Hausa Novels

AKAN FREE WEEDING PICTURE

AKAN FREE WEEDING PICTURE 1&5 FREE BOOK

Related Articles
 ```

_RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MALAM... AMMIEYN KHAUSAR... TAURARUWAR ROYAL STAR WRITE'S CE💃 HEEDAH HYDAR OSTHMAN_
  *MARUBUCIYAR FAHAT, DR HEESHAM PAID, MAIZANAN KANTA PAID, BAƘIN KISHI PAID, ABBAKAR SARAKIEY PAID, ZUCIYAR NAMIJI, SAINA KASHE MIJINA, SILAR ƊA NAMIJI, BR KHALEEL, RAUNIN MACCE, SO SIRRIN ZUCIYA,, AND NOW AKAN  FREE WEEDING PICTURE....*

_ƊAN ADAM AJIZINE KUMA NIƊIN YAR ADAM CE DOLE NAZAMO MAI MANTUWA DAMA AIKATA KUSKURE SABODA HAKA INA ROƘON ALLAH DAMAKU MASOYANA DIK INDA KUKA SAMENI DA KUSKURE KUMUN UZURI HAƊIDA YAFIYA....... INA ROƘON ALLAH YARDA YABAN DAMAR FARA WANNAN LITTAFIN TUESDAY 7/6/2022 JUN ALLAH YASA NA KAMMALASHI LFY INDA NAKEDA KUSKURE ALLAH KAYAFEMUN..... INAJIN DAƊIN BIYAYARDA KUKEMUN MASOYANA ALLAH YABARMU TARE_

YABON GWANI YAZAMA DOLE INA MIƘA GAISUWA TA MUSAMMAN GAREKI SISTER SHAMSIYYA,,,,,, BAN MANTAKI BA MAICIKI MARYAM YUSEEF ALLAH YABAR ƘAUNATA GAREKU INASONKU SOSAI

INA JINDAƊIN YABO DAYAWAN SAƘONNINKU DANAKE SAMU MASOYANA ALLAH YAƘARA MUNA HAƘURI DA JUNA,,, INAJIDAKU ILAHIRIN ƘUNGIYAR ROYAL WRITE’S ASSOCITION,,,,, HAKAMA KU ƳAN GROUP ƊINA NA NOVELS OF MUJAHEEDAH GROUP TINDAGA KAN NA WHATSAPP HARZUWA NA FACEBOOK ALLAH YABAR ƘAUNA MUJAHEEDAH MATAR MLM NAYINKU OVER

BADAN JINDAƊI KAWAI NAKE RUBUTUNA BA DAN MUƊAUKE DARUSUKA MASU KYAU MUWATSARDA MARASA KYAU ALLAH KABAMU IKON ƊAUKA DA WATSARWA AMEEN

BISMILLAHI RAHMANI RAHEEM

   ____✍️ Wani matsakaicin gida na yada zango bazaka kirasu masu ƙuɗiba kuma bazaka kirasu talakawa ba, Ciki na kutsa kai ganin mutane nata kai kawo ciki gadik kan Alamau dai Ana bikine A gidan.

Mutane dayawa nagani kowa da Aikinda ya keyi ɗakin da nake jiyo shewar ƴan mata nakutsa kaiciki,

Zaune gaban madubi na hango wata budurwa farace basosai ba sai faman kwalliya takesha bakin nan harkunne (Araina nace lalle Amaran yanzu haka suke sam basajin nauyi ko kunya ganin ranar bikinsu ce kamar dai Miemie Amaryar zamani littafin Salimat sani littafin yaƙayatu gsky 200 kawai zaka zaki biya ta mallaka maka shi)

Wayar ta tafara ringing Amira miƙomun wayata wataƙilma Sahir ne kekirana to kunjima baku gamamun wannan kwalliyar ba wllh”

Miƙamata wayar tayi tanaɗan rakata da harara,

Ɗauka tayi Hello: baby kungama naku shirin ne,”?

“Sosai baby yanzu haka gamu ƙofar gidan naku kifito muwuce kawai,”

“Owk gani nan zuwa,”

Kit takatse kiran tana ƙoƙarin hanyo wani net ɗin gyale tana sakawa,

 "Kungani gashinan yazo zamuje *FREE WEEDING PICTURE'S* So kujirani Anan idan nadawo maje gyaran gashi ɗin,"

Ɗago kai Amira tayi taƙare mata kallo tsaf, Sanye take cikin wani Yadi mai net wanda Amare kesawa dik yawani ɗameta ɗinkin riga da skert ne ta ɗaure gashinta da ribom wanda tafidashi waje rabin gashin Suraiyya kenan dama kyakykyawa ce balantana gashi tasha kwalliya, “Yanzu Suraiyya saboda Allah haka zaki fita kibishi wai FREE WEEDING PICTURE’S da wannan shegen ɗinkin dubu dik jikinki waje fa,”

“Ikon Allah! to sokike nasaka hijab? ko naje nasa kayan mama,”? Aƙufule tayi maganar

“Ni bance hakaba Suraiyya Amma inason kifahimmata wannan FREE WEEDING PICTURE’S ɗin bafa dole bane inshourt ma idan munduba hadith’s wllh haramun ne,”

“Allahu Akbar! Ashe muna tare da malama bamu sani ba,” Cewar Nazla data faɗa Awani sheƙe tana fari da ido

“Uwar malamai dai da sa’ido wllh wannan da itace Uwata ko yayata da bani tacimu ko numfashi zamuyi saita tuhume mu Akai! so kike nafasa konace masa bazani ba,”?

“Ba Maganar malanta Anan gaskiyace dai kawai nake faɗa muku wllh FREE WEEDING PICTURE’S ɗin nan haramun ne dik lalacewar zamani ne yakawoshi dama halakat damu da yahudawa kesonyi, idan yazama dole kibari sai Anɗaura saikuyi Acan idan kuntare mana Amma yanzu ba Igiyar Auranki kanshi zakibishi wai photo? kuma da wannan Arniyar shigar? Haba suraiyya kada kibiyewa su Nazla wllh haramun ne hakan,”

Mtswwwwww dogon tsaki kawai taja batabi takantaba tafice Abunta, taƙofar baya tabi dan batason tahaɗu da Umma tasan Halinsu ɗaya da Amira dama Abba indama Ace sune suka haifeta tasan data fara wa’azin bakin layi..

Tana fita tahange motarsa shine ƙaɗai cike dan haka tabuɗe tashige Abunta tanamai masa sallama,

Ƙura mata ido yayi kamar wani maye kafin Yace” kinyi kyau Amaryata,”

Ɗan fari da ido tamasa kafin tace,”kaima haka Angona, kaga muje kafin Abba yadawo kuma banason hankalin su yagano bana gidan,”

Jan motar yayi suka nufe Aƙasaitaccen gidan photon MANNIR PHOTO GRAPER
Gidan photon yahaɗu sosai Anan suka shiga sukaɗan zauna dan cike yake damutane Kafin Azo kansu………………….

OHH ANAN ZANƊAN DAKATA IDAN WANNAN LITTAFIN YAFARA MUKU TONAGA COMMENT’S MATAR MLM CE DAI AMMIEYN KHAUSAR……

BASEERATA ITACE ARZIKINA😍

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948
AKAN FREE WEEDING PICTURE’S FREE BOOK

RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MALAM, AMMIEYN KHAUSAR… HEEDAH HYDAR OSTHMAN…. TAURARUWAR ROYAL STAR WRITER’S

🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪 UP-UP-UP

🍂”ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU”🍂

GAJEREN LABARI

🅿️10&15

    Saida layin yazo kansu suka ƙarasa inda Ake pic ɗin, Nanfa naga styel kala kala *(NIKAM MATAR MLM SAIDAI NACE ALLAH SHIRYA ARAINA NACE NIKAM BAMAI SANI YIN WANNAN HAUKAR DAN BAWANI ALBARKA KO DATTAKU ZUWA TARBIYA HAƊIDA TSORON ALLAH ACIKIN WANNAN TABBAS FREE WEEDING PICTURE'S NA YAHUDAWA NE AMMA GASHI SUN ƁATAMU MUN ƊAUKA KAMAR WAYEWA NE ALHALIN WANNAN ƘAUYANCINE GADIK WADDA TAKEDA TAUHIDI.... KUYI HƘR FA DAN TUNATARWA NAKE BADAN CIN ZARAFI BA ASANNU ZAKU GANO MANUFAR TAWA)*


   Zama yayi kan kujerar da Aka tanadar dan ɗaukar pic ɗin, mai photon ya bata umarnin tazauna kan cinyarsa, bakunya balantana tsoron Allah tazauna shikuwa yawani naɗo hannayensa A waist ɗinta yariƙe ta suka zubawa juna ido Sannan Aka ɗauke photon,  

Wani style yasake basu na sukama hannayen juna suna kallon junansu, Nanma sukayi yasake basu na rungumar juna, Kai wa’iyazubillah Allh kashiryamu Allh kaciremana wannan masifar ta free weeding Picture Acikin Al’ummar mu ta musulmai plzz kuce Ameen……

Haka dai suka ƙarashe rashin tarbiyarsu sukawuce gida saikusan yamma likis suka koma, 

Koda takoma ƙawayen nata bakowa Amira ce kawai ta tarar A palourn tana Azkar ɗinta kammala sallarta kenan,

Ko sallama batayi ba dan da sannan tashiga kawai tafaɗa toilet tawatso ruwa tafito zane kawai taɗaura tahaye gado Abunta Tana miƙa dan tagaji sosai.,,

Kallonta Amira tayi Tace,” Yanzu sai yanzu zakidawo? kuma bako sallama balantana kiyi sallah kinzo kinwani kwanta haba Surayya meyasa kike wasu Abubuwa wani sa’ir kamar ba ƴar musulmai ba,”?

Ɗagowa Surayya tayi cikin masifa da ɓacin rai tace,” Kinfaye shishshigi wllh Amira banson Abinda kikemun wai ina ruwanki dani? ke zanma sallar? kinga idan batayani murna kikazo ba so kikoma inda kika fita kawai,”

A wannan lokacin ran Amira yafara ɓaci daga faɗar gaskiya? koda yake dama hakan Abun yake dik wani Mai Aikata badaidai ba idan kayi yunƙurin sanar dashi ko ganar dashi to jahilcinsa da ƙarancin tunaninsa zai hana ya fahimceka,

Batace mata komai ba tamiƙe Amma taƙudiri barin gidan zuwa gobe dan bazata iyazaman ganin wannan baƙin cikin ba…..

WACECE AMIRA? MEYE ALAƘARTA DASU SURAYYA? WACECE NAZLA?⁉️⁉️⁉️⁉️

Nazla Ƙawar surayya ce kanta narawa sam bata damu da Abunda yake yasaɓama tarbiyarta ba koma meye idan taga dama shizatayi Hakan yasami Asali tindaga mahaifinta daya sakemata ƙuɗi sam batada tarbiya Itace Rawa tik-tok facebook whatsApp istergram dadai sauransu, Sun haɗu da Surayya Awani mall ne tindaga ranar suka zama Abokai sannu Ahankali Nazla tajefa Surayya irin rayuwarta tasheƙe Aya suyi vide’o su ɗaura kan medi’a bawani Abu bane garesu Aganinsu wannan shine wayewar……

Amira ƴace ga Ƙanwar Mahaifinta Mlm sule tana da tarbiya sosai bata ƙawaye shiyasa sam rayuwarta takeda haske baruwanta da tallar kanta Amedi’a,

Abban Surayya na mugu son Amira dan kamun kanta da ɗabi’unta na birgeshi hakan yasa dakanshi yanemi subarta tazauna gurinshi,

Sunshaƙu sosai da Surayya saidai Surayya da Nazla sungwalje rayukansu….

Kawo kayan Surayya da Akayine yasa Amira tazo tazo dan taɗan jima da komawa gida tan randa taje bikin saukar ta bata dawoba saida Aka kawo engagement ɗin Surayya tazo, ……

Wannan kenan BARI MUKOMA LABARIN

BASEERATA ITACE ARZIKINA😍

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948

AKAN FREE WEEDING PICTURE’S FREE BOOK

RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MALAM, AMMIEYN KHAUSAR… HEEDAH HYDAR OSTHMAN…. TAURARUWAR ROYAL STAR WRITER’S

🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪 UP-UP-UP

🍂”ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU”🍂

_KUYI HAƘURI KUDA KUKE ƘOƘARIN GANIN NAYI AMFANI DA PRE NIKUMA INA AMFANI DA FREE BANASON GUJE ƘA’IDAR RUBUTU NANE KUMA ATURANCE IDAN ZAKA RUBUTA FREE WEEDING (F) CE BA (P) WURIN PRONOUSING NE ZAKUJI KAMAR P AMMA ARUBUCE F CE KUYI HƘR KADA KUGA KAMAR NAƘI ƘARƁAR GYARANKU A’A BANWUCE GYARABA KUMA NAGODE NAJI DAƊI INSON GYARA AKODAYAUSHE)*

GAJEREN LABARI

🅿️20&25

  Nazla nahango sai shewa take tana ƙoɗa kyawonda Sahir da Surayya sukayi, itakuwa saidaɗi takeji Akafin wani lokaci tuni Naxla tasoma yaɗa pictures ɗin Amedi'a Aikuwa Abunka da medi'a tuni sukafara yaɗuwa har inda nikaina banyi tsammanin zasu kaiba,

Amira na zaune tana faman bawa Abban surayya Haƙuri shida Umma dan ma gwandashi da Umma dan yafita ɗaukar zafi

“Wannan ai zubarmana da mutunci ne akan me za’a fita wannan iskancin daga engagement saizuwa tallan jiki dan ma tsabar iskanci wai FREE WREEDIGN PICTURE’S Ko Aina wannan banzar Al’adar tafito? koda yake kema da laifinki Maryam iyakacin ki sake ma yarinyar nan tana faman iskanci kinkasa hanata sai gantali datake cikin gidan nawa kuma ƴata ce haka wai,”?

Cikin jin haushi yaƙarasa maganar

Umma tace,”Wllh mlm bansani ba bansan sanda Akayi wannan ɗanyen Aikin ba kuma inkaduba zamani ne yazo da haka kowama ai yanayi,”

” Zamani!? Zamanifa kikace Maryam, to idan wannan shine wayewar da zamanin to tabbas munshigo zamani mara kyau kuma mummunan zamani mara kyau kuma wannan banzar Al’adace ta ya hudawa da nasara dasuka zo suka ɓatamuna zuri’a, wai ke Amira ina surayya take ne yanzu,”?

Kanta Aƙasa cikin girmamawa Tace,”Abba tana tana tana……,”

“Amira ƙarya zakifara? kuma Akaina!,”?

Dasauri ta girgiza kai Tace,”A’a Abba tafita inda ƙawarta ne,”

“kingani ba maryam wannan shegiyar ƙawar tata wanda nake baƙincikin ganinsu dik ta ƙarasa ɓatamun ƴa ke kuwa kinzuba ido to wllh kusani bazan ɗauka ba wllh, kuma muddin wanda yaƙiji wllh bazaiƙi gani ba,”

Fuuuuu yabar wurin

“kingani ba nikam in Surayya bata kashemun Aure ba wllh nayi Arziki,” cewar Umma tana barin ɗakin…..

HABILA PALACE Ƙasaitaccen murin shaƙatawa da shan ice-cream Acan nahango Ango Sahir da Abokansa biyu suna yaba photunan,

Banda Muba da yaja fuska gefe

Sahir Yace ,”Waike photunan basu maka bane naga bakayi magana ba Akai,”?

“to mezance saboda Allah wannan ai ba Abun yabawa bane Abun haushi da ɓata tarbiya waiji kuba Aure ba amma kunwani riƙe juna, Wai FREE WEEDING PICTURE’S Wannan ai haramun ne wllh,”

“Allahu Akbar!!! mlm Muba mubarak,”

Tintsirewa da dariya sukayi dukansu,

Yazid Yace,”Amma dai gaskiya Wannan yarin yar Ƴar iskace gaskiya!,”

A ɗan fusace Sahir yace,” kamar ya ƴar iska kasan ƴar waye waima,”?

Shafa guntun gemunsa Yazid yayi “Ai ita ƴar iska baruwanta da zaman iyayenta nagari sarai nasan babanta malami ne amma da taɗauko halin Uban nata aibazata biyeka wannan ba kakuwa san matan kirki kamilallu bazasuyi wannan ba, inda ba ƴar hannu bace ai bazata yarda ba wllh wama yasani ko wani yariga ka sanin Abunda ke ƙasan,”

Aikuwa suka saka dariya banda muba dakecewa ,”kumata zato maikyau fa,”

“Wllh ƴar iskace yanzu koda wasa kana tinanin Ƴar’uwarta Amira ta aikata hakan,”?

Gyaɗa kai muba yayi Aransa yana gasgata maganar Yazid koba komai yasan surayya batada kamun kai Amiransa tafita…

Sannu Ahankali Zuciyar Sahir tafara ɗarsamasa Wasu Abubuwan Game da Surayya………………………………………………………………………………………………

[KUMUN AFUWA DASAMUN GAJEREN PAGE INA BUSY NE WLLH SABODA YAU AKE KAWO ENGAGEMENT ƊIN YAYATA WEDNES DAY 8/6/2022 JUN KUTAYAMU MURNA DA FATAN ALKHAIRI]

BASEERATA ITACE ARZIKINA😍

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948

AKAN FREE WEEDING PICTURE’S FREE BOOK

RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MALAM, AMMIEYN KHAUSAR… HEEDAH HYDAR OSTHMAN…. TAURARUWAR ROYAL STAR WRITER’S

🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪 UP-UP-UP

🍂”ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU”🍂

GAJEREN LABARI

🅿️29&30

SHARING RA’AYINE MAI RA’AYI ZAI IYAMUN KUMA INA GDY GAMASUYI MUSAMMAN DAN ALLAH

     A gidansu mubarak Ankai kayan Aurensu da Amira za'a haɗe bikin nasu da Surayya dik iyaƙoƙarin su Surayya Akan Amira taje suyi *FREE WEEDING PICTURE'S* Sam taƙi Amincewa, 

Shikanshi Abun bawani damunsa yayi ba hakan yasa Suke musu ɗaukar ƙauyawa dikansu…

 A yanzu Sahir yafara zargin Surayya dan lukata da dama yakan ganta A medi'a har mamaki yake idan yaga photunan ta Awata wayar itace startus itace kan d.p.
Yau Akafara program ɗinsu dik wata bidi'ar sukawai keyi banda Amira dan takafe baza tayi ba, dan Addini bance hakan ba,

Su Surayya kam Ansheƙe Aya Anci Ansha Araya Anwatsa medi’a,

Yaune Ake ɗaurin Aurensu kowa ya hallara Baban Angon kawai Akejira dama Angon.

Acan gida kuwa Aiba sai balbalin masifa yake Akan bazai yarda Sahir ya Aure Surayya ba shidai baisonta yarinyar bata masa ba Ayanzu yaga yarda FREE WEEDING PICTURES ɗinsu yazaga duniya kuma Abun bawani shawa yarinya ba kamun kai cewar Abba da ransa yake ɓace yana kallon photunan da wayar tasa……

Kan Sahir Aƙasa Azahiri yana son surayya saidai shima Ayanzu Ansoma ɗarsa masa kokwanto Akanta kuma da Alamar gaskiya sam batada kamun kai.

Mariya Mahaifiyar Sahir Tace,”Amma idan laifine ko ɗanka nada laifi dan tare sukayi photon ai kuma shine Ummul Haba isu dik wani tambaɗewar FREE WEEDING PICTURE’S Wllh cikin ɗari maza keda 98/100 parcent dan idan yace bayaso wllh baza’ayi shiba amma kaga ai suke zuwa suna ɗaukar mata Anazuwa Ayi ai,”

Lami ƙanwar Mahaifiyarsa Tace,”kinyi gaskiya Amma ni Aganina matana ma nada nasu laifin wallh hakama Iyayen nasu, hujja itace Engagement ba Aure bane Ace daga Ankawoshi saikiga Iyayen matan sundaina nasaka ido kan ƴarsu da saurayin kuma samarin ƴanzu ƙiris suke jira su tabbaka ta’asa wasuma da sunan Engagement ɗin wllh suke ɓata ƴaƴan mu sannan saiku kira yaron kufaɗa masa kufa bazaki bar iskancin nan na FREE WEEDING PICTURE’S ba idan yanason hotuna da matarsa baku hanaba bayan Anɗaura sai suje suyi nan ma sukiyaye sakashi medi’a,”

Ajiyar Zuciya Abba yasauke “kenan dai innafahimce ku nabari Aɗaura Auren,”?

“Eh Alhaji baikamata Amusu hakaba laifin na ƴarsu ne bawai nasuba,”

Jinjina kansa yayi kafin Yace,”Bari naje kaima kasameni can daga baya idan kagama shirin,”…………………………………………………

BASEERATA ITACE ARZIKINA😍

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948

AKAN FREE WEEDING PICTURE’S FREE BOOK

RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MALAM, AMMIEYN KHAUSAR… HEEDAH HYDAR OSTHMAN…. TAURARUWAR ROYAL STAR WRITER’S

🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪 UP-UP-UP

🍂”ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU”🍂

GAJEREN LABARI

 *🅿️31&40*

 Yana komawa ɗakin yayi kwanciyarsa.


 Yazid Yace,"Ah meye nakwanciya bayan kowa ya halla gun ɗaura Auren ka? katashi muje kada muƙara yin latti tinɗazum a Sarkin Azarɓaɓin nan Yakai yanata kiran wayar ka wai muyi sauri,"

Mtswww dogon tsaki kawai yaja yamaida idansa yarufe zuciyarsa zafi takemasa shidai Ayanzu baiƙi Afasa Auren nan ba wllh,.

Da mamaki Abbas Yace,”meke damunka yaufa ranar farinciki ce meye nadamuwa kaida Masoyiyarka Surayya ce fa,”

“Kunga malama kun Addabi Rayuwa ta wai uwatace ita Haba kurabu dani bazani ba!,”.

Kallon juna sukayi cike da mamakin meke damunsa ne wai,

Wayarsa tayi ƙarar shigowar saƙo,

Miƙamasa Yazid yayi "Gawayarka Anmaka text fa gashi Anata damunka da kira katashi dan Allah,"

Kamar bazai ƙarɓa ba kuma saiya ƙarɓa yaduba sabuwar number yagani Anturo saƙo

_KANA DAF DA CUTAR KANKA SAHIR AMMA DAN GANIWA IDANUWANKA SAIKA DUBA SAƘONA TA WHATSAPP ƊINKA_


Hannunsa harwa yake yayi saurin shiga WhatsApp ɗin ya buɗe data ganin Number yasa yashiga message ɗin, Abun mamaki da firgitarwa Surayya yaga ni jikin photon.

sanye take cikin farin yadi maitsantsi tasha make up tayi masifar kyau saidai dik rabin breast ɗinta kusan Abayyane suke saboda style ɗin ɗinkin bako mayafi kawai tasha ɗankwalin net gashin kanta dik bayyane, tana yima wani saurayin dake kusa da ita Murmushi yana Atsaye yana mata murmushi,”

Dik ilahirin jikinsa ya mutu take jikinsa ya hau karkarwa, Afili Yafurta “wllh bazata sakuba nafasa Auren wllh nafasa,”

Baiko saurare su Yazid dake tanbayarsa lafiya ba yazura wayarsa Aljihunsa Afirgice yabar ɗakin,

Yana fita yashiga motarsa A 360 yabar wurin ,
Suma hawan ɗayan motar sukayi sukabi bayansa A tsorace ganin irin gudun da yake tafkawa.

Yana ƙarasawa daidai lokacinda yafito daga motar yana ƙoƙarin kutsawa cikin jama’ar danganin yada katar da ɗaura Auran Amma ina.. lokaci yaƙure Shelar mutumin yada katar dashi dayake faɗin AURE YA ƊAURU TSAKANIN SAHIR USMAN DA SURAYYA IBRAHEEM AKAN SADAKI NAIRA DUBU ƊARI

Wata irin hajijiya Yaji baitsammani ba kawai yafaɗi gurin…………………

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948

 _BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

AKAN FREE WEEDING PICTURE’S FREE BOOK

RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MALAM, AMMIEYN KHAUSAR… HEEDAH HYDAR OSTHMAN…. TAURARUWAR ROYAL STAR WRITER’S

🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪 UP-UP-UP

🍂”ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU”🍂

GAJEREN LABARI

 *🅿️49&50*

Cikin tashin hankali su Yazid suka ɗaukeshi zuwa Asibiti dan su Abba naciki basu ganshi ba,

tashi zaune yayi haɗide dafe kansa dake sara masa yayi Ahankali yamiƙe tsaye lokacin Aƙalla 8:30 p.m,

Yazid “Inaza kaje ne baksan bakada lafiya ba,”?

“Ciwon dake damuna A zuci Yazid yafi wanda kedamuna Ajikina wai da gaske Anɗaura Auran nan dani,”?

“Ƙwarai kuwa” cewar Abba dake shigowa ɗakin,

“Meke damunka da Yazid baikirani yaga yamun ba Anan zakayi ta zama? kana tinanin dakwai Abunda zai ruguza Auran nan? Hunmmmmm kana hauka Ai baka isaba koma wane dalili gareka bana buƙatar jinsa yanzu inamai Umartarka katashi kaje kabar Amarya itaƙaɗai,”
Yana gama maganar yafice,

Badan yasoba suka nemi sallama sannan sukawuce dakatar dasu yayi dacewar baya buƙatar rakiyar yatafi Abunsa……..

Acan ɓangaren Amarya kuwa Abun yazama na tsegumi Anɗaura Aure Amma ba Ango Anyako Auren bana dole bane? haka dai Akayita cece kuce da gulmar.

Sosai Abun yaɓata ran Surayya dama Akwanakin nan tana ganin Wasu canji Atare dashi to amma ai wannan walaƙanci ne Ango yaƙi hallartar ɗaurin Aurensa,,,

Nazla kuwa ƙara zuzuta lamarin kawai take…

Kiransa tahauyi Amma sam takasa samu.

Akakai kowacce gidanta, Har Abokanta sukawatse ba labarin Zuwan Ango taci kuka sosai wannan Aibaƙaramin walaƙanci da tozartawa bane.

Har bacci yasoma ɗaukarta taji ƙarar buɗe gate dashigowar motar sa Buɗe idanuwanta tayi haɗida kallon Agogo 12:30 ne, fitowa tayi palourn daidai lokacin shima yashigo yana rufe ƙofar,

Cikin Rawar Murya Tace,”Sahir meyasa kamun wannan walaƙancin haka,”?

Ko kallon inda take baiyi ba yawuce ɗakinsa kawai………………

 _BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948

AKAN PRE_WEEDING PICTURE’S FREE BOOK

RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MALAM, AMMIEYN KHAUSAR… HEEDAH HYDAR OSTHMAN…. TAURARUWAR ROYAL STAR WRITER’S

🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪 UP-UP-UP

🍂”ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU”🍂

GAJEREN LABARI

 *🅿️55&60*

Durƙushewa Agunta tayi tasaki kuka maisauti Itadai batasan tamasa wani Abu ba, kuma iya saninta tasan yana sonta sosai Amma meyasa da rana tsaka zai sauya mata haka? kodai halin nasu ne nayaudara na maza zai nuna mata bayan ya mallaketa? Tajima tana kukan kan takoma ɗakinta takwanta tacigaba da kukan Ahakan har bacci yaɗauke ta,

 Dik kukan da tayi A palourn yanajinta Tausayinta yasomaji har ya miƙe zaije inda take take idanuwansa suka soma haskomasa pic's ɗin nan da Akatura masa komawa yayi yazauna Afili yafurta "kincutar da zukantanmu Surayya kin zubda tarbiyar iyayenki kin ruguza ƙimarki da soyayyar ki A idona wllh na tsaneki," Hawaye masu zafi suka sauka A idanuwansa nadamar Auran take dama Yasani natsatstsiya zai Aura daya sani dabai bari kyanta yaruɗeshi ba, Ahaka dai batare da shima yaci komai ba yanata faman saƙawa da kwancewa har bacci yaɗauke shi,..

Aɓangaren Amira da Mubarak kam sosai suka raya darensu da soyayya haɗida tattalin junansu..

   Ummansa ta Aiko musu Abinci tana ciki tana baccin gajiya shine yaƙarɓa yaɗora kan daining dama Driver ne yakawo Abincin ,

 Zama yayi kan daining ɗin yafara cin Abunsa dik da ƙasan ransa yana tinanin koya take yanzu?

Saukowa ƙasan tayi Yana sanye da yadi fari sol wanda yaƙara bayyanar da kyansa,
Itama farin yadine yasha ɗinkin doguwar riga wanda yamatse ta tsam yafito da yanayin halittarta tayi kyau sosai saidai idanuwan nata sunyi ja sosai Alamar taci kuka,

Tausayinta yaɗarsu A zuciyarta Amma yadage yaɗauke fuskarsa amma fa tamasa kyau sosai.

Ƙarasowa tayi inda yake harƙasa ta sunkuya tagaidashi,

Kamabar bazai Ansai ba kuma saiya dake Ya Ansa da “lafiya” yafaɗa Ataƙaice yana cigaba dacin Abincinsa,

Janyo kujerar da ke facing ɗinsa tayi tazauna tazubawa Abincin ido kawai Amma takasaci,

ɗago kansa yayi ganin bata zuba Abincin ba haɗa ido sukayi, narai narai tamasa da ido tanason fara kuka,

Aikuwa yamiƙe yana ture Abincin gabansa yana ƙoƙarin barin wurin,

Da sauri tamatso tariƙe ƙafarsa tana matso hawaye “Dan Allah Sahir kadaina mun irin wannan horon wllh yamun tsanani, laifin me namaka? tinda nazo gidanka bansan farinciki ba, kaƙi halartar ɗaurin Auren mu nasha tsangwama da zagin mutane Akan wannan sannan Ankawo ni gidanka nanma kaƙi kulani wannan shine sakayyar soyayyar da namaka da wadda kake mun? Haba sahir idan laifi namaka dan Allah kafaɗamun kamun Afuwa wllh nakasa jure wannan hukuncin naka dan Allh kayi haƙuri,”
Taƙarasa zancen cikin matsanancin kuka….

Sosai yaji tausayinta Amma tina pic ɗin yaƙara kular dashi, fisge ƙafarsa yayi yanajan dogon tsaki yabar gidan gaba ɗaya.,

Itakuwa zama tayi Anan tacigaba da rera kukanta…………….

(((((Godiya maiyawa gareki sister Shamsiyya lawar gandi naji daɗin tarbar da kikamun Amun ngd sosai Allh yaƙara muku zaman lpy keda Ahmad ɗinki, kuma Allh ya sauke ki lpy muzo cin Alale💃💃💃💃💃 Mujaheedah nayinki over wllh Allah yabarmu tare🥰💃💃))))))

  _BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948
AKAN PRE_WEEDING PICTURE’S FREE BOOK

RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MALAM, AMMIEYN KHAUSAR… HEEDAH HYDAR OSTHMAN…. TAURARUWAR ROYAL STAR WRITER’S

🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪 UP-UP-UP

🍂”ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU”🍂

GAJEREN LABARI

*🅿️69&70*

Yana fita direct inda suka saba zama yaje neman guri mara hayaniya yayi ya zauna yafaɗa kogin tinani,

Yazid ne ya ƙaraso gurin yayita Magana shida Muba Amma ina sahir yayi nisa cikin tinaninsa sam baijinsu,

bugun ƙafaɗarsa Muba yayi yana zaman yana fuskantarsa “Abokina meke damunka haka,”?

Ajiyar zuciya ya sauke tare da murmushin yaƙe “Bakomai, kawai nazo naɗansha iskane kuma nayi kewar gurin kunsan sabo,”

“Sahir ƙarya bata maka kyau saboda tinfarko kai ba maƙaryaci ba plzz kafaɗamana meke damunka mufa Abokan kane tinna yarinta,” Cewar Muba…

“Sosai gaskiya Muba yafaɗa kumani Aganina yakamata Ace munzarce Abokai munzama Ƴan’uwa,!”.
Cewar Yazid.

Ajiyar zuciya ya sauke ,” Hakane kuna da gaskiya kunzaman kamar yan uwana naɗauke ku Amma kawai dai kutayani Addu’a dan Allah,”

“Shikenan Allah yamana maganin damauwar mu,”
Cewar Yazid.

Da Ameen suka Ansa,

Dagana suka ɗauko wata fira daban dik da Muba ya fahimce matsalar Sahir daga gidansa ne Amma saiya share hakan baihana yaƙudiri kawo musu gyara cikin matsalar tasu ba..

Kwanaki sunci gaba da tafiya Ayanzu har hutun Sahir yaƙare haryanzu ko ɗakinta baitaɓa shigaba balantana wani Abu yashiga tsakaninsu, kuma baifaɗawa kowa Abunda keransa ba, dik muba yazo da matarsa juyin duniya yafaɗa Amma yaƙi, harda barazanar faɗawa su Abba Muba yayi Amma ina Sahir yakafe yaƙi faɗin komai Akai….

Akwana Atashi bikin naxla yazo, tindaga kan t.v, redi’o, mujallu, wayoyin, whatsApp, facebook, istergram, twiter, opera, 2go, tik tok, dai dai sauran su dik wata medi’a saida ta haska PRE_WEEDING PICTURE’S Na Auren Naxla da yakuba, Abunda yajanyo ɗinbin cecekuce na Al’umma..

Zaune yake kan 2’Cter yana faman signing wasu file dake gabansa sanye yake da 3’quater bako riga jikinsa Ga Alamadai yanajin zafi Hankalinsa yana kan Aikinsa sam baiji sallamarta ba, kawai motsinda yaji gaban sana yasa yaɗago saiko suka haɗa ido, kallon idan juna suke, kowanne cikin tsabar ƙauna da missing ɗan’uwansa bama kamar ita, tayi rama sosai, shikanshi yarame Amma tata ramar tafi tashi fitowa,
Har tsoro saida yaji ganin irin ramar tata dama haka tadawo shifa kusan sati 3 baigantaba sunan suna gida ɗayane kawai Amma sam baya son ganinta wani lokacinma mantawa yake tana gidan wllh,

Saurin ɗauke idanta tayi dan bata taɓa ganinsa hakan ba sai yau bashiba kowanne namiji ma bata taɓa ganinsa hakan ba,

Shima ɗauke kansa yayi yacigaba da aikinsa zuciyarsa naɗarsa masa tausayinta Amma sheɗan yanason firƙarfinsa dan pic ɗin ne yashiga tinanowa take yahaɗe rai,”Malama lafiya kika zo kikawani sani gaba haka,”?

Cikin rawar murya Tace,”A’a ba…ko…mai.. kawai… inason..kaban… izini… zanje bikin Ƙawata Naxla ne Anfara Ayau.,”

“Anfara iskancin ba, Ai tinda sheƙe Ayane dole kiri rawar jikin zuwa dagan kinga saiki haɗu da ɗan iskan naki ba, you are free zaki iya tafiya Dik dai wannan da yace Muguwar rawar zaitaka to zaiga miyagun makallata!!,”

Cikin mamaki darashin gano inda maganarsa tadosa ,Tace”Banba himceka ba Sahir me kake nufi,”?

“Kinga malama banason iskanci da raini wato kinrainani ko? shine harda neman nasake maimaitamiki magana ba, wllh tashi kibar nan yanzu kona miki Abunda bahalina ba wllh nadakeki na ɓallaki, kije kita zuwa ni ba ruwana!!!,”..

Ganin batada niyar tashi yasa Yamiƙe yabar gurin…………. ……

BASEERATA ITACE ARZIKINA😍

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948
AKAN PRE_WEEDING PICTURE’S FREE BOOK

RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MALAM, AMMIEYN KHAUSAR… HEEDAH HYDAR OSTHMAN…. TAURARUWAR ROYAL STAR WRITER’S

🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪 UP-UP-UP

🍂”ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU”🍂

GAJEREN LABARI

🅿️79&80

Bayar da ta iya tamiƙe tashirya ta tafi Abunta,

Yaune ranar ɗauren Aurensu Agidan nata Ake wunin bikin wasu wasu ƴanmatan kawai, Saifaman girka Abinci suke Aɗaura wannan Asauke Asaka wancan sam baida labarin shagalin Agidasa Ake, ita kanta batasani ba saida taga su Naxla da kayan girki da ƙawayensu Asannan suke gayamata gidanta zasu zauna, dik Adirare take dan Ayanzu talura Sahir yatsane Naxala fiye da da dama can bawani burge juna suke ba balantana yanzu..

2:30 daidai yadawo gidan dan nemawa kansa Abunda zaici yunwa yakeji dama bayacin Abuncin kasuwa yafison yaɗaura koda indomie ce yaci ko biscuits da lemu,

Tindaga waje yakejin ƙarar ƙiɗa natashi Agidansa da hayaniya Sun maida gidansa kamar Cluve,

Ransa yaɓaci danshi baima kawo bikine suke ba, Shigi yayi dama gate ɗin buɗe yake Yashiga ciki, Fuska ɗaure Yashiga palourn ga ƴanmatanan dik bawani ɗinkin Arziki jikinsu, yama kasa Ansa gaisuwar tasu direct ɗakinsa yanufa Abun mamaki wai ganin Naxla kwance take Yayi kan gadonsa daga ita sai Under kawai tajashi saman ƙirji hakan baihana bayyanar shatin kan nipple dinta ba,

Da sauri yaɗauke idanuwansa natsuwarsa na menan kwacemasa, Cikin ƙaraɗi yafara kiran Surayya! Surayya!! Surayya!!!…

Da sauri tazo ɗakin da gudu dan tana kitching tana aiki jikinta harwani ɓari yake, taƙaraso “gani”

Sam bata lura da Naxla dake kwance Ko Ajikinta tawani lafe kamar bacci take..

“Wannan wane irin iskanci ne Surayya? banida ƙimane A idanuwanki shine zaki barwannan Abar har ɗakina kuma kan gadona!,”

Sai A sannan taga naxla wani tana faman Bacci Abinta, ita kanta Abun yabata haushi Hannu takai taɗan ɗanamata duka daƙarfi “kitashi naxla meye haka? kinsan kayan da kejikinki kuwa? kumafa ɗakin mijina kefa ba matarsa bace dan Allah kitashi!,”

Tana wani miƙa tana ƙara banƙaro gaban tamiƙe zaune tana murza ido “Au to mene ne dan nazo nan? dan munzo gidanki zakimuna gori saboda wannan mijin dama baidamu dakeba ko hannunki yakasa taɓawa shine zakiyi kishi Akanshi? to bari mubar miki gidan naki yanzu,”

Surayya dai kasa magana tayi dan tsorace take ,

Sahir tini yabar Gidan gaba ɗaya…..

Barin gidan sukayi suma banda dariyar shaƙiyanci ba’abinda naxla takeyi itada ƙawayenta dake zaune A palourn gidansu,

Rafsy Tace,”wataƙil daya dawo saki Uku ras zai aikamata,”

Fashewa da dariya sukayi,

Naxla Tace,” Ayanzu kuwa nida Habib Auren ne zai ɗauru,”

Rafsy “Sosai kuwa ba fashi,”

Aɓangaren Sahir kuwa ransa yakai maƙura gashi mai wannan number nayawan matsanta masa da photuna iri iri ga messarge marasa daɗi,

Ɗaukan wayarsa yayi yakira layin Amma kashe kullum hakan take da Anturo masa text Sai Yaneme layi Amma kashe idan ma yayi magana A whatsApp ɗin ba’a masa refly, Text yaturama Surayya kamar haka,.

KADA KIBARI NADAWO NAGA WANNAN MUNAFUKAR FUSKAR TAKI NATSANE KI WLLH KIJE GIDANKU SAINA NEMIKI INKUWA KINSAMI FASIƘI KAMAR DAI KE TO KUYI AURANKU NABAR MASA KE

Yana turamata yakashe wayarsa yanemi ticket yabar garin gaba ɗaya, dan baison Abbansa ko nata yakirashi yaji dalilin Abunda yayi Kuma yanajin son matarsa Amma gsaskiya bazai iya zama da itaba….

Ganin text ɗin baƙaramun tashin hankali tashiga ba yau kukanma kasa zuwama ta yayi,

Ummansa Ce taje gidan tanason ganinsa Tayi kiransa bata samuba kuma taji labarin bajituwa tsakaninsu shine tazo sulhu, Anan tasameta cikin wani hali, ganin dasa wayar gaba tana hawaye kawai yasa taɗauke wayar taduba, ita kanta taji mamakin ganin text ɗin wai daga sahir ne, kiransa tafara Amma swich-off Ahaka suka ɗunguma zuwa gidna su Surayya Abba kam yace bakomai Allah yasa hakan shine Alkhairi, Abba Daddy da Umma sundage da dole sai sahir yazo Anji tabakinsa kuma sunbada haƙuri sosai ga iyayen nata,

Jin labarin baƙaramin daɗi naxla taji ba harda taka rawa, tana cikin wannan saiga Mahaifinta yashigo Aɗan fusace yana faɗa ,”Ni za’a maida mutumin banza kai wannan yarinyar bamu sa’a ba haihuwarki wllh,”

“Wai Alaji lafiya kadafa kama ƴarmu baki idan kai bakasonta ni inason Abuta ehe,”

“Eh hakane saboda kinɓata yarinyar ba, to bari nagaya muku AKAN PRE_WEEDING PICTURE’S Ɗin Mijinta yamata sakin walaƙanci saki Uku bayan Anɗauran Nasu……………

BASEERATA ITACE ARZIKINA😍

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948

AKAN PRE_WEEDING PICTURE’S FREE BOOK

RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MALAM, AMMIEYN KHAUSAR… HEEDAH HYDAR OSTHMAN…. TAURARUWAR ROYAL STAR WRITER’S

🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪 UP-UP-UP

🍂”ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU”🍂

GAJEREN LABARI

🅿️85&90

 _Wannan page ɗin sadaukar wane gareka Muhammad <MAIDUGURI> (MAIYALO DA DADDAWA😜) Naji daɗin goyon bayanka da yabawarka Akan wannan littafin nawa maitaken AKAN PRE_WEEDING PICTUR'S INAYINKA ADIK INDA NAKE KUMA KAKE ALLAH YAƘARA KAUDA MUGUN IDO KANKA NAWAN M.D💃💃💃💃_

INASANE DAKU MASU KUSHE DA ZAGI SAIDAI ZAGINKU BA ABUNDA ZAIMUN KUMA BAZAI HANANI ƘARASA WANNAN LITTAFIN BA IDAN KINJI HAUSHI TO KIDAINA PRE_WEEDING PICTURE'S BA KYAU KAWAI LALACEWAR ZAMANI NE DA HUƊUBAR SHEƊAR HAƊIDA ƘARSHEN ZAMANI FATANA MUJI TSORON ALLAH MUGYARA KABARURRUKANMU TINKAN MUSHIGESU TINATARWACE KAWAI DAGA MUJAHEEDAH MATAR MLM.. AMMIEYN KHAUSAR DAMA MUHAMMAD <MAIDUGURI> AKODA YAUSHE MUNA FATAN AL'UMMARMU TAZAMA TSALKAKKIYA NAGODE ALLAH YASA MUDACE KUMA ALLAH YASA MU AMFANA

A KWAI YUWAR NADAINA TYPING GABA ƊAYA IN ALLAH YAƘADDARA FARUWAR HAKAN

Aɗan razane Naxla tamiƙe “Whats? Daddy kasan me kake faɗa kuwa? Alhaji habib ɗin ne zaimun irin wannan sakin na walaƙanci kuma Abainar jama’a kotarewa banyi ba yamun saki Uku,? kai haba ina!! inagadai bakaji da kyau ba ko banice hakan tafaru da itaba gaskiya,”

Haushi ne yasa Daddy baiƙara magana ba Yakunna t.v ɗin nakin yana faɗin “saiku kalla nan kuga”

Aikuwa har Anwatsa kan medi’a dama masu vide’o sunzo wurin da ƴanjarida sun fara aikinsu kasancewar Alhaji Habib babban mutum ne mai ƙuɗi kuma ɗan siyasa,

Angama komai har Anɗaura Auren naxla da habib Akan sadaki million 3 ras, Saiga kira yashigo wayarsa, Yaɗaga yanata faman washe baki Dan Aganinsa yayi babban kamun tagaban Office, 

“Kasan waka Aura kuwa Habibu? to kashiga medi’a kagani,”

Kit Aka katse kiran, da kallo yabi wayar dan tintasowarsa baitaɓa jin Mahaifiyarsa takira sunansa ba amma yau gashi takira kuma yanayin muryarta dakwai damuwa, danha cikin sauri yahau medi’a..

Aikuwa take yafara cin karo da hotunan naxla haɗida vide’o birjik wai pre_weeding pictures Abun bashawa dik jikinta waje hutunan gashi maza saimata comments da laking Ake itakuwa saiƙara barbaza photunanta take,

Ransane yayi mugun ɓaci baisan hakan take da rawar kaiba da wallh baiyi wannan ganganjin ba, Miƙewa tsaye yayi cikin fusata Yafurta,” Ni Alhaji habib Mainera nasaki matata wadda kuka ɗaura Auran yanzu wato naxla nasaketa Saki ɗaya! biyu!! Uku!!! ras ba gyara kuma dalilin wannan sakin shine AKAN PRE_WEEDING PUCTURE’S.,”

Yana gama faɗin hakan yabar wurin cikin takaici da tsanar dik wata mai ɗora pic A medi’a da biyewa shairin shaiɗan gun wannan la’anan nan Abun wai PRE_WEEDING PICTURE’S…..

Daddy kam kasa Aikata komai yayi yabar wurin cikin ƙunar zuci, Aiko ƴanjarida tin nan suka sami kanun labarai yazamana ko ina shi Ake hasakawa da photunan ta na PRE_WEEDING PICTURES

Zama tayi ƙasa dirshan wata zufa na mata tsiyaya bata taɓa tunanin zata samu mummunan sakamako irin wannan ba, nafarko tanason Habib gashi yanzu ya haramta gareta na biyu gashi nata Hutunan sune suka Zaga duniya shikenan tabar mugun record ba wanda zai Aureta na uku taɓata sunan iyayenta,

“nashiga uku ni naxla wannan wace irin ƙaddarace mai nauyi haka,”?

Dariyar takaici Daddy Yayi Kafin Yace,"Da saura yanzu baki shiga ukun ba dan ina tabbatar mikihar 100 saiki shiga bawai 3 ba tinda kika biye shiɗan ke wayayya ba wai *PRE_WEEDING PICTURES* To gashi Auren ki yatarwatse kuma kinrasa miji kenan saidai kita zama haka, ke kam kinga illarsa yau kuma harda ƙawarki naji Ance Ansaketa itama Dik *AKAN PRE_WEEDING PICTURE'S*..........

Yana gama faɗin hakan yabar ɗakin, Abokan natama watsewa sukayi kowacce tawuce tana dariya haɗida faɗin Alaƙara suna ƙara bada labaran …

Surayya na hanga zaune saifaman share hawaye take tana nadamar yin ƙawance da Naxla dan da baisameta gidansa Aɗakinsa hakan ba da bazai saketa ba,

Ameera ce dake da tsohon cikinta take lallashinta…

Shigowa Abba yayi Palourn da sallama yaɗan kallesu, Tabashi tausayi Amma hakan baihana yafaɗa mata gaskiya ba,

Zama yayi kusa dasu yana fuskantarsu haɗida kunna t.v ɗin Yace,” Kinga Abunda yafaru da sheɗaniyar ƙawar taki,”

dik kansu suka kalle t.v Sosai Surayya tatsorata da lamarin duniya nadamar biyewa zuciya da naxla take nazuwa PRE_WEEDING PICTURE’S Sosai Abba yamata faɗada nisaha haɗida nuna mata illar wannan shegen photunan……….

BASEERATA ITACE ARZIKINA😍

WhatsApp number 07064904617 or call 07031012948

Abba yayi gyaran murya sannn Yace “Sahir kafa ɗamuna dalilin sakin matarka,”

“Abba katanbayeta kaji,” yana sunkuyar da kansa yayi maganar…

“Dungure masa kai Umma tayi “Saboda muna Abokan wasanka Aidole katsaya ɓatamuna lokaci na mutanbayeta, Munganta mukace kuma ai kaine babba koba Aure dan haka ko kafaɗa muna wllh ko naɓata ranka sahir dama inafushi dakai bawai na sauka bane,” taƙare maganar cikin hasala..

Malam Yace,”A’a kada Ayi haka ita tafaɗa muna meye sila,”

Surayya dake matso hawaye Tace,” Wllh Abba bansani ba banmasa komai ba harma yafita ne kawai yaturomun wannan text ɗin wllh bansan komai ba Abba,” taƙarasa maganar tana ɗan matsawa baya,..

“Sahir kayi magana kona saɓa maka wllh,” cewar Mahaifinsa cikin fushi……

Tabbas yalura iyayen nasa sunɗau zafi dan haka yafara bada haƙuri,” Abba kuyi haƙuri wllh inason Matata yanzuma namaidata ɗakinta dan Allah kada kuyi fushi dani dama dan kawai tayi….,”

Saikuma yayi shuru yakasa ida faɗa…

   Muba Yace," Bafa ranar ɓoye ɓoye bace wannan Sahir kafaɗe gaskiya kawai,"

Shuru yayi na ƴanwasu mintuna kafin yafara bada labarin sanda Akaturo masa text da zuwansa ɗaurin Auren dama haryanzu Anan yawan matsanta masa da text kuma idan yakira bata shiga,, Amma wllh inasonta nakasa faɗin wannan ne saboda banason Sunanta yaɓaci idan narabu da ita haka saƙat zata iya Auren wani record ɗinta baiɓaci ba, amma wllh inasonta Abba kumun Afuwa dan Allah,” Yaƙarasa zancen yana nuna nadamar Hukuncin da yaɗauka….

 "Nuna muna photon" Mlm Yace mahaifin Surayya....

Badon yasoba yabada wayarsa take Photunan surayya guda 3 suka bayyana kowanne ɗinkin yaɗameta kuma gawani saurayin kusa da ita suna murmushi wajunansu.
Haka kowa na ɗakin ya kalle pic ɗin, Mlm
Harzuwa kanta Hannunta narawa taduba Hawaye kezuba daga idanuwata tana girgiza kai Sam takasa magana dan batasan mezatace su yarda da ita ba..

Ajiyar Zuciya Mlm Yasauke “Wannan ko bantanbaya ba Nasan kunsan waɗannan photuna na PRE_WEEDING PICTURE’S ɗinsu ne,”

” to amma ina tahaɗu da wannan”
Cewar Ameera dake zubda hawaye…

“Inako tahaɗu da shi inaba gun photunan ba, Sahir kamun daidai kuma Ayanzu nakeson kamata saki 3 taharamta gareta tazauna taɗan ɗane Abunda tashuka ba tazaɓe yin pre_weeding pics ba to itama inason Amata saki 3 Kamar yarda yafaru da ƙawarta ita kanta taɗan ɗana AKAN PRE_WEEDING PICTURE’S ɗin,”

Dasauri Saurin Yace,”A’a kada Ayi haka malam wllh batasan najikin photon ba kawai Azal tafaɗa matane kuma hakan tasameta ne AKAN PRE_WEEDING PICTURE’S,”..…………………………………………………………………

 _BASEERATA ITACE ARZIKINA😍_

WhatsApp number 07064904617 or 07031012948

AKAN PRE_WEEDING PICTURE’S FREE BOOK

RUBUTA LABARI DA TSARAWA MUJAHEEDAH MATAR MALAM, AMMIEYN KHAUSAR… HEEDAH HYDAR OSTHMAN…. TAURARUWAR ROYAL STAR WRITER’S

🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟
{R.S.W.A}

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

MARUBUTA MASU AIKI DA FASAHA DA ZALLAR TSAKWARON AMANA, FAƊAKARWA HAƊI DA NISHAƊANTARWA GAMI DA WA'AZANTARWA HUMMM WANI ABU SAI ROYAL STAR WRITER'S ✍🏻📚✨⭐✨ ASSOCIATION RUWA ƘAƊAI KE MAGANIN ƘISHI (R..S..W..A) 💪💪💪💪 UP-UP-UP

🍂”ALƘALAMINMU🖋️ ƳANCINMU”🍂

GAJEREN LABARI

🅿️99&100

FINAL!
FINAL!!
FINAL!!!

FINAL PAGE INSHA ALLAH....

FRIDAY 17/6/2022

  _Ina godiya ga Allah dayaban ikon kammala wannan littafin nawa mautaken *AKAN PRE_WEEDING PICTURE'S* Wanda nasamu fans Akansa kuma nasami maƙiya dama wanda ke ƙoƙarin kawo gyara Acikin Al'umma Akan wani Aiki maikyau wanda yakasance gaskiya ne to dole ya fuskance ƙalubalai da dama, dan haka najajirce harnaga nakammala littafin dik da saƙwannin ɓatancin ku inasamu Amma bakomai ni dan Allah nake typing ɗina kuma da Aɗau darasi inafatan muɗauke maikyau mara kyau kuma muwatsar Allh yakaremu da imaninmu_

AKWAI YUWAR WANNAN YAZAMA LITTAFINA NA ƘARSHE SAI WASU BAYAN SHEKARU NACIGABA INNA SAMI DAMAR HAKAN AMMA INKO BANSAMU BA TO SHIKENAN.. INAROƘON DIK WANDA NATAƁA ƁATAMA SILAR RUBUTUNA DAN ALLH YAMUN AFUWA YAYAFEMUN ALLAH YAƘARA SADAMU DA ALKHAIRI…

“Ni sunana Sani kuma ina aiki Agidan photon da sukaje, Wata ƙawarta danaga Anfasa Auranta yanzu itace tasani Aikin tabani kuɗi masu yawa Akan na aikata wannan aikin, Ana gobe zasuzo photon naxla tazo taban dubu 10,000 Akan namata aikin idan kunzo photuna na saka wani namiji cikin photon naɗauka batare da ke ko saurayin da zaki Aura yagano ba, da farko naƙi yarda Amma ganin yawan ƙuɗin kuma nasan koban Ansaba wani zai Ansa kawai saina Amince, bayan sunzo Anamusu pic ɗin ne sai Aka kirashi bayan yafita kafin yazo natura wanda muka haɗa plan ɗin dashi danufin yazo bata style ne sai yayi Abunda yasata dariya daga nan nayi Amfani da damar nikuwa nadinga ɗaukar photunan batare datasani ba, bayan tawuce na wanko kamar 50 nabata Amma wllh bansan komai game da itaba, dan Allah kuyafemun wllh shairin shaiɗan ne,”
Yaƙarasa maganar yana kuka……

“Ga kanan babban sheɗan! Ai kaine shaiɗan nin mugu wllh ka kassara rayuwata da Ace ta Aure wani narasata ne wllh dasai nakasheka Azzalumi kawai,” Yamiƙe haryana shaƙo wuyansa dan yaji zafin lamarin sosai..

Da ƙyar Akasamu ya sakeshi yakoma yazauna yana huci, Shikuwa dik ya tsorata ne..

Naxla da tajima da shigowa taji komai dama tazone dan tafaɗe iya nata laifin kuma taba da haƙuri saita same sani yazo yafaɗa Ashe..

Ƙarasow ciki tayi Cikin tazauna kusa da Surayya takama hannunta Tace,” dan Allah kiyafemun wllh naga sakayya tinkan Aje ko ina, kuma wllh ba laifina bane nima Tsohon saurayinki T.j tijjani shiyasani dan yahuce haushin fasa Aurensa dakikayi, kuma dika hakan tasamu ne AKAN PRE_WEEDING PICTURES’ Domun dabakije yinsaba wllh hakan bazata faru dake ba,”

Jinjina kai Malam yayi “To Alhamdullah tinda komai yazama haka saiku yafe juna domun idan kunduba dika hakan tasamu ne saboda wannan banzar Al’adar wai PRE_WEEDING PICTURE’S,”…..

“Hakane Abba Amma dan Allah Kayi haƙuri, kawai tatashi mukoma yanzu,” cewar Sahir cikin magiya yaƙarasa maganar

 "Ban hana takoma ba kuma zata koma Amma kusani Aure bawasan yara bane da za'a tara kaya da Angama wasan Akwashe Idan za'aci gaba kuma Adawo Asake zubawa, Aure na nufin ibadar Allah badan jindaɗi kawai, Sannan mundawo kan wannan banzar Al'adar wai *Pre_weeding picture's* tinwuri mutsarda wannan sha'awar ta wannan photunan domun ba Al'adarmu bace mu musulmai Wannan Al'adar ya hudawa ce da nasara sune keneman ɓata muna zuri'a daneman halakar damu kamar yarda suka ɓata muma mubisu muɓata wllh wannan *PRE_WEEDING PICTURE'S* ɗin haramu ne ba Al'adar musulmai bace ta kafurai ce Arna sune Akasani da dik wannan miyagun ɗabi'un Amma Abun takaici da baƙin ciki waishine ƴaƴanmu musulmai suke, to kunɗaukar harkar Arna taya zakuga daidai? Aiko kullum cikin ganin matsaloli muke wllh, Samun salamarmu ɗaya muwatsarda wannan ɗabi'ar,,,.. Sannan nadawo gareki, kece uwarta yakamata Amatsayinki na uwa Ace kinsan Abunda ƴarki ko ɗanki ke Aikatawa, kada kisaka ido kibarshi yayi kotayi dik Abunda taga dama ko kaga dama, kuma kada kibarshi yazura kansa cikin wannan muguwar Al'adar wai *pre_weeding picture's* ɗin So maganata taƙarshe Allah yasa mudace kuma Allh yabaku zaman lafiya,"

Da Ameen suka Ansa,

Abba Yace,”Kuma kaima kadaina yanke hukunci cikin fushi koda yaushe kazama maiyawan Uzuri kuma kaima kaji tsoron Allah yanzu dai basai munbaku shawarar daina pre-weeding pic ba saboda da idanuwanku kuma dukanku kunga Darasi AKAN PRE_WEEDING PICTURE’S ita Anfasa Auranta kuma sunanta yaɓaci ke kuwa Anrabaki da mijinki sannan kaima dakayi kashiga damuwa dik AKAN PRE_WEEDING PICTURE’S Ɗin,”….

©©©©©©©©££££©££©©©©©©©©©©©©©€®®®®®®®®®®¥¥¥¥

BAYAN WASU SHEKARU

Komai Yasauya Ayanzu Ameera nada yara 3 inda Surayya keda 2 soyayya suke sosai kowacce da mijinta saidai tayakice Naxla Arayuwarta, naxla kam yawan samun suka da chara yasa tahaɗiye zuciyar ta take tamutu,, sosai mutuwar ta tsayawa Surayya Yanzu haka tana zaune A palourn ta tana zubda hawaye,

Shigowarsa kenan yadawo daga office yaransu kuwa suna wurin Umma tana fama dasu, ganinta hakan baƙaramin ɗaga masa hankalin yayi ba, ƙarasowa yayi kusa da ita yazauna daf da ita Yace,” My baby na meke damunki? faɗamun,”

Cikin sheshsheka Tace,”waifa Naxla tamutu kena bazata sake dawowa yanzu shikena daɗa,” tasake rushewa da kuka tayi….

“Comon my baby, kimata Addu’a Allah yagafarta mata bazata so wannan kukan ba kidaina nima banasonshi, Yanzu kitashi muje musake ɗaukar PRE_WEEDING PICTURE’S ko,”?

Yaƙare maganar yana ɗaga mata gira ɗaya.

Turesatayi daga jikinta tana faɗin ,”AKAN PRE_WEEDING PICTURE’S Ai nayi hankali kuma naɗauke darasi wllh,”

Yana dariya Yarungumota jikinsa Yana kissing ɗinta Haɗida Faɗin Nikaina naɗau darasi AKAN PRE_WEEDING PICTURE’S Insha Allah Mundaina wasunma dazasu ɗauke shawararmu dama Darasinda MUJAHEEDAH MATAR MALAM AMMYN KHAUSAR HEEDAH HYDAR OSTHMAN TAURARUWAR ROYAL tako yamuna Allah yasa muɗauka kuma ya Amfanemu, Ameen………………………

NIKANA NACE AMEEN..………………………

TAMMAT BIHAMDULLAH

📝📚 Allah kabamu ikon ɗaukar darasin da keciki maikyau mara kyau kuma muwatsar.,, (Wannan littafin na koyarda damu kuma yana tinatar damu Akan Al’adun banza na yahudawa damuka ɗauka muka ɗaurawa kanmu mu musulmai, Asalin waɗan nan photunan daga Arna ne sune Akasani dasu Amma Abun baƙinciki da takaici shine wai mu musulamai yaran musulmai muke wasu iyayensu nasane sunbarsu to kusani PRE_WEEDING PICTURE’S Haramun ne wllh haramun ne sunsaɓawa shari’a da doka musamman garemu musulmai, kusani Annabi Muhammad S.A.W Yace<>> ()DIK WATA AL’UMMA DAKE KAMANCECE NIYA DA WATA TOKUSANI TANA CIKINSU,,””)))))) Yasalam kenan idan bamu daina ba muma ɗin kamar kafiran muke kuma za’a tadamu cikinsu, wannan ba faɗar Mujaheedah Ammieyn khausar bace faɗar Ma’aikin Allah ne, nikawai nayi ƙoƙarin tinatarwa ne, dama ita tinatarwa Muminai ƙaɗai take Amfana… Kundaiga AKAN PRE_WEEDING PICTURE’S ƊIN IRIN BALA’UKA DA TASHIN HANKALINDA SUKA FAƊA MUSU, inafatan yazama izina ga ƴan baya mudaina wannan muguwar Al’ada…..

“`Waɗanda nataɓa silar wannan littafin dan Allah kumun Afuwa waɗanda nama daidai kuwa ina gdy da comments ɗinku dayawan bibiyata Allh yabar ƙauna niɗince dai Taku Mujaheedah Matar Malam Ammieyn khausar.. Heedah Hydar osthman tauraruwar Royal star writer’s…. Marubuciyar……FAHAT HOT LOVE.. SAINA KASHE MIJINA… BARRISTER KHALEEL… SO SIRRIN ZUCIYA… ZUCIYAR NAMIJI… SILAR ƊA NAMIJI… RAUNIN MACCE BAYA HANA ƊAUKAR FANSA… AKAN PRE_WEEDING PICTURE’S… ALL IS FREE BOOKS……. MAIZAMAN KANTA “PAID BOOK” BAƘIN KISHI “PAI BOOK” DOCTOR HEESHAM “PAID BOOK” ABBAKAR SARAKIEY PAID BOOK” ALL IS PAID BOOKS..…………………………………………………………

INAJINJINA GADIKAN ƳAN ƘUNGIYATA TA ROYAL WRITERS

AKODA YAUSHE DA BASIRARKU NAKE TAKA RAWA MASOYANA

BASEERATA ITACE ARZIKINA😍

WhatsAp number 07064904617 or call 07031012948

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button