Hausa Novels

AUREN K’AUYE – EPISODE 1-2

STORY AND WRITING
Maryam Muhammad Ussaini
(Nazlarh ce)

Related Articles

MOONASH ALK’ALUMA SHIDA DAGA ELEGANT ONLINE WRITER’S ✍️✍️

BANI DA HUJJA
Maimoon

SARƘAƘIYA
Shaahd

BARRISTER SHAHEEDA
Ayush

AUREN ƘAUYE
Nazlarh

ZUMUNCIN ZAMANI
Jikar Nashe

WATA HANYA
Indo
~~

بسم الله الر حمن الر حيم


Episode 1&2

GARIN KADUNA
Zaune yake gaban mahaifiyar shi, wacce a k’alla zata kai shekara 63 a duniya, Alhaji Abdul-Majeed ya duk’ar da kai k’asa saka makon fad’an da take mai, “Haba Majeedu ace har yan zun bakasan ciwon kanka ba kana da yara har biyu, kuma duk sun girma sosai, ka duba kaga Anwar yan zun yana k’asan waje yana karatunshi acan Dubai, ga Islam yan zun tana primary 3, shekara biyar kenan tunda Asma’u wato mahaifiyar su Allah ya yi mata rasuwa kak’iyin auren me ya ke damun kane haka babana?”, ba irin maganar da banyi maka ba kasa dangin babanka nacan K’AUYE sai surutu sukemun wai na barka kak’in aure kamar wai inajin tsoranka duk sun d’aura mini laifi, fad’amini me yake damun ka ne?”.
Majeed kasa cewa komai ya yi ya d’ago da kanshi ya kalli mahaifiyar tashi, ya ce “Ammie na kiya hak’uri zanyi aure idan lokaci ya yi kuma kici gaba da tayani da addu’arki na samun mace ta gari kamar Asma’u na, hawayene ya zubo mishi masu zafi tunawa da ya yi da tsohuwar matarshi.

Ammie tausayin d’an nata ya kamata tabbas tasan Majeed yana matuk’ar k’aunar matarshi Asma’u, kuma gashi Allah ya d’auki rayuwar ta saboda breastcancer da ya kamata.

Tasan da kamar wuya majeed ya samu mata me irin hak’urinta da d’abi’unta, koze samu da wuya ya yi mata irin son da yake ma asma’u, a zuciyar ta ta ce “Allah yajik’anki da rahma Asma’u”.

Majeed yana da shekara 43 a duniya, Amman duk wanda ya ganshi baze ce yana wad’annan shekarun ba,
Kuma Majeed kyakyawa ne na bugawa a jarida majeed yana d’auke da dara-daran manyan idanuwa gashi da dogan hanci bakinshi d’auke yake da pink lips, yana da saje a fuskanshi wanda ya boye girmanshi da kuma she karunsa kwance yake luf-luf yasha gyara da mai, sai sek’i ya keyi, tamkar d’anyen saurayi, base na tsaya na baku labarin had’urwashi ba, sai dai nace Majeed had’add’e ne sosai, me girma da d’auka ka.
————-
Ammie ta ce “Ya hak’uri Majeeduna na bar kuka, kullun inamaka addu’a kuma bazan tab’a gajiyawa ba hark’arshen rayuwata, Allah ya yi maka albarka”.

Sannan ta yi mishi addu’a sosai da nasiha, anan ne take fad’a mishi zasuje K’AUYE gobe idan Allah ya kaimu saboda a dangin babanka anyi musu rasuwa, Majeed ya ce “Tom Ammie Allah ya kaimu”, ta amsa da “Amin”.

Majeed ya yi mata sallama ya tashi ya fita a d’akin, cike da ladabi.
—————

Part d’inshi ya wuce yana shiga ya tarar da islam tana bacci a kan kujera.

Islam kyakyawar yarinya ya ce sosai kamanta d’aya da mahaifinta, fad’in kyawun Islam kam baze fad’u ba.

Murmushi ya yi ya ce “Oh my ciwon kai ta yi bacci, d’aukanta ya yi cak ya haura da ita sama zuwa d’akinta.

Yana shiga d’akin ya kwantar da ita, kiss d’in goshinta ya yi sannan ya rufe ta da blanket ya ce “Love u so much my love, sannan ya fita a d’akin.

Had’add’en bedroom d’inshi ya wuce, zama ya yi a kan dank’aren kujeran dake bedroom d’in.

Dafe kanshi ya yi, gaba d’aya baya son atuna mishi da matarshi Asma’u don mutuwar ta sabo yake dawo mai cikin zuciyarshi.

Kuka ya fashe dashi ya d’auki hoton ta da kekan wani k’aramin table a gaban kujeran, Asma’u kyakyawar mace sosai, sai da ya k’are mata kallo ya ce “Me ya sa kika tafi kika barni masoyiyya ta kinsan cewa rayuwata idan babu ke baza ta yi dad’i me ya sa kikai mun haka?”, kuka ya keyi sosai yana sambatu kamar wani sabon zautacce.

Ya fi minti 30 yana kuka sannan ya ijiye hoton ya tashi ya shiga toilet.
Nanma saida ya yi kuka me ishanshi sannan ya yi wanka da ganan ya d’auro alaula don yana da kyau mutun idan zeyi bacci ya yi alaula kafin ya kwanta, be d’au lokaci ba ya fito d’aure da towel a k’ugunshi, yana goge kanshi da k’aramin towel, Majeed ya had’u sosai ko k’iran jikinshi ka kalla kasan had’add’e ne na gaske.

Gaban mirror yaje ya yi shirin bacci sannan ya hau kan bed ya rufa da blanket, da tunanin matarshi ya yi bacci.

———————
Washe gari da asuba
Yana tashi ya shiga toilet yafara yin wanka ya d’auro alaula daga nan ya fito, farar jallabiya ya saka sallah ya fara’a sannan ya shirya cikin manyan kaya ya yi kyau matuk’ar kyau, jikinshi sai wani ta shi k’amshi ya keyi.

Sannan ya fito daga d’akinshi, downstair ya sauka don yasan Ammieshi tana jiran shi, a part d’inta.

A k’asa ya sami Islam tana breakfast d’inta, Islam tashi ta yi taje da gudu ta rungumeshi, ta ce “Sweet Dad good morning, murmushi ya yiyi ya d’ago kanta daga jikinshi, ya ce “Morning love how was your night?”, Islam ta ce “I’m fine sweet Dad, how about to you sweet me?”.
Majeed ya ce “Alhamdulillah my love”, Islam ta ce “Sweet jiya ina jiranka harna yi bacci baka dawo ba”, murmushi ya yi sannan ya ce “I’m so sorry love ina wurin grandma d’inki ne, kuma da na dawo kinyi bacci”.

Islam ta ce “Alright papa”.

Majeed ya ce “Love ina Nanynki?”, Islam ta ce “Tana bedroom d’ina tunda tagama shiryani zuwa school ta ce “Naje inna Kand’e ta had’a mana breakfast shine na sakko k’asa”.

Majeed ya ce “Kije kice ta tacire miki wannan kayan tasa miki wani kayan zamuyi ta fiya ne, kuma ta shirya miki wani kayan a travel bag d’inki”, Islam dad’i taji ta rungumeshi ta ce “yessssss Daddy”.
Da gudu ta hau upstairs tana murna zasu tafiya.

Murmushi Majeed ya yi ya ce “Love kenan”, sannan ya fita a parlor ya nufa part d’in Ammie.

————————

K’AUYEN LADO

Shatu! Shatu!! Shatuuuu!!!.
Kyakyawar yarinya ce ta fito daga wani k’aramin bukka, wacce baza ta wuce 14 years ba.
Fuskanta a had’e kaman bata tab’a dariya ba, cikin shigan fulani ta yi kyau sosai, Shatu kyakyawa ce sosai, tana dogan gashi har gadon bayanta, ya kusan kai mazaunanta, ta yi k’itso irin tasu ta fulani, hud’u a gaba wato guda biyu-biyu a gefen fuskanta guda biyu a kuma bayanta.

Tana da dogan fuska sai manya idanuwa farare tas gadon hanci kamar ita ta zana kanta, Shatu tana d’auke da k’aramin bakinta wanda gaba d’ayanshi pink ne sai shek’i ya keyi kamar tasa lipstick, kuma ko kwalliya irintasu ta fulani ba ta yi.

Turo baki ta yi ta ce “Nidai fa inno nagaji da wanna tallar nono da furan nan da kike d’auramin, ace ya ya Find’o ma ya mutu ace sai nayi talla bazan huta ba, a radu yau ba inda zani”.

Inno ta saki baki tana kallo Shatu, sannan ta ce “Haba Shatuna kinsan ba wani abun sana’a daza muyi daya wuce wannan nonon da fura d’in, don haka d’auka kije kinjiya, kafin na kira miki Baffanki aradu ya zane miki jiki.
Shatu ta ce “Inno bafa inda zani na fad’a miki…”, aikon bata kai ta rufe baki ba, Baffanta ya fito da k’aton sanda na dukan shanu ya biyo Shatu dashi.

Aikon Shatu da gudu ta fita a gidan, tana gudu tak’i tsayawa duk da Baffa ma ya koma gidan abunshi, Shatu kuwa ko kallon gabanta bata yi.
Kawai ta ji takifar da abu a k’asa meza ta gani, wata yarinya ta zubar ma da nono duka……..

Share fisabilillah🙏

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button