AMINIYA TA CE

Dedicated this page to fatima zarahππ»
1β£to5β£
Da sunan Allah mai rahma mai jin qai, da ya sake bani dama na sake rubuta wani sabon littafi, Ina rokan Allah daya bani ikon kammalawa dan alfarman annabi Muhammad (s a w)
“Zeena ce zaune a class tayi uban tagumi, ta rasa maike mata dadi, mlmn maths nata musu bayani amma bata ma San yana yiba, kaman daka sama taji ana kiranta da sauri ta d’ago kai, ta saki murmushi da kara, suka rungume juna ita da Mysha, Zeena tace haba friend why are you late today,I though you are not coming today, Mysha tayi murmushi tace sorry Zeena na raka daddy airport ne daka nan driver ya Kawo ni, mlmn maths ne Ya katse su tare da fadin Zeena nd Mysha keep quick please, kasan cewan makarantan kudi ne, ba’a takura ma yaran sannan teachers din kaman tsoran student din suke, domin skul din sai dan wane da wane, kowa na tsoran ya bata ma student rai, kar allura ta janyo garma, Zeena tace sorry sir, yaji gaba da gudanar dasu, har ya fita, wani ya shigo, har aka fita break, Zeena suka je, yin break suna tafiya suna fira har suka karasa restaurant din skul din, ga snacks nan kala2 sai wanda kaga daman ci, Zeena ta dauko musu ice cream Mysha kuma ta dauko, cookies suka nufi kan wani table suka ajiye kayan sannan suka zauna, suna ci suna fira, Mysha tace Zeena kin San wani Abu kuwa? Zeena tace a’a sai kin fada, Mysha taci gaba da cewa daddy dazu muna hanya zan raka shi airport yake cewa wai ina Gama secondary skul zai min aure, Zeena ta zaro ido tace what? Sai kace a zamanin da, may be he is joking, mysha tace no Zeena he is not joking, Ya dade yana yin wannan maganan, kuma daddy inya fada Abu toh he is serious, Zeena tayi shuru tare da tausayin kawar tata, can tace toh ke Mysha bakya kula kowa, yanzu wa zaki aura, Mysha tace nima abunda nake tunani kenan, yasa koda yaushe nake jin wani iri idan na tuna bani da saurayi wanda nake so, Zeena tace toh ke yanzu mai zaki fada ma daddy dinki inya tambayeki akan wanda zaki aura, Mysha tace nima ban San amsa din ba, ke gwara ke ko yanzu akace ki fito dashi zaki Kawo shi, duk da ban taba ganinshi ba, har yanzu, Zeena tayi murmushi taji an Kawo zan cen prince dinta, Mysha tace wannan murmushin fah, a dai2 lokacin wani yaro mai suna afraz yazo kusa dasu ya kafa ma Zeena ido kaman tsohon maye yace sannunku yan mata, Mysha ce ta amsa, yace ya naji kunyi shuru, yaci gaba da fadin Zeena wai mai yasa koda yaushe indai kika ganni saiki canza fuska, ki duba duk skul din nan ko wace yarinya so take yau ace ina kulata, amma ke na rasa dalili da yasa bakya so inzo inda kike, Ya kalli Mysha yace please Mysha am I not handsome, Mysha tace you are, infact ma babu macen da zata ganka bata kuma kallonka ba, yayi murmushin jin dadi yace thank, sannan ya kalli Zeena wanda ranta ya Gama baci da Mysha yanda take wasa shi, ta mike da nufin ta wuce, ganin haka yasha gabanta, Ya tare ta, tare da fadin Zeena you better stop this nonsense, how dare you ina magana kina wani tashi zaki wuce, duk wanda suke wajan hankalinsu ya dawo garesu, ta kalleshi ido cikin ido tace you have to know 1 thing I really hate you, I hate everything about you, infact ma bana son ganinka, tsayawa yayi yana kallonta da mamaki, dama zaiga irin wannan ranan har mace ta tsaya tana gaya mishi magana duk yanda yake da kyau ga kudi ga aji, yan mata suke rubi binshi, amma yau y’a mace take wulakanta shi, a gaban mutane, ihun da akeyi a wajan yasa ya dawo daka tunanin daya fada, a dai2 lokacin Zeena ta wuce Mysha ta rufa mata baya, yayin da afraz yaji kafanshi yayi mishi nauyi wani irin kunya ya rufe shi, amma haka ya fita, kai tsaye wajan motanshi yayi yashiga ya tada ta, Ya fita daka skul din,Sheraton hotel ya nufa ya kama d’aki, Ya kwanta idonshi yayi ja babu abunda yake tunani sai abunda Zeena ta mishi, Ya kasa komai Ya tashi dakyar yaje motanshi ya dauko kwalban codein ya kwankwade, sannan ya samu bacci ya dauke shi, a lokacin da Zeena da Mysha suka nufi class, Mysha tace Zeena kin San mai kikayi kuwa? Zeena cikin tsiwa tace mai nayi, tell me, Mysha tace Kin San afraz kuwa kin San waye shi kuwa, Zeena tace ban sani ba ban kuma fatan in sani, plz indai kin San maganan shi zaki min, plz leave me alone, jin haka Mysha tayi shuru, amma a cikin xuciyanta tana tsoran abunda afraz zai mata domin hatsabibi ne, gashi ta wulakanta shi gaban mutane, skul din duk an baza labarin, a lokacin da aka tashi Mysha tabi Zeena dan ta ajiye ta a gida, yau bada matan ta tazo ba, kasancewan ta raka daddy dinta airport, dukansu babu mai magana, can Zeena tace Mysha mai yasa kikayi shuru baki cewa komai, Mysha tayi Dan murmushin yake tace mai zance Zeena wlh ina tsoran afraz, ban San mai zaiyi ba, Zeena tayi dan murmushi tace plz Mysha kinga ni harna manta shidin banza wlh bai isa yamin komai ba, nafi karfinshi, ita dai Mysha jinta kawai take, domin afraz bama a skul dinsu ba, kaf garin Abuja dakyar ne kaji wajan da ba’a sanshi ba, baya ji gashi idan yana son abu, ko miye sai yasan yanda ya mallake shi, kota halin ‘ka’ ka wannan kenan da haka har suka karasa gidansu Mysha ta ajiye ta, ta wuce gida,
Wacece Zeena?
Zeenat abubakar yan asalin garin katsina ne, su uku iyayensu suka mallaka, akwai yayanta adeel wanda yake karatu a kasar Japan sai ita dake aji hudu a famaks sai kanwarta mai suna aysha, suna kiranta da abda, sun taso cikin gata duk da irin gatan da suke ciki suna karatun islamiya kuma sun San addini dai2 gwargwado, mahaifinsu senator ne sau biyar yana ci saboda mutum ne mai rikon Amana kuma dadtijo ne, duk irin kudin da Allah ya mishi bai bar yayanshi sun lallace ba, yana tsaye akan iyalinshi, mutum ne mai son yaga yara sunyi ilimi sai yasa Zeena bata tunanin aure duk da, tana da saurayi wanda yake matukar sonta itama tana sonshi amma baya kasan nan yana China yana kula ma mahaifinshi da wasu aiyuka wajan shekara biyu, kullum suna makale a waya kaf gidansu babu wanda bai San zaheer ba, Zeena mutane da yawa suna mata kallon miskilanci don bata cika son yima mutane magana ba, in kaga ta kula ka toh babban dalili ne, sabanin kanwarta Mysha mai son magana, har wasu na mamakin kaman can nasu, sun hadu da Mysha a skul suka kulla kawance har suka hada iyayensu kawance.
Maryam obamββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
(Mrs nura kuriga)ππΉ
Dedicated this page to zee babyππ»
6β£toπ
“sai wajan shabiyu da wani abu afraz ya farka daka baccin daya dauke shi, Ya tashi tare da mika, komai daya faru duk ya manta, amma ganinshi a hotel yasa ya fara tuno abunda ya faru, lokaci daya yayi tsaki tare da fadin, Zeena you will regret it, toilet ya fada yayi wanka, Ya fito ya shirya ya nufi gida, kai tsaye dakin shi ya nufa, Ya fada kan gado yayi ruf da ciki, yana ta sake2 a ranshi, da haka bacci ya kuma dauke shi,
Zeena ce zaune akan dinning suna breakfast ita da abda, tana yi tana kallon agogo, har mahaifiyarsu wanda suke kira da ummi ta karaso, tace Zeena wannan saurin fah, tace ummi banso inyi late ne, muna da test yau ban samu nayi karatu ba jiya, so inna shiga skul da wuri zan Dan karanta wani abu, ummi tace yanzu na rasa dalilin da yasa bakya daukan karatunki da mahimmanci, kwata2 kinsa wasa inda dane aida kin San abunda kika taka, wai maike damunki ne Zeena? Tayi shuru ganin ummi din ta kafeta da ido yasa tace ummi nima kaina ban sani ba, ummi ta kuma kafeta da ido tana son ta fahimci wani abu daka yar tata, amma ganin babu abunda zata fahimta yasa ta canza maganan da fadin yau in kin dawo daka skul zaki rakani wani waje, ta amsa da toh ta Mike, abda tace ummi nima dani zaki koh? Tayi Dan murmushi tace yes my dear tasa dariya a dai2 lokacin skul boss din su abda yayi horn ta fita da sauri ta wuce.
Mysha da Zeena suna zaune a study room suna ta karatu gefe kuma wasu student ne suma suke ta faman karatun, jin kaman tsayuwan mutum a kanta yasa ta d’aga kai, hada idon da sukayi saida gabanta ya fadi, amma ga mamakinta sai taga yana mata murmushi, ta tashi zata bar wajan, yace haba Zeena mai yayi zafi haka, tace afraz please ka fita daka harka na, bana son kana shiga cikin harkoki na, Ya kafeta da ido yace Zeena dan na miki magana nayi laifi ne? Tayi banza dashi ganin haka yasa ya kwace littafin dake hannunta, ta waigo cike da masifa amma ganin ya tamke fuska gashi sun hada ido, yasa tace plz kaban book dina, Ina karatu, kaman bazai bata ba, komai Ya tuna kuma oho, Ya mika mata littafin, tana amsa tabar wajan, Mysha ta tashi itama, amma jin ya kira sunanta yasa ta tsaya, yace ina son magana dake, tace ina jinka, yace wai mai zanma Zeena ta soni, ni inma samu ta dinga kulani, Mysha tayi shuru can tace afraz mai yasa baza ka barta ba tunda bata sonka, akwai wanda take so, tana fadin haka tabar wajan, Ya bita da kallo tare da wani murmushi wanda shi kanshi yasan dalilin yinshi.
Ummi ce cikin wani tsadaddan leshi mai kalan milk colour flower din jikin leshin kuma purple, yayi mata bala’in kyau, ta nufi dakin Zeena taga itama ta shirya cikin wani material red nd golden, dinki doguwan riga, yayi mata kyau sosai, ummi tace muje Dan Allah kin cika bata lokaci, Zeena tayi murmushi tace na gama ai, ta dauko wani karamin gyale ta yafa, suka fita, cikin wata mota suka shiga mai Kiran Prado, driver yaja su, Zeena tace ummi wai ina zamu haka ne, ummi tayi murmushi tace Mrs hakeem ce ta gaiyace ni dinner gidanta, tace owk, tun daka nan ta kama bakinta tayi shiru, Mrs hakeem wata kawar ummi ce mijinta minister ne na agricultural, sun karasa gidan, sunga motoci da yawa na mutane a gidan daka gani gidan cike yake da mutane, sun shiga falon makil da jama’a Ana ta ciye2, Mrs hakeem na ganin ummi tazo da sauri ta rungumeta sannan suka zauna, Zeena ta gaida ta, ta amsa cike da fara’a, ummi tace wai miye na hada wannan taron? Mrs hakeem tayi dariya tace yau 35yrs da auranmu, ummi tace wow har kun kai haka gskiya lokaci na gudu, anci ansha kowa ya watse daka gidan.
Wayan Zeena keta faman ringing, tayi dan gajeran tsaki ta dauka, ganin sunan mai Kiran yasa tayi sauri ta dauka, tare da fadin hello, ta dayan bangaran ya amsa da gimbiya ta, Ina kika shiga inata kira? Tace sorry dear bacci nake yi, karan Wayan nema ya tashe ni, yace kina bacci kin manta dani, tayi dan murmushi tace ni na isa, yace gest watch, tayi shuru can dai tace fada min, yayi dariya yace ina naija, dazu na sauka, tace what a surprise, amma baka kyauta min ba, shine baka gaya min ba, yayi dariya yace amin afuwa, cikin shagwaba tace anyi ma, yace gobe ina nan tafe, tace sai Kazo nayi missing dinka sosai, yayi murmushin jin dadi yana mamakin jin kalaman nan daka bakin Zeena, wanda ya tabbata baza ta iya gaya mishi tayi missing dinshi a gabanshi ba.
Washe gari Zeena anata shirye2 na taran adeel, Ana ta girke2 kala2 dasu drinks kala daban2, duk wanda yaganta yasan tana cikin farin ciki, bayan ta kammala komai taje tayi wanka ta shirya cikin wani leshi mai ruwan Zuma, da zanan baki a kai, yayi mata kyau sosai, tayi kwalliya na kece raini, duk wanda ya ganta saiya yaba da irin suranta da kyau da Allah yayi mata, ta zauna tana jiran zuwan gwarzon nata don tun dazu ya mata waya yace yana hanya, komai an jera a falon saukan baki, sai kamshin turaran wuta yake.
Wayanta ne yayi kara ta dauka, da sauri ji tayi yace gani a gidansu, tace gani nan, da sauri ta fita, ta iskeshi a mota, yana jiran zuwanta, ta karasa gareshi, Ya kafeta da idon nan nashi, wanda yake rud’a ta, itama kallon nashi ta tsaya yi, Ya kara kyau da wani haske, yace wow my princess kin kara kyau da girma 2yr rabon mu da ganin juna, tayi Dan murmushi tare dajin kunya, tace mai fito mu shiga ciki babu musu yabi bayanta, har falon baki, Ya zauna cikin daya daka kujerun falon, Ya kafe ta da ido, yana mamakin irin girman data kara, da kyau, wani irin sonta yaji yana kara shiganshi, tare da burin yaga ya mallaketa, ta matsa kusa da jerin kayan ciye2 da aka ajiye a falon ta zuba mishi coconut juice, ta mika mishi ya amsa tare da murmushi yasha, sannan ya kalketa yace Zeena har yanzu kina sona kuwa? Ko an kwace min ke, sai taji nauyin maganan daya mata, tayi kasa dakai, a dai2 lokacin Mysha ta shigo falon da sauri tare da fadin ina bakon namu, gabaki daya komai nata ya tsaya ta kasa ko motsi, sai dai a zuciyanta take ta nanata wa, tsarki ya tabbata ga Allah wanda yayi wannan hallita, adeel ne Ya katse mata tunani da fadin Mysha right?mai makon amsa sai tayi murmushi wanda ita kanta bata San tana dashi ba, ta karasa shigowa falon ta zauna, Zeena tace ya akai ka gane ta? Yayi dan murmushi yace nasan itace daka yanayin yanda ta shigo, Zeena ta kalli Mysha wanda ta kafe adeel da ido, tace sai yanzu koh, tace kiyi hakuri Zeena baki mukayi sai yasa banzo da wuri ba, haka suka zauna suna ta fira cikin nishadi, har adeel ya tafi yaba Zeena tsaraba da yawa, itama Mysha ya bata nata.
Mysha ta kasa tsaye ta kasa zaune sai kaiwa da kawowa take a dakinta, tabbas adeel ya hadu kalan namijin da take mafarkin samu kenan, ko wace mace zatayi burin yau ace ta mallake shi, a matsayin miji, wata zuciyan tace mata Mysha mai kikeyi haka, saurayin aminyar ki ce wanda take matukar so, kaman ranta, Ya kamata ki cire wannan tunanin a ranki, dan bai kamace ki ba.
Maryam obamββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
(Mrs nura kuriga)ππΉ
Dedicated this page to hafsy (mamani) π
1β£6β£t2β£0β£
Adeel ne zaune cikin gidansu Zeena a falon baki yana jiran zuwanta, duk da baya kallon kofa, kanshin turaranta yaji yasa yasan ta karaso, da murmushi ya dago ya kalleta, amma ga mamakin shi, ba ita ya gani ba, Mysha ce, cikin wani Riga da wando yan kanti, tace barka da hutawa, Ya amsa da yauwa ya kike, cikin lallausar murya ta amsa da lafiya, kaifa? A dai2 lokacin Zeena ta shigo, ganin Mysha a wajan yasa ta tsaya tare da mata tambayan yaushe kika shigo? Tace yanzu ban dade ba, naga falon nan a bude na dauka kina ciki saina nufo nan, ashe baki riga kin iso ba, suka samu waje suka zauna, adeel ya kafe Zeena da ido, Mysha tana lura dashi duk sai taji wani iri, tunda take wannan ne rana na farko data fara kishi da Zeena sannan kuma rana na farko data yarda zata iya komai dan ta samu adeel, sai a yanzu ta kare mishi kallo, adeel namiji ne wanda ya hadu, Shiba dogo ba kuma ba zaka kirashi da gajere ba, sannan idonshi ma kanshi abun burgewa ne, dan inka kalla idonshi kaman mai jin bacci, (sexy eye) gashi yana da faffadan kirji, gashi yana da haske kaman balarabe, Zeena ce ta katse ta tare da fadin Mysha ya kikayi shuru, tayi firgit tace ina jinki, Zeena ta kafeta da ido tace wai mai kike tunani haka? Tace babu komai, adeel yace Zeena ya maganan mu? Taji gabanta ya fadi, tayi shuru, ganin haka yace Zeena plz kimin magana, tace adeel na fada Maka tun farko kudiri na akan karatu, bani da burin inyi aure yanzu, Ya kalli Mysha yace plz kisa baki, Mysha harga Allah taji dadin jin amsan Zeena, amma a fili sai tace haba Zeena aure ai shine darajan y’a mace, kuma babu abunda yafi ma mace mutunci face yau ace tana d’akin mijinta, kuma koda karatun zakiyi idan kina da aure za’afi mutunta ki, ada ina tunanin kaman mahaifina baimin adalci ba, nason inyi aure daka na kammala secondary school, amma da nayi nazari akan abun sai naga wannan shine babban gata daya nunamin, tunda Mysha ta fara magana adeel ya kafeta da ido tare da mamakin jin irin wannan kalaman a bakinta, yaji ta burgeshi, Zeena tace Mysha hakane, amma kawai bana ra’ayi ne, jin haka adeel ya tashi tare da fadin owk babu damuwa indai kin canza ra’ayi zaki iya nema na, yabar gidan ta bishi da kallo.
Mysha nata jin dadin abunda ya faru yau, tabbas tasan halin Zeena indai tace abu da wuya kuma ta canza, lokaci daya wani haushin Zeena taji yana shiganta, tare da fadin Zeena ba kyau kika fini ba, sai dai ki nunamin hasken fata, hasalima da kadan kika fini haske, kowa yace ke yake so jiba afraz yanda ya mutu a kanta, yaro hadadde sai dai matsala daya bashi da hali, ga adeel shima kowa yace ke, why not me, dole sai na sami adeel at any cost.
Wasa2 yau satin adeel biyu baya zuwa wajan Zeena inta kirashi kuma sai yaga dama yake dauka, koda ya dauka dinma tambaya daya yake mata kin amince, tace adeel kamin hakuri, baya bari ta karasa saiya kashe Wayan, tayi bala’in shiga damuwa tabbas tana son adeel amma bazata iya yarda da kudirishi ba, tana burin tayi karatu mai zurfi kafin aure, domin tana ganin in tayi aure da wuya ta samu cikan burinta.
Yau Monday Zeena da abda suna dauke da kayan skul, abda ta kalli Zeena tace yau ke zaki Kaini skul plz, Zeena ta mata harara tace tunda nice driver koh, gwara ma ki nemi mai kaiki, jin muryan daddy dinsu sukayi yana fadin zo mamana ni dakai na zan kaiki, tayi dariya cike da jin dadi ta nufi mahaifin nata, tana yima Zeena gwalo, Zeena tace ina wasa dake koh, daddy yayi dariya yace haba Zeena mai mamana tayi miki da safen nan kike mata haka, ta dan turo baki irin na shagwaba tace daddy kana taking side dinta koh, babu komai, Ya karasa kusa da ita yace no Zeena dukan ku ina tare daku, jin haka yasa tama abda gwalo itama, ganin haka yasa abda tasa kuka Zeena ta fita da sauri tana dariya, daddy ya kalli abda yace lah kuka zaki sa tace ke raguwa ce, jin haka yasa tayi shuru, yace muje in kaiki, sai in wuce office,.
Alokacin da Zeena takai skul a tare sukayi parking ita da afraz, yayi sauri ya fito ya bude motarta yace fito mu shiga tare mana, ta sakar mai harara, yayi dariya yace in kika bata rai kinfi kyau, tayi tsaki tace wlh afraz kana da naci, wai mai zan Maka ka daina kulani, yace babu, dan komai zaki min bazan daina kulaki ba, tunda ina sonki kuma ke zan aura, ta saki dariya tare da tafa hannu, tace aiko maza sun kare wlh ban auranka, balle ma kai ba namiji bane, Ina maka kallon d’an daudu ne, tana fadin haka ta wuce, ranshi yayi mugun baci yace saina nuna miki ni a cikin mazan ma daban nake, Ya cije lebe u will regret it wallahi Zeena kota wani irin hali saina sameki, shima ya shiga cikin skul din.
Maryam obam ββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to my kawata ta rai da rai nana fidaddusyπππ»
2β£6β£to3β£0β£
“adeel ya aika gidansu Mysha an tsayar da komai na aure amma iyayenta sunce saita kammala secondary skul za’ayi bikin, mahaifin adeel ya yarda da hakan tunda ance bai kai shekara daya ba, zata kammala, kuma yaji dadin ganin gidan da d’an nashi ya nemo aure gidan mutunci,bayan an gama komai suka wuce tare da fatan Allah ya kaisu lokacin,
Su Zeena an kammala jarabawa na zuwa ss2 sunyi hutu, yanzu babu skul, sai a yanzu take kewan adeel sosai kasan cewan suna hutu babu skul, kullum sai zaman gida, duk ta rame tayi dan duhu, gashi number din adeel din duk basa zuwa, tayi mugun shiga damuwa, har ummi ta fahimci hakan tayi tambayan duniya akan mai yake damunta, amsan dai kullum daya ce babu komai, ta dai zuba mata ido ta rabu da ita,
Yau an tashi garin Abuja da sanyi sosai yawanci mutane na dauke da rigan sanyi wasu harda hula, Zeena ta fito daka dakinta duk ta rame jikinta sanye take da Riga da wando ta daura suwaita akai, da hula kalan pink, hannunta dauke da key din mota, ta nufi falo ta tarar da ummi, tace ummi barka da Safiya, ganin yar tata kaman tana cikin ni shadi hakan ya mata dadi, tace yauwa Zeena ina zaki? Tace ummi wajan Mysha zani tace toh sai kin dawo, ta amsa da toh ta fita.
Lokacin da Zeena ta karasa gidansu Mysha tayi parking motar ta, ta nufi cikin gidan, ta tarar da mumy din Mysha a falo ta gaidata, ta amsa cikin fara’a har tana dan tsokanan ta, kin mana yaji dai Zeena kwana biyu bakya zuwa, tayi dan murmushi tace Amin hakuri mumy, tace Mysha tana dakinta, ta amsa da toh, ta nufi dakinta a kwance ta sameta cikin blanket, taja mata kafa, ta dan bude ido, Zeena ta sakar mata murmushi, ganin Zeena yasa ta tashi tare da dan yin gajeran tsaki, Zeena tace baki da matsala Mysha, ta dan ya mutsa fuska kaman bata son magana tace toh mai zai hanani bacci ai wannan sai ke, Zeena tace kaman kin sani wlh bana iya bacci wlh adeel kwata2 bana samun shi a waya, Mysha tace kai Zeena dan Allah kema ki rabu dashi nifa bazan dauka wulakanci ba, mutum ya shareki amma ke kullum kina nan cikin tunanin shi, Zeena tace Mysha wlh ba zaki gane ba, son adeel yamin yawa, yana da irin abubuwan da nake so mijin da zan aura ya kasance dashi, Mysha ta tabe baki tace toh yanzu miye abun yi? Zeena tace nazo muje gidansu ne ko Allah zai sa in ganshi, jin haka Mysha tace haba Zeena kin bada mata wlh akan mai zaki gidansu inya wulakantaki fa, tayi shuru, tabbas Mysha tayi gaskiya hala ma wata ya samu ya manta dani, lokaci daya taji wani bakin kishin adeel ya lullubeta, anya zan iya juran ganin adeel da wata mace kuwa, Mysha tace kinyi shuru, Zeena tace toh Mysha mai zance abun ne duk ya zama wani iri, Mysha tace Zeena ya kamata ki cireshi a ranki tun yanzu, kar nan gaba abun ya zaman miki matsala, Zeena tace Mysha kina ganin kaman Abu mai sauki ne in cire adeel a raina, kin San so kuwa Mysha? Bari kiji so ba wasa bane wani abu ne da yake shiga ran Dan Adam ba tare da notice ba, sai dai kaji ka fada wlh Mysha inda inada halin da zan cire son adeel toh zan cire saboda abu daya, a rayuwa ta banso in kira mutum ya kashe min waya, kinga adeel tunda haka ta faru ya daina daukan wayana kwata2, naso in shareshi inyi fushi dashi amma na kasa, Mysha dai kallonta take tana ganin duk sonda Zeena take ma adeel bata kaita ba, Mysha tace toh dazu da kikeso muje gidansu kin janye kudirin karatun ne, Zeena tace eh zan janye dan banso in rasa adeel dan naga idan nayi wasa zan rasa shi, Mysha tayi dariyan mugunta tare da fadin ai kin rasa adeel Zeena har abada, amma a fili sai tace kai kawata amma naji dadin hakan, yanzu tashi muje gidan nasu muga in yana nan, Zeena cikin murna tace suje, kai tsaye gidansu adeel suka nufa, da suka karasa sun tarar da mai gadi a zaune a wajan gidan suka mai sallama, Ya amsa sannan sukace dan Allah adeel muke nema, yace ai baya nan yana China wajan sati biyu kenan, gaban Zeena ya fadi, yace cikin ku wacece Zeena? Tace gani nan ya dauko takarda ya bata, yace ance in baki inji shi toh ban samu naje ba sai gaki, tace toh amma taya akai ka gane akwai Zeena a nan, Ya dan fara dan in ina, dama ya fada min kina da haske toh ganin haka nace hala cikin ku baza’a rasa Zeena din da yaban sako in bata ba, tace toh nagode suka wuce, saida suka karasa gidansu Mysha ta bude letter din rubutu ne kaman haka,. “Zeena ada naso ki naso in kasance dake a matsayin mata kuma uwar y’ay’ana kin nuna baki ra’ayina toh ina farin cikin shaida miki Zeena nima a yanzu babu sonki ko daya a raina, na samu wacce nake so Dan haka kiyi hakuri kar ki batama kanki lokaci, nagode. Sakin takardan tayi Mysha ta dauka ta karanta tace yanxu haka adeel zai miki lallai namiji badan goyo bane, ko jin abunda Mysha take fada batayi, ta shiga motar ta, ta wuce tuki take amma bata San maike gabanta ba idonta har rufewa yake bata gani sosai, ji tayi garab ta bugi wani mota, mai motan ya fito rai a bace amma ganin Zeena yasa yace Zeena what happen with you hope you are OK, kai kawai ta iya d’aga mishi tana ganin jiri2, mutane keta musu horn ganin ko daga hannu ta kasa yasa ya zagaya ya daukota dakyar ta iya fadin afraz ka daina taba ni, amma ko a jikin shi, yasa ta cikin motanshi sannan ya koma nata ya matsar gefe, Ya dauke nashi a hanya ma, ido ya kura mata tare da wani mugun sha’awanta, tabbas Zeena ta hadu, Ya tada motar ya figa, wani gidan gonanshi ya nufa da ita, bayan sun karasa ya dauketa cak ya kaita wani d’aki, Ya ajiye ta kan gado, yana wani murmushi, Ya fara kokarin cire mata riga..
Maryam obamββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to waleeda luvπ
2β£1β£to2β£5β£
“wasa2 yau wajan wata daya adeel yana fushi da ita, ga Mysha ta rasa gane kanta, ta gefe daya kuma gashi zasu fara exam duk tunani ya mata yawa, ga afraz irin abubuwan da yake mata yayi yawa,
Zeena ta kalli Mysha tace muje study room muyi karatu, Mysha ta dan yamutsa fuska tace no kije kaina yana min ciwo, Zeena tayi dan sororo tana kallon ta, tace muje kisha magani mana, tace ki barni plz Zeena am ok, ganin haka Zeena ta fita, ta nufi study room din tare da tunanin maike damun Mysha kwana2, a lokacin data karasa taga afraz a kofan study room din, shida wasu abokan shi, ta daure fuska ta nufi ciki, shima bai kulata ba, hakan ya mata dadi, inta tuna ya kusa barin skul dinma sai taji wani farin ciki.
Mysha ce zaune a cikin Millennium Park, tana jiran adeel, tana shan drink, bata wani dade ba, yazo, bayan ya zauna ya kalleta babu yabo babu fallasa, yace Mysha lfya kika kirani nan, ko Zeena ta amince ne, ta dan yamutsa fuska jin an kira sunan Zeena, tace nop dama ina son magana dakai ne, yace ok ina sauraranki, ta dan saki murmushi tace adeel kai yanzu kana ganin zaka tsaya jiran Zeena har sai ta kammala karatun ta? Ya danyi shuru can yace bazan iya ba wlh Mysha alhaji na ya dameni yanzu ma yaban nanda wata daya in Kawo mata koya aura min duk wacce yaga dama, plz Mysha kima Zeena magana ko zata tausaya min wlh ina son Zeena kullum da tunaninta nake kwana nake tashi, Mysha tace indai Zeena ce ba zata amince dakai ba, tana da kafiya, babu yanda banyi da itaba amma taki yarda, sai yasa na kiraki in shawarceka, yace ina jinki, tace adeel nima mahaifina yace ina gama secondary school zaimin aure, yace gwd haka yana dakyau ai domin shine ya dace da y’a mace, gidan mijinta, tace haka ne, toh amma akwai matsala yace name kenan, tace bani da saurayi wanda nake so, yace aiya Allah ya baki, tayi dan murmushi tare da kara make murya tace adeel mai zai hana ka nemi aure na, yace what Kin San mai kike fada kuwa Mysha, tace eh na sani adeel, kaga kai an baka 1month ni kuma yanzu gobe zamu fara exam na zuwa ss2, anan kuma zanyi waec, nasan kana San Zeena ita kuma tana da burin karatu mai zurfi kafin aure, kaga nima ina da burin karatun amma dady na yace a d’aki na zanyi, kaga inka aure ni, zamu taimaki juna, zanyi karatu na, idan Zeena itama ta gama saika sakeni ka aureta, yayi shuru can yace sorry Mysha I can’t do it, Ya tashi yabar wajan, tayi tsaki tare da fadin wlh adeel kota wani hali saina zama matarka, taji wani tsanan Zeena a ranta.
Su Zeena an fara exam yanzu ba kaman da ba Mysha an dan sake ma Zeena kadan, afraz an bar skul suma sun kusa fara waec,sai dai yakan dan zo jefi2,
Wayan Mysha kema ringing tayi tsaki ganin sunan adeel yasa tayi sauri ta dauka tare da fadin hello, bai jira ta gama fadin abunda zata ceba, yace ina kofar gidanku, tayi sauri ta tashi ta dauki gyale ta fita, ta sameshi cikin mota ta bude ta shiga, da murmushi a fuskanta, Ya kalleta yace Mysha na amince da kudirinki zan aureki amma zan sakeki bayan Zeena ta Gama karatu, don ita nake so, I tace zabi na, tayi dan murmushi tace babu komai, amma da sharadi yace name, tace karka fadama Zeena yanda mukayi, yace babu komai. Sukayi sallama ya wuce, ta shiga gida tana murna ta sami adeel, tace ai adeel kaida Zeena har abada tayi wani dariya wanda ita tasan mai take nufi.
Yau Zeena tayi mamakin canjin Mysha ganin haka yasa take fada mata adeel ya daina kulata, Mysha tace ki shareshi kema tunda ba’a dole, Zeena tace baki San yanda nake son adeel ba Mysha wlh ina son adeel fiye da komai, duk na rame ko abinci bana iya samun ci in koshi saboda tunanin shi, yaki yamin uzuri, wlh Mysha ban so inyi aure ban kammala karatu ba, domin bazan iya ba mijina kulawan daya dace ba, ga karatu ga hidiman mijina, kinga inna Gama karatun in mukayi aure zai samu kulawa sosai, Mysha tayi shuru amma ji takeyi kaman ta shake Zeena dan haushi, tace Zeena tunda kin dage karatu zakiyi sai kiyi ni bari inje inada abunyi.
Maryam obam ββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to huda babyππ»
3β£1β£to3β£5β£
“Ya cire cardigan din dake jikinta, sai yar riga karama ya rage mai gajeran hannu, Ya kurama kirjinta ido, har wani hadde miyau yake, Ya fara kokarin cire rigan itama, ta dan sa hannu ta rike tare da fadin ruwa2 ya tashi da sauri yaje ya dauko ruwa ya zuba mata maganin bacci a ciki sannan ya juya ya bata tasha duk idonta na rufe, bata san wake mata wannan aikin ba, bata dade dasha ba, bacci mai nauyi ya dauke ta, Ya cire mata rigan ganin kirjinta yasa ya kara rudewa, Ya fara wasa da kirjinta gaba daya ya fita hayyacinshi, afraz yayi nasaran raba Zeena da budurcinta, har ya gama komai bata farka ba, jini keta zuba a jikinta ganin haka yasa mata kayanta ya dauketa cak, Ya Sata a mota kai tsaye inda ya parka motan ta, Ya nufa, yako tarar da motan a wajan ya bude yasa ta a ciki yaja nashi motan ya wuce,
Gaba daya hankalin iyayen Zeena ya tashi, tun dazu aketa nemanta amma ba’a ganta ba, ga wayanta yana ta ringing ba’a daga ba, ganin haka dady dinta ya fita ko za’a dace, amma babu labari, hankalinsu yayi mugun tashi, gashi Mysha tace tun dazu ta wuce, an sanar gidan radio da tv ko Allah zai sa a dace, police sunzo suma an bada report, ummi ganin wajan karfe goma shiru yasa tace bari dai taje gidansu Mysha taji ko wani abu ya faru kafin tabar gidan, jin haka dadyn Zeena shima yace suje tare, suna tafiya suna duba hanya ko Allah zaisa su ganta, driver ke tuka su, ummi tace tsaya2 kaman ga motan Zeena can, bayan driver ya tsaya da motan, da sauri ummi ta fita, ta bude motan sai ganin Zeena tayi cikin jini gabanta ya fadi ta fara salati, ta rike mijinta ta saki kuka mai karfi tare da fadin mai ya sami Zeena na shiga uku, dady yace ba kuka zakiyi ba, mu dauketa mu kaita asibiti, dady ya dauketa suka nufi asibiti da ita, likitoci sun an sheta anyi emergency room da ita, ummi ta kasa samun nutsuwa sai kaiwa da kawowa take yi, ita da dady an rasa mai bama wani baki, kowa yana cikin tashin hankali, likitoci sai wajan shadaya saura suka fito, ummi taje da sauri tace Dr maiya sameta? Dr yace muje office, suka nufi office dinshi bayan sun zauna, daddy yace Dr maiya sameta, dr yace anyi mata fyade ne sannan an bata maganin bacci wanda zai iya kaita nan da kwana biyu bata farka ba, dady yace what? Ummi babu abunda take iya fada sai innalillahi wa inna ilaihira jiun, wani hawaye mai zafi ke zuba daka idonta, dakyar daddy ya samu ta dan nutsu.
Police sun zo bincike akan abun amma ummi tace subar maganan dan bata son tonan asiri, domin bincike akan wannan abun kaman an tozarta yarta ne, ta dai ce koma waye shida Allah.
Kwanan Zeena uku ta farka daka baccin da take, a lokacin data bude idonta wani jiri2 take gani, ganin ta farka ummi ta kira Dr yazo ya kuma dubata yace ma ummi sai su godema Allah tunda ta farka, sannan a hankula komai nata zai koma normal domin kwayar da aka bata mai karfi ne.
Zeena anata samun sauki kwananta goma a asibiti aka sallameta, Mysha tazo sau biyu tana dubata, amma bata San mai aka mata ba, iyayen Zeena din ne kawai suka San mai ya faru da ita, ita kanta Zeena din ta kasa tuna komai, sai dai tana ganin kaman hatsari tayi lokacin da tabar gidansu Mysha.
BAYAN WATA BAKWAI
Alokacin su Zeena an fara waec tunda abun nan ya faru mahaifinta ya hanata zuwa ko ina ita daya saida masu bata kulawa harda skul, anata shirin bikin Mysha da adeel ba tare da sanin Zeena ba a kwana a tashi babu wuya su Zeena an kammala jarabawa, sai a ranan Mysha take fada mata maganan auran ta, Zeena tace haba Mysha aure zakiyi shine sai yanzu kike fad’a min kina ganin kin min adalci, Mysha tace kiyi hakuri Zeena abun ne yazo da haka, tace shikenan wa zaki aura, Mysha tace surprised nake son miki sai ran bikin zaki sani, tace Allah ya kaimu, kin ga da adeel na nan nema daya fito, Mysha tace Allah sarki ai adeel bai kyauta miki ba, Ya miki halin maza da haka dai suka wuce.
Anata shirin bikin Mysha kasan cewan angon baya farin ciki da bikin yasa bai dawo Nigeria ba yace sai Ana gobe bikin zai dawo andai yi komai daya dace, wani abokinshi mai suna ahmad shiya tsaya akan komai kuma shiya sallama yan matan amarya, a ranan da ango din zai dawo suka shirya kamu wanda ya hada manyan mutane, masu ji da Kansu anyi kamu lafiya kowa ya watse.
Yau sati aka daura auren Mysha da adeel, wajan karfe goma, mutane sun taru sosai, anyi kalanda dasu memo an raba ma mutane, a lokacin da Zeena ta gani ba karamin shock tayi ba na ganin adeel tare da Mysha, wani hawaye ya zubo mata wanda bata San yana zuba ba, waje tayi cikin motan ta, tana kara kallon Hoton tana ganin kaman idonta ke nuna mata adeel, amma bashi bane, ta dai tabbatar adeel din ne, tace driver ya kaita gida, yace toh suna tafiya tana ganin jiri2 dama Mysha haka take zata iya cin Amana na, wani hawaye mai zafi ya kara zubo mata, AMINIYA TA CE yau taci Amana ta, ta rabani da abun da nake so, ashe dama haka aminci yake yanzu na aminta da ita amma taci Amana ta dama shine surprised din da Mysha zata bani.
Maryam obamββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to zee babyππ»
3β£6β£to4β£0β£
“wani azababban ciwon kai ne Ya kamata lokaci daya, inda ita take tuki toh da komai zai iya faruwa, shi kanshi driver din dake janta ganin yana yinta ta bashi tausayi duk da bai San maike damunta ba, Mysha why are you doing this to me, u are my best friend, why Mysha, I trust you but you break the trust that I have for you, inda kin fadamin kina son adeel zan iya hakura dashi in bar miki Mysha am not a selfish, you hurt me alot Mysha, ta saki kuka mai karfi, driver yace hajiya Zeena lafiya kuwa? Ta kasa ko motsa baki balle tayi tunanin bashi amsa, jin bata kulashi ba, yasa yaci gaba da tuki, har suka isa gida, da gudu ta shiga gidan kai tsaye dakinta ta shiga, iyayenta suka bita suma dan ganin yanda ta shigo da gudu, amma ta rufe kofan ta, suna ta buga kofan amma taki ta bude, haka suka barta.
Zeena komai Ya tsaya mata kwata2 ta tsani komai, ko fita batayi kullum tana gida, bata komai sai kuka, tare da bakin cikin abunda Mysha ta mata, ta rabata da farin cikin ranta, har yanzu tana mamakin abun, iyayenta na tausaya mata, sun dai yanke hukuncin su turata wajan yayanta zaheer kasar japan ko Allah zaisa ta manta komai, ummi ta shigo d’akin ta ganta tana ta faman hawaye kaman kullum, tace Zeena kiyi hakuri ki cire wannan abun a ranki dan Allah, ta kalli ummi tace haba ummi AMINIYA TA CE, fa Mysha taci Amana ta, ta rabani da masoyi na, ummi dama haka kawaye suke dacin Amana, yanzu babu mutane masu Amana, masu amana sun kare kwata2 ban taba tunanin Mysha zata min haka ba, ummi inda Mysha ta fadamin tana son adeel ni zan iya bar mata, amma ta yanda tamin is painful, ummi ni daya nasan abunda nake ji a raina yanzu babu mai fahimta na, ta saki kuka ummi ta janyo ta, ta rungumeta tana tausayin yar tata, tace Zeena ki daina fadin haka, akwai masu amana kar kiyi judging mutane ba duka aka taru aka zama daya ba, akwai mutane masu aminci, tace ummi amma yanzu sunyi karanci, plz ummi ban San zama a kasar nan, Ina so in bar Nigeria gobe dan ina ganin kaman yanzu abun ya faru, ummi tace shikenan Zeena dama nida dady dinki mun yanke hukuncin ki tafi Japan wajan zaheer kiyi karatun ki a can, tace toh ummi I want to leave tomorrow, ummi tace shikenan amma kibar wannan kukan tace toh ummi ta fita daka d’akin.
Mysha ce zaune a falonta da yasha kayan ado na more rayuwa masu tsadan gaske, tana tunanin ta yanda zata bullo wa adeel, Ya dinga kulata, jin motsin shi tayi, yasa tayi saurin tashi ta nufeshi tare dayin hugging nashi, yayi sauri ya tureta, tare da daure fuska, yace Mysha karki manta nida ke fake marriage mukayi, lokaci kawai muke jira mu rabu, so plz ki daina shige min, domin bazan taba kallonki a matsayin wacce zan iya zama da ita ba, tace haba adeel nifa matarka ce kuma inada hakki a kanka, yace what, hakki matata, yayi wani murmushi tare da fadin dnt you ever think of this thing, you are not my wife, lalle Mysha har kina tunanin hakki, kina da hankali kuwa, kin manta yarjejeniyan mu nida ke, tace no adeel ban manta ba, naji na canza ra’ayi, bazan iya rabuwa dakai ba ina so ka daukeni a matsayin matarka wanda mukayi aure na soyayya, Ya kalleta a wulakance yace Mysha kinyi kuskure you are selfish kinci amanan kawance, but zan nuna miki kuskuranki, tace adeel baka isa kamin komai ba, sonka yasa nayi haka na rasa hanyan da zan sameka saida nabi ta wannan hanyan, yace Mysha sai kinyi dana sanin sani na, kin rabani da Zeena akan selfishness naki, zan zauna dake amma ki sani sai kin gwammace gwara mutuwa akan aurena, domin nan gidan daka yau zai koma miki gidan azaba, babu ke babu farin ciki,. Yana fadin haka ya fita, bai dade ba ya dawo, tare da masu aikin gidan duka, yace duk ya sallamesu, tace haba adeel wa zai dinga aikin? Yace ke, don shine abun daya dace dake, ta saki kuka haba adeel yanzu abunda zaka min kenan, yayi banza d ita ya haura sama, Ya barta a nan, cikin bakin ciki.
Zeena tabar Nigeria ta tafi Japan, da yake acan kasar daddy dinsu nada gida anan yayanta yake zama, toh itama a can zata zauna ummi ta had’a ta ita da wata yar dattijuwa dan ta dinga kula da ita, gashi kuma an kammala mata komai na skul, ta sami course din da take burin samu kuma, doctor, Zeena dan kwana biyu da tayi a kasar taji dadin kasar sosai, zaheer shi yake kaita skul ya dauko ta, kafin ta saba da kasar,.
Afraz zaune a d’akin hotel dake kasar nijar, shida wata mata, ta manne shi, amma ba komai yake tunani ba, sai Zeena tabbas mata suna suka tara, babu irin macen da bai nema ba, amma ya rasa dalilin da har yanzu bai sadu da wanda yaji ya gamsu da ita ba sai Zeena, duk da a lokacin shi daya yayi kadan shi yayi rawan shi, balle ace na sadu da ita cikin son ranta ya zan kasance, wani abu yaji yana to karan zuciyan shi tabbas Zeena ina sonki kuma zanyi farin cikin in mallake ki a matsayin matar aure na, ada ba sonki nake ba sha’awar ki nake amma yanzu, babu komai tare dani face soyayyan gaskiya, Ya lumshe ido, matar dake manne dashi tace Afraz inata magana kayi shiru, Ya dan tureta ya tashi, Ya fara sa kaya, tace ina zaka kuma yace zan koma skul, ban son in kara kwana a kasar nan.
Maryam obamββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to yasmin darling πππ»
4β£1β£to4β£5β£
Zeena an fara sabawa da garin duk da ba fita takeyi ba, daka skul sai gida, koda tana son abu zaheer zai Kawo mata, kuma tana karatun ta cikin kwanciyan hankali, amma har yanzu ta kasa mantawa da adeel kullum dashi take kwana take tashi, duk yanda tayi kokarin ta cire shi a ranta amma abun yaki yi, ji take kaman kullum ana kara mata sonshi ne, ta dai barma Allah zabi akan ya zaba mata mafi alkairi.
Afraz ya dawo London amma kwata2 baya jin dadin kasar, ji yayi babu abunda yake son gani sai Zeena, har mamaki yake, kuma yakan tambayi kanshi wai mai yake damunshi, Ya lumshe ido tare da tuna surar Zeena, wani ni shadi yaji yana shigarshi, Zeena you are the best, kinfi ko wace mace, ke daban kike, burina in mallake ki.
Adeel yana zaune a cikin bedroom dinshi daka shi, sai singlet da shortener, yana danna laptop dinshi yana kallo yana murmushi, Hoton Zeena yake kallo, yana fadin Zeena ke tawa ce, saina mallake ki, you are my, bazan bari in rasa kiba, Mysha ta shigo d’akin harta zo kusa dashi bata sani ba, ganin Hoton Zeena a laptop din yana kallo yasa ranta ya baci, ta fisge laptop din tayi jifa dashi, Ya tashi rai a bace ya tsinka mata mari har sau biyu tare da fadin Mysha I hate you, you are evil, tace adeel ni ka mara? Ya daure fuska yace get out tare da nuna mata kofa, yace sai kin San kin fasa laptop din nan, ta fita da gudu tana kuka, toilet ya fada yayi wanka ya fito cikin kananan kaya ya mishi kyau sosai, Ya nufi d’akin ta, Ya ganta kwance kan gado tana rusa kuka, Ya tabe baki, Ya daka mata tsawa tare da fadin ke naki kukan najin dadi ne, sai na d’an d’ana miki irin radadin da kika sani a ciki, yana gama fadin haka ya fita.
Afraz yazo Nigeria, Ya samu labarin Zeena tana Japan karatu wajan mai gadin gidansu, Ya tambayi number dinta yace baida shi, Ya bashi kudi da yawa yace ga wannan plz ka samo min bayani akan inda take karatu a Japan din, mai gadi ya washe baki yace an Gama, Ya amsa number din Afraz din, akan zai kirashi idan ya samu information akan batun, Afraz ya wuce.
Zeena tana cikin class sun gama lecture, tana jiran zaheer yazo ya dauketa, sai ga wani bature yazo inda take, yace mata hello, Ya sakar mata murmushi ta amsa da hi,tana fadin haka ta tashi da nufin fita, yace mata please I want to talk to you, ta dan tsaya tare da fadin ok, Ya kalleta yace please sit down, batamusa mishi ba, ta zauna, Ya kalleta yace, na ganki a skul din nan, so ina lura dake kaman kina da damuwa, naga baki kula kowa, duk da harshen turanci yake mata maganan, ta kalleshi ta dan daure fuska, tayi shiru, ganin haka ya kuma tambayanta ya kikayi shuru, ganin ya matsa mata da tambaya yasa ta tashi tabar class din, tako ci sa’a ta hango zaheer da sauri ta nufeshi ta bude motar ta shiga, tace bros mai yasa kayi late din zuwa dauka na, Ya kalleta yace sorry little sis, naje amso abu ne, ta dan turo baki, irin na shagwaba, yayi dariya yaja motar suka wuce,
Mai gadin gidansu Zeena ya fad’a ma Afraz komai da komai na wajan da Zeena take karatu, yaji dadin labarin, Ya fara shiri na zuwa Japan,
Afraz an sauka a kasar Japan, bai bari ya huta ba, Ya nufi skul din, amma harya gama yawonshi baiga mai kama da Zeena ba, haka ya koma masaukin shi cikin takaici, haka kullum yake ta sintiri a skul din amma shuru kake ji, babu Zeena balle mai kama da ita, wajan sati daya kenan, yayi tsaki tare da fadin kodai mutumin nan wrong address ya bani, mai ma yasa na yarda dashi, Ya tada motarshi, da nufin ya wuce a dai2 lokacin Zeena ta fito daka class zata mota ya hango ta, da sauri ya fita, amma kafin ya karasa ta shige mota sun wuce, Ya koma da sauri yabi bayansu, har suka nufi gida, toh amma wani abu daya tsaya mishi a rai waye wannan namiji din daya dauko ta, miye halakan su, da yaga tana mishi dariya shima yana mata, wani bakin kishin Zeena din yaji yana shiganshi, wannan ne karo na farko daya taba jin kishin y’a mace.
Maryam obam ββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to yasmin darling πππ»
5β£1β£to5β£5β£
“tunda mum din afraz tayi mai magana akan zata neman mai auran Zeena ya cire duk wani fargaba da yake yi akan zai rasa ta, wannan ne Ya bashi da man yin karatu har suka kammala exam dinsu, kuma shine final year dinshi, zai zama cikakken engineer a quantity survey, a ranan daya gama exam din ji yayi kaman yayi tsalle ya gashi a Japan wajan Zeena domin yayi mugun kewanta, shi koda bata kulashi inya ganta ma dadi yake ji, amma dole yayi hakuri gobe tayi, yayi dan gajeran tsaki yaga dare ya mishi nisa ranan, washe gari da asuba ya tashi yayi sallah, sannan aka fara shiri, duk da wajan 10 zasu tashi yana Gama shiri ya nufi airport, Ya zauna kafin lokaci ya cika.
Zeena tana gida yau bata je lecture ba, ta online take dubawa, wayanta dake gefe yayi kara, ta dauka taga abda, tace little sis yakike, abda ta amsa da lfya tare da fadin ya skul, ta amsa da lafiya, wai yaushe zaki zo Zeena, nayi missing dinki, Zeena tayi dariya tace kaman da gaske, abda tayi dariya tace dagaske nake, Zeena tace in mun gama exam zan zo, mun kusa farawa, jin haka abda tayi kara tare da fadin kizo keda bros zaheer, kice na mishi mata, Zeena tayi dariya tare da fadin wa innan kananan kawayen naki, a ciki kika zaban mai, ta dan turo baki kaman Zeena din tana gabanta, tace haba Zeena yanzu fa ina jss3 going to ss1 kinga ai ba za’a kirani da karama ba, Zeena tayi dariya sosai tace abda baki da dama, tace ina ummi abda tace tana kitchen Zeena tace takai mata Wayan, ta amsa da toh, ta nufi kitchen din taba ummi, bayan ta amsa suka gaisa tace ummi daddy ya fada miki wata magana, tace a’a maganan mai nene, tace akan adeel, ummi tace Zeena har yanzu baki cireshi a ranki ba, tayi shiru, ummi taci gaba da fadin ya kamata kima kanki fad’a, kara girma kikeyi Zeena ya kamata kisan abun da zai yiwu da wanda bazai yiwu ba, ki cireshi a ranki ki fara kema rayuwanki, tace toh ummi, tana fadin haka ta kashe Wayan, tabbas abunda ummi ta fad’a haka ne, Ya kamata ta cire adeel a ranta, amma ta yaya hakan zai faru taya zata cireshi, bayan kullum son shi kara karuwa yake a ranta, wani hawaye ya biyo kuncinta, adeel ka cuceni kaida Mysha kuna can kuna jin dadin rayuwanku kun barni cikin kunci da bakin ciki, sonka yamin yawa, mai zanyi sonka ya fita a raina, Allah sarki Zeena rashin masoyi babu dadi.
Afraz an sauka a kasar Japan, wani farin ciki yake ji tare da nishad’i yazo kasar da masoyiyarshi take, kai tsaye hotel ya nufa ya ajiye kayanshi, Ya fad’a toilet yayi wanka, bayan ya fito ya shirya cikin kananan kaya, yayi kyau sosai, kai tsaye gidansu Zeena ya nufa, yayi nocking, aka bashi izinin shiga, fatima ya gani wacce take kula da Zeena, Ya gaidata cikin harshen hausa da mamaki take amsa wa, don a zaton ta baya jin hausa don baiyi kama damai jin hausa ba, zata iya kiranshi da bature ko balarabe, Ya katse ta tare da fadin dan Allah Zeena nake nema, tace tana baya, ta nuna mai hanyan da zaibi, Ya shiga ya ganta cikin wani yar bukka, ta zabga uban tagumi, duk sai yaji wani kala kasancewan ya ganta a haka ya tabbata tana cikin damuwa, Ya matsa kusa da ita, Ya cire mata hannun, ganin afraz yasa tayi saurin tashi tare da fadin maiya Kawo ka nan, yace Zeena dan Allah ki tausayamin wlh Zeena ina sonki, tayi tsaki tare da fadin nace bana sonka wai afraz dole ne, ya kafeta da ido tare da fadin Zeena nasan abun daya faru da kike tunawa wlh Zeena na canza yanzu ba haka nake ba, tayi shuru bata kulashi ba, Ya matsa kusa da ita, tare da daura hannunshi kan kafadan ta, Zeena kece farin ciki na kece komai nawa, ganin bata kulashi ba ya janyota tare da rungumeta, babu abunda kake ji sai saukar numfashin su, sunyi wajan minti uku a haka, yace Zeena plz ki soni kaman yanda nake sonki, taja da baya tare da fadin afraz you will never change, who give you the right to touch me, let me tell you one thing, niba kalan yan iskan yan matanka din nan bane, so you better respect your self and leave, idonshi ya canza kala, Ya kuma matsawa yana fadin Zeena plz kiyi hakuri ki soni, tace nace bana sonka I hate you, yayi dan murmushi yace Zeena ko kina sona ko baki so na saina aureki kota wani haline, this is a promise, Ya fara tafiya tace afraz ya tsaya ba tare daya waigo ba, tace kace saika aureni koh, to bari kaji dana aureka gwara in mutu, ya waigo tare da matsowa kusa da ita, Ya janyo ta, ganin yanda ya daure fuska yasa ta kasa magana, Ya matsa da bakinshi kusa da nata kaman zaiyi kissing dinta, komai Ya tuna kuma ya fasa ya tureta ya fita, ta fashe da kuka tare da fadin wai mai yake shirin faruwa da ita ne, ta gefe daya ga adeel wanda take mutuwar so, tunanin shi ya hanata komai, ta dayan bangaran kuma afraz wanda yake takura mata, haka ta zauna taci kukanta, ta tashi ta shiga d’akinta.
Tunda wannan abun ya faru bata kara ganin afraz ba, hakan ya mata dadi, shima afraz din a washe garin ranan ya koma Nigeria, domin yaga inya biyema Zeena zai iya rasa ta, iyayenshi sunyi mamakin ganin yanda d’an nasu ya rame lokaci daya, sunyi mai tambayoyi afraz ya taso bai saba da karya ba, komai munin abu indai yayi in suka tambayeshi yana fada musu gaskiya, yace mum Zeena nake so ku nemo min auran ta, dady dinshi yace wannan wani irin sone afraz haka, wannan ne karo na farko daya ma iyayenshi karya tare da boye musu abu, Ya fada musu yanda suka hadu da Zeena amma bai fad’a musu ya mata fyade ba, daddy dinshi yace karka damu yar gidan waye, yace yar gidan senator abubakar daura ce, yace ok shikenan zanje gobe muyi magana dashi, yace thank daddy, Ya tashi yabar wajan cikin murna.
Zeena ta fito daka wanka taji karan wayanta da da sauri ta dauka, taga number ne, ta dannna tare da fadin hello, ta dayan bangaran aka amsa da Zeena, jin muryan tayi ya bugan mata dodon kunne, muryan da take burin ji take son ganin mai muryan, yace Zeena plz kiyi min magana, mai makon magana sai ta fashe da kuka, hankalinshi ba karamin tashi yayi ba, yace Zeena dan Allah ki daina wannan kukan, tace adeel mai yasa ka kirani, yace Zeena na kiraki in fad’a miki har yanzu ina sonki, son da nake miki bazan iya yima ko wace mace ba, plz Zeena ki yarda dani banci amanarki ba, jin haka tace adeel plz ban son wannan maganan, yace shikenan Zeena, amma ina so ki sani ina jiranki har ki gama karatun ki, Zeena ke daya ce macen da nake so kuma nake so in mallaka, kullum da sonki nake kwana nake tashi ta kashe Wayan da sauri, Zeena tayi shuru ta kasa furta ko kallama daya, wai mai yake shirin faruwa ne, Don son adeel tana yi amma mijin AMINIYA TA CE, hmmmm muje zuwa.
Maryam obamββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to sayyada darling πππ»
5β£6β£to6β£0β£
Mahaifin afraz bayan ya shiga d’aki ya dauki waya ya kira mahaifin Zeena, a lokacin mahaifin Zeena yana zaune a bedroom dinshi yana kallon news, yaji karan wayanshi, Ya dauko ganin sunan mai Kiran yasa ya dauka da sauri tare da fadin ranka ya dade barka da dare, mahaifin afraz ya amsa da yauwa, bayan sun gaisa mahaifin afraz yace mai gobe kana gida, Ya amsa da eh ranka ya dade, yace insha Allah gobe zanzo da yamma, mahaifin Zeena yace ranka ya dade lafiya dai koh, yace eh lafiya, mahaifin Zeena yace aida ka bari ni nazo da kaina, yace a’a karka damu zanzo da kaina, yace toh ranka ya dade sai na jika, sukayi sallama, bayan ya kashe Wayan yace lafiya kuwa alhaji umar na sidi yake son gani na, mahaifin afraz yana daya daka cikin manyan mutane a Nigeria, bama Nigeria ba kawai duk Africa, babu inda zaije yace yana son abu ba’ayi mishi ba, baya ga siyasa da yayi shi babban dan kasuwa ne, ranan mahaifin Zeena da tunanin zuwan alh umar na sidi yayi bacci.
Zeena na kwance karar wayanta ne ya tashe ta, ta dauka tare da fadin hello cikin muryan bacci, jin muryan adeel yasa ta watsake, yace Zeena badai ni na tashe ki ba, tace a’a dama yanzu nake son in tashi, jin kaman ta dan sake, yasa yaji dadi, tare da fad’a mata yana so yazo Japan akwai maganan da yake so suyi, tace no adeel plz karka zo ka zauna kawai, yace Zeena kin San yanda nayi missing dinki kuwa? Tayi shuru yaci gaba da fadin da kin San yanda nayi missing dinki da baki cemin haka ba, Zeena na tabbata kema kina kewa na, tayi shuru dai bata kulashi ba, shi daya yake ta maganan shi, yace Zeena plz kimin magana, tace ina jinka, ta rasa mai yasa ta kasa fushi da adeel har take sauraranshi, ganin kaman bata son magana yasa yace gobe yana nan tafe, bai jira mai zata fad’a ba ya kashe wayan, wani farin ciki taji,tare da son ganin adeel, domin itama tana son ganinshi, lokaci daya kuma ta canza fuska, tare da tuna abun da ya faru, adeel kamin nisa yanzu ka auri AMINIYA TA, bazan iya auranka ba, tayi shuru na wajan minti biyar, can tayi tsaki tare da shirin zuwa skul.
Wajan karfe biyar mahaifin afraz yazo gidansu Zeena,tare da wani abokinshi aka saukesu a falon baki, sannan aka cika su da kayan ciye2, bayan sun gaisa cikin girmamawa, mahaifin afraz yace alh abubakar, nazo neman alfarma ne, Ina nema ma d’ana afraz auran yarka Zeena, mahaifin Zeena yace haba ranka ya dade ai kai ka wuce wannan, na bama danka auran Zeena, sukayi godiya sannan abokin mahaifin afraz yace a yanke musu sadaki su biya mahaifin Zeena yace Su bada dubu hamsin, nan da nan yaje mota ya dauko wani akwati da kudi cike a ciki, yace ga wannan 50million ne ni na kara akan sadakin, sukayi godiya sannan mahaifin afraz ya kuma neman alfarma akan yana son a daura auren nan da sati biyu, mahaifin Zeena yace babu matsala, sukayi sallama suka wuce.
A lokacin da dadyn Zeena ya shiga gida, Yama mahaifiyar Zeena din bayani kuma hakan ya mata dadi, domin tana ganin idan tayi aure hakan zai sa ta cire adeel a ranta, sannan tace kar’a fad’ama Zeena din maganan auran, domin karta sama kanta damuwa, tunda ta kusa zuwa in ta dawo sai mu mata bayani, daddyn Zeena ya yarda da shawaran matar tashi.
Adeel ya sauka a kasar Japan, kasancewan yana da address din gidansu Zeena din, Ya nufi gidan amma yayi rashin sa’a tana skul, yace bari yaje ya dawo, hotel ya nuna ya fada toilet yayi wanka, yasa kananan kaya, sannan ya fashe jikinshi da turare, Ya zauna tare da jiran anjima kadan yayi ya koma gidansu Zeena din, sai murmushi yake shi daya.
A lokacin da Zeena ta dawo fatima ta fad’a mata anzo nemanta bata nan, bata damu da ko waye ba, tace ok, ta nufi dakinta tayi wanka, tasa wata doguwan riga, ta dauki littafinta ta nufi bukka, don karatu gobe zasu fara exam, littafin dai yana hannunta kuma inka ganta zaka rantse shi take karantawa, amma tunani take, ganin adeel tayi ta gabanta yana murmushi sai taga kaman gizo, yake mata, tasa hannunta tare da taba fuskanshi, taga bai bace , ta tabbata dai shi dinne, tayi sauri ta cire hannunta, tare da fadin adeel yaushe Kazo? Yayi murmushi tare da fadin tun dazu, ya kura mata ido, yaga ta kara girma da kyau wani sonta ne yake kara shigarshi, itama ta nata ban garan, wani sonshi ne yake kuma shiganta, dukansu sunyi shuru suna kallon Juna, ya katse shurun tare da fadin Zeena kina sona kuwa kaman yanda nake sonki, jin haka yasa ta fashe mishi da kuka, hankalinshi yayi mugun tashi, yace Zeena plz kibar wannan kukan kar ki sani cikin damuwa, tace adeel mai yasa ka gujeni, a lokacin da nake bukatan ka, sannan kuma yanzu ka dawo zaka kara yaudara na, yayi sauri ya rufe mata baki da hannunshi yace Zeena ban yaudareki ba, Zeena kece macen dana fara so, kuma har yanzu banga wacce nake so ba sai ke, Zeena Mysha ce ta rabamu akan selfishness nata nan ya bata labarin yanda sukayi da Mysha, tayi shuru babu abunda take sai hawaye, ta kasa furta komai, ganin haka shima yayi shuru yana kallonta, ganin yanda take kuka bazai iya jure ganin kukan ba, Ya matsa kusa da ita, Ya fara share mata hawayen, tare da fadin plz kibar wannan kukan, jin haka tayi shuru, wani sonshi taji ya kuma karuwa a ranta tare da tausaya mishi, tabbas komai Ya faru laifina ne, inda ban Kawo maganan karatu ba da yanxu munyi aure, da hakan bai faru ba, a yanzu ta yarda bazata iya auran ko wani namiji ba inba adeel ba, domin shi daya take so, shima yana sonta, a ranan Zeena ta sake da adeel kuma tace mishi a shirye take data aureshi, hakan yamai dadi, sannan tace karya sake ya saki Mysha domin tana sonshi kuma komai tayi sonshi yasa tayi hakan, yace babu komai duk abunda tace shi zaiyi, daka karshe yayi mata sallama ya wuce masaukin shi, ranan su duka sun kwana cikin farin ciki.
Maryam obamβββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to yasmin darling πππ»
6β£1β£to6β£5β£
Su Zeena an fara exam, cikin kwanciyan hankali, kullum suna tare da adeel, ji take kaman bata taba shiga wani matsala ba, haka shima ta ban garan adeel din, Ya manta da komai, jira yake ta gama exam su dawo Nigeria tare ayi maganan bikinsu, har zaheer yasan adeel kuma ya yaba da hankalinshi, Zeena ta fito daka lecture ta hango adeel ta wajan wata bishiya ya kura mata ido, harta karaso kusa dashi bai daina kallonta ba, tayi dan murmushi tare da fadin yaushe Kazo, yace tun dazu suka sami waje suka zauna, Ya kuma kafeta da ido, tace adeel lafiya kuwa, yace Zeena tun jiya nake jin wani kala a jikina, tace muje asibiti mana, yace no ba abun asibiti bane, tace toh miye adeel, yace inaji a jikina kaman za’a raba mu, tace adeel wannan wani irin magana ne haka, yace Zeena jikina yana bani haka, ta dan daure fuska tare da fadin sai dai in Kaine zaka gujeni, yace haba Zeena komai zai faru bazan taba gudun kiba, kece farin ciki na, tace toh adeel ka daina wannan tunanin ni taka ce, babu mai raba mu, yace Allah yasa, suka d’an taba fira sannan suka tashi suka wuce.
Anata hidiman bikin Zeena da afraz, ba tare da sanin taba, harta zaheer bai San mai ake shiryawa ba, abda kuma daddy dinsu ya gargadeta akan karta fad’a ma Zeena din tace toh taja bakinta tayi shiru.
A lokacin da dadyn afraz ya fad’a mishi yanda sukayi wani farin ciki ne Ya kamashi tare da kara godema iyayenshi, kuma yana alfahari dasu akan komai yake so suna bashi, tunda yaji wannan labarin bai kara neman Zeena ba, yana ganin ya riga ya gama samun ta, ya rasa wani irin so yake mata, bai taba tunanin zai so mace tace bata sonshi ba sai Zeena, Ya lumshe ido tare da fadin Zeena you are special, zan iya yin komai a kanki Zeena.
Yau Thursday su Zeena an gama exam, ta fito tana murna don gobe zata Nigeria taba dady dinta surprise akan sun dai daita da adeel, kuma a shirye take data aureshi, tayi dan murmushi ta tabbata idan dady dinta yaji wannan labarin zaifi kowa murna, kai tsaye gida ta nufa, tana shiga ta fad’a toilet tayi wanka, ta fito falo ta tarar da zaheer yana kallo tace yaushe ka shigo bros, yace ban dade da shigowa ba, yace ya exam din tayi dan murmushi tare da fadin alhamdlh, yace gobe sai gida, tayi dariya tare da fadin ai wutun ma ba wani mai yawa bane, yace inye hutun wata nawa kikeso a baku, tace kaman 3month yayi dariya tare da fadin Zeena baki da dama, tace goben kaima zaka bimu yace eh tare zamu tafi, fatima itama ta fito kana ganinta kasan tana cikin murna domin ta kosa ta ganta a Nigeria itama, taga yan uwanta da abokan arziki, nan suka zauna suna ta fira gwanin sha’awa,
Adeel ya kira Zeena yace yana gidansu ta wajan bukka, tace tana xuwa, ta tashi da sauri ta dauki dan karamin gyale ta yafa a kanta kasancewan gown ne a jikinta na yan kanti, ta fito ta hango shi a zaune, wani dadi taji tare da kara sonshi ta aiyana a ranta adeel ka hadu, babu macen da zata ganka taji bata sonka, wani kishin shi taji data tuna yana da mata, ta karaso kusa dashi ta zauna ta gefe suna kallon Juna, Ya sakar mata murmushi tare da fadin gobe sai gida koh, ta daga mai kai alaman eh, yace ya exam din, ta amsa da alhamdlh, ya kuma kura mata ido yace Zeena bana gajiya da ganinki, kullum sonki kara karuwa yake a raina, tayi murmushin jin dadi, tace nima haka Kaine mai sani farin ciki, koda ina fushi inna tuna dakai sai inji farin ciki, ya sakar mata ido yana kallonta, tace wannan kallon fah, yace ina mamaki ne Zeena, tace name, yanda kike fad’amin wa innan kalaman da bakin ki, jin haka ta dan rufe fuska tana dariya, sunyi fira sosai daka karshe sukayi sallama akan sai gobe,
A yau juma’a aka daura auren Zeena abubakar da afraz umar na sidi, wajan karfe biyu na rana, daurin auren ya tara manyan mutane sosai, ranan afraz yayi kyautar naira kaman za suyi kuka, domin duk wanda ya gani a masallacin indai mai bukata ne saiya bashi kudi, ranan ji yake kaman an mai bushara da gidan aljanna, mahaifinshi duk yana kula dashi, hakan ba karamin dadi ya mishi ba, na ganin danshi cikin farin ciki, duk wanda suka zo daurin aure sun watse,
Su Zeena sai wajan karfe biyar suka sauka, kowa yaga driver dinshi yana jiranshi adeel ya shiga mota akan sai yazo, suma suka shiga nasu motar, kai tsaye gida suka nufa, Zeena taga gidansu makil da mutane, gabanta ya fadi tace mai yake faruwa, driver na parking ta shiga da sauri tana Kiran ummi abda dady, ga mamakin ta sai ta gansu dukansu, da gudu ta nufi ummi, tace ummi wannan taron fa, ganin bata, bata amsa ba ta nufi dady tace dady wannan taron fah, yayi dariya kije ki huta Zeena kafin muyi magana bata musa ba, ta nufi dakinta, tayi wanka ta fito taga an ajiye mata abinci kala2 a d’akin tayi murmushi ta zauna taci tayi nak, ta kwanta abinta,
A lokacin da adeel yaje gida, yaga Mysha shi harga Allah ya manta da tunda ya tafi bai kirata ba, ta rame tayi duhu, tana ganinshi ta taso da kuka, tana fadin adeel kamin adalci kenan, ka tafi wajan sati biyu amma babu waya, baka San ya nake ba, Ina matsayin matarka, duk sai yaji ta bashi tausayi, bai kuma dace ya mata haka ba, amma saiya dake yace ai bance dole ki zauna ba, yana fadin haka ya haura sama, ta zauna tana ta kuka, d’akinshi ya nufa, Ya fada toilet yayi wanka, ya fito cikin wata shadda dinkin kaftani yayi mishi kyau sosai, sai kamshi ke tashi, yaganta a inda ya barta tana ta aikin kuka, jikin shi yayi sanyi, a gaskiya baya mata adalci matarshi ce, kuma ko babu komai tana da hakki a kanshi, zama yayi ya kira sunanta ta amsa da na’am cikin muryan kuka, yace kinyi abinci ta amsa da eh, yace Kawo min, wannan ne karo na farko daya taba tambayanta abinci, jiki na bari ta nufa kitchen ta Kawo mishi, farfesun kayan ciki da fried couscous, da coconut juice, Ya zauna yaci sannan yace mata ya gode, hakan ya mata dadi sosai, Ya kuma Kiran sunanta ta amsa, yayi shuru can yace mata inaso inyi miki magana tace toh inaji, yace ina so in kara aure, gabanta ya fadi tare da tausayin kanta, ta daure dakyar tace wa zaka aura, yace Zeena ta Mike tsaye tare da fadin Zeena, yace yes ta fashe da kuka tare da rokan shi akan ya auro ko wacece, amma banda Zeena, yayi dan murmushi tare da fadin bazan iya kallon ko wace mace ba inba Zeena ba, ita nake so, itace farin ciki na, yana fadan haka ya fita, ta zauna tana tausayin kanta, tabbas idan adeel ya auri Zeena bazata iya zama a gidan ba, duk irin son da take mishi .
Zeena sai wajan 7 ta farka a lokacin dady dinta ya shigo d’akin, yace Zeena bacci kikayi bayan kin San babu kyau baccin bayan la’asar, tace daddy wlh gajiya ne yasa nayi, Ya nemi waje ya zauna akan wata kujera dake d’akin, tayi murmushi tace daddy wai taron miye akeyi haka, yace Zeena ta amsa da na’am ina so in fad’a miki wani magana, tace toh daddy nima zan fad’a Maka wani magana wanda zai saka farin ciki, yayi dariya tare da fadin mai nene Zeena, tace daddy ka fadamin kafin sai in gaya ma, yace toh Zeena, yayi shuru na wani lokaci can yace Zeena ina so ki zama mai biyayya, sannan ki zama y’a mai bin umarnin iyayenta, tayi dariya tace haba daddy baka taba sani abu naki yima ba, daddy wlh komai kake so indai bai sabama shari’a ba zan yima shi, yaji dadi tare da samun karfin giwa, yace Zeena wa innan mutanan da kike gani sun taru ba dan kowa suka taru ba sai dan ke, taji gabanta ya fad’i, tace daddy dan ni kuma, yace eh, a yau aka daura miki aure, inaso kimin biyayya duk da baki San da auren ba sai yanzu, ta Mike da sauri tare da dafa kirjinta tace aure, ta fara yin baya kaman zata fad’i.
Maryam obam ββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to yasmin darling πππ»
6β£5β£to7β£0β£
Daddy yayi sauri ya riko ta, tare da zaunar da ita akan gado, yace Zeena baki son auren? Tayi shiru babu abunda take sai hawaye, tabbas bana son wannan auren amma taya zan iya kallon daddy ince mai bana so, daddy ya katse ta tare da fadin Zeena kiyi magana nasan ba zaki bani kunya ba, tace daddy Kaine mahaifina baza ka, zaba min abunda zai cutar dani ba, jin haka yace Allah ya miki albarka, yana ta mata godiya, tare da fadin yana alfahari da ita, yace ta tashi ta shirya yanzu za’azo daukanta, ta amsa da toh, sannan ya fita, kuka ta saki mai karfi yanzu na rasa adeel a karo na biyu, a lokacin da muka dai daita, mai yasa haka ya faru dani, jin kaman karar bude kofan d’akin yasa ta goge hawayen fuskanta, ummi ce ta shigo ita da abda, ummi ta zauna ta gefenta tare da fadin Zeena naji dadi da kika yarda da wannan auren kika mana biyayya, yanda kika mana biyayya kema Allah ya baki masu yi miki, ta amsa da ameen, sannan tace abda ta taya ta shiryawa don anzo daukanta, jin haka hawayen da take boyewa suka zubo mata, yanzu wa aka aura mawa ni, Ya zanyi da son adeel, abda tace muje ki shirya, bata musa ba, ta shiga toilet tayi alwala tazo tayi sallah bayan ta idar abda ta taimaka mata ta shirya, ummi da daddy suka kuma shigowa suka mata nasiha akan tabi mijinta tayi mishi biyayya, domin aljannarta yana karkashin kafan mijinta, komai naki yanzu ya koma kan mijinki a yanzu Muda muke iyayenki bamu da iko dake, sai mijinki dan haka kimai biyayya yi nayi bari na bari, babu abunda take sai kuka, ummi ta kama hannunta suka fita falo, a nan yan daukan amarya suka amsheta da yan uwan ummi din akai mota da ita, motocin daukan amarya sun kai hamsin, Zeena kuka take kaman ranta zai fita, abda nata faman rarrashi, hankalinta bai tashi ba sai da taga an kunna mota an fara tafiya, har suka karasa gidan da za’a kaita tana Manne jikin abda, maitama aka kaita wani katoton gida ne suka shiga, gidan ya hadu fadan haduwan gidan ma bata lokaci ne, wata kanwar ummi ta zagayo tace ta sauka da kafar dama tare da bismillah, hakan ko tayi suka shiga cikin gidan, akai sama da ita, cikin wani d’aki aka kaita wanda yaji kayan alatu, wanda suka Kawo amarya suka duba gidan tare da San barka, aka fara shirin tafiya anan hankalin Zeena ya kuma tashi ganin harda abda za’a wuce dakyar ta saki abda suka wuce, aka barta ita daya, tana ta aikin kuka, kanta ya fara ciwo dan taci kuka ta kwanta bata dade ba bacci ya dauke ta.
Wajan karfe goma afraz ya shigo gidan shida wasu abokanshi, yace Su zauna a falo yana zuwa kai tsaye sama ya haura, Ya nufi dakinta ya bude yaga tana bacci, Ya matsa kusa da ita yaga fuskanta ya kumbura da alaman taci kuka, duk sai yaji ta bashi tausayi, ya fita ya kashe mata wutan d’akin, yace ma abokanshi tana bacci bazai kuma iya tashin ta ba, sukace ai dole ma ka tashe ta, yace haba ai tunda ta kwanta sai dai wata rana kun hadu, daya daka cikin abokan mai suna jabir yace inma mu anki taso mana ita ai kai dole ka tashe ta, suka saka dariya sannan ya rakasu suka wuce, bayan ya dawo dakinshi ya nufa ya kwanta amma kwata2 ya kasa bacci, sai tunanin Zeena yake,
Zeena ta farka wajan karfe dayan dare jikinta ya rufeta da zazzabi, ta tashi ta nufi toilet, tayi wanka amma jikin dai sai zafi yake mata, ta kwanta akan carpet din d’akin ta dauko blanket ta rufe kanta tana rawan sanyi,ga yunwa da take ji.
Afraz dai shima ya kasa bacci ya tashi ya nufi d’akin Zeena din ya kunna wutan d’akin ya hangota a kasa tana rawan sanyi, da sauri ya nufeta yace Zeena maike damun ki, jin kaman muryan afraz yasa ta dago da kanta tace afraz, Kaine wanda ka aure ni, bai bata amsa ba, ya dauketa cak ya daura ta kan gadon d’akin sannan yaje ya kashe a.c din d’akin, fita yayi a d’akin Jim kadan ya dawo da cup a hannunshi tea ne a ciki da paracetamol, ya bata taki amsa, ganin haka yasa ya kafa mata kofin a baki, ta fara sha, duka ta shanye sannan ya bata paracetamol tasha, sannan ta kwanta, bata dade ba bacci ya dauke ta, shima a gefenta ya kwanta yana kallonta tare da kara godema Allah daya mallaka mishi Zeena a matsayin mata, ranan afraz kasa bacci yayi, bini2 ya duba Zeena yaga ya take ciki, can yaga jikinta ya fara zufa ya cire mata blanket din, sai wajan karfe biyar ta farka a lokacin afraz ya nufi masallaci, itama toilet ta fada tayi alwala tazo tayi sallah, bayan ta idar ta zauna akan dadduma din, tana tunani yanzu afraz shine mijin da daddy ya zaba min, zan iya kallon afraz a matsayin miji kuwa, wani haushin afraz din taji ya kamata, a lokacin afraz ya bude kofan ya shigo ya ganta kan dadduma yaje kusa da ita ya kira sunanta Zeena bata amsa ba kuma bata d’ago ba, hakan bai dameshi ba yaci gaba da magana ya jikin naki, tace ina ruwanka da jiki na, Malam ka fita ka barni dan Allah, jin haka ya fita dakin shi ya nufa, Ya kwanta, dan jiya baiyi bacci ba.
Tunda adeel ya fita jiya da daddare yaje gidansu wajan alhaji amma yayi rashin sa’a baya nan, sai mahaifiyar shi ya tarar da kannan shi, suka d’an taba fira, mamanshi ta tambayeshi Mysha yace tana gida, tace in gaidaku tace muna amsawa rannan tazo ta wuni a nan ai, yace eyya ya tashi sukayi sallama,
A lokacin daya koma gida yaga Mysha a falo tana gyangyadi, ya matsa kusa da ita wato da bana nan kullum fita kike koh, tayi shuru ya daka mata tsawa bada ke nake ba, tace babu inda naje gidanku kawai naje da gidanmu, yace uban wa yace ki fita, tace kayi hakuri, yace daka yau in kika kuma fita ban sani ba saina bata miki rai, Ya haura sama,.
Wayan shi ya dauka ya kira Zeena amma a kashe hankalinshi duk ya tashi, ya tuna yana da number din zaheer ya kira bugu daya yayi ya dauka, bayan sun gaisa yace mai yakira Zeena number dinta yaki shiga, zaheer yace eh Zeena tana gidanta, yace ban gane ba, zaheer ya fadama adeel abunda ya faru, sakin Wayan yayi tare da zama a kasa, yanzu Zeena tayi aure, kai wasa zaheer yake min, hakan bazai faru ba, Zeena tawa ce, he is joking daukan key din motanshi yayi ya nufi gidansu Zeena din, amma abunda idonshi ya gani ya tabbatar mishi da haka din, ganin motoci yayi da mutane birjik a kofar gidan, Ya tambayi wani a kofar gidan yace mai yar sanata ce take aure yace wacce a ciki, mutumin yace Zeena, hankalin adeel ba karamin tashi yayi ba, ya shiga motarshi yana tuki kwata2 baya ganin gabanshi, bai ma San mai yake yiba, shidai ya farka ya ganshi a asibiti jikin shi duk ansa flasta a jikinshi, yaga alhaji da mamanshi, ga Mysha dake gefe tana ta kuka, alhaji yace sannu adeel ya jikin ya amsa da sauki, kwanan shi biyar aka sallame shi, a asibitin, Allah ya taimake shi babu karaya, sai dai bugawa da yayi a bayan shi.
Zeena tana dakinta a kwance afraz ya shigo d’akin ta daure fuska ya matso kusa da ita ta tashi da sauri ya janyo ta, ta fada kanshi, yace ina zaki, tace ka sake min hannu, yayi dan murmushi tare da kuma janyo ta, suka had’a ido tayi sauri tasa kanta a kasa, yasa hannunshi kan kirjinta ya fara wasa da wajan, ganin haka yasa ta fara kuka, Ya cire hannun shi tare da fadin Zeena plz ki bar wannan kukan, ganin haka yasa ta tashi da sauri tayi wajan toilet, tace afraz I hate you bazan taba sonka ba tana fadin haka tayi sauri ta shige toilet, yayi murmushi ya fita tare da fadin zanyi maganin ki.
Maryam obam ββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to basma darling πππ»
7β£0β£to7β£5β£
Jin karan kofan d’akin yasa ta fito, tare da rufe kofan ta da key, tayi tsaki yanzu wannan ne miji na, ai wlh ba zaka taba samun abunda kake soba a waje na.
Afraz tunda ya fita daga d’akin ta, gidan ya bari gaba daya, bai dawo ba sai wajan karfe tara, a lokacin tana falon kasa tana kallo har ya shigo bata sani ba, ji tayi an rukota ta baya, ta saki ihu, duk ta tsorata, ta bashi dariya amma saiya dake, ta fara kokarin kwace kanta daka rikon daya mata, ya sake ta, ganin haka yasa ta tashi zata gudu ya kuma kamo ta, tace ka sake ni, yai kaman bai jita ba, ya kuma janyo ta, Ya zaunar da ita kan kafanshi, ta daure fuska, ganin shima ya tamke fuska yasa ta kasa cewa komai, yace kinci abinci, ta daga mai kai alaman eh, ya janyo wani leda, ya bata, bata musa ba ta amsa, ta tashi daga jikinshi tayi sauri tayi sama, ya bita da kallo harta bace sannan ya kauda kanshi, yayi murmushi ya rasa wani irin so yake ma Zeena.
Bayan taje d’aki ta bude ledan taga kaza ne da ice cream da abinci, ta bude kazan taci da ice cream, tayi nak, ta fad’a toilet tayi wanka ta fito tana shafa mai, a lokacin ya shigo d’akin ya kura mata ido, ta waiga ta ganshi ta tashi da sauri tare da fadin miye na shigo min d’aki babu neman izini, yayi dan murmushi tare da fadin nida d’akin matata saina nemi izini, ganin yana matsowa yasa tayi shuru, tana matsawa baya, har ta hade da bango, shima ya karasa ya manneta, suna shakan numfashin juna ganin yanda yake kallonta yasa tayi kasa dakai, wani nugun sha’awanta yake ji, wanda bazai iya hakuri ba a wannan lokacin, daukanta yayi cak, ganin haka ta fara wintsil2 amma ko a jikinshi dakinshi yayi da ita, ya ajiyeta a kan gadon d’akin sannan ya rufe kofan, ganin haka ta fara kuka tare da fadin dan Allah afraz karka min komai kayi hakuri, yace Zeena nifa mijinki ne, kuma ina bukatanki, tace bana so bana sonka dan Allah karka min komai, yace bakya sona koh, tace eh, yace owk shikenan bari in kira daddy dinki saiki fad’a mishi ni kuma saina sauwake miki, jin haka tace karka had’a ni da iyayena bana so, yace toh ki bani hakki na, tun daka lokacin bata kuma magana ba, nima ganin haka na fita daka d’akin, na koma da asuba naga Zeena tana ta kuka shi kuma afraz yana ta rarrashi yana bata hakuri, dakyar ya shawo kanta tayi shuru ya kaita toilet yace ta shiga tayi wanka, ganin kaman bata da niyan shiga ya dauketa yasa ta cikin ruwan zafi, ya kura mata ido wani sonta yake kara shiganshi, ganin kallon da yake mata yasa ta kuma sakin kuka, duk ya rud’e yana tambayanta mai nene, tace ka fita, yayi dariya ya tashi ya fita.
Adeel ya yanke hukuncin komawa China da zama domin bazai iya zama a nja ba, yaga Zeena tare da wani mijin, tunda ya tabbatar tayi aure komai nashi ya canza abu kadan, yaita fad’a akai, ga saurin fushi da yake yi yanzu wanda duk bayayi da, itama Mysha ta samu labarin Zeena tayi aure hakan ya mata dadi domin tana ganin yanzu zata samu mijinta, tayi alkawarin ko zuciyan dutse gareshi saiya sota, wannan kenan.
Zeena inta tuna abun daya faru tsakaninta da afraz sai tai ta kuka, yanzu ya rabata da adeel kenan, yayi nasara akan ta, ta tuna lokacin daya mata alkawari saiya mallake ta, gashi yanzu ya sameta, wani takaici taji tare da bakin ciki, tace afraz zaka iya samu na, amma ba zuciya na ba, bazan taba sonka ba,
Afraz tunda ya sami Zeena duk ya daina harkan mata, domin duk yawon barikin da yayi bai hadu da wacce takai Zeena ba, tunda ya sami Zeena yanzu bashi da wani buri illa ace Zeena ta fara sonshi, shine abunda yake fata.
Yau watan Zeena uku da aure, tana zaune a falo, afraz ya fito, ta kalleshi tace ina son magana dakai, yace inaji, tace inaso inje gida yau yace ba yanzu zaki fara fita ba, ta dan marairaice tace plz, yace in kina so kije gida sai kin min kiss a baki, jin haka yasa ta daure fuska tare da kau dakai gefe, yace ok ni na fita ganin zai fita yasa ta tashi da sauri ta shiga gabanshi, yaso yayi dariya yanda yaga tazo da gudu amma saiya dake, ta rufe idon ta, yace ai bani zan miki ba, ke zaki min, ta dan turo baki, ganin yana kallonta tace toh ka daina kallo na, Yayi dariya yace in ban kalleki ba taya zaki min, tayi shuru tana kallon kasa yace ni zan fita in ba zakiyi ba, da sauri tayi mishi kiss din sannan ta ruga da gudu, Ya bita da kallo yana dariya, ya koma ya zauna a falo din, Jim kadan ta fito cikin wani material mai kalan c green ya mata kyau sosai, yace Zeena yanzu haka zaki fita babu mayafi, tace toh ba’a mota bane, yace koma a miye ban yadda da hakan ba, ki koma kije kisa hijab muje, kaman za tayi kuka ta koma ta dauko hijab din, yace kinga yanda kikayi kyau kuwa, ta turo baki, suka fita, wani super market suka je, yace suje tayi musu tsaraba suka shiga ta dauka abubuwan d zata dauka ya biya suka wuce, bayan ya sauketa yace wajan 5 zaizo daukanta tace toh, ta shige, masu gadin gidan yasa suka shigar da kayan tsaraban,Ya wuce.
Da gudu ta shiga cikin gidan ta fada jikin ummi dake zaune akan kujera tana kallo, ummi tace miye haka karki karyani, tayi dariya tace kai ummi bakiyi missing dina ba, tace banyi ba, ta turo baki tare da fadin bari daddy yazo dama shine yake sona, jin haka ummi tayi dariya abda ta fito da gudu sukayi hugging juna, tace wow zee zee dina kinga yanda kika kara kyau da haske, Zeena tayi dariya tare da fadin haba, abda tace dagaske, tun shigowan Zeena ummi ta lura da hakan, tana zargin kaman ciki take dashi, nan suka zauna suna ta fira, har daddy ya dawo shida zaheer, shima daddy yaji dadin yanda yaga yar tashi cikin kwanciyan hankali, wanda ada yake farga akan idan Zeena tayi aure, babu wanda yasan fyade aka mata, amma a yau ya cire ganin yar tashi cikin jin dadi, zaheer yace ya maganan skul dinki tace ina yi ta online, yace ok sai a kara bada himma, tace toh bros,sai bayan magrib afraz yazo daukan Zeena, a lokacin ya shigo suka gaisa da mahaifin Zeena din da ummi, mahaifin Zeena nata sa mishi albarka, ummi tace ma Zeena tazo zata mata magana kafin su wuce, tace toh ta tashi suka nufi d’akin ummi din, ummi tace Zeena ciki kike dashi, tace a’a ummi banda komai, jin haka ummi tabar maganan, tace gaskiya kinyi dacen miji, ji yanda yake kula dake sosai ki rike mijinki dakyau, ada ina fargaban idan kikayi aure duk mijin da kika aura bazai ga darajarki ba, tace ummi kaman ya, nan ummi ta fad’a mata abun daya faru, ta tashi da sauri tace fyade tare da fadin afraz.
Maryam obamββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to my fancy habiba πππ»
7β£5β£to8β£0β£
Ummi tace ki zauna Zeena amma ina tayi hanyan waje, ganin haka itama ummin ta rufa mata baya, falo ta nufa taga daddy shi daya, yace Zeena kije mijinki yana jiranki tun dazu, dan Allah Zeena ki zauna da mijinki lafiya, yaron yana da kirki, wani hawaye ne Ya zubo mata na takaici yanxu idan daddy yasan afraz shine wanda ya mata fyade ya zai dauka abun, tace toh daddy nagode, tayi waje ta sameshi a mota yana jiran ta, da murmushi yace sai yanzu kika fito, ganin tayi banza dashi yasa ya lura da hawayen da takeyi, hankalinshi ya tashi a duniya babu abun daya tsana kaman yaga Zeena tana kuka, yace Zeena mai nene, mai akayi miki, waya taba ki, ganin bata da niyan yi mishi magana yasa yaja motar, tuki yake amma zuciyan shi yana tafarfasa, gani yake kaman an mata wani Abu ne, har suka karasa gida, suna shiga ta fita da sauri ganin haka shima ya bita, yana fadin Zeena Zeena amma ko ta waigo ta kalleshi harta shiga d’akinta, Ya bita shima ya kamo mata hannu yana fadin haba Zeena mai ya faru kike ta kuka, plz ki fad’a min, ta waigo cikin kuka tace afraz wlh ka cuceni ka cuci iyayena sun daukeka mutumin kirki amma basu San ko kai waye ba, na tsaneka bana son ganinka, jin haka duk ya rude yace Zeena maiya faru wai don Allah, tace afraz ka rabani da budurcina kayi min fyade, jin haka yasa gaba daya ya dauke wuta, har d’aci yaji bakinshi yana mishi, ganin yana yinshi yasa ta tabbatar dashi dinne, dakyar ya iya cewa Zeena kiyi hakuri, wlh nayi nadama akan abunda nayi miki, tace afraz wlh ba zaka taba canzawa ba, ka cuceni duk da abun daka aikata sai da kaje ka nemi aurena domin wani manufa naka, yace Zeena wlh na aureki ne tsakani da Allah, Zeena nayi miki fyade ne dan in rama wulakancin da kika min a gaban mutane, amma bayan haka sai Allah ya jarabceni da sonki, Zeena wlh son da nake miki na gaskiya ne bazan iya rayuwa ba tare dake ba, tace afraz ban taba sonka ba bazan kuma taba sonka ba, kana da son kanka ka, kai da kanka kasan ban dace dakai ba, rayuwa na ba kalan naka bane, na tsare kaina amma saida ka tozartani, bazan taba yafe Maka ba, yace Zeena kiyi hakuri nima nasan ban kyauta ba, koda son da nake miki aka barni, nasan wannan babban sakayya ne, ta toshe kunnenta, tace dan Allah ka fita ka barni, yace zan fita Zeena amma dan Allah kibar wannan kukan tace ina ruwanka dani, jin haka ya kama hanyar fita har yazo bakin kofa ta kira sunan shi afraz, Ya waigo tace bazan iya zama dakai ba zan fad’ama daddyna abun da kamin na tabbata bazai barni in zauna dakai ba, jin haka ya matso yana fadin Zeena ki tausayamin ina sonki inna rasa ki, banga amfanin rayuwa na ba, wani jiri takeji yake dibanta tace afraz wlh kaβ¦. Ta fad’i kan gadon d’akin da sauri ya nufeta yana fadin Zeena Zeena duk ya rude ya rasa abun yi, Ya dauketa cak ya nufi waje da ita, cikin mota yasa ta, kai tsaye asibiti ya nufa da ita, aka shigar da ita cikin emergency room,
nan da nan likitoci suka tsaya a kanta Ana ta aune2, afraz ya kasa tsaye ya kasa zaune kanshi keta sara mai, duk wanda ya ganshi yasan yana cikin tashin hankali, Jim kadan Dr din ya fito yace afraz ya sameshi a office, bayan yaje office din Dr din yace mai congratulations your wife is pregnant, afraz cikin murna yace what ciki, you mean Zeena tana da ciki, dr yace yes harna wata biyu, yace zan iya ganinta Dr yace ka barta ta huta, kuma sannan ku daina tasar mata da hankali yanzu jininta ya hau, kasan mace mai ciki bata son damuwa, afraz yace insha Allah, Ya fito sai a sannan ya samu nutsuwa, abda ya kira ya fad’a mata Zeena tana asibiti an kwantar da ita, ta rude tare da fadin maiya sameta, yace karta damu ciki take dashi da murna ta kashe Wayan ta nufi d’akin ummi ta fada mata, ummi tayi dariya tare da fadin ai dama na sani, taje ta fad’a ma daddy yace toh su shirya sai suje, ummi tace in sunje ita zata kwana da ita, daddy yace babu damuwa, hakan ko akayi suka nufi asibitin sun tarar da afraz a reception, ya nuna musu d’akin da aka kaita, suka shiga, kwata2 shi ya kasa shiga d’akin domin a yanzu kunya had’a ido yake da Zeena, koda suka shiga tana bacci bata farka ba, dady da abda suka fito zasu wuce afraz ya raka su, sannan ya dawo dakyar ya daure ya shiga, ganin bata farka ba yayi ajiyan zuciya, ummi tace afraz kaje gida ka huta, ya amsa da toh sannan ya fita,.
Sai wajan karfe biyun dare ta farka taganta a gadon asibiti, ga ummi kuma a gefe tana sallah, abubuwan daya faru suka fara dawo mata, jin muryan ummi tayi tana fadin kin farka Zeena sannu, ta amsa da yauwa, ummi ta had’a mata tea amma tace bata sha, ummi tace ai kodan abunda ke cikin ki kyasha tace ummi ciki na kuma, tace eh tunda yanzu bake daya bace, a nan ne ta gane inda ummi ta dosa, tace ciki nake dashi yanzu cikin afraz a jikina, ummi ta mika mata kofin ta amsa tasha.
Afraz shima daya je gida kasa baccin yayi yana fargaban kar Zeena ta fad’a ma iyayenta, ta gefe daya kuma yana farin cikin zai samu d’a, Ya janyo wayanshi ya kira mum dinshi har sau biyu ba’a dauka ba, Ana ukun ne ta dauka tace afraz lafiya kuwa, yace mum Zeena nada ciki, cikin murna tace wow tana ina, yace tana asibiti, tace gobe zata ita da daddy dinshi, mum din afraz taji dadin wannan labarin zata samu jika, tana son yara sai kuma Allah ya bata kwaya d’aya,
Washe gari afraz tun wajan karfe 7 ya nufi asibiti amma duk sammakon shi, daya je ya tarar da mum dinshi, tana kusa da Zeena tana bata abinci, suka hada ido da Zeena din ta sakar mai Harara, sannan tayi kasa da kanta, yace ya jikin ta amsa da sauki, sannan ya gaida ummi ta amsa cikin fara’a, yace mum ina daddy tace anjima zai zo, mum din afraz tace ma ummi taje gida ta huta zata zauna da Zeena din, babu yanda ummi ta iya dole ta wuce driver din mum din afraz ya kaita gida,..
Kwanan Zeena uku aka sallameta, mum din afraz tace gidanta zata tafi da Zeena afraz bai so hakan ba, amma dole ya hakura, aka wuce da Zeena din, Kwanan ta biyu gidan mum dinshi shima yace ya dawo gidan, yana tsoran kwana shi daya, mum ta Harare shi, tace toh da bakai daya kake kwana ba, yayi dariya tare da Sosa kai, afraz shima ya tare a d’akinshi na gidan, Zeena ta lura da yanda afraz yake zumudi akan cikin, hakan ya mata dadi don tana ganin ta sami hanyan da zata Rama abun daya mata, idan suna zaune mum ta Kawo abinci sai taki ci, tace ta koshi ta lura da hakan yana bata mishi rai, amma idan baya wajan tana ci,
Satin Zeena biyu gidansu afraz, Ya matsa ma mum dinshi akan zasu koma gidansu, dakyar ta yarda aka samar ma Zeena wata yar dattijuwa,mai suna jamila don ta dinga kula da ita.
Tunda suka dawo bata sakar ma afraz, hakan bai dameshi ba, shi abun daya dameshi yanda bata son cin abinci, yana zaune a falo jameela ta haura sama da abinci, sai gata ta sauko dashi, yace wannan ba abincin Zeena bane tace eh tace bata ci, ranshi ya baci yace mai taci, jameela tace babu abunda taci, Ya amsa abincin ya haura sama rai a bace, tana zaune akan gado tana game a wayanta, Ya shigo cikin fushi ya fisge Wayan tare da mika mata abincin, yace Zeena wannan wani irin abune ni na miki laifi a kaina zaki rama ba akan yaro na ba, wanda bai San komai ba, zan iya juran komai amma bazan jura wannan ba, ko kallo bai isheta ba, yace Zeena ki amsa wannan abincin kici, taki amsa babu yanda baiyi da ita ba, amma taki amsa, ganin haka ya fita rai a bace Jim kadan sai gashi da ummi, ummi tama Zeena ta tas, tace da badan kina da ciki ba wlh dazai nayi mugun bata miki, babu shiri ta dauki abincin taci, ummi tace ma afraz ai duk shine yake mata wasa sai yasa take iskanci, ummi ta wuce, afraz ya dawo tana ganin shi ta saki kuka, nan ya zauna yana ta rarrashi.
Maryam obamββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to my fancy habiba πππ»
8β£0β£to8β£5β£
Adeel yana kwance a bedroom dinshi, Mysha ta shigo da plate dauke da kayan fruit a ciki, ta ajiye mai a gefe, tace adeel ka tashi kaci, ya amsa da toh, ya tashi ya faraci ita kuma ta koma gefe tana kallonshi tana murmushi, ci kawai yake amma yana tunanin Zeena ya rasa mai yasa kullum son Zeena yake kara karuwa a ranshi, duk yanda yayi kokarin ya cireta a ranshi amma abun yaki, wani zubin har tausayin Mysha yake yanda take bashi kulawa sosai amma bai taba jin sonta ba, tunda suka zo China ya dan sakar mata, domin yana tsoran kar Allah ya kamashi da hakkin ta, itama kanta tasan ba sonta yake ba, tasan Zeena yake so, sai yasa har gobe take jin haushin Zeena, kuma take kishi da ita.
Afraz tunda Zeena ta sami ciki kullum Ana gida Ana kula da ita, baya zuwa ko ina, daka tayi motsi kadan yace miye, ganin haka yasa da gangan ma sai tayi abu, shi kuma sai ya rude yaita tambayanta mai nene, mai kike so, tace wannan tace wancan sai ya Kawo tace bashi ba, ga abunda take so, haka zai koma ya nemo mata, inya Kawo kuma tace ta koshi, haka kullum suke,
Zeena tana kwance a d’aki, tana tunanin yanda zata Japan, tana tunanin dakyar afraz ya barta, jin karan bude kofan da yayi ne yasa ta rufe ido kaman mai bacci, ya zauna akan gadon kusa da ita, yasa hannunshi a bakinta yana wasa dashi, ta dan bude ido daya, suka had’a ido yayi dariya tare da fadin har kin tashi, ta dan turo baki tare da fadin mutum yana baccin shi, Kazo kana damu na, yayi dariya tare da fadin ai ba zaki iya bacci ba in ina kusa, ta daure fuska tare da turo baki, yayi dariya yace idan kina fushi kinfi kyau, ya Mike bari inje in dawo, tace afraz ya amsa da na’am tace exam din mu a Japan kasan dole inje, yayi shuru can yace bari in dawo sai muyi maganan, tace toh har ya kusa fita tace ina zaka, da mamaki yake kallonta wannan ne karo na farko data taba tambayan shi ina zashi, hakan ya mishi dadi yace zani wajan budurwana ne, abun ya bata mata rai amma sai ta dan dake, duk yanda ta dake saida fushin ya fito, yayi dariya yace ashe Ana sona, ta sakar mishi Harara, ya fita yana dariya,
Tunda afraz ya fita ta kasa zaune ta kasa tsaye yanzu afraz dagaske tad’i zaije, wani bakin ciki taji ya taso mata, tayi tsaki inma yaje tadin ni ina ruwana, wata zuciyar tace da ruwanki mana mijinki nefa, ta dauki wayanta ta kira shi, bai dauka ba, ranta ya baci ta kuma kira bai dauka ba, ta zauna tana huci, ya bude kofan d’akin ya shigo ta sakar mai harara, yace bakiyi bacci ba, wani haushi ya kamata ya zauna a kusa da ita tare da fadin ance in gaidaki, ta daure fuska tace ka fitar min a d’aki, yace haba Zeena daka fadan sako ki bari in baki labarin abunda ya faru jin haka yasa ta fara mishi kuka, yace Zeena kin San ban San wannan kukan naki plz kiyi shuru, ya janyo ta ya kwantar da ita kan kirjinshi, yace Zeena ke bakya sona dan nace naje tadi shine kike kuka, ta kuma sakin kukan ai dole kaje tadi tunda ni ka cuceni kamin ciki shi yasa kake min haka, yaso yayi dariya amma saiya dake, yace haba Zeena ba haka bane so nake in Kawo miki wacce zata dinga taya ki aiki, tace bana so ai inada jamila, inma mutum daya yayi kadan ko masu aiki nawa ne ummi zata iya Kawo min, yayi dan murmushi najin dadi ya tabbata yanzu Zeena ta fara sonshi tunda har ta fara kishin shi, yace ni ban cika son masu aiki ba kinga idan ko matata ce zata fi kula dake, a matsayinki na yayarta, tace Allah ya kiyaye in zama yayarta taje ta nemi yayarta bani ba, ta tashi daka kan kirjin nashi cikin fushi, yace come on Zeena ina zaki kin San ban San fushin ki, tayi banza dashi, ganin haka yace kin San banso inga kina damuwa kar kisa babyna shima cikin damuwa, tace wato wannan bata ni yake ba, ta baby dinshi yake ba, ta kwanta ta baya tare da juya mishi baya, abun ya bashi dariya shima ya kwanta ta gefenta,.
Zeena yanzu indai taga afraz ya fita toh haka zata zauna cikin fushi da kunci, taita tunanin ya fita tad’i ne, shi kuma afraz din yana mata hakan ne don yaga ko tana sonshi, ya fito cikin kananan kaya ya mishi kyau yana ta kamshi, ya kalleta yace Zeena nayi kyau kuwa, ta kauda kai gefe, yayi dariya tare da fadin plz ki fad’amin in banyi kyau ba, in canza kaya kar inje tad’i taki fitowa, tayi tsaki tare da tashi ta haura sama ya bita da kallo yana dariya, Jim kadan sai gata ta fito dauke da key din mota a hannunta, yace ina zaki tayi banza dashi, ya tare ta, ta saki kuka tace ni ka matsa min in wuce gidan mu, yace haba Zeena akan wani dalili zaki gida, jin haka tayi shuru ya kuma tambayanta tayi shuru, ya kamo mata hannu yace zo muje na fasa fitan, jin haka yasa taji dadi harta yarda suka koma ciki.
Adeel yana office amma duk ya kasa komai, yana tunanin Zeena wanda ya zaman mishi aiki kullum, ya lumshe ido tare da fadin Zeena Allah ya jarabce ni da sonki, na rasa yanda zanyi in cireki a raina, na kasa yarda da na rasa ki, kullum zuciya na tana yaudara na, akan ban rasa ki ba, karan wayanshi ne ya katse shi, ya dauka yaga Mysha ce, yayi dan tsaki sannan ya dauka, tace adeel yaushe zaka dawo ina so muje hospital inga Dr, yace anjima tace toh sai Kazo bai bata amsa ba ya kashe Wayan,.
Afraz yace ma Zeena ta shirya suje Japan din,ta hada kayanta sukaje suka ma kowa sallama, washe gari suka cala harda jameela, wani gida suka sauka, gidan duk da bashi da girma sosai amma ya hadu, afraz yana ba Zeena kulawa sosai, ita da kanta yanzu ta yarda tana son afraz, amma ta kasa nuna mishi, bata san ya Riga ya ganota ba, satinsu biyu suka dawo Nigeria, afraz yayi siyayyan kayan yara sosai na mata da maza, d’aki daya aka ware aka shirya komai yasa ansa na mace dana miji, yace duk wanda aka haifa ga kayanshi nan.
Cikin Zeena yakai wata takwas, amma inka ganta zaka ce haiyuwa yau ko gobe ne, don cikin yayi girma sosai, afraz yace in kika haifi mace sunanki zan sa Zeena, tayi dariya tace saboda me, yace Zeena saboda ina sonki, kullum sonki kara karuwa yake a raina, tayi dan murmushin jin dadi, yace amma ni har yanzu ba’a sona, ta dan turo baki suka hada ido tayi sauri ta kawar da kanta gefe, yayi dariya yace idan namiji kika haifa sunan wa zaki sa, tace ka bari saina haiyu sai in fad’ama, yace shikenan Allah ya kaimu wannan ranan Zeena, ji nake kaman yanzu inga kin haiyu, ki haifar min mace mai kama dake, tayi dariya tace in namiji ne kuma yayi kama dakai, ya kalleta yace Zeena kina son ki haifa mai kama dani tace eh, a ranta tace afraz kana da kyau, inna haifa mai kama dakai ba karamin kyau zaiyi ba, nan suka zauna suna ta fira cikin so da kauna, aka kira afraz a waya ya dauka tare da fadin gani nan zuwa, bayan ya kashe yace Zeena bari inje in dawo, tace ina zaka yace wasu kaya dana bada oder dinsu aka Kawo, tace daka bari gobe mana afraz yace bazan dade ba ta dan turo baki, yayi dariya tare da fadin Zeena say you love me, ta turo baki yayi dariya sannan ya fita, ita dai bata so wannan fitar ba, dan yanzu bata son afraz yana nisa da ita.
Tunda afraz ya fita har wajan karfe goma bai dawo ba, duk ta rud’e, ta kirashi baya shiga, hankalinta ba karamin tashi yayi ba, ta fito falo ta zauna, taji ana buga kofan falo din da sauri ta nufi falo din tare da fadin sai yanzu ka dawo koh, amma abunda ta gani yasa ta tsorata police ta gani guda biyu, suka ce kece matar afraz koh, ta amsa da eh, sukace yayi accident a halin yanzu yana asibiti, tace innalillahi wa inna’ilaihira jiun, da sauri ta koma ta dauko hijab tabi su, kai tsaye asibitin suka nufa, a lokacin suma su mum din afraz din suka zo da daddy dinshi, Zeena ganin yana yin afraz yayi mugun bata tsoro, duk jikinshi ansa flasta kuka take kaman ranta zai fita, tana fadin afraz saida nace karka fita amma kaki, mai yasa ka fita afraz, yayi mata dan murmushi yana son yin magana amma ya kasa, tace afraz ina sonka, yayi murmushi a dai2 lokacin oxygen din da aka samai ya tsaya.
Maryam obamββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to my fancy habiba πππ»
9β£0β£to9β£5β£
A lokacin da dady din afraz yazo asibitin yaga yaran, yace namijin Sak afraz a lokacin yana yaro, ya tambayi Zeena akan wani suna take so a musu huduba dashi tace asa ma namijin afraz, mumy sai da tayi hawaye don jin dadin sunan, macen kuma tace asa sunan mumy din afraz, jin haka mum din tace a’a marigayi ya taba fad’a mata indai ya haifi mace sunan matarshi zai sa, jin haka yasa Zeena ta saki kuka mum ta rarrashe ta tayi shuru, anyi ma macen huduba da Zeena, tana ta samin sauki kwananta biyar aka sallameta daka asibitin suka koma gida, tana ta samun kulawa wajan mumy din afraz, idan ta zauna taita kallon yaran tana jin sonsu na shiganta, tana fadin ina ma afraz yana nan yaga yaranshi, wani hawaye mai zafi yake fita daka idonta, idan mumy ta sameta cikin wannan halin taita mata nasiha akan ta daina sa damuwa karta jama kanta matsala.
Yau juma’a kuma ranan sunan Zeena da afraz, mutane sun taru sosai an hada gagarimin biki, mum ba karamin kudi ta kashe ba wajan siyayyan kayan yara, itama ummi din Zeena tayi siyayya sosai, Zeena babu abun da take sai kuka, har ummi tayi fushi da ita, tana ta fad’a yau ranan suna amma kin zauna kina ta kuka, sai kiyi tayi, mum tace haba ummi aiba fad’a zakiyi mata ba, ai ba’ama yaro haka, tace yi shuru Zeena kinji ki daina wannan kukan, ganin yanda mum take rarrashin Zeena yasa abun ya bata haushi tace aiki ya ganku, ita kuma Zeena tana kuka ne tare da aiyana wa dama mijinta yau yana raye yaga wannan ranan, da wani irin taro zai had’a inta tuna hakan sai taita kuka, anyi suna kowa ya watse duk wanda yazo sunan yaga yaran sai yaji kaman ya wuce dasu dan kyau.
Mysha tana zaune da dan cikinta na wata Bakwai, adeel yana ta mata hidima, duk abunda tace shi yake mata, don adeel Allah ya yishi da son yara, duk ya tare gida wajan kula da Mysha don yana burin shima yaga danshi na cikin shi, itama ganin yana son cikin yasa take amfani da daman take kara tusa mishi kanta, kuma babu laifi yana biye mata, ba kaman daba,
Zeena tana zaune tana karatu ta cikin system dinta afraz da small Zeena suna ta wasa, yaran yanzu watan su goma sai wayau, gashi basu da kiriniya, harta nono bai dame suba, ganin haka yasa aka fara basu abinci, a lokacin da suka cika shekara daya da wata biyu ta yaye su, a lokacin suka shirya tafiya umra ita da yaranta da abda, sunje umra sun gama aikin su, suna ta yawo suna siyayya yawanci siyayyan duk kayan yaran ne, sun fito daka wani shagon kayan yara a lokacin Mysha da adeel suka zo shiga shagon suma, tare da yaransu wanda adeel ya rike a hannunshi, ganin Zeena yasa ya tsaya ita kuma Mysha ta daure fuska ta shiga cikin wajan tare da fadin sai dai ka kalleta amma tama nisa tunda tayi aure, Zeena ta bita da ido da mamaki, ya matsa da murmushi yace Zeena kece a nan tace eh, abda ta gaida shi, ya amsa da fara’a, yace yaranki ne wa innan abda ce ta bashi amsa da eh, ya kamo hannun small Zeena yace wow so cute, ganin haka shima afraz ya matsa kusa dashi yana dariya, yaji yaran sun birgeshi, ya aiyana dama ace yaran shine, yace ina dad dinsu fa, dukansu sukai shuru Zeena tayi gaba, yace ma abda ya naga kinyi shuru tace dad dinsu ya rasu, yace INNALILLAHI’WA INNA’ILAIHIRA JIUN, nan yama abda gaisuwa sannan yace ta bashi number dinta zai kirata yama Zeena gaisuwa ta amsa da to ta bashi number dinta na nigeria don gobe zasu wuce,ta kama hannun yaran suka wuce suna ta mishi bye2 shima yana musu, harga Allah yaji mutuwan mijin Zeena ya kuma tausaya mata tare da yaranta,
A lokacin daya shiga cikin shop din yaga Mysha tana cika tana batsewa, tace kai abun da kayi kana ganin ka kyauta kenan, dan wulakanci kaje ka tsaya kana musu magana, ni ka shareni ina jiranka a nan, ya daure fuska tare da fadin na tsaya kiyi abun da zakiyi, ya juya tare da fadin in kin gama abun da kikeyi ki sameni waje, wani bakin ciki ne Ya kamata tare da tsanan Zeena,.
Ranan adeel kasa bacci yayi daka ya rufe ido Zeena yake gani,tare da yaranta wanda yaji yana matukar so, yaran abun burgewa, toh amma mai yasa Zeena ta kasa tsayawa su gaisa ma dakyau, take ta daure fuska, Mysha tace inafa ta magana kayi banza dani, ya d’aga kai yace inaji, tace daka nan zamu dubai dinko, yace no Nigeria zamu wuce, tace Nigeria, da mamaki take mai tambayan, yace eh, jin haka yasa ta zauna tare da tunanin mai zai kai adeel Nigeria, bayan babu zuwa nja a tsarinshi yanzu, kai akwai wani abu, haka ranan dukansu suka kwana tare da tunani ita da adeel din,.
Su Zeena sun koma gida, ita Zeena tunda mijinta ya rasu take zaune wajan mum din afraz din, yanzu haka ma gidansu afraz din suka sauka, abda ita ta wuce gida, kwanansu biyar da dawowa adeel suma suka dira a Nigeria, an gyara musu gidansu, a nan suka sauka, a ranan ya kira abda ta dauka bayan sun gaisa yace ina Zeena, tace tana gidan iyayen mijinta, anan take yanzu, yace a ina kenan, ba tare da wani abuba abda ta fada mai gidan yayi godiya tare dayi mata sallama,
Washe gari adeel ya nufi gidan, ya samu masu gadin gidan yace yazo wajan Zeena, suka cemai injiwa zamu ce, yace adeel kace mata nazo yi mata gaisuwa, jin haka suka bude mai gate din ya shiga gidan, a lokacin Zeena da mum suna falo suna fira, mai gadin yayi sallama bayan sun amsa yace Ana sallama da Zeena taji gabanta ya fadi tace waye yake nema na, yace wai adeel yazo miki gaisuwa, tace kaje kace bana nan, Jin haka mum tace mai gadin yace tana zuwa ya amsa da toh ya fita, mum tace waye shi, tayi shuru can tace wani friend dina ne, mum tace haba Zeena shine ba zaki fita ba, ai babu kyau wulakanci, maza ki tashi kije, ta amsa da toh badan ranta yaso ba, ta dauki dogon hijab tasa sannan ta fita, ta sameshi cikin mota ta zagaya ta inda yake ta tsaya yayi dan murmushi shima ya fito daka motan, yace Zeena ya gida ta amsa da lafiya, sannan ya mata gaisuwa ta amsa data gode, ta fara tafiya yace haba Zeena ina zaki muna magana, tace gida zan shiga, tunda kamin gaisuwa din, yace Zeena wai mai yasa kike haka ai ya kamata ki Kawo min yaran mu gaisa dasu, ta daure fuska tare da fadin toh, ta shiga cikin gidan ya bita da kallo, Jim kadan sai gata ta fito tare da yaran, ta tsaya ta gefe yana ma yaran wasa suna ta dariya gasu da baki suna ta mai surutu yana dariya ya dauko leda guda biyu ya basu suka amsa suna murna, ya kalli Zeena da tasha mur yace to ni zan wuce sai wani lokacin, ta amsa da toh an gode, ta kama hannun yaran suka fara kuka ganin adeel zai wuce.
Maryam obamββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to my fans πππ»
8β£5β£to9β£0β£
Shima komai nashi ya tsaya, ganin haka ta fara girgiza shi, tana fadin afraz, dr ya shigo da sauri yace Su bashi waje, nan ya fara yan dube2 amma ina rai yayi halinshi, Zeena ta bude kofan ta shigo da sauri itama mum ta biyo ta, tace Dr ya tashi, dr yace sai dai kuyi hakuri Allah ya mishi rasuwa, Zeena ta saki dariya tare da fadin no afraz bazai mutu ba, ta matsa kusa dashi tana fadin afraz ka tashi ka karyata wannan Dr din, nasan ba zaka mutu ka barni ba, get up afraz, taja hannunshi taga yayi nauyi, ta saki ya fadi sharaf, ta saki kuka afraz why mai yasa ka tafi a lokacin da nake bukatan ka, afraz saida sonka yamin yawa sannan zaka tafi ka barni, ka tashi your unborn child is waiting for you, ba haka mukai dakai ba afraz ka tashi ta fara girgiza shi, mum dinshi ita Suman tsaye tayi ta kasa ko motsi, a dai2 lokacin dad dinshi shima ya shigo cikin rudewa ganin afraz din yasa ya tabbatar ya rasu, hawaye ke zuba a idonshi, ya matsa kusa da matarshi wanda ko digon hawaye yaki ya zubo mata a ido, gaba daya ta shiga cikin d’imuwa, Zeena ta taso da sauri tace dad kace ya tashi, yace Zeena kiyi hakuri afraz bazai tashi ba, addu’a kawai zamu mai, tace dad afraz ya mutu dagaske, yace eh Zeena ta fara baya2 tana fadin no no he will not die and leave me lokaci daya jiri ya dauketa ta fadi kasa, da sauri dad din afraz ya fita ya kira Dr, nan da nan aka fara dubata, shi kuma afraz aka daukeshi akai gida dashi da safe za’a kaishi gidanshi na gaskiya, labarin mutuwan ya baza ko ina, su abda suma sun zo asibitin, ita zauna da Zeena ummi kuma tana gidansu afraz din, kwata2 hawaye yaki zuba a idon mum sai zuciyanta dake faman buga mata, ummi tana ta mata maganan da zata danji sanyi, kiyi hakuri duk mai rai mamaci ne, kar ki zama mai butulci a lokacin da Allah zai baki shi bai fad’a miki ba, har kika sameshi kika nuna farin cikin ki, yanzu Allah ya dauki kayanshi sai ki zama mai hakuri duk son da kike mai Allah yafi sonshi, sai a sannan kukan yazo mata tace shine daya dan dana haifa yau na rasa shi, don me bazan damu ba, afraz shine komai nawa shine kwai na dana mallaka yau na rasa shi, mutuwa mai yasa baki daukeni ba, ummi ta to she mata baki, tare da fadin kar kima Allah butulci karki manta rayuwa akwai mutuwa kuma koda afraz bai mutu yanzu ba zai mutu wata rana, ki zama mai hakuri da dan gana, a yanzu babu abun da afraz yake so sai addu’a wannan kukan bashi da amfani, tayi shuru tare da fadin haka ne, ta tashi da sauri ta nufi dakinta sai gata da alkur’ani ta matsa kusa da inda aka ajiye afraz din ta fara karatu tana kuka,
Zeena wajan karfe hudu ta farka, ta bude idonta tare da fadin afraz ta tashi zaune, taga ansa mata drive, ta tsige abun ta tashi da sauri, jin kaman motsi yasa abda ta farka taga Zeena na kokarin bud’e kofa da sauri ta tashi tace Zeena ina zaki, tace abda ina afraz, tayi shuru, tace abda dagaske afraz ya rasu, abda tace Zeena kizo ki zauna, tace no ta bude kofa ta fita abda ta rufa mata baya tana kiranta ganin bata da niyan tsayawa yasa ta koma da sauri ta dauki jakanta ta fito bata ga Zeena din ba, da sauri ta shiga motarta, tayi waje ta hangota tace ta shigo suje, babu musu ta shiga, gidan su afraz din suma suka nufa, sun shiga falon gidan sunga ummi da mum suna ta karatu gefe kuma afraz ne kwance an rufe shi, da sauri ta karasa wajanshi ta bude shi, taga fuskanshi kaman mai yin bacci, tace afraz mai yasa kamin haka ka tashi in fad’ama abun da kake so kaji, afraz ina sonka ina sonka afraz, baby dinka yana son ya rayu dakai plz ka tashi kar ka maida baby dinka maraya, ummi ta matso kusa da ita, tace Zeena ta rungume ta, tana kuka ummi afraz ya tafi ya barni, saida nace karya fita ummi amma yaki, inda bai fita ba da hakan bai faruba, ummi tace Zeena kiyi shuru ki daina fadin haka koda bai fita ba indai kwananshi ya kare bazai kara koda kwana daya ba, tace ummi bazan iya rayuwa ba tare da afraz ba ummi ina sonshi ummi mai yasa haka yake faruwa a kaina, ta kuma sakin kuka, ummi tace ta daina kuka tamai addu’a ne, ta matsa kusa dashi tana tamai addu’a tana kuka, duk wanda yake wajan saida ya tausaya mata.
Mutane sun taru a kofar gidansu afraz din sosai daka gari2 mutane keta zuwa, anyi mishi wanka an mai sutura dama an barshi sai wajan 8:30 za’a kaishi gidanshi na gaskiya hakan ko akayi, a lokacin da aka dauko shi Zeena kuka take kaman ranta zai fita, ta kankame gawan, dakyar aka banbare ta, aka wuce dashi, rayuwa kenan, afraz yayi mutane sosai, Allah yasa mu cika da imani,
Ana ta zuwa musu gaisuwa kota ina, Zeena kwata2 taki cin komai, anyi2 taki ci, saida mum din afraz tazo da kanta sannan ta yarda taci, shima ita take bata a baki, ci kawai take amma bata jin dadin komai, inta kalla cikin ta saita fashe da kuka, tana fadin afraz ka tafi baka ga baby dinmu ba.
A yau akayi addu’an uku, mutane kowa ya watse, an barsu su kadai, ciki harda ummi wanda tun da akayi rasuwan itama tana gidan ita da abda, yanzu daka Zeena sai mum din marigayi afraz da dad dinshi, suka rage a gidan sai masu yi musu hidima, Zeena duk ta rame tayi baki kullum tana cikin hawaye, mum taita bata baki akan tayi hakuri ta rage damuwa ba ita daya bace, inta kiyin shuru saita ce mata da afraz yana nan ba zaiji dadin wannan kukan ba, inta ji hakan sai tayi shuru.
Wata ranan juma’a da yamma Zeena tana zaune tana karatun alkur’ani mum ta shigo d’akin ta zauna a gefe, Zeena ta saki kara tare da fadin ciki na, mum tace Zeena sannu tashi muje asibiti, ta kira daya daka cikin masu aikin gidan suka kama Zeena din aka sata a mota sukai asibiti da ita, tana ta faman fadin ciki na, nan da nan akai labour room da ita, mum ta kira ummi ta fada mata bata dade ba tazo, tare da abda, sun dauki wajan awa uku amma shiru babu labari sai azaba da Zeena din kesha, akace dole sai an mata operation domin ba zata iya haiyuwa da kanta ba, suka ce sun yarda ayi, nan da nan likitoci sukayi kanta aka fara aiki, su ummi babu abun da ake sai addu’a, wajan karfe goma da wani abu Dr ya fito yana murmushi tare da fadin congratulations an sami twins, baby girl nd baby boy, mum ta d’aga hannu tana ma Allah godiya, suka cewa Dr din zasu iya shiga yace eh, da sauri suka nufi dakin, Zeena tana kwance yaran na gefe, babu abun da take sai hawaye, mum ta dauki yaran duka yaran kaman afraz kaman an tsaga kara, kaman yayi yawa sosai, mum itama ta fara hawayen tace Allah sarki afraz, Allah yaji qanka, ummi tace Zeena ki daina wannan kukan, tace ummi naso afraz yaga wannan ranan inga wani irin murna zaiyi, ya dade yana burin zuwan wannan ranan, ta kuma zubo da wani hawayen wani son yaran taji yana shiganta tare da tausaya musu.
NOTE: masu cewa afraz bai kamata ya mutu ba, inya mutu novel din ya baci, kufa tuna Allah baya barin wani dan wani yaji dadi, kuma karku manta duk mai rai mamaci ne. Rayuwa akwai mutuwa akwai tsufa kar ko da yaushe mu dinga mantawa da mutuwa, duk da novel ne wannan ya kamata mu dinga sawa akwai mutuwa a ciki ba kullum ace sun kasance tare cikin jin dadi da kwanciyan hankali ba, indai akace kullum haka ne Ya zama babu amfani rubuta littafi tunda ana mantawa da mutuwa ya zama shirme, sau da yawa ina rubuta akan abun da yake faruwa ne, Allah yasa mu dace
Maryam obamβββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to aysher likymo πππ»
9β£5β£to1β£0β£0β£
Ganin haka yasa yace kar suyi kuka zai dawo, yaja motarshi ya fita, ganin ya fita din suka saka kuka, ta fara rarrashin su, har Suka shiga ciki, mum tace mai aka musu, tace kawai daka sunga zai tafi suke wannan kukan, tace aiya yaro kenan ta tashi ta janyo jikokin nata ta fara rarrashinsu, sukayi shuru suka mika mata ledan daya basu, su chocolate ne dasu biscuit, kalan na waje dinnan sune kala2 a ciki, mum tace harda tsaraba dole kuyi kuka dan zai tafi, Zeena ta danyi murmushi,.
Bayan Zeena ta shiga d’aki ta kwanta yanzu twins wajan kakarsu suke kwana, ita a yanzu adeel baya cikin tsarin rayuwanta tunda ta rasa mijinta ta cire komai a ranta, take ganin ba zata iya kara kallon wani namiji ba da sunan so ko aure ba, yayanta ma sun isheta rayuwa, wannan abun Zeena tasa a ranta.
Adeel tuki yake amma yana ganin Zeena, ya rasa wani irin azababban so yake mata, ga yaranta wanda suka shiga ranshi jinsu yake kaman yaranshi, har yakai gida yana wannan tunanin, a lokacin daya shiga cikin falon gidan yaga Mysha tana cika tana batsewa, yace ina ahmad, tayi banza dashi, ganin haka yace ba dake nake magana ba, tace na kaishi gidan mu, ya daure fuska tare da fadin bana hanaki fita ba, ba tare da izini na ba, ta yamutsa baki tare da fadin duk ka gama abunka fita ne dai sai nayi, dama tunda naji kace mu dawo nja nasan akwai dalili, dama mijin waccen yar iskan ne Ya mutu wato shine ka dawo ka jajubota, toh wlhβ¦.. Saukan mari taji, ta rike wajan tana hawaye, yace ki dinga sanin abunda zaki fad’a akan Zeena, domin Zeena ta fiki itace macen da nake so kuma har gobe nake burin aure, darajan Zeena din kikeci shi yasa nake jure duk wani abu naki nake zama dake, inda badan ita ba, dana dade da rabuwa dake, tace adeel akan wata mace kake fadamin haka, ta shige dakinta da gudu tana rusa kuka, yayi tsaki ya kuma barin gidan.
Tunda Mysha tasan Zeena bata da aure, ta shiga cikin damuwa, ta takura ma adeel akan su koma China amma yaki, yace mata ya dawo kenan, haka suke zama kullum ita bata jin dadinshi shima baya jin dadinta, duk abubuwan da takeyi mai da dan yaji dadi duk ta daina, kullum sai mita, inya gaji ya bata waje, shi yanzu babu abunda yake damunshi illa ace yau ya sami Zeena.
Zeena tana falo suna wasa da twins saiga mai gadi nan yayi sallama ta amsa sannan ya shigo, yace gashi wai inji adeel yace abama twins, leda ne manya2 guda uku, ta amsa tare da fadin kace angode, yace aiya wuce, ta amsa da toh, mum ta fito tace a’a wa innan kayan fah, tace adeel ne yace a Kawo masu afraz, mum tayi dariya tare da fadin Allah sarki baya gajiya da hidima, tunda yazo mata gaisuwa bai kara zuwa ba, sai dai yaba mai gadi kaya ya Kawo ma yaran, mum ta bude ledan taga kaya ne masu tsadan gaske ya siyo da takalmi masu kyau, mum ta kalli Zeena tace ya kamata dai nima in mishi godiya, Zeena tayi shuru bata ce komai ba, mum tana son duk wanda yake son jikokinta bata iya boye son su ako ina, ko ‘kuda bata so ya taba mata su, sai yasa bata cika son suna fita sosai ba.
Adeel ya yanke hukuncin turawa wajan iyayen Zeena, don wannan karan dagaske yake, bazai bari ya kuma rasa taba, hakan ko akayi iyayenshi sunje sun sami dadyn Zeena sun mai magana, yace Su bashi dan lokaci kadan zai kirasu sukayi godiya tare da sallama, a lokacin daya je, gida ya sanar da ummi, a lokacin zaheer yana wajan, yace ma dady ai Zeena tana son adeel domin kuwa a ranan da suka dawo da maganan zai turo ta dawo, sai kuma ta tarar da ana bikinta, dady yayi shuru tare da tuna lokacin tabbas Zeena tace tana son fada mai magana, duk sai yaji tausayinta ya kamashi, yace Zeena kin min biyayya kin auri mijin dana baki, ya aiyana a ranshi akan wannan karan zai cika mata burinta ya aura mata adeel.
Dadyn Zeena Yama mahaifin afraz bayani yayi na’am da abun yace dama ya kamata tayi aure, a lokacin da Dady afraz ya fada mum din afraz yanda sukayi da mahaifin Zeena ba karamin dadi taji ba, nan ta fadama dady irin hidiman da adeel yake ma twins, shima yaji dadin hakan, dady yace yasan baban Yaron sosai dan gidan mutunci ne,.
Dadyn Zeena ya kira magabatan adeel ya fad’a musu akan su turo ayi komai, sunyi godiya sosai, cikin kwana uku suka Kawo komai da komai da ake bukata, duk wannan abun da akeyi Zeena bata San wainar da ake toyawa ba,
Adeel yasa anci gaba da gina mai gidanshi, wanda da ya tsaya, ya tafi China, yanzu anci gaba da gina gidan a ciki yake son saka matanshi dan yace wanda suke ciki yayi karami, ummi ta kira mum tace Zeena tasan da batun auren kuwa mum tace a’a bata sani ba, ummi tace mum ta fada mata, tace shikenan, hakan ko akayi Zeena tana zaune a d’aki tana karanta wani littafi mum ta shigo tace Zeena ina son magana dake, tace to mum, tace Zeena ansa bikinki keda adeel nan da wata biyu, tace what mum aure, mum tace eh, tace dan Allah mum kar kumin haka babu aure a tsari na ta saki kuka, mum tana ta rarrashi tace kiyi hakuri Zeena ba zaiyu mu barki haka ba, dole kiyi aure Zeena, tace no mum bazan iya auren kowa ba mum, bana son yin aure mum, jin haka taba mum din tausayi tasan duk macen da mijinta ya rasu yawanci ana samun irin wannan matsalan kafin su sake aure, tace kiyi shuru Zeena in bakya so babu mai miki dole, jin haka yasa tayi shurun,
Mum ta kira ummi washe gari ta fada mata Zeena bata son auren, ummi tace zata zo ta sameta suyi magana, ko awa daya basuyi ba ummi tazo, ta sami Zeena din tace miye dalilin ta nakin auren tace ummi kawai banso inyi aure ne, jin haka ummi tace toh bari kiji ko kina so ko bakya so sai kinyi wannan auren, so kike mu ajiye ki kita zama a gida babu aure to gwara ma ki canza tunani, babu abun da take sai kuka, har ummi ta gama ta fita, mum tana ta bata baki har tayi shuru, ta dai yanke wannan karan ba zata bari a mata dole ba, domin yanzu ta cire shi a tsarinta.
Maryam obamββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to my fans πππ»
1β£0β£0β£to1β£0β£5β£
A lokacin da ummi ta koma gida tama dady magana akan a daura auren nan da sati biyu, in yaso saita tare daka baya, dady yace akan wani dalili kuma, bayan an tsaida rana kuma yanzu a canza, ummi tayi shuru bata kuma cewa komai ba, jin haka dady yace akwai wani matsala ne, tace a’a babu, naga kaman ansa lokacin ne yayi yawa, dady yayi shuru can yace ai kaman yanzu ne, zaki ga yayi, abda ta shigo falon da fara’a a fuskanta, ummi tace anyi nasara kenan, tayi dariya tare da fadin eh ummi, ta mika ma ummi takardan tace lallai abu yayi kyau, dady tace mai nene, ummi tace waec din tane, yace har ya fito, yanzu sai shirin zuwa high instuition kenan, tace eh dady, tana dariya, nan suka zauna suna ta fira cikin sha’awa,.
Tunda ummi tazo gidan tama Zeena magana, babu wanda ya kuma mata maganan auren, hakan ya mata dadi dan tana ganin kaman an fasa ne, ita kwata2 yanzu adeel baya cikin tsarinta, domin kuwa ba zata iya kishi da Mysha ba, domin yanda taga Mysha a saudiya ta musu, Ina ga in sun hada miji, wani hawaye ya zubo mata tare da fadin afraz ka tafi ka barni gashi yanzu ina cikin kunci, babu mai rarrashi na, Ina ma kana nan da duk haka bai faru ba, mutuwa ta rabani dakai masoyi na, a lokacin da nake son kasancewa dakai, lokacin da nake bukatanka, ta kuma zubo da wani hawayen afraz ka tafi ka barni da sonka, a raina, naso ace tare muka mutu, duk wannan maganan da takeyi a fili take, mum ta shigo d’akin taji duk abunda take fad’a, taji tausayin Zeena din sosai, ta matsa kusa da ita, tace Zeena ki daina fadin haka, afraz ya tafi yabar miki yaranshi Zeena ki daina sa wannan abun a ranki, afraz addu’a yake bukata, sannan kuma yaranshi duk da basu sanshi ba, ki fad’a musu waye babansu su taso suna mai addu’a indai kikayi haka kin mai babban gata, kuma kin nuna mishi dagaske kina sonshi, ta kuma fashewa da kuka ta rungumi mum din,.
Yau an tashi garin Abuja ana zafi, Zeena tama twins wanka tasa musu kaya mara nauyi, tana zaune taji zafin itama ya isheta duk da a.c a kunne yake, ta tashi ta sami mum tace zata wajan ummi, mum da fara’a tace kai yau wani rana, tunda afraz ya rasu sau biyu taje gidansu, itama tayi murmushi, mum tace ai kin kyauta Zeena amma zama waje daya babu dadi, shi yake sama mutum yaita tunani, tace hakane, tace ma mum ta wuce ganin zata fita twins suka bita da gudu, suka makale ta, abun ya bata dariya tace ku koma ku taya mum fira, suka ki sakinta, mum tace haba ya zaku min haka, dawa zaku barni a gida, kuzo muje muma anjima zamu fita, ganin mum zata zo inda suke suka sa kuka, mum tace kuyi shuru tare zaku, jin haka sukayi shuru suna dariya, suka fita suna ma mum bye2, tace zaku dawo ai ku sameni,
Kai tsaye gidansu Zeena ta nufa, bayan tayi parking ta shiga, taga motar dady a gidan alaman yana gida kenan, sun shiga falon gidan da gudu abda tazo ta kamo hannun twins, tana fadin what a surprise yanzu nake son kiranki ince zanzo sai gaku, Zeena tace kedai abda kin iya tsara zance, tayi dariya tare da fadin ki tambayi dady kiji, a gabanshi na fada, jin haka dady yace to ai tunda tazo shikenan, nan ta gaida dady ya amsa cikin fara’a ya kira jikokin shi, suka zo wajan shi yana musu wasa, ummi tace ma afraz yazo ya noke alaman a’a, tace au niko to yau babu auren na sallameka, dady yayi dariya yace kishin ne ya motsa kinga amarya tazo ko, sukayi dariya, Zeena da abda suka shige ciki,
Bayan sun shiga Zeena take tambayan abda akan maganan bikin da ake shirin yi, yana nan ko an fasa, abda da mamaki tace a fasa kuma, aike zaki fi kowa sani ai, tunda kuna waya da adeel din, ni nasha mako kinzo mu tattauna akan bikin ne, Zeena ta sakar mata harara tare da fadin sai ki tattauna dashi ai, abda tace mai yayi zafi kuma, Zeena tace abda Kin San wani abu, kin dai San yanda abubuwa suka faru a baya toh ina so kiban shawara, ada naso adeel Mysha ta aure shi, daka baya na gano, abunda yasa ya aureta, a lokacin Allah yasa bani zai aura ba, nima na auri afraz bana sonshi amma daka baya Allah ya dauramin sonshi, har ya rasu ya barni da mugun sonshi a raina, wanda a yanzu nake kallon bazan iya kallon wani namiji da sunan so ba, ko aure ba, gashi su ummi sun tsaida ranan aurena da adeel, abda bazan iya kishi da Mysha ba, taya zan rusa wannan auren, abda tace haba Zeena ban taba tunanin haka daka gareki ba, dady yasan ba zaki bashi kunya ba shiyasa ya amsa musu, kuma bros zaheer ya fada mishi kina son adeel, shi yasa ma harya amsa maganan auren kuma dady yayi hakan ne dan ya faranta miki, bama haka ba idan kince baki son auren haka zaki bar yaranki babu uba, ai ya kamata yau ace sun taso da wanda zasu dinga kira da mahaifinsu,kuma na tabbata yanda adeel yake sonki zai rike miki yaranki, tace abda banki taki ba adeel fah mijin Mysha ne AMINIYA TA, abda tace to sai me dan mijin tane, idan ita bata ji kunyan aurenshi ba, taci amana toh kece zaki ji kunyan aurenshi, aiba zamanta zaki yiba, Zeena tayi shuru tabbas maganan abda hakane kuma gaskiya ta fad’a, toh amma yanzu taya zata kalli adeel a matsayin mijinta, harta iya zaman aure dashi, wata zuciyan tace don yaranki zakiyi, sai wajan 5 Zeena suka koma gida, da gudu twins suka shiga suka fad’a kan mum dake zaune a falo tace oyoyo, suka saki dariya da murna na ganin mum, nan suka nuna mata kudin da dady ya basu,tace to su bama mamansu ta ajiye musu, suka nufi Zeena suka bata, nan suka zauna suna ta fira da mum,
Bikin yana ta gabatowa, ita Zeena harga Allah bata murna da auren, dan tana ganin kaman taci amanan afraz idan ta sake wani auren, gashi a yanzu babu daman tace ta fasa domin bikin baifi sati daya ba, ga adeel tunda yazo mata gaisuwa bai kara zuwa wajanta ba, sai dai twins da yake aiko ma da kaya, kala2 hakan yana mata dadi sosai, tana zaune a waje kan kujera ta gaban swimming pool dan zafin yau yayi yawa, aka bude gate din gidan aka shigo, motar tayi packing ta bayanta, ya fito yazo inda take yace barka da hutawa, ta waiga taga adeel, ta amsa babu yabo babu fallasa, ganin hakan yasa ya sami karfin giwa, yace Zeena nazo muyi magana ne, bata amsa Shiba, shima hakan bai dameshi ba, yaci gaba da magana, Ina so inji mai kike bukata, ta dan tabe baki tare da fadin bana bukatar komai, yace ok babu damuwa ya ciro kudi yan dubu daya2 ya bata bandir biyar yace ga wannan ki saima su twins sweet, tace no ka barshi an gode, ya danji wani iri, amma sai yace ai bake naba ba, so baki da right din da zaki ce a barshi, tace amma aiβ¦β¦ Ya katse ta tare da fadin na wuceβ¦β¦β¦
Maryam obamββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to my fans πππ»
1β£0β£5β£to1β£1β£0β£
Ganin haka yasa ta diba kudin, ta shiga ciki itama, tare da fadin ni wannan auren ba sonshi nake ba, kawai dai so ake amin dole, tayi tsaki, tare da tausayin kanta,..
Anata hidiman biki, ango shi daya yake hidimar shi, amma Zeena ko a jikinta, itama Mysha bata San da batun ba, yadai ce mata zasu koma sabon gidansu ta shirya kayanta hakan ko akayi, tana ta shiri suka koma, a lokacin da suka koma taga yanda yayi tsarin gidan abun sha’awa, gidan babba ne, falon gidan ya hadu sosai, ya nuna mata wani kofa yace nan ne dakinta, ta bude taga falo sannan taga kofofi guda uku taga bedroom ne ko wanne akwai toiled a ciki, kuma duk dakunan ansa kayan gado a ciki, sannan falon ma data gani shima an hada shi, tace wancan shine babban falo kenan,ta fito ta nufi wata kofar taganta a rufe, ta matsa wanda yake kusa dashi shima a rufe, tayi dan tsaki to miye na rufe kofofin ma toh, ta koma babban falon ta ganshi yana tama ahmad wasa, yana dariya tace sauran kofofin can fa, mai yasa aka rufe, ya tamke fuska tare da fadin ainan ba hurumin ki bane, tace kaman ya, yayi banza da ita, ganin haka ta fara surutu ta inda take fita ba tanan take shiga ba, jin haka ya tashi yabar wajan.
Yau ranan laraba kuma a ranan aka kai akwatin auren Zeena, gidan su ummi aka kai, mum ta tafi can aka bar Zeena da twins, akwati 24 aka kai mata ko wanne cike da kaya masu tsada, abun dai ba’a magana, sai San barka, a ranan itama yakai ma Mysha nata akwatin, tace adeel wannan akwatinan fah, yace nama nama amarya tane, kema na miki, komai kala daya nasa muku, sai dai colour din na ban banta, tunda ya fara magana tasa mai ido tana kallonshi, wani hawaye yake zuba a fuskanta dama tasan za’ayi haka, tun zuwan su gidan Nan take zargin hakan, tace adeel wa zaka aura ba tare da fargaba ba ko tsoro yace Zeena, tace what Zeena kake nufi zaka auro ka Kawo ta cikin gidan Nan, yace yes, tace wlh baka isaba ba adeel dan rashin adalci ka rasa wacce zaka auro sai Zeena, ta saki kuka, yace Mysha ke har kina tunanin banyi miki adalci ba, ai bai kamata kima cemin hakaba, kanki ya kamata ki kira da hakan, tace adeel ka auro koma wace ce, bazan damu ba, amma dan Allah karka auro Zeena, yace Mysha kiyi hakuri Allah yasamin son Zeena, bazan iya fasa aurenta ba, tace adeel ka tausaya min nima ina sonka adeel, nasan kayi hakan ne dan ka rama abinda nama, duk sai yaji ta bashi tausayi yace Mysha badan in rama abunda kikamin ba yasa zan auri Zeena, keda kanki kin San yanda nake son Zeena, Mysha bazan wulakantaki ba dan na auri Zeena ba, taci gaba da kuka yana ta bata baki ganin bata da niyan yin shuru yasa ya bata waje, ganin ya tashi taci gaba da kukan ta, tasan idan Zeena ta shigo gidan nan zata koma bora, yanzu ma yata kare balle Zeena tana gidan, tace Zeena sai nasa adeel ya tsaneki.
Yau juma’a aka daura auren Zeena da adeel, ranan Zeena kuka take tayi tana fadin ita bata son wannan auren, amma ina babu mai sauraronta, tun Ana saura kwana biyu bikin ta koma gidan ummi, abda cema mai bata baki, ummi ta shigo d’akin taga tana ta kuka, nan ummi ta mata ta tas, tare da fadin in batayi shuru ba saita saba mata, ganin ran ummi din ya baci yasa tayi shuru, mum ta shigo d’akin ta tarar da ummi tana huci tare da fada, nan tace ma ummi ta daina mata fad’a haka ai rarrashinta za’ayi ba fad’a ba, ummi tace wani rarrashi ne ba’a mata ba, amma dan iskanci tazo tana ta kuka da yake ta raina mutane, ki duba ko wanka taki tashi tayi, jin yanda ummi take ta fad’a yasa ta tashi da sauri tayi toilet nan taci gaba da kukan ta, tayi mai isarta sannan tayi wanka ta fito, abda ta mata makeup tare da taya ta sa kaya, tayi kyau sosai, ta fito falo suna ta gaisawa da mutane, ummi ganin haka yasa ta saki ranta,.
Mysha tun safe itama take aikin kuka a d’aki tana fargaban a Kawo mata Zeena gida, amma babu yanda ta iya domin aikin gama ya Riga daya gama, son adeel dinne yasa ta kin barin gidan, dan har mahaifiyarta tace ta dawo gida, amma taki,
Wajan karfe 8 a Kazo daukan Zeena, tana ta rusa kuka, iyayenta sunyi mata nasiha sosai akan ta zauna lafiya ita da mijinta da abokiyar zamanta, aka fito da ita aka kama hanya, har aka karasa gidan tana kuka, abda dake gefe tace Zeena fito kiga gidan da aka Kawo ki, ya hadu sosai, tama abda harara sai kace tana ganinta, a cikin masu Kawo ta harda mum, tace ta fito da bismillah, hakan ko tayi suka shiga ciki, babu kowa da yake sun san dakin Zeena din suka bude suka shiga, tsarin dakinta yayi kyau sosai, itama da falo da 3bedroom ne a ciki, sun dan zauna kadan kafin suka wuce tana ta kuka, bayan sun tafi ta kifa kanta a giwa tana ta kuka,
Adeel wajan karfe goma ya shigo gidan, kai tsaye dakin Mysha ya nufa, yaga tana ta rafsa kuka, duk sai yaji ta bashi tausayi, ya zauna yana ta rarrashinta, yace taci abinci, ta girgiza mai kai alaman a’a, ya dauko daya daka ledan daya shigo dashi ya bude kaza ne a ciki, ya bata yace gashi taci, ta amsa, ya tashi tare da fadin saida safe, nan ta kuma sakin kukan haka ya fita ya barta, cikin kunci da bakin ciki, yanzu adeel zai kwana da Zeena a matsayin matarshi, wani bakin kishi taji yana dibanta,.
A lokacin daya shiga d’akin Zeena da sallama, yaga tana ta kuka, ya zauna kusa da ita, yace haba Zeena wannan kukan fa, na tabbata tun dazu kikeyi, ya kamata kiyi shuru kibar wannan kukan, jin bata kulashi ba, kuma bata daina kukan ba, yasa ya d’aga mata kai tayi sauri ta matsa baya, ganin haka yace ga abinci kici karki zauna da yunwa, ya fara bude mata, kaza ne da yogurt, ya mika mata ta amsa, ya fita daka d’akin ganin haka yasa tayi sauri ta rufe kofan ta da key, shima falo ya nufa ya kwanta kan kujera, ya daura hannunshi akan kanshi, babu abunda yake sai tunani, wai yau shida Zeena suna matsayin mata da miji, ranan da suke ta buri, amma ranan tazo Zeena kwata2 bata murna, yanzu Zeena bata sona kenan mijinta take so, wani irin kishi yaji ya rufe shi.
Maryam obamββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to my fans πππ»
1β£1β£0β£to1β£1β£5β£
Ga kanshi dake ta sara mishi, a falon ya kwanta har bacci ya dauke shi, ita kuma Zeena bayan fitanshi itama kwanciyan tayi abunta, sai wajan asuba ta farka taje toilet tayi alwala tazo tayi sallah, bayan ta idar taji kaman ana mata nocking, taso ta share komai ta tuna kuma ta tashi ta bude kofan, taga adeel ne Ya shigo tare da fadin kinyi sallah, ta d’aga mai kai alaman eh, ya bude daya daka cikin d’akin ya shiga wanda ya ware nashi, bayan ya shiga tayi dan tsaki ta nufi d’akin ta itama,
Mysha tun jiya ta kasa bacci sai aikin kuka, babu abunda take gani sai adeel da Zeena, tana ganinsu a tare a matsayin ma’aurata, tace ni nayi sake ya kamata in dau mataki, tayi dariya tare da fadin Zeena nasan ko ke wacece, nasan yanda zan miki keda kanki zaki bar gidan nan, wannan tunanin da tayi shi yasa bacci ya dauketa
Zeena tunda ta koma bacci sai wajan 10 ta farka, ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta shirya cikin wani doguwar rigan material, duk da batayi makeup ba tayi kyau, ta zauna ta zabga tagumi tace koya twins suke yanzu oho, duk kewarsu ya kamata, ta dauki wayanta ta kira mum, bugu daya ta dauka, Zeena ta gaidata mum ta amsa cikin fara’a, bayan sun gama gaisawa tace ina twins mum tace sun fita da dady yanzu, tace to a gaidasu, mum tasan Zeena kewarsu take domin bata taba tafiya koda na wuni daya bane ba tare dasu ba, tace in sun dawo zata kirata, ta amsa da toh sukayi sallama, a dai2 lokacin adeel ya shigo cikin kananan kaya ya mishi kyau sosai sai kamshi yake tashi, ya kalleta yace an tashi lafiya, ta amsa da lafiya, yace muje muyi breakfast, taji gabanta ya fad’i, don bata san wani irin tarba Mysha zata mata ba, yace let go, tace no bana jin yunwa, ya kafeta da ido ganin irin kallon da yake mata yasa ta daure fuska tare da tashi tasa hijab, yayi dan murmushi yace mai kika ci, ki tashi muje ban San musu, ta mike suka fita tare sun sami Mysha a falo tasa wani top mai hannu daya da 3quater jeans, ta daure fuska kaman bata taba dariya ba, adeel yace Mysha ina breakfast ban gani a dining ba, tace breakfast banyi ba, yace saboda me, tace bashi aka Kawo ni in dinga yiba, ita wanda kaje ka kwana a wajanta ta baka mana, ranshi ya baci sosai amma saiya dake, ya kalli Zeena yace bari in Kawo miki abunda zaki ci, tace no kabarshi kawai, yace akan me kinci wani abu ne, Mysha ta kwashe da dariya tare da fadin yau ina ganin ikon Allah, ganin haka yasa Zeena ta juya tayi dakinta, shima ya bita, bayan sun shiga d’akin ya rasa mai zaice mata, can dai yace kiyi hakuri Zeena bari inje in dawo, ta amsa da toh sannan ya fita, Mysha na falon har yanzu tana ganin shi ta fara bala’i tana fadin an dai zama mijin tace, kana wani binta kana kaudi ko kunya baka ji, yayi banza da ita ya fita, har yaje ya dawo ya sameta a zaune a falon tana kad’a kafa tace Malam nima fa yunwa nake ji, ya mika mata leda daya sannan ya wuce ta bishi da harara, a lokacin daya shiga d’akin Zeena ya ganta a kwance amma idonta biyu, yace ki tashi kici abinci, bata amsa ba amma ta tashi, ya mika mata, ta amsa sannan ya fita, dakinshi ya shiga ya kwanta, ranshi ya baci akan abunda Mysha ta mishi, ina kyaleta ne kawai saboda Zeena, amma duk da hakan zanyi maganin ta, yayi dan tsaki wayanshi dake gefe ya fara kara ya dauka yaga Mysha ce, yayi rejecting Kiran, ta kara kira, da yaga hakan saiya kashe Wayan gaba daya,.
Sai wajan karfe biyu ya fito ya shiga d’akin Zeena, ya ganta tana ta aikin kuka, nan ya zauna yana tambayanta akan mai nene, mai aka mata take kuka ko Mysha ce, ta girgiza mai kai alaman a’a, ya matsa kusa da ita tare da janyota kirjinshi, nan gabanta ya hau bugu, yace kiyi shuru Zeena bana son wannan kukan, ta dan tsagaita da kukan da takeyi, yace ta tashi su shirya suje suyi lunch, tace a’a taci sauran abincin safe, yace ok, ya fara wasa da gashin kanta, wani irin sonta yake shiganshi tare da wani sha’awarta, jin bugun kofa sukayi anayi kaman za’a balla, da sauri ya tashi ya bude kofan yaga Mysha ce tana huci, tace toh Malam saika fito ka nemo min abincin da zanci, yace kina da hankali kuwa Mysha, tace ban sani ba, in banda wulakanci Kazo ka ajiye mutum babu abinci, yace wani kalan abinci ne babu miye babu a gidan Nan, tace ni dafaffe nake so, dan bazan iya girki ba, yace ok ya rufe kofan ya barta a nan waje tana ta bala’i, Zeena tana ta kuka dama abunda take tsoro kenan irin wannan abun, gashi kuma an fara, yace dan Allah Zeena kibar wannan kukan, bata kulashi ba taci gaba da kukan, dakyar ya rarrasheta tayi shuru, tace ya tashi yaje ya siyo mata abincin, yace babu inda zashi tunda akwai abinci a gidan, ganin ta bata rai yasa yace bari yaje, bai sami Mysha a falo ba ya fita,
Yau Zeena zata bar girki, Mysha zata amsa, ya kirasu dukansu falo akan su tsara yanda zasu dinga kwana, ranan Mysha ta sake kaman ba ita ba, itace ma ta yanke tace kwana biyu2 ya kalli Zeena yace kinji hakan yayi, jin haka yasa tace inma bai mata ba ni haka na tsara, yace Mysha ki dawo cikin hankalinki bake nake tambaya ba, jin haka yasa tayi shuru tana hararan Zeena, Zeena tace duk yanda kuka tsara yayi, Mysha ta tabe baki, sannan yace ya maganan abinci ya zakuyi, Mysha tayi caraf tace duk mai girki zata dinga yi, ita dai Zeena bata ce komai ba, sai bugun da zuciyanta yake mata, ita kwata2 bata son wannan zaman jinta take kaman akan wuta take, domin irin kallon da Mysha take mata abun ya isheta, adeel yace shikenan hakan yayi, jin haka Zeena ta tashi tayi ciki, ya tashi da nufin ya bita, Mysha ta shiga gabanshi tace ka manta yau nice dakai, Ina kake kokarin zuwa, yace kaman ya dan yau girkin kine banda iko inga matata, tace hakane, yace ok hakan ko akayi, ya fasa shiga, Zeena ko tana shiga d’aki ta dau wayanta taga misscall din mum da sauri ta kirata, ta dauka suka gaisa sannan take tambayanta komai lafiya tace eh, ta bata afraz yana ta mata surutu wani ta gane wani kuma tayi dariya, mum taba small Zeena itama suna ta surutu tana dariya, tayi kewan yaran ta sosai, sun dauki lokaci suna ta surutu, sannan sukayi sallama.
Bayan Mysha ta gama dinner, ta jera a dining adeel yace taje ta kira Zeena, tace toh, ta nufi d’akin Zeena din ko nocking batayi ba ta bude kofan ta shiga taga bata falo dinta, taje wata kofa ta buga jin kaman ana buga kofa yasa ta fito, taga Mysha ce,ganin kayan dake jikin Zeena din yasa ta daure fuska tare da wani bakin kishi, wani top ne mai gajeren hannu da skin tie tasa ribbon ta kama kanta, ganin kallon da take mata yasa tace lafiya kuwa, tace ke ko kunya bakya ji, kin auri mijin kawarki, tir da halinki, Zeena tayi dariya tace ni ko ke, jin haka Mysha ta kuma tamkewa tace karki fad’amin magana dai, Zeena tace ni banda ma lokacin ki ta bude kofa ta shige, tabar Mysha da bakin ciki, ta fita ta sami adeel akan dining yace ina Zeena din, tace tana d’akin ta, tace ta koshi, yace kaman ya mai taci, tace oho aiba gadinta nake ba, ya tashi ya nufi d’akin Zeena din ya ganta a kwance yace Zeena ki tashi kizo kici abinci, ta amsa da toh, ganin bata tashi ba yace ina jiranki, ta tashi ta dauki hijab, tasa suka fita tare, Mysha tayi tsaki, ta zuba ma adeel abinci ta zuba nata, Zeena itama tasa kadan, bata wani ci da yawa ba, ta ajiye tare da mikewa, adeel yace ina zaki baki gama cin abinci ba, tace na koshi, tayi gaba abunta, Mysha tace ikon Allah yau ina ganin abunda yafi karfina, yayi banza da ita, dan duk abunda take yana tara tane, yau yake so yayi maganin ta.
Maryam obamββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to my fans πππ»
1β£1β£5β£to1β£2β£0β£
Bayan adeel ya kammala ya tashi daka kan dining din, ya nufi gefen Mysha, itama ganin haka yasa ta bishi, don ta zauna ne taga ko zaije d’akin Zeena, bayan ya shiga ya bude dakin shi ya shiga, toiled ya fad’a yayi wanka ya fito yaga Mysha daka ita sai night gown, kallo daya ya mata ya kauda kai gefe, bayan ya gama shiri ya kwanta ta gefen gado, ganin bai kulata ba yasa tayi tsaki tare da fad’in ikon Allah, ya tashi fuska a daure yace ta tashi tabar d’akin, tace kaman ya, wlh babu inda zani in tashi in fita kaje d’akin wancan munafukar koh, ranshi ya kuma baci yace bari kiji Mysha duk abunda kikeyi na gaji dashi bazan dauka ba dan haka kije gidanku na gaji, tace toh, ta juya baya tare da fadin Allah ya kaimu gobe zan wuce,
Ranan Mysha kasa bacci tayi domin ba zata iya komawa gida ba, koda lokacin da adeel yake bata wuya bata koma ba, balle yanzu da take ganin ya kara aure, wato ta basu waje suyi abunda suke so, tace no way, lokaci daya tayi dan murmushin takaici, ta tashi da sauri ta fara hawaye tana rokan adeel akan yayi hakuri bazata kara ba, yayi banza da ita don har ya fara bacci ta tashe shi, ganin bai kulata ba, yasa tace duk abunda take mai zata daina sannan zasu zauna lfya ita da Zeena, jin haka yasa yace shikenan, tace mai ta gode ta koma ta kwanta tana goge hawayen tare da dan murmushi.
Washe gari Mysha tun wajan 7 ta shiga kitchen ta had’a breakfast, ta jera akan dining, ta koma d’aki tayi wanka sannan ta tashi adeel, shima ya shirya, bayan sunje kan dining, ta tashi bari inje in kira Zeena hakan yamai dadi, ya amsa da toh, kai tsaye d’akin Zeena din ta nufa ta bude kofan, taje kusa da kofar da taga ta fito jiya tayi nocking Zeena ta bude kofan, Mysha taya mutsa fuska, tare da fadin ki fito muyi breakfast, kina wani kasa2 dakai kaman wata munafuka, Zeena tayi shuru, Mysha tayi tsaki ta fita, Zeena ta koma ta dauki dankwalin atamfan ta, ta daura, sannan ta fito, bayan Zeena ta zauna ta gaida adeel ya amsa tare da fadin kin tashi lfya, ta amsa da eh, Mysha ta zuba ma adeel breakfast sannan tasa ma Zeena tace ga naki in yayi kadan sai in kara miki, Zeena da mamaki take kallon ta,tace yayi haka, suna ci Mysha tana dan Jan Zeena da fira, wani Zeena ta amsa wani kuma tayi murmushi, adeel shiko yau yana cikin nishad’i, bayan sun kammala Zeena tayi d’akin ta, adeel da Mysha suka zauna suna dan taba fira jefi2 yin firan kawai yake amma kwata2 hankalin shi da tunanin shi, yana wajan Zeena yana son zuwa wajanta, ya tashi yace bari inje mu gaisa da Zeena ta amsa da toh, yaji mamaki dan baiyi zaton haka daka gareta ba, amma saita amsa, yace ya kamata ma ki dauko ahmad, tace toh anjima zan dauko shi, ya nufi d’akin Zeena, bayan ya shiga ya ganta tana waya da mum, bayan sun gama ta kalleshi tace nagode mum tace ka kaima su twins kaya, yace dan na kai musu kaya shine kike min godiya dan nama yarana hidima, taji dadin abunda yace, tayi dan murmushi, ya kafeta da ido wani irin shaukin sonta ke shiganshi, ganin yanda yake kallon ta yasa taji wani iri, yayi murmushi yace mai kike bukata, ta amsa da babu komai yace ok, ya fita daka d’akin, har lokacin Mysha tana falo, tana ganin shi tace dama kai nake jira ka fito in wuce, yace ok ki gaida mum nd dad ta amsa da toh sannan ta wuce tare da fadin yace ma Zeena ta fita, d’akin Zeena ya koma a lokacin tana toilet, bai dade da shigaba yaga ta fito da alama wanka ta karayi dan towel ne a daure a jikinta, ya kafeta da ido, ta dauko hijab dinta da nufin tasa, yazo yayi hugging dinta ta baya, tare da amsan hijab din, ya fara wasa da gashin kanta wanda ta jika da ruwa, yayi dan murmushi tare da fadin very soon zaki bani cute baby kaman ki, jin haka yasa ta matsa da sauri tare da daure fuska, ya kuma janyota, ta fad’o jikinshi, ya fara kokarin cire mata towel din jikinta gaba daya ta sandare ta kasa ko motsi haka ya dinga wasa da ita, yasa jikinta yayi sanyi, ta saki kuka, ya fara magana kaman yana rad’a yace Zeena mai nene, tace ka kyakeni bana so, jin haka yasa ya sake ta, tare da barin d’akin, tana ganin ya fita ta tashi dakyar tasa ma d’akin ta, key, ta dawo ta kwanta,
Mysha tunda ta fita ta kasa sakewa dan gani take kaman Zeena da adeel suna tare yanzu tayi dan tsaki, ta dauki ahmad tace ma mamanta zasu wuce, tace tun yanzu tace mum zanyi dinner a gida inna koma, Ina so ki samo min mai aiki wacce ta iya girki nan da kwana2 na gaji da wannan girkin, maman tayi dariya tace toh shikenan zan sa a samo miki, ta amsa da to suka wuce, a lokacin da suka shiga gida taga babu motar adeel, tayi ajiyan zuciya cikin jin dadi, tace yauwa basa tare, lokaci daya kuma ta gimtse kodai tare ma suka fita, da sauri ta dauki ahmad sukai ciki, d’akin Zeena din tayi, tana ta nocking kaman zata balla kofan, Zeena ta fito tace lafiya kuwa, Mysha ta mata kallon sama da kasa, tace lafiyan ya Kawo haka, Zeena tayi dan murmushi tace toh Allah ya karo lafiyan, nan Mysha ta kumbura tare da fadin mai kike nufi kina nufin banda lafiya, ko mai, Zeena tace ni bance haka ba, keda kike da lafiya dan nace Allah ya karo ai ba laifi bane, Mysha ta matso kusa da Zeena kaman zata daketa, nan Zeena tayi sauri tayi baya tace badai fad’a zaki dani ba, rufamin asiri, kiyi hakuri, Mysha tace aikin banza ai wlh idan kika fad’a abun da yafi karfin bakin ki saina zane ki a gidan Nan, suna cikin haka saiga adeel Mysha tana ganinshi tace Zeena muje kitchen ki tayani muyi dinner yau a gajiye nake wlh, Zeena da mamaki take kallon ta, ta kasa furta komai, ganin haka yasa Mysha ta kuma cewa kiyi hakuri inna takura miki ki barshi zanyi, adeel yace zama ta taya ki ko Zeena, sai a sannan tasan adeel yana wajan, tace lallai Mysha makira ce, amma a fili sai tace kanta na ciwo, Mysha tace Allah sarki ban sani ba, Allah ya sawake bari inje inyi in barki ki huta, adeel yanda yaga Zeena tayi mata baiji dadi ba, amma saiya basar ya mata uziri, Zeena ta koma d’aki, shi kuma ya dauki ahmad yana mai wasa, ya shiga d’akin Zeena din yaga tana danna waya, yace kinsha magani ta amsa da eh fuska a daure ganin haka yasa ya fita, ita kuma tayi dan tsaki ta kwanta abunta,
Yau Zeena ita zata karbi girki dan haka, tun wajan 4 tayi kitchen taga duk yayi ‘kura ta zauna ta goge ko ina, ta maida komai wajan shi, sannan ta daura girki, tayi tuwo miyan danyan kubewa, da yaji nama da kayan ciki, tayi Mango juice ta jera akan dining sannan ta fad’a toilet tayi wanka tasa wata doguwar riga na yan kanti, ta kama gashinta da ribbon, sannan tasa wani karamin gyale ta daure kanta dashi tayi kyau sosai, ta fito falo din taga Mysha da adeel, Mysha tace yanzu nake kokarin tashi in kiraki, yunwa nake ji, Zeena tace aida kinci basai kin jirani ba, adeel tunda ta fito ya kafeta da ido, ji yake kaman yaje yayi hugging dinta, amma babu dama, tazo ta zuba musu, ita kuma ta koma kan kujera tana kallo, adeel yace kizo kici abinci mana, tace no na koshi, yace mai kikaci tace babu komai, ya tashi tare da plate din abincin yazo inda take, ya zauna ya fara bata tana ci,tana kallon Mysha wanda ta kumbura kaman zata fashe, dama tayi hakan ne dan ta nuna mata itama ta iya makircin,shi kuma adeel din kwata2 ya manta da Mysha tana wajan.
Maryam obamββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to my fans πππ»
1β£2β£0β£to1β£2β£5β£
Mysha ta tashi da sauri tabar wajan, ganin haka Zeena yasa itama tace ma adeel ta koshi, yace ki kara ci kad’an, tace no, ka barshi jin ihun Mysha sukayi, da sauri adeel yayi d’akin, yana fadin lafiya Mysha mai nene, tace ciki na, yace mai ya sameki tace murd’a min yake, yace tashi muje asibiti, tace bazan iya ba ka taimaka min, yace ina zuwa yana fita tayi dariya tare da fadin yau kwanan kine Zeena amma ni zan amshe, Jim kadan sai gashi da Zeena din sun shigo, ta kuma langwabe wa, adeel yace Zeena ta dauki ahmad ta kaishi d’akinta ta amsa da toh, ta daukeshi ta kaishi, shi kuma adeel ya dauki Mysha yayi mota da ita, kai tsaye asibiti suka nufa, an duba ta, aka bata magani suka dawo gida wajan karfe goma da wani abu, a lokacin Zeena harta fara bacci, taji kaman ana taba ta, da sauri ta tashi taga adeel tace har kun dawo ya jikin nata, ya amsa da sauki sannan ya dauki ahmad, ya fita, tunda ya fita bai dawo ba, daka yazo zai fita Mysha taita nishi, ganin haka saiya dawo ya zauna da ita, ita kuma Zeena baccin ta tayi abunta, sai wajan asuba tayi bacci sannan ya fita masallaci, yayi sallah, bayan ya dawo ya duba ta yaga tana ta bacci, kai tsaye d’akin Zeena ya nufa, yaga tana sallah,ya zauna akan gado, harta idar bata tashi ba taci gaba da zama akan dadduman, ganin bata da niyan tashi yasa yazo inda take ya zauna a ‘kasa ya kamo hannunta da take wasa dashi, yace Zeena kiyi hakuri kin jini shuru sai yanzu ta samu tayi bacci, tace babu komai ta tashi ta haye gado, ganin haka shima ya haye gadon ya janyota jikin shi,ya manneta kaman zata gudu, da haka bacci ya dauke shi, ganin yayi bacci yasa ta zame jikinta cikin nashi ta nufi kitchen don ta had’a breakfast, ta had’a farfesun fresh fish, tayi sandwich da tea ta jera kan dinning ta koma dakinta taga har yanzu yana bacci, ta fad’a toilet tayi wanka ta shirya cikin wasu kananan kaya Riga da wando tayi kyau sosai duk da batayi makeup ba,ta fashe jikinta da turare sai kamshi ke tashi, ta koma falo dinta ta zauna tana kallo, sai wajan 10 ya farka yaga bata kusa ya shiga toilet shima ya fito ya shirya, ya ganta a falo tana kallo wani sonta yake shigar shi, musamman shigan da tayi wanda ya rud’a shi, tabbas Zeena ta hadu, jin kaman ana kallon ta yasa ta waigo, suka had’a ido ya sakar mata murmushi tayi sauri tayi kasa dakai, ya matso kusa da ita tare da janyota jikin shi, suna shakan numfashin juna, ta kasa ko motsi, yasa hannunshi ya d’ago mata kai, ya kafeta da ido itama ta kasa, ‘kasa da kanta jin bakinshi tayi cikin nata sun dauki lokaci cikin haka kafin ya sake ta, ta fara mayar da numfashi ta kasa ko tashi dan gaba daya ya kashe mata jiki, jin hannunshi tayi cikin kirjinta tare da kara rungumota, ganin dagaske yake yasa tace breakfast is ready, yayi dan murmushi ya matsa kusa da kunne ta, yace kece abinci na, ta dan tureshi ya kuma yin dariya ganin yanda take daure fuska, yace Zeena ina sonki, nan taji gabanta yana bugu da sauri ta tashi tayi bedroom dinta nan ta saki kuka, jin ta dade bata fito ba, yasa ya bita yaga tana kuka yace lafiya kuwa Zeena tayi shiru babu amsa, ya matsa kusa da ita tare da fad’in ban San kukan ki Zeena plz, nan ta kuma jin wani hawayen sau da yawa adeel yana mata abubuwa shigen na afraz, dakyar ya samu tayi shuru, suka fita falo don yin breakfast,baiga Mysha ba yasan tana bacci har yanzu dan haka baiko leka d’akinta ba suka fara yin breakfast.
Mysha itama tuntuni ta farka taga adeel baya wajan tayi dan tsaki yanzu saida yaje d’akin waccen mayyar, wani bakin ciki taji yana damun ta, yanzu duk abunda na shirya a banza tayi tsaki ta tashi, ta fito falo taga Zeena da adeel suna cin abinci suna fira cikin Jin dadi, nan ranta ya kuma baci ji take kaman ta shage Zeena dan takaici, adeel yace Mysha har kin tashi ta amsa da eh, nan Zeena tace ya jikin, tace da sauki kiyi hakuri naso in taso in taya ki aiki, bacci yaci karfina, adeel yace keda baki da lafiya Mysha ina ke ina tayata aiki, Zeena tace lallai Mysha ke daban kike, nan Zeena ta dan fahimci wani abu, anya ciwon Mysha ba karya bane kuwa, inma karya tayi tama kanta, amma zan nuna mata tayi kuskure, Mysha ce ta katse ta tare da fad’in ahmad jiya baiyi miki kuka ba, Zeena tace a’a aini yara suna sona, Mysha ta turo baki tare da fadin Allah sarki, Zeena ta kalli adeel wanda bini2 idonshi na kanta, tace ya kamata inje inga su twins, nayi missing dinsu, adeel yaji dadin wannan maganan dan dama yana neman dama ne da zasu fita shida Zeena, yace ok dama zan fita yanzu ki shirya sai in kaiki, jin haka Mysha tayi caraf tace nima bari in shirya muje tare, yace no keda baki da lafiya ina ke ina fita, tace na warke ai, yace kiyi hakuri ki zauna kar kije abun ya kuma tashi, haka ta hakura dan babu yanda ta iya, don idan ta matsa zai gane karya takeyi, Zeena ta tashi taje ta shirya cikin wani atamfa dinkin riga da skirt ya mata kyau sosai, tasa gyale kalan kayan, ta fito falo, adeel ya kalleta yace ta koma tasa hijab indai tana so ta fita, nan taji wani hawaye na shirin zuba daka idonta, da sauri ta koma tasa hijab, suka fita, Mysha kaman zata fashe dan bakin ciki, tace kuje Ku dawo zan nuna miki naki kadan ne Zeena.
Hotel ya nufa da ita, bayan sun shiga yace ta fito su shiga, bata musa ba ta fito, yaje yayi komai da komai ita bata san mai yake yiba, dan tana zaune nesa da inda yake, yazo yace suje ta bishi, wani d’aki suka shiga taga ya zauna akan gadon d’akin sai a sannan tace mishi mai suka zoyi nan, ya tashi yazo kusa da ita ya fara cire mata hijab din jikinta,ganin haka gabanta ya fara fad’i, harya cire hijab din, ya cire mata rigan jikinta, tace adeel Mβ¦.. Kafin ta karasa abunda take son cewa yasa bakinshi cikin nata, nima ganin haka na fita na basu waje,
Mysha tunda suka fita take ta zarya ta kira adeel bai dauka ba, tayi tsaki yanzu hala suna can tare suna cin Amana na, wani haushin Zeena take ji, gashi plan dina na jiya bai yiba, tunda ya koma d’akinta ya kwanta, tayi dan dariya tare da fadin Zeena sai nasa adeel ya wulakanta ki, da kanshi zai koreki,.
Zeena tana toilet tana wanka tare da hawaye, shi kuma adeel yana kwance kan gado cikin nishad’i, tabbas mata suna suka tara kuma ko wace mace tana da nata baiwar da Allah ya mata, har Zeena ta fito ta ganshi a kan gado suka had’a ido tayi sauri tayi kasa dakai wani irin kun yanshi, take ji, yayi murmushi ya matso kusa da ita, yayi hugging dinta, tare da fad’a mata I luv u Zeena, you are my happiness, jin tayi shuru yace bari insa miki kaya ta saki kuka yace mai nene, tace bana so zansa dakai na, yayi dariya ta diba kayanta tayi toilet, ya bita da kallo yana dariya harta fito fuskanta a daure yace mai nene kuma, tace kayana duk ya yamutse, taya zani gidan mum a haka, yace ai yau babu zuwa gidan mum gida zamu koma, tace plz ka kaini, yace a haka, tayi shuru can tace toh ka kaini gida in canza kaya sai muje, yayi dariya tare da fadin zan dauko miki twins in Kawo miki su, ba karamin dadi taji ba, suka koma gida, sunga Mysha a falo tama Zeena kallon sama da kasa, tare da aiyana wa a ranta, anya ba wani waje sukaje ba, dubi yanda adeel yake ta wani zumudi sannan bada wannan kayan ya fita ba, ita kuma Zeena kayanta ya yamutse ta kasa, nan taji kirjinta yana buga mata, ta daure tace har kun dawo nasha aiko dasu twins din zaku dawo, Zeena ta fahimci tana so tasan daka inda suke ne, tace eyya ai bamu samu munje ba, munje wani waje ne, nan Mysha ta kumbura, adeel yabar wajan yayi gefen Zeena ganin haka Mysha ta taso taje gaban Zeena tace ina kukaje, Zeena ba tare da tsoro ba tace hotel muka je, dan bama son takura, wani kululun abu ne ya tsaya mata a wuya, ta cakumi wuyan Zeena.
Maryam obamββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to my fans πππ»
1β£2β£5β£to1β£3β£0β£
SALAM MY FANS PLZ KUYI HAKURI NAJIN BAN MUKU POSTING KULLUM KWANA2 BAN ZAMA GA DAD DINA BASHI DA LAFIYA PLZ KUSA SHI A ADDU’A, SANNAN KU KARA HAKURI NA KUSA KAMMALA MUKU NOVEL DIN NGD
Zeena ta fara kokarin cire hannun Mysha daka wuyanta, ta kasa domin ba rukon wasa tayi mata ba, sai da tayi dagaske kafin ta samu ta tureta da kafa tayi ‘kasa, ta tashi ta wanke Mysha da mari a dai2 lokacin adeel ya fito ya tsaya yana kallonta rai a bace, yace miye haka Zeena kina da hankali kuwa, ganin adeel din itama Mysha tasa kuka tana fadin daka tambayan yara sai ki mareni, ran adeel ya kuma baci, yace ma Zeena kin kyauta ki bata hakuri, Zeena tayi shuru taki bata hakurin ganin haka ranshi ya kuma baci ya dinga fad’a ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, ganin haka yasa Zeena tayi d’akinta da gudu tana kuka, ita kuma Mysha sai rusa kuka take, ranshi ya baci sosai ya fita yabar gidan, ganin ya fita Mysha ta tashi tana dariya tare da fad’in yanzu kika fara ganin haka Zeena, tunda kika auran min miji,.
Zeena tunda ta shiga d’aki bata fito ba, har wajan 7 gashi itace da girki, kanta keta sara mata ga zazzabi daya rufeta lokaci daya, dan taci kuka sosai, tana ganin adeel bai mata adalci ba, ya kamata ya tambaye ta, yaji ta bakinta, amma ya rufeta da fad’a ya daura mata laifi.
Adeel shima sai wajan 9 ya dawo tare dasu twins, yaga Mysha a falo tana ganin shi, ta tashi da sauri tana fad’in yauwa gwara da ka dawo yanzu, yace lafiya, tace ni yunwa nake ji sosai, yace yunwa kaman ya babu abinci ne, tace toh mai girki batayi ba, ga ahmad harya gaji yayi bacci da yunwa, ranshi ya baci yaja hannun su twins yayi d’akin Zeena din yaga tana kwance tana rawan sanyi da sauri ya karasa wajanta tare da taba jikinta yaji zafi, duk yabi ya rude yace Zeena maike damun ki, tayi shuru ba tare data kulashi ba, ganin haka yasa ya d’agata duk sai yaji ta bashi tausayi, yace fever kikeyi, ta d’aga mai kai alaman eh, ya fita falon ta ya shigo dasu twins tana ganinsu ta tashi da sauri tayi hugging dinsu tana hawaye, shi kuma ya fita kitchen ya fita ya had’a mata tea ya Kawo mata tasha sannan tasha magani, ya kuma fita d’akin Mysha yayi wanda take ta murna ta had’a su, yau adeel zaiyi maganin Zeena, tana ganin ya shigo ta zabga tagumi tace adeel wlh yunwa nake ji, yace Mysha Zeena bata jin dadi, ki taimaka ki daura abinci, ranta ya baci tace wlh bazai yiwu ba, akan mai zan daura aiba girki na bane, ya tsaya yana kallonta da mamaki yace idan kin daura kinma kanki, tace bazan daura ba kuma a Kawo min abinci dan yunwa nake ji, in banda ni an raina ni har zaka zo kace in daura abinci tunda gani baiwa ita yar hutu, toh bata isa ba, in makircinta yana aiki a kanka to ni bazai yi a kaina ba, tana ta surfa bala’i ganin haka ya fita ya barta, wajan saida abinci yaje ya siyo musu, yakai ma Zeena nata da yaran ta, sannan yakai ma Mysha itama ta amsa tare da fadin wlh aiki ya ganka, bai kulata ba ya fita.
Ya shiga d’akin shi ya kwanta, can ya dauki waya ya kira Zeena kaman ba zata dauka ba, ta dai daure ta dauka, yace Su twins sunyi bacci ne, ta amsa da eh, yace ok kizo d’aki na, Ina son ganinki yanzu, yana fad’in haka ya kashe Wayan, tayi dan gajeran tsaki sannan ta tashi, tasa hijab ta nufi d’akin ta shiga ta ganshi a zaune yana kallo, ta tsaya a tsaye tana sauraranshi, yace kizo ki zauna, kaman karta zauna ta dai daure ta zauna, yace ya jikin tace da sauki, tana fadin haka ta tashi zata fita ya tashi ya janyota ta baya, ta fado kan jikin shi, ta fara hawaye yasa hannu yana goge mata, yace kiyi hakuri Zeena kibar wannan kukan shima da kanshi yasan bai mata adalci ba, ya kamata ya tanbayeta mai yasa tayi hakan, dan yasan haka kawai ba zata mari Mysha ba, ta katse shi tare da fad’in bacci nake ji, yace a nan zaki kwanta tare dani, jin haka yasa tayi shuru bata kara magana ba, yace kiyi hakuri Zeena, daka yau ko mai ya had’aki da Mysha karki kara cewa zaki taba ta, kinji, ta d’aga kai alaman eh, yaci gaba da cewa idan ta miki wani abu ki fad’a min ni da kaina zan dauki mataki, ta amsa da toh, ta tashi ta kwanta ta gefen gadon, shima ya kwanta tare da daura hannunshi a kanta, da haka bacci ya dauke su, ita kuma Mysha cikin takaici ta kwanta dan taga duk abun data had’a bata samun yanda take so.
Tunda Zeena ta tashi tayi sallah, taje taga su twins suna ta bacci abun su, ta nufi kitchen dan daura breakfast, ta soya doya da kwai sannan ta had’a kunun gyad’a, tayi farfesun kaza, ta jera akan dining, ta gyara ko ina, a dai2 lokacin Mysha ta fito ta sakar ma Zeena harara, Zeena ganin haka yasa ta wuce tabar wajan dan yanzu bata da lokacin ta, d’aki ta shiga tayi wanka ta tashi su twins ta musu wanka suma ta shirya su, afraz yace mum nan ina ne, Zeena tayi dariya tace gidanku ne nan, adeel ya shigo d’akin da gudu suka tashi suna dady yayi dariya tare da d’aga small Zeena sama, shima afraz yace sai an d’aga shi, yayi dariya shima ya d’aga shi, nan suka fita falo yin breakfast, sun tadda Mysha akan dinning din tana cin abinci, ko kallo basu isheta ba, taci gaba dacin abincin ta, adeel yace an tashi lfya, ta amsa a dakile lafiya, ganin haka shima ya shareta, suka fara cin abinci su twins suna ta surutu su Zeena suna ta dariya, Mysha tace dalla ku mana shuru kunzo kun dame mu da surutu, small Zeena ta tashi ta make Zeena, ran adeel ya baci yace miye haka Mysha yara nefa, tace toni ina ruwana, an Kawo mana yara suna mana hayaniya, yace sai yau nasan baki da hankali Zeena ta kama hannun yaran tayi ciki dasu, Mysha tace aiba karya nayi ba, ya tashi ya bata waje ya shiga wajan Zeena yaga tana hada kayan yaran, yace lafiya kike hada musu kaya, tace yau zasu koma, yace akan wani dalili, tace hakanan yace toh babu inda zasu, tace kayi hakuri bazan iya bari su kara kwana a nan ba, yace indai ban isa dake ba toh kiyi abunda kika ga dama, ya fita ya bata waje, tayi shuru tare da bakin cikin abunda akama yaran ta, tabbas zan iya jure komai amma bazan bari a wulakanta yara naba, domin sune rayuwa na, tun daka ranan bata bari suna zuwa babban falo komai sunayi a gefenta, hakan na damun adeel, yanda yaga tana janye yaran bata bari suna fita suna sake wa, satinsu daya mum tace su dawo, Zeena bata soba, amma haka suka koma shima adeel yaso mum tabar musu yaran, taki tace su take gani taji dadi sannan ba zata iya barin jikokinta suyi rayuwan agolanci ba,.
BAYAN SHEKARA DAYA
Zeena tana d’aki ita da adeel suna fira cikin so da kauna, ta tashi da gudu tayi bayi tana ta amai, ya bita da sauri duk ya rude yana mata sannu, bayan ta gama sukayi asibiti, nan aka dubata akace tana da cikin wata daya da sati biyu waiyo zo kuga murna wajan adeel,nan suka dawo lokacin sun tarar da Mysha a falo tana ganinsu, tace an daiji kunya kuma sai Allah ya saka min yau girki na amma ka fita da ita, yace Mysha kiyi hakuri lalura ne yasa hakan, tace babu wani lalura ita bata da mota ne da ba zata ita kadai ba, nan Zeena tayi ciki da gudu tana kokarin amai, shima yabi ta, toh fa nan Mysha kanta ya kulle tare da tambaya kardai ace ciki gareta, kai anya bata da komai taya hakan ma zai faru, tace inko cikin ne dana bani ni tunda na haifi daya har yanzu shuru amma ace ita ta samu aiko dana yarda namiji munafiki ne, nan ta zauna tana ta tunani kala2
Maryam obamββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to my fans πππ»
1β£3β£0β£to1β£3β£5β£
Jin adeel ya dade bai fito ba yasa tabi bayanshi, ta shiga falon taje kofan d’akin Zeena din tana ta nocking, adeel ya fito Zeena na biye dashi, tace toh Malam sai muje haka, cin amanan ya isa, ya kalleta yace haba Mysha wannan wani irin magana ne, tace ai dole kace haka, inka manta yau girki nane dan mai zaisa ka fita da ita, sannan kuma yanzu ka biyota d’aki, yace bata jin dadi ne na kaita asibiti shine laifi, ko kece ran girkinta baki da lafiya bata isa ta hanani kaiki asibiti ba, ai dole kace haka, tunda ka zama mara adalci, ganin tana ta surfo magana ga Zeena a wajan yaja hannunta suka fita, d’akinta yayi da ita sannan ya sake ta, yace kina da hankali kuwa Mysha anya baki fara tabuwa ba kuwa, wlh da hankali na, dan mai zaka cuceni sannan inki magana, dan nayi magana shine kake cemin banda hankali, wlh da hankali na sarai, yace toh wannan bala’in da kikeyi mai zai amfana miki, miye riban shi, tayi tsaki tare da fadin ai wlh bala’i yanzu na fara indai akace cuta na za’a dinga yi, ahmad dake kwance ya tashi yana kuka ganin yanda mamanshi ke ihu, adeel yayi sauri ya dauke shi, yana rarrashin shi, tayi tsaki ta amshi danta tayi falo dashi, adeel yace Allah ya shiryaki yasa ki gane.
Zeena wannan cikin yana bata wahala, harta dan rame, ga yawan amai da takeyi, adeel yana tausaya mata sosai, yau itace da girki duk ta rasa mai zatayi mai dan sauki dan yanda take jin jikinta kaman ba zata iya komai ba, Jin sallama tayi da sauri ta tashi tare da fadin muryan wa nake ji, abda tazo da sauri tayi hugging din Zeena tare da fadin I miss you, sis,Zeena tayi dariya tace saukan yaushe, abda tace jiya na dawo muna hutu, Zeena tace kaga mutanan dubai yanda aka kara kyau, abda tayi dariya sannan tace naga kin rame kin kara haske kodai an samu abun ne, Zeena ta harare ta da wasa tace sa ido, daka zuwa har kin fara, abda tayi dariya tace aiko makaho ya ganki yasan akwai magana, Zeena tace iye yarinya an iya hausa, abda tace sai kace ba yar hausawa ba, dan nayi wannan karamin hausan, Zeena tayi dariya tace abda nayi kewanki wlh,, amma dai a nan zaki kwana koh, ta zaro ido tare da fadin rufamin asiri in kwana gidan siriki na, Zeena takai mata dukan wasa tace toh anty babba, suna cikin haka saiga Mysha ta kallesu tayi tsaki tare da fadin an dai bani, abda ta kwashe da dariya Mysha tace ke dawa kike wannan dariyan badai dani kike ba, abda tace da wanda ya tsargu dashi nake, nan Mysha ta hasala tace ke bari kiji in kina tashen rashin kunyanki toh wlh kasan da wanda kike don bake bace sa’a ta, abda ta tashi Zeena tace abda kiyi shuru, abda tace wlh Zeena ba zanyi shuru ba, ta kalli Mysha sama da kasa tace ke yanzu ko kunya bakya ji, duk cin amanan da kikayi amma kinzo kina wani kumfan baki, nan Mysha ta d’aga hannu zata mareta abda ta rike hannun tace idan Zeena kina mata ita tana kyaleki toh ni ba ita bace dan bazan dauki raini ba, kinci daraja daya duk da irin mugun halin ki, ke abokiyar zaman yar uwata ce, amma dasai na miki dukan tsiya wlh, Mysha ta tsaya tana kallon ta da mamaki, tace lallai yarinya kinyi baki sai kin San ni kika ma rashin kunya, abda tace ke din banza mai zakiyi, kiyi duk abunda za kiyi ina dai2 dake, ganin abda dagaske take kuma inta biye mata komai zai iya faruwa tayi saurin barin wajan, abda ta kalli Zeena tace dama irin wannan zaman kukeyi, Zeena tace mai yasa zaki mata haka, karki manta AMINIYA TA CE, kuma abokiyar zama na, abda tace wannan ba aminiyar ki bace domin inda aminiyarki ce baza ta miki abunda tayi ba, wlh sis Mysha bata da kunya kuma bata san abunda takeyi ba, in banda raini muna zaman mu tazo ta tsokane mu, Zeena tace aida baki kulata ba dakin barta da halinta, ni yanzu mubar wannan zancen, ummi tace auren bros zaheer nan da wata biyu, kina nan har sai anyi bikin ko zaki koma, abda tace babu inda zani sai an gama bikin, Zeena tace zaki missing abubuwa fah, tace hutun yana da tsawo, tace au yanzu naji magana,nan suka tashi sukayi kitchen suka daura girki, cikin kan kanin lokaci suka gama, abda tayi shirin tafiya gida Zeena tace ta kwana amma taki tace gida zata, adeel yayi sallama ya shigo yace yau wa nake gani, abda tayi dariya tace inlow sai yanzu ka dawo, saida kaga zan tafi, yace amin hakuri ban san kinzo ba da nabar komai na dawo, yace amma laifin Zeena ne da bata kirani ba, abda tace toh ni zan gudu, adeel yace ki mana kwana biyu mana, tace wai ni gidan mu zan wuce ko ku barni in wuce ko in muku kuka, Zeena tace toh bismillah, tayi dariya tare da fadin na tafi, Zeena tace tazo gobe ta taya ta aiki, tace shikenan, ta wuce, adeel ya shiga d’akin Zeena yayi wanka sannan ya shirya ya kalli Zeena yace kullum kina kara kyau ta dan turo mai baki tace a haka din, yayi dariya yace kinfi kyau ai a hakan, tace muje kayi dinner suka fita tare, yace ina Mysha tace tana d’akinta, yace ina zuwa ya nufi gefen Mysha din, ya ganta a kwance yace ta tashi suje suyi dinner, tace toh ta tashi suka fita tare, ganin Zeena a dinning din yasa ta daure fuska, Zeena ta bude abincin nan warin abincin ya hau mata kai tayi d’akinta da gudu, adeel ya bita nan Mysha tace wlh da sake ni za’a mayar yar iska, wato ciki ya mata ni kuma ko oho kenan, toh wlh adeel baka isa ba, itama tabi bayansu taga adeel din yana rike da Zeena yana wani lallaba ta, tace toh munafiki yanzu ciki ka mata toh wlh baka isa ba, yau sai anyi ta, da mamaki yake kallon ta, yace Mysha ki kama bakin ki, tace ai dole kace haka tunda kaci Amana ta, yace amanarki name naci, tace dan mai zaisa ka mata ciki wlh baka isa ba sai anyi ta, ta kare yau din nan, ta dinga magana ta inda take shiga bata nan take fita ba, ranshi yayi mugun baci nan ya matsa kusa da ita ya wanke ta da mari, ta saki ihu ta matsa kusa da Zeena tana kokarin dukanta.
Maryam obamββ
[4/4, 8:05 PM] Hawwa: π©ββ€βπβπ©AMINIYA TA CEπ©ββ€βπβπ©
π
π
NAββ
MARYAM ALHASSAN DAN’IYA ππ
Dedicated this page to my fans πππ»
1β£3β£5β£to1β£4β£0β£
Adeel yayi sauri ya janyo ta, Zeena wanda tayi Suman tsaye dan tsoro, tace ka sake ni, yau sai anyi ta, ta kare, ta kuma zabura zata nufi Zeena, ganin haka Zeena ta matsa da sauri tayi baya, shi kuma ya kuma janyo ta, tare da marinta har sau biyu yace kije na sakeki saki daya,nan komai nata ya tsaya, da mamaki ta kalle shi, tace adeel saki, nika saka takan wannan banzan, ya kalleta yace wannan ya rage naki ya kama hannun Zeena sukai ciki, suka barta a nan, bayan sun shiga Zeena harda sama d’akin key tayi adeel yayi murmushi, dan tana ganin Mysha Zata iya shigowa ciki, adeel ya zauna akan gadon d’akin ya daura hannu akan kanshi, duk sai yaba Zeena tausayi, ta matsa kusa dashi tace adeel gaskiya banji dadin abun da kayi ba, yasa mata hannu a baki alaman tayi shuru,yace Zeena wani kalan adalci ne banma Mysha amma duk bata gani, ban taba cin amanarta ba ran girkin ta, amma ita bata da wani Abu kullum sai zargi, na rasa wannan irin halin nata, Ina zama da ita ne saboda ke da kuma yarona, amma yanzu na gaji gwara ta wuce, dan wata rana zata iyayi miki komai karta je ta kashe min baby, Zeena tayi shuru bata ce komai ba, ganin haka yasa yace ki daina tunani kar kisa baby dina cikin damuwa shima, tayi dan murmushin yake,ita harga Allah bata ji dadin sakin daya ma Mysha ba.
Mysha ta nufa d’akin ta, tana ta rusa kuka, tare dajin haushin Zeena, tace Zeena saboda ke adeel ya sake ni, yanda ya sake ni kema haka saiya sake ki, dan bazan barki ba, ta diba wasu daka kayanta tasa a akwati tayi gidansu ita da ahmad, tana shiga taga mamanta da gudu ta fad’a kanta tana kuka, mahaifiyar ta duk ta rude tana tambaya lafiya, mai ya faru, tace mum adeel ya sake ni, maman tace what saki, tace eh mum, tace kiyi shuru ki daina kuka bari in kira dady dinki, maman ta tashi ta nufi d’akin dad din Mysha din, Jim kadan sai gasu tare sun fito, mahaifin ta, yace maiya faru, nan ta fad’a mishi karya da gaskiya ranshi ya baci yace tayi shuru taje d’aki zai nemi adeel din, maman tace neman shi akan me mai za’a mai kawai ka barshi, yace ai ba’a haka dole shima inji ta bakinshi wannan shine adalci, tace wani adalci bayan ya wulakanta mana y’a harda saki kuma, ni na yarda da y’ata ba zata min karya ba, yace hakane amma koma dai miye dole inji ta bakin shi, yana fad’in haka ya koma d’aki, ranan Mysha kasa bacci tayi sai aikin kuka, tabbas tana son adeel irin son da ba zata iya musultawa ba, Zeena kece silan komai saboda ke ya sake ni, tayi murmushi tare da fad’in adeel dole in koma gidanka ko dan darajan dana,.
Zeena tana falo tayi uban tagumi kaman wacce aka ma mutuwa, adeel ya fito daga d’aki yaga yanda ta zabga tagumi, ya karasa gareta tare da cire mata hannun, yace tunanin mai kikeyi haka Zeena, tayi dan nishi sannan tace adeel dan Allah kayi hakuri ka dawo da Mysha, jin haka yasa ya daure fuska tare da fadin indai kika ci gaba da fad’a min wannan maganan zaki ga fushi na, tace adeel nasan bata kyauta ba amβ¦. Ya d’aga mata hannu tare da fadin ni na fita, ta bishi da kallo cikin takaici, ita dai tana so ya dawo da Mysha dan tasan Mysha tana son adeel sosai kuma sonshi yasa take duk abunda take yi, haka ranan Zeena ta zauna cikin tunani.
Mysha duk irin gatan da mum dinta take mata, bata jin dadin zaman gidan, ita burinta yau ace ta koma gidan adeel, domin inta tuna yana tare da Zeena wani bakin ciki take ji, tare da tsananta, Zeena na rasa dame kika fini da yasa komai nake so sai kin raba ni dashi, kowa ke yake so, miye banda shi wanda ke kike dashi, kukan ahmad ne yasa tayi sauri ta dauke shi, tana jijjiga shi,
Mahaifin Mysha ya kira adeel, akan maiya had’a shi da Mysha nan ya fada mishi irin abubuwan da take mai, ran mahaifin nata ya baci sosai, yace ma adeel ya gode saiya neme shi sukayi sallama, yana zuwa gida ya kira Mysha ita ma mamanta ta fito, nan ya zayyane mata abun da Mysha tayi, itama taji mamaki tace Mysha ce take hakan, gaban Mysha sai fad’i yake dan tasan yau ta bani, mahaifin nata yace kin kyauta tunda zaman gida kika zaba saiki zauna, kin samu yaro mai hakuri kinje kina mai abunda kika ga dama, inda wani ne daya dade da koranki ko kuma ya miki dukan tsiya, tunda baki da kirki daka yau zan kafa miki doka bake ba fita, ki zauna a gida tunda shi kike so mutuniyar banza, mamanta tace Mysha ina kika koyo wannan bakin halin wanda ban sanki dashi ba, ke kin taba ganin inama babanki haka, babu abunda Mysha take sai kuka, domin tasan tunda dad dinta yayi fushi da ita, tasan yanzu bata ba wani jin dadi, dad dinta yace ta tashi ta basu waje, ta tashi da gudu tayi d’aki tana aikin kuka,
Bikin zaheer ya matso anata shirye2, dakyar adeel ya bar Zeena taje gida tayi sati daya, anata shagalin biki gidansu Zeena ya cika da mutane sosai, an daura auren zaheer da amaryan shi Zaynab yar garin adamawa, washe garin daurin dauren zasu koma Japan domin ya samu aiki a can haka ko akayi ango da amarya suka wuce yan biki kowa ya watse, adeel ya kira Zeena yace yaushe zaki dawo, tace nan da 2week dan na gaji da hidiman biki, Ina so in dan huta, ya kashe Wayan Jim kadan ya kuma kira yace fito ina kofar gidanku, yana gama fadin haka ya kashe Wayan,sai gata ta fito ta zagaya ta shiga cikin motan tana shiga yaja suka wuce, tace ya zaka wuce dani banyi ma ummi sallama ba, yace ki kirata a waya, tun daka lokacin bata kuma cewa komai ba har suka isa gida, ranan Zeena tasan mijinta yayi kewanta kaman itama yanda tayi,
Mysha ce zaune ahmad nata wasa ta rame da danyi duhu, kullum tana cikin tunani ga iyayenta sun daina sakan mata sosai, mu samman ma dady dinta, gashi bata fita ko ina, inta kira adeel baya dauka, sai dai ta mai text tana bashi hakuri akan ya maidata, shima babu reply, sai a yanzu take nadaman abunda tayi, wani hawaye ya xubo mata, adeel sanka da kuma kishinka yasa nayi duk wa innan abubuwan, gashi yanzu ya tashi a banza tunda ka sakeni, lokaci daya taji tana nadaman abunda tayi, domin tasan nata kishin ya wuce musali,cikin wannan halin mum dinta ta sameta a ciki, ta tausaya ma yar tata, tace Mysha ki daina wannan kukan domin bashi da amfani, kuma komai Ya faru ke kika jama kanki, tace mum wlh ina son adeel dan Allah mum kisa dady ya mishi magana ya mayar dani, mamanta tayi shuru, tace Mysha dad dinki yayi fushi sosai dakyar in zaima adeel magana amma zan jaraba bashi hakuri.
Cikin Zeena yakai wata7 tana samun kulawa wajan adeel, kullum yana nuna mata so da kauna, itama tana iya kokarin ta wajan nuna mishi kulawa, suna zaune a falo wayanta yayi ringing ta dauka taga number ne, ta kara a kunne jin muryan Mysha tayi tana kuka, tace Zeena dan Allah kiyi hakuri akan abunda na miki, Zeena tace babu komai, sannan tace dan Allah kisa adeel ya dawo dani, wlh Zeena Allah ya jarabce ni da sonshi, Zeena tayi dan murmushi wanda bai kai ciki ba, tace zan mai magana duk yanda mukai zaki jini, ta kashe Wayan sannan ta kalli adeel wanda ya bata rai, tace lafiya kuwa naga ka daure fuska, yace banso kimin maganan Mysha plz, tace haba adeel karfa ka manta akwai yaro a tsakaninku ko danshi ya kamata kayi hakuri ka dawo da ita, yace Zeena bazan iya dawowa da Mysha ba, domin Mysha ba macen aure bace, Zeena tayi kaman za tayi kuka tace adeel ka dawo da ita saboda Allah, badan halinta ba, kuma na tabbata tayi nadama tunda harta kirani tana kuka akan inyi hakuri akan abunda tamin, nan yayi shuru dakyar Zeena ta samu ta shawo kanshi ya yarda,..
Adeel da Mysha sun dawo matsayin mata da miji Mysha ta canza kaman ba ita ba, komai ita take ma Zeena tace bata so tana komai tunda ba ita kadai bace, adeel har dan kiba yayi saboda yanzu ya sami kwanciyan hankali a gidanshi,
Adeel shi ya dauke biya masu twins karatu yana musu hidima kaman yaran daya haifa, Zeena kullum tana kara godewa Allah akan baiwar da yayi mata, ita da Mysha sun fara business Ana Kawo musu kaya daka waje suna sai dawa, Mysha da Zeena Ana zaune Ana fira, Zeena taji kaman ana tsungulinta a mara, tun tana ji kadan harta fara ji sosai, nan ta saki kara Mysha tayi sauri ta riketa tana fadin Zeena lafiya maike damun ki, tace Marana, dakyar Mysha tasa ta a mota sukai asibiti suna zuwa akace haiyuwa ne, akai labour room da ita ko minti talatin ba ayi ba ta haifa yarta mace, sai a sannan Mysha ta kira adeel take fad’a mai, zo kuga murna nan da nan yazo asibitin, yaga yar kaman Zeena sai dai ta dauko kalan hancin shi, yarinyan kyakyawa,
Zeena da baby dinta suna samun kula wajan Mysha sosai, ranan suna yar taci sunan ummi habiba, suke kiranta da ma-ma, mum tasai ma yarinyan kaya da yawa, haka itama ummi, ga wanda Mysha itama tayi, abda itama tayi aure ta auri wani saurayinta wanda suke san juna sosai, a dubai zata zauna saboda karatun ta.
BAYAN SHEKARA BIYAR
Zeena zaune da yaranta su uku, ma-ma da sadeeq sai anan, suna ta wasa, Mysha ta shigo ita da yaranta da gudu yaran suka tashi suna tsalle na ganin yan uwansu, Zeena tace har kun dawo kunyi sauri, Mysha tace wlh kuwa duk na gaji, itama yaran Mysha biyu, ahmad da saudat, nan yaran sukai waje suna wasa, ita kuma da Mysha suna ta hira, har adeel ya dawo, shima ya zauna anayi dashi, yace yanzu dai kun daina bani kulawa aure zan kara, jin haka Zeena ta tamke fuska, Mysha tace ai babu wacce ta isa ta shigo wannan gidan, yace haka kika ce, zaku gani ai jin haka Zeena tabar wajan, Mysha ta saki dariya tare da fadin sai kaje kaba aminiyata hakuri, yayi dariya shima sannan ya tashi ya nufi d’akin Zeena din, tana ganin shi ta kawar dakai gefe, yayi dariya yace haba amarya ta, jin haka ta saki kuka tana fadin ni ka daina cemin amarya wanda zaka aura ita zaka kira da haka, yayi dariya tare da fadin kece amarya ta, tunda na sameki na cire ko wace mace a raina, taji dadin abun da yace, yace ashe dai ana kishi na, ta rufe fuskanta da hannu, yayi dariya nan suka fada faranta ma juna nima dai a nan zan tsaya.
ALHAMDULILLAH
Zaku iya samun novels dina a grp dina :maryam obam novels
Maryam obam ββ
08060860886