BA JINSIN MU Bace page 1-2

🅿 1-2
Short story
“Abdallah, wllh ba jinsin mu bace, ka rabu da yarinyan nan, kaje ka kawo mana fitina a gida, kullum sai a dinga raza nani, ba zai sa’bu ba Sam. Ka maida ta inda ka d’ako ta, taimako kace zakayi, to wanda kayin nan ya isa haka, Hakka kawai ina zaman zamana, ka zo mun gida da abinda zai rin’ka bani tsoro, to nagaji haka, tunda kazo da ita gidan nan ban sake barci cikin kwanciyan hankali ba, yau kimanin kwana ashirin kenan”.
” Da daddare a dinga min wani irin eyhu a gida, don kaga uban ka bashi a raye shiyasa, amma da yana da rai ai baka Isa ba” fad’a take masa sosai kamar ba d’an ta d’aya tilo da take tsananin so ba. Kuma shine farin cikin ta tun bayan mutuwan uban sa, shekaru kusan ashirin da biyar kenan, domin ya mutu Abdallah na da shekaru kusan biyu a duniya.
Sai da yaga ta tsagai ta, sannan yace cikin sanyin murya “inna ta, mutum ce, Allah mutum ce, kawai sai dai idan baki addu’a kike kwan tawa, shiyasa kike mugun mafark……….” Zanci uban ka kakiyayeni, koda kaje islamiya ai inace kafin ka fara tafiya nina fara koya maka addu’o’e? eye? Kasani sarai kakanninka mlmai ne, ai da bana addu’a da abin yafi haka, da kaina ba wani ya gayamin ba, naga yarinyan nan ta koma wata halitta da ban, mai matu’ka ban tsoro, ba’kin’kirin fuskan ta ya koma, sannan ho’kora manya-manya, wanda tunda nake ban ta’ba ganin wannan halitan ba”.
“” Don Allah yaron kirki, yaron albarka nasan ka da biyayya ka tai maka ka bar gidan nan da fitinan nan, ko na samu nayi barci cikin walwala, hankali na ya kwanta, kaji yaron kirki?””” Magana cikin kwantar da kai tayi masa.
Bai ce da ita komai ba, ya fito d’akin.
Har ya bar parloun yaji kamar kuka ta hanyan baya, kukan bana kowa ba, illah stella.
Nufan wurin yayi jikin sa har rawa yake, domin a duniyan nan ya tsani kukan ta, bai so sam idan yaji hankali sa tashi yakeyi, neman natsuwan sa yake ya nema yarasa.
Koda yaje ta bayan, itace tsugune sai kuka take, cikin tashin hankali ya tsuguna a gaban ta tare da cewa “” menene? Me aka miki eyeh? Wani abu na damun kine?”” Duk ba ansa, sai yasa hannun sa ya d’ago da fuskan ta, tare da kallon cikin idon ta, idonun sunyi jazir saboda tsaban kukan da tasha, jikin ta har yayi zafi.
“” Baza ki gayamin damuwan ki ba ko? Kinfi son na rasa walwala ta ko? kinsani sarai ban juran ganinki cikin damuwa, ga zazza’bi har ya kamaki, baki min addalci sam, why beby?”””.
Tausayin sa mai tsananin ne ya kama ta, sai ta rungume sa, tasani ba ‘karya a cikin kalamun sa, gaskiya yake fad’i har cikin ransa.
“To amma kulawan da yake bata yayi yawa, to ko dai shima yana son tane kamar yadda take son sa?” .
“” Inah bazai yuwu ba, domin bazan iya cutar da kai ba sam, daga soyayya sai aure, to tayaya zamuyi aure, mama gaskiya ta gaya ni ba jinsin Ku bane, babu aure tsakanin mu, bazan iya cutar da kai ba Sam, domin kai ba mugu bane kai nagari ne, kai mutum ne, niko fah”” sai ta fashe da matsanancin kuka, kuma duk maganan da take, a cikin zuciyar ta take.
Idanun sa sunyi jazir, zuciyar sa sai bugawa take, cikin tashin hankali yace “yanzu baza kibar kukan nan ba ko? Kinfiso zuciya ta ta buga ko?” Da sauri ta girgiza masa kanta.
‘Dagota yayi tare da share mata hawaye yace “oyah had’iye kukan haka idan baso kike mu ‘bata ba” da sauri ta had’iye.
“” Friend me aka miki ne?”” Murmushi tayi tare da cewa “ba’a min komai ba” tace tana mai kashe masa ido d’aya.
“” Oh idan na gane jin dad’i ne yayi miki yawa ko? Ko kuma tunanin ‘yan uwan ki kike?” girgiza kai tayi idon ta a cikin nasa, tana mamakin wannan bil’adaman sam zuciyar sa mai kyau ce, yana da tsananin tausayi da imani, “me zesa ni na cuceshi, no! no!!! babu gaskiya, na ‘kosa nayi abinda ya kawoni na ‘kara gaba, ina cika ma Hanzina burin ta zan barka har abada, bazan sake dawo wa gare ka ba, kai mai hallaci ne a gareni, ba zan maka butulci ba, ina firgitar da mama da gangan ne, domin yanzu haka ya kamata na bar gidan nan. To amma bansan meyasa zuciya ta bata son barin ka ba” ..
“Tunanin me kikeyi ne wai?” .
Murmushi tare da d’age girah ta jingina kanta a kafad’an sa, tare da kallon ‘kwayan idon sa.
Jiyayi tace “kai manah, tunanin ka nake” lakace mata hanci yayi tare da cewa “banson shashanci, yau ya motso kenan? d’agani mlm, muje muyi breakfast” tare da d’aga ta.
Mai mako ta tafi sai tawani narke masa tare da kyanciya a kafad’an sa, “muje mana”.
Ta’ki d’aga sa.
“” Oh ni Abdul tawa ta sameni, yau shagwa’ba ne ya tashi ko? Pls muje ni yunwa nakeji kuma zan makara a office, pls muje ko? kinga inson nai duk abinda ya kamata don zani ‘kwauye jibi asabar insha Allahu, kar na dawo aiki yayi min yawa” .
Murgud’a baki tayi tare da kwaikwayon sa ta fece a guje.
Karkad’a kai kawai yayi tare da bin bayan ta yana murmushi, yama man ta da abinda innar sa tace Sam, domin idan yana tare da d’iyan arnan nan mantawa yake da komai.
***
Koda ya gama kintsawa kamar yadda suka saba kamar mata da miji.
Ta d’aukan masa jakar sa, domin raka sa wurin motar sa, bayan ta saka masa, shi kuma yana tsaye a jikin motan duk inda tai yana kallon ta da murmushi d’auke a kyakykyawan fuskan sa.
Itama jingina tayi kamar yadda yayi, kamar yadda idon sa ke kanta haka itama tayi, kafad’un su manne da juna.
Kamar an fizgo magana a bakin sa yace “me zai sa bazaki musulunta ba? Musulunci zaifi dace wa dake”.
Murmushi da kamar an halice ta dashi tayi masa, wanda ke ‘kara haska ka fuskan ta.
” Yes shi yafi cancan ta dake” d’age gira tayi masa alamun tambaya
Yace “sosai ma kuwa, kiga bari na wuce kullum sai kinsa na makara” zum’buro baki tayi tare da cewa “ni d’in?” Girgiza kai kawai yayi tare fad’awa mota.
Dariya tayi ta wuce ciki tare da d’aga masa hannu.
Dariya yake tayi shima a cikin mota har yaje office murmushi ne d’auke a fuskan ta, “to meyasa ga mutum kana gani wai kace ba mutum ba? Innah kenan ciwon tsufa ya tashi”.
****
4:30 ya bar office, Allah Allah yake ya koma yayi tozali da kyakykyawa fuskan ta.
Yana tafiya yaji ta cikin mota ance ” kafita harkan matana, idan ba haka ba zamu wulakan taka, daga kai har dangin Ku gaba d’aya ” waige 2 yaka yi, amma bai ga kowa ba, ya kuma rasa ta ina maganan ta fito, sai ji yayi ana dariya da wani irin murya mai ban tsoro “hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh”.
“” Innahlilahi wa’innah illahir raju’un””” ya kama addu’a ba qaqqautawa…