Hausa Novels

AUREN K’AUYE – Episode 7&8

STORY AND WRITING
Maryam Muhammad Ussaini
(Nazlarh ce)

Related Articles

MOONASH ALK’ALUMA SHIDA DAGA ELEGANT ONLINE WRITER’S ✍️✍️

BANI DA HUJJA
Maimoon

SARƘAƘIYA
Shaahd

BARRISTER SHAHEEDA
Ayush

AUREN ƘAUYE
Nazlarh

ZUMUNCIN ZAMANI
Jikar Nashe

WATA HANYA
Indo
~~

بسم الله الر حمن الر حيم


Episode 7&8

Ammie wani fira suka farayi, Majeed gaba d’aya zufa ya gama wanke mishi fuskarshi.

Shatu ce ta fito sanye da wasu kayan fulanin, ga dukiyan fulaninta ana kallo ba bra a jikinta, har shatin nipple d’inta a ana gani, hips d’inta kuwa ya nuna sosai daman shatu a kwai manyan hips, gashi kaf kayanta na fulani ne, ba wasu kayan, balle tasa.

Majeed tunda ta fito yake binta da wani irin kallo, a zuciyarshi ya ce “Wai wannan abar zan aure?”.
Shatu murgud’a mishi baki ta yi saboda kallon da taga yana mata kaman yaga kashi, ko sannu bata ce musu ba taje ta zauna kusa da Ammie.

Baffa ya ce “Ke Shatu meye haka ko sannu bakisan kice ma mutane ba, amman kinzo kin zauna a kusa da ita sai kace wata sa’arki, Shatu tura baki ta yi ta ce “Baffa wllh baka sona yan zun komai kayi tamun fad’a gwanda ma naje gidan me gari ta na fad’in haka ta tashi, zata fita a gidan.

Ammie ta ce “Zonan Shatu”.
Shatu zuwa ta yi ta ce “Maman birni yaushe zamu tafi birnin na gaji da zaman garin nan kowa baya sona harda Baffa da inno ma.

Ammie ta ce “Zauna tukunan”.
Zama Shatu ta yi, Ammie ta ce “Waya fad’a miki ba a sonki kowa yana sonki kawai dai halin kine marasa kyau ba aso”.

Shatu ta ce “To shine sai a dunga min fad’a harda duka.
Ammie ta ce “Yanzun dai jeki kiyi sallah sannan kici abincinki sannan ki had’a wasu abunda kike buk’ata banda kaya zan siya miki wasu kayan idan muje can, gobe idan Allah ya kaimu sai mutafi can birnin”.
Ai Shatu tana jin haka ta tashi da sauri ta fara rawa irin tasu ta fulani tana juya k’ungunta a hankali.

Ta shige bayan gidan na kara domin ta yi alaula.

Majeed haka kawai yaji ya tsani Shatu, saboda yafahimci bata da kunya ko kad’an shikuma baya son yarinya mara kunya, balle wai ace wacce za aura mishi tabbbb d’i jammm aikon akwai matsala dole ya yi ma Ammie magana akai.

——————
Ammie ta ce “Bukar a kiye dukanta don allah ko yi mata fad’a bashi bane mafita, nasiha ce da tausa sa kalamai masu dad’i.

Yanzun idan anyi auren nan muka tafi za tayi makaranta islamiyya da boko, kuma insha allahu zata dena duk wad’annan abubuwan, daman harda rashin mahammadiyya na damunta, a dunga barin yara suna zuwa ko makaranta allo ne don Allah”.

Baffa suka yi ma Ammie godiya sosai, ta ce ba komai ai duk jini d’aya ne.
Majeed kuwa be k’ara cewa ba, har Ammie ta ce “su tashi su tafi.

Ammie ta ce musu, “Zasu tafi kuma su shirya kayan Shatu na amfani, don ana d’aura auren zasu wuce da ita, jirgin 1 zasu hau ya kaisu garin Kaduna.

Suka ce insha Allahu zasuyi hakan, sannan Ammie ta ce “Don Allah karsu fad’a mata game da maganar auren suka ce insha Allahu baza su fad’a mata ba.

Sannan Ammie ta yi musu godiya suka fita a gidan.
———————
‘Bangaren Me gari kuwa, tuni ya sanar ma da yan’uwa da abokan arzik’i aure Shatu da majeed.

Wasu sunyi farin ciki dajin haka wasu kuwa cewa suke suna tausayin Majeed don zeyi fama da Shatu don batajin magana.
——————
Ammie da Majeed gidan me gari suka koma Majeed ya wuce masallaci cike da muwa, ita kuma ta shiga fadan me gari, tana shiga ta fad’a mishi yadda sukayi da Baffan Shatu.
Me gari ya ce “MashaAllah”, Allah ya kaimu goben, ta amsa da ameen sannan ta koma cikin gidan me garin, can ta tarar da Islam tana wasa da yara sa’aninta.

Islam tana ganin Ammie taje ta rungume ta ta ce “Grandma ina kukaje da Daddy bangan ku ba tun d’azun nake neman ku?”.

Ammie ta ce “Sorry my little baby, gashi mu dawo Daddynki yana masallaci kuma yan zun zai dawo muma muje muyi sallah ko, Islam ta d’aga kanta alaman eh ta rik’e hannunta suka tafi masaukin su.

Sallah sukeyi sannan Ammie ta d’auko mata su snacks da chocolate amsa tayi ta fara ci, Ammie kuwa nono da furan da tazo dashine ta d’auko ta fara sha.

Majeed ne ya shigo da gudu Islam ta fad’a jikinshi, tana “wlcm Dady”.
Majeed ya ce “Thank you my dolls, murmushi Islam ta yi sannan Majeed ya nema wuri ya zauna.

Nono da furan Ammie ta mik’a mishi amsa ya yi ya farasha don yana son nono da fura sosai.
A hankali ya d’ago kai ya kalli Ammie sannan ya ce “ Don Allah kibar maganar wannan auren bazan iya aure wannan yarinyar ba, ta yi yarinya sosai ko Anwar d’ina ya girmeta, kuma bata da kunya kiduba irin rashinjin maganar da take d’auko masu Baffa, kuma idan mukaje Kaduna da ita akasan itace matar da aka auramin abokanai na da yan’uwa zasuyi magana akai kuma zasuyin min dariya.

Ammie ta ce “So what?”, Majeed ya ce “Hmmm Ammie don Allah a soke wannan auren bana so”.

Ammie ta ce “Ba abunda zai hana wannan auren, ni ina so”, Majeed zeyi magana da sauri Ammie ta dakar dashi.

Majeed shiru ya yi don yasan ran Ammie ya b’aci ne, shi kuma baya son wannan shirme auren da za’ayi mishi sai kace k’aramin yaro, don a ganin shirmen aure ne wllh, kamar shi a had’a shi aure da yarinya k’arama kamar Shatu.

—————
Bayan sallar juma’ane aka shaida d’aurin auren Aisha Abubakar Usman & Majeed Muhammad Usman, Shatu & Majeed.

Alhamdulillah kowa yana cikin farin ciki amman banda Majeed wanda akasami akasin haka.

Shatu kuwa anata murna zataje birni ko Mairo bata fad’a mawa ba, kuma batasan da d’aurin aurenta ba, kuma ba aso ta sani yanzun, da anmata mata aure……

“WAYE MAJEED KUMA ME YE HALAK’AR SHI DA SHATU?”.

Mu had’u a page na gaba muji waye Majeed da Shatu, kuma yazaman su zai kasan ce.

Yawan comment d’inku yawan typing d’in da zanyi….✍️✍️✍️

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button