Hausa Novels

BABU SO Chapter: 66

jimawa, Anaam dafe da kanta dake mata ciwo saboda kukan da tasha ɗazun, ga jikinta har yanzu sam baya mata daɗi irin na shiga sabuwar rayuwar da ba’a saba ba. Aysha ce ta amsa masa sallamarsa, ya ƙaraso ciki idonsa akan Anaam. Ya miƙama Aysha dake masa
sannu ledar hanunsa.
“Ita wannan lafiya kuwa?”.
“Kanta ne ke mata ciwo, nayi-nayi tasha
magani kuma taƙi”. Zaune yakai kusa da ita,
ya janye hanunta dake dafe da kanta. Kasa
kallonsa tai, dan haka kawai take jin wani irin
matsanancin kunyarsa. Shiko ya matuƙar
shagala ne a kallon kwalliyar dake zane akan
fuskarta, a kasalance yakai hannunsa kan
haɓarta ya ɗago fuskar da ƙyau, hakan sai ya
tilasta mata ɗago nata idanun dake cike da
ƙwalla ta kallesa. Ba ƙaramin jarumta yay
wajen jawo numfashinsa dake neman
kufcema ƙirjinsa ba, ya matsota jikinsa tare
da ɗaura hanunsa saman goshin nata. “Wannan idon naki kinyi kuka da shi, ko
muje asibiti ne?”.
Ya faɗa a hankali cikin kunenta. Kanta ta
girgiza masa da ƙara lafewa a jikin nasa har hakan ya so bashi mamaki. Dan yasan dai koshi ya ringumeta turesa take kota janye jikinta, amma yanzu ga saɓanin hakan yana

Related Articles

gani, koda yake tunda abin nan ya faru ya fahimci ta zama wata shiru-shiru, tsiwar taɗan ragu kaɗan ko likimo ne, mata sunji maza
kenan. Fitowar Aysha ta sakata janye jikinta, shima sai ya miƙe yana faɗin, “Bara na watsa
ruwa sai a samo miki magani”.
Baki ta ɗan tura masa da kaiwa kwance. “Ni
basai nasha magani ba fa”.
Juyowa yay daga niyyar barin falon da yayi,
“Oh tunda hakane tashi na fasa barinki anan ɗin”.
Dole badan taso ba ta miƙe, dan ya tsuke fuska babu alamar wasa, duk da dama dai tunda ya shigo babu fara’ar tattare da shi. Aysha da tuni ta koma kitchen yay kira. Fitowa
tai da sauri tana amsawa. “Gyaramin fruits ɗin nan”.
“To Yaya. Ko’a haɗa salad?”.
“Duk yanda kikai is ok”.
Kanta ta gyaɗa masa, shi kuma ya kama
hanun Anaam suka fice. Ta bisu da kallo murmushi bayyane akan fuskarta. Tana fatan ALLAH ya hana su Mommy raba wannan auren har abada. Dan sun kasance abin birgewa best couple ever matuƙa”.
Koda suka iso sashen nasa a falon ya zauna, ya riƙota saman cinyarsa ya zaunar. Yanzun ma cikin mamaki yaga ta lafe a jikinsa. Ya ɗan murmusa da shafar fuskarta idonunsa na bin

fuskarta dake ƙwaɓe alamar rashin jin daɗi da kallo.
“Kodai har yanzu garden ɗin na zafinne? Noorie!?”.
Kanta ta sinne a ƙirjinsa da riƙo hanunsa dake kaiwa jikinta, dan zuwa yanzu ta fahimci mi yake kira garden ɗin. “Yaya Please ka
daina”.
“No Aunty babu wannan zancen”.
Ya faɗa cikin kwaikwayon muryarta. Murmushi ya kufce mata tare da ƙara cusa kan nata cikin jikinsa. Dan yanda yay maganar ya matuƙar bata dariya. Shima murmushi yay da kaima wuyanta kisses. Tsoro ne ya kamata, tai ƙoƙarin jan jikinta baya amma ya hana
hakan.
“Wayyo kaina zai fashe Yaya”.
Dakatawa yay daga ƙoƙarin cusa hanunsa cikin rigarta. Ya riƙo kannata. “Ayya. Sorry, sorry”. Sake langaɓewa tai kamar gaske. A ƙasan ranta kuwa dariyace ke taso mata tana dannewa. Da gaske kan nata na ciwo, amma yanda takeyi ɗin yanzu harda pretending. Yin hakan kuma shine mafita a gareta saboda ganin yana neman sakin layi, itako a yanzu in ba giyar wake tasha ba mizai kaita sallama masa ya kasheta. Ai anyi kenan babu ƙari tunda abun azaba kawai akesha a ciki. Ita jiya tunaninta gaba ɗaya akan tayaya wasu matan

ke iskanci a cikin wannan wahalar? Ko kuwa
su basajin abinda taji da bazata taɓa
mantawaba har duniya ta tashi.
Zaunar da ita yay a kujerar ya shiga bedroom
ɗinsa. Dai-dai nan Fadwa tai sallama. Anaam tai kamar bazata amsa ba sai kuma ta amsa ciki-ciki. Sam Fadwa bataji an amsa ba, sai dai sanin halin mai sashen da kuma halin da suke ciki na fushi da juna ya sata shigowa a ganinta kobai amsa ɗin ba zata shigo. Turuss ta ɗanyi na ganin Anaam, sukaima juna kallon cikin ido kowacce ta janye da takaicin ƴar uwarta da tsagwaron kishi.. Basuyima juna magana ba, Fadwa ta nema waje ta zauna.
Fitowarsa ta saka Fadwa ɗaga kai tana kallonsa, shima ita ɗin yake kallo da mamaki a ƙasan zuciya, sai dai a fuska babu ko ɗigon hakan sai ma janyewa da yay cikin halin ko’in kula ya nufi Anaam dake kallonsu ta ƙasan ido. Ita dai bata san sunada wata matsala ba a gidan. Dan haka bata kawo komai a ranta ba game da ɗaure-ɗauren fuskar tasu. A hanun
kujerar da take kwance ya zauna, “Tashi kisha. Kimmaci abinci kuwa?”.
Sai da ta ɗan saci kallon gefen Fadwa sannan
ta ɗan tura baki da narke fuska. “Ni banajin
ci”.
“Uhhm baƙya son ci, yarinyar nan ki rage

taɓaran nan naki, yanzu abincin ma sai kin
nuna masa hali? Yanzu dai kinga ba’a shan
magani sai da abinci, faɗamin mi zaki ci?”. Kallonsa ta ɗanyi da juya ƙwayoyin
idanunta, sai kuma ta narke fuska da girgiza
kai. “Da gaske bana son ci, barci nakeji kawai”. “Uhm-uhm fa, bana son zama da yunwa
sam! Ki dai sha ko fruits ɗin can ne idan Aysha ta kawo. Zakisha ko?”. Ya ƙare maganar da ranƙwafowa kanta yana sinsinar wuyanta. Ta gefen ido ta saci kallon Fadwa, sai taga su take kallo fuskarta ciɗin-ciɗin kamar zata fashe har wani jajaja takeyi na alamar ɓacin rai abunka da fari. Murmushi tai mai sanyi dakai hannu ta shafi fuskar tasa a ranta tana faɗin (Ashe kin san akwai ciwo ni kike yi masa kiss a gabana, zan koya miki iya zaman duniya). Hanunta da take neman janyewa ya cafke da sauri yana maidashi akan tattausan
gashin kumatun nasa. “Kin yarda zaki sha?”. “Ni dai ɗan kaɗan”.
Ta faɗa a shagwaɓe.
Da ƙyar ya iya jan numfashi, dan shagwaɓar
tata ba ƙaramin susutashi take ba. “Good girl”.
Murmushi tayi da janye hanun. Riƙeta yay, ta
marairaice masa. “Nifa fitsari zanyi”. “Okayy to ana buƙatar abokin rakkiya?”.
“Naƙi wayon”.

Ta faɗa da zille masa tana ƴar dariya. Bedroom ɗinsa ta nufa batare da ko sashen Fadwa ta kallaba. Tana shiga ta zube a gadonsa dan babu wani fitsari dama. Kawai dai taba Fadwa space ne. Domin rama abinda tai mata bashike nufin bazata mata adalci ba. Kuma koba komai yanzu kawai ta nuna mata cewar alwashinta tabbatacce ne akan mantar da Yaya MM ita in har tana a tare da shi.
Shiko daga can da kallo ya bita har saida ta shige, a hankali ya haɗiye murmushi kan fuskarsa. Miƙewa yay kamar zai bar falon. Tasan idan tai wasa da wannan damar zatafi haka shan wahala. Kamar yanda Mama (Gwaggo halima) ta faɗa mata ba haka ake buƙata ba, taje ta shirya dashi kodan kasancewar gobe ne zata amshi girki, suna buƙatar tai aiki da wasu fitinannun maganin mata da aka kawo dominta tun daga ƙasar sudan.
“Dan ALLAH kayi haƙuri” ta faɗa da sauri tana ƙoƙarin haɗiye hawayen da tun ɗazun take son su zubo ko zata samu sassauci. Ratseta yay zai wuce tai azamar riƙosa. Bai juyoba amma ya dakata. Ta share hawayenta hanunta riƙe da nasa. “Dan ALLAH kayi haƙuri, nasan nayi kuskure. Amma wlhy

sharrin shaiɗanne”.
Ransa a ɓace ya dubeta da wani mugun kallo
daya matuƙar neman gigitata. Saurin sakinsa tai da girgiza masa kai. “Nasan nayi kuskure amma dan ALLAH kayi haƙuri haka bazata
sake faruwa ba”.
“Tashi kibar min falo”.
“Please Soulmate dan ALLAH”.
Sallamar Aysha ce ta sakashi haɗiye maganar
bakinsa, ya koma ya zauna da amsa mata. Itama hawayenta ta shiga sharewa idonta na satar kallon ƙofar bedroom ɗinsa, dan zuciyarta raya mata take Anaam na wajen laɓe tana saurarensu. Sosai takejin raɗaɗi da ɗacin hakan, amma taci alwashi komi zai faru a yanzu ɗin bashi ne Anaam ɗin zataci itama zata rama.
Aysha ta dire tray ɗin hanunta a gabansa, fuskarta da murmushi ta gaida Fadwa da taƙi kallonta saboda kar Aysha ta fahimci tayi kuka. Kanta kawai ta jinjina mata. Ayshan bata damu ba, dan tasan halin Fadwa wani lokacin itama akwai yarfi. Hankalinta ta maida akan Share!, “Yaya a zuba?”. Kai ya girgiza mata alamar a’a, sai kawai tai musu sallama ta fice a ranta tana ayyana akwai matsala gaskiya, sai dai rashin ganin Anaam
yasa taji wani iri.
Kusa da shi ta taso ta dawo, “Soulmate……”

Hannu ya ɗaga mata a fusace. “Fadwa! leave me alone. Tashi ki fita”.
Idanu ta tsura masa zuciyarta na mata
raɗaɗi, tasan a cikin fushi yake, kuma shi baya
son yanke ma mutum hukunci cikin fushi. Jiki
a saɓule ta tashi ta fice wasu hawaye masu
zafi da jin matuƙar tsanar Anaam na ƙaruwa a
ranta. Dan a ganin duk an mata hakane
saboda Anaam, ta kuma tabbatar ba haka
iyayen Anaam suka bar Share! ɗin ba kamar
yanda Mama ta sanar mata yanzun.
Ya jima zaune a wajen zuciyarsa na masa
raɗaɗi da ƙuna, baya son ɓacin rai da damuwa, yama rasa ina zai kama da halin matan nasa. Ya samu ita Anaam ɗin ta sakko ya fara samun kwanciyar hankali ita kuma Fadwar na neman rikita masa lissafi. dole ne ya musu sabon shiri na zama da kowacce da halinta. Yasan duk abinda Anaam zatai tana yinsane a karan kanta sannan bata da ɓoye- ɓoye. Fadwa kam ya fahimci akwai zugar mutane baibaye da ita, dan tun zuwan Anaam gidan ya fahimci ta ajiye wasu halayenta na zahiri ta aro waɗansu daban, idan bai tashi tsaye a kanta ba zasu iya laɓewa a bayanta su tarwatsa masa farin cikin gidansa, shi kuma harga ALLAH yana sonta itama. Ya furzar da numfashi mai ɗaci, tunawa da Anaam dake

cikin bedroom ya sashi miƙewa ya nufi bedroom ɗin. Da mamaki yake kallonta kwance a gado har tayi barci, ya tsugunna saitin fuskarta yana sakin murmushi da kai hannu ya shafa kanta. “Dama fitsarin ƙarya ne kenan?”.

Idanu ta buɗe a hankali dan dama barcin baiyi nisa ba, sai kuma ta maida zata lumshe da ture masa hannu. Hannun nata ya riƙo cikin nashi, fuskarsa gab da tata, “Tunda kin
tashi muje kisha fruit ɗin”.
“Ni na ƙoshi barci nakeji Yaya”.
“Ni kuma ban yarda ba idan kika sha sai kiyi barcin”.
“Uhhum-uhhum”. Ta faɗa tana noƙe
kafaɗarta. Miƙewa yay yana murmushi, ya
ɗagata gaba ɗayanta. Watsal-watsal ta farayi
da ƙafafunta. “Wayyo Yaya! Wayyo Yaya ni ka
saukeni na ƙoshi”.
“Wayyo Aunty! Wayyo aunty ni bazan
saukeki ba sai kinsha”. Ya faɗa dai-dai suna kaiwa falon………
End of book

 Leave a comment

Post
omments
114367267047203523862
Jazakillahu biljannah.Dama ance mahakurci mawadaci,Allah karabamu da zugar mutane akan rayuwar auranmu
2 hours ago
C

Contact Us
Arewa Books Publishers WhatsApp: 09031774742
Email: [email protected]
Navigation
Home About FAQ’s
Social
Facebook Instagram
Legal
Privacy Policy Terms of Service

Copyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button