Hausa Novels

BANGARE NAH ( part of me)

ALHAMDULILLAHI ALAH KULLI HALIN

Related Articles

wannan labarin na BANGARE NAH labarine mai matukar sarkakiya da kulli dakuma tsantsar cin Amana da zalunci soyayyar karya son abun duniya.. Kuma kagaggen labari ne… Ina fatar zan sami hadin kanku my fans. Kubiyoni damin jin yaya zata kasance

🅿<><><><><><><><><><>1⃣➡2⃣

<><><><><><><><><><><“FCT ABUJA UNGUWAR maitama wani hamshakin gidane na alfarma family mai cike da farinciki da da kaunar juna hajiya SALMA ce zaune acikin kayataccen paloun ta tana kallon labarai a CNN wayarta ce tafara ruri neman agaji

Cikin nutsuwa ta mika hanu ta dauka tare da amsawa…

“Assalamu Alaikum”

Daga dayan bangare tajiyo sautin kuka “Aunty Salma ki taimake ni”….

“Subhanalillah” sister Aisha lafiya?

Cikin kuka tacigaba ki taimakeni yaya salma MUNUBIYAH tana neman tafi karfina tunda ta gama school na rasa gane mata dan ALLAH sister ina son ta dawo gidanki saboda na sami sauki kozata daina wannan halin nata……. Hajiya SALMA cikin sanyin murya ta tasoma magana…..,,

“Kada ki damu sister wannan bazai zama matsalaba” ki bari zan shirya zuwan nata dama ina neman ma taimaki agurin aiki kinga hakan sai yaza kamar tazo cikin sauki”

“Cikin murna tace nagode sister wallahi idan kika yi hakan da kin kyautamun”…….. “Kada ki damu sai mun yi magana ki sanarda ita tafara shiri Alhaji yana dawowa zakiji ni insha Allah”……. “Nagode sister Allah yabar zumunci atare suka ajiye wayar”…….

“Hajiya salma tayi shiru na tsayin lokaci daga bisani tamike tashiga dakinta kwanciyarta kenan bacci mai nauyi ya sace ta”………..

Acikin bacci takuma yin wannan mafarkin dai wanda yazamar mata sabo kullun sai tayi sai dai na yau ya bambanta da kowanne wata kyakkyawar yarinya ce mai matukar kyau ahankali ta ta karaso gurinta cikin maganarta mai dadi tace kada ki damu zan kular miki da yaranki zan warware komai kawai kije insha Allah zan iya sannu ahankali kowa sai ya gane gaskiya ki tafii! Ki tafii! Ki tafii!!! Nace dake, “tamkar haske ta bata tajuya ko ina amma ba kowa sai dai wani katon rami daya ke gaban ta katon gaske sai wata yarinya matashiya wacce shekarunta basu wuce 20years ba fuskarta dishi -dishi ta dage ta hankada ta cikin wannan katon ramin maimatukar duhu”

Tafarka cikin matukar tsoro da firgici “innalillahi’wa’innah ilaihirra’ju’un” gumii duk ya jika mata jiki jagab jikinta yana matukar rawa,
ASHRAB da FARHA suna zaune agefenta mummy lafiya hanu tasanya ta rungumesu tafashe da kuka mai tsuma zuciya ina kaunarku yaranah bana son na rabu daku ina kaunarku sosai

“Maganar tata sai tazoh musu wani iri mummy lafiya Ashrab ta tambaya tare da damuwa itace babba dan haka sai ta tsinci kanta adamuwa farha ganin yayarta cikin damuwa yasanya ta jin wani iri…..

Ta matsa kusa ta kara rungume ta tace muna kaunarki dan Allah ki sanar damu damuwarki kinga yaya Ashrab duk ta damu

“Ta dago takallesu na tsayin lokaci sannan tace ba komai kawai dai mafarki nayi ne kuma irin dai wanda na sabayi sai dai na yau yayi matukar tsoratar dani Amma kada ku damu inafatar bakomai insha Allah”,,,

“Muma muna fatar hakan muma Amma mummy mekike ganine awannan mafarkin naki ne”?

Ta dago mubar zancen Ashrab kutafi kuyi sallah dadyn ku yace zai kira muyi vedio call insha Allah

Cikin farin ciki suka hau ihun murna haka suka fice daka dakin cikin zumudin jiran kiran Abban nasu…..

Karfe 7:00pm dai-dai kiran Alhaji MUSADDIQ yashigo tangameme yar WAYAR hajiya SALMA cikin zumudi suka rankayo dukan su cikin farinciki dady barka da dare ASHRAB tace cikin girmamawa FARHA ma haka sannan hajiya salma cikin sakakkiyar fuskarsa ya yi murmushi ya amsa cikin farin ciki da kaunar iyalinsa ya kk yace cikin farin ciki…… Hajiya taja ajiyar zuciya hummmmm!! Dady muna cikin kewar ka yakamata ka dawo wallahi ina bukatar ka akusa dani……. Cikin kulawa ya amsa( what happened my dear) ,,

Ki sanar dani dear kinsan bana son damuwarki ko kadan “no don’t mind, “insha Allah everting clost to an end,

“what do you mean dear? “”

Kada ka damu my dear when are you coming back?

Gobe zan dawo bazan iya zama ba dear kuna bukata ta gobe jirgin safe zan biyo insha Allah farha ta kwala ihu my dady Tamike tasoma jan shokii dady Allah ya kaimu dama mummy bata hira damu kwanan nan mu kadawo muringa ball wallahi munyi mising ball two days……

Dariya yayi kada ki damu autan dady gobe ma zakiyi ball don’t worry kinji mamanah hajiya Salma tayi shiru tana sauraron su tana kara jin kaunar family dinta cikin ranta…… Can ta tuna da mafarkinta take taji zuciyarta ta tsinke me mafarkina yake nufi ni salma?”

Magana yakeyi amma tayi nisa a tunani hakan ya kara tayar da hankalin Alhaji MUSADDIQ matuka Ashrab ta janye kanwarta farha suka bar gurin ahankali ta dago kayi hakuri wallahi kaina. Ne ya tafi caji cikin murya mai rauni…… “Tabashi tausayi matuka, “dear kina cikin damuwa nafuskanci haka tun lokacin da muka fara waya”……

Hawaye masu zafi suka zubo mata akumatu kada ka damu idan kadawo zamuyi magana diff ta kashe wayar ya mike jikinsa babu kwari

“menene damuwarki dear?

Menene yake barazana da farin cikin ki masoyiyata?….
“Bazan taba samun sukuni ba har saina naga karshen damuwarki”…. “Kiyi Hakuri ina nan tafe gareki” …..

WASHE GARI

tun karfe bakwai Alhaji yabar garin ikko ya nufo Abuja, yayi dai-dai da zuwan MUNUBIYAH gidan saukarta ke nan cikin zumudi ita da yaranta suka rankaya tarbarshi hakan sai ya ya susa munu ganin sunfi nuna zumudin ganin Alhaji akanta 😨too munu inbanda abunki ai Alhaji ne abun marmari bakeba bakuwa😂,

tana zaune tana kalon yanda hajiya salma take zuba shagwabarta agaban yarah batare da jin kunyaba hakan sai ya dasa wani abu azuciyar munubiyah jitayi gaba daya Alhaji yagama tafiya da imanin ta tabbas irin shi ne mafarkinta dan haka zata san abunyi 😨ashe akwai Matsala babbah munubiyah kin manta da matsayinki ne?

To masu karatu sainaji daga gareku

Yawan COMMENT YAWAN TYPING…..

VOTE
SHARE PLSSSSS

TAKUCE LAURAT MUH’D BELLO

💞💕💞💕💞💕💞💕💞

BANGARE NAH
(part of me)

             💕💞💕💞💕💞💕💞💕💞

WRITING BY

LAURAT MUH’D BELLO

DAGA MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH
YA CUTAR DANI
YAR’ZAMANI
(mai kwadayin duniya)

And now

👇

BANGARE NAH
(part of me)

AREWA WRITES ASSOCIATION


💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦


https://www.facebook.com/104534761033461/posts/119016616251942/?app=fbl

ALHAMDULILLAHI

MASOYANAH COMMENT DINKU YANA SAKANI ACIKIN FARINCIKI
INAYINKU IRIN OVER DIN NAN I A LOVE U WUJIGA-WUJIGA💓

🅿<><><><><><><><><><>3⃣➡4⃣

<><><><><><><><><><><“bakin ciki takaici duk ya addabi zuciyar munu ji take kamar ta shake wuyan hajiya Salma kishin ta takeji sosai azuciyar ta tamike tare da yin gyaran murya hajiya ta dago”

“Tana murmushi tace ayyah munu kiyi hakuri na manta da ke kinsan idan dear yana tare dani mantawa nake da kowa, “maganar da hajia
salma tayi takara tunzurah zuciyar munu, ta washe baki na munafurci tace ba komai mummy hakan yanada kyau ai”😁ta washe baki kamar da gaske nan kuwa ita kadai tasan abunda ta ta kudurah aranta”,,

“Toooo😨 Allah ya tsare dai dan fah akwai Matsala”

“Ta kwallawa delu kira, ta zoh cikin gaggawa na’am hajiya tace cikin girmamawa ki nunawa munu dakinta kinji ko, kuje munu idan kina bukatar wani abu ki sanar dani kinji koh kisaki jikin ki,

“Ta kara narkewa ajikin mijinta wanda ganin hakan munu taji kamar zuciyarta ta fito waje saboda kishi”

Suna shiga dakin tajuyo “to delu kike ko wa? kin gama aikin ki sai kiyi waje koh, “kuma daga yau idan har bani na gayyacekiba to bana son nakara ganinki, delu mai aiki ta dago cikin mamaki ta kalleta batare da tace da ita komai ba tajuya zata fice daga dakin har ta kusa kai kofar ta kirata kuma wallahi kika sake naji wata magana agurin mummy wallahi ni ba ruwana da tsufan da kikayi, idan kinji to jiki ya tsirah……

Delu har tuntube tayi, saboda tsoron yanda munu tayi maganar saboda tagama fuskantar lallai munu bata da mutunci kuma ga alama zata iya yin komai kamar yanda tace….”lallai munu daga zuwanki”

WASHE GARI

“tun shida munu tafara jin hayaniya da ihun FARHA DA ASHRAB tare da dadyn su suna hand ball “wallahi dady ni naci amma shine zakace Ashrab ce ni gaskiya bazan yarda, ba tasoma buga kafa,
na shagwaba hajiya salma ta taso zo zo zo yarinyar mummy ya akayi ne? cikin shagwaba tace ba dady bane ta fashe da kukan shagwaba to ya isa ta dago haba dady yazakayiwa yar’auta haka?”yayi dariya ya matso kusa da ita yanzu tsaya me kike so ayi autar dady, gaya mun ko mene tadago cikin murmushi tsere nakeso muyi sai nagani idan yanzu zakayi mun aringizo, “kuma baza’ayi da Ashrab ba mummy ke zakibawa kowa maki”

A’a tsere kuma Farha eh mummy ki duba sosai kisan dady yanda yake haka kuwa akaya suka zama cikin shiri Ashrab itace bangaren dady mummy tana bagaren Farha,….. Dan haka aka fara gasa hajiya ta hura usur ai kuwa kamar barewa farha ta wuce dady cikin yan mintina tayi masa fittt ta wuceshi tun kafin su iso mummy tafara winner we are winner da kyar dady ya karaso saboda dama farha mugunta tamasa tasan ita zata ci so take sai ta rama ai kuwa yana karasowa Ashrab ta mika masa glucos dady kasha naga ka gaji 🤣tana dariya

Ya karba ya sha sosai ita kuwa mummy da farha sai murna suke sun yi winning

Saida dady yasamu nutsuwa ya dago yanzu auta muguntar da kika yimun ke nan zan rama ni gobe seeming zamuyi zamu gani mummy tace A’a wallahi bazai yuyu ba sai dai acanja wani abun haka wasa ta tashi farha nayiwa dady da Ashrab dariya

Munubiyah tana daga tsaye gefen window dinta tana kallonsu tace aikin banza duk yazama kamar wani sakarai sai wani biye musu yakeyi kamar wani sha-sha-sha…… Ai wallahi duk sai na yi maganin ku dukan ku banzaye kawai😏…

Tabdijam too Allah ya tsare

Tasaki labulen cikin bacin rai taso magana cikin hasada da bakin ciki yazama dole nasan yanda zanyi na janyo hankalin Alhaji dole ne yasoni kota halin kaka sai nayi sanadin rushewar wannan farin cikin

Wannan farincikin bana son nacigaba da ganinsa indai ina raye….

Haka ta wuni cikin bakin ciki hajiya salma ta tura delu kiran munubiya bayanda ta iya tadoshi dakin ba kowa asaman dan haka ta doshi dakin babu tunanin komai ahankali tasomajin magana kasa-kasa wallahi insha Allahu na dauki wannan alwashin sai na mallaki gidan da abunda yangidan suke takama dashi indai ina raye kaidai bari kawai a’a a’a kada kazoh abunda yasanya bazan zoh ba kasan suna ganin ni bakuwace agarin kabari sai an kwana biyu tukunnah akwai abunda nake shiryawa aa my darling ka fahinceni mana bana son mutanen gidan su ganoni da wuri kaidai kabari kawai nima wallahi hakuri kawai nakeyi ina fama da rashinka akusa dani na sani amma kayi hakuri eh to sai anjima bana son wani yajini ina waya kasan inason sai kowa yagama yarda dani ne kagane ai…… Bey sai mun hadu eh diffffff!! Ta datse kiran…..

Jikin delu yasoma rawa babu abunda take fade sai innalillahi wa’innah ilaihi’raju’un. Da kyar ta iya dai-daita nutsuwarta ta soma kwan-kwasa dakin ahankali cikin tsoron masifar munubiyah…..

Waye tace cikin sanyin murya duk tunaninta hajiya salma ce delu ta ce nice ranki ya dade hajiya tana jiranki akasa cikin izzah da mulki tace dama kice kikemun bugu haka tafada tare da bude kofar afusace hanu tasaya ta fincikota da karfi ta iza keyarta ciki ta kalleta kinkai minti nawa anan? “yanzu nazoh” ki gayan gaskiya ba abunda kikaji?”

“Cikin rainin hankali delu tace kamar na me ranki yade” fice mun daga daki, “kice da ita ganinan zuwa”….

“To delu tace ta ficedaga dakin ciki sauri gabanta yana faduwa tabbas akwai matsala agidan nan tabbas matukar ina raye bazan bari acutar da su hajiya ba insha Allah”……

Suna zaune a darning suna cin abinci hajiya sai zuba shagwabar ta take shikuwa oga sai lallabata yake farha tana kusa dashi dady wai mummy kawai kake so da yaya Ashrab amma ni bakasona ta karasa maganar tana langabar da kai abun tausayi me zasuyi sai dariya yayi dai-dai da isowar munubiya jitayi kamar ta koma saboda bakin ciki

Haka ta karasa ta sunkuya dady good morning batare da ya dago ba, yace morning ya cigaba da cin abincin shi ranta ya sosu matuka amma ta tajuya ta gaida hajiya cikin sakin fuska ta amsa naga baki fitoba shi isa na aika kizoh kiyi break…..

“Bacci nakeyi ne mum shi isa tajuya ta kalli delu tare da sakar mata muguwar harara ta ja kujera wacce take kallon Alhaji yanda zasu gajuna sosai dashi

Shikuwa ogan bai ma san tanayi ba dan shi ayanzu baya ganin kowacce macce sai matarsa ruhinsa kuma masoyiyar sa SALMA

duk rabin cin abincin nata kallon Alhaji ne amma dai-dai da sakan bai dago ya kalleta ba abincinsa kawai yake ci yana kuma ciyar da matar sa farha ta zauna tana kallon shi can kuma tace dady ina kaunarka kai da mummy dariya sukayi atare sukace muma muna kaunarki Auta

Ashrab tayi dariya ni bakya kaunata no my sister wallahi duk duniyar nan idan kika cire dady da mummy bana son kowa sai ke ina sonki yar’uwata yayata farinciki na tashi tayi tazoh ta rungume ta kam suna murmushi lomar bakinta da kyar ta iya hadiyeta ta mike mum zan shiga ciki naji kaina yafara ciyo tajuyo tana murmushi tace Ayyah Sorry idan kin shiga kisha magani kinji tana tafiya ta amsa to mum…….. Ji take kamar kafarta bazata iya kaita daki ba saboda azabar da zuciyarta ke mata………

Tana shiga dakin sai hawaye shar kamar an bude fanfoh 😨 too aiki ya sameki munubiya

Sukuwa basu kosan tana yiba haka suka cigaba da hirar su irin ta nagartaccen family mai cike da farin ciki da kwanciyar hankali……

Da kyar ta iyakarasawa dakin tana shiga dakin sai kuka hawaye sharrrrrr kamar an bude fanfoh😨toooo aiki ya sameki munubiya

Haka ta wuni adakin ta cikin bakinciki da takaici a kwance take tayi zumbur ta dauko waya tasoma kiran layin saurayinta BASSAM

Bugu daya ya dauka darling kana ina ina cikin matsala yaza’ayi mu hadu baby ni banda damuwa ke dai ya za’ayi ke ki fito tayi shiru can ta mike kajirah ni zuwa miti talatin muhadu inda muke haduwa…… To yace sukayi sallama ta ajiye wayar tasoma shirya kayarda zata yi tasamu ta fita daga gidan

Tana zaune hajiya Salma ta turo dakin tare da yin sallama tace mun ya jikin naga baki futo ba tun dazu ta shagwaggwabe fuska yanzu dama nakeson zuwa asibiti naji jikin ya matsa mun Ayyah tace basai kinjeba bari na kira family doctor na ya dubaki ta dago cikin kissa mum kibari naje asibitin inaga zaifi kinga kafin ya zoh wata kila ni naje ina ga zaifi ai

Tayi shiru can kuma tace to ba damuwa ki shirya in yaso baba umar direba sai ya kaiki ta dago tace na gode mum cikin yan mintina ta shirya direba ya dauketa sai sharaton hotel baba umar ya kalleta hajiya ai nan ba asibiti bane ba ta dago tayi masa kallon wulakanci tace to sai me ai nasan inda nazoh kuma wallahi idan naji zancen agurin hajiya ni zanyi sanadin aikin ka dan haka sai ka kiyaye

Tabdijam muje zuwa dai to kome MUNUBIYAH Tazoh yi hotel?

Koma dai menene zakuji kudai kubiyoni

YAWAN COMMENT YAWAN TYPING

VOTE
SHARE PLSSS

TAKUCE LAURAT MUH’D BELLO

08164949554

💞💕💞💕💞💕💞💕💞

BANGARE NAH
(part of me)

          💞💕💞💕💞💕💞💕💞

WRITING BY

LAURAT MUH’D BELLO

DAGA MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH
YA CUTAR DANI
YAR’ ZAMANI
(mai kwadayin duniya)
And now

👇

BANGARE NAH
(Part of me)


AREWA WRITES ASSOCIATION


💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦


https://www.facebook.com/104534761033461/119016616251942/?app=fbl

FREE PAGE

BISMILLAHIR~ RAHMANIR~RAHEEM.

ALLAHUMMAH INNI’AUZUBIKA MINAL BARASI WALJUMI, WAL’JUZAMI WAMIN SAYYU’IL ASKAM….

AMEEN YA HAYYU YA QAYYUM..

DEDICATED TO AUNTY. HAU’WA SPECIAL GIFT TO MY LOVELY FAMILY…..

🅿<><><><><><><><><><>5⃣➡6⃣

<><><><><><><><><><” ALLAH ya baki hakuri ya gyarah parking din motar ta fice daga motar batare da tace dashi komai ba jijjiga kansa yayi azuciyarsa yace lallai wannan yarinyar sai ankiyaye ta dan na fuskanci batada mutunci”

Dakinda BASSAM ya gayamata can ta dosa tana shiga ya rungumeta suka shiga aikata masha’ar su dama can sun saba aikata mummnar dabi’ar su sai bayanda suka gama iskancin su tukunah ta ce BASSAM Ina cikin Matsala”

Ya janyota jikinsa sosai “bakida damuwa indai har muna tare dake”

“Ta tirushi daga jikinta”

“Yakamata kagane mafita nake nema” ya manna mata kiss agoshi

Ya kike so ayine”

Shawarah nake nema ya zanyi wallahi inason Alhaji MUSADDIQ idan har ban sameshi ba zan iya mutuwa

Yaji zafin maganarta ya share “to ki sanar dashi abunda kike so mana nafasanki munu idan kinason Abu bazaki taba hakurah ba harsai kin samu”,,.

Tayi wani shu’umin murmushi ta dago “kana ganin hakan zaifi? akwaifah matsala fa?”kasanfa dan iskan baya ganin kowa sai wannan banzar matar tasa dakuma yan’iskan ya’yan nasa nifah banida wani kima agidan shakuwar family tayi yawa wallahi……

Yayi dariya toki hakura mana inaganin zaifi tunda harke da kanki kince family sun shaku dayawa….. Ya janyota inasonki munu ki soni mana kirabuda family nan…..

Ta janye jikinta tamike tare dayi masa wani wulakantaccen kallo kanada hankali kuwa BASSAM? Kasan Abunda kakecewa kuwa?
kasan yanda nake son Alhaji Musaddiq kuwa?”

“Kasan yanda nake son mallakar dukiyar gidan hajiya SALMA kuwa?”

“To wallahi bazan taba barin wannan damar tawa ba,dan Haka shawarar ka nake nema idan kayi haka kaima kaci arziki kafita daga cikin wannan bakin talaucin da kake ciki idan kuma ba hakaba zaka dauwama acikin bakin talaucinda ka gada a gurin danginka matalauta….

Ta mike cikin bacin rai zata fice daga dakin yayi saurin rikota tsaya mana munu zo muyi magana menene na bacin ran to” tayi banza dashi batare da tace komai ba mekikeso nace nace dake ki sanar dashi idan har bai Aminceba kawai a kaddamar masa saboda bashida wani Amfani…… Ta dago kamar yaya a kaddamar masa to kawai ya kauce kinga kowa ya rasa keda hajiyar taki koya kike gani tayi shu’umin murmushi inason Alhaji fah Amma shawarar ka tayi………

Kaga zancen shakuwa ya kare kenan sai muci duniyar mu da dukiyar ba wani mafadi dan na fuskanci yana da tsare gida dayawa…..

Ta duba agogon hanunta karfe 5:00pm na yamma ta mike arazane nashiga uku haka lokaci yaja Allah dai yasa wancen banzar bai tafi ba kada yaje ya hadani da hajiya dan na fuskance shima dan iskane……

Ta fito cikin sauri BASSAM yana binta kamar wani wawa😂 koda suka fito farfajiyar hotel din babu baba direba babu dalilin sa jikinta har rawa yake nashiga uku kagani ko dama nasan wannna dan rainin wayon sai yabata mun shiri tan gurin wayarta ta soma ruri

Tana dubawa hajiya SALMA ce jikinta kamar dan mazari ta dauki wayar tare da dai-daita nutsuwar ta

“Hello hajiya tace ahankali tamkar marar lafiyar gaske”,,

“Munubiyah! kina inane ga deriba nan yadawo tun dazu ba ke”

“Ta Kara raunana muryar ta, “hajiya doctor din ne ya dan bani hutu na awa hudu, to banida number dinsa baranta na sanar dashi, sai yanzu kuma ina fitowa shine ban ganshiba hajiya kice ina jiransa jiri nake ji sosai bana son yawan magana”

“Ayyah munu to ba damuwa gashinan zuwa nida har hankalina ya tashi wallahi”…

“Hajiya yace dake wani abu ne?”

“A’a ba abunda yace kawai dai yadawo gida tayi ajiyar zuciya mai karfi har hajiyar taji

“lafiya munu?”

“Akwai matsala ne? “

“A’a zuciyata nakeji wani iri ina jiransa ta datse kiran”….

Hankalin hajiya Salma atashe baiwar Allah sarkin tausayi ta fito tana kwallawa baba umar direba kira ya taho cikin sauri ya russuna ranki ya de gani tace yi maza kaje ka dauko munubiyah ashe likitan ne yadan bata hutun awa hudu shi isa kaga baka ganta ba kayi sauri dan Allah tace bata jin dadi sosai kada tayita jirah…… Yayi tsaye cikin mamaki baice komai ba yace to ya shiga motar ya fice daga gidan…..

Zuciyar sa cike da tunani fal afili yace tabdijam wannan yarinyar bala’ice….

Har ya isa hotel din tunani yake suna tsaye itada da BASSAM makale da juna tamkar gam

Yana shiga ya hangosu😨idonsa kamar yafado kasa dama wannan yarinyar haka take tabdijam lallai

A zuciyarsa yace hajiya kina tare da bala’i dan wallahi wannan yarinyar masifa ce

Duba kigani tana nan tana holewar ta amma tayi karya da likita..

Ta ganshi amma shu’umar sai ta kara narkewa ajikin BASSAM takaici ya ishi baba direba ya fito ya nufi inda take muje ko yace zuciyarsa cike da takaici ta dago ta gallamasa harara takunah ta juya sweet heart zan tafi sai kaji yanda mukayi ……

Murmushi yayi tare da manna mata kiss a kumatu ta tayi wani irin fari da ido tajuya ta shige motar baba umar direba yaja da karfi saida ta dungura ta gaba🤣
Hankalinta atashe tace lafiya meye haka?….

Kamar dariya ta subuce masa ya hadiye sorry hajiya

Azuciyarsa yace ga iskanci ga shegen tsoro🤣

“Ka kula dan Wallahi ina son raina dan iskanci kana nema ka ruguza mun shiri yadago da sauri shiri kuma?”

Ta shareshi dan tayi kusan sakin bakinta……. “Wannan kuma bai shafeka ba katafi ahankali kaji ko”

Bai kuma cewa komai illah tunanin wane irin shiri ne wannan munubiya take yi?

“Me wannan yarinyar take shiryawa su hajiya dan yasan tabbas akwai wani abu. Kuma jikinsa yana bashi akan su hajiya ne”……

“To menene wannan shirin?”

Har suka isa gidan zuciyarsa tana cikin tunani yana parking ta fito tana tafiya tana dafa bango tare da dafa kanta kamar da gaske hajiya salma ta karaso gunta cikin sauri ta riketa sannu munu jikin ne tadaga kanta shidai baba direba yana kallon ikon Allah

FARHA tana tsaye agurin haka kawai ita dai munu bata yi mataba ta tabe baki ko sannu batace da itaba

Mum ki saketa mana tace A’a FARHA bakiga batada lafiya au batada lafiya ne

Daga haka bata kuma cewa komai ba hakan kuwa sai ya sosa ran munu azuciyarta tace lallaima yarinyar nan sai nayi maganin ki wallahi…

Suka shiga ciki ASHRAB tana zaune afalo tana har hada kan wasu takardun da dady yasata hadawa tun shigowar munu I don’ta yana man ASHRAB babu burinta illah taga ko takardun menene ake hadawa..

Hajiya Salma ta rakata har dakinta tace ki kwanta ki huta zamuyi magana anjima idan kin tashi…..

Maganar me kuma mum tayi murmushi ki bari kawai yanzu bakyajin dadi zamuyi magana anjima… Ta fice daga dakin

Hajiya tana fita daga dakin ta mike zaune kamar wacce aka tsikara wace magana ce wannan mum take so muyi Allah dai yasa aikin ne zan farah shike nan nasami damar Kara kusanta kaina da dukiyar Alhaji nasami damar fallasa sirrin zuciyata

Ta fada saman gadon da karfi tana murmushi my dream will soon become true ta sheke da dariya kamar wata sha-sha-sha….

Delu tana kofar dakin tana jinta ta rike baki

Ahankali ta salallaba tabar kofar dakin zuciyarta cike da wasiwasi

Hakan nan ta fito paloun gidan wasai saboda amatse take taji abunda mum zata sanar da ita

ASHRAB ce kawai a paloun hakan sai. Yayi.Mata dadi ta karasa gunda take azaune tana wani murmushin mugunta tace my cousin sister kina zaune ke kadai batare da ta dago ba tace eh sister aiki nake dady ne yasakani tattarah ta kardun duka kadarar shi data mum tunsafe nake abu daya wallahi na gaji sosai

Gabanta yafadi kadara kuma to saboda tsaro kinsan yanzu mutane basuda tabbas banki zai kai yafi kwanciyar hankali

Tayi murmushin yake hakan yana da kyau ai inbanda dady kudin da kadarar nasa sunada yawa ne dayake tsoro haka takarasa cikin dariya kamar ba wani abu

ASHRAB Ba wayo tadago sai taga bama ita take kalloh ba tace lallai sister kinsan kuwa nawane. A’a

ta ina zanyi nasani sister”

Ta bude baki kenan zatayi magana dady yayi sallama yashigo ta mike oyoo. Oyooo dady oyoo taje dagudu ta rungume shi ya daga yajuya sannan ya ajiyeta sannu da zuwa dady

Ya amsa cikin far in ciki sannu da aiki kingama dai ko

Ta da ja ajiyar zuciya hummmmm!! Ban gama dady amma nayi kusa

Wallahi yau dady duk ka gajiyar dani

Yaja kumatun ta uwar son jiki hada takardun ne angaji cikin shagwaba tace Allah dady aiki ne mai wuya

Ni ajiyewa ma zanyi sai gobe zan karasa bara na kai dakina na ajiye 😨 dakin ki a’a ban yarda ba kikai dakina ki ajiye mun munu datake zaune tanajin su ta ciji lebanta taga samu taga rashi duk shirinta na ta bugi cikin ASHRAB ya ruguje ta mike dady sannu da zuwa tace tana yi masa kallon kurillah baiko dago ba lafiya yace agajarce ya taya ASHRAB kwashe sauran takardun da ya fuskanci munu tana son ganin kona menene muje ko suka bar gurin batare da ta sunkara kallonta ba

Bakinciki da da takaici yagama cika mata zuciya tayi kwafah tamike tabar gurin zuciyarta tanata tafarfasa….

Tana shiga dakinta tabuga kofar dakarfii jikake gammm!!

Delu datake a makale tana kallon komai ta fashe da dariyah harda hawaye🤣

Itakuwa tanacan sai kullawa take tana war-warewa ta daki hannunta yazama dole na gano takardun nan tunkafin dare yayi mun😨tooo

Alhaji saika canja shiri dan kunada yar’majiya tare daku…

Muhadu A next page danjin yazata kaya….

Takuce
AKULLUN

LAURAT MUH’D BELLO

YAWAN COMMENT
YAWAN TYPING

VOTE&SHARE PLSSSSSS

08164949554

💞💕💞💕💞💕💞💕💞

BANGARE NAH
(part of me)

           💞💕💞💕💞💕💞💕💕

WRITING BY

LAURAT MUH’D BELLO

DAGA MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH
YA CUTAR DANI
YAR’ZAMANI

And now

👇

BANGARE NAH
(part of me)


AREWA WRITES ASSOCIATION


💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦


https://www.facebook.com/104534761033461/posts/119016616251942/?app=fbl

BISMILLAHIR~RAHMANIR~RAHEEM..

BISMILLAHIL LAZI LAYADUR’RUMA ISMIHI SHAI’UN FIL ‘ARDI WALA’FISSAMA’I WAHUWAS SAMI’UL ALIM

🅿<><><><><><><><><><>9⃣⏩🔟

<><><><><><><><><><><“A fusace ta fito daga office din baba direba yana jiranta a mota”

“Ko kallonsa batayi ba tayi wucewar ta cikin matsanancin fushi”

Daga kafadarsa yayi danshi dama yasan za’ayi haka dan yasan sarai Alhaji bazai dauki wannan iskancin ba..

Tana fita daga ma’aikatar ta tari adai-daita tashiga jitake kamar zuciyarta Kamar zata tarwatse saboda takaici…

Tun ahanya tayiwa BASSAM waya ringing daya ya dauka

“ya akayi ne?”

Cikin disasshiyar murya “tace kana ina BASSAM ? “inason mu hadu ina cikin matsala”

” ina sharaton kishigo kawai”

“To kawai tace ta kashe wayar ta”

Baba direba yabi bayanta ahankali yana bin bayan adai-daitar har suka isa sharaton hotel dama yasan haka saita faru domim kuwa ya gama fuskantar munu yar bariki ce ta ajin karshe

Cikin sauri ta biya mai adai-daita ta shiga cikin kamar zata tashi sama

Baba direba ya fito shima yabiyo bayan ta room mai lambar 107

tashiga a kofar yatsaya tana shiga ta fada jikin BASSAM ta fashe da kuka mai karfi

“BASSAM!

“Alhaji MUSADDIQ! baya sona ya tabbatar mun da bazai taba sona ba”

yaji dadin maganar amma bai nuna ba ya janyota jikin sa ya sumbace ta toki kiyi shiru mana inaga bai kamata ki bata lokacin ki kiyi kuka ba sweet heart ki kyaleshi kawai inaga zaifi..

“Ta dago jajayen idanuwan ta, ta kalleshi

Ta girgiza kanta wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Bazan kyaleshi ba

“Idan har bazai soniba to wallahi sai naga bayansa inyaso kowa ma yarasa”

” wannan shine kudiri nah, ni munubiya ban taba kudirar abuba na gagara aiwatar dashi ba

“ka shirya mun yarah”

Ayau nakeso ku kaddamar masa bana son Alhaji MUSADDIQ yakoma gida inason kota halin kaka yau kada ya kwana acikin duniyar nan.

“Inason yau na dan-danawa iyalan Alhaji MUSADDIQ bakin ciki da kunci da radadin Abunda yayi mun

“Baisan ba’a tabani ba dan duk wanda yanemi shiga gonata to wallahi sai na hada dashi na nome dan ni bakar zuma ce mai mugun harbi…”

Maganar ta girgiza BASSAM sosai ya janyo hanayenta sweet heart basai andauki wannan hukuncin ba inaga ki share kawai wallahi inajin tausayin iyalinsa dashi kansa

Amma fa shawara ce cikin tsawa “to bana bukata ai wallahi tunda na iya dukan mahaifiyata banga wani wanda zai sha gaba naba ban hankada shiba wallahi”

“Ya daga kafadar sa”

“Well wannan ba matsalata bace kamar karfe nawa kike son a aiwatar da aikin”

“Da dare idan yadawo kina nufin agida za’a kashe shi inaga wannan ba shawara baceba saboda unguwar tanada tsaro sosai”

“Kuma kinsan za ‘a zargi wani abu inaga ki bari kawai a kashe shi ta hanya mai sauki”

“ta dago ta yaya?”

“Yayi murmushi yace ta hanyar zuba masa poisin acikin abun sha kona ci wanda idan yaci ahankali zai ringa cuta har yamutu batare da kowa ya zargi wani abuba”

“Ta kankameshi sosai ajikinta BASSAM inasonka ada naso akashe munshi agaba na a shakemun dan iska har sai ya mutu”

“Bakida hankali ai sai bincike ya kawo kanki kema amma yanzu idan yasha slow poisin ba mai tunanin komai har ya gangara ya ware kawai muci dukiyar mu da tsinke”…….

“Baba umar direba jikinsa har rawa yakeyi saboda tashin hankali da kyar ya iya barin kofar dakin ya fice daga hotel din”

Ya ja mortar sa da karfi yabar harabar gurin duk da sanyin AC da ke cikin motar Amma gume yakeyi ya jike jagab

Addu’a yakeyi yana sharara gudu Allah ya tsareka Alhaji Allah ya kareka da sharri wannan bakar muguwar azzaluma mai fuska biyu

“Baifi mintina talatin ba ya isa gidan idi mai gadi yabude masa kofa ko gyarah parking baiyi ba ya fito, “idi Alhaji ya dawo kuwa?”

“Eh”

“Yana ciki tun dazu Amma lafiya kake tanbaya?” “kuma sai naga kamar hankalinka atashe yake lafiya?”

” Ba komai kawai ina tanbaya ne”

Ya wuce dakinsa saboda baya tare da nutsuwar sa ya idan yace zai dade to idi zai gano wani abu

Alhaji MUSADDIQ yana jikin hajiya Salma yayi lamo kamar mai bacci ta dago fuskarsa dear ya na ganka haka lafiya kuwa

Ya kara janyota jikinsa sonki ne yake dawainiya da zuciyata Amma bana tare da damuwar komai ya shafi face dinta ya gangaro izuwa labbanta ya kai bakinsa ya sunbaceta

Ta dada janyoshi jikinta dear inaganin canji atare da kai kasanar dani kasan bazan juri ganin ka haka ba kayi gaggawar Sanar dani tunkafin zuciyata ta Gaza

“Kada ki damu kawai gajiya ce amma bana tare da damuwar komai”

Ta langabar da kanta Allah yasa haka dear

Daga nan zance ya sauya suka shiga sabuwar duniyar masoya ina ganin haka na janyo iyalan kafa ta na fito dan da alama idanuwana basu iya kalloh😆 ba

Ya manta shaf dawata munu danshi daukar ta yakeyi wata sha-sha-sha ce 😨 tabdijam

Aikuwa munu ta dauki damarar daukar fansa

ASHRAB tana zaune tana typing saman cumputer FARHA ta matsa kusa da ita ta dafata yaya dama ina son na tanbayeki ta dakata da typing dinda take ta dago tace meya faru

Dan Allah kina son zaman Aunty munu gidan nan

Dariya tayi tace idan bana so ya zanyi Amma me yasa kika yimun wannan tanbayar

Tace ni wallahi bana son zamanta agidan nan haka kawai nakejin bana kaunar ganinta agidan nan

Allah yasani badan ko muna da arziki ba a’a kawai dai zuciyata takasa Aminta da ita

Idan na ganta sai naji gabana ya fadi

Narasa meyasa inajin tsoro sosai kada Aunty munu ta cutar damu

ASHRAB ta ajiye abunda takeyi tace ashe kema zuciyar ki tana yimiki wannan tunanin nima haka nake ji game da ita Amma kuma data zauna tare damu sai naga kamar zuciyar muce kawai take zargi insha Allah ba matsala ki sa hakan acikin zuciyar ki…

Jinjina kanta tayi to yaya Ashrab zanyi kokarin ganin na yaki zuciyata Insha Allah

Munu sai da ta tanadi poison din da zasuyi amfani dashi tukunnah tabaro hotel din sai misalin karfe 7:00pm ta dawo gida

A farfajiyar gidan suka ci karo da baba umar direba ko akallonsa batayi ba baranta tace dashi wani abu tayi shigewar ta ciki

Girgiza kansa yayi yakuma kudira aransa zai taimaki Alhaji indai yana raye

Tana shiga ciki bakowa acikin paloun kowa yana dakinsa sai delu kadai tana kwashe kayan abincin da sukaci har ta wuce ta kuma dawowa baya delu zoh ta dago na’am tace kizoh nace dake

Tace to ta waiga bakowa tukunnah ta tanbayeta Alhaji ya dawo ne

Tanbayar tabata mamaki tace ” Eh

Amma meye na tanbaya haka kawai sunyi dinner ne

Nan ma tace eh

Ta juya aranta tace zakaci ubanka wallahi ko yanzu ba tsallakewa kayiba.

Yau’wa akwai lemo a fridge eh tace agajarce dan ta fara jin tagaji da tanbayar ta haura sama ciki sauri

Tana shiga ta fada wanka ta tsaftace jikinta da kazantar da ta dauko

“Ta fada gado ita salla bama ‘a zancenta dan kwata-kwata bata tunanin ta ma”

“Sai karfe1:00am ta tashi ta sauko kasa cikin sanda ta nufi bangaren Alhaji musaddiq yana zaune yana aikin da bai karasa ba a office
Lemon fresh milk a gefensa yana aiki yana korawa”

“Yajuya gunda hajiya Salma take kwance tana barci kanta bai hau dai-daiba ya mike ahankali ya sunkuya ya dauketa ya Nufi daki da ita”

“Ya shimfidar da ita saman gado harya mike ta janyo hanunsa dear ka kwanta mana kabari gobe ka karasa ya shafi fuskarta to bara naje na dauko takardun sai nabari sai goben”

“Munu tana ganin ya shiga dakin cikin azama tayi wuf ta shiga ta bude lemon ta tuttula masa poison aciki tayi sauri ta fice daga palourn.. Cikin sauri”

“Yana zuwa baiyi tunanin komai ba ya dauki lemonsa ya kora yadan taba aiki tukunnah ya shiga ciki”

“Ya ajiye takardun a ma’ajiyar su yadowo kusa da hajiya ya zauna ya kara janyo lemonsa ya cigaba da sha ahankali saida ya shanye lemon tass tukunnah ya ajiye ya je ya kuskure bakinsa ya dawo ya kwanta akusa da matar sa”

“Jikinsa yaji yayi masa weak sosai ahankali yakeji kamar jikinsa yana canja masa alamar rashin lafiya yakeji ajikin sa da kyar ya iya bacci saboda yanda yakeji”

“Allah sarki Alhaji musaddiq 😭 ina tausaya maka”

“Munu tayi maka cizon dan maciji”

“Allah dai ya kyauta”

“Tun daga ranar Alhaji musaddiq yafara rashin lafiya a tsaye batare da yabari iyalansa sun sani ba”

“Yafara gazawa dan kullun acikin abunshan sa sai ya sha wannan gubar batare da yasani ba duk sa idon delu wannan lokacin Allah bai bata ikon gani ba hajiya salma tafara fuskanci bashida lafiya”

“Amma shi ya ki ya Amince da hakan yana kwance ramar sa ta fito sosai hajiya salma ta zauna akusa dear yakamata kaje asibiti baikamata ka zauna agida ba”

“Ya janyo hanunta shikadai yasan wahalar da yakeji numfashin sa jiyake kamar zai dauke masa da kyar yake jansa ya some magana ahankali dear ki daina damuwa nagaya miki ba wani Abu bane ba”

“Ya Dade yana kallonta tukunnah yace ina son ki koma office ki cigaba da tafiyarda da harkokin kamfanin bazai yuyu ni ina kwance ke kina gida ba kema kada hakan yazama andunkusar da kamfanin”…

“Dear tayaya zan tafi office nabarka agida kwance acikin halin ciyo, “ni gaskiya bazan iya ba ya janyo hanunta ki fahince ni mana ta dago rauna naniyar fuskarta kada ka damu ga ASHRAB nan da Aunty ta munubiya sai su cigaba da jan komai na kamfanin”…….

“Yana jin sunan munubiya yakara damke hanun hajiya salma sosai tamkar zai tsaga hanun ta bude idanuwanta sosai lafiya”

“Ke nake bukatar ki kasance a gurin, “a’a ni bazan iya barinka acikin ciyo ba na gaya maka munubiya da Ashrab zasu iya komai naga yarinyar tana da hankali kuma tayi karatu mai zurfi karin abun abunda ta karanta ke nan kaga babu wata damuwa insha Allah”

“Kallonta kawai yakeyi yana kara jin tausayin ta cikin zuciyar sa saboda ya fahimci har yanzu bata san ko wacece munubiya ba”

dear! dear!! “magana fah nakeyi amma sai kallo nah kakeyi nifah wallahi nafara tsorata ta fashe da kuka mai sauti da kyar yadan yunkura ya janyota menene kuma na kukan kallon da nakeyi miki baya nufin komai tayaya zan iya dauke idanuwana daga kallonki kada ki manta salma kece ruhi na numfashi na kece kadai nake kallo naji dadi aduniyar nan bana ganin kowace mace a idanuwana sai ke ina sonki sosai ,salma Allah kada yabawa masu son rabamu damar hakan inason kasancewa daku salma kune farin cikin rayuwata amma inajin kamar sai kuma yayi shiru yakasa karasa wa”

“Ta dago cikin sauri kamar me? mekake ji dear kasanar dani dan Allah zuciyata tayi rauni

Ta kara kankameshi kamar wani zai kwace mata shi numfashin sa yafara sama-sama ta mike cikin hanzari ta lalibo wayar ta, doctor ibrahim ta kira family doctor dinsu ringin daya ya dauka ganin kiran awannan lokacin yasanya yayi saurin dauka

“Assalamu alaikum”

“Doctor kayi sauri Alhaji bashida lafiya dan Allah doctor yana cikin wani hali”

“Subahanillah”

“Ganinan zuwa ki bani mintina goma dama ina cikin unguwar”

Ta katse wayar ta koma cikin sauri gurin sa kallonta kawai yakeyi
Yana jan numfashi ahankali

Su Ashrab ne sukayi sallama suka shigo ita da Farha

“Ganin halinda dadyn su yake ciki yasanya su karasawa cikin sauri hankalin su atashe,

“dady sannu kallonsu kawai yayi hakan yakara karyar da zuciyar su sai suka fara kuka ahankali ya bude bakinsa yace dady addu’a yake bukata ayanzu ba kuka ba yarana abun alfaharina”

“Yayi murmushi suma duk sai sukayi Farha tace dady Allah yabaka lafiya Amin autar dady Ashrab tace dady Allah yabaka lafiya

Amin yace yarinyar dady yayi shiru na dan lokaci kana ya lalibo kasan filonsa ya dauko wasu makullai ya mikawa hajiya Salma ta karba tare da tanbayar sa na menene yace na duk wata dukiyar gidan nan ce yayi dai-dai da shigowar munubiya dakin karaf akunnenta hajiya Salma tayi mamakin ganinta dakin kasancewar bangaren Alhaji ne ba wani bako dayake shiga bangaren daga shi sai iyalan sa

“Haka kawai ta tsinci kanta da boye makullin ta yanda bayanda munu zata iya ganinsa

Karo na farko data fara boyewa munu wani abu tunda tazo gidan

😨tabdijam

Muje zuwa dai yanzu muka fara

TAKUCE A KULLUN

LAURAT MUH’D BELLO

YAWAN COMMENT YAWAN TYPING

VOTE
COMMEN
SHARE…………….

08164949554

💞💕💞💕💞💕💞💕💞

BANGARE NAH
(part of me)

         💞💕💞💕💞💕💞💕💕💞

WRITING BY

LAURAT MUH’D BELLO

DAGA MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH
YA CUTAR DANI
YAR’ ZAMANI
(mai kwadayin duniya)

And now

👇

BANGARE NAH
(part of me)


AREWA WRITES ASSOCIATION


💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦


https://www.facebook.com/104534761033461/posts/119016616251942/?app=fbl

BISMILLAHIR~RAHMANIR~RAHEEM..

🅿<><><><><><><><><><><>7⃣⏩8⃣

<><><><><><><><><><“har karfe daya munu ta’kiyin bacci ta fito daga
dakinta ba motsin kowa agidan ankashe wutar kowane bangare duhu ya mamaye kowane gurin ahankali ta salallaba tayi bangaren Alhaji Musadiq ahankali take tafiya kafarta ba takalma ta haurah sama cikin sanda….

Magana takeji kasa-kasa hajiya kinga takardun nan gobe yakamata nakaisu kinsan abari yahuce shi ke
kawo rabon wani hajiya Salma ta ja dogon numfashi na’amince dear amma meyasa kake son ka kaisu banki ne

“Akwai dalili wanda ayanzu ba lallai kisan shi ba”

“dalili kuma dear?” ya jinjina kansa munu tana tsaye akofar tanaji

“Kasa-kasa hajiya Salma ta dago tashafi gefen fuskar sa na yarda da kai dear basai kasanar dani ba gobe da karfe nawa zakatafi kai takardun?”

Ta kara dora kunnenta sosai saboda taji time din da zai bar gidan

Inaga ai 8:00am yayi kinga kafin nakai 9:00am sai nayi acikin lokaci

Taja ajiyar zuciya tare da sakin shu’umin murmushi ta juya tabar kofar dakin

Cikin sauri harda tuntube garin sauri tana shiga ta lalibo wayarta tasoma kiran BASSAM

Bacci yafara daukarshi can yaji wayarsa ya lalibo ta yana ganin sunanta ya watsake daga baccin

Sweety ya akayi ne kashirya gobe zakayi mun aiki ka shirya yaranka gobe da misalin karfe 8:00am zaka zoh nan amma kada ka karaso

Inason Alhaji yana fitowa kubishi akwai wasu takardu da zaku karbo mun agunsa…

Yayi dariya kada kidamu ki dauka aikin ya kammala

Basu wani dauki lokaciba sukayi sallama

“delu tana ji jikinta yayi sanyi matuka haka ta ja jikinta takoma daki tana ta tufka da warwarar yanda zata taimaki Alhaji”….

Suna kammala wayar ta jafar da ita tana wani irin murmushi da alama bazan sha wahalaba gurin mallakar dukiyar gidan nan.

Nayi alkawarin bazan dauwama acikin talauci ba kamar yanda nataso acikinsa tabbas wannan alkawarine dana daukarwa kaina…

Toooo😨

Washe gari Alhaji yana dawowa daga masallaci asuba ya dauki babbar akwatin yayi bayan gidan da ita ya waiga baiga kowaba tukunnah yasanya makulli yabude kofar yashiga

Dakine babba sosai duk wani sirrin gidan yana cikin dakin ya sunkuya ya janyo wata katuwar akwati babba sosai yasanya makulli itama yabude ta kudine dallar amurka gata nan jere ashirya su da duk gwala-gwalan su Hajiya Salma da yaransa ya saka dakardun aciki daga can kasan akwatun yamayar ya rufe ya mayarda ita mazaunin ta ya gyarah gurin ya mike ya mayarda makullin bayan wani tangamemen katon hoton hajiya salma idan har ba angaya makaba baza taba tunanin ajiya ake agurin ba yafito daga dakin nanma ba kowa har yashiga gidan ba motsin kowa agidan duk suna bacci.. .

Alokacin munu batama san awace duniya take a ba🤣

Gari yana washewa kiran Bassam yashigo wayar ta cikin bacci ta daga ya akayi? “mun shirya komai yana fitowa ki sanar dani” ok tace ta kashe wayar”…

Ta mike cikin hanzari ta sauko kasa..

Suna break dukansu saboda suna karyawa da wuri gidan.. Kowa yayi mamakin ganinta alokacin FARHA ta kalleta shekeke ita dai hakan nan takejin batason munu da son samun tane da ta daina rabarsu kwata-kwata wallahi

Ta kure dady da ido hajiya salma tace “munu kema yau kintashi da wuri?”

“eh mum yunwa ce ta tashe ni wallahi”

To ki zauna ki karya ko, taja kujerah kusa da dady ta zauna tana zama farha ta gallamata harara cikin tsiwa tace “A’a munu mufah ba mai zama kusa da dady sai mum” ,,”dan haka ki tashi, “inaga yaya Ashrab ita yakamata tazama partner dinki ba dady ba”…..

Ashrab tace “hakane wannan dokar muce mu ya’yan dady suka kwashe da dariya mum da dady bawanda yace komai Farha ta mike oya get up kidawo kusa da yaya Ashrab inaga itace sa’arki

Haka ta mike jiki asanyaye tare da jin kunya duk ta dabai-bayeta tare da jin matsanancin takaicin FARHA ta koma kusa da Ashrab delu tana gefe dariya kamar ta hallakata tabbas taji dadin yanda Farha tayiwa munu

Ya mike to ni zan wuce ya dauki breif case dinsa sauri nakeyi zan wuce banki daga can zanje gurin aiki

Hajiya tamike itama suka rakashi har su farha saida ta shigar dashi har mota tukunah suka dawo ciki

Munu tana daki har ta kirah shi awaya ta sanar dashi fitar Alhaji musaddiq

Suna zaune amota ya wuce ahanakli suka ringa binsa a baya ya kula da ana binsa tunda ya fito murmushi kawai yayi saboda dama yasan za’ayi haka

delu ta sanar dashi komai😨lallai delu sai agaidake

Tsayawa yayi gefen titi kamar zai duba abu yashiga neman wata waya

Aikuwa kamar jirah suke suka zagayeshi suka turashi mota saboda gurin akwai mutane suna dan wucewa..

Lafiya menayi muku BASSAM daya rufe fuskarsa da marks cikin izza yace futo da takardun nan

“Alhaji musaddiq yace wane takardu kuma?” ya buga masa tsawa mai rikitarwa kada ka raina muna hankali kaji ko

“Babu zancen rainin hankali ku duba inbanda wayata bana tare da komai”

Hanu BASSAM yasa ya finciko brief case ya zazzage ta tas babu komai mai amfani a ciki

“Abun ya daurewa BASSAM kai yafito afusace yana fita suka biyo bayansa Alhaji yana ganin sun fice ya ja motar sa da karfi ya bar gurin”

Wayarta yasoma kira tana dauka tasaki lafiyayyen murmushi kamar tana gaban sa ka’ajiye agunka zamuyi waya cikin Bacin rai yace kada ki kara batamun rai malama

Kwance take saida tamike zaune ya ‘akayi ne

Haba sweet heart dama kinsan wahala kawai zaki bamu kika tasheni tunda sassafe

To bawasu takardu inaga dai kunnenki baiji dai-dai ba kokuma idanuwanki gizo kawai sukeyi miki ba wasu takardu dan wallahi ko katin ATM bamu samuba barantana wasu takardun kadarah a tare dashi

“Impossible! what do u just said? i think i don’t understand what you are saying”

“Munu don’t be stupid!

“I told you what I saw”

Kinga yanzu am not in the mood kawai zamuyi waya difff ya kashe wayar sa

Ta mike kamar mahaukaciya bazai yuyuwa wallahi, wallahi bazai yuyuba ta fashe da kuka mai tattare da bakin ciki da takaici

“Wallahi saina samu abunda nake nema agidan man kota halin kaka ban taba neman abu bansamu ba dan haka zan sake shiri wallahi bazan hakura ba”

“Toooo😨aiki ya sameki kuwa munu”….

Taci gayu na fada aji tafito kaitsaye bangaren mum ta nufa suna zaune ita da FARHA mum ki gaya mun meya sami dady kinki

Suna cikin haka tashigo dakin farha tana ganinta ta hade girar sama data kasa tamkar bata taba dariya ba ta karasa gunda suke tace mum
Dan Allah zanje gidan kawata najwa jiya ne sukayi bikin zagayowar haihuwarta bansamu naje ba

Hajiya salma tayi murmushi tace kada kidamu munu kije amma kada ki dade kinsan dear baya son yawo

Tana murmushi bazan dade ba

Takalli farha sister ba magana, “farha ta dago tayi mata wani kallon raini tace sai kin dawo”

Yanda ta kalleta sai taji wani iri ta fuskanci farha kanta yana hayaki ba kamar Ashrab ba

“Sai na dawo tace tana yake”

“Mum tace to Allah ya tsare, ki gaida ta, zataji tace tafice daga dakin zuciyarta tana kara hura mata wutar tsanar FARHA

tana fita mum tace baby nah na fuskanci bakwa jituwa keda munu meyasa yar’uwar ki ce fah

Tadago mum wallahi bansan abunda yasanya nakejin bana son ganinta akusa da muba tun zuwanta gidan nan naji hankalina yakasa kwanciya da ita

Jikina yana bani kamar akwai wani abu datake boyewa

Dafata tayi tasoma magana ahankali kada ki zargi komai FARHA bawani wanda yakeda masaniya akan abunda yake boye sai Allah shi isa nake kyautata zato na akullun dan Haka ki nutsu ki ajiye zuciyarki guri daya kidaina zargin komai kinji ko

domin mazon Allah yasanar damu cewar

Mu kiyayi zato domin shi zato shine mafi karyar zance

Ta daga kanta alamar taji amma fa zuciyarta ta gagara jin zata yarda da munu dan tabbas jikinta yana sanarda ita akwai wani Abu…..

Munu tana fita tasami baba direba yana hutawa tayimasa wani kallon raini muje ma’aikatar Alhaji musaddiq

Yayi mamaki sosai ina kika ce? aikaji kada ka raina mun hankali..
Ya janyo mota ba yanda ya iya… Tashiga tana wani yatsina kamar taga kashi

Suna fita kaitsaye ma’aikatar su Alhaji ta nufa suna isa ma aikatar munu takara rikicewa taga tamfatsetsen guri katon gaske har rawa jikinta yakeyi saboda rudewa

Baba direba yana kallonta yayi murmushi aransa yace indai Alhaji ne kigama abunki yarinya

Tashiga tana tafiya mai jan hankali kusan kowa idonsa yana kanta yanda take tafiyar kamar mai gasar sarauniyar kyau kai tsaye office dinsa ta nufah ba neman izini ba komai ta dannah kanta ciki

Yana zaune ya lumshe idanuwansa sanyi air condition yana ratsa shi yagaji matuka

Kamshin gurin ya canja yaji bai bude idanuwansa ba yasoma magana wayace ashigo mun ba neman izini

Asanina duk dan musulmi yasan mahimmancin sallama dan Haka koma kiyi sallama

Taji kunya sosai ta koma tayo sallama tashigo

Ya bude kyawawan idanuwansa gabanta ya yi mummunar faduwa jikake damm! dammm!! Fatt! Fatt!!

“Alhaji barka da ranah”

Tana ininah jitake kamar zata saki fitsari a wando saboda kwarjinin da yayi mata

Idonsa yana kanta duk sai ta dabar barce inajinki

“Meya kawo ki?”

Nan ma saida hanjinta ya kada

“Ba komai dama nace bara nazoh na gaida ka ne”

“Saboda wane dalili ya katseta?”

“Ba komai saboda zumunci”

Gida daya muka kwana mukayi break a table daya duka bai isaba har sai kin biyoni nan

Ya mike yana tafiya cikin kasaitar sa dan Alhaji musaddiq badai ajiba ko mace albarka

Ya tako har gunta ke!! “yace cikin daga murya ta dago cikin sauri
Ya nuna mata hanya tashi ki fita Alhaji katsaya ka saurare ni dan Allah”

“Babu wata magana dazaki iya sanar dani ayanzu nasan nufinki dan ni ba karamin yaro bane ba na dade da fahimtar manufarki”

“Ki sa azuciyarki ni musaddiq babu wata macenda zata taba tasiri azuciyata kamar Salma, “saboda itace kadai muradin raina itace wacce zuciyata ta Aminta da ita bazan taba son wata ya’mace ba sai ita dan haka ina son ki saka azuciyarki bazan taba sonki ba har karshen numfashi nah dan haka ki tashi ki fice mun”,,

Banza marar aji wallahi koda mata sun kare bana tunanin zan soki dan ke ba sa’an tafiya ta bace

Mace irin Salma itace muradin zuciyata kuma zabina ta har abada

Ta mike zuciyarta tana kuna duk abunda zaka ce kace wallahi ina sonka

Soyyayarka tana zagaye acikin jinin jikina bazan iya rayuba matukar zan ganka da wata macen nayi Alwashin sai na dauki mataki kajirah ka gani

Kije kuma kada ki fasa akan hajiya salma raina fansa ne agareta

Har takai kofa tajuyo zakaga abunda zai biyo baya wallahi sai kasan wa kataba

“Ni munubiya ba’a tabani akwana lafiya wallahi! Wallahi!! Wallahi!!!
Sai nayi sanadin ranka nida ita salman dakake tutiya da sonta kowa ma yarasa wannan shine Alkawarinda na dauka”

“Ayau basai gobe ba zaka gani tafice daga office din zuciyarta a matukar fusace……………!!!

Tabdijam😨🤔munu mikike son aikatawa ne?

Allah dai yatsare

Muje zuwa dai

Kuyi manage da wannan bana jin dadi

TAKUCE A KULLUN

LAURAT M BELLO

COMMENT
VOTE

SHARE PLSSSSSSSS

08164949554

💞💕💞💕💞💕💞💕💞

BANGARE NAH
(part of me)

          💞💕💞💕💞💕💞💕💞

WRITING BY

LAURAT MUH’D BELLO

DAGA MARUBUCIYAR LITAFIN

SUKHAINAH
AND NOW
👇

BANGARE NAH
(part of me)


AREWA WRITES ASSOCIATION


💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦


https://www.facebook.com/104534761033461/posts/119016616251942/?app=fbl

BISMILLAHIR~RAHMANIR~RAHEEM
ALHAMDULILLAHI ALAH KULLI HALIN🤲

jan hankali garemu yan’uwa musulmi duba da yanayin da muke ciki na wannan jarabawar ya ku yan’uwa musulmi mu sani Allah dole ya jarabce mu domin kuwa munkasance masu tsallake iyakokin ubangiji duk wani abu da Allah ya hanemu ayanzu ana aikatashi zinace-zinace yayi yawa shaye-shaye yayi yawa madigo yinsa ake luwadi yinsa akeyi cin dukiyar maraya
Tayaya Allah bazai jarabcemu ba yakamata muyi hankali wannan cutar kadai tazama iznah agaremu mukomawa Allah mukiyaye hakokin ubangiji mu yawaita istigifari ga Allah ko zamu samu sassauci agurin Allah domin shine kadai zai tsallakar damu muna tawassali da sunayenka kyawawa Allah ka karemu da wannan cutar ta duniya kayafe mana karamana lafiya ka
tausaya mana Allah dan tausayinka ga bayinka Ya Allah kaini Allah muna rokon ka da kokon baran mu ya hayyu ya qayyum Allah ka karemun da wannan cutar kaka re dukanin yan’uwa musulmi baki daya ka kawamana karshe wannan itila’in daya saukar mana Dan dai-daituwar Al-arshinka ya mahaliccin mu AMEEN YA ALLAHU YA RAHMAN WANNAN SAKON TUNATARWANE DAGA YA

ASTAGFURULLAH WA’ATUBU ILAI😭🤲 Ameen ya Allah

🅿<><><><><><><><><><>1⃣1⃣⏩1⃣2⃣

<><><><><><><><><><><><“Idon ta yana kan hajiya da abunda take boyewa sai dai ba abunda take iya hangowa”

Tana shiga doctor yana shigowa hakan yakara dakatar da ita gurin son ganin abunda take son ta hango.

doctor yace hajiya dama jikin yayi tsanin haka eh tace a raunane ya karasa gurinsa yafara dubashi
Ya juyo hajiya da an dan ragu ko, “akwai tanbayoyin da zanyi masa munubiya ta dago karaf tace kaga doctor duk nan we are family so I think you don’t have any problem to do what you want to do

Hajiya Salma tace a’a mey be he want do something which is personal da bai kamata wani yajiba
Ya daga kansa upcouse kinsan duba marar lafiya Abu ne na daban kada kuyi mun mummunar fahimta
Farha tace kada kadamu Aunty mu je ko doctor kayi aikinka muje aunty munu tsayuwar me kikeyi tana tsaye so take sai taji abunda yake damun sa dakuma adadin kwanakin da yarage masa ya mutu
Wai tunanin me kikeyi ne ta turata gaba muje nace taja ajiyar zuciya mai karfi tukunnah ta fita daga dakin
hajiya da doctor kowa yayi mamakin tsayuwa ta amma banda Alhaji musaddiq dan shi yagama fahimtar ta tuni, salma tana gefe azaune doctor ya ake ciki

Ya dago a gaskiya hajiya bazan boye miki ba kamar yanda yake boye miki yazama dole na sanar dake Alhaji musaddiq ya dago yana girgiza kansa doctor na gaya maka mubar zancen nan hajiya Salma ta mike wane zance doctor dan Allah idan kasan wani abu game da wannan jinyar ta dear ka gaya mun dan Allah

Yan da ta rude sai ta kara bashi tausayi ya katse ta zan sanar dake amma sai kinyi mun alkawarin bazaki sanar da Iowa ba kuma zaki kwantar da hankalin ki

Ta daga kai alamar amincewa insha Allahu doctor nayi maka Alkawarin ba wanda zai sani ko kuma yaji koda su Ashrab ne….

Yayi shiru kana yace hajiya wannan cutar ta Alhaji tabbas da sahun wani ta waro ido 😨 kamar yaya ban ganeba yace ina nufin wani ne yake shirya salwantar da rayuwar Alhaji ta hanyar zuba masa guba acikin abinci ko kuma a abun sha

“What” tace da karfi bakinta yana rawa tace waye wannan hawaye suka ringa sintiri akan fuskarta… Likita yace kiyi ahankali shi’isa Alhaji yaki yasanar dake tuntuni yana zuwa asibiti kuma yana karbar magani amma maganar ta gaskiya gubar tayi masa illah sosai saboda ayanda na fuskanta yasha ta sosai batare da yasani ba

Amma insha Allah zamu san abunyi kuma yazama wajibi ki saka ido sosai akan duk wani motsin yan gidan nan da ma’aikatan ku, tabbas mai son cutar daku yana tare daku

Tadaga kai cikin jimami insha Allahu likita za’a kiyaye sosai yanzu likita menene abunyi

Yanisa zan dauke Alhaji zantafi dashi asibitina acigaba da bashi kulawa acan

Kuma bama bukatar vitors saboda dakile koma waye, to doctor to ya maganar jinya kuma? “kada ki damu zan kula da komai”

Wannan ba matasala bace….

Suna fita su munubiya Farha ta janyeta saida suka bar bangaren baki daya tukunah tace Aunty ki zauna mujirah fitowar doctor bandan tana soba ta zauna amma jinta takeyi kamar saman kaya sotake kota halin kaka taji abunda likita zaifada….. ..

Ashraba tana zaune bata ce dasu uffan ba ita kawai rashin lafiyar dady ce agaban ta

Delu tafito cikin damuwa tace Ashrab ya ake cikin jikin yallabai tabude bakinta kafin tace wani abu munu tasoma magana tayaya zata sani wancen dan iyayin likitan yakiyabari muji abunda ke damun sa Farha tace A’a kada ki ga laifin likita fah ai baizama lallai sai munji abund yake damun saba Addu’a zamuyi koma menene Allah yabashi lafiya

Haka ne kam munu ta dago ta gallamata harara ta dauke kanta daga kallonta tace bari na cigaba da aiki nah rana tana Dada yi tace baba delu mun gode da kulawar ki

Haba ranki ya dade ai anzama daya bakin ciki duk yakara mamaye zuciyar munu

Tamike bara naje na duba Farha ta dago

Waini Aunty munu na rasa gane miki duk kinbi kin wani damu kamar kece ma marar lafiyar tayi dariyar yake wallahi dole na damu jin Alhaji nakeyi kamar babana na cikina bana son na rasa shi kamar yanda na rasa baba nah

To wayace dake za’a rasashi yakamata ki san abunda zaki fada ai wallahi ina tabbatar miki har abada muna tare da dady dan ba inda zaije kima daina yimana fata e eh hee😏

‘A’a ki fahimce ni kwarai kuwa ai nagama fahintar ki sokike dady ya mutu to wallahi ta Allah bata mutunba wallahi

Ashrab tace ke farha Aunty kike gaya wa magana haka ya isheki haka
Aunty kiyi hakuri kinsan har yanzu yarinya ce batada cikakken hankali

Tayi yake wanda yafi kuka ciyo kada kidamu nasan bata fahimceni bane ba……. Wallahi na fahimceki sarai

Tamike ta bar gurin tana cika tana batsewa

Ashrab ta matso kusa da munu tace Aunty kiyi hakuri dan Allah kinsan dai halin farha idan ranta yabace

Nasani kuma zanyi maganin abun insha Allah Ashrab tadago
Banganeba kamar yaya

Ina nufin zan kiyaye agaba insha Allah😁. Tayi dariya

Nan kuwa ita tasan mugun kudirinda tayi aranta

Tamike bara naje daki ko naga likitan bai fitoba haryanzu… To Aunty munu nima tashi zanyi

Sunmike kenan saiga su Alhaji sun fito tare da doctor Ashrab takarasa gurin dady ta sannu dady ya daga mata munu ta karaso tana wani shu’umin murmushi tace sannu dady ko kallonta baiyi ba barantana tasamu ya amsa Farha tace dady sannu ya amsa yana murmushi Auta tace na’am dady yace zamuje asibiti Ayimana addu’a kinji ko

dady zaka dawo yau ya jinjina kansa A’a sai na sami sauki dady zan bika tafada cikin shagwaba A’a utar dady ki zauna gida ga mum dinki nan munu tace doctor tafiya zakuyi da gaske?”

Yayi mamakin tanbayar sosai Eh yace ciyon nasa har yakai aje asibiti akwanta

Aa kada ki damu muna dan wani bincike ne gabanta yafadi rassss!!
bincike kuma bincike me kuma doctor nifa duk ban gane ba wane irin rashin lafiya ne wai

Kada ki damu zazzabin cizon sauro ne ba wani abu babba ba… dan haka ki kwantar da hankalin ki

Hajiya salma tace na gode munu da irin damuwar da kikayi da mijina kedin kinada matsayi babba azuciyata..

Tayi dariya ba komai mum jinsa nake kamar yanda kike jinsa azuciyar ki kinga kuwa damuwa dashi tazama dole

Hajiya Salma bata san kwanan zancenba tayi murmushi na gode da kulawa munu suka wuce Alhaji musaddiq ya gallah mata wata uwar harara har saida hanjin cikinta ya kada

Ya kalli matar sa ina kaunarku Ahalina kamar yanda nake son rayuwata duk runtsi duk wahala bana tunanin akwai wata yar tsakuwa da zata ruguza farincikin gidan nan insha Allahu

Yayi murmushi ya wuce yana jin jiki amma ya daure saboda kada munu ta fahimci yana jin jikin nasa maganar Alhaji musaddiq ta tsayawa doctor arai da kuma yaran Sa amma ita hajiya ba abunda ta sanya aranta.

Sororo tayi agurin azuciyarta tace mutun sai shegen taurin ran tsiya komai dai daurin ranka sainaga bayan ka tajuya ta nufi dakinta

Tana shiga ta dannawa BASSAM kira ya dauka muryar sa ciki ya akayi sweet heart bacci ma kakeyi to tashi bacci bai same is ba

Ya zauna kamar tana ganinsa wani abu ne yafaru

Abubuwa bama daya ba wai kasan dan iskan nan yana nan daram nifa wallahi bazan kyaleshi ba yaza’ayi kasamo mana poison mai karfi ne wanda yana sha yayi masa bugu daya kowa ma yahuta

Na biyu na fuskanci inada wata damuwa, “wace damuwa kuma

FARHA na fuskanci koda na kawarda Alhaji to FARHA itace my another problem dan haka ita ba kasheta zanyi ba kassarata zanyi na zaunarda ita takoma batada wani Amfani ba’a kawomun raini. nabar mutun ya zauna lafiya

Munu dan Allah kada ki taba wannan yarinyar kefa da kanki kikace yarinya hankali bai gama ratsata ba

Dakata mun BASSAM aikin ka nasaka kayi dan haka kada ma ka bata bakinka ka ganni nan wallahi zuciyata kamar ta fir’auna nake dan haka ina fada ne tare da cikawa ina jiranka da sakonah…. Ta katse kiran

Tajefar da wayar ai wallahi tunda na kashe mahaifina to banga wanda zan bari ba

Ai kuma wallahi sai na koyawa FARHA hankali😨ALLAH sarki farha na tausaya miki

BASSAM ya rike wayar jikinsa asanyaye shi bai taba ganin zuciya irin ta munubiya ba rama Alkhairi da cuta

Allah ya shirye ki

Yamike ya fice daga hotel din zuwa neman poison dan yazarmasa dole ya nemo

Su Alhaji musaddiq suna zuwa asibitin likita yabashi gado daga nan suka fara kulawa ta musamman saboda yana bukatar kulawar

Hajiya salma ta dade a asibitin sannan ta dawo gida domin bin umurnin likita….tundag lokacin kuma gidan yazama wani iri yakoma ba dadi ita kuwa muguwar tana nan tana kullah yarda zatayi taga ta karasa shi

Saidai wani abu tarasa sanin awace asibitin aka kwantar da Alhaji barantana ta samu nurse ta cigaba dayi mata aiki

Kuma tanajin nauyin tanbayar mum kada ta zargi wani abu gashi bata shiri da baba direba ta rasa Tudun dafawa

Haka ta hakura tana jiran tasamu wata dama

To masu karatu laifin dadi karewa anan zan dakatar da wannan littafin sai mun hadu bayan sallah idan Allah ya kaimu

Ina mana fatan shiga Azumi lafiya

TAKUCE AKULLUN

LAURAT M BELLO

COMMEN
VOTE
SHARE

08164949554

💞💕💞💕💞💕💞💕💞

BANGARE NAH
( part of me)

💞💕💞💕💞💕💞💕💞

WRITING BY

LAURAT MUH’D BELLO

DAGA MARUBUCIYAT LITTAFIN
SUKHAINAH


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦


https://www.facebook.com/104534761033461/[email protected]

ALLAHUM AAJIRNII FI MUSIBATI WA’AKLIFNI KAIRAN MINHA.
AMEEN🤲

Helloooooooooooo my fan’s barkamu da sake saduwa😍

<><><><><><><>1⃣3⃣⏩1⃣4⃣<><><><><><><><>

<><><><><><><><><><>”Haka ta wuni batare da tasan abun yiba jikinta kwata-kwata bayada wani karfi taso matuka ta kawar da Alhaji musaddiq daga doron kasa saboda ganinsa tamkar wani tabo ne azuciyar ta yazama dole tanemi mafita”

“Hajiya salma! kullun cikin kulawa take daga dukanin wani movement na yan gidan kamar yanda likita ya umurceta amma kwata-kwata ta kasa gano komai sai tafara zargin toko a wani gurin ne Alhaji yaci wannan gubar ba anan bane”

Tana zaune adaki kanta yadau zafi, FARHA tashigo dakin tare dayin sallama ahankali ta dago tare da amsawa takarasa kusa da ita ta dafata mummy na fahinci kwanan nan kina tare da damuwa ta ja ajiyar zuciya tare da kirkiro murmushin da baikai zuciyar ta ba ta janyo yarta ajikin tace kada wannan yazar miki wata damuwa rashin lafiyar daddy ce take damuna amma ba komai kinji koh”

Humm! tace mummy nasan ni yarinya ce amma ina kula da idan wani yana tare da damuwa to baran tana damuwar da ta dameki mummy ni nasan akwai wani abu ba iya damuwara rashin lafiyar daddy bane ba”

Kawai dai kina boyewa ne bazan matsa da sai naji abunda yake faruwa bane amma dan Allah mummy ki rage addu’a inaga sai tafi ba yawan tunani ba

Ta dago ina mamakin yanda kike tsara zance farha kamar wata babba dariya tayi mummy ai nima babbace farha bata bar dakin ba har saida taga mummy dinta ta rage damuwar da take shinfide a fuskarta

“Allah sarki ya’ya rahma ne”

” munu ta fito cikin kwalliya ta kece raini. Cikin tafiyarta ta kasaita ta karasa gurin mum ta sunkuya kamar da gaske mum zan fita hajiya salma ta dago tana murmushi tace sai ina munu aka caba kwallaiya haka gidansu wata kawata zanje dubiya Ayyah to sai kin dawo amma dan Allah ka dawo da wuri kinsan bana son yawo

Insha Allah zanyi kokarin ganin na dawo da wuri mum tayi dariya tace yaw’wa dan Allah ki kiyaye kinga Alhaji baya son yawon shi isa nake kokarin kiyaye dokar sa

Azuciyar ta tace zan kuwa yi maganin sa indai nice

“Ta dago tana murmushin mugunta tace b komai mum za’a kiyaye insha Allah ai dake komai yazoh karshe dan nayi kusan karasa aikin

Ba abunda hajiya salma ta kawo azuciyar ta tayi murmushi tace kije kada ki makara ta mike tana yauki ta fita……..

Tana fita gidan baba direba shi kuma yana ficewa daga gidan dan haka ba wata motar da zata fita da ita hakan nan ta fita ta tare adai-adaita sai hotel ahankali baba direba yake bin bayanta har suka isa hotel din akan idonsa ta biya mai adai-adaitar kudinsa yasamu guri yayi parking ya fito cikin shigarda bata taba ganeshi ba saboda ko ni da kyar na iya gane shi yana binta har dakinta da zata hadu da Bassam

“A kofar yatsaya na wasu dakiku kafin daga bisani ya bar gurin zuciyarsa cike da tsoro da firgicin abunda kunnuwansa suka ji masa”..

“Yajima zaune a acikin motar yarasa abunyi sai tufka yake yana warwara ya jaaa dogon numfashi yace yazama dole nasan abunyi bazai yuyu nabar wannan yarinyar ta aikatawa iyalan Alhaji musaddiq abunda ta kudirah ba koda zan rasa numfashi na yafada cikin daga murya idanuwansa ya kada yayi ja tamkar wani zakii!….

Da karfi yaja motarsa yabar harabar hotel din zuciyar sa acunkushe

Kai tsaye asibitin da aka kwantar da Alhaji musaddiq ya nufa bai wanisha wahalar ganin saba kasancewar sa sanenne a asibitin

“Har dakinda aka kwantar da Alhaji yashiga, “ganinsa yasanya shi shiga wani hali dan gaskiya jikin ba’a cewa komai saidai godiyar Allah
Kwance yake kamar wata gawa dan yakara week sosai

Tausayinsa da na iyalinsa suka kara dabaibaye zuciyar baba direba hawaye masu zafi suka gangaro masa yakarasa gurin gadon da yake akwance ahankali yasoma magana”

“Sannu yallabai ya karfin jikin?”

“Daga kansa yayi yabude bakinsa cikin matsanan cin jinjiki ahankali yace Alhamdulillah”

“Baba direba yace Allah ya kara sauqi Alhaji Allah yatashi kafa dunka ya mayarda kai cikin iyalinka…,,

Ya dago jajayen idanuwansa yasoma magana baba direba jikina yana bani bazan tashi ba inajin rabuwar mu ta kusa saboda yanda nakeji nikadai na sani

Ya karasa kusa dashi ya janyo hanuwan sa Alhaji kadai na fadar haka insha Allah zaka tashi zaka koma rayuwa kamar da cuta ba mutuwa bace….

Ya lashi busassun lebunan sa yace kaje ka dauko mun hajiya da yarah na inason muyi sallama tunkafin ruhina yabar gangar jikina

“Hankalin baba direba yakai kololuwar tashi, jikinsa yayi matukar sanyi yana kuka haka yafice daga asibitin ya nufi gida dauko su hajiya….

“Tana daki azaune jinta take wani iri haka kawai jikinta yake yimata nauyi, FARHA ta shigo dakin tareda ASHRAB azaune suka tadda ta tayi tagumii cikin sauri suka karaso gunda take mum lafiya suka fada lokaci guda….

“Ta dago bakomai haka kawai nake jin bana jin dadi hawaye suka gangaro mata jikina yana bank wani abu zai faru damu marar dadi ya’yanah inajin tsoron abunda zai faru”

“Jikinsu yayi matukar sanyi mum menene yafaru Ashrab tafada a raunane?”

“Jikina ne yake sanar dani something bad is going to happen”

“Mummy kisanar damu idan a kwai wani abu dan Allah”….

“Suna cikin haka delu ta shigo tare da yin sallama ranki ya dade baba direba yana magana,

“Ta dago to kawai tace kice dashi ina zuwa,

“Suna fitowa paloun ayanda ta hango baba direba tasan tabbas akawai wani abu ta karaso cikin sauri baba lafiya dai koh? “naga kamar kana cikin damuwa”

“Yayi kokarin saita nutsuwar shi yace insha Allahu hajiya Alhaji ne yace nazoh na dauke ku yana son ganin ku…. “Gabanta ya yayi mummunar faduwa bakinta yana rawa ta soma magana baba direba kada fah hasashena yazama gaskiya dan Allah kace dani zato kawai nake ba gaskiya bane…….. “Jikinsa yakara sanyi yace babu wani abu kada ki sanya komai aranki Alhaji yasami sauqi sosai…….. Tamike muje baba bazan sami nutsuwa ba matukar idanuwana basu ganemun shiba bazan ta’ba samun nutsuwa ba”…..

“Gaba dayansu suka fita suka nufi asibitin”……..

“Kirjin ta sai bugawa yakeyi babu sassauci saboda fargaba zuciyarta a tsinke take ahankali ta tura kofar dakin tare da yin sallama arufe yake har kansa da farin mayafin da ganinsa kadai ya isa ya sanar dakai tabbas akwai wani mumman al-amarinda ya faru”

“Jikinta yana rawa ta karasa gurin ahankali ta daga mayafin kwance yake tamkar kace tashi ya tashi amma ina rai yariga da yayi halinsa wata razananniyar kara tasaki tare da sulalewa kasa a sume”

“Allahu akbar😭

Kumuje zuwa my fan’s kuyi hakuri kunjini shiru kwana biyu nayi nauyi ne

I love you all my fan’s

Daga laurat m bello

Share
Vote

Comment………….

💞💕💞💕💞💕💞💕💞

BANGARE NAH
(part of me)

   💞💕💞💕💞💕💞💕💞

WRITING BY
LAURAT MUH’D BELLO

DAGA MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH

AND NOW
BANGARE NAH
(part of me)

~BISMILLAHIR~RAHMANIR~RAHEEM~………

~ALLAHU AKBAR KABEERAN~


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦


https://www.facebook.com/104534761033461/[email protected]
                *1️⃣5️⃣⏩1️⃣6️⃣*

<><><><><><><><><>”Tim kawai sukaji hajiya salma ta danfara a tayil dinda yake shimfide a dakin cikin gaggawa sukayo kanta suna kuka mummy ki tashi, haka likitoci suka kawo mata dauki cikin gaggawa emergency aka nufa da ita saboda asamu a ceto ranta”………….
“Yayin da yaran abun duniya ya ishesu Farha ta karasa gurin da daddy yake akwace kamar kace dashi tashi ya tashi cikin shesh shekar kuka take magana daddy nah nasan kana jina dan Allah ka tashi kada ka manta da alkawarin da ka daukar mun kace zaka rayu tare damu bazaka taba rabuwa damu ba me yasa zaka karya alkaqwarin da kayi
Muna matukar bukatar ka a kusa da Allah ka tashi ta fada jikin gawa ta cigaba da kuka kamar ranta zai fita
Ashrab t matso kusa da ita cikin kuka ta janyota jikin ta Kiyi hakuri autar daddy duk irin alkawarinda mutun ya dauka baya ta’ba cika shi saida izinin Mahaliccin sa dan haka kiyi hakuri daddy ya tafi kuma bazai ta’ba dawowa ba saidai muyi masa addu’a Allah ya sadashi da rahma”
Ta janye daga jikinta a’a Ashrab kada muyi haka dake da bakinsa ya gayamun haka dan haka ki bari naje na tayar dashi ninasan yana sona zai tashi
Wallahi ina son daddy bazan iya jure rashin shi ba shi isa bazan bari zuciyata ta sabu da yarda da yatafi ba jikina yana bani da daddy na yana nan da ransa doguwar suma yayi
Kuka mai karfi ya subuce mata katashi daddy dan Allah katashi gidan mu zai zama kamar kango idan har baka tare damu kada ka manta da yanda muka shaku muke rayuwa mai dadi cikin so da kaunar junan mu daddy dan Allah ka tashi……
Likitoci suka shigo farha na ganin sun doshi gurin daddy ta cikin sauri ta taso cikin daga murya tace kada ku kuskurah kuce zaku taba mun daddy daya daga cikin su ya masto kusa da ita kiyi hakuri Farha daddy ya rigada ya rasu abunda zai zamar masa gata ayanzu a kai shi makwancin shi kiyi hakuri ki fawwalawa Allah komai saiki ga ya sanya miki sassauci acikin ranki
Ta dago jajjayen ida nuwanta tace kana tunanin na yard da daddy ya mutu, to idan ma kana tsamanin haka tunanin ka yagayamaka ba dai-dai ba dan ni nasan yan nan da ransa……
Tausayin yarinyar yagama cika zukatan su domin kuwa sukansu sun san irin shakuwar da family yayi amma ba yanda aka iya hakan nan za’ayi hakuri
Baba direba ya kasa cewa komai tausayin yaran ya gama dabaibayeshi ya matso kusa da Farha da ta kankame gawar daddy ta hana kowa yaje kusa da ita har Ashrab tsaye take tana kallon yar’uwarta tana kuka ta kasa aiwatar da komai……. Cikin dabara ya matsa kusa da ita ya tausasa muryar shi yace yarinyar daddy ni nan ina bayanki bazan bari atafi da daddy ba saboda nima ban yarda da ya mutuba kinga karbi kisha ya mika mata lemo mai sanyi kamar jira take take ta karba ta sha sosai kafin yan mintina tafara ganin mutane dishi-dishi can kuma ta sulale kasa bacci mai nauyi yayi gaba da ita
Baba direba ya taimakawa Ashrab suka daurata agadon da yake kusa dana gawar Alhaji cikin sigar rarrashi yace kiyi hakuri hakan da akayi shine kawai mafita saboda idan har tana gani bazata yarda ayi komai ba bada wata manufa nayi hakan ba hasalima banyi hakan ba saida umurnin likita Ta dago na fahimta baba nikaina nasan hakan shine kadai mafita
Ta ja dogon ajiyar zuciya tace ya jikin mum ya jijjaga kansa jiki kam ba’a cewa komai saidai addu’a amma hajiya tana cikin wani hali
Ta share hawayen da suka gangaro mata tace baba direba wannan wace irin jarrabawa ce tazoh mana alokaci daya.
Kada ki damu Allah yana iya sauya rayuwar kowane bawa alokacin da yaso yakuma ga damar hakan ita jarrabawa Allah yakanyiwa bayinsa ne saboda ya gwada imanin sa idan kayi hakuri ka jure sai Allah ya buda maka ta inda bakayi zato ba
“Ta kara goge hawayen da suka gangaro mata wallahi baba direba dauriya kawai nake ji nake kamar nima mutuwar zanyi, …….”haka mutuwa take ya’ta musamman ta iyaye sai dai hakuri amma akwai d’aci ya mike bara naje likitoci suna jirana ya fice daga dakin yana goge hawaye”….. ‘Kafin kace meye wannan duka yan’uwa da abokanan Alhaji musaddiq sunji rasuwar sa na kusa da na nesa kowa ya zoh ba’a samu yin jana’izar saba sai washe gari alokacin hajiya salma ta farfado Farha ma haka sadai ita hajiyar zaune kawai take bata cewa da kowa uffan sai hawaye dasuke zuba tamkar fanfoh……
Bayan an kammala shiryashi aka kawashi gurin iyalansa suyi bankwana hajiya salma ta kasa cewa komai sai kuka da takeyi farha tayi zaune kamar mutun butumi itama dai kamar bata cikik hayyacinta dan maganganun da take kadai sun isa su tabbatar da hakan….. Kusan kowa da yake gurin saida ya zubar da hawaye domin kuwa iya tausayi wad’anan iyalan sun bawa mutane tausayi matuka haka aka dauke shi aka fitar dashi domin sadashi da makwancin sa na gaskiya……..
Gidan yayi shiru mutane sai kaiwa da kawowa suke yan zuwa gaisuwa…. Mahaifiyar munubiya itama tana gidan saidai wani abun mamaki da daure kai duk wannan abun da akeyi munu bata sani ba domin kuwa tun jiya bata gidan tana can hotel tare da abokin sha-shancinta suna sheke ayarsu tun adaren jiya maman ta take neman wayar ta amma akashe
Haka uwar takwana acikin kunci da kuma Allah wadarai da halayyar munu ace gidan da kake zaune ayi rasuwa amma kai bakada ko labari Allah dai ya kyauta…..

“Washe gari sai 10:00 pm na dare ta dawo gida tun a gate din gidan taso ta gane akawai abunda ke faruwa amma saboda batada mutunci ta share da baba direba tafara haduwa tayi masa kallon wulakancin da ta saba tayi shigewar ta ciki batare da tayi masa magana ba kamar ya sanar da ita amma kuma yanda yake cike da jin haushinta sai ya fasa yaga to meye amfanin hakan dama ita hakan zata soh tunda dama ba wani jituwa sukayi ba…. Ta baya tabi saboda bata son kowa ya ganta baran tana a dameta da tambayar ina ta kwana tana shiga ta yi wanka tabi lafiyar gado kafin yan mintina bacci yayi gaba da ita”…..

Wannan ke nan

Tun asuba maman munu ta nufi dakinta tajima tana buga kofar amma shiru zuwa yanzu hankalin ta yafara tashi anya munu tana da hankali kuwa….. Can taji anbude kofar cikin masifar da tasabayiwa delu amamakinta taga maman ta ta tsaya cike da mamakin ganinta lafiya tace da ita kekuma yaushe a gari me kika zoh yimun da sassafe daki….”maganar ta kona mata rai matuka ta dake ta dannah kanta cikin dakin batare da tace da ita komai ba,….. “Tana mai jin haushin maman zata takura mata tace wai yaushe kika zoh ne kuma ma me kika zohyi nifa wallahi bana son takurawa nan dinma bazaki barni na huta ba sai kinbiyoni ki takura mun”….
“Ta dago jajayen idanuwanta tace bazaki taba gyarah rayuwar ki ba kenan munu banzoh gidan nan dan na takura miki ba hasalima dalili ne ya kawoni ta share hawayen da suka gangaro mata tace,
” Kina da masaniyar abunda yafaru kuwa? ta dago tana mata kallon raini tace ni ki gaya mun kawai sai wani janrai kike yi me kuma yafaru? “
” Allah yayiwa Alhaji Musaddiq rasuwa yau kwan biyu kenan
Babu kunya ba tsoron Allah munu ta daga hanu tasoma magana Alhamdulillahi nayarda kwallon mangwaro na huta da kuda”
” Kan Aisha yayi mugun kullewa da zantukan munu me kike nufi da hakan me kike nufi dayin hamdallah rasuwa fah nake gaya miki amma naga kamar ma hakan kikaso

“Ta dago bazaki ganeba bantaba tsintar kaina afarin cikin da na tsinci kaina ba yanzu zanbaki goron Albishir ta bude baki zata kara magana ta dakatar da ita ya isa haka sarkin zuba ki tafi inason zan kara yin bacci kafin na zoh naga iyalan ALHAJI MUSADDIQ…… naga kuma waye yakamata yazama next targate”

“Ta sheke da dariya kamar wata boss”

“Tooooooo🙄wannan family’s kun hadu da bala’i sadai addu’ace zata fiddaku daga tarkon munubiya”

“Kuyi hakuri zan dinga yimuku kadan saboda zaman typing din yana yimun wahala yanzu”

TAKUCE AKULLUN

LAURAT M BELLO

SHARE
VOTE

COMMENT……………… ..

💞💕💞💕💞💕💞💕💞

BANGARE NAH
(part of me)

 💞💕💞💕💞💕💞💕💞

STORY & WRITING BY
LAURAT MUH’D BELLO
(Maman khairat)

MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH

AND NOW
….BANGARE NAH
part of me

~ALHAMDULILLAHI ALAKULLI HALIN~

~WANNAN SHAFIN NAKI NE KIYI YANDA KIKE SO DA ABUNKI SHUGABA TA GARI
WATO AUNTY HAU’WA MAMAN USMAN ALLAH YAKARA MIKI HAKURI DA JURIYAH~
~AMEEN YA ALLAH~


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦


https://www.facebook.com/104534761033461/[email protected]

¶BISMILLAHIR¶ RAHMANIR¶ RAHEEM¶••••••

  *A'UZU BIKALIMATILLAHI TAAMATI MINSHARRI MA KALAQ*
     *AMEEN*                  1️⃣7️⃣⏩1️⃣8️⃣

“Sai da tasha baccinta tukunah ta fito zuwa bangaren hajiya salma tana zaune dai kamar kullun bata iya cewa komai sai sharar kwallar da take wacce ita ta zamar mata tamkar abinci yaranta suna kusa da ita a zaune kowa zuciyar sa ba dadi, ta shiga cikin nutsuwa kamar ta kirki hawaye suna zuba kamar fanfoh”…..
“Tunda ta shigo farha ta sakar mata wata uwar harara, ji take kamar ta shaketa dan takaici, haka kawai takejin matukar kiyayyar ta aranta munu bata zame ko’ina ba sai kusa da hajiya salma tana zuwa ta rungumeta ta kara fashewa da kuka mai shiga zuciya,……

“Hajiya salma ta kara rungumeta sosai tana kuka mai tsuma zuciya

Farha datake kusa da ita ta mike a fusace ta finciko ta gefe bama bukatar kukanki na munafurci,

“Yau daddy kwanansa biyu da rasuwa amma sai yau kike kuka sai yau kika san da rasuwar shi sai yau kikasan da iyalansa”

“Wallahi na tsane ki inajin tsanarki acikin zuciyata ta bar gurin cikin kuka”

“Hajiya salma ta kalleta tace kiyi hakuri kada maganganunta su tasiri a zuciyar ki Farha har yanzu ita yarinya ce kara”…

“Tayi wani shu’umin murmushi ba damuwa mum nasan dacin mutuwar ne bai gama sakin taba hakan bai wani dameni ba”…..

“Haka rayuwa tacigaba da tafiya agidan margayi Alhaji musaddiq zaman kadaici darashin wallawa yacigaba da gudana agidan ..yayinda munu tacigaba ta kulle-kullenta na ganin tasami babban mukami a kamfanin su hajiya salma”

“Sai bayanda hajiya tagama takabar ta takoma aiki amma kana ganinta kasan bata tare da wallawa tunanin Alhaji ya gagarah barin zuciyar ta komai takeyi sai ya fado cikin ranta”

“Haka yaranta Ashrab da munu dukansu suna aikin a kamfanin yayinda Farha taciga da karatun ta”

“Tunda munu ta fuskanci ana samun makudan kudi akamfani ta kudira aranta duk yanda zatayi sai kamfanin ya dawo hanunta saidai wannan lokacin tana bin abunne cikin hikima gudun kada ayi saurin gano shirinta……


BAYAN WANI LOKACI MAI TSAHO


“Tun bayanda Alhaji musaddiq ya yarasu yau kimanin shakara uku ke nan amma hajiya salma ta gagarah yin aure gani take tamkar idan tayi aure ta ci amanar kaunarda take masa ne

Wata ranar lahadi suna gida kasancewar ta week end ne tana zaune ita kadai adaki tayi zurfi acikin tunani munu tayi sallama tashigo dakin

Ta sauke ajiyar zuciya tare da amsa sallamar murmushi tayi a’a munu fita zakiyi ne ta tambaya?

A’a gunki nazoh da akawai maganar da zamuyi ne

To bismillah ina jinki tayi shiru tana tunanin ta inda zatafara hajiya salma

Tace da matsala ne naga kamar kina cikin damuwa

Taja ajiyar zuciya mai karfiii hummmm!

Mum dama ba wani abu bane dama wani ne yazoh gunki yana palourn kasa yana jiranki nayi kokarin ganin na hanashi amma saida ya shigo

Hajiya salma ta yatsine fuska mamaki karara ya bayyanah afuskarta tasoma magana tace wani kuma to daga ina?

Banida wani wanda mukayi dashi zaizoh nemana

Amma kice dashi ina zuwa just give me five minit ina futowa…….

To tace tafice daga dakin zuciyarta tana dakan uku-uku dan bata san yanda hajia zata karbi abun bah

Cikin yan mintin ta fito sanye cikin wani pink din material mai matukar santsi da sheki fuskarta ba kwallaiya amma tayi matukar kyau dama hajiya salma badai kyau ba sai dai yar rama da tayi kadan wannan kuma bayada nasaba da yawan tunin tsohon mijinta uban ya’yan ta….. dayazamar mata tamkar ibadah….

Yana tsaye rungume da hannayensa ya juya bayansa baza a iya hango fuskarshi ba amma zaka iya hango tsantsar kyan surarshi dakuma kuriciya

Tana dosar gurin gabanta yafadi sakamakon jin kamshin turaren sahibitinta kuma abun kaunar ta Alhaji musaddiq da sauri ta karasa gurin da yake tare da yin sallama

Yajiyo ahankali tare da amsa sallamar kyakkyawa ne na ajin farkon fari ne tas dogo ne mai yalwataccen fadin kirji sajenda yake kwance a gefen fuskarshi yakara sanya asalin kyansa ya fito sosai

Saida tayi da gaske ta iya dai-daita kanta sannan ta ce dashi bismillah kazauna mana

Shikansa baiyi zaton haka take da asalin kyau ba tabbas yau ya samu dame akala dan agaskiya yanda munubiya take gaya masa hajiya sai yaga kamar ba abunda ta fada acikin rabin kyanta

Aransa yace lallai yasan zai kwashi rabonsa dan ya tabbatar da sauran ta……. Jikinta ya tabbatar masa da hakan

Haka zuciyoyinsu suka fada kogin tunani alokaci guda

Can hajiya salma takatse shirun da tsambayar dan saurayi ban ganekaba ko su Ashrab za’ayi maka magana dasu……. Yayi murmushin gefen baki wanda ya kara futoda kyansa karara ya nisa yace

Gunki dai nazoh

Yabata amsa yana mai yin kayataccen murmushi abun yabata mamaki matuka ni kuma?

Yes yace nazoh ne da kokon barata agareki ma’abuciya kyau da kwarjini

Kalaman sa sun soki zuciyarta matuka amma ta share

Tace nayi mamaki kuwa duba da ganinka yaro matashi kyau ace yarinya kaje gareta bani ba

Kada kiyi saurin yanke hukunci nike nakeso kuma ke nakeson takasance mun wani bangare nah tabude baki zatayi magana ya dakatar da ita

Zanbarki kiyi tunani idan kin gama ga kati na nan akwai duk wasu bayanai na aciki SUNANA BASSAM ASIM na barki lafiya ya fice daga palourn cikin tafiya ta kasaita……..

Hummmmmmmm!!! Lallai akawai kwakwakiya kenan

Toko yaya za’ayi da su Farha iyayen rigima

Dan tabbas idan har tasumu labari akwai babbar matsala

Takuce. AKULLUN

LAURAT M BELLO

IDAN HAR BANGA RUWAN COMMENT BA TO ZAN AJIYE ALKALAMIN NAH NA HUTA DAN BAZAN DINGA WAHALA BAH

COMMENT YA GAGARAH

INA BUKATAR GANIN CANJI DAKA GAREKU…………

💞💕💞💕💞💕💞💕💞

BANGARE NAH
(part of me)

   💞💕💞💕💞💕💞💕💞

STORY&WRITING
BY
LAURAT MUH’D BELLO
(maman khairat)

MARUBUCIYAR LITTAFIN
SUKHAINAH

AND NOW

BANGARE NAH
part of me

Bismmillahir rahmanir Raheem

Ina farawa da sunan Allah mai rahma mai jikai……

Wanna shafin nakune masoyan littafin BANGARE NAH…. ALLAH YABAR KAUNA AMEEN YA ALLAH……..


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


💦{Arewa ginshiƙin al’ummah}💦


https://www.facebook.com/104534761033461/[email protected]
       ...  ...   ...    ...  1️⃣9️⃣⏩2️⃣0️⃣

“BASSAM ASIM! shine sunan da taketa mai-maitawa a zuciyarta hakika abun yazo mata a bazata”

“Yaron tabbas yayi saidai kuma yarintar shi itace abar dubawa tayaya zata iya tarayyah da yaronda ta kusa haifa wannan dacewar shi Ashrab shine dai ba ni ba”

“Tayi zurfi atunani Farha ta shigo palourn bakinta dauke da sallama ta mai-maita sallamar har kusan sau uku amma hajiya salma bata ma santana yiba hakan sai ya bawa Farha mamaki matuka”

Kusa da ita takarasa tare da dafa kafadar ta mummy lafiya inata sallama amma naga kamar hankalinki yana wani gurin firgigit!! tayi ta dawo cikin hankalinta,

Na am Farha baby kin dade ne ban jiba ta zauna akusa da ita ta janyo hanayenta mummy nah lafiya? Meyake faruwa ne kinsan fah bana son damuwar ki

Hajiya salma taja dogon ajiyar zuciya tace bakomai yarinya ta damuwar tana da nasaba da office ne kada hakan yazama damuwa agareki kinji yarinyar dady takarasa maganar cikin sakakkiyar fuska tamkar ba wani abun da yake damunta…….

“Haka ta zauna cikin tunani tsahon dogon lokaci batare da ta sanarda yaranta komai ba

“BASSAM yana fita daga gidan ya kirah munubiya tana murmushin samun galaba hello tace cikin narkewar murya yace my sweet heart every things is don kuma ga alama komai zai tafi yanda aka shirya shi”

“Ta sheke da dariyar samun nasara tace dama na gaya maka ai bana tunanin dama rashin samun nasara saboda ban taba farawa nakasa karasawa ba”

“Ya lumshe idanuwan sa yace ai na fahimci ta fada fah”

Tayi dariya tace dama nasan zata fada bana tunanin akwai macenda zata kasa fadawa komar ka BASSAM kaidin na daban ne ni nasani

Saidai kuma inason kasani wannan auren na manufa ne ban amince kasaki jikin ka sosai ba dan Wallahi banida kyau kuma kai ma kasan da haka

Ya lumshe idanuwan sa kamar tana ganin sa yace kada wannan yazamar miki damuwa ai bana tunanin akwai wata matar da zata fiki matsayi a gurina”

Yanda yayi maganar har wani yarrrrrrr taji jikinta yayi ta lumshe idanuwanta ina fatar haka BASSAM saboda bazan iya sharing dinka da kowa ba kaidin na musamman ne agareni ina sonka sosai…… Ko wannan zan daure ne kawai saboda inada abunda nake nufi da hakan amma idan ba haka ba babu gangan cinda zai sanya nayi wannan danyen aikin”

🙄tabdijam”……

BANGAREN HAJIYA SALMA

Tunani kyakkyawar fuskar shi ya gagarah barin zuciyar ta yayinda sunan sa yake yawo acikin zuciyar ta bayan ko wacce dakika kala mansa sunyi matukar tasiri azuciyar ta

Ta ja dogon hajiyar zuciya hummmmmm!!

A hankali take tambayar kanta me hakan yake nufi ya kamata ki nutsu Salma wata zuciyar take sanar da ita

Kada kyau da kuruciyar shi yayi tasiri azuciyar ki, ki ajiye wannan shirmen gefe zuciyar ta takara sanar da ita…..

Ta kwanta sosai a kan gadon ahankali tace me yake shirin faruwa dani ne ta runtse idanuwanta gam… Tabbas yakamata na dawo cikin hankalina.. Soyayya ba tawa bace abun kunyar ma da yaro sa’an kanina mtssssss taja dogon tsaki wannan ai abun kunya ne”

Har karfe 12:00am na dare tana abu daya can wayar ta tashiga neman taimako tayi matukar mamakin ganin waya awannan lokaci ta sanya hanu ta dauka number an boye ta abun ya kara daure mata kai ta share har saida ta tsinke aka kara kira karo na biyu nan ma taki dauka kirrrrrr taji shigowar sako yashigo da har ta share shi wata zuciyar tace ki duba mana ta janyo wayar ta bude

My soul shine rubutun farko a sakon
Gabanta yafadi shine sunan da Alhaji musaddiq yake kiranta dashi a mafi yawancin lokaci.

“Tunaninki yaki barin zuciyata tsahon dogon lokaci soyayyarki taki barina sukuni
Ina neman sassauci daga ma, abuciya kwarjini da kamshi hakika kedin haske ce wanda baya ta’ba disashewa

Ki tausayawa zuciyar masoyinki mai matukar kaunarki …………

Akwance take amma saida ta mike zaune ta maimata karanta sakon yafi akirga

“Kalamansa taketa mai-mai tawa taja ajiyar zuciya mai karfi na shiga uku….

“Ta furta ahankali ya zanyi,….. “Yayita kira amma takasa samun sukunin dauka saboda zuciyarta tagama rauni…,,

“A nasa bangaren murmushi yayi na gefe baki yace a fili salma yanzu muka fara bazan taba kyaleki ba har sai na cika burin zuciyata akan ki”

“Soyayyar gaskiya nake miki ba wai son yarjejeniya ba dan Haka bazan taba hakura ba 🙄tabdijam lallai akwai tashin bama-bamai kenan idan har munu tagano manufar ka”…..

“Ashrab da Farha sun gama fahimtar mum dinsu tana cikin damuwa amma abun mamaki taki ta sanar dasu komai sunyi tambayar duniya amma amsarta bata wuce ba komai”

“Hakan nan suka hakura badan sun yarda ba ,.. Munubiya kuwa farinciki fal zuciyarta dama haka takeso domin kuwa hakarta ta fara cimma ruwa saida Farha tatafi school tukunnah ta nufi dakin hajiya salma, tana zaune kamar kullum tana aiki wato tunani munu tayi sallama ta shigo dakin tundaga nesa tasaki murmushi sannan ta karasa gurinta ahankali ta dafa ta mummy lafiya naga kamar kinada damuwa,….. “Ta dago tare da jan dogon ajiyar azuciya kana tace”

“Ba kama bace munu ina tare da damuwa wallahi tun lokacin da bassam ya bayyana cikin rayuwata banida sauran sukuni har yau…… Cikin rashin fahimta tace waye kuma haka mum ta dago wannan bakon mana tajim alamar tunani can tace aw wannan yaron na kwanaki ta jinjina kai shi munu…… Kece kike ganinsa yaro amma zuwanshi yana da tattare da abubuwan al-ajabi kamar yaya mum?

“Hakika yazoh da babban al-amari munu ta dago nifah ban ganeba har yanzu mum ta rigo hanunta sona yake munu.. Kalmar so da ta furta Bassam yana yimata ya yi matukar kona zuciyar munu ta rintse idanuwanta wata zuciyar tace ki nutsu munu ta yi murmushi tace….

“Ni aganina wannan ba abun damuwa bane ki amince mana inaganin yafi zaman ki ahaka kada ki manta shekarun ki karuwa suke zamanki ba miji inaga baiyi ba”

“Na sani munu ba abunda nake tunani sai ya’yanah matsalar ta yarana ce bansan ya zan sanar dasu ba abun kunyar ma ni yaron yayimun kankanta wallahi inajin kunyar sanarda Ashrab da Farha gaskiya”

“Kan uba Bassam dina ne karami ta fada azuciyar ta a fili tayi dariya tace nifa har yanzu banga wata damuwa ba inaganin ki amince kawai tunda naga kamar kina son shi,……. “Tayi shiru na yan dakiku kana tace bansani ba har yanzu ban tantanceba kaina yashiga caji na rasa tudun dafawa”

“Munu ta dafa ta tace kiyi abunda zuciyar ki ta yarda dashi kada kibari damarki ta kubuce miki yaranki bazasu zama silar rugujewar farin cikin ki ba ta mike wannan itace shawarata….. “Tana gama magana ta fice zan wuce office sai kin fito”……

“Bata samu damar amsawa ba saboda kanta ya kulle matuka ahankali tace tabbas inajin wani abu gameda Bassam tokuma ya zanyi da yarah nah,……. “Wani bangare daga cikin zuciyar ta yace ki hakura Salma inaganin zaifi kiso farincikin ya’yanki”

“Wata killa yaron yanada wata manufah akan ki KIRJINTA yayi wata mummunar faduwa RASSSSSS!!! .sai a lokacin tafara wani tunani na daban”

“To idan haka nefa ya kenan wunin ranar duka ba inda taje office dinma kasa tafiya tayi haka tayita tunanin mafita”…..

“Karfe 5:00pm dai-dai BASSAM yayi parking a kofar gidan hajiya salma a lokacin baba direba yana zaune shi kadai agurin yayi mamakin ganinsa a gidan yataso saboda ya murza masa rashin mutunci yace malan dakata gurin wa kazoh Bassam ya dago cikin kallon rainin wayo yace gurin masoyiya ta Salma nazoh ko kanada matsala da hakan….. “Gaban baba ya fadi ya yadago da sauri wace Salma”

“Yace wacce kasani bani guri kajikoh kana bata mun lokaci ya bangaje baba yayi shigewar shi ciki kansa tsaye tana zaune a palourn tana kallon wata tasha kamshin sa ne yafara ziyartar hancinta ta lumshe idanuwanta a tunaninta ko gizo ne kawai batayi auneba tajiyo sallamar sa cikin sassanyar muryarsa mai dadin sauraro ta jiyo a cikin sauri sukayi ido biyu da juna”…………

“Dan Allah kuyi manage dashi zaman yana bani wahala yanzu”

TAKUCE A KULLUN

LAURAT M BELLO

SHARE
VOTE

COMMENT…………….

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button