Hausa Novels

AUREN K’AUYE – EPISODE 5-6

STORY AND WRITING
Maryam Muhammad Ussaini
(Nazlarh ce)

Related Articles

MOONASH ALK’ALUMA SHIDA DAGA ELEGANT ONLINE WRITER’S ✍️✍️

BANI DA HUJJA
Maimoon

SARƘAƘIYA
Shaahd

BARRISTER SHAHEEDA
Ayush

AUREN ƘAUYE
Nazlarh

ZUMUNCIN ZAMANI
Jikar Nashe

WATA HANYA
Indo
~~

بسم الله الر حمن الر حيم


Episode 5&6

Banya fitan Shatu ne Ammie ta kalli me gari, sannan ta ce “Me ze hana a had’a auren Shatu da Majeed”, me gari ya ce “kamar kin shiga zuciyata Hafsatu, nima abun ya dad’e acikin rai na kenan, sai dai ina duba kaman basu dace ba, don Shatu bata da kunya ga rashinjin magana da d’ebo maganar mutanen gari ga masifa taya ze iya zama da ita?”.

Ammie ta ce “Ina ganin ranka yadad’e idan aka musu auren zamu tafi da ita can birni kaga zata waye acan kuma zata dena abunda ta keyi, me gari ya ce “Eh wannan shawar ta yi amman kinsan ta ya majeed zai amince a aura mishi wannan k’aramar yarinyar da ya aifeta kinsanfa ko anwar d’anshi ya bata shekara d’aya fa”.

Ammie ta ce “Ba matsala bane tunda a musulincin bai hana ba, kumaai Shatu yar uwarsa ce baze ki aurenta ba, indai naci gaba da biye ma Majeed to wllh bazeyi aure ba”.

Me gari ya ce “Tom Allah ya tabbatar mana da alkhairi yan zun kitashi kije gidan, saiki magana da Baffan Shatu nima zanyi magana da sauran yan‘uwa Ammie ta ce “Tom insha Allahu kuwa”.

Sannan ta tashi ta fita a fadan me garin, ko wurin Islam bata jeba don tasan tana wurin matan me gari, gidan su shatu ta nufa.
————
Shatu tana shiga gida, ta tarar da baffanta da kuma Majeed suna hira akan tabarma, dariya ta kyalkyale dashi ra k’asari sa da gudu ta zauna a gabansu tana dariya.

Majeed ya mutse fuska ya yi ya ce “Shatu me ye haka kuma?”, Shatu ta ce “Inawuni ya Majeed”, Majeed kin amsawa ya yi yaci gaba da magana da Baffa, tura baki Shatu ta yi ganin yadda ya Majeed ya share ta, tashi ta yi tana k’un k’unai wai ace ana gaida mutun ma yana banza da mutane don kawai d’an birni ne shi, mtsssww yama samu ne”.

Aikon jin saukan bulala ta yi a bayarta, da sauri ta zube a k’asa tana sosa bayanta, d’aga kai ta yi taga Baffanta da igigar d’aure shanu, ai bata gama rufe idonta ba taji saukar wata bulala tako ina a jikinta, ihu ta farayi tana birgima a k’asa, Inno kuwa fad’i take ka k’ara mata malam”, Majeed da sauri ya tashi yaje kusa da Baffa ya ce “Baffa don Allah ka kyaleta haka, Baffa tsayawa ya yi ya ce “Majeedu kenan bakasan yarinyar nan ba ne, innanta ta turata tallar nono tak’i zuwa sam, sannan taje tana d’auko min magana, d’azun babar Rahane tazo ta fad’amun wai ta zubar ma da Rahane nononta duka ta turata tallah”.

Sannan kuma anzo ankawo k’aranta ta zuba ma da Jauro karara a jikinshi, kuma ta d’ibi wakenshi, ka duba rashin kunyar da take maka, kaga jikinta a jik’e taje tana wanka a rafi salon ta jawomun wani jarabar, zula mata bulalar ya yi ya ce “Ina wanken da kuka kwasan mishi”.

Shatu kuka take tana wllh k’aryane suke min ni ban d’iba waken ba, kuma yau ko Rahane ban gani ba”.

Sosai baffa yake zula mata bular tana ihu tana rok’anshi ya kyaleta, shikuma yana tambayar ina waken?”, Majeed shima k’ok’arin kwace bulalar ya keyi amman ina dukanta kawai baffa ya keyi.

Shatu cikin azaban dukan da yake mata ta ce “Munsiyar ne nida Mairo, Ammie ce ta shigo gidan da sauri don tun a k’ofar gidan akejin ihun Shatu.

Ammie ta ce “Haba bukar me nake gani kuma haka?”, Baffa tsayawa ya yi da dukan da yake mata ya ce “Barka da zuwa Addana”, Ammie ta ce “Bazan amsa ba”, da sauri Ammie taje ta d’aga Shatu daga k’asa.

Shatu rungume Ammie ta yi jikinta na rawa tana kuka, Ammie shafa kanta takeyi sosai tana lallashinta a jikinta.

Ammie rungume da ita suka k’arisa kan tabar ma, ta zaunar da ita itama ta zauna, Shatu sosai take kuka, dakyer Ammie ta tasa ta yi shiru, d’agota ta yi daga jikinta ta ce “Shatu zaki bini birni muje tare?”, Shatu da sauri ta ce “Eh”.
Ammie ta ce “Tom shi kenan jikiyi wanka kicire wannan kayan kisa wani wanda yake rufe miki jiki sosai, kinsan kayan nan irin naku sai a hankali, Shatu tashi ta yi dakyer abunka da fulani farin fata jikinta duk yayi jawur wani wurin kuwa ya tashi.

Majeed ne ya ce “Ammie sai yan zun kikazo?”, Ammie ta ce “Ohoo kana kallon ana dukanta baka hana ba ai”, Majeed ya ce “Sorry Ammie nayi k’ok’arin yin hakan amman Baffa yak’i hak’ura ne”.

Ammie ta ce “Na dawo kan ka shine zaka dunga dukanta kamar jaka”, Baffa ya ce “Ba haka bane Adda hafsa, Shatu batajin magana ne shi ya sa”, Amie ta ce “Tom nidai kar asake don Allah ba duka bane zai gyara mutun, shi yasa ma nazo da maganar ka bani ita muje can birni da ita”.

Inno ce tazo ta ije musu nono da fura, a gabansu sannan suka gaisa da Ammie, Ammie ta amsa cike da fara’a anan ne ta ce mah, inno “ta zauna mana”, zama inno ta yi.

Sannan suka k’ara gaisawa da yi musu ta aziyyar rasuwar da akai musu, ta gaida baffa da jikin shi, anan ne Ammie take fad’a musu shawarar da suka yanke da mai gari.

Ai Majeed yana jin haka gabanshi ya fad’i rassss dammm, a zuciyar shi ya ce “Ko ya rasa matar aure meye zeyi da Shatu, batajin magana gata yarinyar cikinshi a matsayin wacce zai aura inaaaa, zeyi magana kenan Ammie ta yi saurin dakatar dashi, sannan ta ce “Kuma inason auren nan da gobe a d’aurashi tunda daman gobe jumma’a in Allah ya kaimu”.

Baffa shiru ya yi jim sannan ya kalli inno wacce ta yi wuk’i-wuk’i da ido don batasan a rabata da Shatu don ita kad’ai suka haifa.

Baffa ya ce “Amman Adda Hafsa kina ganin hakan ba wani matsala kinga ba wani wayau ne da Shatu ba kuma shi d’an nawa ba wai yana sonta bane kawai Adda hafsee a canza wani shawarar”.

Ammie ta ce “Hakan alkhairi ne ba wai matsala ba, ko kamanta Shatu yar uwarsa ce taya zai ce baya sonta koda wasa Bukar bana son k’ara jin haka”.
Baffa ya ce “Tom kiya hak’uri Adda Hafsat allah ya tabbatar mana da alkhairi”.

Ammie ta amsa da ameen sannan ta kalli Majeed taga lokaci d’aya ya fita daga cikin hayyacinshi……

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button