuna k'arshe Mai kyau 👌, Allah karabamu da MAK'IYAN mu na fili dana bayyane, ya Allah Wad'anda suka rigamu komawa gareka Allah kajik'ansu kaimusu gafara ya Allah,. Ya Allah kaimuna maganin Wad'annan masifun da fitintinun, Allah kabamu zaman lafiya da Arziki Mai Amfani, ya Allah Kashiga tsakanin nagari da mugu, ya Allah kabamu shuwagabanni nagari masu tsoron Allah wad'an da zasu dakatar da Wannan b'arnar da Ake Aikatawa,ya Allah kaimuna maganin Wannan tsananin damuke ciki, Ya Allah kashiryemu, ka Kare Idanuwanmu daga kallon Haram, ya Allah katsare hannuwanmu daga rubuta had'ida rubuta Haram, Ya Allah katsaremu da cin Haramun.... Ya Allah Idan mutuwar mu tazo Kasa mucika da imani tareda kalmar=====LA'ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADU RASULILLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM=== ALLAHUMMA AMEEN YA ALLAH🤲🤲*

 _Yau 1/2/2023 First February nafara wannan littafin Allah ka k'addareni dagamashi lafiya AMEEN YA ALLAH_

 ```1/2/2023 first February Wednesday```

              Free🅿️ 1 to 5

      _BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM_

            .....Wani tangamemin gida Mai matik'ar kyau na yada Zango, Ahankali nashiga gidan,.  Masha Allah shine Abinda bakina ya furta Domin kuwa fad'ar Irin tsaruwar gidan b'ata Lokaci ne Kawai reader's nabaku Wannan Assignment ku tsara yarda yake dakanku,.

         Parts_ parts ne kusan guda 3 cikin gidan, inda Naga yafi burgeni can na nufa, tura k'ofar d'akin nayi shuru bakomai sai k'arar A.c d'akin ya tsaru komai Pink & milk ne yahad'u matik'a,

Kwance nahange wani had’ad’d’en guy wanda idan zan Ayyana shekarunsa bazasu haura 30 ba, dik da bacci yake hakan baihana bayyanar kyansa ba,

 Yanayin fuskarsa ya sauya nantake yasoma juyi kan gadon Yana surattai

 "D'ana *ANNUR!!!* Katashi kabinciko gaskiyar kada kabari mutuwar mahaifinka tatafi Abanza"

“Ya ANNUR zanfad’a rami kazo kataimakeni wayyoo,” tiffff tafad’a ramin tareda sakin k’ara,

Afirgece ya farka daga Wannan mugun baccin maid'auke da mummunan mufalkai dak'arfi ya furta Meenal!!

  Da sauri tafalka tareda lalubar makunnin wutar d'akin dake jikin gadon,

 Zaune ta hangeshi ya dafe Kai sai gumi yake tsatstsafo mishi dik irin sanyin dake d'akin,

 "Subhanallah dear meke damunka Wannan wane irin mafalki ne kake yawanyi haka, Kuma dazarar kayishi saika rasa natsuwarka, shin bakayi Addu'a bane kafin ka kwanata,"?

Khausar taje fasa tanbayar,

Kasa magana yayi danshi kawai yasan halinda Yake cikin ga kanshi kamar zai tarwatse saboda ciwo yarasa wanne irin mafalki ne wannan Wai meyasa me k’anwar sa? Kodai bata mutu bane?

Ganin shuru Bai motsa ba Kuma baibata Ansaba yasa tamik’e tasauko daga Kan gadon gabansa ta zauna k’asan gadon tareda kamo fuskarsa d’ayan hannunta Yana dafe da kansa,

Addu’o’i tasoma masa tana tofa masa Dan ganin take kamar harda shafar Aljanu tareda shi,

Sund'auke lokaci Ahaka tana Masa Addu'o'in saida taga yasami natsuwa sannan takama hannunsa had'ida fad'ar "jekayi Alwala lokacin sallah ya k'arato"

Baiyi magana ba dama can Shiba gwajin magana bane, Amma kuma yaji natsuwa bisa Wad'annan Addu'o'in data masa,

Shiyasa koda yaushe yake Alfahari da ita Domin tanada ilimi hak’ik’a Auren macce Mai lilimi duniya ne.

Kan yafito harta gyara d’akin duka Yana fitowa tashiga toilet d’in, shikuwa casbaharsa ya d’auka sannan yafito direct d’ayan part d’in yanufa yayi nocking saida yaji gyaran murya Alamar wanda zaitada yatashi sannan yawuce masallaci,

Saikusan k’arfe 7:30 yadawo bainufe part d’insu ba parts d’in d’azun dayayi nocking shiya nufa, tura k’ofar yayi yashiga da Sallama Abakinsa,

Zaune Kan sallaya wata y’ar dattijuwa nagani wadda kamarsu da ANNUR d’in hartayi yawa ko ba’a fad’ama ba kasan mahaifiyarsa ce,

Saida ya zauna kansa Ak’asa yace,”Ina kwana umma fatan kintashi lafiya,”

Cikin murmushi ta Ansa”lafiya k’alau babana amma bakada lafiya ko,”?

“A’a ummuna kawai kaina ne yake d’an mun ciwo,”

Shuru tayi kafin tace"kayi wannan mafalkin ko,"?

Zubamata Ido kawai yayi Yana mamakin yarda Koda Bai fad'a mata yayi wannan mafalkin ba indai zata ganshi Ranar to saita gano yayi shi, Kodai tasan wani Abu Akai Tana b'oye masa ne,? Zuciyar sa tayi saurin k'wab'arsa had'ida cewa "kull ANNUR ba wani Abu da Umma zata b'oye maka"

Kamar tashiga zuciyarsa kawai sai yaga Tayi murmushi tace”ANNUR inaji Ajikina Kamar y’ata Meenal tana raye saidai wani sashen zuciyata Yana tinatar da Abunda yafaru cewar Meenal tamutu, babana ka daina tunani dayawa kaji,”

"To Ummana zankiyaye Nagode, zanje nashirya Dan inason fita aiki,"

“To Allah yatsare mun Kai Babana”

“Ameen Ameen Ummana”

Ficewa yayi

Girgiza Kai Umma tayi Aranta tana fad’in “ba yanzu zanfad’a maka gaskiyar ba Babana kamin Uzuri zuwa Nan gaba k’ad’an…………………..

Kowacce irin gaskiya ce wannan????? Hunmmmm Yanzu nafara labarin kudai mukasace tare Dani Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 Domin sanin gaskiyar.

     _BASEEERATA ITACE ARZIKINA 😍_

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948
[2/2, 5:06 PM] My Number: D.S.P ANNUR.💫
PAID BOOK #300 ONLY

*FEBRUARY (2)  2023*

 _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA (18) SAURAYINA (19 D.S.P ANNUR PAID BOOK..==..... And Other's BUT NOW (19) D.S.P ANNUR PAID BOOK..... loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱

      _Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken *D.S.P ANNUR.* Ina fatan yabada darussuka ga kowacce macce Kai hardama mazan baki d'aya Allah ka k'ara shiryamu dukanmu_

   *INAYIN LITTAFAINA BADAN NEMAN SUNA KO D'AUKABA KAWAI INAYINE DOMUN BADA DARASI DA FAD'AKAR DA AL'UMMA BAKI D'AYA....... AKODA YAUSHE ALK'ALAMIN MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 BAYA RUBUTA SHIRME KO BATSA KO LALATA RAYUWAR AL'UMMA SAIDAI INA K'OKARIN WAYAR DA KAN AL'UMMA DAMA DAWO DAMU KAN HANYA MADAIDAICIYA ALLAH KA TSAREMU DA AIKATA AIKIN DANA SANI.. INASONKU MASOYANA ADIK INDA KUKE NID'IN CE DAI TAKU HAR KULLUM MAISON GANIN FARIN CIKINKU MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱*

 *Kwanaki sai gudu suke shekaru sai shud'ewa suke inda mutuwa take riskar kowanne bawa, Rayuwa sai ficewa take inda mutuwa tana maye gurbinta, ya Allah 🙏 kajik'anmu tinkan mukoma gareka, ya Allah kasomu kasa Asomu, ya Allah kaimuna k'arshe Mai kyau 👌, Allah karabamu da MAK'IYAN mu na fili dana bayyane, ya Allah Wad'anda suka rigamu komawa gareka Allah kajik'ansu kaimusu gafara ya Allah,. Ya Allah kaimuna maganin Wad'annan masifun da fitintinun, Allah kabamu zaman lafiya da Arziki Mai Amfani, ya Allah Kashiga tsakanin nagari da mugu, ya Allah kabamu shuwagabanni nagari masu tsoron Allah wad'an da zasu dakatar da Wannan b'arnar da Ake Aikatawa,ya Allah kaimuna maganin Wannan tsananin damuke ciki, Ya Allah kashiryemu, ka Kare Idanuwanmu daga kallon Haram, ya Allah katsare hannuwanmu daga rubuta had'ida rubuta Haram, Ya Allah katsaremu da cin Haramun.... Ya Allah Idan mutuwar mu tazo Kasa mucika da imani tareda kalmar=====LA'ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADU RASULILLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM=== ALLAHUMMA AMEEN YA ALLAH🤲🤲*

 _Yau 1/2/2023 First February nafara wannan littafin Allah ka k'addareni dagamashi lafiya AMEEN YA ALLAH_

Free 🅿️6to10

          Bakowa palourn daya shiga direct yawuce bedroom d'insa ya shiga wanka, bayan yafito yashirya tsaf cikin uniform d'insu na police, Mai fari da Baki yayi kyau Sosai farin gilas d'insa daya zamemasa jiki sashi ya d'auko yasa,  manyan takalmi rufaffi yasaka yafito, Kan daning table ya hangota tana had'a Abinci,

Da murmushi Kan fuskarsa ya k’arasa wurin tareda rungumarta tabayanta cikin sanyin muryarsa yace”Matar D.S.P ANNUR Yau tamakara Bata shirya mijinta da hannunta ba, kusan shine Kawai yayita wahala., zantafi Aiki dear,”

         Maida masa martanin murmushinsa tayi kafin tace"Amun Afuwa kada Asamin Hancock hannayena ciwo suke *D.S.P ANNUR* yamun Uzuri, Ah zauna kayi breakfast tukuna dan nasan da kabar gidan nan sainayi missing d'inka kafin nasake ganinka"

Tak’arasa maganar tana janyosa Kan kujerar daning table d’in.

    Zama yayi Yana rik'e da hannunta still Yana k'ok'arin d'aurata kan cinyarsa Yace," Ai Hancock Bata isa taje hannun Matar ANNUR ba Allah yakare faruwar hakan ma, Ah bazan jimaba ai, Kinga nayi letting fita fa,"

   "Koma yaya ne sai mijina yacika cikinsa zai fita"

Mik’ewa tayi Kan cinyarsa tayi seving d’insa dakanta tacidashi Saida ya k’oshi sannan tabarshi

"Mijina kayi Kyau da yawa, kamar na sauya maka uniform" tak'arasa maganar tana D'an tsuke fuska

“Hahhhh kishin ba, Kinga saina dawo kimin Addu’a,”

“To mijina Allah yatsare munkai Dama da hagunka yarabaka da shairin mutum dama Aljan kadage gun Nemo halak kabar Haram banda danne gaskiya kabi k’arya koda yaushe kaji tsoron Allah kaji D.S.P ANNUR,”

“In Sha Allah my dear zanyi dik Abunda kikace, ki kula da gida da Umma dama ke kanki banda yawo fa,” saina dawo

   "Baka jiba mijina"

“Oh my dear meye nayi letti fa”

Taku uku tayi tasa meshi kiss maitsayawa Arai tamasa daidai kan zuciyar sa kafin tajuya Takoma ciki tana fad’in “Allah yakai lafiya”

Murmushi maikyau yasaki tareda shafar saitin zuciyar tasa yana murmushi,
Ficewa yayi cikin sauri saida yabiya ya fad’ama Umma sannan yawuce.

 Motarsa maik'yau madaidaiciya yahau tareda nufar gun Aikin nasa,

Yana shiga inda Aka tanada don parking Yayi, yafito Sauran y’an sandan suka Fara Sara masa suna gaisuwa,

D’aga musu hannu Kawai yayi yashiga office d’insa

Files d’in dake Kan table d’in yafara Aiki kansu,

“Assalamu’Alaikum ogarh Yanzu wata mata takiramu Tace urgent call wata budurwa tasamu hatsari inda motar ta kama da wuta cikin ikon Allah dai munje Kuma Matar bata mutu ba Saidai kamar tanason fad’ar Wani Abu Saidai Sargent lulwanu ya hana mushiga ganin nake kamar da lauje cikin nad’i ogerh”
Saida yayi k’asa da murya sannan ya fad’e maganar

Sanin halin waye Sargent lulwanu yasa Annur fara wani nazari Domin lulwanu Akwai handama rashin godiya indai kan kud’i ne ba Abunda bazai iyayi ba,

“Wace Asibiti Aka kaita,”?

dawoma specialist kuma ogerh y’ar talakawa ce ga Alama, Ina ganin Kamar da saka hannun wani cikin hatsarin Nan”

 "Kada kadamu copur sale, Yanzu muje can dan sanin wasu mahimman Abubuwa, muje ka d'auko motar,"

“Angama ogerh”

Basu Jima sosai ba suka isa wurin

Sanin waye D.S.P ANNUR hakan yasa bawani janjani Aka barshi Yashiga

Sau d’aya ya kalle yarinyar baisake kallon taba Domin ba k’aramin Jin jiki take ba,

Cikin dakewar zuciya ya matsa kusa da ita Ahankali yace”sannu shin kozaki iya fad’amun Abunda ya sameki,”?

 Cikin tsananin Azaba tad'an janyo wata takarda tajefar k'asa,

Duk’awa yayi ya d’auko tamkar rame Haka yaga zane jikin takardar bayan zanen ba Komai

Idansa nakan takardar yana nazarin zanen kawai saiyaji k’arar fad’uwar Abu d’agowar da zaiyi yaganta k’awance kasa Tana fad’in

“kabinciko gaskiyar kada kabari mutuwar mu tatafi Abanza kada kabari suci gaba da Aikata badaidai ba kaceci sauran mutane D.S.P ANNUR Kataimake ni Anwar wayyoo zanmutu kanemo Adalci da……..,”

Mak’alewa maganar tayi saboda numfashin ta daya fara tserewa,

Shikuwa kasa komai yayi tamkar mafalkinsa Haka yakejin sautin maganar yarinyar

Dafe kansa dake juya masa Yayi k’okarin tina wani Abu yake Amma sam yakasa kalma d’aya ke Kai komo A k’wak’walwarsa “Kada kabari mutuwata tatafi Abanza kabinciko gaskiyar d’ana ANNUR, ya ANNUR Kataimake ni zanmutu wayyoo” tiffff tafad’a ramin

Luuuuu yayi baya zaifad’i amma da taimakon mahaifin yarinyar ya tareshi Saidai dik da hakan yajima da somewa

Cikin sauri Aka d’auke yarinyar tariga ta mutu,

Dole Aka koma Kan Annur k’arin ruwa Aka masa inda Aka bashi gado, su copur ne suke tare Dashi

Iyayen yarinyar kuwa d’aukar gawar sukayi sukatafi da ita,.

 *AFTAR SOME HOUR'S*

Ahankali yafara bud’e idanuwansa

“Sannu ogerh ka falka Allah yabaka lafiya Bari nakira doctor” cewar copur cikin sauri yafita

Kansa ke masa ciwo Wai meke faruwa dashi ne Kodai Yanada tab’in k’wak’walwa ne?

Shigowa sukayi sauran suna masa sannu

Doctor d’in yace”sannu ranka yadad’e dakwai inda ke maka ciwo ne,”

"Doctor Ina yarinyar kada kacemin itama tamutu,"? Tanbayar da Annur yajefawa doctor Kenan

  Sauke Ajiyar zuciya doctor d'in yayi Kafin yace"sai hak'uri yallab'ai dama ai mutuwa tana Kan kowa"

“In shout dai itama ta mutu,”?

“Eh yallab’ai”

“Meye hak’ik’anin gaskiyar Abunda ya sameta,”?

Shuru Doctor d’in Yayi Domin Idan Bai mantaba Ankirashi A waya kuma Anmasa gargad’in fad’ar gaskiyar Abunda ya sameta had’ida barazanar fad’ar gaskiyar Abunda ya sameta.,

Cikin D’an dakewa yace”ha… hatsari ne kawai yallab’ai,”

Yana gama fad’ar hakan yayi saurin barin d’akin

Mik’ewa zaune Annur yayi tareda zare k’arin ruwan Yana fad’in”muje copur sale Amma koma meye da Abunda doctor yab’oye,”

“Amma yallab’ai bakada lafiya ai,”

“Kaidai muje gidansu yarinyar kawai”……………………………………….

   _BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍_

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948

[2/2, 10:29 PM] My Number: D.S.P ANNUR.💫
PAID BOOK #300 ONLY

*FEBRUARY (2)  2023*

 _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA (18) SAURAYINA (19 D.S.P ANNUR PAID BOOK..==..... And Other's BUT NOW (19) D.S.P ANNUR PAID BOOK..... loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱

      _Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken *D.S.P ANNUR.* Ina fatan yabada darussuka ga kowacce macce Kai hardama mazan baki d'aya Allah ka k'ara shiryamu dukanmu_

   *INAYIN LITTAFAINA BADAN NEMAN SUNA KO D'AUKABA KAWAI INAYINE DOMUN BADA DARASI DA FAD'AKAR DA AL'UMMA BAKI D'AYA....... AKODA YAUSHE ALK'ALAMIN MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 BAYA RUBUTA SHIRME KO BATSA KO LALATA RAYUWAR AL'UMMA SAIDAI INA K'OKARIN WAYAR DA KAN AL'UMMA DAMA DAWO DAMU KAN HANYA MADAIDAICIYA ALLAH KA TSAREMU DA AIKATA AIKIN DANA SANI.. INASONKU MASOYANA ADIK INDA KUKE NID'IN CE DAI TAKU HAR KULLUM MAISON GANIN FARIN CIKINKU MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱*

 *Kwanaki sai gudu suke shekaru sai shud'ewa suke inda mutuwa take riskar kowanne bawa, Rayuwa sai ficewa take inda mutuwa tana maye gurbinta, ya Allah 🙏 kajik'anmu tinkan mukoma gareka, ya Allah kasomu kasa Asomu, ya Allah kaimuna k'arshe Mai kyau 👌, Allah karabamu da MAK'IYAN mu na fili dana bayyane, ya Allah Wad'anda suka rigamu komawa gareka Allah kajik'ansu kaimusu gafara ya Allah,. Ya Allah kaimuna maganin Wad'annan masifun da fitintinun, Allah kabamu zaman lafiya da Arziki Mai Amfani, ya Allah Kashiga tsakanin nagari da mugu, ya Allah kabamu shuwagabanni nagari masu tsoron Allah wad'an da zasu dakatar da Wannan b'arnar da Ake Aikatawa,ya Allah kaimuna maganin Wannan tsananin damuke ciki, Ya Allah kashiryemu, ka Kare Idanuwanmu daga kallon Haram, ya Allah katsare hannuwanmu daga rubuta had'ida rubuta Haram, Ya Allah katsaremu da cin Haramun.... Ya Allah Idan mutuwar mu tazo Kasa mucika da imani tareda kalmar=====LA'ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADU RASULILLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM=== ALLAHUMMA AMEEN YA ALLAH🤲🤲*

 _Yau 1/2/2023 First February nafara wannan littafin Allah ka k'addareni dagamashi lafiya AMEEN YA ALLAH_

Free🅿️11 to 15

_Littafin nak'udi ne kidaure kibiya sannan kisamu dika complete 300 ne kawai ba yawa_

 ...........Koda suka Isa gidan har Angama jana'izar ta mutane ne kawai zaune sai sauran y'an uwanta,

Fitowa sukayi daga motar suka k’arasa wurin, cire takalminsa yayi bayan sungaisa ya zauna,

    "Baba ya hak'uri"

“Alhamdulillah mungode Allah kaima ya naka jikin,”?

“Da sauk’i gajiyar Aiki ce kawai, in ba damuwa baba kozan maka wata tanbaya,’?

   "Inajinka"

"Shin ita wannan matashiyar da Allah yak'arb'e Ranta tanada Abokan gaba ne,"

  "A'a ko d'aya yallab'ai Domin Ramatu yarinya ce wadda baruwanta da sha'anin kowa, Abinda yafi komi bani mamaki Wai motar ta takama da wuta bayan bama motarta bace ta k'awarta ce kuma sai ita k'ad'ai zata mutu yallab'ai,"

Kuka yasa Yana share hawayen sa,

Jikin Annur yayi sanyi baison ganin kukan kowa Koda na yarone Balantana babba tsoho kamar wannan,

“Baba kayi hak’uri Allah yajik’anta da rahama yabaku hak’uri, Amma in sha Allah indai da sa hannun wani A mutuwar tata to kowaye saina gano kuma za’a hukuntashi, Amma baba saikunyi hak’uri da yawan tanbayoyin mu, Yanzu dai zamu barku kuji da mutane amma zamu dawo ko kuma kunemomu sannan dazarar kunsamu wani evidence to kunemeni ga number ta,”

Mik’awa baba card d’insa yayi sannan yawa sauran mutanen sallama suka wuce,

“Ogerh Nima na fahimce wani Abu Kan labarin Anya ba saka hannun k’awarta? Kuma Ina zata sannan Taya takasance ita k’ad’ai,”?

 "Kanada gaskiya Sargent kasan me?  yarda Naga motar ba hatsari bane kawai An samata wuta ne, Amma Abun tanbayar Anan meya fidda yarinyar da Wannan Lokacin? Tayaya girman Alak'arsu take da k'awar ta ta? Aikin me yarinyar take,"?

“Eh Tabbas Hakane ogerh Amma Meyasa baka tanbaye mahaifinta ba yanzu,”?

“Saboda Yana cikin Wani yanayi mutuwar ta ratsashi Amma inason nasaka Ido kan wannan doctor d’in,”

 "Yallab'ai Ina zamu Yanzu gida Zan saukeka nawuce da motar ko,"?

"No banason komawa yanzu batareda na bud'a file Kan Wannan Case d'in ba,"

“Amma ogerh kabari sai gobe mana ko kaje da file d’in gida yanzu fa k’arfe 7:30 Dare ya Fara Kuma Anfara Kiran magarib, sannan bakada lafiya”

.

“Nasani sagent kawai kayi Abunda nace ban motar katafi Abunka kawai kai,”

"Sanin waye ogerh d'insa yasa bai sake magana ba,  Yana Kai kansa gida ya tsaya ya sauka yabashi key d'in motar Yana fad'in "Allah ya tsare ogerh" yawuce

         Saida yafara shiga masallaci yayi Sallah sannan yakoma office, file ya d'auka yafara rubutu Akai,

Yajima Yana nazarin Case d’in sannan yafito sukayi sallama da masu night duty yafice. masallaci ya tsaya Dan gabatar da Sallar Isha,.

"Ke khausar kina nan kina bacci Abinki ko? Lalle yaran zamani ba'asan Ciwon kaiba Ace mijinka yafita tinsafe har dare baidawoba Amma har kikeda idanuwan bacci"

Mik'ewa tayi daga baccin da yafara d'aukar ta, bugun k'ofar da fad'an da Umma keyi yatada ta,

K’arasowa bakin k’ofar tayi tana fad’in”A’a wallahi Umma bansan baccin ya d’auke ni bane Ina k’arasa sallah ko tashi banyi ba baccin yafara fisgata,”

 "Ke dalla can shasha Ai Dole kiyi bacci tinda bakisan zafinsa ba," Mtswwww dogon tsaki taja tareda barin wurin,.

  Zama d'aya daga cikin kujerun palourn tayi tana zabga tagumi itadai bata san me ta tarewa uwar mijinta ba Kullum cikin masifa take koda laifin ko babu, gasu gida d'aya da babbar Aminiyarta Kuma Matar Abokinsa amma bata Bari taje can parts d'insu Humaira danyin fira, gwandama kwanakin baya Humaira d'in tana Yawan zomata Ayanzu basunan mijinta yaje k'arin karatu a Dubai Anan tahuta da mitar Umma itakam gatanan tana fama, 

Duba Agogon bangon tayi ya buga k’arfe 11:00 inda sabo yaci Ace tasaba da halin Annur Amma Koda yaushe tanajin zafin jimawarsa waje,.

 Umma Nata babbaka fad'a tadawo wajen Balcony d'in tazauna itak'adai sai maigadinsu datake hangowa Yana zaune danshikam badai bacci ba yanata kora shayinsu na buzaye,.

Shikuwa bayan fitowarsa daga masallacin yaji k’arar shigowar sak’o bud’ewa Yayi yaga sak’o Kamar haka……

“”” D.S.P ANNUR Kada Kashiga hurumin da banaka ba domun rawar kanka yafara yawa kada Kashiga Abunda ba ruwanka itama haka tayi saita fuskance hukuncin mu ka kula””””

Yajima yana maimaita karanta sak’on tareda k’arfin halin Kiran layin Amma switch off

Dik k’okarinsa ganin yasami wani Abu Akai Amma baisamu ba,

Towaye wannan kuma????

Nidai Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 banace ba ina tare dakai fa nida readers

Anan ne yak’ara b’ata Lokaci, duba wayarsa yayi ganin 11:00 Saida zuciyar sa tabuga sanin Yashiga hakken Matar sa, ga mahaifiyarsa da komai dare Bata bacci saiya dawo, Abu d’aya yatuna hankalinsa ya kwanta shine gobe Saturday Yana gida,. Da saurin Yashiga motarsa yanufe gida.,

 Ranta yafara b'aci da suya Hawaye suka soma zarya Kan fuskarta ko Abinci Bata iya ciba gashi wayarta tafashe kusan kwana biyu kenan tanata binsa Amma yak'i siyo mata,.

Hong yayi Aka bud’e masa Yashiga ganin Umma waje yasa cikin sauri yak’arasa har k’asa ya tsuguna Yana gaidata

“Meya tsaidaka haka Babana bayan kasan kanada mak’iya,”?

“Wallahi Ummana wani sabon Case muka samu Wanda yake hannuna shiyasa,”

“To babana Arik’a kulawa Allah yataimaka Saida safe kaje kaci Abinci, ka kwanta dare yayi Sosai,”

 "To Ummana Allah yatashemu lafiya ga Wannan" leda ya Bata ta Ansa tana masa Addu'a tawuce

Komawa mota tayi yad’auko d’ayan ledar Yashiga nasu part d’in,

    Haske dik ya gauraye palourn Amma baiganta nan ba,

Rufe k’ofar yayi Yana sallama had’ida k’arasa Shiga palourn

Ansa sallamar tayi kafin tace"sannu da zuwa, ga Abincinka can Kan daning"

Tana ida maganar tawuce d’akin ta

Kasa matsawa gaba Yayi Balantana baya, saka makon ganin Hawaye Kan fuskarta muryarta ma ta tabbatar masa Tasha kuka yau d’in,

Wurin dining yaduba Abincin Yana Nan da yawansa hakan ya tabbatar masa da bataci Komai ba Kenan………..

_Kuyi hak'uri wallahi Inada matsalar idanuwa_

BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948
[2/4, 9:01 AM] My Number: D.S.P ANNUR.💫
PAID BOOK #300 ONLY

*FEBRUARY (2)  2023*

 _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA (18) SAURAYINA (19 D.S.P ANNUR PAID BOOK..==..... And Other's BUT NOW (19) D.S.P ANNUR PAID BOOK..... loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱

      _Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken *D.S.P ANNUR.* Ina fatan yabada darussuka ga kowacce macce Kai hardama mazan baki d'aya Allah ka k'ara shiryamu dukanmu_

   *INAYIN LITTAFAINA BADAN NEMAN SUNA KO D'AUKABA KAWAI INAYINE DOMUN BADA DARASI DA FAD'AKAR DA AL'UMMA BAKI D'AYA....... AKODA YAUSHE ALK'ALAMIN MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 BAYA RUBUTA SHIRME KO BATSA KO LALATA RAYUWAR AL'UMMA SAIDAI INA K'OKARIN WAYAR DA KAN AL'UMMA DAMA DAWO DAMU KAN HANYA MADAIDAICIYA ALLAH KA TSAREMU DA AIKATA AIKIN DANA SANI.. INASONKU MASOYANA ADIK INDA KUKE NID'IN CE DAI TAKU HAR KULLUM MAISON GANIN FARIN CIKINKU MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱*

 *Kwanaki sai gudu suke shekaru sai shud'ewa suke inda mutuwa take riskar kowanne bawa, Rayuwa sai ficewa take inda mutuwa tana maye gurbinta, ya Allah 🙏 kajik'anmu tinkan mukoma gareka, ya Allah kasomu kasa Asomu, ya Allah kaimuna k'arshe Mai kyau 👌, Allah karabamu da MAK'IYAN mu na fili dana bayyane, ya know Wad'anda suka rigamu komawa gareka Allah kajik'ansu kaimusu gafara ya Allah,. Ya Allah kaimuna maganin Wad'annan masifun da fitintinun, Allah kabamu zaman lafiya da Arziki Mai Amfani, ya Allah Kashiga tsakanin nagari da mugu, ya Allah kabamu shuwagabanni nagari masu tsoron Allah wad'an da zasu dakatar da Wannan b'arnar da Ake Aikatawa,ya Allah kaimuna maganin Wannan tsananin damuke ciki, Ya Allah kashiryemu, ka Kare Idanuwanmu daga kallon Haram, ya Allah katsare hannuwanmu daga rubuta had'ida rubuta Haram, Ya Allah katsaremu da cin Haramun.... Ya Allah Idan mutuwar mu tazo Kasa mucika da imani tareda kalmar=====LA'ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADU RASULILLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM=== ALLAHUMMA AMEEN YA ALLAH🤲🤲*

 _Yau 1/2/2023 First February nafara wannan littafin Allah ka k'addareni dagamashi lafiya AMEEN YA ALLAH_

        _SECOND TO THE LAST FREE PAGE IN SHA ALLAH_

Free🅿️16 to 20

         .... Tabbas Yasan khausar tanada hak'uri Kuma tanada juriya kusan shekara 2 da Auren su Amma baitab'a ganin fushin taba koda Ranta yab'aci takan danne Domin kawai nemamasa nasa farinciki gashi sama da shekara d'aya da mutuwar iyayenta yakan tausaya mata Sosai, gashi wannan Aikin nasa ya Hana yabata farinciki yau harta Kai ganuna fushinta,

Cikin sanyin jiki yak’arasa bakin k’ofar d’akin ya tura Amma rufe d’akin,

Jiyo sautin kukanta yayi jikinsa yak’ara sanyi,

Cikin sigar lallashi yace”My dear Dan Allah kiyi hak’uri ki bud’e k’ofar kinji,”

Shuru batako motsaba kawai tacigaba da kukanta ne Domin shine Kawai zatayi tasami salama Aranta

“Matar D.S.P ANNUR kada kiyi fushi da gudan jininki mana nasani ban kyauta ba Amma Dan Allah kiyi hak’uri ki bud’e k’ofar kinji, idan baki bud’e ba, nikaina bazan samu salama ba, Kuma bazanci Komai ba,”

   Cikin muryar kuka tace"katafi karabu Dani tinda Aikinka yafini mahimmanci, saboda Allah ANNUR Ace kafita tinsafe Wai har 11:30 zuwa 12:00 sannan zaka dawo bayan kasan kanada Mata fisabilillah kamun Adalci? Gashi Wannan wayar ma kak'i siyamun bayan kanada Arzikin siyenta, Kuma Koda yaushe kada kifita bawanda yake zuwa Inda nake Tinda Nima bana zuwa why Annur 

Idan kadaina Sona kawai ka sallameni na k’ara gaba Wallahi Nagaji Annur,” kukan da yaci k’arfinta ne yasata yin shuru.

Rawa jikinsa ya d’auka idan da Abinda yafi firgitashi baiwuce Ace yarabu da Khausar ba Yana Mata sonda shikanshi baisan Adadin shiba,

“Naji nad’auke laifuka na, kitaimaka ki bud’e kada muyi kwanan bak’in ciki kinji my wife”

Ganin batada niyar bud’ewa yasa yakoma Kan kujerar palourn ya zabga tagumi Kansa har wani ciwo ciwo yake masa,

Wata dabarar ta fad’omasa da saurin yamik’e yashige d’akinsa baijima ba saigashi Yasake fitowa d’auke da tarin makullai a hannunsa yazo yafara gwadawa cikin sa’a kuwa yasamu d’ayan yayi take d’akin ya bud’e da sauri Yashiga ciki, cikin sauri yak’arasa Kan gadon Yana janyota jikinsa,

K’okarin fisgewa take tana fad’in”karabu Dani Ni ka k’yaleni Annur”

Ganin batada niyar tsayawa yayi saurin had’e bakinsu guri d’aya,

Zazzafan kisses Yashiga aika mata tako ina hannayensa kuwa suna neman mafaka cikin rigarta inda Still bakinsu Yana had’e,.

Mutsu mutsu take tana neman k’watar kanta Amma takasa saboda ba k’aramin rik’o yamata ba,

Kuma gashi yajima Bai nemeta ba, shiyasa dik yawani haukace mata,

Still Bata daina neman k’wace kanta ba dik da itama tana buk’atarsa Amma yau saita nuna fushinta dole ya gyara,

Da k’arfi tasamu ta tureshi Takoma palourn ta zauna kan kujera tana maida numfashi,

Had’ida share hawayenta Domin yaune Karo na farko Data hanashi hakkensa.

Tana fita d’akin ya kwanta Saboda wani wahallen ciwo da mararsa tafara masa, yajima kwance kafin yasami relief, yasani yakaita mak’ura ne shiyasa

Ahankali yafito Kan kujerar ya hangota zaune tahad’a Kai da guywa tana kuka

Cikin sanyi ya matso inda take had’ida yin Neel down da guywarsa k’asa Yace cikin wani irin murya”kiyi hak’uri kidaina kukan tashi kici Abinci please banason kukan”

Batace Masa Komai ba Kuma Bata motsa ba

Mik’ewa Yayi ya d’auko Abincin yazuba dakansa yakai bakinta

Kaucewa tayi tareda cewa”nafa k’oshi Kuma ga dare yayi Ina Jin bacci,”
Mik’ewa tayi danufin barin wurin Amma saitaji yarik’o hannunta had’ida Mata nuni data zauna,

Ba musu ta zauna
Abincin yahau bata saida ya tabbatar ta k’oshi sannan ya d’auke ta cak Kamar yarinya yakaita kan gadon had’ida rufa mata barko sannan Yashiga tolet tanajinsa yayi wanka harya shirya sannan yazo ya kwanta Kan gadon, baimata Komai ba dan ya fahimce fushi take Sosai Dashi

To ASSUBAH TAGARI nidai Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 nayi
Nan….

**************

“Ranka yadad’e Allurafa na Shirin tono garma dan wallahi shegen yaron Nan yanason ganin bayanmu”

     "Habadai Alhaji Musa kada k'aramin k'waro ya d'aga maka hankali mana, mema zaiyi wai,"

“A’a fa tanimu wallahi nikaina gani nake da matsala, yaron Nan baida tsoro gashi da yawan ibada ga matar Nan tasa itama Kullum cikin ibada Tayama zamu kaishi k’asa,”

 "Yarda muka Kai mahaifinsa da y'ar uwarsa Haka shima zamu kaishi" cewar Alhaji sani

“Amma kuwa idan har munason yin wannan nasarar to Dole mufara rabashi da matarsa,” cewar Alhaji tanimu

“Hakane maganar ka Domin kuwa itace lagonsa, Dan Haka zamusaka A satota kuma muyi tsafi da ita,” cewar Alhaji musa

Dariya Suka saka gabaki d’ayan su had’ida watse zaman..

Tawagar matsafa kenan, Alhaji musa, sani, tanimu sune babbar tawagar sai Sauran Abokan San duniyarsu,

Sunriga sunb’ace da neman duniya cikinsu wasu sunbada y’ay’ansu wasu sunbada iyayensu wasu matansu dadai sauransu,

Mutuwar Humaira ma kusan sune silar kwashe jininta wanda da taimakon k’awarta Hajara, Wanda ba Wanda yasan Hajara tana cultism koda kuwa y’an gidansu….

Hajara tinda ta bud’e Ido taga Annur taji mugun sonsa Aranta shikenan tafara neman tsafaceshi Saidai tarasa damar hakan saboda baya wasa da ibada, Amma tayi nasarar wargaza bincikensa kansu Wanda dik tamantar da kowa Kan Case d’in………..

kuyi manage banada chagy Wallahi

    _BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍_

   WhatsApp group 07064904617 or call 07031012948

D.S.P ANNUR.💫
PAID BOOK #300 ONLY

*FEBRUARY (2)  2023*

 _RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱..._

MARUBUCIYAR... (1)Fahat hot-luv Free book, (2) Barrister khalee Free book, (3) Zuciyar namiji Free book, (4)Saina kashe mijina Free book, (5) Akan pre-wedding pictures free book, (6)Shagala Free book, (7) Silar d'a namiji Free book, (8) Maizaman kanta paid book, (9) Abbakar sarakeey paid book, (10) doctor Heesham paid book, (11) jinin Mulki paid book, (12) Bak'in kishi paid book, (13) Raunin macce baya hana d'aukar fansa free book. (14) ZAYYAN 💞 ZEEYAT PAID BOOK. (15) MAKARANTAR KWANA FREE BOOK. (16) SHAGALA FREE BOOK,, (17) SO SIRIRIN ZUCIYA (18) SAURAYINA (19 D.S.P ANNUR PAID BOOK..==..... And Other's BUT NOW (19) D.S.P ANNUR PAID BOOK..... loading..... Dika na Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱

      _Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah mad'aukakin sarki Mai bayarda baiwa gawanda yaso Kuma sanda yaso Ina godiya ga Allah Allah daya sake bani dama had'ida baseerar sake kawomuku sabon littafina maitaken *D.S.P ANNUR.* Ina fatan yabada darussuka ga kowacce macce Kai hardama mazan baki d'aya Allah ka k'ara shiryamu dukanmu_

   *INAYIN LITTAFAINA BADAN NEMAN SUNA KO D'AUKABA KAWAI INAYINE DOMUN BADA DARASI DA FAD'AKAR DA AL'UMMA BAKI D'AYA....... AKODA YAUSHE ALK'ALAMIN MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱 BAYA RUBUTA SHIRME KO BATSA KO LALATA RAYUWAR AL'UMMA SAIDAI INA K'OKARIN WAYAR DA KAN AL'UMMA DAMA DAWO DAMU KAN HANYA MADAIDAICIYA ALLAH KA TSAREMU DA AIKATA AIKIN DANA SANI.. INASONKU MASOYANA ADIK INDA KUKE NID'IN CE DAI TAKU HAR KULLUM MAISON GANIN FARIN CIKINKU MUJAHEEDAH MATAR MLM AMMYN KHAUSAR 🤱*

 *Kwanaki sai gudu suke shekaru sai shud'ewa suke inda mutuwa take riskar kowanne bawa, Rayuwa sai ficewa take inda mutuwa tana maye gurbinta, ya Allah 🙏 kajik'anmu tinkan mukoma gareka, ya Allah kasomu kasa Asomu, ya Allah kaimuna k'arshe Mai kyau 👌, Allah karabamu da MAK'IYAN mu na fili dana bayyane, ya know Wad'anda suka rigamu komawa gareka Allah kajik'ansu kaimusu gafara ya Allah,. Ya Allah kaimuna maganin Wad'annan masifun da fitintinun, Allah kabamu zaman lafiya da Arziki Mai Amfani, ya Allah Kashiga tsakanin nagari da mugu, ya Allah kabamu shuwagabanni nagari masu tsoron Allah wad'an da zasu dakatar da Wannan b'arnar da Ake Aikatawa,ya Allah kaimuna maganin Wannan tsananin damuke ciki, Ya Allah kashiryemu, ka Kare Idanuwanmu daga kallon Haram, ya Allah katsare hannuwanmu daga rubuta had'ida rubuta Haram, Ya Allah katsaremu da cin Haramun.... Ya Allah Idan mutuwar mu tazo Kasa mucika da imani tareda kalmar=====LA'ILAHA ILLALLAHU MUHAMMADU RASULILLAHI SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM=== ALLAHUMMA AMEEN YA ALLAH🤲🤲*

 _Yau 1/2/2023 First February nafara wannan littafin Allah ka k'addareni dagamashi lafiya AMEEN YA ALLAH_

  _LAST FREE PAGE 21 TO 30 IN SHA ALLAH SATURDAY 4/2/2023 FEBRUARY_

PAGE 🅿️ 21 to 30

            ......"Sanin kinason Anwar shiyasa mukeson kimana Wannan Aikin," cewar Alhaji tanimu

"Taya kake tinanin nida kaina zanbada gudun muwar cutarda Abunda nakeso,"? Cewar Hajara

“Maganar banza kike wane irin jind’ad’i ne bamu bakiba, ke yanzu Dan munzo neman buk’ata gareki saiki k’i? Wallahi Baki isaba Hajara kokibi umarnin mu komu kasara hadda Taki rayuwar Domin a tsarin k’ungiya ba Wanda ya isa yamuna taurin kai,”

“Wallahi Koda zaku kasheni bazan Bari wani Abu yasami Annur ba Amma zanbada gudun muwa wurin ganin Anhallaka matarsa Amma bandashi,”

“Kunga enough eh munason kishiga aikin wurin samun dam shiga cikin jikin matarsa harta yarda dake daga saiki Sato Mana ita zamu hallakata inda ke Kuma saiki Samu Annur d’in,” Cewar Alhaji musa

“Amma Alhaji musa Bai,”…………..

D’aga masa hannu yayi Alamar dakatarwa kafin yace” nine shugaban nagama magana Hajara zaki iya tafiya,”

“To Shugaba Nagode Kuma Nanda kwana biyu Aiki zaiyu” ficewa d’akin taron tayi

“Sainake ganin Kamar kayi kuskure idan kaduba D.S.P ANNUR mukeson kaiwa bawai matarsa ba Amma meyasa zaka yanke hukuncin barin shi bayan kasan muddin Yana raye burinmu bazai tab’a cikaba,”

“Matsala tadakai k’wak’walwar ka bataja, shin Taya mukaga bayan mahaifinsa Bata hanyar yudara ba? Taya muke neman zautashi da mugayen mafalkai? Babbar matsalarmu matarsa Domin Koda yaushe itace ke d’aurashi kan hanyar Ubangiji, yayinda zamucigaba da sakawa mahaifiyarsa nauyin Baki kada tafad’a Masa komai, itakuwa Hajara muda kanmu zamuga bayanta Domin dodo zamuba jininta data Gama muna Amfani,”

Shek’ewa da dariya sukayi suna Amanna da shawarar shugaban nasu,”

Sam baisamu bacci Daren jiya ba Domin damuwa tarufesa nafarko fushi da matarsa take dashi na biyu dik yamanta komai case d’in Yana k’ok’arin Tina wani Amma yakasa Tina Komai, Yana Haka har Akakira Sallar Assubah yamik’e Yana watsar da tinanin Dan kansa yafara Ciwo

Bayan yagama shirin zuwa masallaci ya tadata tayi Sallah shikuwa yafice masallaci,.

Saida haske yafara bayyana sannan yadawo gurin mahaifiyarsa Yashiga Suka gaisa

Kallansa tayi Tace”Wai meke damunka Babana cikin kwanakin Nan dik kabi ka rame musamman daga jiya zuwa yau,”

Gyara Zama yayi Yace”Amma Umma nakai mizanin da zansan gaskiyar labarin Abunda yasami babana da k’anwata,”

Shuru tayi kafin tace”sanin komai baida mahimmanci gareka Domin Wanda ya mutu bazai dawoba babanka yariga ya mutu,”

“To waya kashe su Wai? Meyasa nake ganinsu A mafalkaina? Wai Kodai inada tab’in k’wak’walwa ne,”?

“A’a babana bako d’aya Amma nikaina narasa dalilin kasa fad’a maka Amma dai kacigaba da Addu’a sannan Nan kusa gaskiya zata bayyana,”

 "To Ummana Allah yasa," barin part d'in yayi yanufo nasa 

Tagama shirya daning tana kitchen tana wanke-wanken kayanda ta tab’a tajiyo shigowar sa har kitchen d’in da sallama

Ansawa tayi batareda tajuyo ba Tace “sannu da dawowa”

Baiyi magana ba yak’arasa inda take had’ida rungumarta ya d’aura kansa Abayan ta,

“I’m really sorry my love, kidaina ignoring d’ina nakasa jurewa,”

Ita kanta tana Azabtar da kanta ne gashi tanajin wani iri Ajikinta

D’aura hannayenta tayi Kan nasa tace,”shikenan yawuce mijina na hak’ura kaima kayi hak’uri kaji,” tak’arasa maganar tana shigewa jikinsa

Murmushi Maisauti yasaki had’ida sunbatar goshinta sannan Yace” bakimin komai ba my dear nine da laifin Kuma Ina dad’a bada hak’uri,”

“To na hak’uri yanzu sakeni nakaiwa Umma Abinci nadawo muci namu ko,”?

  "Bani kawai Zan kaimta kishiyar namu,"

“To ai bangaisa da Umma d’in ba kabari naje,”

“Zakije ne ai yanzu dai Ayi Abunda nace kawai,”

“To yallab’ai,”

“Hahhhhhhhh yallab’ai nadawo Kuma” ya Anshe Abincin ya kaimata

“Au babana Kaine kadawo mai yawon kawomin Abincin,”?

Yana Sosa Kai yace,”a’a Ummuna kawai ganin Aikin dayawa ne shiyasa nace tabari nakawo Amma zata zo ai,”

“Allah ya kyauta, nidai nafara Gajiya yarinya batako Haihuwa nagaji da zama da ita wallahi,”

Shuru yayi baice Komai ba Saida tagama fad’an sannan yamik’e yafice

      Wannan shine mak'asudin tsanar Khausar da Umma tayi ganin shekara 2 Bata Haihuba,.

Bai nunamata Komai ba tareda ita sukaci Abincin suna gamawa yace”jeki shirya kid’an rakani wani gun,”

Cikin Murna Tace,”dagaske mijina yau Dani zaka fita,”

Yana murmushi ganin Murna kan fuskarta Yace”Sosai kedai Yi sauri Kona tafi na barki,”

“Ah Yanzu zanzo my dear”

Cikin k’ank’anen lokaci harta tashirya saidama tajirashi

Kalan dressing d’in ta yayi shima farin yadi yasaka sunyi kyau

Tare suka fito suka biya Inda Umma

“Ina kwana Umma” Cewar khausar

“Da bankwana ba ai bazaki ganni ba, Wai ma dan walak’anci tin sanda safiyar ta waye sai Yanzu zakizo gaidani, da uwarki ce ai bazakiyi jinkiri ba,”

Kanta nak’asa tace”Dan Allah Umma kiyi hak’uri wallahi nad’an makara ne,”

“Eh lalle ai dole ki makara dama can ke sakarya ce baki Aje Komai ba sai bacci”

Cikin k’osawa da kalaman Annur yace,”Umma Ayi hak’uri baza’a K’ara ba in Sha Allah Yanzu zamu fita ne,”

“Shasha sakarai dik tabi ta dabaibayeka yarinya gata juya ba haihuwa Amma ka kasa rabuwa da ita Nidai nafara gajiya, gangalin ba Ainatafi k’wari , saikun dawo,”

Saurin mik’ewa tayi tafice hawaye na biyo fuskarta

Cikin Azama yabiyota hak’uri ya Fara bata yana lallashinta

Daurewa kawai tayi Amma Abun yamata zafi

Babban mall ya kaisu inda yazab gamata siyayya harda waya

Murna takeyi tana Masa godiya

Daidai hanyar fitowarsu Suka had’u da Hajara,

Ganinsu cikin farinciki hakan ba k’aramin haushi yabata ba, cikin sauri tasaka hannunta jaka tashafo wani magani cikin dabara tayi baya Kamar zata fad’a Kan Khausar cikin saurin itakuma tad’an rik’eta take tasamu damar shafamata wannan maganar ga hannunta

“Ah subhanallah ke lafiya,”? Cewar Anwar Yana rik’o Khausar datayi wani baya Haka Kawai bayan had’uwar jikinsu

“Bakomai yallab’ai kawai fa taimakona tayi, gaskiya kinada kirik’i sister Nagode in badamuwa kiban number ki,”

Wani irin haushi taba Annur taya haka kawai zata buk’aci number ta daga taimako?

“Ah bakomai saidai kiban Taki domun Yanzu muka siye Wayar,”

“To gashi sister Dan Allah kimin magana kinji,”

“In Sha Allah zanmiki nagode”

Wucewa sukayi Annur Yana fad’a kanme zata Bata number ta………………………….

“`HUNMMMMMM YANZU WASAN YAFARA SAIDAI KASH ANAN KUMA FREE PAGE YAK’ARE IDAN KINA KANA BUK’ATAR KASANCEWA DA WANNAN LITTAFIN TO KA HANZARTA BIYAN 300 D’INKA KAWAI DAN SANIN WAD’ANNAN CHAKWAKIYAR…………….

Shin khausar zata Sami cikin kuwa ta fita hantarar uwar mijinta?

Shin D.S.P ANNUR zaisamu damar Sanin gaskiyar?

Shin su Alhaji tanimu zasuyi nasara?

Hajara zata samu cikan burinta na Auran Annur kuwa?

Shin Annur zaisan gaskiyar?

Mezai Aikata idan yasan gaskiyar?

Shin zasu sami nasarar sace matarsa kuwa? Idan sun d’auketa zasu kasheta? Ko zata sira ne?

Wanne Hali Annur zaishiga bayan idan Aka d’auke matarsa?

Shin mesukama mahaifinsa?

K’anwarsa da gaske tananan raye kuwa??

To Nimadai Mujaheedah Matar Mlm Ammyn khausar 🤱 banace ba Domin sani kawai muhad’e a NEXT PAGE da 300 Amma………..

BASEERATA ITACE ARZIKINA 😍

WhatsApp number 07064904617 call 07031012948

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button