AUREN K’AUYE EPISODE 3-4

STORY AND WRITING
Maryam Muhammad Ussaini
(Nazlarh ce)

MOONASH ALK’ALUMA SHIDA DAGA ELEGANT ONLINE WRITER’S ✍️✍️

BANI DA HUJJA
Maimoon

SARƘAƘIYA
Shaahd

BARRISTER SHAHEEDA
Ayush

AUREN ƘAUYE
Nazlarh

ZUMUNCIN ZAMANI
Jikar Nashe

WATA HANYA
Indo
~~

بسم الله الر حمن الر حيم


Episode 3&4

Yarinyar da Shatu ta zubar ma da nono ta fashe da kuka ta ce “Wllh Shatu saikin biyani ko kuma naje gida na fad’ama Inno”.

Shatu ta kwashe da dariya cikin fulan tan ci ta ce “Je ki saikin dawo wllh Rahane ko kinje ba abunda za suyi mini, gwanda ma ki d’auki k’waryar nonon ki wuce gida, idan kuma kika je kinsan saura wllh, sai na jaki yafi ki jin dad’i”.

Rahane tasan ba k’aramin aikin Shatu bane ta yi mata mugun duka ta fashe da kuka tana “Na shiga uku ni Rahane wllh yau baba Lantiyo kashe ni za ta yi”, Murmushi Shatu ta yi ta ce “Kawai kije kice mata nine nan na zubar miki ba abuda zai faru”, murmushi da kuka Rahane ta yi ta ce “Don Allah da gaske kike Shatu?”.

Shatu taja dogon tsakin mtssswww sannan ta had’e fuska ta ce “Na tab’a miki wasa ne?”, Rahane ta ce “A’a da saurin ta kwashe k’ayan furan nata ta koma hanyar gidan su.

————
Bangaren su Majeed kuwa harsun wuce airport, daman jirgin 8:AM zasu hau.

Basu wani d’au lokaci ba girgin nasu yayashi zuwa yola.


Shatu kuwa tana karya kwanan ta had’u da Hard’o timke fuska ta yi kamar bata tab’a dariya ba, Hard’o ya ce “Haba masoyiyata me yasa kike mun haka ne wai?”, Shatu cikin masifa ta ce “Dallah malam matsamun a hanya sai tsamin hammata kakeyi kafin warin ya kashe ni”.

Hard’o ya ce “Haba masoyiyya me ya sa kike mun haka ne, don Allah?”, ki bari a d’aura mana aure aradu zan baki shanaye guda biyar”, ya fad’a yana dariya.

Tsaki taja ta sa hannu ta tureshi ya fad’i k’asa timm, ita kuwa ta yi wuce warta tana wankarta cikin fulatanci.

Gidan su k’awarta Mairo ta wuce, tana zuwa taci sa’a kuwa Baffan Mairo baya nan don ya hanata zuwa gidan, wai tana koya ma Mairo rashinjin magana.

Bukkan Mairo ta wuce dama babar Mairo bata da lfy shi ya sa bata fitowa da ga bukka.

Mairo ta samu tana shan nono da fura, ta k’wace ta hausha.

Mairo ta ce “Ke Shatu taya kika shigo kinsan Baffa ya kusan dawo wa ko”, Shatu ta ce “Ke ni ba wannan ba yau naji ance Jauro yana kwasan wanke a gonar sa”, Mairo ta ce “Eh to meya faru ne?”, murmushi ta yi ta ce “Tashi zakiyi muje mud’e bo”, Mairo ta ce “Ni dai bazani ba”, Shatu ta ce “Wllh sai kinje tashi muje ko kuma na fasa miki baki”, Mairo tana jin haka ta ce “Ya hak’uri k’awallina tashi muje Tom”, don tasan zata aika.

K’waryar nonon ta ije suka fita a bukka, suna tafiya suna tsokana mutane.

Shatu bata tsaya ba saida suka je gonar Jauro, saman bishiyar wurin ta hau a b’oye itakuma Mairo tana ta k’asa jikin bishiyar a b’oye itama.

Shatu bud’e hannunta ta yi ashe ta d’ibo karkara, ta hura mai kad’an a baya, take Jauro yahau susa bayanshi, Shatu ido ta yi ma mairo alaman ta fara d’ibar waken.

Aikon Mairo ta fara d’ibar wake ta bayanshi shikuma yana ta susa Shatu tana saman bishi tana mishi dariya, garin dariya bata ankare ba taji ta ta fad’o timm ak’asa, da sauri ta yarfe hannunta tana “Ouushhhhhhhhh da zafi Mairo zo mugudu, Mairo ta rik’e ledar wanken da k’arfi taje ta rik’o hannun Shatu wacce da k’yer ta tashi suka fara gudu don mutane harsun fara binsu, ana musu ihun b’arayi.

Shatu da Mairo gudu kawai suke yi, basu tsaya ko ina ba sai da sukaje gidan Latin mai k’osai, sunci sa’a ba wanda ya ya inda suka shiga.

Lanti da ke zaune tana wanke waken taga shigowar su, ta ce “Shatu lafiya kuwa?”, Shatu da Mairo nishi kawai suke yi, Shatu ta ce “A’a kawai muna ‘yar rige-rige ne nida ita shi ya sa”.

Lanti ta ce “Tom ya akayi ne?”, Shatu ta ce “Inno ce ta ce “Na kawo miki wake ki siyya”, lanti ta ce “Yawwa kawo mugani”, mik’a mata waken Mairo ta yi, lanti ta ce “Ai wannan ko mudu be kai ba, zan bata d’ari biyar kawai”, dad’i ne yaka shatu ta ce “Tom kawo kawai”, lanti ta mik’o musu d’ari biyar d’in, suka amsa suka fice daga gidan.

Shatu basu wuce ko ina ba sai rafin su don suyi wanka kuma su suya wara da kud’in don akwai mai wara a bakin rafin.

—————
Jirgin su k’arfe 10 ya sauka a garin yola.
Daman Majeed yana kasuwanci a yola,shi ya sa akazo d’aukan su.

Suna shiga motan Majeed ya ce “K’AUYEN LADO zaka kaimu, aikon take motansu ya bar airport d’in suka nufa k’auye.

*
11:23Am suka isa k’auyen daman kuma ansan da zuwansu.
Gidan me gari zasu sauka, Islam kuwa dad’i take ji tazo k’auye sai shirme takeyi wa su Ammie.

Gidan me gari aka kaisu tunda suka shiga k’auyen aketa binsu har gidan me garin, driver yana parking aka mamaye jikin motan, driver da sauri yazo ya bud’e musu k’ofar motan suka fito.

Majeed yasan daman idan yazo haka suke mai, kud’i ya d’auko ya bada a raba musu, su kuma suka shiga cikin gidan me garin.
Har d’akin da zasu zauna aka kaisu, me gari murna ya ishe shi don ganin jikanshi da tattab’a kunnenshi wato Islam.

A binci yasa akakawo musu harda nono da fura, sai dai islam baza ta iya cin abincin su ba, daman Majeed ya sani.
Shiyasa yasa nanny d’inta ta zubo mata su snack da yawa da su chocolate sweet biscuits da dai sauran su haka yazo mata dasu.

Majeed kuwa nonon kawai yasha Ammie ne ma tasha nonon da dambu wanda yasha gyad’a.

Bayan sun huta ne suka nufa cikin gidan, domin yimusu gaisuwa da ta’aziyya, kowa sai kallon su ya keyi islam kuwa taga farin jinin daga k’arshe ma hanata bin su Ammie suka yi.

Har fadan me gari sukaje, anan ne me gari yake fad’a musu cewa suje gidan Baffan Majeed wato kanin mahaifin shi, su gaidashi saboda bashi da lafiya, hira suka fara dagan nan kuma me gari ya yi mishi magana akan har yan zun beyi aure ba, Majeed ya ce “Zeyi idan lokaci ya yi, me gari ya ce “Insha allahu ma ya yi, zanyi magana da mamanka akan hakan, Majeed ba tare da ya gane abunda me gari yake cewa ba, ya ce “Ammie ni zan wuce, Ammie taso suje tare amman saboda me gari ya nuna yana son magana da ita yasa ta ce mishi yaje zata zo daga baya.
Majeed tashi ya yi ya fita a fadan.
————
Shatu kuwa tana wanka a rafi akazo aka kira ta, wai yan uwansu na birni sunzo, ai Shatu da sauri ta fito a rafin, gashi kayanta a jik’e yake sharkaf ta tafi da gudu jikinta sai d’igan ruwa ya keyi.

Shatu gida me gari ta nufa koda taje can akace mata suna fadan me gari, shiga fadan ta yi ta tattarar da Ammie jikinta ta fad’a tana murna ta ce “Maman birnin ashe kunzo?”, Ammie cike da mamaki take kallon Shatu yadda jikinta yake zubar ruwa gashi itama duk ta jik’ata da ruwan.

Ammie ta ce “Eh Shatu munzo amman yaushe zaki girma ne duba jikin fa yadda kike zubar da ruwa”, Shatu ta ce “Eh MAMAN birnin naje rafi wanka ne shine akacemun kunzo ban bari kayan jikina ya bushe ba”.

Me gari ya ce “Haba matan me ye haka kuma?”, Shatu ta ce “Wai kai tsohon nan mai bakin goro ina ruwanka ne bana ce kadena mun magana ba na dena sonka wllh cike da murgud’a baki, baba me gari ya ce “Nima dai bana sonki yan zun tunda inno ta ce mun kina sati bakiyi wanka ba, Shatu za ta yi magana, Ammie ta ce “Shatu jeki gida kiyi wanka kicire wannan kayan ki dawo, ya yankima yana can gidan ku”, Shatu da sauri ta tashi ta ce “Tom amman fa zan dawo”, ba tare da jira me Ammie zata ce ba ta fice a d’akin da gudu…..

More comment more typing…..✍️

Share fisabilillah🙏🙏🙏

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*