BABU SO Chapter: 63/64

Menu
Dashboard
My Library
Create Story
Home
About us
FAQ’s
Privacy Policy
Terms of service
Logout
BABU SO
Chapter: 63
Share:
Report
BABU SO
View: 432
Words: 2.3K
Chapter 63
63
………Tsaf ya shanye jambakin, zaune takai tana sauke numfashi, shima barin wajen yay da ɗan hanzari, tanaji ya buɗe toilet amma bata iya ta ɗago ba. Babu jimawa ya fito da alama wata sabuwar alwalar ya sakeyi. Ƙofa ya nufa batare daya yarda ya sake kallonta ba yana faɗin, “Ki tashi kiyi salla”.
Iska ta furzar mai ƙarfi da dagowa tana kallon kanta ta cikin mirror, sai kawai ta samu kanta da kai hannu ta shafi lips ɗin nata da sakin murmushi. “Fitinanne”. Ta faɗa a hankali tana mikewa. Itama alwalar ta ɗauro, bayan ta gabatar da salla samun kanta tai da komawa gaban mirror ta sake gyara fuskarta da ƙyau cikin simple kwalliya. Kwalli, lipstick ɗin daya saka mata ta ɗan gyara girarta siririya da ƙara powder. Ita a karan kanta sai da ta tsaya kallon kan nata dan wani ƙyau taga ta kara, tai guntun murmushi da ɗaukar turare ta ƙarama jikinta..
Ana idar da salla ya dawo gidan, saboda makara salla daya nema yi bai shiga sashen Fadwa ba ya wuce, yanzu kam daya dawo sai ya fara nufar can, wannan ƙa’idarsace, akowace salla in har yana gida sai ya tabbatar da mace tayi hankalinsa ke kwanciya, ko yana office yakan ƙokarta ya kira domin tambayar kinyi salla, hakan ya ƙara ƙarfafa Fadwa domin waya takan ɗauki hankalinta ta kasa tashi yin salla akan lokaci kafin zuwanta gidansa matsayin mata. A bedroom ya sameta ta idar da salla fuskarta duk babu walwala. Ya ɗan tsura mata ido na wasu sakanni kafin ya ƙaraso ciki sosai. Sau ɗaya ta kallesa ta janye idonsa da masa sannu ciki-ciki.
“Wani abu ya faru ne?”.
Ya tambaya a maimakon amsa mata sannun da tai masa. Batai magana ba, sai dai ta sake ɗan tsuke fuska.
“Nasan kin jini fa”.
Kamar bazatai magana ba sai kuma ta ɗago idanunta dake tara ƙwalla tana kallonsa, “Soulmate karka juyamin baya dan kayi aure, maƙiya zasu iya yimin dariya”.
Mamaki shinfiɗe akan fuskarsa yake kallonta. “Juya baya kamar ya? Anyi wani abu ne?”.
“In ma ba’aiba ga hanyar yi nan an ɗakko ai. Tunfa da matarka ta dawo gidan nan yau baka sake leƙoni ba, kana ganin hakan adalci ne? Yaufa ko zuwa kacemin na tashi nai salla bakayi ba, kuma tun ɗazun kana’a sashenta ita dan daga can ka wuce massallaci, gaka nan harda canja kaya alamar yin wanka”.
“Dama kin saka a ringa miki gadina ne? Ko kuma shiga sashen nata ma akwai wata ƙa’ida ta mintunan da zanyi na fito? Ni da matata kuma kina tuhumata dayin wanka kamar wanda ya ajiye wata karuwa”.
“Niba haka nake nufi ba, amma dai koyaya ai sai kana adalci. Jiya yini guda kuna tare a asibiti, hakama yau tun fitar safe da kai kuka dawo tare kana a sashenta”.
Sosai ɓacin rai ya bayyana akan fuskarsa, idanunsa daya tsareta da su har suna canja launi. “Okay ke da sokike na watsar da ita kenan a asibitin nazo na tare a wajenki bayan nine sanadin zuwanta can. Ko kuma dan kar ranki ya ɓaci bazanyi wanka a sashenta ba?. Look Fadwa idan kikace zaki ɗaukemu zuwa wannan layin bazaki taɓa shan lalai a wajena ba. Idan kin manta bara na tuna miki, Juwairiyya matata ce, idan yanzu na shiga inda take ta rayamin kasancewa da ita zan samar da wannan farin cikin nai wanka na fito koda anjima hakan zai ƙara bijiromin idan ma wannan kikema zagaye-zagaye zargin nayi. K da ita duk abu ɗaya kuke a wajena, ina fatan kuma tsaida adalci akan kowaccenku. Duk wacce take da wani tuggu nason rinjayata gareta ita kaɗai na cutar da ƴar uwarta ALLAH ya hanata wannan damar ko wacece a cikinku. Abu na ƙarshe dazan gaya miki shine daga yau ki sani Ina son Juwairiyya! bawai cushenta akai minba kamar yanda na fahimci ke tunaninki ke kaiki. Yanda na aureki domin so bisa jagorancin iyaye haka itama na aureta, kuma koda ace iyayenmu basu ɗaura mana aure ba ni da kaina Zan nema aurenta, dan hakan burina ne, hatta wannan gidan da sunanta aka ginashi itama, kema shaidace tunda sashe biyu kika tarar. Kinga sai ki sakama zuciyarki salama, ki nisanta kanki da zama mai fuska biyu a gareni, dan bazan daina kasancewa da ita ba domin farin cikin. Sannan ita bata taɓa nuna damuwa da kasancewata a wajenki ba abinda ke gabanta takeyi, mtsoww stupid har kina faɗamin wai na dinga adalci”. Ya juya ya fice a fusace.
Da gaske Fadwa tayi mutuwar zaune tun fara maida mata raddi da yayi, ga wata irin zufa dake jiƙa duk sassan jikinta sharkaf. Buga ƙofar da yay da ƙarfi ya sata zabura ta dawo hayyacinta, rawa lips ɗinta suka fara alamar magana take sonyi amma taƙi fita, sai kuma ta mike zumbur tana rarumar wayarta ta kunna fitila duk da kuwa ɗakin akwai hasken wutar nefa. Tabbas maganin data zuba ɗin gashi nan, sannan ya taka kuma ai kamar yanda Aunty Safarah da Mama suka tabbatar mata idan ya taka babu wani magana da zatai ya musa mata. Hakama zoben da suka bata na mallaka har biyu gashi a hanunta, sun kuma tabbatar mata mata da yawa suna rububin saya kuma yana aiki akan mazajensu. Mi (hakan ke nufi?) ta tambayi zuciyarta ƙirjinta na bugawa da sauri-sauri idonta ƙyam akan zoben mallakar dake a yatsanta tana murzashi da tunanin ko batayi dai-dai bane ɗazun daya sshigo.
*_(Mata ku daina ruɗar da kanku da wannan zoben da kuke saya, wai miyasa munada ilimi amma basirarmu ke toshewa akan kayan matane?. Kwanaki nai wata baƙuwa, kamar wasa muna hira sai aka kai har kan illar shaye-shayen maganin mata da wasu mata suka maida tamkar ibada a rayuwarsu har ana ribatarsu da su ana basu kayan tsubbu a zuwan maganin mata kamar dai fadwa. Sai kawai take bani labarin ai wani zobe ma ya shigo wai na mallaka. Ana saidawa dubu uku har sama da haka. Ban ɗauka abin serious ba sai a wajen wani taron suna. Hhh abin dariya, mu anan yankin ma tsabar dukan hancin da akema mata zoben ana saida musu ne a 5k 6k 7k har 10k idan aka tabbatar ke hamshaƙiya ce, kunsan kuma su wannan manyan matan sunfi son ace abu nada kuɗi mai yawa sunfi bashi daraja. Humm abin mamaki wai sai ga mata na mugun rububin zobe kamar ƙiftawar ido ya ƙare, har wasu na shiga damuwa basu samu ba. 🤦🏻haba mata mi muke son mu zama ne wai dan ALLAH? Shin wai mallakar nan mizata amfana miki? Nasan kowace mace tana so mijinta ya sota ya kuma ƙaunaceta, amma sai nakega akwai hanyoyi masu ƙyau da zakibi shi namiji ya soki domin ALLAH. Sannan ku fahimta da ƙyau wlhy namijin bahaushe komin son da yake miki da wahala ya lalace a jikinki koda yaushe kamar wasu a cikin ƙabilun nan. Ɗabi’ar da suke nuna mana kuma ba itace rashin so ba, dan kinga mace na nanaye a media da miji bashike nufin ita ƴar gata bace, dan kinji mijin novel ya lalace jikin mace karki ɗauka dole naki mijin sai ya kasance a haka ki yarda yana sonki. Wani abun ana sakashine kawai dan nishaɗi. Mu kiyayi zantuka ko labarai ga ƙawayenmu su gidajensu kaza kaza ta yanda hankalinki zai tashi kiga gazawar mijinki, wlhy koyaya mijinki yake sunansa jan gwarzo, idan kika nutsu yanada tasa baiwa da kalar soyayya da farin cikin da yake baki kema ba sai lallai irin wancan da kike hange ba. Idan kina cikin wani ƙunci a gidan aurenki ki ɗauka harabawace ke kuma bautar ALLAH kikeyi sakamakonki nagaresa, idan kikai haƙuri sai ya sakaki a aljanna. Amma mu kiyayi zurmawa akan shaye-shayen magungunan matan nan da bamusan kansu ba suzo suna mana illa a banza a wofi, su kansu wasu a cikin masu saidawar basu da ilimi a kansu bamu kawai sukeyi. Ki samu mai inganci wanda kika yarda da hadinsa da mai saidashi ki saya kisha gwargwado bata yanda zaki saka kanki a dana saniba kizo kina jama kanki illa da kwasar imfection a banza a wofi. Kuyi hakuri masu magani nasan akwai nagari acikinku dan kowane sana’a akwai na kwarai akwai na banza. Masu na banzar suke bata na kwarai da disashesu akasa ganinsu a idanun al’umma. amma dan ALLAH mata a kiyaye, zoben nan da sayensa gara ki samu kazarki kici tai miki amfani babu abinda ke tattare da son zuciya dake zama ɗorarre).
Sashensa ya nufa rai ɓace, ya zube a falo yana cigaba da jan tsaki, shi ya rasa mike damun waɗannan yaran, musamman ma Fadwa, dan Anaam ita kai tsaye take abunta bata iya ɓoye-ɓoye ba. Kuma tunda ya santa haka take, tunda ko’a shigowarta gidan nan ya hukuntata sau da yawa akan yima Fadwa abu amma hakan bai hana ta ƙara gobe a zahiri babu wani ƙumshe-ƙumshe. Itako Fadwa yau ta nuna ita mai kirki ce, musamman idan da Anaam a waje, anjima ya sameta tana baƙin rai da ƙananun magana akan Anaam kaza-kaza. Ya rasa mike damun tunaninta, shi kuma ya tsani wannan banzan halin dan yana kamanceceniya dana munafukai. Ƙwafa yay mai ƙarfi, a ransa yana ayyana zaima tufƙar hanci….
★★★
“Blood zan baki wata shawar dan ALLAH ki fahimceni”. Aysha ta faɗa tana direma Anaam plate na abinci data dafa musu a gabanta.
Wayar da take latsawa ta ajiye, da maida hankali ga Ayshan. “Tofa shawarar mi kuma blood?”.
“Ta zamanki a wannan gidan. Na fahimci gaba ɗaya a haguggunce kike, sai dai na miki uziri domin rayuwace da baki saba da ita ba kuma baki santa ba. Kin tashi a rayuwar da kowa yana komai akaran kansa kuma kai tsaye batare da wani munafunci ba ko boye-boye, dolene a wannan gaɓar kisha wahala sai dai nai alƙawarin bazan bari hakan ta faru ba. Blood daga yanzu dan ALLAH komi Fadwa zatai miki ki daina nuna ƙinsa a gaban Yaya koda ace bai miki ɗin ba, domin na fahimci da wannan makamin take amfani wajen kai miki duka a tsakaninki da Yaya. Ki duba ranar yanda ya nuna jin haushinsa akan abinda kikayi, wlhy ina ganinta sanda take murmushi, hakama yau da muka dawo, dan munafunci hardafa rakomu nan”
Murmushi tayi da ɗaukar spoon ta fara cin abincinta dan tafi son cinta da zafi. “Amma blood ban katseki ba, miye amfanin kwaikwayon halin wani bayan hanyace mara ƙyau, ɓoye ƙinta kamar yanda take ƙina bashine zaisa na birgeta ba ko shi na birgesa. Tsakanina da ALLAH idan nace zan zauna shanye haukar wannan matar zan kamu da ciwon hawan jini, nafi yarda da kamun na maka a wuce wajen dan nasan itama munafunci kesata yimin wani abun”.
Sallamarsa ta tilasta Aysha haɗiye abinda tai yunƙurin faɗa, dole ta juya tana amsa masa. Anaam kam kallo ɗaya tai masa ta ɗauke. Shiko kasa ɗauke nasa idon yay a kanta, ko sannun da Aysha tai masa hannu kawai ya iya ɗaga mata. Kujerar dake facing Anaam ya zauna. Hakan yasa Aysha miƙewa a ɗan ɗarare tace, “Yaya a kawo maka abincin?”.
Abincin ya kalla na wasu sakanni, sai kuma ya miƙe daga inda yake ya koma kujerar da Anaam ke zaune kasancewar 2sitter ce. “Bara naci kaɗan anan kawai”.
Cikin jin daɗi Aysha tai murmushi, Anaam kuwa ɗagowa tai idanu a ware tana kallonsa, ya ɗaga mata gira da kashe mata ido ɗaya yanda Aysha bazata lura ba, da sauri ta kalli sashen da Ayshar take, sai dai ita hankalinta ma ba kansu yake ba.
Spoon ɗin hanunta ya zare da sakin guntun murmushi, yana motsa lips ɗinsa a hankali alamar akwai abinda ya faɗa. Batai tunanin da gaske yake ba, sai ganin ya ɗiba yakai bakinsa tayi.
“Wai da gaske kakeyi?”.
Ta faɗa cikin magana ƙasa-ƙasa dan kar Aysha taji tana waro masa idanu da ƙyau.
Shima ƙasa yay da muryar tasa cikin kwaikwayonta da kashe mata ido yace, “Bayan wannan zahirin kina buƙatar ganin wani ne?”.
Idanun ta ƙara warowa sosai “Are you ok?”.
“I’m not…”.
Ya bata amsa a taƙaice yana danne dariyarsa dan da gaske tayi bala’in diriricewa. Tsabar son ƙureta abincin ya ɗibo yakai bakinta. Da sauri takai hannu zata kare. “Idan kikaƙi amsa ALLAH cak zan maidoki jikina sannan na baki wanda na tauna a bakina kuma a gabanta harda tsotse lipstick ɗina”.
Yanda ta saki baki da hanci tana kallonsa ya sashi dungure mata kai yana murmushi, tana buɗe baki da nufin yin magana ya juye mata shi. Dole tai saurin rufe lips ɗinta dakai hannu ta kare bakinta. Dai-dai nan Aysha da ta wuce kitchen batare da sun sani ba ta dire babban tray data shirya abinci kamar yanda akema kowanne magidanci a saman centre table ɗin gabansu. Lokaci guda suka sauke ajiyar zuciya, Anaam ta kalleta shiko ya fiske fuskarsa na komawa normal kamar ba shine ke murmushin ba.
Aysha na ƙoƙarin barin falon Anaam tai saurin faɗin, “Blood ina kuma zaki? Kizo muci abincin mu”. Da sauri Aysha ta shige bedroom ɗin baƙi kamar ma bata jita ba.
“Yaya ka gani fa ka koreta?”.
“So take ki samu ladan da mata ke samu kema, tunda garden ɗina kin haɗa baki da doctor ɗin can kar naje barruwa.”
Maganarsa ta farko kawai ta fahimta. Dan haka cike da basarwa ta bashi amsa. “Matarka ai tana dafa maka ta samu ladan, kaga ya wadatar da kai ai”.
Shima fahimtar hakan ya sashi juya harshe zuwa yaren Maley.
“Ke minene naki sunan?”.
“Kanwarka kaima da kowa an sani”.
“Really?”.
“Yap!”.
“Idan suka ganki da tsarabar furen garden sai su cireni a jerin Yayun naki ai ok”.
“Kai ka san wani garden Yaya”.
“Kema kin sanshi sai dai ƙari. Ni fa janbakin nan ya tsolemun ido a bani na shanye kayana k……”
Abincin data ɗebo ta juye masa a baki kamar yanda yay mata shima ɗazun, dole ya haɗiye sauran maganar itako ta shiga ƙyalƙyala dariya dan lauma babba ne……..✍
Next Chapter
Leave a comment
Post
Comments
No Comments posted yet
Contact Us
Arewa Books Publishers
WhatsApp: 09031774742
Email: [email protected]
Navigation
Home
About
FAQ’s
Legal
Privacy Policy
Terms of Service
Social
Facebook
Instagram
Copyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io
63
64
BABU SO
Chapter: 64 Share:
Report
BABU SO View: 167 Words: 2K
Chapter 64 64
……..Dariya take tana masa gwallo. Fuska ya
ɓata, da harɗe hannayensa a ƙirji irin yayi
fushin nan. Yanda yay ɗin sai ya saka Anaam
shiga ƙyalƙyala dariya da faɗin.
“Kai Yaya shagwaɓa kuma?! ALLAH kamafi
ƙyau a haka fuskanka so cute”. Ta ƙare
maganar da kashe masa ido dariyarta mai
ƙaramin sauti na bayyana fararen haƙoranta.
Ta nuna lips ɗinta da kaɗa masa idanunta
dake cikin gilashi.
“Indai lipstick ɗin nan ne Yaya ba shansa
zakai ba garama ka haƙura”.
“Oh oh haba princess kiji tausayina mana”.
Yaya maganar da matsar da fuskarsa gab da
tata.
Baya taja dasa hanunta ta kare bakinta,
“Babu wani princess na daɗin baki fa Yaya,
barima kaga na shanye abuna, idan baka
ganiba ai dole ka haƙura”.
Yana ƙoƙarin riƙota ta tura lips ɗinta cikin
baki da sauri.. Idanunsa ya waro sosai yana
kallonta cikin langaɓe wuya. Ta fito da lips ɗin
tana dariya da masa gwalo. “Sai kaci abinci yanzu babu”.
“Ni ko? Yarinya zan rama ne”.
Dariyarta ta cigaba dayi ƙasa-ƙasa, shiko ya
ɗauka spoon ɗin ya cigaba da cin aincinsa
fuskarsa da ɗan murmushi.
“Nifa yaya karka cinye min abinci na”.
Idanunsa ya ɗago yana kallonta, sai kuma ya
ɗibo abinci ya nufi bakinta, “Ba marowaci bane irinki ai hahh”.
Bakin ta buɗe ba musu ya zuba mata, a
hankali ta shiga taunawa da faɗin, “Nima ai
bana rowa”.
“Kika min yanzun?”.
“Baga abincina kana ci ba”.
Murmushi kawai yayi batare da yace komai
ba. Itama bata sake magana ba, ya cigaba da bata abincin shima yana ci. Suna gab da kammalawa wayarsa tai ring, ɗauka yay ya duba, ganin Khaleel sai kawai ya ɗaga. Bata san mi’akace masa a wayarba, sai gani tai ya miƙe da kama hanunta….
Da mamaki take kallonsa zatai magana ya girgiza mata kansa. Baki ta ɗan tura dan ita dai bata ƙoshi da abincin ba, sai dai babu yanda zatai dole ta bisa. Hango Khaleel jikin wata mota mai ƙyau fara tas jingine ya sata zare hanunta cikin nasa, bai ce komai ba har suka ƙaraso. Ita ta fara gaida Khaleel ɗin, ya amsa mata fuska da murmushi sannan ya maida hankalinsa ga Yayansa. Gaisheshi yay
da girmamawa. Ya amsa masa da kulawa. “Daga ina haka mazan fama?”.
Murmushin Khaleel ya faɗaɗa dan yana son Yayan nasa ya kirasa da sunan nan. Wani ɗan ƙaramin gi! ya ɗakko a gaban motar, ya dubi Anaam dake kallon motar da ita kanta an
naɗeta da zaren gi!. Sai kuma ya sake maida kallonsa ga Share” ɗin da shima dai motar yake kallo. “Saƙone daga Abie. Abawa Granny”.
Idanu ta waro matuƙa da kai hannunta duk biyu saman bakinta, sai kuma ta dubi Share” da shima murmushi ke shimfiɗe akan fuskarsa. Shine ya amsa ya buɗe key na mota ya bayyana. Ai batama san sanda ta rungume Share” da faɗin, “Wayyo Yaya daɗi zai kasheni”.
Rungumeta yay shina da sakin dariya kamar yanda Khaleel shina ke dariyar. Ɗagowa tai ta amsa key ɗin tana kallo, sai kuma ta ɗagasa a saitin fuskar Share” tana kaɗa masa. Murmushi ya sake saki mai faɗi da faɗin, “ALLAH ya sakama Abie da alkairi Congratulations dear”.
Da amin ta amsa, Khaleel ma ya amsa da
kallonta. “Congratulations Granny. Saura
kuma tukuyci na, k ko Yaya wazai bani?”. “Karka damu Yaya Khaleel, saika zaɓa”. Ta
bashi amsa da shigewa motar da Share” ya buɗe mata, daidai nan Fadwa ta fito hakama Aysha. A tare suka ƙaraso wajen, Fadwa da gaba ɗaya ranta ke’a jagule tun maganganun da Share” ya yaɓa mata ta dubi Khaleel fuska a tsuke. Kafinma tai magana ya nuna musu
motar ita da Aysha yana murmushi. “Ƙyautace daga Abie aka kawoma Anaam”.
“Woow!!” Aysha ta faɗa cikin zaro ido da
shafa motar tana kallo, Fadwa kam mutuwar
tsaye tai. Dai-dai nan Share” da Anaam dake
cikin motar suka fito kowanne fuskarsa har
yanzu da murmushi. Khaleel ya miƙa mata
hannu, “Nifa a tafamin tukuycina”. Kafin tace komai Share” dake danna
wayarsa ya miƙa masa, saka details ɗinka”. “Woow da kyau babban yaya da gudu kuwa”. Yanda Yay ɗin ya saka Anaam da Aysha
kwashewa da dariya. Shigar saƙo a wayarsa yasa bai tankasu ba, ya buɗe da sauri, “What!”. Ya faɗa yana ɗago kai da sauri ya kalli Share”. “Yaya duk tukuyci?”.
Murmushi Share” yay da kallon Anaam,
“Idan tace a ƙara maka ma sai a ƙara maka
ai”. A salon da yay maganar da ɗage mata gira
ya sakata rufe fuskarta da dukkan tafin
hanunta dan taji kunya. Matsota yay tare da
ranƙwafawa saitin kunenta. “Nima ina jiran
nawa tukuycin yanzun nan, inba hakaba a
gaban Khaleel zanyi…..”
Da sauri ta buɗe idanunta… “Kayi mi?”.
Maimakon amsa sai ya nuna mata lips ɗinsa cikin kashe ido. Sarai tasan zaiyi ɗin, amma sai ta kauda ido da nufin cewa a’a. Akan Fadwa da sam bata san da wanzuwarta a
wajen ba ta saukesu. Sukaima juna kallon ido cikin ido, ita ta fara kauda idonta da sakin wani tattausan murmushi mai ma’anoni da yawa ta maido dubanta ga Share”. Murmushi ta sakar masa shima ta ɗan saci kallon Aysha dake a mota hankalinta baya kansu, ta maida ga Khaleel, ganin shi ɗin dai zaiga komai sai ta ɗanyi jimm na tunani. “Yaya Khaleel kalla can”. Ta faɗa da sauri tana mai ɗane Share” a bazata ta manne tausasan lips ɗinta kan nasa lips ɗin.
Numfashinsa neman shiɗewa yay saboda
rashin zaton hakan daga gareta. Baya ta nema
janyewa ya ƙara cafkesu da saka hannu biyu
saman ƙugunta ta zuba masa mintsini a gefen
ciki da janye jikinta kunya kamar ta nutse.. Khaleel daya waiga baiga komai ba ya juyo
da nufin hararar Anaam, ai babu shiri ya sake
maida kansa gefe da sauri yana dafe bakinsa
da sakin siririyar dariya. Aysha da bata san
mike faruwa ba ta fito a motar tana rungume
Anaam da faɗin, “Wayyo blood motar nan ta
haɗu wlhy ALLAH yasa a kashe da kai”. Wani
bahagon tari ya sarƙe Fadwa, cikin sassarfa
kamar zata kife ƙasa dan sauri tabar wajen
hawaye masu azabar zafi na kufce mata. Gaba ɗayansu kallonsu suka maida gareta,
dan sai yanzu ma shi Share” yasan Fadwar
na’a wajen. Cike da son basarwa itakam Anaam ta rungume Ayshar. “Thanks you blood, thanks you”. Shima dai gogan ya basar a binsa kamar komai bai faru ba, ya nunama Khaleel hanya alamar su shiga ciki idonsa akan Anaam. Anyi sa’a itama ta ɗago suka haɗa ido. Baki ta ɗan murguɗa masa. Ya taune lips dinsa da sakin murmushi alamar azakizo hannu. Kafaɗa ta ɗage masa da labe baki irin na i don’t care taja hanun Aysha suka koma motar…
Da ƙyar Fadwa ta iya kai kanta sashenta
saboda jiri dake ɗibarta da lulluɓe ganinta
gaba ɗaya. “Subahanalillhi. Hajiya lafiya?”. Mmn Abu ta faɗa da nufo Fadwa da sauri
dake neman zubewa ta tareta. Kuka ta sakar mata kamar wata karamar yarinya, maman Abu duk sai ta rikice. Kamata tai har bedroom. Tana son tambayarta mike faruwa tana jin tsoro, dole ta fito ta barta cikin damuwa. Tadai san labarin kitse baya wuce ƙoƙi dan ta jima da fahimtar Fadwa na cikin jerin mata masu tsananin kishi. Gata da hali irin na ɓoye abu a rai da idan bakai dogon nazari akanta ba saika ɗauka kishiya cutarta take musamman irin Anaam da bata iya ɓoye abinda ke ranta. “ALLAH ya ƙyauta”. Ta faɗa
da komawa kitchen ta cigaba da aikinta…..
Anaam kam da tuni sun koma ciki tana can cikin farin ciki tana waya da Mamie da Abie ta video call. Addu’a take zubama iyayen nata harda hawaye, yayinda suma suke kallonta murmushi shimfiɗe a fuskokinsu da tsananin ƙaunarta da tausayinta harma da alfahari da ita na kai mutuncinta gidan aurenta. Dan aunty mimi ta sanarma Mamie komai, hakama Mamie ta sanarma Abie, shiyyasa ya danƙara mata mota najin alfahari da ita akan riƙe tarbiyyar da sukai mata. Sai dai su kansu sun san sun kaita wani filin gwagwarmayar rayuwane na yankin kaddararta, amma sukanji sassauci da tunawa zumincin ALLAH suke son karfafawa insha ALLAHU sadaukarwarsu bazata taɓa zama a banza da wofi ba..
Tafiyar dai Aysha bata yuwu a yau ba, dan tuni Share” ya fice gidan tare da Khaleel yin godiya ga Abie, Anaam kuma sai ta ƙara samun sauƙin jikinta insha ALLAH zai kaita. Sai da suka fara biyawa ta o”ice yin wasu muhimman baƙi, ba wani dogon zama sukai ba sai zuwa monday idan ya dawo aiki.
Takardar da zai basu suje su duba kafin zaman ya nema ya rasa, cikin ɗan dafe kai ya dubu Khaleel da Fharhan. “Inaga fa nama bar file ɗin nan a gida wlhy, Khaleel saika koma
kenan dan dole ne mu basu suje su duba.” “Okay bara naje ai bawani nisa bane”.
“Okay ba damuwa, kafin ka isa zan kira su
ɗakko maka kawai”.
Kansa ya jinjina masa ya fice. Shi kuma ya
shiga ƙoƙarin kiran layin Fadwa. Harta tsinke ba’a ɗagaba, yay mata uzirin ko bata kusa ya sake kira, amma nan ma dai hakan, ya ƙara kira har sau uku sai aka koma danna masa number busy. Ransa ya sosu matuƙa, dan ya gane tana kan sani. Amma sai ya shanye kodan baƙin dake tare da shi ya maida akalar kiran ga Anaam. Gama wayarta da su Abie kenan kiran nashi ya shigo, bugu biyu ta ɗauka har yanzu muryarta cike da farin ciki tai masa sallama. A hankali ya sauke ajiyar
zuciya, ya amsa mata.
“Har yanzu murnar motar ce?”.
“Humm Yaya bazaka ganeba”.
Murmushi yayi, “Okay idan na dawo ai sai ki
ganar dani, yanzu nidai nutsu na saki aiki”. “Okay” ta faɗa kanta tsaye.
“Ki duba a study table ɗina, akwai wani file green a wajen ki ɗaukama Khaleel zai zo ya amsa yanzun”.
“Tom”.
Ta duba a kurkusa inda yace amma bataga
file ɗin ba, sai dai kuma hankalinta ne kawai
bai kaiba saboda ya dannesa da wani book.
Ta shiga bin komai daki-daki da kallo tana
ɗan ɗagawa harda buɗe drawers ɗin wajen.
Saukar idonta akan wani ɗan akwati ya sata
nutsuwa tana kallonsa, harta maida drawer
ɗin ta rufe sai kuma ta sake buɗewa ta ciro
akwatin. “Uhhm su Alhaji Yaya mm mi kuma
ake ɓoyewa anan? Koma dai miye zuciyata na
son gani”.
Tana ƙoƙarin buɗewa kira ya shigo wayarta,
shine dan haka ta ɗaga. Kafinma yay magana
tace “Yaya ban ganiba fa, inata nema kuma
tun ɗazun”.
“Kamarya? Bayan nasan yana nan akusa-
kusa. Ki ɗan ɗaga kayan wajen Khaleel na waje yana jiranki amfani zanyi da shi”.
“Oh sorry kamarma gashi anan ka ɗaura littafi akai”.
“Ok ki kai masa yana jiranki”.
Koda ta kaima Khaleel littafin sashen ta sake dawowa. Dan zuciyarta naga akwatin nan haka kawai batare data san dalili ba. Kiciniyar buɗewa ta shigayi, da ƙyar ta dace ya buɗu bayan ta haɗa da ƴan dabaru. Da
littafi ta fara cin karo, ta ɗan jujjuyashi tana taɓe baki ta ajiye. Sai envelope brown babba. buɗeta tai ta zaro albom na hotuna mai tudu sosai sai dai bai cika girma ba a tsaho. “Hotunan sirri ne kenan su Yaya aka ɓoy….” ta kasa ƙarasa abinda ta faro. Ko’a magagin barci aka tasheta babu gilashi a idonta aka nuna mata hoton babu gargada zata bada amsar itace. Hotone da taga irinsa yafi guda ashirin a gidansu. Hoton ne da aka ɗauketa a ranar haihuwarta tun a asibiti. Tana rungume a hanun Yaya Share” Abie da aunty Mimi sun sakashi tsakkiya suna leƙenta a hannunsa ya babbake ya hanasu gani. Da sauri ta koma na ƙasa, shi kuma a ranar sunanta ne ita da shi, na gaba itace da shi da Mamie da Abie da aunty Mimi. Ta cigaba da buɗe albom ɗin mamaki fal ranta dan ta kasa fahimtar ma’anarsa. Hotuna na gaba sun kasance a gurare daban-daban. Wani wajen ita kaɗai, wani ita da shi, wani har da su Abie. Ranar birthday ɗinta na cika shekara ɗaya. “Ya ALLAH” ta faɗa tana cigaba da kallonsu daki- daki. Jikinta ya ɗan fara rawa ganin hotunan da har tana a shekarar shiga primary, secondray, kai har jami’a ma akwai, bayan zuwa lokacin Share” baya tare da su. Duk wani hoton birthday ɗinta akwaisa, hakama
hotunan bikin salla kona wani taron makaranta kona islamiyya duk akwai. Hoton ƙarshe da yay matuƙar bata mamaki shine na ranar ɗaurin aurensa da Fadwa, itama kuma ranar nata ɗaurin auren da bata sani ba. Rubutun da yay a jikin hoton ya matuƙar firgitata……….
End of book
Leave a comment
C
Post
omments
No Comments posted yet
Contact Us
Arewa Books Publishers WhatsApp: 09031774742
Email: [email protected]
Navigation
Home About FAQ’s
Social
Facebook Instagram
Legal
Privacy Policy Terms of Service
Copyright 2021, Arewa Books | ALL RIGHTS RESERVED | Powered by thinkcrypt.io