BABU SO – PAGE 74 – 75

*_❤🔥BABU SO....!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
BABU SO👉🏻AREWABOOKS
74
…….Dariya kawai yake dannewa dan sarai duk ya gama fahimtar inda ta dosa. Sai dai shi yasan a yau bawai zai iya haƙuri bane gara ya maidata ƴar hannu a wuce wajen. Amma a zahiri ya basar tamkar bai san mitake ba. Dan koda ya kammala shan shayin toilet ya shiga ya dauro alwala. Shafa’i da wutiri yayi sannan ya hawo gadon bayan ya fita ya leƙa tsakar gidan ta windows ɗinsa na falo. Ganin babu wani damuwa ya dawo bedroom ɗin shima ya hau gadon ya kwanta. A hankali ya kwanto bayanta yana mai ɗaga duvet din da taja har saman kanta.
“Bana faɗa miki ni ba’a juyamin baya a gado ba?”.
Shiru tai ita ala dole tayi barci. Yaji a jikinsa pretending ne kawai, dan haka ya fara mata cakulkule. Duk yanda taso fiskewa hakan ya gagara, dole ta fara dariya da ture hanunsa. Bai bartaba har sai da yaga ta juyo yanda yake bukata. Ya haɗe goshinsu waje guda yana murmushi. “Ni na rasa miyasa kika rainani”.
“Saboda kana mun mugunta mana”. Ta faɗa tana murmushi.
“Kin cika tsokana ne shiyyasa”.
Hanunsa da yake cusawa jikinta ta mintsina. “Ouch!!”. Ya faɗa batare daya janye ba. Murmushi tayi zata kauda kanta ya riƙo fuskar. Duk yanda taso ƙwacewa babu damar hakan. Dan wani salo ya ɗauka wanda yasha banban da karatun farko daya koya mata. Cikin kankanin lokaci ya sakata sakin masa jiki ya fara yanda yake so. Tafiya tayi tafiya sun gama cakuɗa juna yanda suke so ya ɗauka babban hanyar garden. Ai tuni mutuniyar taku ta fara sakin magiya da roƙo amma ya nuna mata sam yau babu ɗaga ƙafa garden zai sake komawa ziyara. Hankalinta bai kara tashi ba sai da taji yana ambaton addu’a…
Wiya kam dai yau ma ta shata, duk da dai ba irin ta farko bace dan babu ma haɗi, dan yau ya bita a hankali kamar yanda Dr Bilkisu ta gargaɗesa. Yau din ma dai harda kukanta. Amma baiyi nisaba kamar na waccan ranar. Tasha albarka kala-kala tare da daɗaɗan kalaman da suka sanyaya mata rai raɗaɗin taji ya raguma. ya taimaka mata ta shiga ruwan zafi kafin su dawo gadon ya bita da tukuycin tausar data sakata yin barci. Ajiyar zuciya ya sauke mai nauyi da sake sakar mata kiss a lips da idanunta yana faɗin, “ALLAH yay miki albarka”. Daga haka shima ya rungumeta suka lula duniyar barcin tare..
WASHE GARI
Rashin sabon ɗaukar gabaran gida kafin fita aiki yasa saida taimakonsa dana Aysha suka shirya fita akan lokaci, gashi sai langaɓewa take wai jiya ya wahal da ita. Shi dai nashi murmushi kawai, itako tana faman tura baki da tsuke fuska. Kamar kullum tayi ƙyau cikin kayan hidimar ƙasa, sai dai ta ɗaura Abaya yau a sama sannan ta naɗa veil ɗin abayar a kanta. Ƙin fitowa tai har saida ya shiga sashen Fadwa sukai sallama ya fito sannan ta fito suka wuce. A hanya take tambayarsa yaushe zata fara koyan tata motar. Shiru kamar bazaice komai ba. Sai da ya kaucema mai napep ɗin dake neman shiga masa hannu sannan ya ɗan dubeta bayan yaja tsaki da yima mai napep ɗin daƙuwa.
“Mu bari weekend, idan kuma Fadwa ta koya miki to?”.
Baki ta tura gaba sai dai batace komai ba. Hakan yasashi fahimtar zancen nasa bai amsu ba. Ya girgiza kai kawai ransa fal mamakin kishin matan nasa. Ita kanta Fadwan daru ya barta tanayi akan fitar tashi da Anaam. Wai sai dai idan ranar girkintane kawai zasuke tafiya tare. Amma ranar nata bata yarda ba. Itama baice mata komaiba yay fitowarsa, to ga Anaam ɗin ma yace Fadwa ta koya mata mota ta nuna bata so.
Ita ya fara saukewa, da gargaɗi mai girma akan Yaseer sannan yay gaba. Ya samu tarba ta musamman a wajen staffs nashi. Inda sukai ƴar gajeriyar walima lokacin break acewarsu tunda ba’ai ta aure ba. Kasancewar ya samu aiki da yawa Khaleel ne yaje ya maida Anaam gida, shiko sai bayan isha’i ma ya kona gidan. Sanda ya iso ya iske komai yanda yake buƙata, dan dawowar Anaam ɗin tayi amfani sosai.
Yau ɗin ma dai yasha sharafinsa, inda mutuniyar tasa taita masa raki, baibi takanta ba, amma yabita a sannu gudun ɓaro aiki. Washe gari har wani farin ciki takeji zai koma wajen Fadwa ta huta, duk da dai kishinsa na zaune daram a ranta babu sassauci. Safiyar talata sai dai yayma Fadwa ƙaramin hauka akan fitarsa da Anaam sannan suka samu dai-daito, dan ta dage bazai ɗauka Anaam ba dan ranar girkintane. Amma ganin ya juye mata yanda bata kauna dole tai shiru, ya fita ya barta tana rusar kuka
Haka kwanaki suka cigaba da tafiya, tun Anaam na masa raki a duk ranar girkinta harta fara zama ƴar hannu, duk salon da yazo mata da shi zata amsa kuma ta bashi haɗin kai yanda zai samu farin ciki. Babu abinda ya dameta da sabgar Fadwa, abinda ke gabanta kawai takeyi, sai dai kuma bata ragawa idan Fadwan ta shiga shirginta. Dan kuwa saita tsefeta tas ake samun zaman lafiya a gidan. Shareff yayi kurarin yayi masifar akan tsiwarta amma a banza, dan tace in ba'a shiga gonartaba bazata shiga ta mutum ba. Ita kuma Fadwa tsokanar magana ne matsalarta. Komai ta gani saita tanka. Duk kankantarsa sai tayi magana ga Shareff ɗin ko ga Anaam. Sauki ɗaya aka samu ta rage kai ƙararsa wajen iyaye, koda yake yanzu fa itada Mommy babu wani mutunci, dan kuwa ranar daya kaisu gidan su duka domin gaishesu Anaam tasha kallo, Mommy ta dinga yamutse-yamutse, abibda ya bata dariya Fadwa zata fara iyayi ita masu Mommy, mommy ta gwaleta. Aiko ta fita baki gumtse tana danne dariya. Tuni ta gudu gidansu wajen Mamie, inda ta ruƙunƙumesu harda kukanta wai tayi missing nasu. Suma sunyi missing nata matuƙa, amma sai suka dinga lallashinta. lokacin da Fadwa da Shareff suka shigo gaida su Abie ɗin kowa yayi mamaki Fadwa, dan yau babu rashin kunya ta gaishesu da girmamawa saboda tsoron butsutsun Shareff, dan kafin su taho ya buga mata warning bana wasa ba akan su Abie ɗin. Sai kuma abinda Mommy tai mata a gaban Anaam ya sake dagula mata lissafi.
Zuwansu gidan da kwana biyu maganar auren Bibah da Shareff ta fito, dan kuwa a kwanakin nan dama sunata bugawa ne tsakaninsa da su Mommy, ta kuma tabbatar masa idan yana fa son zama da matansa sai ya auri Bibah, a gefe kuwa burinta ita da Gwaggo ya auri Bibahn su fidda Fadwa da Anaam kuma a gidan dan sun ɗau alwashin bazasu barshi zama da su ba.
Wannan maganar aure itace ta tada gagarumar ƙurar data tada hankalin kowa a family guda biyu, dan kuwa sarƙa-sarƙar tayi yawa ai. Saboda Shareff na ɗan gatan duniya sai a dinga haɗa masa ƴaƴan dangi yana aure dai. Mamie da Abie dai basu ce komai ba, sun kuma yima Anaam nasiha akan koda a fuska karta nunama Shareff komai. Taji ciwo a ranta, sannan taci kuka amma sai tabi maganar iyayenta.
A ɓangaren Gwaggo Halima kuwa sabon yaƙi ne ya tashi tsakaninta da su Mommy, nanfa aka shiga ƴar tone tonen asiri ta yanda har akaima Shareff asirin daya nisantashi da su Abie. Abubuwa dai babu daɗi, dan tsabar takaicinsu Daddy har sai da yaji ƙwalla sun cika masa ido. Gwaggo Halima tace sai Fadwa ta koma gida babanta yace ƙarya haramun, idan Fadwa ta rrabuda Shareff ta nema wani uban bashi ba. To itama dai tana son mijinta, duk da kuwa maganar zai ƙara aure yake, kuma da kawarta data san sirrikanta.
Ruguntsumin masifa akeci na haƙiƙa a wannan gaɓa tsakanin Fadwa da Bibah, Gwaggo Halima da su Mommy da maman bibah. A gefe kuma ga shirye-shiryen bikin Aysha, sai kuma Khaleel da tasa budurwar shima. Sosai hankalin Shareff ya kasu. Ga company, ga rikicin Mommy da Gwaggo data noƙe tabar Mommy na raba hali. Ga rikicin Fadwa, Dan ita Anaam da sauƙi. Bata fasa komai da take masa ba amma yabar ganin murmushinta gaba ɗaya itama. Dama zuwa yanzu da motarta take fita wajen aiki kasancewar ta ƙware, dan bai kulla sati biyu yana koya mataba da yake ta saka kanta sai gashi ta iya, idan zasu fita yana gaba tana biye da shi, komuma tana gaban yana biye da ita duk dai dan ta ƙara sanin hanya.
An shiga shagalin bikin Aysha ne cikin ruguntsumin maganar Bibah, amma hakan bai hana Shareff sharɗantama matan nasa zuwa taron bikin ba. To Anaam ma basai an sharɗanta mata ba. Bikin Aminiya ya wuce tace bata zuwa, hakama Yaya Khaleel. Dan haka tun ranar kamu tace masa zata koma can gidan gaba ɗaya har sai biki ya tashi. Da farko yace bai amince ba, tako saka masa kuka. Da farko shareta yayi, sai dai ganin kukan nata bana kare bane yace taje cikin fushi. Sai kuma jikinta yay sanyi.
Yayi zaton zai taso aiki ya tarar ta wuce, sai ya samu tana gida babu ma niyyar tafiyar tare da ita. Ganin kallon da yake binta da shi ya sata tunzura baki gaba ta ɗauke kanta gefe.
Baki ya ɗan taɓe, “Motar ce babu mai komi?”.
“Ni na fasa”.
Ta faɗa idonta na cikowa da ƙwalla.
“Dalili?”.
Kuka ta fashe masa dashi. “Toni ya kake so nayine dan ALLAH Yaya. Taya zanje wani waje kana jin haushina. Salon kawai kasa ALLAH ya sakani a wuta”.
Ɗan murmushi yayi da girgiza kansa yana furzar da huci. “Ni bance ina fushi dake ba kar kimun sharri, kune dai kuke fushi dani akan abinda na tabbatar muku nima bana ra’ayinsa. Mi zanyi da wata Bibah can da har zamu zauna kuna dagula min lissafi. Kun haɗe kai ku a dole bakwa son kishiya. Kun san tun yaushe ake maganar nan ina ta yaƙin ganin bata fitaba? amma kuke ɗaukar laifi kuna ɗauramin. Koda yake ke nagama kamar baki damu da zuwan amaryar tawa ba, dan kwanakin nan wata ƙiba kikeyi da haske ƙyawu na musamman na fita a fuskarki, kamar wata black American”.
Throw pillows ta ɗauka ta fara jefa masa. Ya shiga karewa yana dariya. Ganin haka ya sata mikewa ta haye kansa tana cigaba da kai masa kananun duka da pillow. Dariya yake mata da son kwace filon yana karewa, har dai ALLAH ya bashi sa’a ya damƙe hanun ya mirgina ta koma ƙasa yana a sama. Turesa ta farayi shi kuma yana kai mata kisses a wuyanta zuwa ƙirji. Kukan shagwaɓa ta fara masa ya koma mata cakulkule dole ta fara ƙyarƙyala dariya. Daga haka labarin ya canja aka koma neman lada. Dama a kame yake kwanakin nan ko nauyi bai iya saukewa saboda zafin da kansa ya ɗauka matuƙa…………✍
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻
[27/11, 10:55 pm] Iyatawa Rafel: Typing📲
*_❤🔥BABU SO....!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
BABU SO👉🏻AREWABOOKS
75
……..Rungume yake da ita yana sanya mata albarka bayan samun nutsuwarsu. “Noorie na wai miye sirrinne?. Kwana biyun nan fa kin ƙara zama mai tsadar tsada ta gasken gaske. ALLAH gigitani kike na manta da kaina gaba ɗaya. Ni’imomi sun ƙara cika garden ɗina”.
Kunya ta sakata tura kanta a ƙirjinsa tana murmushi. “Kai Yaya ko kunya bakaji?”.
“Kunyar mi zanji ina a gaban autar mata. Idan ban faɗa miki abinda ke raina game da ƙyautarki da ALLAH ya bani ba mi zanyi tauraruwa a cikin taurari?”. Ya ƙare maganar da manna mata kiss a gefen kunne. Tsam ta ƙara matsesa a cikin jikinta. Ƙaunarsa ta musamman na sake ratsa zuciya da ɓargonta. A duk sanda take tare da shi mantawa take da kowa da komai, bata tuna bayan ita akwai watanta. Farin ciki take bashi fiye da hasashen zuciya. Kamar yanda shima yake riritata tamkar ƙwai a cokali. Ya gama ɗorata da koya mata salo-salo na rayuwa dakan ƙara raunana rauninta taji koda agaban wanene batajin shakkar nunasa matsayin Jan-gwarzonta….
Sumbatar goshinta yay cikin katse mata tunani, ya ɗagota suna mai kallon juna a tsakiyar ido. “Anya bani da ajiyar baby a wajen nan Noorie?”.
Idanu ta waro sosai a kansa. Ya dage mata gira daya da ƙyafta idanun yana murmushi. “Am serious kin canja Juwairiyya. Jiba nan ya ƙara girma. Baƙya raki kamar da, saima so cikin zalama. Garden ya ƙara zama zakwai-zaƙwai”.
Doke masa hannu tai da ƙoƙarin juya baya ya riƙota. “Shike nan, shike nan na daina magana. Yanzu dai na haƙura Ki shirya kije kawai, bazan hanaki zuwa bikin ƙawarki ba”.
“Woow dan ALLAH da gaske My hero?”.
“Yes my Heartbeat”.
Wani irin ɗan ihun farin ciki tayi, tare manne lips ɗinsu waje guda. Cikin ƙanƙanin lokaci ta susuta masa lisaafi…..
(🚶🏻🤕jaraba).
★Shi da kansa ya kaita, bayan yayima Fadwa magana ta shirya itama taje ɗin har sai biki ya tashi tace a'a. Bai matsanta mataba ya ƙyaleta, dan shima dai yana buƙatar ɗaya ta zauna tare da shi kar a maidashi gwauro.
Sosai Anaam ta tsinta kanta cikin farin cikin ganinta tare dasu Abie ɗinta. Nan fa sabuwar shagwaɓa ta tashi. Suko suna biye mata dan farin cikine baibaye da zukatansu. A ranar akai ƙunshi, sai dai tana nane da su Mamie bata shiga cikin gida ba. Washe gari kamu ta tashi duk batajin daɗin jikinta tun safe. Amma sai ta danganta hakan da kewar Shareff dake damunta. Tun wajen sha biyu ta shige cikin gida, kasancewar sashen Mom dana Mommy duk cike yake da baƙi saita nufi sashen aunty Amarya dan su Aysha nacan da gayyar ƙawayenta. Tuni ta shige cikinsu anata shan shafta har akai mata ƙunshi da Aysha ta matsa. Tun ana lallin take complain ayi maza a gama kanta ciwo yake, Aysha na hararar ta wai ƙunshinne bataso, in ma an gama anjima kaɗan tare zasuje Saloon ko taƙi ko taso.
Kamar wasa tace musu jiri takeji, kuma tana ganin hayaniyar gidance, Aysha dai taita lallaɓata ta shige bedroom ɗin aunty Amarya ta kwanta. Sai da ƙawayen amarya suka gama shiri suka fita tsakar gida Aunty Rahma ta shigo ta gata ita da Aunty Bintu. Sune suka sakata tashi dole tai wanka. Amrah ta kawo mata kayanta ta shirya anan. Jin yanzu babu jirin saita fito tsakar gida inda kamu ke gudana. Dan ƙarfin hali harda shiga fili taima amarya liki. Masu kiɗan kwarya suka shiga koɗata da kirarin Amaryar babban yaya Shareff. Ana haka Khaleel ya shigo shi da Shareff da Maheer. Anaam ta nufesu tana murmushi ta farama Khaleel ɗin liƙi. Hakan yasa aka dawo aka baibayesu masu kiɗan ƙwarya na cigaba da kwarzantata. Shareff dake kallonta yana murmushi baima san ya zaro nasa ƴan kudaɗen ba ya fara liƙeta, hakan yasa shima Maheer zarowa yana musu liƙin su duka uku. Aifa sai waje ya ɗauka ihu, dangi aka zagayesu su duka huɗun ana musu liƙi. Tun Anaam najin hayaniyar sama-sama harta fara jinta nesa-nesa. Idanunta suka fara limshewa tai baya zata sulale Shareff daya farga yay saurin tarota jikinsa. A take waje ya ɗau shiru. Da sauri Aunty Bintu ta kawo ruwa aka shafama Anaam ɗin saita kawo nannauyan numfashi. Kanta ta riƙe hawaye na ziraro mata. “Yaya kaina, kaina zai fashe Yaya”.
Hankali tashe ya sungumeta akai sashen aunty Amarya da ita, dan nan ɗinne kawai keda karacin mutane, dama ƙawayen amaryane sai danginta tsiraru kasancewar ba ƴar kano bace, kuma duk sun fito. Maheer ne yay kiran Dr Jamal. Cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi ya iso, har yanzu Anaam na'a jikin Shareff tana masa kukan kanta. Yana riƙe da kan yana mata addu'a, su aunty Amarya zagaye da su. Dan hatta Mom da Aunty Mimi duk suna a wajen. Tuni kuma an kaima Mommy da Gwaggo rahoto sai dai basu fitoba. Mamie ma nacan cikin damuwa a tsakar gida amma dattakonta ya hanata shigowa taga halin da Anaam ɗin ke'a ciki. Su Daddy dai suna can gidan su Anaam din tare da Abie dan can ɗin babu mutane sosai duk anyo nan cikin gida.
A kallo ɗaya Dr Jamal ya fahimci matsalar Anaam ɗin, dan haka ya kalli Shareff cikin ido. Hararsa yayi yana motsa laɓɓansa ahankali alamar magana yayi sai dai bata fitoba kasancewar falon cike yake da su Mom. Jininta ya ɗiba ya kuma bata maganin ciwon kan kawai. “Inaga zanje ai text first, amma dai tasha maganin sai taje inda babu wannan hayaniyar ta kwanta ta huta. Inba hakaba ciwon kan zai cigaba da damunta. Zuwa da safe insha ALLAHU zan kawo sakamakon ”.
“Kana nufin wannan maganin kawai zaka bata ka barmin mata cikin ciwo kenan?”.
Shareff ya faɗa cikin suɓutar baki dan ya ma manta da su aunty Mimi dake wajen. Babu wanda baiyi murmushi ba, ƙanensa na gulmarsa a zuciya ina miskilancin nasa yaje. Sai dai babu mai damar cewa komai. Maheer kam jikinsa ne yay sanyi, ya dubi matarsa da sam tama ƙi sakewa a gidan saboda a wajensa ma bata samu farin ciki ba. Auren watanni huɗu ya kasa sakin ransa ko kusantarta yaƙi yi, ita kuma ta tura masa aniyarsa duk abinda ya dace mace ta gari taiwa miji bata gazaba tana masa gwargwadon iyawarta.
Yanzun ma ko kunya babu shine ya kaita can gidansu dan acanne kawai akeda ƙarancin hayaniya. Kai tsaye sama ya kaita ɗakin Mamie ya kwantar a kan gado, yana daga zaune kanta bisa cinyarsa yana tofa mata addu’a a kanta aunty Mimi ta shigo ɗauke da ƙaramar roba da towel ƙarami a ciki. Shine ya amsa, tai murmushi a ranta tana faɗin, (Ƴan banzan yara dakun cigaba da pretending da rabo ya kashe har mu bama ku kaɗai ba. Dan wannan daga gani ciki ne). A zahiri kam juyawa tai tayi ficewrta ta bar musu ɗakin. Towel ɗin ya dinga matsewa a cikin ruwan yana goga mata a goshi zuwa fuska har wuyanta da hannayenta. Sai da kanta dake zafi ɗau ya huce sosai sannan ya koma kafafunta. cikin ƙanƙanin lokaci sai ga barci ya ɗauketa. Ya sauke ajiyar zuciya da komawa gefen gadon ya tsugunna saitin fuskarta. Kallonta yake da murmushi, ƙaunarta na ƙara ratsashi. Ya kai lips ɗinsa kan nata ya sumbata, hakama idanunta dake lumshe. Har cikin ransa yana fatan hasashensa ya zama gaskiya. Addu’a daya jima yanayi ta samun rabo daga kowaccensu ta tabbata a wannan karon. Dan ko kwana biyu ba’ai ba da gama yima Fadwa ƙorafi akan hakan.
Shigowar Mamie data kasa haƙuri ce ta sashi mikewa yana shafar ƙeya. Haka kawai yanzu yake jin tsananin kunyarsu ita da Abie babu gaira babu sabar. Cikin sanɗa da dabara ya zare jikinsa ya gudu a ɗakin…..
Su Daddy ma sun shigo dubata bayan sallar isha'i, har sannan kuma bata tashi ba tanata barci. Sun mata addu'ar samun lafiya suka fice. Sai da Abie ya rakatane ya dawo domin sake duba tilon ƴar tasa. Yana a ɗakin Shareff ya dawo, ji yay duk ya daburce, dan haka yaki sakewa ya gudu, duk da Abie nace masa ya dawo shi fitama zaiyi amma yaƙi tsayawa wai dama yazo ya sake dubatane zai wuce gida goma tayi.....
WASHE GARI al’ummar wannan family suka tashi da farin cikin bayyanar cikin Anaam ɗan watanni biyu da wasu kwanaki da adadinsu baida yawa na cika watanni uku. Zokaga murna wajen su Mamie da su Daddy. ALLAH mai alheri, su sunsha kuka da damuwar rashin samun haihuwa da wuri ga Anaam da bata rufa watanni huɗu ciff ba da ciki. Wannan rahama ce ta UBANGIJI mai yin yanda yaso a lokacin da yaso. Isar wannan al’amari kunen Gwaggo da Mommy tamkar saukar aradune a tsakiyar dare mai duhuwa. Dama dama ma Mommy bataji zuciyarta ta zafafa ba a wannan karon har hakan ya bata mamaki. Amma Gwaggo gaba ɗaya birkicewa tayi har bakinta ya dinga subucewa wajen sakin wasu maganganu. Koda ta kira Mommy gefe kan hakan sai Mommyn ta nuna mata ita duk da bata son Anaam da su Abie taji son cikin dan koba komai gudan jinin Shareff ne ai. Wannan furuci ya matuƙar ƙona zuciyar Gwaggo. Dan haka ta ɗau alwashin sai ta ɓata taron bikin nan. Cikin halin ko’in kula Mommy tai komawarta cikin danginta ta cigaba da hidimarta. Gwaggo ta bita da kallo zuciyarta na suya matuƙa, ita Nafisa zataima wannan ɗibar albarkar, to ai idan tasan wata bata san wataba wlhy. Barin wajen tai fuuu kamar zataci tun tuɓe zuwa sashenta tana ƙulla wutar da zata kunno a gobe idan ALLAH ya kaimu.
Bayyanar cikin Anaam ta matuƙar tada hankalin Fadwa, musamman dataga kamar dai nata Shareff bai wani zumuɗi ba ko rawan kai a zahiri. Amma kuma yanayinsa na son nuna kulawa ga Anaam ya tabbatar mata nunawarsa a fili bashi ke nufin baya son haihuwaba. Kawai dai hakan naturally ɗin halayyarsace ɓoye sirrin zuciya. Ba ita kaɗaiba hatta Gwaggo Halima maganar cikin nan ya tada mata hankali. A karon farko sai gata gidan Shareff ɗin dan bata taɓa zuwa ba. Cikin shirin tafiya gidan biki take, dan acewarta zataje bikin Khaleel ne bana Aysha ba, dan ita da Mommy a yanzu babu shiri kwata-kwata, saima yaƙar juna da akeyi.
Kuka sosai Fadwa ta dinga yimata akan ta shiga uku itakam, ga Anaam tazo a bayanta ta samu ciki amma ita tun miscarriage data samu babu wani bayani (Karfa ku manta ko Gwaggo Halima bata san Fadwa zubda ciki taiba. Ƙawayenta ne da Gwaggo kawai suka san wannan sirrin, sai ko Anaam. Gwaggo ma ita da Bibah da hajiya Luba maman Bibah kawai suka sani).
“Kinga kwantar da hankalinki a gama hayaniyar bikin nan sai mu tafi Germany kiga likita, karma ki bari wani abu ya tada miki hankali kinji shalele”.
Lallashin Mamanta ya saka mata samun ƴar nutsuwa harta shirya ta bita sukaje gidan bikin, inda da ace sun san mi Gwaggo ke ƙullawa da basuje ba, sai dai bawa bai isa sanin gaibuba daga kadarar abinda zai faru a minti guda na gaibunsa sam………✍
Humm, yau fa akeyinta🚶🏻🤕🚴🏼😝.
ZAFAFA BIYAR
INAYAH
MamuhGee
GURBIN IDO
Safiya Huguma
SANADIN LABARINA
Hafsat Rano
FARHATAL QALB
(Miss Xoxo)
BABU SO
Billyn Abdul
Littafi daya 300
Littafi biyu 400
Littafi uku 500
Littafi hudu 700
Littafi biyar 1k
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻